ha_ulb/44-JHN.usfm

1653 lines
98 KiB
Plaintext

\id JHN
\ide UTF-8
\h Yahaya
\toc1 Yahaya
\toc2 Yahaya
\toc3 jhn
\mt Yahaya
\s5
\c 1
\p
\v 1 A cikin farko akwai Kalma, Kalmar kuma tana tare da Allah, wannan Kalma kuwa Allah ne.
\v 2 Shi kuwa tare da Allah yake tun farko.
\v 3 Dukan abu ta wurinsa aka yi su, babu abin da aka halitta sai ta wurin sa.
\s5
\v 4 A cikinsa rai ya ke, kuma wannan rai ya zama haske ga dukan mutane.
\v 5 Hasken ya haskaka a cikin duhu, kuma duhun bai rinjaye shi ba.
\s5
\v 6 Akwai wani mutum wanda Allah ya aiko, mai suna Yahaya.
\v 7 Ya zo a matsayin mai ba da shaida game da hasken, domin kowa ya ba da gaskiya ta wurinsa.
\v 8 Ba Yahaya ne hasken ba, amma ya zo ne domin ya shaida hasken.
\s5
\v 9 Wannan shine haske na gaskiya mai ba da haske ga dukan mutane, da ke zuwa cikin duniya.
\s5
\v 10 Yana cikin duniya, kuma an halicci duniya ta wurinsa, amma duniya bata san shi ba.
\v 11 Ya zo wurin nasa, amma nasa basu karbe shi ba.
\s5
\v 12 Amma duk iyakar wadanda suka karbe shi, suka kuma ba da gaskiya ga sunansa, ya ba su 'yanci su zama 'ya'yan Allah.
\v 13 Wadanda aka haife su ba ta wurin jini ba, ko ta wurin nufin jiki, ko nufin mutum, amma ta wurin Allah.
\s5
\v 14 Kalmar kuma ya zama jiki ya zauna cikin mu. Mun ga daukakarsa, daukaka irin ta makadaici shi kadai wanda ya zo daga Uban, cike da alheri da gaskiya.
\v 15 Yahaya ya yi shaida akansa yana kira da karfi, cewa, "Wannan shine wanda na yi magana a kansa cewa, 'Shi wanda ke zuwa bayana, ya fi ni, domin ya kasance kafin ni.'"
\s5
\v 16 Domin daga cikarsa ne muka karbi alheri akan alheri.
\v 17 Gama shari'a ta zo daga wurin Musa. Alheri da gaskiya sun zo ta wurin Yesu Almasihu.
\v 18 Babu lokacin da wani ya taba ganin Allah, shi wanda shi kadai ne Allah, wanda ke jingine da kirjin Uba, shi ya bayyana shi.
\s5
\v 19 Wannan ita ce shaidar Yahaya sa'adda Yahudawa suka aika da Firistoci da Lawiyawa zuwa gareshi don su tambaye shi, "Wanene kai?"
\v 20 Ya fada dalla dalla, kuma bai musunta ba, yana amsa masu cewa, "ba nine Almasihu ba."
\v 21 Sai suka tambaye shi, "To kai wanene? Kai Iliya ne?" Yace, "Ba ni ba ne." Suka ce, "Kai ne anabin?" Ya amsa, "A'a".
\s5
\v 22 Sai suka ce masa, "Kai wanene, domin mu bada amsa ga wadanda suka aiko mu? Me kake fadi game da kanka?"
\v 23 Yace, "Ni murya ne, da ke kira cikin jeji, 'Ku daidaita hanyar Ubangiji,' kamar yadda annabi Ishaya ya fada."
\s5
\v 24 Su wadanda aka aika daga wurin Farisawa suke. Sai suka tambaye shi cewa,
\v 25 "To don me kake baftisma idan kai ba Almasihu bane, ko Iliya, ko annabin?".
\s5
\v 26 Yahaya ya amsa masu, cewa, "Ina baftisma ne da ruwa. Amma a cikinku akwai wani tsaye wanda ba ku sani ba,
\v 27 shi wanda ke zuwa bayana, wanda ko igiyar takalminsa ban isa in kwance ba."
\v 28 Wadannan abubuwa sun faru ne a Baitanya, a dayan ketaren Urdun, a wurin da Yahaya ke Baftisma.
\s5
\v 29 Washegari, Yahaya ya ga Yesu yana zuwa wurinsa ya ce, "Duba, ga Dan Ragon Allah wanda ke dauke zunubin duniya!
\v 30 Wannan shine wanda na fada maku cewa, "Shi wanda ke zuwa bayana ya fi ni, domin ya kasance kafin ni.'
\v 31 Ban san shi ba, amma saboda a bayyana shi ga Isra'ila ne nazo ina baftisma da ruwa."
\s5
\v 32 Yahaya ya shaida, cewa, "Na ga Ruhu yana saukowa kamar kurciya daga sama, ya kuma zauna a kansa.
\v 33 Ban gane shi ba, amma shi wanda ya aiko ni in yi baftisma cikin ruwa ya fada mani cewa, 'duk wanda ka ga Ruhun ya sauka kuma ya zauna a kansa, shine wanda ke yin baftisma cikin Ruhu mai tsarki.'
\v 34 Na gani, na kuma shaida cewa wannan shine Dan Allah."
\s5
\v 35 Kuma, washegari, da Yahaya na tsaye da biyu daga cikin almajiransa,
\v 36 suka ga Yesu na wucewa, sai Yahaya ya ce, "Duba, ga Dan rago na Allah!"
\s5
\v 37 Sai almajiransa biyu suka ji ya fadi haka, suka kuwa bi Yesu.
\v 38 Da Yesu ya waiwaya ya gan su suna bin sa, sai ya ce masu, "Me kuke so?" Suka amsa, "Rabbi (wato 'Mallam'), ina kake da zama?"
\v 39 Yace masu, "Zo ku gani." Sai suka zo suka ga inda yake zama; suka zauna da shi ranan nan, gama wajen sa'a ta goma ne.
\s5
\v 40 Daya daga cikin wadanda suka ji maganar Yahaya suka kuma bi Yesu shine Andarawus, dan'uwan Siman Bitrus.
\v 41 Ya fara neman dan'uwansa Siman yace masa, "Mun sami Almasihu" (wanda ake kira 'Kristi').
\v 42 Ya kawo shi wurin Yesu. Yesu ya dube shi yace, "Kai ne Siman dan Yahaya. Za a kira ka Kefas," (ma'ana, 'Bitrus').
\s5
\v 43 Washegari, da Yesu yana shirin tafiya zuwa Galili, sai ya sami Filibus, ya ce masa, "ka biyo ni."
\v 44 Filibus dan asalin Baitsaida ne, garin Andarawus da Bitrus.
\v 45 Filibus ya sami Natana'ilu yace masa, "Mun same shi, shi wanda Musa ya rubuta shi a cikin attaura, da annabawa: Yesu Dan Yusufu, Ba-Nazarat."
\s5
\v 46 Natana'ilu ya ce masa, "za a iya samun wani abu nagari a Nazarat?" Filibus yace masa, "Zo ka gani."
\v 47 Yesu ya ga Natana'ilu yana zuwa wurinsa sai yayi magana game da shi, "Duba, Ba-Isra'ile na hakika wanda babu yaudara a cikinsa."
\v 48 Natana'ilu yace masa, "Ta yaya ka san ni?" Sai Yesu ya amsa masa yace, "Tun kafin Filibus ya kira ka, sa'adda kake a gindin baure, na gan ka."
\s5
\v 49 Natana'ilu ya amsa, "Rabbi, Kai Dan Allah ne! Kai Sarkin Isra'ila ne!"
\v 50 Yesu ya amsa masa yace, "Don na ce maka, 'Na gan ka a gindin Baure', ka gaskanta? Za ka ga abubuwa da suka fi wannan girma."
\v 51 Sai yace, 'Hakika, hakika ina gaya maka, zaka ga sammai a bude, mala'ikun Allah kuma suna hawa suna sauka akan Dan Mutum."
\s5
\c 2
\p
\v 1 Bayan kwana uku, akwai aure a Kana ta Galili, mahaifiyar Yesu kuma tana wurin.
\v 2 An gayyaci Yesu da almajiransa zuwa auren.
\s5
\v 3 Da ruwan inabin ya kare, maihafiyar Yasu tace masa, "basu da ruwan inabi."
\v 4 Yesu yace mata, "Mace, me yasa kika zo wurina? Lokaci na bai yi ba tukuna".
\v 5 Maihafiyarsa tace wa ma'aikatan, "Ku yi duk abin da yace maku."
\s5
\v 6 To akwai randunan ruwa na dutse guda shidda a wurin wadanda Yahudawa ke amfani da su domin al'adansu na tsarkakewa, kowace zata iya daukar durom guda.
\v 7 Yesu yace masu, "Cika randunan da ruwa". Sai suka cika randunan makil.
\v 8 Sai yace wa ma'aikatan, "Ku diba daga ciki ku kai wa shugaban biki." Sai suka yi hakannan.
\s5
\v 9 Shugaban bikin ya dandana ruwan da ya zama ruwan inabin, amma bai san inda ya fito ba (amma ma'aikatan wadanda suka jawo ruwan sun sani). Sai ya kira ango
\v 10 yace masa, "Kowane mutum yakan raba ruwan inabi mai kyau da farko, kafin mai arhar bayan an shanye mai kyaun. Amma kai ka ajiye mai kyaun sai yanzu."
\s5
\v 11 Wannan alama ta farko ce da Yesu yayi a Kana ta Galili, ya kuma bayyana daukakarsa, almajiransa kuma suka gaskata da shi.
\s5
\v 12 Bayan wannan, Yesu, da mahaifiyarsa, da 'yan'uwansa da almajiransa suka tafi Kafarnahum, kuma suka zauna can wasu 'yan kwanaki.
\s5
\v 13 To idin ketarewa na Yahudawa ya kusato, Yesu kuwa ya wuce zuwa Urushalima.
\v 14 Ya iske wadanda suke sayar da shanu da tumaki da tantabaru, masu canjin kudi kuma na zaune a wurin.
\s5
\v 15 Sai yayi tsumingiya da igiyoyi ya kore su duka daga cikin haikalin, duk da tumakin da shanun. Sai ya watsar da sulallan masu canjin kudin ya birkitar da teburansu.
\v 16 Yace wa masu sayar da tantabaru, "Ku fitar da wadannan abubuwa daga nan. Ku daina maida gidan Ubana wurin kasuwanci."
\s5
\v 17 Almajiransa suka tuna a rubuce yake, "Himma domin gidanka za ta cinye ni."
\v 18 Sai shugabannin Yahudawa suka amsa suka ce masa, "Wace alama za ka nuna mana, da shike kana yin wadannan abubuwan?"
\v 19 Yesu ya amsa, "Ku rushe wannan haikali, kuma a cikin kwana uku zan gina shi."
\s5
\v 20 Sai shugabanin Yahudawa suka ce, "An dauki shekaru arba'in da shidda kamin a gama gina wannan haikalin, za ka dau kwanaki uku kadai wajen gina shi?"
\v 21 Amma yana nufin haikali na jikinsa ne.
\v 22 Bayan da aka tashe shi daga matattu, sai almajiransa suka tuna ya fadi haka, suka kuma ba da gaskiya ga nassi da wannan kalami da Yesu ya fada.
\s5
\v 23 Kuma, da yana Urushalima a idin ketarewa, a lokacin idin, mutane da yawa suka gaskata ga sunansa, sa'adda suka ga alamun da ya yi.
\v 24 Amma Yesu bai yadda da su ba domin ya san su duka,
\v 25 saboda baya bukatar wani ya shaida masa game da mutum, domin ya san abinda ke cikin sa.
\s5
\c 3
\p
\v 1 akwai wani Bafarise da ake kira Nikodimu, shugaba a cikin Yahudawa.
\v 2 Wannan mutum ya zo wurin Yesu da dare ya ce masa, "Rabbi, mun sani cewa kai malami ne da kazo daga wurin Allah, gama ba wanda zai iya yin wadannan alamu da kake yi sai idan Allah na tare da shi."
\s5
\v 3 Yesu ya amsa masa, "Hakika, hakika, idan ba a sake haifuwar mutum ba, ba zai iya ganin mulkin Allah ba."
\v 4 Nikodimu ya ce masa, "Yaya za a sake haifuwar mutum bayan ya tsufa? Ba zai iya sake shiga cikin cikin uwarsa kuma a haife shi ba, zai iya?"
\s5
\v 5 Yesu ya amsa, "Hakika, hakika, idan ba a haifi mutum da ruwa da kuma Ruhu ba, ba zai iya shiga cikin mulkin Allah ba.
\v 6 Abin da aka haifa ta wurin jiki, jiki ne, kuma abin da aka haifa ta wurin Ruhu, Ruhu ne.
\s5
\v 7 Kada ka yi mamaki don na ce maka, 'dole a maya haifuwar ka.'
\v 8 Iska takan hura duk inda ta ga dama. Ka kan ji motsin ta, amma ba ka san inda ta fito ko inda za ta tafi ba. Haka duk wanda aka haifa daga Ruhu."
\s5
\v 9 Nikodimu ya amsa yace masa, "Yaya wannan zai yiwu?"
\v 10 Yesu ya amsa yace masa, "Kai malami ne a Israila amma ba ka san wadannan al'amura ba?
\v 11 Hakika, hakika, ina gaya maka, muna fadin abubuwan da muka sani, kuma muna shaida abubuwan da muka gani. Duk da haka ba ku karbi shaidar mu ba.
\s5
\v 12 Idan na gaya maka abubuwan da ke na duniya amma baka gaskata ba, to yaya zaka gaskata idan na gaya maka abubuwa na sama?
\v 13 Babu wanda ya taba hawa zuwa sama sai dai shi wanda ya sauko daga sama: wato Dan Mutum.
\s5
\v 14 Kamar yadda Musa ya ta da maciji a jeji, haka ma dole a ta da Dan Mutum
\v 15 domin dukan wadanda suka bada gaskiya gareshi su sami rai na har abada.
\s5
\v 16 Gama Allah ya kaunaci duniya sosai, har ya ba da makadaicin Dansa, domin duk wanda ya bada gaskiya gareshi, kada ya mutu, amma ya samu rai madawwami.
\v 17 Gama Allah bai aiko da Dansa cikin duniya domin ya kayar da duniya ba, amma domin a ceci duniya ta wurin sa.
\v 18 Duk wanda ya bada gaskiya gare shi ba a kayar da shi ba, amma duk wanda bai bada gaskiya gare shi ba an riga an kayar da shi, domin bai bada gaskiya ga sunan wannan da shi kadai ne Dan Allah ba.
\s5
\v 19 Wannan shi ne dalilin shari'ar, domin haske ya zo duniya, amma mutane suka kaunaci duhu fiye da hasken, sabili da ayyukan su na mugunta ne.
\v 20 Domin duk wanda ke mugayen ayyuka ya ki haske, kuma baya zuwa wurin hasken domin kada ayyukansa su bayyanu.
\v 21 Sai dai duk wanda yake aikata gaskiya kan zo wurin hasken domin ayyukansa, da ake aiwatarwa ga Allah, su bayyanu.
\s5
\v 22 Bayan wannan, Yesu da almajiransa suka tafi kasar Yahudiya. A can ya dan zauna tare da su ya kuma yi Baftisma.
\v 23 Yahaya ma yana Baftisma a Ainon kusa da Salim domin akwai ruwa da yawa a can. Mutane na zuwa wurin sa yana masu Baftisma,
\v 24 domin a lokacin ba a jefa Yahaya a kurkuku ba tukuna.
\s5
\v 25 Sai gardama ta taso tsakanin almajiran Yahaya da wani Bayahude akan al'adun tsarkakewa.
\v 26 Suka je wurin Yahaya suka ce, "Rabbi, wanda yake tare da kai a dayan ketaren kogin Urdun, kuma ka shaida shi, duba, yana baftisma, kuma mutane duka suna zuwa wurin sa."
\s5
\v 27 Yahaya ya amsa, "Mutum ba zai iya samun wani abu ba sai an ba shi daga sama.
\v 28 Ku da kanku zaku shaida na ce, 'Ba ni ne Almasihu ba' amma amaimakon haka, 'an aiko ni kafin shi.'
\s5
\v 29 Amaryar ta angon ce. Yanzu abokin angon, wanda ke tsaye yana saurarensa, yana murna sosai saboda muryan angon. Murnata ta cika domin wannan.
\v 30 Dole shi ya karu, ni kuma in ragu.
\s5
\v 31 Shi wanda ya fito daga sama ya fi kowa. Shi Wanda ya zo daga duniya, na duniya ne, kuma game da duniya yake magana. Shi wanda ya fito daga sama yana saman kowa.
\v 32 Ya shaida abubuwan da ya ji ya kuma gani, amma babu wanda ya karbi shaidarsa.
\v 33 Duk wanda ya karbi shaidarsa ya tabbatar Allah gaskiya ne.
\s5
\v 34 Domin duk wanda Allah ya aika kan yi magana da kalmomin Allah. Domin bai bada Ruhun da ma'auni ba.
\v 35 Uban ya kaunaci Dan, ya kuma ba da dukan komai a hanunsa.
\v 36 Shi wanda ya bada gaskiya ga Dan ya na da rai madawwami, amma wanda ya ki yiwa Dan biyayya ba zai ga rai ba, amma fushin Allah na kansa.
\s5
\c 4
\p
\v 1 Da Yesu ya sani cewa Farisawa sun ji cewa yana samun almajirai yana kuma yi masu baftisma fiye da Yahaya
\v 2 (ko da shike ba Yesu da kansa ke yin baftismar ba, amma almajiransa ne),
\v 3 ya bar Yahudiya ya koma Galili.
\s5
\v 4 Amma ya zamar masa dole ya ratsa ta Samariya.
\v 5 Ya zo wani birnin Samariya, mai suna Sika, kusa da filin da Yakubu ya ba dansa Yusufu.
\s5
\v 6 Rijiyar Yakubu na wurin. Da Yesu ya gaji da tafiyarsa sai ya zauna gefen rijiyar. Kusan karfe goma sha biyu na rana ne.
\v 7 Wata mace, Ba-Samariya ta zo domin ta dibi ruwa, sai Yesu ya ce mata, "Ba ni ruwa in sha."
\v 8 Gama almajiransa sun tafi cikin gari don sayen abinci.
\s5
\v 9 Sai ba-Samariyar tace masa, "Yaya kai da kake Bayahude kake tambaya ta ruwan sha, ni da nike 'yar Samariya?" Domin Yahudawa ba su harka da Samariyawa.
\v 10 Sai Yesu ya amsa yace mata, "In da kin san kyautar Allah, da shi wanda yake ce da ke, 'Ba ni ruwan sha,' da kin roke shi, sai kuma ya ba ki ruwan rai."
\s5
\v 11 Matar tace masa, "Mallam, ga shi ba ka da guga, kuma rijiyar tana da zurfi. Ina za ka samu ruwan rai?
\v 12 Ai ba ka fi Ubanmu Yakubu ba, ko ka fi shi, shi wanda ya ba mu rijiyar, shi kansa kuma ya sha daga cikin ta, haka kuma 'ya'yansa da shanunsa?"
\s5
\v 13 Yesu ya amsa yace mata, "duk wanda ya sha daga wannan ruwan zai sake jin kishi,
\v 14 amma duk wanda ya sha daga ruwa da zan ba shi ba zai sake jin kishi ba. Maimakon haka, ruwan da zan bashi zai zama mabulbular ruwa a cikinsa wanda ke bulbula zuwa rai madawwami."
\s5
\v 15 Matar tace masa, "Mallam, ka ba ni wannan ruwa yadda ba zan kara jin kishi ba ba kuma sai na zo nan don in dibi ruwa ba."
\v 16 Yesu ya ce mata, "Je, ki kira maigidanki ku zo nan tare."
\s5
\v 17 Matar ta amsa tace masa, "Ba ni da miji." Yesu yace, "Kin fadi daidai da kika ce, 'ba ni da miji,'
\v 18 domin kin auri mazaje har biyar, kuma wanda kike da shi yanzu ba mijin ki bane. Abinda kika fada gaskiya ne."
\s5
\v 19 Matar tace masa, "Mallam, Na ga kai annabi ne.
\v 20 Ubaninmu sun yi sujada a wannan dutse, amma kun ce Urushalima ce wurin da ya kamata mutane su yi sujada."
\s5
\v 21 Yesu ya ce mata, "Mace, ki gaskata ni, cewa lokaci na zuwa wanda ba za ku yi wa Uban sujada ba ko akan wannan dutse ko a Urushalima.
\v 22 Ku kuna bauta wa abinda ba ku sani ba. Mu muna bauta wa abinda muka sani, gama ceto daga Yahudawa yake.
\s5
\v 23 Sai dai, sa'a tana zuwa, har ma ta yi, wadda masu sujada na gaskiya za su yi wa Uba sujada a cikin ruhu da gaskiya, domin irin wadannan ne Uban ke nema su zama masu yi masa sujada.
\v 24 Allah Ruhu ne, kuma mutanen da ke yi masa sujada, dole su yi sujada cikin ruhu da gaskiya."
\s5
\v 25 Matar ta ce masa, "Na san Almasihu na zuwa (wanda ake kira Kristi). Sa'adda ya zo, zai bayyana mana kowane abu.
\v 26 Yesu ya ce mata, "Ni ne shi, wanda ke yi maki magana."
\s5
\v 27 A daidai wannan lokaci, almajiransa suka dawo. Suna ta mamakin dalilin da yasa yake magana da mace, amma babu wanda yace, "Me kake so?" Ko kuma, "Don me ka ke magana da ita?"
\s5
\v 28 Sai matar ta bar tulunta, ta koma cikin gari, tace wa mutanen,
\v 29 "Ku zo ku ga wani mutum wanda ya gaya mani duk wani abu da na taba yi. Wannan dai ba Almasihun bane, ko kuwa?"
\v 30 Suka bar garin suka zo wurinsa.
\s5
\v 31 A wannan lokacin, almajiransa suna rokansa, cewa, "Mallam, ka ci."
\v 32 Amma ya ce masu, "ina da abinci da ba ku san komai akai ba."
\v 33 Sai almajiran suka ce da junansu, "Babu wanda ya kawo masa wani abu ya ci, ko akwai ne?"
\s5
\v 34 Yesu ya ce masu, "Abincina shine in yi nufin wanda ya aiko ni, in kuma cika aikinsa.
\v 35 Ba ku kan ce, 'akwai wata hudu tukuna kafin girbi ya zo ba?' Ina gaya maku, daga idanunku ku ga gonakin, sun rigaya sun isa girbi.
\v 36 Shi wanda ke girbi yakan karbi sakamako ya kuma tattara amfanin gona zuwa rai na har abada, ta haka shi mai shuka da shi mai girbi za su yi farinciki tare.
\s5
\v 37 Gama cikin wannan maganar take, 'Wani na shuka, wani kuma na girbi.'
\v 38 Na aike ku ku yi girbin abinda ba ku yi aiki a kai ba. Wandansu sun yi aiki, ku kuma kun shiga cikin wahalarsu.
\s5
\v 39 Yawancin Samariyawan da ke wannan birni suka gaskata da shi sabili da labarin matar data bada shaida, "Ya gaya mani duk abinda na taba yi."
\v 40 To sa'adda Samariyawa suka zo wurinsa, sai suka roke shi ya zauna tare da su, ya kuwa zauna wurin kwana biyu.
\s5
\v 41 Wasu da dama kuma suka gaskata domin maganarsa.
\v 42 Suka cewa matar, "Mun bada gaskiya, ba saboda maganar ki kadai ba, amma mu kanmu munji, yanzu kuma mun sani cewa wannan lallai shine mai ceton duniya."
\s5
\v 43 Bayan wadannan kwana biyu, ya bar wurin zuwa Galili.
\v 44 Domin Yesu da kansa yace, ba a girmama annabi a kasarsa.
\v 45 Da ya zo Galili, Galiliyawan suka marabce shi. Sun ga dukan abubuwan da ya yi a Urushalima wurin idin, domin su ma sun je idin.
\s5
\v 46 Kuma ya koma Kana ta Galili inda ya mayar da ruwa zuwa ruwan inabi. Akwai wani ma'aikacin fada wanda dansa na rashin lafiya a Kafarnahum.
\v 47 Da ya ji cewa Yesu ya bar Yahudiya ya koma Galili, sai ya tafi wurin Yesu ya roke shi ya sauko ya warka da dansa wanda ke bakin mutuwa.
\s5
\v 48 Yesu yace masa, "Idan ba ku ga alamu da mu'ujizai ba, ba za ku gaskata ba."
\v 49 Ma'aikacin ya ce masa, "Mallam, ka sauko kafin da na ya mutu."
\v 50 Yesu yace masa, "Je ka. Dan ka ya rayu." Mutumin ya gaskata maganar da Yesu ya gaya masa, Sai yayi tafiyarsa.
\s5
\v 51 Yayin da yake sauka kasa, bayinsa suka same shi, suna cewa, danka yana raye.
\v 52 Sai ya tambaye su sa'ar da ya fara samun sauki. Suka amsa masa, "Jiya a sa'a ta bakwai zazabin ya bar shi."
\s5
\v 53 Sai Uban ya gane cewa wannan sa'a ce Yesu ya ce masa, "Jeka, danka na raye." Sabili da haka, shi da dukan gidansa suka bada gaskiya.
\v 54 Wannan ce alama ta biyu da Yesu ya yi bayan da ya bar Yahudiya zuwa Galili.
\s5
\c 5
\p
\v 1 Bayan haka akwai idi na yahudawa, kuma Yesu ya tafi Urashalima.
\v 2 To a cikin Urashilima kusa da kofar tumaki akwai tabki, wanda ake kira Baitasda da harshen Ibraniyanci, yana da shirayi biyar.
\v 3 Taron mutane dayawa masu ciwo da, makafi da guragu da shanyayyu suna kwance a wurin. \f + \ft Mafi kyawun kwafin tsoffin ba su da jumlar, \fqa suna jira a dama ruwan \fqa* . \f*
\v 4 \f + \ft Mafi kyawun kwafin kwafi ba su da aya 4, \fqa Gama mala'ikan Ubangiji kan sabko a cikin tabkin ya dama ruwan, wanda ya fara taba ruwan sai ya warke komai cutar da yake da ita \fqa* . \f*
\s5
\v 5 Akwai wani mutum a bakin tabki yana kwance yana da rashin lafiya har shekara talatin da takwas.
\v 6 Da Yesu ya gan shi yana kwance a wurin sai ya gane ya dade a wurin, sai ya ce masa, "Ko kana so ka warke?"
\s5
\v 7 Sai mai rashin lafiyar ya amsa ya ce, "Malam, bani da kowa da zai sa ni a cikin tabkin idan ruwan ya motsa. Yayinda na ke kokari sai wani ya riga ni."
\v 8 Yesu ya ce masa," Ka tashi ka dauki shimfidarka ka tafi."
\s5
\v 9 Nan dan nan Mutumin ya warke, ya dauki shimfidarsa ya tafi. Ranar kuwa Asabar ce.
\s5
\v 10 Sai Yahudawa suka ce da wanda aka warkar din, "Ai, Asabar ce, bai kuwa halatta ka dauki shimfidarka ba."
\v 11 Sai ya amsa ya ce, "Ai wanda ya warkar da ni, shine ya ce mani 'Dauki shimfidarka, ka tafi."
\s5
\v 12 Suka tambaye shi, "wane mutum ne ya ce maka, 'Dauki shimfidar ka yi tafiya'?"
\v 13 Sai dai, shi wanda aka warka din, ba san ko wanene ya warkar da shi ba, domin Yesu ya riga ya tafi aboye, saboda akwai taro a wurin.
\s5
\v 14 Bayan haka, Yesu ya same shi a Haikalin, ya ce masa, "ka ga fa, ka warke. To, kada ka kara yin zunubi don kada wani abu da ya fi wannan muni ya same ka."
\v 15 Sai mutumin ya tafi ya gaya wa Yahuduwa cewa Yesu ne ya warkar da shi.
\s5
\v 16 To saboda haka Yahudawa suka fara tsanantawa Yesu, don ya yi wadannan abubuwa ran Asabar.
\v 17 Yesu kuwa ya amsa masu ya ce, "Ubana yana aiki har yanzu, ni ma ina aiki."
\v 18 Saboda haka, Yahudawa suka kara nema su kashe shi ba don ya keta Asabar kadai ba, amma kuma domin ya ce Allah Ubansa ne, wato yana maida kansa dai-dai da Allah.
\s5
\v 19 Yesu ya amsa masu ya ce, hakika hakika, ina gaya maku, Dan ba ya yin kome shi kadai, sai abin da ya ga Uba yana yi.
\v 20 Domin Uban na kaunar Dan, yana kuma nuna masa dukan abinda shi da kansa yake yi, kuma zai nuna masa abubuwan da suka fi wadannan, domin ku yi mamaki.
\s5
\v 21 Gama kamar yadda Uba yakan tada matattu ya kuma basu rai, haka Dan ma yake bada rai ga duk wanda ya nufa.
\v 22 Gama Uban ba ya hukunta kowa, sai dai ya damka dukan hukunci ga Dan,
\v 23 domin kowa ya girmama Dan, kamar yadda suke girmama Uban. Shi wanda ba ya girmama Dan, ba ya girmama Uban da ya aiko shi.
\s5
\v 24 Hakika, hakika, duk mai jin Maganata, yana kuma gaskata wanda ya aiko ni, yana da rai madawwami ba kuma za a kashe shi ba, domin ya ratse daga mutuwa zuwa rai,.
\s5
\v 25 Hakika hakika, ina gaya maku, lokaci na zuwa, har ma ya yi da matattatu za su ji muryar Dan Allah, wadanda suka ji kuwa za su rayu.
\s5
\v 26 Kammar yada Uba ya ke da rai a cikinsa, haka ya ba Dan don ya zama da rai cikin kansa.
\v 27 Uban ya kuma ba Dan ikon zartar da hukunci, saboda shi ne Dan Mutum.
\s5
\v 28 Kada ku yi mamakin wannan, domin lokaci na zuwa da duk wadanda suke kaburbura za su ji muryarsa,
\v 29 su kuma fito: wadanda suka aikata nagarta zawa tashi na rai, wadanda suka aikata mugunta kuwa zuwa tashi na hukunci.
\s5
\v 30 Ba na iya yin kome ni da kai na. Yadda na ke ji, haka nake yin hukunci, Hukunci na kuwa na adalci ne, domin ba nufin kaina nake bi ba, sai dai nufin wanda ya aiko ni.
\v 31 Idan zan yi shaida game da kaina, shaidata baza ta zama gaskiya ba.
\v 32 Akwai wani wanda ya ke bada shaida game da ni, na kuwa sani shaidar da yake bayarwa game da ni gaskiya ce.
\s5
\v 33 Kun aika zuwa wurin Yahaya, shi kuma ya yi shaidar gaskiya.
\v 34 Duk da haka shaidar da na karba bata mutum bace. Na fadi wadanan abubuwa domin ku sami ceto.
\v 35 Yahaya fitila ne mai ci, mai haske ne kuma, kun yarda ku yi farinciki da haskensa dan lokaci kadan.
\s5
\v 36 Amma shaidar da ni ke da ita ta fi ta Yahaya karfi. Domin ayyukan da Uba ya bani ni in yi, wato ainihin ayyukan da nake yi, su ne suke shaida ta cewa, Uba ne ya aiko ni.
\v 37 Uba wanda ya aiko ni, shi da kansa ya shaide ni. Ba ku taba jin muryar sa ba, ko ganin kamanninsa.
\v 38 Maganarsa kuwa ba ta zaune a zuciyarku, domin baku gaskata da wanda ya aiko ni ba.
\s5
\v 39 Kuna nazarin littattafai, don a tsammaninku a cikinsu za ku sami rai Madawwami, alhali kuwa su ne suke shaidata.
\v 40 kuma baku niyyar zuwa wurina domin ku sami rai.
\s5
\v 41 Ba na karbar yabo daga wurin mutane,
\v 42 amma na sani baku da kaunar Allah a zuciyarku.
\s5
\v 43 Na zo a cikin sunan Ubana, amma ba ku karbe ni ba. Idan wani ya zo da sunan kansa, za ku karbe shi.
\v 44 Ta yaya za ku ba da gaskiya, ku da kuke karban yabo daga junanku, amma ba ku neman yabon dake zuwa daga wurin Allah?
\s5
\v 45 Kada ku yi tunani zan zarge ku a wurin Uba. Mai zargin ku shine Musa, wanda kuka sa begenku a cikin sa.
\v 46 Inda kun gaskata Musa, da kun gaskata da ni domin ya yi rubutu game da ni.
\v 47 Idan kuwa ba ku gaskata abin da ya rubuta ba, ta yaya za ku gaskata maganata?"
\s5
\c 6
\p
\v 1 Bayan waddannan abubuwa, Yesu ya ketare tekun Galili, wanda a ke kira tekun Tibariya.
\v 2 Sai taro mai yawa suka bi shi domin suna ganin alamu da yake yi akan marasa lafiya.
\v 3 Sai Yesu ya hau dutse ya zauna a can tare da almajiransa.
\s5
\v 4 (Kuma da idin Ketarewa, wato idin Yahudawa, ya kusato.)
\v 5 Da Yesu ya daga kai sai ya ga babban taro yana zuwa wurinsa, sai ya ce ma Filibus, "Ina za mu sayi gurasar da Mutanen nan za su ci?"
\v 6 (Ya fadi haka ne domin ya gwada shi, saboda shi kansa ya san abin da zai yi.)
\s5
\v 7 Filibus ya amsa masa, "gurasar dinari biyu ma ba zata ishi kowannensu ya samu ko kadan ba."
\v 8 Daya daga cikin almajiransa, wato Andarawus, dan'uwan Siman Bitrus, ya ce masa,
\v 9 "Ga wani dan yaro nan da dunkule biyar na sha'ir, da kifi biyu. Amma menene wadannan za su yi wa mutane masu yawa?"
\s5
\v 10 Yesu ya ce, "ku sa mutane su zauna."( wurin kuwa akwai ciyawa.) Sai mazajen suka zauna, sun kai wajen dubu biyar.
\v 11 Sai Yesu ya dauki gurasar, bayan da ya yi godiya, sai ya rarraba wa wadanda suke zaune. Haka kuma ya rarraba kifin gwargwadon abin da zai ishe su.
\v 12 Da Mutanen suka ci suka kuma koshi, sai ya ce wa almajiransa, ku tattara gutsattsarin da suka rage, kada ya zama asara."
\s5
\v 13 Sai suka cika kwanduna goma sha biyu da gutsattsarin gurasar nan biyar da ya rage bayan da kowa ya ci.
\v 14 Da jama'a suka ga alamar da ya yi, sai suka ce, "Hakika wannan shi ne annabin nan mai zuwa cikin duniya.
\v 15 "Da Yesu ya gane suna shirin zuwa su dauke shi da karfi da yaji su nada shi sarki, sai ya sake komawa kan dutsen da kansa.
\s5
\v 16 Da yamma ta yi, sai almajiransa suka gangara teku.
\v 17 Suka shiga cikin jirgi, suka haye teku zuwa kafarnahum. (A lokacin duhu ya yi, Yesu kuwa bai riga ya iso wurinsu ba tukuna.)
\v 18 Iska mai karfin gaske tana kadawa, kuma tekun yana hargowa.
\s5
\v 19 Bayan da almajiran suka yi tuki na wajen kimanin mil ashirin da biyar ko talatin, sai suka hango Yesu yana tafiya a kan teku ya kuma kusa da jirgin, sai suka firgita.
\v 20 Amma ya ce masu, "Ni ne! kada ku firgita."
\v 21 Sa'an nan suka yarda suka karbe shi a cikin jirgin, kuma nan da nan jirgin ya kai gacci.
\s5
\v 22 Kashe gari, sauran taron da suke tsaye a dayan hayin tekun suka ga cewa babu wani jirgi a wajen sai dayan, Yesu kuma bai shiga ciki da almajiransa ba, amma almajiransa suka tafi su kadai.
\v 23 Sai dai, akwai wadansu jirage da suka zo daga Tibariya kusa da wurin da taron suka ci gurasa bayan da Ubangiji ya yi godiya.
\s5
\v 24 Sa'anda taron suka gane cewa Yesu da almajiransa ba su wurin, su da kansu su ka shiga cikin jiragen suka tafi Kafarnahum neman Yesu.
\v 25 Da suka same shi a hayin tekun, suka ce masa, "Mallam, yaushe ka zo nan?"
\s5
\v 26 Yesu ya amsa masu, da cewa, "hakika, kuna nema na ne, ba don kun ga alamu ba, amma domin kun ci gurasar nan kun koshi.
\v 27 Ku daina yin wahala a kan neman abinci mai lalacewa, sai dai a kan abinci mai dawwama wanda zai kaiku ga rai madawwami wanda Dan Mutum zai ba ku, domin Ubangiji Allah ya sa hatiminsa a kansa."
\s5
\v 28 Sai suka ce Masa, "Me za mu yi, domin mu aikata ayyukan Allah?
\v 29 Yesu ya amsa, "Wannan shi ne aikin Allah: wato ku gaskata da wanda ya aiko."
\s5
\v 30 Sai suka ce masa, "To wace alama za ka yi, don mu gani mu gaskata ka?
\v 31 Me za ka yi? Kakanninmu sun ci manna a jeji, kamar yadda aka rubuta, "Ya ba su gurasa daga sama su ci."
\s5
\v 32 Sa'an nan Yesu ya ce masu, "hakika, hakika, ina gaya maku ba Musa ne ya ba ku gurasa nan daga sama ba, amma Ubana ne ya baku gurasa ta gaskiya daga sama.
\v 33 Gurasar Allah itace mai saukowa daga sama mai kuma bada rai ga duniya,"
\v 34 Sai suka ce masa, "Mallam, ka rika ba mu irin wannan gurasa kodayaushe."
\s5
\v 35 Yesu ya ce masu, "Ni ne gurasa mai ba da rai. Wanda ya zo wurina ba zai ji yunwa ba, wanda kuma ya gaskanta da ni ba zai kara jin kishi ba.
\v 36 Amma na gaya maku cewa, hakika kun gan ni, duk da haka ba ku ba da gaskiya ba.
\v 37 Duk wanda Uba ya bani zai zo gare ni, wanda kuwa ya zo gare ni ba zan kore shi ba ko kadan.
\s5
\v 38 Gama na sauko daga sama, ba domin in bi nufin kaina ba, sai dai nufin wanda ya aiko ni.
\v 39 Wannan shi ne nufin wanda ya aiko ni, kada in rasa ko daya daga cikin wadannan da ya bani, sai dai in tashe su a ranar karshe.
\v 40 Gama wannan shi ne nufin Ubana, duk wanda yake ganin Dan ya kuma gaskata da shi zai sami rai madawwami, ni kuma zan tashe shi a ranar karshe.
\s5
\v 41 Sai Yahudawa suka yi gunaguni akansa, domin ya ce, "Nine Gurasar da ta sauko daga sama."
\v 42 Suka ce, "Ba wannan ne Yesu Dan Yusufu, wanda Ubansa da Uwarsa mun san su ba? Ta yaya yanzu zai ce, 'Na ya sauko daga sama'?
\s5
\v 43 Yesu ya amsa, ya ce masu, "Kada ku yi gunaguni a junanku.
\v 44 Ba mai iya zuwa wurina sai dai in Uba wanda ya aiko ni ya jawo shi, ni kuwa zan tashe shi a rana ta karshe.
\v 45 A rubuce yake cikin litattafan anabawa cewa, 'Dukkansu Allah zai koya masu'. Duk wanda ya ji ya kuma koya daga wurin Uba, ya kan zo gare ni.
\s5
\v 46 Ba cewa wani ya taba ganin Uban ba, sai shi wanda yake daga wurin Allah - shine ya ga Uban.
\v 47 Hakika, hakika, wanda ya bada gaskiya, yana da rai Madawwami.
\s5
\v 48 Ni ne Gurasa ta rai.
\v 49 Ubanninku sun ci manna cikin jeji, suka kuma mutu.
\s5
\v 50 Ga gurasa da ta sauko daga sama, domin mutum ya ci daga cikinta ba kuwa zai mutu ba.
\v 51 Ni ne gurasa mai rai da ya sauko daga sama. Duk wanda ya ci daga gurasar, zai rayu har abada. Wannan gurasar da zan bayar jiki na ne don ceton duniya."
\s5
\v 52 Sai Yahudawa suka fusata a tsakanin junansu suka kuma fara gardama, cewa, "Yaya mutumin nan zai iya bamu naman jikinsa mu ci?
\v 53 Sai Yesu ya ce masu, "hakika, hakika, in ba ku ci naman jikin Dan mutum ba, ba ku kuma sha jininsa ba, ba za ku sami rai a cikin ku ba.
\s5
\v 54 Dukan wanda ya ci nama na ya kuma sha jinina yana da rai Madawwami, ni kuwa zan tashe shi a ranar karshe.
\v 55 Domin namana abinci ne na gaske, jinina kuma abin sha ne na gaskiya.
\v 56 Duk wanda ya ci namana, ya kuma sha jinina yana zamne a ciki na, ni kuma a cikinsa.
\s5
\v 57 Kamar yadda rayayyen Uba ya aiko ni, nake kuma rayuwa saboda Uban, haka ma wanda ya ci namana, zai rayu sabo da ni.
\v 58 Wannan itace gurasar da ta sauko daga sama, ba irin wadda Ubanninku suka ci suka mutu ba. Dukan wanda ya ci gurasar zai rayu har abada."
\v 59 Yesu ya fadi wadan nan abubuwa a cikin majami'a sa'ad da yake koyarwa a Kafarnahum.
\s5
\v 60 Da jin haka, da yawa daga cikin almajiransa suka ce, "Wannan Magana yana da karfi, wa zai iya jinta?"
\v 61 Yesu, kuwa da yake ya sani a ransa da cewa almajiransa suna gunagunin wannan, sai ya ce masu, "Wannan ya zamar maku laifi?
\s5
\v 62 Yaya Ke nan in kun ga Dan Mutum yana hawa inda yake a da?
\v 63 Ruhu shine mai bayar da rai; Jiki ba ya amfana komai. Kalmomin da na fada maku ruhu ne, da kuma rai.
\s5
\v 64 Amma fa akwai wadansun ku da ba su ba da gaskiya ba. Domin tun farko Yesu ya san wadanda ba su ba da gaskiya ba, da kuma wanda zai bashe shi.
\v 65 Ya fada cewa, "shiyasa na gaya maku, ba mai iya zuwa wurina, sai ta wurin Uban."
\s5
\v 66 Bayan haka, da yawa daga cikin almajiransa suka koma da baya, ba su kara tafiya tare da shi ba.
\v 67 Sai Yesu ya ce wa goma sha biyun, "ku ba kwa so ku tafi, ko ba haka ba?
\v 68 Bitrus ya amsa masa ya ce, "Ya Ubangiji, gun wa za mu je? kai kake da maganar rai madawwami.
\v 69 Mu kwa mun gaskata mun kuma sani kai ne mai tsarkin nan na Allah."
\s5
\v 70 Yesu ya ce masu, "Ba ni na zabe ku, goma sha biyu ba, amma dayanku Iblis ne?"
\v 71 Wato yana magana akan Yahuda dan Siman Iskariyoti, shi kuwa daya daga cikin sha-biyun ne, wanda zai ba da Yesu.
\s5
\c 7
\p
\v 1 Bayan wadannan abubuwa Yesu ya zagaya cikin Gallili, saboda baya so ya shiga cikin Yahudiya domin Yahudawa suna shirin su kashe shi.
\v 2 To Idin Bukkoki na Yahudawa ya kusa.
\s5
\v 3 Sai 'yan'uwansa suka ce da shi, "ka tashi ka tafi Yahudiya, domin almajiranka su ga ayyukan da kake yi su ma.
\v 4 Ba wanda ya ke yin wani abu a boye idan dai yana so kowa da kowa ya san shi. Da yake ka na yin wadannan abubuwa sai ka nuna kan ka a fili ga duniya.
\s5
\v 5 Domin ko 'yan'uwansa ma basu bada gaskiya gare shi ba.
\v 6 Yesu ya ce dasu, "lokaci na bai yi ba tukuna, amma ku koyaushe lokacin ku ne.
\v 7 Duniya baza ta iya kin ku ba, amma ta ki ni saboda ina fadin cewa ayyukanta ba su da kyau.
\s5
\v 8 Ku ku je wurin idin, ni ba zan je wurin idin ba domin lokacina bai yi ba tukuna.
\v 9 Bayan da ya gaya masu wadannan abubuwa, ya tsaya a cikin Gallili.
\s5
\v 10 Amma bayan da 'yan'uwansa su ka tafi wurin idin shi ma ya tafi, amma a asirce ba a fili ba.
\v 11 Saboda Yahudawa suna neman sa a wurin idin, su na cewa "Ina yake?"
\s5
\v 12 Akwai maganganu dayawa a kansa cikin taron. Wadansu suna cewa, "shi mutumin kirki ne." Wadansu kuma suna cewa,"A'a yana karkatar da hankalin jama'a."
\v 13 Amma duk da haka ba wanda ya yi magana a fili a kansa saboda suna jin tsoron Yahudawa.
\s5
\v 14 Sa'anda aka kai rabin idin, sai Yesu ya shiga cikin haikali ya fara koyarwa.
\v 15 Yahudawa suna mamaki suna cewa,"Yaya aka yi wannan mutum ya sami ilimi dayawa haka? Shi kuwa bai je makaranta ba."
\v 16 Yesu ya ba su amsa ya ce,"Koyarwata ba tawa ba ce, amma ta wanda ya aiko ni ce."
\s5
\v 17 Idan wani yana so ya yi nufinsa, za ya gane koyarwannan ko daga wurin Allah ta zo, ko ko tawa ce ta kaina.
\v 18 Ko wanene yake maganar kansa, yana neman darajar kansa kenan, amma ko wanene ya nemi darajar wanda ya aiko ni, wannan mutum mai gaskiya ne, babu rashin adalci a cikin sa.
\s5
\v 19 Ba Musa ya baku dokoki ba? Amma duk da haka ba mai aikata dokokin. Me yasa ku ke so ku kashe ni?
\v 20 Taron suka ba shi amsa, "Ka na da aljani. Wanene yake so ya kashe ka?"
\s5
\v 21 Yesu ya amsa ya ce masu, "Nayi aiki daya, dukan ku kuna mamaki da shi.
\v 22 Musa ya baku kaciya, {ba kuwa daga Musa take ba, amma daga kakannin kakanni ta ke}, kuma a ranar Asabar kukan yi wa mutum kaciya.
\s5
\v 23 Idan mutum ya karbi kaciya ranar Asabar, domin kada a karya dokar Musa, don me kuka ji haushi na saboda na mai da mutum lafiyayye sarai ranar Asabar?
\v 24 Kada ku yi shari'a ta ganin ido, amma ku yi shari'a mai adalci."
\s5
\v 25 Wadansun su daga Urushalima suka ce, "wannan ba shine wannan da suke nema su kashe ba?"
\v 26 Kuma duba, yana magana a fili, sannan ba wanda ya ce da shi komai. Ba zai yiwu ba mahukunta su sani cewa wannan Kristi ne, ko ba haka ba?
\v 27 da haka, mun san inda wannan mutum ya fito. Amma sa'anda Kristi za ya zo, ba wanda zai san inda ya fito."
\s5
\v 28 Yesu yayi magana da karfi a haikali, yana koyarwa ya na cewa, "Kun san ni kuma kun san inda na fito. Ban zo domin kaina ba, amma wanda ya aiko ni mai gaskiya ne, ku kuwa baku san shi ba.
\v 29 Ni na san shi domin daga wurinsa na fito, kuma shine ya aiko ni."
\s5
\v 30 Suna kokari su kama shi, amma ba wanda ya iya sa masa hannu domin sa'arsa ba ta yi ba tukuna.
\v 31 Duk da haka wadansu dayawa a cikin taron suka bada gaskiya gare shi suka ce,"Sa'anda Kristi ya zo, zai yi alamu fiye da wadanda wannan mutum ya yi?"
\v 32 Farisawa suka ji tattarmukan suna yin rada a kan wadannan abubuwa game da Yesu, Sai manyan malamai da Farisawa su ka aika jami'ai su kama shi.
\s5
\v 33 Sa'annan Yesu yace ma su," jimawa kadan ina tare ku, sa'annan in tafi wurin wanda ya aiko ni.
\v 34 Za ku neme ni ba za ku same ni ba; inda na tafi, ba za ku iya zuwa ba."
\s5
\v 35 Yahudawa fa su ka cewa junan su, "Ina wannan mutum zai je inda ba za mu iya samun sa ba? Ko za ya tafi wurin Helinawa na warwatsuwa ya koyawa Helinawa?
\v 36 Wace kalma ya ke fadi haka, 'za ku neme ni amma ba za ku same ni ba; inda na tafi, ba za ku iya zuwa ba'?"
\s5
\v 37 To a rana ta karshe, babbar rana ta idin, Yesu ya mike ya yi magana da karfi cewa, "Idan kowa yana jin kishi, ya zo wuri na ya sha.
\v 38 Shi wanda ya bada gaskiya gare ni kamar yadda nassi ya fadi, daga cikin sa rafukan ruwa na rai za su bulbulo."
\s5
\v 39 Amma ya fadi haka a kan Ruhu, wanda wadanda suka bada gaskiya gare shi za su karba; ba a ba da Ruhun ba tukuna, saboda ba a rigaya an daukaka Yesu ba.
\s5
\v 40 Wadansu a cikin taron, sa'anda suka ji wadannan kalmomi, suka ce, "Wannan lallai annabi ne."
\v 41 Wadansu suka ce, "Wannan Almasihu ne." Amma wadansu suka ce, "Almasihu zai fito daga Gallili ne?
\v 42 Ba nassi ya ce Almasihu zai fito daga cikin dangin Dauda daga Baitalami ba, daga kauyen da Dauda ya fito?
\s5
\v 43 Sai aka sami rabuwa a cikin taron saboda shi.
\v 44 Da wadansun su sun kama shi, amma ba wanda ya sa masa hannu.
\s5
\v 45 Sa'annan jami'an suka dawo wurin manyan Fristoci da Farisawa, wadanda suka ce," me yasa ba ku kawo shi ba?"
\v 46 Jami'an su ka amsa, "Ba mutumin da ya taba yin magana kamar haka."
\s5
\v 47 Farisawa suka amsa masu, "kuma an karkatar da ku?
\v 48 Ko wani daga cikin mahukunta ya bada gaskiya gare shi, ko kuwa daga cikin Farisawa?
\v 49 Amma wannan taro da basu san shari'a ba, la'anannu ne."
\s5
\v 50 Nikodimus ya ce masu, (shi wanda ya zo wurin Yesu da, daya daga cikin Farisawa),
\v 51 " Ko shari'armu bata hana hukunta mutum ba, sai ta ji daga gare shi ta kuma san abin da ya aikata ba?"
\v 52 Suka amsa masa suka ce,"kai ma daga Galili ka fito? Ka yi bincike ka gani ba annanbin da zai fito daga Galili."
\s5
\v 53 Daga nan sai kowa ya tafi gidansa.
\s5
\c 8
\p
\v 1 Yesu ya je Dutsen Zaitun.
\v 2 Da sassafe ya dawo Haikali, dukan mutane kuma suka zo wurin sa; yazauna koya masu.
\v 3 Sai marubuta da Farisawa suka kawo mace wadda aka kama ta tana zina. Su ka sa ta a tsakiya.
\s5
\v 4 Sai su ka ce da shi, "Malam, wannan mace an kama ta tana cikin yin zina.
\v 5 A cikin shari'a, Musa ya bamu umurni mu jejjefe irin wandannan mutume, kai me ka ce game da ita?"
\v 6 Sun fadi haka ne domin su gwada shi su sami abinda za su zarge shi da shi, amma Yesu ya sunkuya yayi rubutu da yatsansa a kasa.
\s5
\v 7 Sa'adda suka cigaba da tambayar sa, ya mike tsaye yace masu, "shi wanda ba shi da zunubi a cikin ku, ya fara jifar ta da dutse."
\v 8 Ya sake sunkuyawa, ya yi rubutu da yatsansa a kasa.
\s5
\v 9 Da suka ji haka, sai suka fita dai-dai da dai-dai, kama daga babbansu. A karshe dai aka bar Yesu shi kadai, tare da matar wadda ta ke a tsakiyar su.
\v 10 Yesu ya tashi tsaye ya ce da ita, "mace, ina masu zargin ki? Ba wanda ya kashe ki?
\v 11 Ta ce, "Ba kowa, Ubangiji" Yesu ya ce, "Ni ma ban kashe ki ba. Ki yi tafiyar ki, daga yanzu kada ki kara yin zunubi."
\s5
\v 12 Yesu ya kara yin magana da mutanen cewa, "Ni ne hasken duniya, shi wanda ya biyo ni, ba zai yi tafiya cikin duhu ba, amma za ya sami hasken rai.
\v 13 Farisawa suka ce masa, "Kana bada shaida a kan ka, shaidarka ba gaskiya ba ce."
\s5
\v 14 Yesu ya amsa ya ce masu, "Ko ma na bada shaida a kai na, shaidata gaskiya ce, na san daga inda na fito da inda zan tafi, amma ku baku san daga inda na fito ba, baku kuma san inda zan tafi ba.
\v 15 Kuna shari'a ta son kai, ni ko ban yi wa kowa shari'a ba.
\v 16 Ko ma da na yi shari'a, shari'ata gaskiya ce domin ba ni kadai ba ne, amma ina tare da Uba wanda ya aiko ni.
\s5
\v 17 I, a cikin dokarku an rubuta cewa shaidar mutum biyu gaskiya ce.
\v 18 Ni ne ni ke shaidar kaina, kuma Uba wanda ya aiko ni ya na shaida ta.
\s5
\v 19 Su ka ce da shi, "Ina ubanka?" Yesu ya amsa ma su ya ce, "baku san ni ba balle Ubana, in da kun san ni da kun san Uba na kuma."
\v 20 Ya fadi wadannan kalmomi a kusa da wurin ajiya sa'adda ya ke koyarwa a cikin haikali, kuma ba wanda ya kama shi saboda sa'arsa bata yi ba tukuna.
\s5
\v 21 Ya kara cewa da su,"Zan tafi, za ku neme ni ba za ku same ni ba, za ku mutu cikin zunubinku. Inda ni ke tafiya, ba za ku iya zuwa ba".
\v 22 Yahudawa su ka ce,"Zai kashe kansa ne, da ya ce inda ni ke tafiya ba za ku iya zuwa ba?"
\s5
\v 23 Yesu ya ce masu ku daga kasa kuke, Ni kuwa daga bisa ni ke. Ku na wannan duniya ne, Ni kuwa ba na wannan duniya ba ne.
\v 24 Shiyasa na ce maku za ku mutu cikin zunubanku. In ba kun bada gaskiya NI NE ba, za ku mutu cikin zunubanku.
\s5
\v 25 Sai kuma suka ce da shi,"Wanene kai?" Yesu ya ce masu, "Abin da na gaya maku tun daga farko.
\v 26 Ina da a bubuwa da yawa da zan gaya maku, in kuma hukunta ku a kai. Duk da haka, wanda ya aiko ni, mai gaskiya ne, abubuwan da naji daga wurin sa, wadannan abubuwan su ni ke gaya wa duniya."
\v 27 Ba su gane ba yana yi masu magana a kan Uban.
\s5
\v 28 Yesu ya ce, "Sa'adda kuka tada Dan Mutum sama sa'annan za ku gane NI NE, kuma ban yi komi domin kaina ba. Kamar yadda Uba ya koya mani, haka nike fadin wadannan abubuwa.
\v 29 Shi wanda ya aiko ni, yana tare da ni kuma bai bar ni ni kadai ba, domin kullum ina yin abubuwan da suke faranta masa rai."
\v 30 Sa'adda Yesu ya ke fadin wadannan abubuwa, dayawa suka bada gaskiya gare shi.
\s5
\v 31 Yesu ya gayawa wadancan Yahudawa da suka bada gaskiya gare shi, "Idan kun tsaya a cikin magana ta ku almajiraina ne na gaskiya,
\v 32 Kuma za ku san gaskiya, gaskiya kuwa zata 'yantar da ku."
\v 33 Suka amsa masa, "Mu zuriyar Ibrahim ne kuma bamu taba yin bauta wurin kowa ba, yaya za ka ce, 'Za a 'yantar da ku'?"
\s5
\v 34 Yesu ya ce masu, "Hakika, hakika, ina ce maku, dukan wanda ya ke aika zunubi bawan zunubi ne.
\v 35 Bawa kuwa, ba ya zama a gida dindindin, da yana zama dindindin.
\v 36 Saboda haka, idan Dan ya 'yantar da ku zaku zama 'yantattu sosai.
\s5
\v 37 Na san ku zuriyar Ibrahim ne, kuna so ku kashe ni saboda kalma ta bata da wurin zama a cikin ku.
\v 38 Na fadi abubuwan da na gani a wurin Ubana, ku kuma kuna yin abubuwan da kuka ji daga wurin ubanku."
\s5
\v 39 Suka amsa suka ce masa, "Ibrahim ne ubanmu" Yesu ya ce masu, "Da ku 'yayan Ibrahim ne da kun yi ayukan da Ibrahim ya yi.
\v 40 Amma, yanzu kuna so ku kashe ni, mutumin da ya gaya maku gaskiyar da ya ji daga wurin Allah. Ibrahim bai yi haka ba.
\v 41 Kuna yin ayyukan ubanku. Suka ce masa, "mu ba a haife mu cikin fasikanci ba, muna da Uba daya: Allah."
\s5
\v 42 Yesu ya ce masu, "Inda Allah Ubanku ne, da kun kaunace ni, gama na zo daga wurin Allah kuma ga ni anan, gama ba domin kaina nazo ba, shine ya aiko ni.
\v 43 Meyasa baku gane magana ta ba? Ai saboda ba za ku iya jin maganata ba ne.
\v 44 Ku na ubanku, shaidan ne, kuma kuna so ku yi nufe-nufe na ubanku. Shi mai kisan kai ne tun daga farko kuma ba ya tsayawa gaskiya saboda da babu gaskiya a cikin sa. Sa'anda yake fadin karya, yana maganar halinsa ne domin shi dama makaryaci ne da uban karya kuma.
\s5
\v 45 Dayake ina fadin gaskiya baku bada gaskiya gare ni ba.
\v 46 Wanene a cikin ku ya kama ni da zunubi? Idan na fadi gaskiya don me ba ku gaskanta ni ba?
\v 47 Shi wanda yake na Allah ya kan ji maganar Allah, ku ba kwa jin maganar Allah da yake ku ba na Allah bane,"
\s5
\v 48 Yahudawa suka amsa suka ce masa, "Bamu fadi gaskiya ba da muka ce kai Basamariye ne kuma kana da aljan?"
\v 49 Yesu ya amsa, "Ni ba ni da aljan, ina girmama Ubana, ku kuma ba kwa girmama ni."
\s5
\v 50 Ba na neman daraja domin kaina, akwai wanda ke nema yana kuma hukuntawa.
\v 51 Hakika, hakika, iIna ce maku, dukan wanda ya kiyaye maganata, ba za ya ga mutuwa ba."
\s5
\v 52 Sai Yahudawa su ka ce masa, Yanzu mun sani kana da aljan. Ibrahim da annabawa sun mutu, amma kai ka ce, ' dukan wanda ya yi biyayya da maganata ba zai dandana mutuwa ba'.
\v 53 Ai baka fi ubanmu Ibrahim girma ba wanda ya mutu, ko ka fi shi? Annabawa kuma sun mutu. Wa kake daukar kanka ne?."
\s5
\v 54 Yesu ya amsa, "Idan na daukaka kaina, daukaka ta banza ce, Ubana ne ya daukaka ni. Wanda kuka ce shi ne Allahnku.
\v 55 Ku kuwa ba ku san shi ba, amma ni na san shi. Idan na ce ban san shi ba, na zama kamar ku kenan, makaryaci. Sai dai, Ni na san shi ina kiyaye maganarsa.
\v 56 Ubanku Ibrahim ya yi farinciki da ganin rana ta; ya gan ta kuma ya yi murna."
\s5
\v 57 Yahudawa su ka ce masa, "Baka kai shekara hamsin ba tukuna, ka taba ganin Ibrahim?"
\v 58 Yesu ya ce masu, "Hakika, hakika, ina ce maku, kafin a haifi Ibrahim, NI NE."
\v 59 Suka dauki duwatsu za su jefe shi, amma Yesu ya boye kansa, ya fita daga haikali.
\s5
\c 9
\p
\v 1 Da Yesu yana wucewa, sai ya ga wani mutum makaho tun daga haihuwa.
\v 2 Sai almajiransa suka tambaye shi, "Mallam, wa yayi zunubi, mutumin ne ko iyayensa, har aka haife shi makaho?"
\s5
\v 3 Yesu ya amsa, Ba mutumin ne ko iyayensa suka yi zunubi ba, amma domin aikin Allah ya bayyana a cikinsa.
\v 4 Dole mu yi aikin wanda ya aiko ni tunda rana. Dare na zuwa inda ba mai iya yin aiki.
\v 5 Yayinda ina duniya, ni ne hasken duniya."
\s5
\v 6 Bayan da Yesu ya fadi wadannan abubuwan, ya tofa yawu a kasa, ya kwaba kasar da yawunsa, sai ya shafe idanun mutumin da kasar.
\v 7 Ya ce masa, tafi, ka wanke a tafkin Siloam (ma'anarsa: aike)." Sai mutumin ya tafi, ya wanke, ya dawo yana gani.
\s5
\v 8 Sai makwabtansa da mutanen da da suka gan shi tun can yana roko suka ce, "Ba wannan mutum ne wanda ya ke zaune yana roko ba?"
\v 9 Wadansu suka ce, "shi ne." Wadansu suka ce, "A'a, amma yana kama da shi." Amma shi ya ce, "Ni ne wannan mutum."
\s5
\v 10 Suka ce masa, "To yaya aka bude maka idanu?"
\v 11 Sai ya amsa, "Mutumin da ake ce da shi Yesu shi ya kwaba kasa ya shafa mani a idanuna ya ce mani, 'je ka kogin Siluwam ka wanke.' Sai naje na wanke, sannan na samu gani."
\v 12 Suka ce masa, "Ina yake?" Ya amsa, "Ban sani ba."
\s5
\v 13 Suka kawo mutumnin da yake makaho a da wurin farisawa.
\v 14 A ranar asabar ne kwa Yesu ya kwaba kasa ya bude masa idanu.
\v 15 Har yanzu farisawan suka tambaye shi yadda ya sami ganin gari. Ya ce masu, "Ya sa mani kasa a idanuna, na wanke, kuma yanzu ina gani."
\s5
\v 16 Wadansu daga cikin farisawa suka ce, "Wannan mutum ba daga Allah yake ba domin ba ya kiyaye ranar Asabar. "Wadansu suka ce, "Yaya mai zunubi zai yi irin wadannan alamu?" Sai rabuwa ta shiga tsakanin su.
\v 17 Sai suka tambayi makahon kuma, "Me kake cewa game da shi dashike ya bude maka idanu?" Makahon ya ce, "shi annabi ne."
\v 18 Har yanzu kam Yahudawan basu yarda da makantarsa ba da ganin gari da ya samu, sai da suka kirayo iyayen shi wanda ya sami ganin garin.
\s5
\v 19 Su ka tambayi iyayen, "Wannan shine yaronku da kuka ce an haife shi makaho? Yaya yanzu ya ke iya gani?"
\v 20 Sai iyayen suka amsa masu, "Mun san wannan yaronmu ne kuma a makaho aka haife shi.
\v 21 Yadda ya ke gani yanzu, bamu sani ba, kuma wanda ya bude masa idanu, bamu sani ba. Ku tambaye shi, ba yaro ba ne. Zai iya magana don kansa."
\s5
\v 22 Iyayensa sun fadi wadannan abubuwan, domin suna ji tsoron Yahudawan. Gama Yahudiyawan sun rigaya sun yarda duk wanda yace Yesu Almasihu ne, za a fitar dashi daga majami'a.
\v 23 Domin wannan ne, iyayensa suka ce, "Ai shi ba yaro ba ne, ku tambaye shi."
\s5
\v 24 Suka sake kiran mutumin dake makaho karo na biyu, suka ce masa, "Ka girmama Allah. Mu kam mun sani wannan mutum mai zunubi ne."
\v 25 Sai wannan mutum ya amsa, "Ban sani ba ko shi mai zunubi ne. Abu guda daya na sani: da Ni makaho ne, amma yanzu ina gani."
\s5
\v 26 Sai su ka ce masa, "Me ya yi maka? Ta yaya ya bude idanunka?"
\v 27 Ya amsa, "Na rigaya na gaya maku, amma ba ku ji ba! Don me kuke so ku sake ji? Ko kuma kuna so ku zama almajiransa, haka ne?
\s5
\v 28 Sai suka kwabe shi suka ce, "kai ne almajirinsa, amma mu almajiran Musa ne.
\v 29 Mun sani Allah ya yi magana da Musa, amma wannan mutum, bamu san ko daga ina ne ya zo ba."
\s5
\v 30 Mutumin ya amsa masu ya ce, "Tirkashi, baku san inda ya fito ba, duk da haka shi ya bude mani idanu.
\v 31 Mun san da cewa Allah baya jin masu zunubi, amma idan wani mai ibada ne yana kuma yin nufinsa, to yana jin sa.
\s5
\v 32 Tunda duniya ta fara ba a taba jin cewa wani ya bude idanun wanda aka haifa makaho ba.
\v 33 In mutumin nan ba daga Allah yake ba, ba zai iya yin komai ba."
\v 34 Suka amsa suka ce masa, "an haife ka cikin zunubai, yanzu kana so ka yi mana koyarwa?" Sai suka fitar da shi.
\s5
\v 35 Yesu ya ji cewa sun fitar da shi daga majami'a. Da ya same shi sai ya ce masa, "Kana bada gaskiya ga Dan Allah?"
\v 36 Sai ya amsa masa yace, "Wanene shi, Ubangiji, da zan bada gaskiya gare shi?"
\v 37 Yesu yace masa, "Ai ka gan shi, shine wanda yake magana da kai."
\v 38 Mutumin ya ce, "Ubangiji, Na bada gaskiya." Sai ya yi masa sujada.
\s5
\v 39 Yesu ya ce, "Don hukunci na zo wannan duniya domin wadanda ba su gani su gani, saboda kuma wadanda suke gani su zama makafi."
\v 40 Wadansu Farisawa wadanda suke tare da shi suka ji wadannan abubuwan, suka tambaye shi, "Muma makafi ne?"
\v 41 Yesu ya ce masu, "Inda ku makafi ne, da ba ku da zunubi, amma yanzu kun ce, 'Muna gani', don haka zunubinku ya tabbata.
\s5
\c 10
\p
\v 1 "Hakika, Hakika, ina ce maku, wanda bai shiga ta kofa zuwa garken tumaki ba, amma ya haura ta wata hanya, wannan mutum barawo ne da dan fashi.
\v 2 Wanda ya shiga ta kofa shine makiyayin tumakin.
\s5
\v 3 Mai gadin kofar zai bude masa. Tumakin suna jin muryarsa, ya na kuma kiran tumakinsa da sunayensu, ya kuma kai su waje.
\v 4 Bayanda ya kawo su duka a waje, yana tafiya a gabansu, sai tumakin su bi shi, domin sun san muryarsa.
\s5
\v 5 Ba za su bi bako ba amma sai dai su guje shi, domin basu san muryar baki ba."
\v 6 Yesu ya yi masu magana da wannan misali, amma basu gane wadannan abubuwa da yake gaya masu ba.
\s5
\v 7 Sai Yesu ya ce masu kuma, "Hakika, Hakika, Ina ce maku, Ni ne kofar tumaki.
\v 8 Dukan wadanda suka zo kamin ni barayi ne da yan fashi, amma tumakin ba su ji su ba.
\s5
\v 9 Ni ne kofa, In kowa ya shiga ta wurina, zai sami ceto, zai shiga ya fita ya kuma sami wurin kiwo.
\v 10 Barawo ba ya zuwa sai don ya yi sata, ya kashe, ya kuma hallakar. Na zo ne domin su sami rai su kuma same shi a yalwace.
\s5
\v 11 Ni ne makiyayi mai kyau. Makiyayi mai kyau yana bada ransa domin tumakinsa.
\v 12 Wanda yake dan sako kuma, ba makiyayi ba, wanda ba shine mai tumakin ba, in ya ga kyarkeci na zuwa sai ya saki tumakin ya gudu. Sai kyarkecin ya dauke su ya kuma warwatsa su.
\v 13 Ya gudu domin shi mai aikin kudi ne kuma bai damu da tumakin ba.
\s5
\v 14 Nine makiyayi mai kyau, na kuma san nawa, nawa kuma sun san ni.
\v 15 Uban ya san ni, ni ma na san Uban, na kuma bada raina domin tumakin.
\v 16 Ina da wadansu tumaki wadanda ba na wannan garken ba. Wadannan, kuma, dole in kawo su, su ma za su ji muryata saboda za su zama garke daya da makiyayi daya.
\s5
\v 17 Domin wannan ne Uban yake kauna ta: Na bada raina domin in same shi kuma.
\v 18 Babu wanda zai dauke shi daga wurina, amma ina bayar da shi da kaina. Ina da ikon bada shi, ina da iko in dauke shi kuma. Na karbi wannan umarnin daga wurin Ubana."
\s5
\v 19 Tsattsaguwa ta sake tashi tsakanin Yahudawa domin wadannan kalmomin.
\v 20 Dayawa a cikinsu suka ce, yana da aljani, kuma mahaukaci ne. Don me ku ke sauraronsa?"
\v 21 Wadansu suka ce, wadannan ba kalmomin wanda yake da aljani ba ne. Ko mai aljani zai iya bude idanun makaho?"
\s5
\v 22 Sai lokacin idin Tsarkakewa a Urushalima ya zo.
\v 23 A lokacin damuna ne, Yesu kuwa yana tafiya a shirayi cikin haikalin Sulaimanu.
\v 24 Sai Yahudawa suka zagaye shi suka ce masa, "Har yaushe ne za ka bar mu cikin shakka? In kai ne Almasihun, ka gaya mana dalla-dalla."
\s5
\v 25 Yesu ya ce masu, "Na gaya maku, amma baku gaskata ba. Ayyukan da nake yi a cikin sunan Ubana, su ke yin shaida a kaina.
\v 26 Duk da haka baku gaskata ba domin ku ba tumakina ba ne.
\s5
\v 27 Tumakina suna jin murya ta; Na san su, suna kuma bi na.
\v 28 Ina ba su rai na har abada; ba za su taba mutuwa ba, babu wanda zai kwace su daga hannu na.
\s5
\v 29 Ubana, wanda ya bani su, ya fi kowa girma, kuma ba mai iya kwace su daga hannun Uban.
\v 30 Ni da Uban daya ne."
\v 31 Sai Yahudawa suka dauki duwatsu kuma domin su jajjefe shi.
\s5
\v 32 Yesu ya amsa masu, "Na nuna maku kyawawan ayyuka masu yawa daga wurin Uban. Saboda wane daga cikin wadannan ayyukan kuke jefe ni?"
\v 33 Sai Yahudawa suka amsa masa, "ba don wani aiki mai kyau muke son mu jefe ka ba, amma don sabo, domin kai, mutum ne, amma kana mayar da kanka Allah."
\s5
\v 34 Yesu ya amsa masu, "Ba a rubuce yake a shari'arku ba, 'Na ce, "ku alloli ne"'?"
\v 35 In ya kira su alloli, su wadanda maganar Allah ta zo gare su (kuma ba za a iya karya nassi ba),
\v 36 kuna gaya wa wanda Uban ya kebe ya kuma aiko cikin duniya, 'Kana sabo', domin Na ce, 'Ni dan Allah ne'?
\s5
\v 37 In ba na aikin Ubana, kada ku gaskata ni.
\v 38 Amma, idan ina yin su, ko ba ku gaskata da ni ba, ku gaskata da ayyukan saboda ku sani, ku kuma gane cewa Uban yana ciki na, ni kuma ina cikin Uban."
\v 39 Suka sake kokarin kama shi, amma ya yi tafiyarsa, ya fita daga hannunsu.
\s5
\v 40 Ya yi tafiyarsa kuma har gaba da kogin Urdun zuwa inda Yahaya ke yin baftisma ada, ya kuma zauna a wurin.
\v 41 Mutane masu yawa suka zo wurinsa, suka ce,"Hakika Yahaya bai yi wasu alamu ba, amma dukan abubuwan da Yahaya ya ce game da wannan mutum gaskiya ne."
\v 42 Mutane dayawa suka bada gaskiya gare shi a wurin.
\s5
\c 11
\p
\v 1 To wani mutum mai suna Li'azaru, yayi rashin lafiya. Shi mutumin Baitanya ne, wato kauyen su Maryamu da 'yar'uwarta Matta.
\v 2 Wato wannan Maryamu da ta shafe Ubangiji da mur ta kuma share masa kafafunsa da gashin kanta, wadda dan'uwanta Li'azaru ke rashin lafiya.
\s5
\v 3 'Yan'uwannan mata suka aika sako wurin yesu, cewa, "Ubangiji, duba, shi wanda kake kauna yana rashin lafiya".
\v 4 Da Yesu ya ji, sai ya ce "Wannan ciwo ba zai kai ga mutuwa ba, amma domin daukakar Allah ne, domin Dan Allah ya sami daukaka tawurin ta".
\s5
\v 5 Yesu yana kaunar Matta, da 'yar'uwarta da Li'azaru.
\v 6 Da yaji cewa Li'azaru na rashin lafiya, sai ya tsaya kwana biyu a inda ya ke.
\v 7 Bayan haka, sai ya ce wa almajiransa, "Bari mu je Yahudiya kuma."
\s5
\v 8 Sai almajiransa suka ce masa, "Mallam, harwayau Yahudaya na neman ka domin su jefe ka da duwatsu, kuma kana son komawa can?"
\v 9 Yesu ya amsa, "Ba sa'a goma sha biyu ce ta haske a rana guda ba? Idan mutum ya yi tafiya da rana, ba za ya yi tuntube ba, domin yana gani ta wurin hasken wannan duniya.
\s5
\v 10 Amma idan mutum ya yi tafiya chikin dare, za ya yi tuntube domin haske ba ya tare da shi.
\v 11 Ya fadi wadannan al'amura, kuma bayan wadannan abubuwa, sai ya ce masu, "Abokinmu Li'azaru ya yi barci, amma zan je don In tashe shi daga barci".
\s5
\v 12 Sai almajirai suka ce masa, "Ubangiji, idan barci yake yi, ai za ya farka."
\v 13 Yesu kuwa ya yi maganar mutuwar Li'azaru ne, amma su suna tsammani yana magana akan barci ne na hutu.
\v 14 Sai Yesu ya yi masu bayani cewa, "Li'azaru ya mutu.
\s5
\v 15 Ina farinchiki domin ku, da bani a wurin domin ku gaskata. Bari mu je wurinsa."
\v 16 Toma wanda ake kira Dan tagwaye, ya ce wa sauran almajirai, "Bari mu tafi domin mu mutu tare da Yesu."
\s5
\v 17 Da Yesu ya iso, sai ya tarar cewa Li'azaru ya rigaya ya yi kwana hudu a kabari.
\v 18 Baitanya kuma tana kusa da Urushalima, 'yar tafiya marar nisa ce a tsakanin su.
\v 19 Yahudawa dayawa sun zo wurin Maryamu da Matta domin su yi masu ta'aziyar mutuwar dan'uwansu.
\v 20 Da Matta ta ji cewa Yesu na zuwa, sai ta tafi domin ta same shi, amma Maryamu na zamne a cikin gida.
\s5
\v 21 Matta ta ce wa Yesu, "Ubangiji, da kana nan tare da mu, da dan'uwana baya mutu ba".
\v 22 Ko yanzu na san cewa duk abinda ka roka a wurin Allah, za ya ba ka.
\v 23 Yesu ya ce mata, "Dan'uwanki za ya rayu kuma.
\s5
\v 24 Sai Matta ta ce masa, "Na san zaya rayu kuma a tashin mattatu na ranar karshe."
\v 25 Yesu ya ce mata, "Ni ne tashin matattu, ni ne kuma rai; wanda ya bada gaskiya gare ni, ko ya mutu, za ya rayu;
\v 26 Kuma duk wanda yake raye, ya kuma bada gaskiya gare ni, ba zai mutu ba dadai. Kin gaskata da wannan?"
\s5
\v 27 Sai ta ce masa, "I, Ubangiji, Na gaskata cewa kaine Almasihu, Dan Allah, wanda ke zuwa duniya.
\v 28 Sa'adda ta fadi haka, sai ta koma ta kira yar'uwarta Maryamu gefe guda. Ta ce, "mallam ya iso, kuma yana kiran ki."
\v 29 Da ta ji haka, sai ta tashi da sauri ta tafi wurin sa.
\s5
\v 30 Yesu bai rigaya ya shiga kauyen ba, yana nan inda Matta ta zo ta same shi.
\v 31 Da Yahudawan nan dake tare da Maryamu, wato wadannan da suka zo mata ta'aziya, suka ga ta fita daga chikin gida da sauri, sai suka bi ta, suna tsammanin cewa ta tafi ta yi kuka ne a kabari.
\v 32 Da Maryamu ta kai inda Yesu ya ke, sai ta fadi gaban sawayensa, ta ce, "Ubangiji, inda kana tare da mu, da dan'uwana bai mutu ba".
\s5
\v 33 Da Yesu ya gan ta tana kuka, da wadannan Yahudawa da suka bi ta, sai ya yi juyayi a ruhu ya damu kuma;
\v 34 sai ya ce, "A ina kuka kwantar da shi?" Sai suka ce masa, "Ubangiji, zo ka gani."
\v 35 Yesu ya yi kuka.
\s5
\v 36 Sai Yahudawa suka ce, "Dubi yadda yake kaunar Li'azaru!"
\v 37 Amma wadansun su suka ce, "Shi wannan mutum da ya iya ba makaho ganin gari, da bai iya hana wannan mutum mutuwa ba?
\s5
\v 38 Yesu yana cikin juyayi kuma a cikin kansa, sai ya tafi kabarin. Kabarin a kogo ne an kuma rufe bakinsa da dutse.
\v 39 Sai Yesu ya ce, "A kawar da dutsen." Matta yar'uwar Li'azaru wanda ya mutu, ta ce wa Yesu, "Ubangiji, Yanzu jikin ya ruba domin ya kai kwana hudu da mutuwa".
\v 40 Yesu ya ce mata, "Ba na ce maki idan kin gaskata za ki ga daukakar Allah ba?"
\s5
\v 41 Sai suka kawar da dutsen. Yesu ya daga idanunsa ya ce, "Uba, na gode maka domin kana ji na."
\v 42 Na san kana ji na a kowane lokaci, amma domin wannan taro da ke tsaye kewaye da ni nike wannan magana, domin su bada gaskiya cewa kaine ka aiko ni."
\s5
\v 43 Bayan ya yi wannan magana, sai ya daga murya ya ce, "Li'azaru, ka fito!"
\v 44 Sai mataccen ya fito; kafafunsa da hannayensa na daure da likkafani, fuskarsa kuma na lullube da tsumma. Yesu ya ce masu, "Ku kwance shi, ya tafi".
\s5
\v 45 To dayawa daga cikin yahudawan da suka zo wurin Maryamu suka kuma ga abinda Yesu ya yi, suka gaskata da shi;
\v 46 amma wadansu suka koma wurin farisawa suka fada masu abubuwan da Yesu ya yi.
\s5
\v 47 Sai manyan firistoci da farisawa suka tara majalisa wuri guda, suka ce, "menene za mu yi?" Mutumin nan yana alamu masu yawa.
\v 48 Idan mun kyale shi haka, duka za su gaskata da shi; Romawa za su zo su kwace wurinmu da al'ummar mu.
\s5
\v 49 Duk da haka, wani daga cikin su wato, Kayafas wanda shine babban firist a wannan shekara, ya ce da su, "baku san komai ba".
\v 50 Ba ku lura cewa ya fi maku kyau mutum daya ya mutu domin mutane, a maimakon dukan al'umma ta hallaka."
\s5
\v 51 Ya fadi wannan ne ba don kansa ba, amma sabo da shine babban firist, ya yi anabci ne cewa ya kamata Yesu ya mutu domin al'ummar;
\v 52 kuma ba don alummar kawai ba, amma domin a tattara 'ya'yan Allah da suke warwatse ko'ina wuri daya.
\v 53 Tun daga wannan rana suka fara neman hanyar da za su kashe Yesu.
\s5
\v 54 Tun daga nan Yesu ya dena tafiya a sarari chikin Yahudawa, amma sai ya koma wani yanki kusa da jeji a wani gari da ake kira Ifraimu. A can kuma ya zamna da almajiransa.
\v 55 Idin ketarewa na Yahudawa ya yi kusa, da yawa sun tafi Urushalima daga yankin kasar kamin ranar idi domin su tsarkake kan su.
\s5
\v 56 Suka shiga neman Yesu, suna magana da junan su yayin da suke tsaitsaye a haikali, cewa "me kuke tunani? Ba za ya zo idin bane?"
\v 57 Babban firist da farisawa sun rigaya sun ba da umurni cewa duk inda aka ga Yesu a zo a shaida domin su kama shi.
\s5
\c 12
\p
\v 1 Kwana shidda kafin idin ketarewa, Yesu ya zo Baitanya inda Li'azaru yake, wato wannan da Yesu ya tada daga matattu.
\v 2 Sai suka shirya masa abinci a wurin kuma Matta ce ke hidima, Li'azaru kuwa ya kasance cikin wadanda ke kan tebiri tare da Yesu.
\v 3 Sai Maryamu ta dauki wani turare da aka yi da man nard, ta shafe kafafun Yesu da shi, ta kuma share kafafun nasa da gashin kanta. Sai gida ya cika da kamshin turaren.
\s5
\v 4 Yahuza Iskariyoti, daya daga cikin almajiransa, wanda zai bashe shi, ya ce, "
\v 5 "Me yasa ba a sayar da wannan turare dinari dari uku a ba gajiyayyu ba?"
\v 6 Ya fadi haka ba don ya damu da gajiyayyu ba, amma domin shi barawo ne: shi ne ma'aji, kuma yana sata daga jakkar kudi.
\s5
\v 7 Yesu ya ce, "Ku kyale ta ta ajiye abinda ta tanada domin jana'iza ta.
\v 8 Gajiyayyu suna tare da ku a koyaushe, ni kuwa ba zan kasance da ku koyaushe ba.
\s5
\v 9 To babban taron Yahudawa sun ji cewa Yesu yana wurin, sai suka zo, ba don Yesu kawai ba amma domin su ga Li'azaru, wanda Yesu ya tada daga matattu.
\v 10 Sai manyan firistoci suka kulla makirci akan yadda za su kashe Li'azaru shima;
\v 11 domin saboda shi ne yahudawa dayawa suka je suka bada gaskiya ga Yesu.
\s5
\v 12 Kashegari, babban taro suka zo idin. Da suka ji cewa Yesu na zuwa Urushalima,
\v 13 Sai suka dauki ganyen dabino suka fita gari suka tare shi da kira mai karfi suna cewa, "Hosanna! Mai albarka ne wanda yake zuwa cikin sunan Ubangiji, Sarkin Isra'ila.
\s5
\v 14 Yesu ya sami wani Aholakin jaki, ya hau kansa; kamar yadda aka rubuta,
\v 15 "Kada ki ji tsoro ke 'yar Sihiyona; duba, ga Sarkinki na zuwa, zaune a kan danJaki".
\s5
\v 16 Almajiransa basu fahimci wannan al'amari ba da farko, amma bayan da aka daukaka Yesu, sai suka tuna cewa an rubuta wadannan abubuwa game da shi, kuma sun yi masa wadannan abubuwa.
\s5
\v 17 Sai taron da ke tare da Yesu a ranar da ya kira Li'azaru daga kabari ya kuma tashe shi daga matattu, suka bada shaida.
\v 18 Domin wannan ne kuma taron suka zo domin su sadu da shi saboda sun ji cewa ya yi wannan alama.
\v 19 Don haka, sai farisawa suka shiga magana a tsakanin su suna cewa "Duba, babu abinda zaku iya yi; kun ga, duniya ta gama bin sa.
\s5
\v 20 Akwai wadansu Helinawa cikin wadanda suka je sujada a idin.
\v 21 Wadannan suka tafi wurin filibus, mutumin Betsaida da ke Galili, suka ce masa, "Mallam, muna so mu ga Yesu.
\v 22 Filibus ya tafi ya fadawa Andrawus; sai Andrawus ya tafi tare da Filibus, suka kuwa gaya wa Yesu.
\s5
\v 23 Yesu ya amsa masu ya ce, "sa'a ta zo da za'a daukaka Dan mutum.
\v 24 Hakika, hakika, Ina ce maku, in ba kwayar alkama ta fadi kasa ba ta mutu, za ta kasance ita kadai; amma idan ta mutu, za ta bada 'ya'ya masu yawa.
\s5
\v 25 Duk wanda yake son ransa, zai rasa shi; amma wanda ba ya son ransa a duniyan nan za ya kiyaye shi domin rayuwa ta har abada.
\v 26 Idan wani na bauta mani, to bari ya biyo ni; kuma duk inda nike, a can bawana zai kasance kuma. Duk wanda ke bauta mani, Uban zai girmama shi.
\s5
\v 27 Yanzu raina na cikin damuwa, to me zan ce? 'Uba, ka cece ni daga wannan sa'a? Amma Saboda wannan dalili ne na zo wannan sa'a.
\v 28 Uba, ka daukaka sunanka". Sai wata murya daga sama ta ce, "Na daukaka shi, zan kuma sake daukaka shi.
\v 29 Daganan sai taron dake tsaye kuma suka ji muryar, suka ce an yi tsawa. Wasu suka ce, "Mala'ika ya yi magana da shi".
\s5
\v 30 Yesu ya amsa ya ce, "wannnan murya ta zo ba saboda ni ba, amma domin ku."
\v 31 Yanzu za'a shar'anta duniya. Yanzu za'a kori mai mulkin duniyan nan.
\s5
\v 32 Sa, annan ni, idan an daga ni daga duniya, zan jawo dukan mutane zuwa gare ni".
\v 33 Ya fadi wannan ne domin ya nuna irin mutuwar da za ya yi.
\s5
\v 34 Taro suka amsa masa cewa, "Mun ji a cikin shari'a cewa Almasihu za ya kasance har abada. Yaya za ka ce, 'za'a daga dan mutum'? Wanene wannan dan mutum?"
\v 35 Yesu ya ce masu, "Nan da lokaci kadan za ku kasance da haske, ku yi tafiya tun haske na tare da ku, kada duhu ya mamaye ku. Wanda ke tafiya cikin duhu, bai san inda za shi ba.
\v 36 Ku gaskata ga haske tun yana tare da ku domin ku zama yayan haske". Yesu ya fadi wadannan abubuwa sannan ya tafi ya boye masu.
\s5
\v 37 Kodashike Yesu ya yi alamu da dama a gabansu, duk da haka ba su gaskata shi ba.
\v 38 Saboda maganar annabi Ishaya ta cika, wadda ya ce, "Ubangiji, wa ya gaskata rahoton mu? Ga wa kuma hannun Ubangiji ya bayyana?
\s5
\v 39 Saboda wannan dalili basu gaskata ba, gama Ishaya ya sake cewa,
\v 40 ya makantar da su, ya kuma taurare zuciyarsu, saboda kada su gani da idanunsu, su kuma sami fahimta da zuciyarsu, su juyo wurina in warkar da su.
\s5
\v 41 Ishaya ya fadi wadannan abubuwa ne domin ya hangi daukakar Yesu ya kuma yi magana game da shi.
\v 42 Amma duk da haka, dayawa cikin shugabanni suka gaskata Yesu. Amma saboda farisawa, basu shaida shi a sarari ba, domin kada a kore su daga majami'a.
\v 43 Suna son yabo daga mutane fiye da yabon dake zuwa daga Allah.
\s5
\v 44 Yesu ya yi magana da babbar murya, ya ce, "Wanda ya gaskata ni, ba ni yake gaskatawa kadai ba, amma kuma yana gaskata wanda ya aiko ni,
\v 45 kuma wanda ke gani na, yana ganin shi wanda ya aiko ni.
\s5
\v 46 Na zo ne a matsayin haske a duniya, saboda duk wanda ya gaskata da ni ba za ya yi tafiya cikin duhu ba.
\v 47 Duk wanda ya ji maganata baya gaskata ba, ba ni hukunta shi; gama ban zo in yi wa duniya hukunci ba, amma don in ceci duniya.
\s5
\v 48 Wanda ya ki ni, ya kuma ki ya karbi magana ta, akwai wanda za ya yi masa hukunci. Kalmar da na fada, ita ce za ta yi masa hukunci a rana ta karshe.
\v 49 Maganar da ni ke yi, ba ra'ayina ba ne. Amma Uba wanda ya aiko ni shi ke bani umarni game da abin da zan ce da abin da zan fadi.
\v 50 Na san umarninsa rai ne madawwami, don haka na ce - kamar yadda Uba ya fada, haka ni ma nake fadi."
\s5
\c 13
\p
\v 1 Kamin bukin idin ketarewa, sa'adda Yesu ya san lokaci ya yi da zai tashi daga wannan duniya zuwa wurin Uba, da yake ya kaunaci nasa wadanda ke duniya- ya kaunace su har karshe.
\v 2 Iblis ya rigaya ya sa a zuciyar Yahuza Iskariyoti dan Saminu, ya bashe da Yesu.
\s5
\v 3 Ya san cewa Uba ya bada kome a hannunsa, kuma ya zo daga wurin Allah, kuma zai koma wurin Allah.
\v 4 Ya tashi daga cin abincin, ya tube tufafinsa, ya dauki tawul ya lullube kansa da shi.
\v 5 Sa'an nan ya zuba ruwa a bangaji, ya fara wanke kafafun almajiran, yana shafe su da tawul din da ya lullube jikinsa da shi.
\s5
\v 6 Ya zo wurin Bitrus Saminu, sai Bitrus ya ce masa,"Ubangiji, za ka wanke mani kafa?"
\v 7 Yesu ya amsa ya ce, "Abin da nake yi ba za ka fahimce shi yanzu ba, amma daga baya za ka fahimta."
\v 8 Bitrus ya ce masa, "Ba za ka taba wanke mani kafa ba." Yesu ya amsa masa ya ce, "In ban wanke maka ba, ba ka da rabo da ni".
\v 9 Bitrus ya ce masa, "Ubangiji, ba kafafuna kadai za ka wanke ba, amma da hannayena da kaina."
\s5
\v 10 Yesu ya ce masa, "Duk wanda ya yi wanka ba ya da bukata, sai dai a wanke kafafunsa, amma shi tsarkakakke ne baidaya; ku tsarkakakku ne, amma ba dukanku ba."
\v 11 (Don Yesu ya san wanda zai bashe shi, shiyasa ya ce, "Ba dukanku ne ke da tsarki ba.")
\s5
\v 12 Bayan Yesu ya wanke masu kafafu, ya dauki tufafinsa ya zauna kuma, ya ce masu, "Kun san abin da na yi muku?
\v 13 kuna kirana, 'Malam, da Ubangiji,' kun fadi daidai, don haka Nake.
\v 14 Idan ni Ubangiji da kuma mallam, na wanke maku kafafu, ya kamata kuma ku wanke wa junan ku kafafu.
\v 15 Gama na baku misali, saboda ku yi yadda na yi maku.
\s5
\v 16 Lalle hakika ina gaya muku, bawa ba ya fi mai gidansa girma ba; dan aike kuma ba ya fi wanda ya aiko shi girma ba.
\v 17 Idan kun san wadannan abubuwa, ku masu albarka ne idan kun aikata su.
\v 18 Ba ina magana akan dukanku ba; Na san wadanda na zaba. Amma domin Nassi ya cika: 'Shi Wanda ya ci gurasata, ya tayar mani'.
\s5
\v 19 Ina fada maku wannan yanzu tun kafin haka ta faru domin sa'adda ta faru, ku gaskata Ni ne.
\v 20 Hakika, hakika, Ina gaya maku, wanda ya karbi wanda na aiko, Ni ya karba, wanda kuma ya karbe ni, ya karbi wanda ya aiko ni.
\s5
\v 21 Bayan Yesu ya fadi haka, ya damu a ruhu, ya yi shaida ya ce, "Lalle hakika, ina gaya muku cewa daya daga cikinku zai bashe ni."
\v 22 Almajiran suka kalli juna, suna juyayin ko akan wa yake magana.
\s5
\v 23 Daya daga cikin almajiransa, wanda Yesu yake kauna, yana a teburi, jingine a kirjin Yesu.
\v 24 Siman Bitrus ya ce wa almajirin, "ka fada mana ko akan wa ya ke magana."
\v 25 Sai ya sake jingina a kirjin Yesu, ya ce masa, "Ubangiji, wanene?"
\s5
\v 26 Sannan Yesu ya amsa, "Shine wanda zan tsoma gutsuren gurasa in ba shi." Sannan bayan ya tsoma gurasar, sai ya ba Yahuza Dan Siman Iskariyoti.
\v 27 To bayan gurasar, sai shaidan ya shige shi, sai Yesu ya ce masa, "Abinda kake yi, ka yi shi da sauri."
\s5
\v 28 Babu wani a teburin da ya san dalilin dayasa ya fada masa wannan.
\v 29 Wadansu sun yi tsamanin cewa, tun da Yahuza ne ke rike da jakkar kudi, Yesu ya ce masa, "Ka sayi abinda muke bukata don idin", ko kuma ya bada wani abu domin gajiyayyu.
\v 30 Bayan Yahuza ya karbi gurasar, sai ya fita nan da nan. Da daddare ne kuwa.
\s5
\v 31 Bayan Yahuza ya tafi, Yesu ya ce, "Yanzu an daukaka Dan mutum, kuma an daukaka Allah a cikinsa.
\v 32 Allah zai daukaka shi a cikin kansa, kuma zai daukaka shi nan da nan.
\v 33 'Ya'ya kanana, ina tare da ku na wani gajeren lokaci. Zaku neme ni, kuma kamar yadda na fadawa Yahudawa, 'in da zan tafi ba za ku iya zuwa ba.' Yanzu kuma na fada maku wannan.
\s5
\v 34 Ina baku sabuwar doka, ku kaunaci juna; kamar yadda na kaunace ku, haka kuma ku kaunaci juna.
\v 35 Ta haka kowa zai san ku almajiraina ne, idan kuna kaunar juna."
\s5
\v 36 Siman Bitrus ya ce masa, "Ubangiji, ina za ka?" Yesu ya amsa ya ce, "Inda za ni, ba zaka iya bi na ba yanzu, amma zaka bini daga baya."
\v 37 Bitrus ya ce masa, "Ubangiji, don me ba zan iya binka a yanzu ba? Zan bada raina domin ka."
\v 38 Yesu ya amsa ya ce, "Za ka bada ranka domina? Lalle hakika, ina gaya maka, kafin zakara ya yi cara zaka yi musu na sau uku."
\s5
\c 14
\p
\v 1 "Kada zuciyarku ta bachi. Kun gaskata da Allah, sai kuma ku gaskata da ni.
\v 2 A gidan Ubana akwai wurin zama dayawa. Da ba haka ba, da na fada maku, domin zan tafi in shirya maku wuri.
\v 3 In kuwa na je na shirya maku wuri, zan dawo in karbe ku zuwa wurina domin inda nake kuma ku kasance.
\s5
\v 4 Kun san hanya inda zan tafi."
\v 5 Toma ya ce wa Yesu, "Ubangiji, bamu san inda za ka tafi ba, yaya za mu san hanyar?"
\v 6 Yesu ya ce masa, "Ni ne hanya, ni ne gaskiya, ni ne rai; Ba mai zuwa wurin Uba sai ta wurina.
\v 7 Da kun san ni, da kun san Ubana kuma. Amma daga yanzu kun san shi, kuma kun gan shi."
\s5
\v 8 Filibus ya ce wa Yesu, "Ubangiji, ka nuna mana Uban, wannan za ya ishe mu."
\v 9 Yesu ya ce masa, "Ina tare da ku da dadewa, amma har yanzu baka san ni ba, Filibus? Duk wanda ya gan ni, ya ga Uban. Yaya za ka ce, 'Nuna mana Uban'?
\s5
\v 10 Baka gaskata cewa Ina cikin Uban, Uban kuma yana ciki na ba? Maganganun da nake fada maku, ba da ikona nake fadi ba, amma Uban ne da yake zaune a ciki na yake yin ayyukansa.
\v 11 Ku gaskata ni cewa ina cikin Uban, Uban kuma na ciki na, ko kuwa ku bada gaskiya domin ayyukan kansu.
\s5
\v 12 "Lalle hakika, ina gaya maku, duk wanda ya gaskata ni zai yi ayyukan da nake yi, kuma zai yi ayyuka fiye da wadannan, domin zan tafi wurin Uba.
\v 13 Duk abinda kuka roka da sunana, zan yi shi domin a daukaka Uban cikin Dan.
\v 14 Idan kuka roke ni komai cikin sunana, zan yi shi.
\s5
\v 15 "Idan kuna kaunata, za ku kiyaye dokokina.
\v 16 Sa, annan zan yi addu'a ga Uba, zai kuwa baku wani mai ta'aziya domin ya kasance tare daku har abada.
\v 17 Ruhun gaskiya. Wanda duniya ba zata iya karba ba, domin bata gan shi ba, ko ta san shi. Amma ku kun san shi, domin yana tare da ku, zai kuma kasance a cikin ku.
\s5
\v 18 Ba zan barku ku kadai ba; zan dawo wurin ku.
\v 19 Sauran dan gajeren lokaci, duniya kuma ba zata ka ra gani na ba, amma ku kuna gani na. Saboda ina raye, kuma zaku rayu.
\v 20 A wannan rana zaku sani ina cikin Ubana, ku kuma kuna ciki na, ni ma ina cikin ku.
\s5
\v 21 Shi wanda yake da dokokina yake kuma bin su, shine ke kauna ta, kuma shi wanda ke kauna ta Ubana zai kaunace shi, Ni ma kuma zan kaunace shi in kuma bayyana kaina gare shi."
\v 22 Yahuza (ba Iskariyoti ba) ya ce ma Yesu, "Ubangiji, meyasa za ka bayyana kanka a gare mu, ba ga duniya ba?"
\s5
\v 23 Yesu ya amsa ya ce masa,"Kowa yake kauna ta, zai kiyaye maganata. Ubana kuwa zai kaunace shi, za mu zo wurinsa mu zauna tare da shi.
\v 24 Shi wanda baya kauna ta, ba ya kiyaye maganganuna. Maganar da kuke ji ba daga gareni take ba, amma daga Uba wanda ya aiko ni take.
\s5
\v 25 Na fada maku wadannan abubuwa, sa'adda nake tare da ku.
\v 26 Saidai, mai ta'aziyar- Ruhu Mai Tsarki wanda Uba zai aiko cikin sunana, zai koya maku kome, kuma zai tunashe ku dukan abinda na fada maku.
\v 27 Na bar ku da salama; ina ba ku salamata. Ba kamar yadda duniya ke bayarwa Nake bayarwa ba. Kada zuciyarku ta baci, kuma kada ku tsorata.
\s5
\v 28 Kun ji dai na fada maku, 'zan tafi, kuma Zan dawo gare ku'. Idan kuna kaunata, za ku yi farinciki domin za ni wurin Uban, gama Uban ya fi ni girma.
\v 29 Yanzu na fada maku kafin ya faru, domin idan ya faru, ku gaskata.
\s5
\v 30 Ba zan kara magana mai yawa da ku ba, domin mai mulkin duniyan nan yana zuwa. Bashi da iko a kai na,
\v 31 amma domin duniya ta san cewa ina kaunar Uban, Ina yin daidai abinda Uban ya Umarce ni. Mu tashi mu tafi daga nan.
\s5
\c 15
\p
\v 1 "Nine itacen inabi na hakika, Ubana kuwa shi ne manomin.
\v 2 Yakan cire duk wani rashe a cikina da ba ya bada 'ya'ya, mai bada 'ya'ya kuwa ya kan gyara shi domin ya kara bada 'ya'ya.
\s5
\v 3 Kun rigaya kun tsarkaka saboda maganar da na yi muku.
\v 4 Ku zauna ciki na, Ni kuma cikin ku. Kamar yadda reshe ba ya iya bada 'ya'ya shi kadai sai ya zauna cikin itacen, haka kuma ba za ku iya ba, sai kun zauna ciki na.
\s5
\v 5 Ni ne itacen inabi, ku ne rassan. Wanda ya zauna ciki na, ni kuma cikin sa, yana bada 'ya'ya dayawa, gama in ba tare da ni ba, ba za ku iya yin kome ba.
\v 6 Wanda kuma bai zauna a ciki na ba, akan jefar da shi kamar reshe, ya bushe, kuma sukan tattara rassan su jefa a wuta, su kone.
\v 7 In kun zauna a ciki na, maganata kuma ta zauna a cikin ku, sai ku roki duk abinda kuke so, za a kuwa yi maku.
\s5
\v 8 Ta haka ake daukaka Ubana: cewa ku bada 'ya'ya dayawa, kuma cewa ku almajiraina ne.
\v 9 Kamar yadda Ubana ya kaunace ni, haka Ni ma na kaunace ku; Ku zauna cikin kaunata.
\s5
\v 10 Idan kun kiyaye dokokina, za ku zauna cikin kaunata kamar yadda Na kiyaye dokokin Ubana, na kuma zauna cikin kaunarsa.
\v 11 Ina gaya maku wadannan al'amura domin farincikina ya kasance a cikin ku, kuma domin farincikinku ya zama cikakke.
\s5
\v 12 "Wannan shine umarnina, cewa ku kaunaci juna kamar yadda na kaunace ku.
\v 13 Babu wanda ke da kaunar da tafi haka, wato ya bada ransa domin abokansa.
\s5
\v 14 Ku abokaina ne idan kuna yin abubuwan da na umarce ku.
\v 15 Nan gaba ba zan kara ce da ku bayi ba, don bawa bai san abinda Ubangijinsa ke yi ba. Na kira ku abokaina, domin na sanar da ku duk abinda na ji daga wurin Ubana.
\s5
\v 16 Ba ku kuka zabe ni ba, amma Ni ne na zabe ku, na aike ku don ku je ku bada 'ya'ya, 'ya'yanku kuma su tabbata. Wannan ya zama domin duk abinda kuka roki Uba a cikin sunana, zai baku.
\v 17 Na baku wannan umarni: domin ku kaunaci juna.
\s5
\v 18 In duniya ta ki ku, ku sani cewa ta kini kafin ta ki ku.
\v 19 Da ku na duniya ne, da duniya ta kaunace ku kamar nata. Amma saboda ku ba na duniya bane, na kuma zabe ku daga duniya, don haka duniya take kin ku.
\s5
\v 20 Ku tuna da maganar da na yi muku, 'Bawa ba ya fi Ubangijinsa girma ba.' Idan sun tsananta mani, ku ma za su tsananta maku; Idan sun kiyaye maganata, za su kuma kiyaye maganarku.
\v 21 Za su yi maku duk wadannan abubuwa saboda sunana, don basu san wanda ya aiko ni ba.
\v 22 Da ban zo na yi masu magana ba, da basu da zunubi, amma yanzu, basu da wata hujja don zunubinsu.
\s5
\v 23 Duk wanda ya ki ni ya ki Ubana.
\v 24 Da ban yi ayyukan da babu wanda ya taba yinsu a cikin su ba, da basu da zunubi, amma yanzu sun gani, sun kuma ki ni da Ubana duka.
\v 25 An yi wannan kuwa domin a cika maganar da ke rubuce a cikin shari'arsu, ' Sun ki ni ba dalili.'
\s5
\v 26 Sa'adda Mai Ta'aziya- wanda zan aiko maku daga wurin Uban, wato, Ruhun gaskiya, wanda ke fita daga wurin Uban-ya zo, zai bada shaida a kai na.
\v 27 Ku ma kuna bada shaida saboda kuna tare da ni tun daga farko.
\s5
\c 16
\p
\v 1 "Na fada maku wannan ne domin kada kuyi tuntube.
\v 2 Zasu fitar da ku daga majami'u. Amma, sa'a tana zuwa, wadda idan wani ya kasheku, zai yi zaton aikin Allah yake yi.
\s5
\v 3 Za suyi haka ne kuwa domin ba su san Uban ko ni ba.
\v 4 Na fada maku wadannan abubuwa ne domin in lokacin da zasu faru yayi, ku tuna na fada maku." Ban fada maku wadannan abubuwa ba tun da farko, domin ina tare da ku.
\s5
\v 5 Yanzu kuwa za ni wurin wanda ya aiko ni, duk da haka a cikinku, ba wanda ya tambaye ni, 'Ina za ka?'
\v 6 Amma saboda na fada maku wadannan abubuwa, bakin ciki ya cika zuciyarku.
\v 7 Amma ina gaya maku gaskiya: zai fi ye maku in na tafi. Domin in ban tafi ba, Mai Ta'aziyya ba zai zo gare ku ba, in kuwa na tafi, zan aiko shi gare ku.
\s5
\v 8 Idan kuwa ya zo, Mai Ta'aziyyar zai fadarkar da duniya a kan zunubi, da adalci, da kuma hukunci.
\v 9 Game da zunubi, domin basu gaskata da ni ba,
\v 10 Game da adalci, domin za ni wurin Uba, kuma ba za ku sake ganina ba,
\v 11 game da hukunci kuma, domin an yanke wa mai mulki duniyan nan hukunci.
\s5
\v 12 "Akwai abubuwa da yawa da zan gaya maku, amma ba za ku iya fahimta a yanzu ba.
\v 13 Saboda haka, sa'adda Ruhu na gaskiya ya zo, zai bishe ku a cikin dukan gaskiyar, domin ba zai yi magana don kansa ba, sai dai duk abin da ya ji, shi zai fada, zai kuma sanar da ku al'amuran da zasu faru.
\v 14 Zai daukaka ni, domin zai dauko abubuwa dake nawa ya sanar da ku.
\s5
\v 15 Duk abinda Uba yake da shi, nawa ne. Domin wannan ne nace zai dauko abubuwa da yake nawa ya sanar da ku.
\v 16 "Bayan dan lokaci kadan, ba zaku kara ganina kuma ba. bayan dan lokaci kadan kuma, zaku gan ni."
\s5
\v 17 Sai wadansu almajiransa sukace wa juna, "Me nene wannan da yake fadi mana, 'Bayan dan lokaci kadan ba zaku gan ni ba, bayan dan lokaci kadan kuma zaku gan ni?' da kuma, ' zan tafi wurin Uba'?"
\v 18 Saboda haka sukace, "Me nene wannan da yake fada, 'Bayan dan lokaci kadan'? Bamu san abinda yake fada mana ba."
\s5
\v 19 Yesu kuwa ya ga suna so su tambaye shi, sai ya ce masu, "Wato kuna tambayar juna ne abinda nake nufi da cewa, "Bayan dan lokaci kadan ba zaku gan ni ba, bayan dan lokaci kadan kuma zaku gan ni'?
\v 20 Hakika, hakika, ina gaya maku, zaku yi kuka da makoki, amma duniya za ta yi farin ciki, zaku cika da bakin ciki, amma bakin cikinku zai koma farin ciki.
\v 21 Mace takan ji zafi lokacin da take nakuda don lokacin haihuwa ya zo. Amma da zarar ta haifi jinjirin nan, ba ta kara tunawa da zafin, domin ta na fariciki an haifi mutum a duniya.
\s5
\v 22 To yanzu dai kuna bakin ciki, amma zan sake ganinku, kuma ba wanda zai iya kwace maku wannan farin ciki.
\v 23 A rannan, ba zaku tambaye ni komai ba. Hakika hakika, ina gaya maku, komai kuka roki Uba a cikin sunana zai ba ku shi.
\v 24 Harwa yau, ba ku roki komai cikin sunana ba. Ku roka, zaku karba, domin farin cikin ku ya zama cikakke."
\s5
\v 25 "Na fada maku wadannan abubuwa cikin karin magana. Amma sa'a tana zuwa da ba zan kara fada maku komai ba cikin karin magana, amaimakon haka zan gaya maku komai a sarari game da Uba.
\s5
\v 26 A ranar nan, zaku yi roko a cikin sunana kuma bance maku zan yi addu'a ga Uba a madadinku ba,
\v 27 domin Uba da kansa yana kaunarku, domin kun kaunace ni, kun kuma gaskata daga wurin Uban na fito.
\v 28 Daga wurin Uban na fito, kuma na shigo duniya. Har wa yau, kuma zan bar duniya in koma wurin Uba."
\s5
\v 29 Almajiransa sukace, duba, "Yanzu kake magana a sarari, ba cikin karin magana ba!
\v 30 Yanzu mun sani ka san komai, ba sai wani ya tambaye ka ba. Ta haka muka gaskata daga wurin Allah ka fito."
\v 31 Yesu ya amsa masu yace, "Ashe, yanzu kun gaskata?
\s5
\v 32 Duba, sa'a na zuwa, I, sa'ar ta yi, da za a warwatsa ku, kowa ya koma gidansa, kuma ku bar ni ni kadai. Duk da haka kuwa ba ni kadai nake ba, domin Ubana yana tare da ni.
\v 33 Na fada maku wannan ne domin a ciki na ku sami salama. A duniya kuna shan tsanani, amma ku karfafa: na yi nasara da duniya,"
\s5
\c 17
\p
\v 1 Da Yesu ya fadi wandannan abubuwa, sai ya tada idanunsa sama ya ce, ya Uba, sa'a ta zo; ka daukaka Danka, domin Dan shi ya daukaka ka,
\v 2 kamar yadda ka ba shi iko akan dukkan 'yan adam, ya ba da rai madawwami ga duk wanda ka ba shi.
\s5
\v 3 Wannan ne rai madawwami: wato su san ka, Allah makadaici na gaskiya, da shi kuma wanda ka aiko, Yesu Almasihu.
\v 4 Na daukaka ka a duniya, na gama aikin da ka ba ni in yi.
\v 5 Yanzu, ya Uba, ka daukaka ni tare da kai da daukaka wadda ni ke da ita tare da kai tun kafin duniya ta kasanci.
\s5
\v 6 Na bayyana sunanka ga mutunen da ka ba ni acikin duniya. Na ka suke, ka ba ni su, sun kuwa kiyaye maganarka.
\v 7 Yanzu kuwa sun san duk iyakar abinda ka ba ni daga gare ka yake,
\v 8 don kuwa maganganun da ka fada mani. Na fada masu, sun kuma karba, sun sani kuwa hakika na fito daga gareka ne, kuma sun gaskata kai ne ka aiko ni.
\s5
\v 9 Ina yi masu addu'a. Ba domin duniya ni ke yin addu'a ba, amma domin wadanda ka bani gama na ka ne.
\v 10 Gama dukan abinda ke nawa na ka ne, naka kuwa nawa ne, an kuma daukaka ni a cikinsu.
\v 11 Ba na cikin duniya kuma, amma wadannan mutane suna cikin duniya, ni kuwa ina zuwa wurin ka. Ya Uba mai Tsarki, ka adanasu cikin sunanka da ka ba ni domin su zama daya, kamar dai yadda muke daya.
\s5
\v 12 Lokacin da ina tare da su, na adanasu acikin sunanka da ka ba ni. Na kiyaye su, kuma ko daya kuwa daga cikinsu ba ya bace ba, sai dai dan hallakar nan, domin Nassi ya cika.
\v 13 Amma yanzu ina zuwa wurinka, Ina fadar wadannan abubuwa tun ina duniya, domin farin cikina ya zama cikakke a zukatansu.
\v 14 Na ba su maganarka, kuma duniya ta tsane su domin su ba na duniya ba ne, kamar yadda ni ba na duniya ba ne.
\s5
\v 15 Ba ina roko ka dauke su daga cikin duniya ba, amma domin ka tsare su daga mugun nan.
\v 16 Su ba na duniya ba ne, kamar yadda ni ba na duniya ba ne.
\v 17 Ka kebe su domin kanka cikin gaskiya. maganarka gaskiya ce.
\s5
\v 18 Kamar dai yadda ka aiko ni cikin duniya, haka kuma na aike su cikin duniya.
\v 19 Na kebe kaina gareka sabili da su, domin su ma kansu a kebe su gareka cikin gaskiya.
\s5
\v 20 Ina addu'a ba domin wadannan kadai ba, amma har da wadanda zasu gaskata da ni ta wurin maganarsu,
\v 21 Domin su zama daya dukansu, kamar yadda kai, ya Uba, ka ke ciki na, ni kuma na ke cikin ka. Ina roko suma su kasance a cikinmu, domin duniya ta gaskata cewa ka aiko ni
\s5
\v 22 Daukakar da ka bani, ita nake basu, domin su zama daya, kamar yadda mu ke daya;
\v 23 ni a cikinsu, kai kuma a ciki na. Domin su kammalu cikin zama daya, domin duniya ta sani cewa ka aiko ni, kuma ka kaunace su, kamar yadda ka kaunace ni.
\s5
\v 24 Ya Uba, ina so wadanda ka ba ni, su ma su kasance tare da ni inda nake, domin su dubi daukakata da ka yi mani. Domin ka kaunace ni tun kafin halittar duniya.
\s5
\v 25 Ya Uba mai adalci, duniya kam, ba ta sanka ba, amma ni na sanka; kuma wadannan sun sani kai ne ka aiko ni.
\v 26 Na sanar masu da sunanka, zan kuma sanar da shi domin kaunar da ka yi mani ta kasance a cikinsu, ni kuma in kasance a cikinsu,
\s5
\c 18
\p
\v 1 Bayan Yesu ya fadi wadannan maganganu, ya fita shi da almajiransa zuwa daya barayin kwarin Kidiron, inda wani lambu ya ke, ya kuma shiga da almajiransa.
\v 2 Yahuza ma wanda zai bashe shi ya san wurin, domin Yesu ya saba zuwa wurin da almajiransa.
\v 3 Yahuza kuwa, bayan ya dauko kungiyar soja daga manyan firistoci, da Farisawa, da 'yan majalisa, suka zo wurin, rike da fitilu, da cociloli, da makamai.
\s5
\v 4 Sai Yesu, da ya san duk abinda ke faruwa da shi, yayiwo gaba, yace masu, "Wa kuke nema"
\v 5 Suka amsa masa su ka ce, "Yesu Banazare" Yesu yace masu, Ni ne" Yahuza kuma, wanda ya bashe shi, yana tsaye tare da sojojin.
\s5
\v 6 Sa'adda ya ce masu, "Ni ne", suka koma da baya, suka fadi a kasa.
\v 7 Ya sake tambayarsu kuma, "Wa ku ke nema?" su ka ce, "Yesu Banazare."
\s5
\v 8 Yesu ya amsa, "Ai, na gaya maku cewa, Ni ne. In kuwa ni ku ke nema, ku bar wadannan su tafi abinsu;"
\v 9 Wannan kuwa domin maganar daya fada ta cika, "Daga cikin wadanda ka ba ni, ko daya bai bace mani ba."
\s5
\v 10 Saminu Bitrus kuwa, da ya ke yana da takobi, ya zaro ya kai wa bawan babban firist sara, ya dauke masa kunnensa na dama, sunan bawan Malkus ne.
\v 11 Yesu ya ce wa Bitrus, "Mai da takobin ka kubenta. Ba zan sha kokon da Uba ya ba ni ba.'?
\s5
\v 12 Sai sojojin da hafsan, da 'yan majalisar Yahudawa, suka kama Yesu, suka daure shi.
\v 13 Da fari suka tafi da shi wurin Hanana, don shi surukin Kayafa ne, wanda ya ke shi ne babban firist a shekaran nan.
\v 14 Kayafa kuma shi ne ya ba Yahudawa shawara, cewa ya fiye masu mutum daya ya mutu domin mutane.
\s5
\v 15 Saminu bitrus ya bi bayan Yesu, haka kuma wani almajirin yayi. Almajirin nan kuwa sananne ne ga babban firist, sai ya shiga har farfajiyar babban firist din tara da Yesu;
\v 16 Amma bitrus kuwa ya tsaya a bakin kofa daga waje. Sai daya almajirin da ya ke sananne ga babban firist ya fita, yayi magana da macen da ta ke tsaron kofar, sa'an nan ya shigo da Bitrus.
\s5
\v 17 Sai yarinyar mai tsaron kofar ta ce wa Bitrus, "kai ma ba kana cikin almajiran mutumin nan ba?" Yace "bani ba."
\v 18 To, barorin da dogaran Haikali suna tsaye a wurin, sun kuwa hura wutar gawayi, suna jin dumi, gama ana sanyi. Bitrus ma yana tsaye tare da su yana jin dumin.
\s5
\v 19 babban firist ya tambayi Yesu game da almajiransa da koyarwarsa kuma.
\v 20 Yesu ya amsa masa, Ai, na yi wa duniya magana a bayyane. Na kuma sha koyarwa a majami'u da Haikali in da Yahudawa duka sukan taru. Ban fadi komai a boye ba.
\v 21 Don me kake tambaya ta? Ka tambayi wadanda suka saurare ni a kan abinda na fada, ai, sun san abinda na fada.
\s5
\v 22 Sa'adda Yesu ya fadi wannan, wani daga cikin 'yan majalisar da ke tsaye a wurin ya nushi Yesu, yace, "Kana amsa wa babban firist haka."
\v 23 Yesu ya amsa masa yace, "Idan na fadi mugun abu to, ka bada shaida kan hakan. In kuwa dai dai na fada, to, dan me za ka nushe ni?"
\v 24 Sai Hanana ya aika daYesu a daure wurin Kayafa, babban firist.
\s5
\v 25 To Saminu Bitrus yana tsaye yana jin dumin. Mutanen kuwa suka ce masa, "Anya kai ma ba cikin almajiransa ka ke ba?" Sai yayi musu yace, "A'a, ba na ciki."
\v 26 Sai wani daga cikin bayin babban firist, wato dan'uwan wanda Bitrus ya fillewa kunne, yace, "Ashe, ban gan ka tare da shi a lambun ba?
\v 27 Bitrus ya sake yin musu, nan da nan kuwa zakara yayi cara.
\s5
\v 28 Daga wurin Kayafa kuma suka kai Yesu fadar Gwamna. Da asuba ne kuwa, su kansu ba su shiga fadar Gwamnan ba, wai don kada su kazantu su kasa cin jibin Ketarewa.
\v 29 Sai bilatus fa ya fita zuwa wurinsu, yace, "Wane zargi ku ke kawowa akan mutumin nan?
\v 30 "Sai suka amsa suka ce, "idan da mutumin nan bai yi mugun abu ba, me zai sa mu yi kararsa a wurin ka"
\s5
\v 31 bilatus yace masu, "Ku tafi da shi da kan ku mana, ku hukunta shi bisa ga shari'arku!" Sai Yahudawa su kace masa, "Ai, ba mu da ikon zartar da hukuncin kisa akan kowa."
\v 32 Sun fadi Wannan ne don a cika maganar da Yesu yayi, wadda ta kwatanta irin mutuwar da zai yi.
\s5
\v 33 Sai bilatus ya sake shiga cikin fadar Gwamnan, ya kira Yesu ya ce masa, "kai sarkin Yahudawa ne?"
\v 34 Yesu ya amsa, "wannan fadarka ce, ko kuwa wadansu ne suka ce da ni haka a wurinka?"
\v 35 Bilatus ya amsa "Ni ba Bayahude bane, ko kuwa?" Ai, jama'arka ne da manyan firistoci suka bashe ka gareni. "Me ka yi?"
\s5
\v 36 Yesu ya amsa, "Mulkina ba na duniya nan ba ne. Da mulkina na duniyan nan ne da barorina za su yi yaki kada a bashe ni ga Yahudawa. To, mulkina ba daga nan ya ke ba."
\v 37 Sai Bilatus yace masa, "Wato ashe, sarki ne kai?" Yesu ya amsa, "Yadda ka fada, ni sarki ne. Domin wannan dalili aka haife ni, domin kuma wannan dalili na zo cikin duniya, don in bada shaida game da gaskiya. Kowane mai kaunar gaskiya kuma yakan saurari muryata."
\s5
\v 38 Bilatus yace masa, "Menene gaskiya?" Bayan da ya fadi haka, ya sake fitowa wurin Yahudawa, yace masu, "Ni kam, ban sami mutumin nan da wani laifi ba.
\v 39 Amma dai kuna da wata al'ada, in Idin Ketarewa ya yi, na kan sakar maku mutum daya. To, kuna so in sakar maku sarkin Yahudawa?"
\v 40 Sai suka sake daukar kururuwa suna cewa, "A; a, ba wannan mutum ba, sai dai Barabbas." Barabbas din nan kuwa dan fashi ne.
\s5
\c 19
\p
\v 1 Sai Bilatus yayi wa Yesu bulala.
\v 2 Sojojin kuwa suka saka rawanin kaya. Suka kuwa dora wa Yesu a kai suka sa mashi kaya irin na saurata.
\v 3 Suka zo wurin sa sukace, "Ranka ya dade, sarkin Yahudawa! sai suka nushe shi.
\s5
\v 4 Sai Bilatus ya sake fita waje yace masu, "Dubi, zan kawo maku mutumin domin ku sani ban same shi da wani laifi ba",
\v 5 Yesu kuwa ya fito, da rawanin kaya da kaya irin na sarauta. Sai Bilatus yace "Ga mutumin nan".
\v 6 Da manyan firistocin tare da yan majalisar suka ga Yesu, sai suka yi ta ihu suna cewa "A gicciye shi, A gicciye shi" Sai Bilatus yace masu, "ku dauke shi ku gicciye shi, ni kam ban same shi da wani laifi ba".
\s5
\v 7 Sai Yahudawan sukace mashi, "Ai muna da shari'a, kuma bisa ga shari'ar ya cancanci mutuwa domin ya mai da kansa Dan Allah".
\v 8 Da Bilatus ya ji wannan zance sai ya tsorata kwarai.
\v 9 Sai ya sake shiga fadar Gwamna, yace wa Yesu, "Daga ina ka fito?" amma Yesu bai amsa mashi ba.
\s5
\v 10 Sai Bilatus yace masa "Ba zaka yi mani magana ba? Baka san ina da iko in sake ka ba, kuma in gicciye ka?
\v 11 Yesu ya amsa masa, "Ai ba ka da iko a kaina sai dai in an baka daga sama, Saboda haka, wanda ya mika ni a gare ka shine mafi zunubi".
\s5
\v 12 Da jin haka, sai Bilatus yayi kokari a sake shi, amma sai Yahudawa suka tada murya sukace, "In ka saki mutumin nan, kai ba abokin Kaisar bane, duk wanda ya maida kansa sarki, ya sabawa Kaisar".
\v 13 Da Bilatus ya ji irin maganganunsu sai ya fito da Yesu waje ya kuma zauna akan kujeransa a inda ake kira "Dakalin shari'a," a Yahudanci kuma, "Gabbata."
\s5
\v 14 To a ran nan ana shirye shiryen idin ketarewa, da misalin sa'a ta shidda kenan, wato tsakar rana, Bilatus yace wa Yahudawan "Ga sarkin ku!"
\v 15 Su kuwa suka yi ihu, a tafi da shi, a tafi da shi, a gicciye shi, Bilatus yace masu "In gicciye sarkin ku? Sai manyan firistocin sukace "Ba mu da wani sarki sai Kaisar".
\v 16 Sai Bilatus ya mika Yesu domin su gicciye shi.
\s5
\v 17 Sai suka tafi da Yesu, ya fito yana dauke da gicciyen zuwa wurin da ake kira "Wurin kwalluwa" da Yahudanci kuma "Golgota".
\v 18 Suka gicciye Yesu a wurin, tare da wasu mutum biyu, daya a kowane gefe, Yesu kuwa na tsikiya.
\s5
\v 19 Bilatus kuwa ya rubuta wata alama a kan gicciyen, "YESU BANAZARE, SARKIN YAHUDAWA".
\v 20 Yahudawa da yawa kuwa suka karanta wannan alama domin wurin da aka gicciye Yesu yana kusa da Birnin. Alamar kuwa an rubuta ta da Yahudanci, da Romanci, da Helenanci.
\s5
\v 21 Sai manyan firistocin yahudawa sukace wa Bilatus, kada ka rubuta sarkin Yahudawa, amma kace, 'wannan yace "Ni ne sarkin Yahudawa"'.
\v 22 Bilatus kuwa ya amsa, "Abinda na rubuta na rubuta kenan."
\s5
\v 23 Bayan da sojojin suka gicciye Yesu, sai suka yayyaga rigarsa kashi hudu, kowane soja da nasa, kashin, sai kuma alkyabbar. Alkyabbar kuwa bata da dinki an saka tane daga sama har kasa.
\v 24 Sai sukace wa junansu, "Kada mu yaga alkyabbar, amma kuzo mu jefa kuri'a a kan ta mu gani ko wanene zai dauke ta, anyi haka ne domin a cika nassi cewa "Sun raba rigata a tsakaninsu, sun kuwa jefa kuri'a domin alkyabbata.
\s5
\v 25 Sojojin suka yi wadannan abubuwa. Uwar Yesu, da 'yar'uwarta, da Maryamu matar Kilofas, da kuma Maryamu Magadaliya. Wadannan mataye suna tsaye kusa da gicciyen Yesu.
\v 26 Da Yesu ya ga mahaifiyarsa da almajirin nan da yake kauna tsaye kusa da juna, yace, "Mace, dubi, dan ki!"
\v 27 Sai yace wa almajirin, "Dubi, mahaifiyarka!" Daga wannan sa'a almajirin ya dauke ta zuwa gidansa.
\s5
\v 28 Bayan wannan Yesu, saboda ya san yanzu komai ya kammala, domin a cika nassin, sai yace "Ina jin kishi.
\v 29 A gefensu kuma akwai gora cike da ruwan inabi mai tsami, sai suka tsoma soso a cikin ruwan inabin mai tsami suka daura a wata sanda sai suka mika masa a baki.
\v 30 Da Yesu ya tsotsi ruwan tsamin, sai yace "An gama" Sai ya sunkuyar da kansa ya kuwa saki ruhunsa.
\s5
\v 31 Sai Yahudawan, domin ranar shirye shirye ne, domin kada a bar jikunansu akan gicciye har ranar asabacin (domin asabacin rana ce mai muhimmanci), suka roki Bilatus ya kakkarye kafafunsu kuma ya saukar da su.
\v 32 Sai sojojin suka zo suka karya kafafun mutum na farko da kuma mutum na biyun wadanda aka gicciye tare da Yesu.
\v 33 Da suka iso kan Yesu sai suka tarar ya riga ya mutu, sai basu kuwa karya kafafunsa ba.
\s5
\v 34 Duk da haka daya daga cikin sojojin ya soki kuibin shi da mashi, nan da nan sai jini da ruwa suka fito.
\v 35 Wanda ya ga wannan, shi ya zama shaida, shaidarsa kuwa gaskiya ce. Ya sani cewa abinda ya fada gaskiya ne saboda ku ma ku gaskata.
\s5
\v 36 Wadannan sun faru ne domin a cika nassi, "Babu ko daya daga cikin kasusuwansa da za'a karya".
\v 37 Kuma wani nassin yace, "Zasu dube shi wanda suka soka."
\s5
\v 38 Bayan wadannan abubuwa, Yusufu mutumin Arimatiya, wanda yake almajirin Yesu ne (amma a boye saboda tsoron Yahudawa) ya roki Bilatus izini domin ya dauke jikin Yesu. Bilatus kuwa ya bashi izini, sai Yusufu yazo ya dauki jikin.
\v 39 Nikodimu ma ya zo, wanda da farko ya zo wurin Yesu da daddare, ya kawo hadin man kamshi na mur da al'ul wajen nauyin awo dari.
\s5
\v 40 Sai suka dauki jikin Yesu suka sa shi a likkafanin lillin tare da kayan kamshin nan, domin jana'iza bisa ga al'adar Yahudawa.
\v 41 To a wurin da aka gicciye shi kuwa akwai wani lambu, a cikin lambun kuma akwai sabon kabari wanda ba'a taba sa kowa ba.
\v 42 Da yake ranar shirye shirye ce ta Yahudawa, kabarin kuwa na kusa, sai suka sa Yesu a ciki.
\s5
\c 20
\p
\v 1 To da sassafe ranar farko ta mako, da sauran duhu, Maryamu Magadaliya ta zo kabarin, ta tarar an kawar da dutsen daga kabarin.
\v 2 Sai ta ruga da gudu zuwa wurin Saminu Bitrus tare da almajirin nan da Yesu ke kauna, tace masu, "Sun dauke Ubangiji daga kabarin, bamu kuwa san inda aka sa shi ba."
\s5
\v 3 Sai Bitrus tare da almajirin nan suka fita, kuma suka tafi kabarin,
\v 4 dukansu suka ruga da gudu tare, amma daya almajirin ya riga Bitrus isowa kabarin,
\v 5 Sai ya sunkuya ya leka ciki, ya ga likkafanin lillin a wurin, amma fa bai shiga ciki ba.
\s5
\v 6 Sai Saminu Bitrus ya iso daga bayansa sai ya shiga kabarin, ya tarar da likkafanin lillin a ajiye.
\v 7 sai fallen kuma da yake kansa. Ba'a ajiye tare da likkafanin ba amma aka linkeshi aka ajiye shi daban.
\s5
\v 8 Sai almajirin nan da ya riga isa kabarin shi ma ya shiga ya gani, sai ya ba da gaskiya.
\v 9 Har ya zuwa wannan lokacin basu san nassin daya ce zai tashi daga matattu ba.
\v 10 Sai almajiran suka sake komawa gida kuma.
\s5
\v 11 Amma Maryamu tana tsaye a bakin kabarin tana kuka. Yayin da take kuka, sai ta sunkuya ta leka cikin kabarin.
\v 12 Sai ta ga mala'iku guda biyu cikin fararen kaya zaune, daya ta wurin kai daya kuma ta wurin kafafu inda aka kwantar da Yesu.
\v 13 Sukace mata, "Uwargida don me kike kuka? Sai tace masu, "Domin sun dauke Ubangijina, ban kuwa san inda suka ajiye shi ba.
\s5
\v 14 Bayan ta fadi haka, ta juya sai ta ga Yesu tsaye a wurin. Amma bata san cewa Yesu bane,
\v 15 Yesu yace mata, "Uwargida, me yasa kike kuka? Wa kuma kike nema? Domin tana zaton shine mai kula da lambun, sai tace masa, "Maigida in kaine ka dauke shi, gaya mani inda ka sa shi, ni kuwa in dauke shi."
\s5
\v 16 Yesu yace mata, "Maryamu". Sai ta juya, tace masa da Armaniyanci "Rabboni!" wato mallam.
\v 17 Yesu yace mata, kada ki taba ni, domin har yanzu ban hau wurin Uba ba tukuna, amma kije wurin 'yan'uwana kice masu, zan je wurin Ubana da Ubanku, Allahna da kuma Allahnku".
\v 18 Maryamu Magadaliya ta je tace wa almajiran, "Na ga Ubangiji" Ta kuma ce ya fada mata wadannan abubuwa.
\s5
\v 19 Da yamma a wannan rana, a rana ta farko ta mako, almajiran suna kulle a daki saboda tsoron Yahudawa, Yesu yazo ya tsaya a tsakaninsu, yace "Salama Agareku".
\v 20 Bayan ya fadi haka, sai ya nuna masu hannuwansa da kuibinsa. Da almajiran suka ga Ubangiji, sai suka yi farin ciki.
\s5
\v 21 Yesu ya sake ce masu, "salama agareku. "Kamar yadda Uba ya aiko ni, haka Ni ma na aike ku".
\v 22 Da Yesu ya fadi haka, sai ya hura masu lumfashinsa, yace masu, "Ku karbi Ruhu Mai Tsarki.
\v 23 Duk wanda kuka gafarta wa zunubai, an gafarta masa; kowa kuka rike zunubansa, an rikesu."
\s5
\v 24 Toma, daya daga cikin sha biyun, wanda ake kira Dan Tagwai, baya tare dasu lokacin da Yesu ya bayyana.
\v 25 Sauran almajiran sukace masa "Mun ga Ubangiji". Sai yace masu, "In ban ga gurbin kusoshi a hannuwansa ba, in sa yatsana a gurbin kusoshin ba, in kuma sa hannuna cikin kuibinsa ba, ba zan bada gaskiya ba.
\s5
\v 26 Bayan kwana takwas har wa yau almajiran na cikin gida, Toma ma na tare dasu, kofofin suna kulle, sai ga Yesu a tsakaninsu yace, "Salama agareku".
\v 27 Sa'an nan yace wa Toma, "Iso nan da yatsanka, dubi hannuwana. Miko hannunka kuma kasa a kuibina, kada ka zama marar bada gaskiya, sai dai, mai bada gaskiya".
\s5
\v 28 Toma ya amsa yace "Ya Ubangijina da Allahna!"
\v 29 Yesu yace masa, "Wato saboda ka gan ni, ka bada gaskiya? Albarka ta tabbata ga wadanda basu gani ba, amma kuwa sun bada gaskiya.
\s5
\v 30 Yesu yayi wadansu alamu da yawa dabam dabam a gaban almajiransa, wadanda ba'a rubuta a littafin nan ba.
\v 31 Amma an rubuta wadannan ne, domin ku bada gaskiya Yesu shine Almasihu, Dan Allah, ta wurin gaskatawa kuma ku sami rai cikin sunansa.
\s5
\c 21
\p
\v 1 Bayan wadannan abubuwa, Yesu ya sake bayyana kansa ga almajiran a bakin tekun Tibariya. Ga yadda ya bayyana kansa:
\v 2 Saminu Bitrus na tare da Toma wanda ake kira Dan Tagwai, da Natana'ilu daga Kana ta kasar Galili, da 'ya'yan nan na Zabadi, da kuma wadansu almajiran Yesu biyu.
\v 3 Saminu Bitrus yace masu, "Zani su." sukace masa "Mu ma za mu je tare da kai." Sai suka fita suka shiga jirgi, amma a daren nan basu kama komai ba.
\s5
\v 4 To, gari na wayewa, sai ga Yesu tsaye a bakin gaci, amma almajiran basu gane cewa Yesu bane.
\v 5 Sai Yesu yace masu, "Samari, kuna da wani abinda za a ci?" Suka amsa masa sukace "A'a".
\v 6 Yace masu, "Ku jefa taru dama da jirgin zaku samu wasu." Suka jefa tarunsu har suka kasa jawo shi don yawan kifin.
\s5
\v 7 Sai almajirin nan da Yesu yake kauna yace wa Bitrus, "Ubangiji ne fa!" Da Saminu Bitrus yaji, Ashe, Ubangiji ne, yayi damara da taguwarsa, (don a tube yake), ya fada a tekun.
\v 8 Sauran almajiran kuwa suka zo a cikin karamin jirgi, (domin basu da nisa da kasa, kamar kamu dari biyu zuwa sama), janye da tarun cike da kifi.
\v 9 Da isowarsu gaci, sai suka ga garwashin wuta a wurin da kifi akai, da kuma gurasa.
\s5
\v 10 Yesu ya ce masu "Ku kawo wandansu daga cikin kifin da kuka kama yanzu".
\v 11 Sai Saminu Bitrus ya hau, ya jawo tarun gaci, cike da manyan kifaye dari da hamsin da uku (153). Amma duk da yawansu, tarun bai tsage ba.
\s5
\v 12 Yesu yace masu, "Ku zo ku karya kumallo". Daga cikin almajiran kuwa babu wanda yayi karfin halin tambayarsa "Ko shi wanene?" Domin sunsani Ubangiji ne.
\v 13 Yesu zo ya dauki gurasar ya ba su, haka kuma kifin.
\v 14 Wannan shine karo na uku da Yesu ya bayyana ga almajiransa bayan tashinsa daga matattu.
\s5
\v 15 Da suka karya kumallon, Yesu yace wa Saminu Bitrus, "Bitrus dan Yahaya, kana kaunata fiye da wadannan?" Bitrus yace masa "I ya Ubangiji, ka sani ina kaunarka" Yesu yace masa "Ka ciyar da 'ya'yan tumakina".
\v 16 Ya sake fada masa karo na biyu, "Saminu Dan Yahaya, kana kaunata?" Bitrus Yace masa "I ya Ubangiji, ka sani ina kaunarka". Yesu yace masa, "Ka lura da Tumakina".
\s5
\v 17 Ya sake fada masa, karo na uku, "Bitrus Dan Yahaya, kana kaunata? Sai Bitrus bai ji dadi ba domin Yesu ya fada masa karo na uku, "Kana kaunata" Yace masa, "Ubangiji ka san komai duka, ka sani ina kaunarka." Yesu yace masa "Ka ciyar da tumaki na.
\v 18 Hakika, hakika, Ina gaya maka, lokacin da kake kuruciyarka, kakan yi wa kanka damara, ka tafi inda ka ga dama. amma in ka tsufa, zaka mike hannuwanka wani yayi maka damara, ya kai ka inda baka nufa ba."
\s5
\v 19 To Yesu ya fadi haka ne domin ya nuna irin mutuwar da Bitrus zai yi ga daukakar Allah. Bayan ya fadi haka, sai yace wa Bitrus, ka biyo ni.
\s5
\v 20 Bitrus ya juya sai ya ga almajirin da Yesu yake kauna yana biye dasu; wanda ya jingina a kirgin Yesu lokacin cin jibin nan da yace "Ya Ubangiji, wanene zai bashe ka?"
\v 21 Da Bitrus ya gan shi, yace wa Yesu "Ya Ubangiji, Me mutumin nan zai yi?"
\s5
\v 22 Yesu yace masa, "Idan ina so ya zauna har in dawo ina ruwanka? Ka biyo ni."
\v 23 Wannan zance ya yadu cikin 'yan'uwa cewa, wannan almajirin ba zai mutu ba. Alhali Yesu bai cewa Bitrus, wannan almajirin ba zai mutu ba, Amma "Idan ina so ya zauna har in dawo ina ruwanka?"
\s5
\v 24 Wannan shine almajirin da yake shaida wadannan abubuwa, wanda ya rubuta su, kuma mun tabbata shaidarsa gaskiya ne.
\v 25 Akwai kuma sauran abubuwa da yawa wanda Yesu yayi. Idan da an rubuta kowannensu daya bayan daya, ina gaya maku, ko duniya bazata iya daukar litattafan da za a rubuta ba.