ha_ulb/65-3JN.usfm

35 lines
1.9 KiB
Plaintext

\id 3JN
\ide UTF-8
\h 3 Yahaya
\toc1 3 Yahaya
\toc2 3 Yahaya
\toc3 3jn
\mt 3 Yahaya
\s5
\c 1
\p
\v 1 Daga dattijon zuwa ga Gayus, wanda nake kauna da gaske.
\v 2 Ya kaunatace na, ina addu'a domin ka samu albarka cikin kowanne al'amari, da kuma koshin lafiya, kamar yadda ruhun ka yake lafiya.
\v 3 Na yi farin ciki kwarai sa'adda wadansu 'yan'uwa suka zo suka ba da shaida a kan bangaskiyar ka, kamar yadda ka ke bin gaskiya.
\v 4 Ba abin da ya fi faranta mani rai kamar in ji yayana suna tafiya cikin gaskiya.
\s5
\v 5 Ya kaunatace na, kana aiki da aminci zuwa ga 'yan'uwa da baki,
\v 6 wadanda suka shaida kaunar ka a gaban ikilisiya. Zai yi kyau ka yi masu taimako da kyakkyawar salama, ta hanyar da ta dace da masu ibada,
\v 7 domin sabili da sunan nan ne suka fito, ba su kuma karbar kome a hannun al'ummai.
\v 8 Don haka ya kamata mu karbi irin wadannan mutane, domin mu zama abokan aiki tare da su a kan gaskiya.
\s5
\v 9 Na rubuta wasika zuwa ga ikilisiya, amma Diyotariffis, wanda ya fi kowa son girma a cikinsu, bai karbe mu ba.
\v 10 Saboda haka, idan na zo, zan tuna masa da irin ayukkan sa, da kuma yadda yake babbata sunayen mu a wurin jama'a da miyagun kalmomi. Wannan ma bai ishe shi ba, har ma yana kin karbar 'yan'uwa. Ya kuma hana wadanda suke son su yin hakan, harma ya kan kore su daga ikilisiya.
\s5
\v 11 Ya kaunatace na, kada ka yi koyi da mugun abu, sai dai abu mai kyau. Dukan wanda yake yin abu mai kyau na Allah ne; mai aikata mugunta kuma bai san Allah ba.
\v 12 Dimitiriyas yana da kyakkyawar shaida a gun kowa har a wurin gaskiyar da kanta. Mu ma mun shaida shi, ka kuma san shaidar mu gaskiya ce.
\s5
\v 13 Ina da abubuwa dayawa da zan rubuta maka, amma ban so in rubuta maka su da alkalami da tawada ba.
\v 14 Ina sa zuciya mu sadu ba da dadewa ba, sa'annan mu yi magana ido da ido.
\v 15 Bari salama ta kasance tare da kai. Abokanmu suna gaishe ka, kuma ka isadda sakon gaisuwar mu ga sauran abokai da sunayen su.