[ { "title": "Muhimmin Bayani:", "body": "Sarki Yoram ya ci gaba da yin magana da sarki Yehoshafat." }, { "title": "Ko za ka tafi tare da ni yaƙi gãba da Mowab?'", "body": "Kalmar \"ka\" na nufin Yehoshafat, amma ma nan nufin shi da sojojinsa. Anan \"Mowab\" na nufin \"sojojin Mowab\" AT: \"Kai da sojojinka za ku bini mu yi yaƙi gãba da sojojin Mowab?\" (Duba: figs_synecdoche)" }, { "title": "Zan je", "body": "Yehoshafat yana cewa shi da sojojinsa za su yi yaƙi da sarki Yoram gãba da Mowab. AT: \"za mu tafi da kai\" (Duba: figs_synecdoche)" }, { "title": "Ni ma kamar ka ne, mutanena kuma kamar mutanenka ne, dawakaina kamar dawakanka ne.", "body": "Yehoshafat na gaya wa Yoram ya yi amfani da shi, mutanen sa, da sojojinsa don biyan buƙatunsa. Ya yi wannan maganar kamar su na Yoram ne. Za a iya bayyana cikakkiyar ma'anar wannan bayani. AT: \"Mu na a shirye muyi dukkan abinda ka ke son muyi. Sojojina da dawakaina a shirye suke su taimakeka\" (Duba: figs_explicit)" }, { "title": "'Ta hanyar jejin Idom", "body": "\"shiga ta cikin jejin Idom\"" } ]