51 lines
2.7 KiB
Plaintext
51 lines
2.7 KiB
Plaintext
\id PHM
|
|
\ide UTF-8
|
|
\h Filimon
|
|
\toc1 Filimon
|
|
\toc2 Filimon
|
|
\toc3 phm
|
|
\mt Filimon
|
|
|
|
\s5
|
|
\c 1
|
|
\p
|
|
\v 1 Bulus, daurarren Yesu Almasihu, da kuma dan'uwa Timotawus zuwa ga Filimon, kaunataccen abokinmu da kuma abokin aikin mu,
|
|
\v 2 da Afiya yar'uwanmu da Arkifus abokin aikin mu a filin daga, da kuma Ikilisiyar da take taruwa a gidan ka:
|
|
\v 3 Alheri da salama su kasance gare ka daga wurin Allah Ubanmu, da Ubangiji Yesu Almasihu.
|
|
|
|
\s5
|
|
\v 4 Kowane lokaci ina gode wa Allah. Ina ambaton ku cikin addu'oi na.
|
|
\v 5 Na ji labarin kauna da bangaskiya da ka ke da ita a cikin Ubangiji Yesu da dukkan yan'uwa masu bi.
|
|
\v 6 Ina addu'a zumuntar bangaskiyarka ta inganta ga kawo sanin kowane kyakkyawan abu dake cikin mu a cikin Almasihu.
|
|
\v 7 Na yi farinciki kwarai, na kuma ta'azantu saboda kaunarka, saboda zukatan masu bi sun kwanta ta wurin ka, dan'uwa.
|
|
|
|
\s5
|
|
\v 8 Saboda haka, ko da ya ke ina da gabagadi a cikin Almasihu domin in ba ka umarni ka yi abinda ya kamata ka yi,
|
|
\v 9 duk da haka sabo da kauna, na fi so in roke ka- Ni, Bulus, dattijo, a yanzu kuma ga ni dan kurkuku domin Almasihu Yesu.
|
|
|
|
\s5
|
|
\v 10 Ina rokon ka saboda da na Onisimus, wanda na zama uba a gare shi sa'adda nake cikin sarkokina.
|
|
\v 11 Domin a da kam, ba shi da amfani a wurin ka, amma yanzu yana da amfani a gare ka da kuma a gare ni.
|
|
\v 12 Na kuma aike shi wurinka, shi wanda ya ke a cikin zuciyata kwarai.
|
|
\v 13 Na so da na rike shi a wuri na, domin ya rika yi mini hidima a madadin ka, a lokacin da ni ke cikin sarkoki saboda bishara.
|
|
|
|
\s5
|
|
\v 14 Amma ba na so in yi wani abu ba tare da sanin ka ba. Ba ni so nagarin aikinka ya zama na dole amma daga kyakkyawar nufi.
|
|
\v 15 Watakila dalilin da yasa ya rabu da kai na dan lokaci ke nan, domin ka karbe shi kuma har abada.
|
|
\v 16 Daga yanzu ba za ya zama bawa ba kuma, amma fiye da bawa, wato kaunataccen dan'uwa. Shi kaunatacce ne musamman a gare ni, har fiye da haka ma a gare ka, a cikin jiki da kuma cikin Ubangiji.
|
|
|
|
\s5
|
|
\v 17 Idan ka maishe ni abokin hidima, ka karbe shi kamar yadda za ka karbe ni.
|
|
\v 18 Idan kuwa ya yi maka abinda ba daidai ba ko kuwa kana bin sa wani abu, ka dauka yana wurina.
|
|
\v 19 Ni, Bulus, na rubuta wannan da hannuna: zan biya ka. Ba kuwa cewa sai na gaya maka cewa ina bin ka bashin kanka ba.
|
|
\v 20 I, dan'uwa, ka yi mani alheri cikin Ubangiji; ka ba zuciyata hutu a cikin Almasihu.
|
|
|
|
\s5
|
|
\v 21 Saboda Ina da tabbaci game da biyayyarka, na rubuta maka. Na san za ka yi fiye da abinda na roka.
|
|
\v 22 Harwayau, ka shirya mani masauki. Domin ina fata ta wurin adu'oinku, nan ba da dadewa ba za a maida ni wurin ku.
|
|
|
|
\s5
|
|
\v 23 Efafaras, abokina cikin Almasihu Yesu a kurkuku yana gaishe ka,
|
|
\v 24 haka ma Markus da Aristarkus, da Dimas, da Luka abokan aikina.
|
|
\v 25 Bari Alherin Ubangiji Yesu Almasihu ya kasance da Ruhunka. Amin.
|