ha_ulb/64-2JN.usfm

33 lines
1.8 KiB
Plaintext

\id 2JN
\ide UTF-8
\h 2 Yahaya
\toc1 2 Yahaya
\toc2 2 Yahaya
\toc3 2jn
\mt 2 Yahaya
\s5
\c 1
\p
\v 1 Daga dattijon zuwa ga uwar gida zababbiya da yayanta, wadanda nake kauna da gaskiya, ba ni kadai ba, amma da dukan wadanda sun san gaskiya -
\v 2 domin gaskiya da take cikinmu za ta kuma kasance tare da mu har abada.
\v 3 Alheri da jinkai da salama za su kasance tare da mu, daga Allah Uba da kuma daga Yesu Almasihu Dan Uba, a cikin gaskiya da kauna.
\s5
\v 4 Na yi murna sosai sa'anda na sami wadansu yayanki suna tafiya cikin gaskiya, kamar yadda muka karbi wannan umarni daga Uba.
\v 5 Yanzu ina rokon ki, uwar gida, ba kamar ina rubuta maki sabon umarni ba, amma wannan da muka samu tun da can, cewa mu kaunaci junanmu.
\v 6 Wannan kuma itace kauna, cewa mu yi tafiya bisa ga umarnin sa. Wannan shine umarnin, daidai kamar yadda kuka ji da fari, da cewa ku yi tafiya a cikinsa.
\s5
\v 7 Gama masu yaudara sun fito a duniya, wadanda ba su yarda cewa Yesu ya zo cikin jiki ba. Wannan ne mayaudari da kuma magabcin Almasihu.
\v 8 Ku dubi kanku, domin kada ku rasa abubuwan da mu duka muka yi aiki a kansu, amma domin ku karba dukan sakamon ku.
\s5
\v 9 Duk wanda ya ci gaba da tafiya ba cikin koyarwa Almasihu ba, ba shi da Allah. Wanda ya zauna cikin koyarwar kwa yana tare da Uban da kuma Dan.
\v 10 Duk wanda ya zo wurinku, ba tare da wannan koyarwar ba, kar ku karbe shi cikin gidanku, kada ma ku gaishe shi.
\v 11 Domin duk wanda ya gaishe shi ya yi tarayya da shi kenan cikin miyagun ayyukan sa.
\s5
\v 12 Ina da abubuwa dayawa da nake so in rubuta maki amma al'kalami tawada da takarda baza su iya daukar su duka ba. Amma duk da haka ina begen zuwa gare ki domin mu yi magana fuska da fuska, domin farin cikn mu ya zama cikakke.
\v 13 Yayan yar'uwarki zababbiya suna gaishe ki.