ha_ulb/13-1CH.usfm

1749 lines
110 KiB
Plaintext
Raw Blame History

This file contains invisible Unicode characters

This file contains invisible Unicode characters that are indistinguishable to humans but may be processed differently by a computer. If you think that this is intentional, you can safely ignore this warning. Use the Escape button to reveal them.

\id 1CH
\ide UTF-8
\h Littafin Tarihi Na Ɗaya
\toc1 Littafin Tarihi Na Ɗaya
\toc2 Littafin Tarihi Na Ɗaya
\toc3 1ch
\mt Littafin Tarihi Na Ɗaya
\s5
\c 1
\cl Sura 1
\p
\v 1 Adamu, Set, Enosh,
\v 2 Kenan, Mahalalel, Yared,
\v 3 Enok, Metusela, Lamek.
\v 4 'Ya'yan Nuhu su ne Shem, Ham da Yafet.
\s5
\v 5 'Ya 'yan Yafet su ne Gomer, Magog, Madai, Yaban, Tubal, Meshek, Tiras.
\v 6 'Ya'yan Gomer su ne Ashkenaz, Rifat da Togarma.
\v 7 'Ya 'yan Yaban su ne Elisha, Tarshish, Kitiyawa, da Rodanawa.
\s5
\v 8 'Ya'yan Ham su ne Kush, Masar, Fut da Kan'ana.
\v 9 'Ya'yan Kush su ne Seba, Habila, Sabta, Ra'ama da Sabteka.
\v 10 'Ya'yan Ra'ama su ne Sheba da Dedan. Kush ya zama mahaifin Nimrod, wanda shi ne ya fara zama jarumi a duniya.
\s5
\v 11 Masar ya zama mahaifin mutanen Ludawa, da Anamawa, da Lehabawa, da Naftuhawa, da
\v 12 Fatrusawa, da Kasluhawa (daga wannan tushen Filistiyawa suka fito), da Kaftorawa.
\s5
\v 13 Kan'ana ya zama mahaifin Sidon, ɗan farinsa, da kuma Hitiyawa.
\v 14 Shi ne ya zama kakan Yebusawa, Amoriyawa, Girgashawa,
\v 15 Hibiyawa Arkiyawa, Siniyawa da
\v 16 Arbiyawa, Zemarawa, da Hamatawa.
\s5
\v 17 'Ya'yan Shem su ne Elam, Ashur, Arfazad, Lud, Aram, Uz, Hul, Geter, da Meshek,
\v 18 Arfazad shi ne ya zama mahaifin Shela, Shela kuma ya zama mahaifin Eber.
\v 19 Eber na da 'ya'ya biyu. Sunan ɗayan Feleg, gama a zamaninsa ne duniya ta rabu. Sunan ɗan'uwansa Yoktan.
\s5
\v 20 Yoktan ya zama mahaifin Almodad, Shelef, Hazamavet, Yera,
\v 21 Hadoram, Uzal, Dikla,
\v 22 Obal, Abimayel, Sheba,
\v 23 Ofir, Habila, da Yobab, duk waɗannan daga zuriyar Yoktan ne.
\s5
\v 24 Shem, Arfazad, Shelah,
\v 25 Eber, Feleg, Rewu,
\v 26 Serug, Nahor, Tera,
\v 27 Abram shi ne Ibrahim.
\s5
\v 28 'Ya'yan Ibrahim su ne Ishaku da Isma'il.
\v 29 Waɗannan su ne 'ya'yansu: Ɗan farin Isma'il Nebayot ne, sa'an nan Kedar, Adbeel, Mibsam,
\v 30 Mishma, Duma, Massa, Hadad, Tema,
\v 31 Yetur, Nafish, da Kedema. Waɗannan su ne 'ya'yan Isma'il.
\s5
\v 32 'Ya'yan Ketura, ƙwarƙwarar Ibrahim su ne Zimran, Yokshan, Medan, Midiyan, Ishbak da Shuwa. 'Ya'yan Yokshan su ne Sheba da Dedan.
\v 33 'Ya'yan, Midiyan su ne Efa, Efer, Hanok, Abida, da Elda'ah. Dukkan waɗannan zuriyar Ketura ne.
\s5
\v 34 Ibrahim ya zama mahaifin Ishaku. 'Ya'yan Ishaku su ne Isuwa da Isra'ila.
\v 35 'Ya'yan Isuwa su ne Elifaz, Ruwel, Yewush, Yalam, da Kora.
\v 36 'Ya'yan Elifaz su ne Teman, Omar, Zefo, Gatam, Kenaz, Timna da Amalek.
\v 37 'Ya'yan Ruwel su ne Nahat, Zera, Shamma, da Mizza.
\s5
\v 38 'Ya'yan Seyir su ne Lotan, Shobal, Zibiyon, Ana, Dishon, Ezer, da Dishan.
\v 39 'Ya'yan Lotan su ne Hori da Homam, Timna 'yar'uwar Lotan ce.
\v 40 'Ya'yan Shobal su ne Alban, Manahat, Ebal, Shefo, da Onam. 'Ya'yan Zibiyon su ne Aiya da Ana.
\s5
\v 41 Ɗan Ana shi ne Dishon. 'Ya'yan Dishon su ne Hemran, Eshban, Itran, da Keran.
\v 42 'Ya'yan Ezer su ne Bilhan Za'aban, Ya'akan da Akan. 'Ya'yan Dishan su ne Uz da Aran.
\s5
\v 43 Waɗannan su ne sarakunan da suka yi mulki a ƙasar Idom kafin wani sarki ya yi mulki bisa Isra'ilawa. Bela ɗan Beyor, sunan birninsa Dinhaba ne.
\v 44 Da Bela ya mutu, Yobab ɗan Zera na Bozra ya yi mulki a gurbinsa.
\v 45 Da Yobab ya mutu, Husham na ƙasar Temanawa ya yi mulki a gurbinsa.
\s5
\v 46 Da Husham ya mutu, Hadad ɗan Bedad, wanda ya ci Midiyan a ƙasar Mowab, ya yi sarauta a gurbinsa. Sunan birninsa Avit.
\v 47 Da Hadad ya mutu, Samla na Masreka ya yi sarauta a gurbinsa.
\v 48 Da Samla ya mutu, Shawul na Rehobot wadda a kan kogin ya yi sarauta a gurbinsa.
\s5
\v 49 Da Shawul ya mutu, Ba'al-Hanan ɗan Akbor ya yi mulki a gurbinsa.
\v 50 Ba'al-Hanan ɗan Akbor ya mutu, Hadar ya yi mulki a gurbinsa. Sunan birninsa Fawu. Sunan matarsa Mehetabel ce ɗiyar Matred ɗiyar Me Zahab.
\s5
\v 51 Hadad ya mutu, shugaban iyalin Idom su ne Timna, Alba, Yetet,
\v 52 Ohalibama, Elah, Finon,
\v 53 Kenaz Teman, Mibza,
\v 54 Magdiyel, da Iram. Waɗannan su ne shugabannin a Idom.
\s5
\c 2
\cl Sura 2
\p
\v 1 Waɗanan su ne 'ya'yan Isra'ila maza: Ruben, Simiyon, Lebi, Yahuda, Issaka, Zebulun,
\v 2 Dan, Yosef, Benyamin, Naftali, Gad da Asha.
\s5
\v 3 'Ya'yan Yahuda su ne Er, Onan, da Shela, waɗanda ɗiyar Shuwa ta haifa masa Bakan'aniye. Er ɗan farin Yahuda, mugu ne a gaban Yahweh, sai Yahweh ya kashe shi.
\v 4 Tama, surukarsa, ta haifa masa Ferez da Zara. Yahuda yana da 'ya'ya biyar maza.
\s5
\v 5 'Ya'yan Ferez su ne Hezron da Hamul.
\v 6 'Ya'yan Zera su ne Zimri, Etan, Heman, Kalkol, da Darda su biyar cur.
\v 7 Ɗan Karmi shi ne Akar, wanda ya kawo matsala ga Isra'ila lokacin da ya saci abubuwan da aka keɓe domin Yahweh.
\v 8 Ɗan Etan shi ne Azariya.
\s5
\v 9 'Ya'yan Hezron su ne Yeramil, Ram, Kaleb.
\v 10 Ram ya zama mahaifin Aminadab, Aminadab ya zama mahaifin Nashon, shugaba ne cikin zuriyar Yahuda.
\v 11 Nashon ya zama mahaifin Salmon, Salmon ya zama mahaifi Bo'aza.
\v 12 Bo'aza ya zama mahaifin Obed, Obed ya zama mahaifin Yesse.
\s5
\v 13 Yesse ya zama mahaifin ɗan farinsa Eliab, Abinadab na biyu, Shimeya na uku,
\v 14 Netanel na huɗu, Raddai na biyar,
\v 15 Ozem na shida, sai Dauda na bakwai.
\s5
\v 16 'Yan'uwansu mata su ne Zeruyiya da Abigel. 'Ya'yan Zeruyiya su ne Abishai, Yoab da Asahel, su uku.
\v 17 Abigel ta haifi Amasa, mahaifinsa Yeter ne Ba'isma'ile.
\s5
\v 18 Kaleb ɗan Hezron ya haifi 'ya'ya daga matarsa Azuba, da kuma Yeriyot. 'Ya'yansa maza su ne Yesher, Shobab, da Ardon.
\v 19 Azuba ta mutu, sai Kaleb ya auro Efrat, wacce ta haifa masa Hur.
\v 20 Hur ya zama mahaifin Uri, Uri kuma ya zama mahaifin Bezalel.
\s5
\v 21 Daga baya Hezron (da ya cika shekaru sittin) ya auri ɗiyar Makir, mahaifin Giliyad. Ita ta haifa masa Segub.
\v 22 Segub ya zama mahaifin Yayir, wanda ya mallaki birane ashirin da uku a ƙasar Giliyad.
\s5
\v 23 Geshur da Aram suka ci garin Yayir da Kenat, har da garuruwa sittin na kewaye. Duk waɗannan mazauna zuriyar Makir ne, mahaifin Giliyad.
\v 24 Bayan mutuwar Hezron, Kaleb ya kwana da Efrata, matar Hezron mahaifinsa. Ta haifa masa Ashhur, mahaifin Tekowa.
\s5
\v 25 'Ya'yan Yeramil, ɗan farin Hezron, su ne Ram ɗan fari, Buna, Oren, Ozem, da Ahija.
\v 26 Yeramil ya na da wa ta mata, wadda ta ke da suna Atara. Ita ce uwar Onam.
\v 27 'Ya'yan Ram, ɗan farin Yeramel, su ne Ma'az, Yamin, da Eker.
\v 28 'Ya'yan Onam su ne Shammai da Yada. 'Ya'yan Shammai su ne Nadab da Abishur.
\s5
\v 29 Sunan matar Abishur Abihel ne, ta kuma haifa masa Ahban da Molid.
\v 30 'Ya'yan Nadab su ne Seled da Affayim, amma Seled ya mutu ba shi da 'ya'ya,
\v 31 'Ɗan Affayim kuwa Ishi ne. Ɗan Ishi shi ne Sheshan. Ɗan Sheshan shi ne Ahlai.
\v 32 'Ya'yan Yada, ɗan'uwan Shammai, su ne Yeter da Yonatan. Yeter ya mutu ba shi da 'ya'ya.
\v 33 'Ya'yan Yonatan su ne Felet da Zaza. Waɗannan su ne zuriyar Yeramil.
\s5
\v 34 Sheshan ba shi da 'ya'ya maza, sai dai mata. Sheshan ya na da bawa, Bamasare, mai suna Yarha.
\v 35 Sai Sheshan ya ba baransa Yarha ɗiyarsa ta zama matarsa. Ita ce ta haifa masa Attai.
\s5
\v 36 Attai ya zama mahaifin Natan, Natan ya zama mahaifin Zabad.
\v 37 Zabad ya zama mahaifin Eflal, kuma Eflal ya zama mahaifin Obed.
\v 38 Obed ya zama mahaifin Yehu, kuma Yehu ya zama mahaifin Azariya.
\s5
\v 39 Azariya ya zama mahaifin Helez, Helez ya zama mahaifin Eleyasa.
\v 40 Eleyasa ya zama mahaifin Sismai, Sismai kuma ya zama mahaifin Shallum.
\v 41 Shallum ya zama mahaifin Yekamiya, Yekamiya kuma ya zama mahaifin Elishama.
\s5
\v 42 'Ya'yan Kaleb, ɗan'uwan Yeramil, su ne Mesha ɗan farinsa, wanda shi ne mahaifin Zif. Ɗansa na biyu, Maresha, shi ne mahaifin Hebron.
\v 43 'Ya'yan Hebron su ne Kora, Taffuwa, Rekem, da Shema.
\v 44 Shema ya zama mahaifin Raham, mahaifin Yorkiyam. Rekem ya zama mahaifin Shammai.
\s5
\v 45 Ɗan Shammai kuwa shi ne Mawon, Mawon shi ne mahaifin Bet Zur.
\v 46 Efah, ƙwarƙwarar Kaleb, ta haifi Haran, Moza, da Gazez. Haran ya zama mahaifin Gazez.
\v 47 'Ya'yan Yahdai su ne Regem, Yotam, Geshan, Felet, Efah da Sha'af.
\s5
\v 48 Ma'aka, ƙwarƙwarar Kaleb, ta haifi Sheber da Tirhanah.
\v 49 Ita ce kuma mahaifiyar Sha'af mahaifin Madmanna, Sheva mahaifin Makbena da mahaifin Gibeya. Ɗiyar Kaleb ita ce Aksah. Waɗannan su ne zuriyar Kaleb.
\s5
\v 50 Wàɗannan su ne 'ya'yan Hur, ɗan farinsa daga Efrata: Shobal mahaifin Kiriyat Yerim,
\v 51 Salma mahaifin Betlehem da kuma Haref mahaifin Bet Gader.
\s5
\v 52 Shobal mahaifin Kiriyat Yerayim yana da zuriya: Harowe, rabin jama'ar Manahatawa,
\v 53 da kuma iyalin Kiriyat Yerayim: na Itirawa da na Futiyawa, da na Shumatawa da Mishrayawa. Daga waɗannan ne Zoratawa da Eshtawolawa suka fito.
\s5
\v 54 Waɗannan su ne dangogin Salma: Betlehem, Netofatawa, Atrot Bet Yowab, da rabin Manahatawa - Zoritawa,
\v 55 dangogin marubuta waɗanda suka zauna a Yabez: Tiratawa, Shimiatawa, da Sukatawa. Waɗannan su ne Kenitawa zuriyar da suka fito daga Hammat, kakan Rekabawa.
\s5
\c 3
\cl Sura 3
\p
\v 1 Waɗannan su ne 'ya'yan Dauda da aka haifa masa a Hebron: ɗan fari shi ne Amnon, ta wurin Ahinowam daga Yezriyel; na biyun shi ne Daniyel, ta wurin Abigel daga Karmel;
\v 2 na ukun shi ne Absalom, wanda uwarsa ita ce Ma'aka, ɗiyar Talmai sarkin Geshur. Na huɗun shi ne Adonijah ɗan Haggit;
\v 3 na biyar shi ne Shefatiya ta wurin Abital; na shida shi ne Itreyam ta wurin Egla matarsa.
\s5
\v 4 Waɗannan shida aka haifa wa Dauda a Hebron, inda ya yi sarauta shekaru bakwai da wata shida. Sa'an nan ya yi sarauta a Yerusalem shekaru talatin da uku.
\v 5 Waɗannan 'ya'ya maza huɗu ta wurin Batsheba ɗiyar Ammiyel aka haifa masa su a Yerusalem: Shamuwa, Shobab, Natan, da Suleman.
\s5
\v 6 Wasu 'ya'ya maza na Dauda su ne: Ibhar, Elishuwa, Elifelet,
\v 7 Nogah, Nefeg, Yafiya,
\v 8 Elishama, Eliyada da Elifelet.
\v 9 Waɗannan su ne 'ya'yan Dauda maza, banda 'ya'yan da ƙwaraƙwarai suka haifa masa. Tamar 'yar'uwarsu ce.
\s5
\v 10 Ɗan Suleman shi ne Rehobowam. Ɗan Rehobowam shi ne Abiya. Ɗan Abiya shi ne Asa. Ɗan Asa shi ne Yehoshafat.
\v 11 Ɗan Yehoshafat shi ne Yehoram. Ɗan Yehoram shi ne Ahaziya. Ɗan Ahaziya shi ne Yo'ash.
\v 12 Ɗan Yo'ash shi ne Amaziya, Ɗan Amaziya shi ne Azariya. Ɗan Azariya shi ne Yotam.
\s5
\v 13 Ɗan Yotam shi ne Ahaz. Ɗan Ahaz shi ne Hezekiya. Ɗan Hezekiya shi ne Manasse. Ɗan
\v 14 Manasse shi ne Amon. Ɗan Amon shi ne Yosiya.
\s5
\v 15 Ga 'ya'yan Yosiya na farkon shi ne Yohanan, ɗansa na biyu Yaho'iakim, ɗansa na uku Zedekiya, ɗansa na huɗu Shallum.
\v 16 'Ya'yan Yeho'akim su ne Yeho'iacin da Zedekiya.
\s5
\v 17 'Ya'yan Yaho'iacin, ɗan bautar talala, su ne Sheltiyal,
\v 18 Malkiram, Fedayiya, Shenazza, Yekamiya, Hoshama da Nedabiya.
\s5
\v 19 'Ya'yan Fedayiya su ne Zerubabel da Shimei. 'Ya'yan Zerubabel su ne Meshullam da Hananiya; Shelomit 'yar'uwarsu ce.
\v 20 Wasu 'ya'yansa maza biyar kuwa su ne Hashuba, Ohel, Berekiya, Hasadiya, Yushab-Hesed.
\v 21 'Ya'yan Hananiya su ne Felatiya da Yeshayiya. Ɗansa shi ne Refayiya, waɗansu sauran zuriyoyin su ne Arnan, Obadiya, da Shekaniya
\s5
\v 22 Ɗan Shekaniya shi ne Shemayiya. 'Ya'yan Shemayiya su ne Hattush, Igal, Bariya, Niyariya, da Shafat.
\v 23 'Ya'yan Niyariya guda uku su ne Eliyonai, Hizkiya, da Azrikam.
\v 24 'Ya'yan Eliyonai su bakwai ne su ne Hodabiya, Eliyashib, Felayiya, Akkub, Yohanan, Delayiya da Anani.
\s5
\c 4
\cl Sura 4
\p
\v 1 'Zuriyar Yahuda su ne Ferez, Hezron, Karmi, Hur da Shobal.
\v 2 Shobal shi ne mahaifin Reyayiya. Reyayiya shi ne mahaifin Yahat. Yahat shi ne mahaifin Ahumai da Lahad. Waɗannan su ne dangogin Zoratawa.
\s5
\v 3 Waɗannan su ne kakannin dangogin da ke cikin birnin Itam: Yezriyel, Ishma, da Idbash. Sunan 'yar'uwarsu Hazzelelfoni.
\v 4 Feniyel shi ne kakan dangoginn da ke cikn birnin Gedor. Ezer shi ne na asalin dangogin da ke cikin Hushah. Waɗannan su ne zuriyar Hur, ɗan farin Efrata kuma shi ne asalin Betlehem.
\s5
\v 5 Ashur mahaifin Tekowa ya na da mata biyu, Helah da Na'arah.
\v 6 Na'arah ta haifa masa Ahuzzam, Hefa, Temeni, Hahashtari. Waɗannan su ne 'ya'yan Na'arah.
\v 7 'Ya'yan Helah su ne Zeret, Zohar, Itnan,
\v 8 da Koz wanda ya zama mahaifin Anub da Hazzobeba, da dangogin zuriyar da suka fito daga Ahahel ɗan Harum.
\s5
\v 9 Yabez ya sami girmamawa fiye da 'yan'wansa. Mahaifiyarsa ta kira shi Yabez. Ta ce, "Domin na haife shi cikin azaba."
\v 10 Yabez ya kira bisa sunan Yahweh na Isra'ila ya ce, "Idan da za ka albarkace ni da gaske, ka faɗaɗa mani iyakata, hannunka ya kasance tare da ni. Idan ka yi haka ka kare ni daga cuta, domin in 'yantu daga azaba!" Sai Yahweh ya amsa addu'arsa.
\s5
\v 11 Kaleb ɗan'uwan Shuhah shi ne mahaifin Mehir, wanda shi ne mahaifin Eshton.
\v 12 Eshton shi ne mahaifin Bet Rafa, Faseya, da Tehinna, wanda shi ne mahaifin Ir Nahash. Waɗannan su ne mutanen da suka zauna a Reka.
\s5
\v 13 'Ya'yan Kenaz su ne Otniyel da Serayiya. 'Ya'yan Otniyel su ne Hatat da Meyonotai.
\v 14 Meyonotai ya zama mahaifin Ofra, Serayiya ya zama mahaifin Yowab wanda ya kafa Ge-Harashim, mutanen masassaƙa ne.
\v 15 'Ya'yan Kaleb 'ɗan Yefune su ne Iru, Elah da Na'am. Ɗan Elah shi ne Kenaz.
\v 16 'Ya'yan Yehallelel su ne Zif, Zifa, Tiriya da Asarel.
\s5
\v 17 'Ya'yan Ezrah su ne Yeter, Mered, Efer, da Yalon. Matar Mered Bamasariye ta haifi Miriyam, Shammai, da Ishba, wanda shi ne mahaifin Estemowa.
\v 18 Waɗannan su ne 'ya'yan Bitiya, ɗiyar Fir'auna, wadda Mered ya aura. Matar Mered Bayahude ta haifi Yarid, wanda shi ne mahaifin Gedor; Haba, wanda ya zama mahaifin Soko; da Yekutiyel, wanda shi ne ya zama mahaifin Zanowa.
\s5
\v 19 Matar Hodiya 'yar'uwar Naham, tana da 'ya'ya maza biyu, ɗaya daga cikinsu ya zama mahaifin Keila Bagarme. Ɗayan kuwa shi ne Eshtamowa Bamaakate.
\v 20 'Ya'yan Shimon su ne Amon, Rinna, Ben-Hanan da Tilon. 'Ya'yan Ishi su ne Zohet da Ben-Zohet.
\s5
\v 21 Zuriyar Shela ɗan Yahuda su ne Er mahaifin Leka, La'ada mahaifin Maresha da dangogin da ke sana'ar linin a Bet Ashbiya,
\v 22 Yokim, mutanen Kozeba, da Yo'ash da Saraf, da ya yi mulki a Mowab da Yashubi Lehem. (Wannan labari daga daɗaɗen rubutu ne.)
\v 23 Waɗannan su ne maginan tukwane da suka zauna a Netayim da Gedera, suka yi wa sarki aiki.
\s5
\v 24 Zuriyar Simiyon su ne Nemuyel, Yamin, Yarib, Zera da Shawul.
\v 25 Shallum ɗan Shawul ne, Mibsam ɗan Shallum ne, kuma Mishma ɗan Mibsam ne.
\v 26 Zuriyar Mishma su ne ɗansa Hamuyel, Zakur jikansa da Shimei tattaɓa kunnensa.
\s5
\v 27 Shimei yana da 'ya'ya goma sha shida da 'ya'ya mata shida. Ɗan'uwansa bai haifi 'ya'ya da yawa ba, saboda haka dangoginsu ba su yi yawa kamar mutanen Yahuda ba.
\v 28 Su ka zauna a Biyasheba, Molada, da kuma Hazar Shuwal.
\s5
\v 29 Sun kuma zauna a Bilha, Ezem, Tolad,
\v 30 Betuwel, Horma, Ziklag,
\v 31 Bet Markabot, Hazar Susim, Bet Biri, da Sha'arayim. Waɗannan su ne biranensu har ya zuwa mulkin Dauda.
\s5
\v 32 Ƙauyukansu biyar su ne Itam, Ain, Rimmon, Token, da Ashan,
\v 33 da dukkan ƙauyukan da ke kewaye har zuwa Baalat. Waɗannan su ne mazauninsu, kuma suka adana tarihin zuriyarsu a rubuce.
\s5
\v 34 Shugabannin dangi su ne Meshobab, Yamlek, Yosha ɗan Amaziya,
\v 35 Yowel, Yehu ɗan Yoshibiya ɗan Serayiya ɗan Asiyel,
\v 36 Eliyonai, Ya'akoba, Yeshohaiya, Asayiya, Adiyel, Yesimiyel, Binayiya
\v 37 da Ziza ɗan Shifi ɗan Allon ɖan Yedayiya ɗan Shimri ɗan Shemayiya.
\v 38 Waɗannan da aka ambata da sunaye shugabanni ne cikin dangoginsu, dangoginsu kuma su ka ƙaru ainun.
\s5
\v 39 Su ka tafi kusa da Gebor, yamma da kwari, domin su nemi makiyaya saboda garkunansu.
\v 40 Suka kuwa sami makiyaya mai dausayi. Ƙasar mai girma ce, ba fitina ga kuma salama. Dã Hamawa suka zauna a wurin.
\v 41 Waɗannan da aka lisafta da sunaye sun zo ne a zamanin Hezekiya sarkin Yahuda, suka hari mazaunin Hamawa da na Mewunawa, waɗanda su ke a wurin. Suka hallakar da su gaba ɗaya suka gãje wurin sabili da sun sami makiyaya mai dausayi domin garkunansu.
\s5
\v 42 Mutane ɗari biyar daga kabilar Simiyon su ka tafi Tsaunin Seyir, tare da shugabaninsu Felatiya, Niyeriya, Refayiya, da Uzziyel 'ya'yan Ishi.
\v 43 Suka ci sauran Amelikawa 'yan gudun hijira, suka zauna a can har zuwa yau.
\s5
\c 5
\cl Sura 5
\p
\v 1 'Ya'yan Ruben ɗan farin Isra'ila - Ruben shi ne ɗan farin Isra'ila, amma aka ba da girman ɗan farinsa ga 'ya'yan Yosef ɗan Isra'ila domin Ruben ya ƙazantar da gadon mahaifinsa. Saboda haka ba a lisafta shi a matsayin ɗan fãri ba.
\v 2 Yahuda shi ne mafi ƙarfi cikin 'ya'uwansa, shugaba kuma zai fito da ga cikinsa. Amma albarkar ɗan fari na Yosef ne -
\v 3 'ya'yan Ruben ɗan farin Isra'ila su ne Hanok, Fallu, Hezron da Karmi.
\s5
\v 4 Waɗannan su ne zuriyar Yowel: Ɗan Yowel shi ne Shemayiya. Ɗan Shemayiya shi ne Gog. Ɗan Gog shi ne Shimei.
\v 5 Ɗan Shimei shi ne Mika. Ɗan Mika shi ne Reyayiya. Ɗan Reyayiya shi ne Ba'al.
\v 6 Ɗan Ba'al shi ne Bira, wanda Tilgat Filesa sarkin Asiriya ya kai su bautar talala. Bira shugaba ne cikin kabilar Ruben.
\s5
\v 7 Waɗannan su ne 'yan'uwan Bira cikin dangoginsu ga yadda aka lisaftasu cikin rubutun tarihin asali: Yeyel shi ne babba, Zekariya, da
\v 8 Bela ɗan Azaz ɗan Shema ɗan Yowel. Suka zauna a Arowa, har can nesa da Nebo da Ba'al Meyon,
\v 9 daga gabas kuma har zuwa goshin jejin da ya miƙe zuwa Kogin Yuferatis. Wannan ya zama haka domin suna da garken dabbobi da yawa a ƙasar Giliyad.
\s5
\v 10 A zamanin Saul, kabilar Ruben ta faɗa wa Hagarawa ta ci su. Suka zauna a rumfunan Hagarawa a dukkan ƙasar da ke gabashin Giliyad.
\s5
\v 11 'Yan kabilar Gad suka zauna kusa da su, a cikin ƙasar Bashan har zuwa Saleka.
\v 12 Shugabanninsu su ne Yowel, wanda shugaba ne, da Shafan shi ma wani shugaba ne, da Yanai da Shafat a Bashan.
\v 13 'Yan'uwansu ta wurin iyalan mahaifisu su ne Mika'el, Meshulam, Sheba, Yorai, Yakan, Ziya, da Eber - su bakwai cur.
\s5
\v 14 Waɗannan mutane da aka ambata a baya su ne zuriyar Abihal, Abihal ɗan Huri ne, Huri ɗan Yarowa ne. Yarowa ɗan Giliyad ne. Giliyad ɗan Mika'el ne. Mika'el ɗan Yeshishai ne. Yeshishai ɗan Yahdo ne. Yahdo ɗan Buz ne.
\v 15 Ahi ɗan Abdiyel ɗan Guni, shugaba ne a iyalin mahaifinsa.
\s5
\v 16 Sun zauna a Giliyad, da Bashan da cikin garuruwanta da kuma cikin dukkan makiyayan ƙasar Sharon har zuwa goshin iyakarta.
\v 17 An rubuta waɗannan dukka bisa ga tarihin asali a kwanakin Yotam sarkin Yahuda da kuma Yerobowam sarkin Isra'ila.
\s5
\v 18 Rubenawa da Gadawa, da rabin kabilar Manasse su na da jarumawa dubu arba'in da hudu gwanayen mayaƙa, ɗauke da garkuwa da takobi da masu harbi da baka.
\v 19 Suka kai hari ga Hagarawa, Yetur, Nafish, da Nodab.
\s5
\v 20 Suka sami taimakon yin yaƙi da abokan gabarsu daga Mai iko dukka. Da haka ne, su ka ci Hagarawa da dukkan waɗanda ke tare da su. Wannan ya faru domin Isra'ilawa sun yi kuka ga Allah cikin yaƙin, ya kuma sauraresu domin sun dogara gareshi.
\v 21 Suka washe dabbobinsu, tare da raƙuma dubu hamsin, tumaki 250,000, jakai dubu biyu, da mazaje 100,000.
\v 22 Sabili da Allah ya yi yaƙi domin su, suka kashe maƙiyansu da yawa. Suka zauna a ƙasarsu har lokacin zuwa bautar talala.
\s5
\v 23 Rabin kabilar Manasse suka zauna a ƙasar Bashan har zuwa Ba'al Harmon da Senir (wato Tsaunin Harmon).
\v 24 Waɗannan su ne shugabannin gidajen ubanninsu: Efer, Ishi, Eliyel, Azriyel, Irmiya, Hodabiya, da Yadiyel. Waɗannan ƙarfafa ne kuma jarumawan mutane ne, shahararrun mutane, shugabannin gidajen ubanninsu.
\s5
\v 25 Amma suka yi rashin aminci ga Allahn kakanninsu. A maimako, sai suka yi sujada ga allolin mutanen ƙasar, waɗanda Allah ya hallakar a gabansu.
\v 26 Allah na Isra'ila ya zuga Ful sarkin Asiriya (ana kiransa Tilgat Filesa sarkin Asiriya). Ya kwashe waɗannan zuwa bautar talala Rubenawa, da Gadawa da rabin kabilar Manasse. Ya kawo su Halah, Habor, Hara, har kuma ya zuwa kogin Gozan, in da suke zaune har wa yau.
\s5
\c 6
\cl Sura 6
\p
\v 1 'Ya'yan Lebi su ne Geshon, Kohat, da Merari.
\v 2 'Ya'yan Kohat su ne Amram, Izhar, Hebron da Uzziyel.
\v 3 'Ya'yan Amram su ne Haruna, Musa da Miriyam. 'Ya'yan Haruna su ne Nadab, Abihu, Eliyeza da Itama.
\s5
\v 4 Eliyeza ya zama mahaifin Finehas sai kuma Finehas ya zama mahaifin Abishuwa.
\v 5 Abishuwa ya zama mahaifin Bukki. Sai Bukki ya zama mahaifni Uzzi.
\v 6 Uzzi ya zama mahaifin Zerahiya, Zerahiya yazama mahaifni Merayot.
\s5
\v 7 Merayot ya zama mahaifni Amariya, Amariya ya zama mahaifni Ahitub.
\v 8 Ahitub ya zama mahaifin Zadok, Zadok ya zama mahaifin Ahima'az.
\v 9 Ahima'az ya zama mahaifin Azariya, Azariya ya zama mahaifin Yohanan.
\s5
\v 10 Yohanan ya zama mahaifin Azariya wanda ya yi hidima a haikalin da Suleman ya gina a Yerusalem.
\v 11 Azariya ya zama mahaifin Amariya kuma Amariya ya zama mahaifin Ahitub.
\v 12 Ahitub ya zama mahaifin Zadok, Zadok ya zama mahaifin Shallum.
\s5
\v 13 Shallum ya zama mahaifin Hilkiya, Hilkiya ya zama mahaifin Azariya.
\v 14 Azariya ya zama mahaifin Serayiya, sai kuma Serayiya ya zama mahaifin Yozadak.
\v 15 Aka kama Yozadak aka tafi da shi a tsare lokacin da Yahweh ya aika Yahuda da Yerusalem bautar talala ta hannun Nebukadnezza.
\s5
\v 16 'Ya'yan Lebi su ne Gashom, Kohat, da Merari.
\v 17 'Ya'yan Gashom su ne Libni, da Shimei.
\v 18 'Ya'yan Kohat su ne Amram, Izar, Hebron da Uzziyel.
\s5
\v 19 'Ya'yan Merari su ne Mali da Mushi. Waɗannan ne suka zama kabilar Lebiyawa bisa ga gidajen ubanninsu.
\v 20 Zuriyar Gershon ya soma da ɗansa Libni ɗan LIbni kuwa Yahat ne. Ɗansa kuwa Zimma ne.
\v 21 Ɗansa Yohat ne. Ɗansa Iddo ne. Ɗansa Zera ne. Ɗansa Yeyaterai ne.
\s5
\v 22 Zuriyar Kohat: Ɗansa shi ne Aminadab. Ɗansa kuwa shi ne Kora. Ɗansa shi ne Assir.
\v 23 Ɗansa shi ne Elkana. Ɗansa shi ne Abiyasaf. Ɗansa shi ne Assir.
\v 24 Ɗansa shi ne Tahat. Ɗansa shi ne Uriyel. Ɗansa shi ne Uzziya. Ɗansa shi ne Shawul.
\s5
\v 25 'Ya'yan Elkana su ne Amasai, Ahimot, da wani ɗa kuma da aka kira Elkana.;
\v 26 Ɗansa shi ne Zofai. Ɗansa shi ne Nahat.
\v 27 Ɗansa shi ne Eliyab. Ɗansa shi ne Yeroham. Ɗansa shi ne Elkana.
\s5
\v 28 'Ya'yan Sama'ila su ne ɗan farinsa Yowel, da Abiya na biyu.
\v 29 Ɗan Merari shi ne Mahli. Ɗansa shi ne Libni. Ɗansa shi ne Shimei. Ɗansa shi ne Uzza.
\v 30 Ɗansa shi neShimeya. Ɗansa shi ne Haggiya. Ɗansa shi ne Asayiya.
\s5
\v 31 Waɗannan su ne sunayen mutanen da Dauda ya sa su bisa hidimar waƙa a haikalin Yahweh, bayan da akwatin alƙawari ya sami hutawa a wurin.
\v 32 Suka yi hidima ta wurin waƙoƙi a gaban rumfar sujada, rumfar taruwa, har sai da Suleman ya gina haikalin Yahweh a Yerusalem. Suka aiwatar da hidimarsu bisa ga umarnin da aka ba su.
\s5
\v 33 Waɗannan su ne suka yi hidima da 'ya'yansu. Daga dangogin Kohatawa aka sami Heman mawaƙi. Ga kakanninsa idan an koma lokacin baya: Heman ɗan Yowel ne. Yowel ɗan Sama'ila ne.
\v 34 Sama'ila ɗan Elkana ne. Elkana ɗan Yeroham ne. Yeroham ɗan Eliyel ne. Eliyel ɗan Towa ne.
\v 35 Towa ɗan Zuf ne. Zuf ɗan Elkana ne. Elkana ɗan Mahat ne. Mahat ɗan Amasai ne. Amasai ɗan Elkana ne.
\s5
\v 36 Elkana ɗan Yowel ne. Yowel ɗan Azariya ne. Azariya ɗan Zefaniya ne.
\v 37 Zefaniya ɗan Tahat ne. Tahat ɗan Assir ne. Assir ɗan Ebiyasaf ne. Ebiyasaf ɗan Kora ne.
\v 38 Kora ɗan Izar ne. Izar Kohat ne. Kohat ɗan Lebi ne. Lebi ɗan Isra'ila ne.
\s5
\v 39 Abokin Heman Asaf ne, shi ya tsaya a hannun damarsa. Asaf ɗan Berekiya ne. Berekiya ɗan Shimeya ne.
\v 40 Shimeya ɗan Mika'el ne. Mika'el ɗan Ba'asiya ne. Ba'asiya ɗan Malkiya ne.
\v 41 Malkiya ɗan Etni ne. Etni ɗan Zera ne. Zera ɗan Adaya ne.
\v 42 Adaya ɗan Itam ne. Itam ɗan Zimma ne. Zimma ɗan Shimei ne.
\v 43 Shimei ɗan Yahat ne. Yahat ɗan Geshon ne. Geshon ɗan Lebi ne.
\s5
\v 44 A hannun hagun Herman akwai abokansa su ne "ya'ya Merari. Su ne waɗannan Etan ɗan Kishi. Kishi ɗan Abdi ne. Abdi ɗan Malluk ne.
\v 45 Malluk ɗan Hashabiya ne. Hashabiya ɗan Amaziya ne. Amaziya ɗan Hilkiya ne.
\v 46 Hilkiya ɗan Amzi ne. Amzi ɗan Bani ne. Bani ɗan Shemer ne.
\v 47 Shemer ɗan Mahli ne. Mahli ɗan Mushi ne. Mushi ɗan Merari ne. Merari ɗan Lebi ne.
\s5
\v 48 Aka ba abokan aikinsu Lebiyawa dukkan hidimar rumfar sujada, gidan Yahweh.
\s5
\v 49 Haruna da 'ya'yansa suka yi hidimar miƙa baye-baye bisa bagadi domin baye-bayen ƙonawa; da kuma baiko bisa bagadin turare domin dukkan aiki a wuri mafi tsarki. Waɗannan baye-baye suka yi kaffara domin Isra'ila, bisa ga dukkan abin da bawan Allah Musa ya umurta.
\s5
\v 50 Zuriyar Haruna kenan bi da bi: Ɗan Haruna shi ne Eliyeza. Ɗan Eliyeza shi ne Fenihas. Ɗan Fenihas shi ne Abishuwa.
\v 51 Ɗan Abishuwa shi ne Bukki. Ɗan Bukki shi ne Uzzi. Ɗan Uzzi shi ne Zerahiya.
\v 52 Ɗan Zerahiya shi ne Merayot. Ɗan Merayot shi ne Amariya. Ɗan Amaraiya shi ne Ahitub.
\v 53 Ɗan Ahitub shi ne Zadok. Ɗan Zadok shi ne Ahima'az.
\s5
\v 54 Ga wuraren da aka ba zuriyar Haruna su zauna, wato, zuriyar Haruna waɗanda ke daga dangin Kohatawa (rabo na fari nasu ne).
\v 55 Aka ba su Hebron a ƙasar Yahuda da kuma makiyayarta,
\v 56 amma jejin birnin da ƙauyukansa aka ba Kaleb ɗan Yefunne.
\s5
\v 57 Aka ba zuriyar Haruna: Hebron (birnin mafaƙa), da Libna da makiyayarta, Yattir, Estomawa da makiyayarta,
\v 58 Hilen da makiyayarta, da Debir da makiyayarta.
\s5
\v 59 Aka ba zuriyar Haruna: Ashan da makiyayarta, Yutta da Bet Shemesh da makiyayarta;
\v 60 daga kabilar Benyamin aka ba su Geba da makiyayarta, Alemet da makiyayarta, da Anatot da makiyayarta. Dukkan biranen iyalen Kohat guda goma sha uku ne.
\s5
\v 61 Ga sauran zuriyar Kohat ta wurin kuri'a aka ba su birane goma daga rabin kabilar Manasse.
\v 62 Ga zuriyar Gershon a cikin dangoginsu da bam da bam aka ba su birane goma sha uku daga cikin kabilar Issaka, Asha, Naftali, da rabin kabilar Manasse a Bashan.
\s5
\v 63 Aka ba zuriyar Merari birane goma sha biyu dangi bayan dangi, daga kabilar Ruben, Gad da Zebulun.
\v 64 Sai mutanen Isra'ila suka bada waɗannan birane da makiyayarsu ga Lebiyawa.
\v 65 Aka ba su ta wurin ƙuri'a garuruwan da aka zana a baya daga kabilun Yahuda, Simiyon da Benyamin.
\s5
\v 66 Ga wasu dangogin Kohatawa aka bada birane daga gundumar Ifraim.
\v 67 Aka basu: Shekem (birnin mafaƙa) da makiyayarta a ƙasar duwatsu ta Ifraim, Gezer da makiyayarta,
\v 68 Yokmiyam da makiyayarta, Bet Horon da makiyayarta,
\v 69 Aijalon da makiyayarta, da Gat Rimmon da makiyayarta.
\s5
\v 70 Rabin kabilar Manasse suka ba Kohatawa: Aner da makiyayarta da Bileyam da makiyayarta. Waɗannan suka zama mallaƙar sauran dangogin Kohatawa.
\s5
\v 71 Zuriyar Geshon daga dangogin rabin kabilar Manasse, aka ba Golan a Bashan da makiyayarta da Ashtarot da makiyayarta.
\v 72 Kabilar Issaka ta ba zuriyar Geshon: Kedesh da makiyayarta, Daberat da makiyayarta,
\v 73 Ramot da makiyayarta, da Anem da makiyayarta.
\s5
\v 74 Daga kabilar Asha Issaka ta karɓi: Mashal da makiyayarta, Abdon da makiyayarta,
\v 75 Hukok da makiyayarta, da Rehob da makiyayarta.
\v 76 Suka karɓa daga kabilar Naftali: Kedesh a Galili da makiyayarta, Hammon da makiyayarta, Kiriyatayim da makiyayarta.
\s5
\v 77 Ga sauran zuriyar Merari aka ba su daga kabilar Zebulun: Yokheyam, Kartah, Rimmono da makiyayarta da Tabor da makiyayarta;
\v 78 daga na kabilar Ruben a hayin Yodan a Yeriko, a gabashin kogin: Beza a cikin jeji da makiyayarta, Yahza da makiyayarta,
\v 79 Kedemot da makiyayarta, da Mefa'at da makiyayarta.
\s5
\v 80 Daga kabilar Gad, Lebiyawa suka karɓi: Ramot a Giliyad da makiyayarta, Mahanayim da makiyayarta,
\v 81 Heshbon da makiyayarta, da Yazer da makiyayarta.
\s5
\c 7
\cl Sura 7
\p
\v 1 'Ya'yan Issaka huɗu su ne: Tola, Fuwa, Yashub, da Shimron.
\v 2 'Ya'yan Tola su ne; Uzzi, Refayiya, Yeriyel, Yahmai, Ibsam, da Sama'ila. Su ne shugabannin gidajen ubanninsu, daga zuriyar Tola an lissafa su cikin jarumawa a zamanin su. Sun kai mutum 22,600 a cikin zamanin Dauda.
\v 3 Dan Uzzi shi ne Izrahiya. 'Ya'yansa su ne Mika'el, Obadiya, Yowel da Ishiya, dukkansu biyar ɗin shugabannin zuriya ne.
\s5
\v 4 Tare da su kuma suna da taron rundunar yaƙi zambar talatin da shida, bisa ga tsarin dake na dangogin kakanninsu, gama suna da mata yawa da 'ya'ya.
\v 5 'Yan'uwansu, mayaƙan mutane daga dukkan kabilar Issaka, suna da jarumawa dubu tamanin da bakwai, bisa ga lissafin tarihin asalinsu.
\s5
\v 6 'Ya'yan Benyamin uku su ne Bela, Beker, da Yediyayel.
\v 7 'Ya'yan Bela guda biyar su ne Ezbon, Uzzi, Uzziyel, Yerimot, da Iri. Su sojoji ne kuma shugabannin gidajen ubanninsu. Mutanen su sun kai 22,034 mayaƙan mutane, bisa ga jerin lissafin dangogin kakanninsu.
\s5
\v 8 'Ya'yan Beka su ne Zemirah, Yo'ash, Eliyeza, Eliyonai, Omri, Yeremot, Abijah, Anatot, da Alemet. Dukkan waɗannan 'ya'yansa ne.
\v 9 Lissafin dangoginsu yakai 20,200 shugabannin gida idajen ubanninsu kuma jarumawa.
\v 10 Ɗan Yediyel shi ne Bilhan. 'Ya'yan Bilhan su ne Yewush, Benyamin, Ehud, Kena'ana, Zetan, Tarshish, da Ahishaha.
\s5
\v 11 Dukkan waɗannan 'ya'yan Yediyayel. Jerinsu cikin zuriyarsu sun kai 17,200 shugabannin gidajen ubanninsu kuma mayaƙa maza da su ka cancanci hidimar soja.
\v 12 (Shuffitawa da Huffitawa 'ya'yan Ir, da Hushitawa ɗan Aher ne.)
\s5
\v 13 'Ya'yan Naftali su ne Yahziyel, Guni, Yezer, da Shillem. Waɗannan su ne jikokin Bilha.
\s5
\v 14 Manasse ya na da ɗa mai suna Asriyel, wanda ƙwarƙwararsa Ba'aramiye ta haifa. Ta kuma haifi Makir, mahaifin Giliyad.
\v 15 Makir ya ɗauko mace daga wurin Huffitawa da Shuffitawa. Sunan 'yar'uwarta shi ne Ma'aka. Wata zuriyar Manasse kuma shi ne Zelofihad, wanda 'ya'yansa mata ne kaɗai.
\v 16 Ma'aka matar Makir, ta haifa masa ɗa ta kira shi Feresh. Sunan ɗan'uwansa kuma shi ne Sheresh, 'ya'yansa kuma Ulam da Rakem.
\s5
\v 17 'Ɗan Ulam kuma shi ne Bedan. Waɗannan su ne zuriyar Giliyad ɗan Makir ɗan Manasse.
\v 18 'Yar'uwar Giliyad Hammoleket ta haifi Ishhod, Abiyeya, da Mahla.
\v 19 'Ya'yan Shemida su ne Ahiyan, Shekem, Likhi, da Aniyam.
\s5
\v 20 Zuriyar Ifraim su ne kamar haka: ɗan Ifraim shi ne Shutela. Ɗan Shutela shi ne Bered. Ɗan Bered shi ne Tahat. Ɗan Tahat shi ne Eleyada. Ɗan Eliyada shi ne Tahat.
\v 21 Ɗan Tahad shi ne Zabad. Dan Zabad shi ne Shutela. (Ezer da Eleyad mutanen Gat ne suka kashe su, mutanen da aka haifa cikin ƙasar, lokacin da suka je su sace masu shanunsu.
\v 22 Ifraim mahaifinsu ya yi makoki dominsu kwanaki da yawa, 'ya'uwansa kuma suka zo don su ta'azantar da shi.
\s5
\v 23 Ya kwana da matarsa. Sai ta yi ciki ta haifi ɗa. Ifraim ya kira shi Beriya, saboda masifa ta zo wa iyalinsa.)
\v 24 Ɗiyarsa ita ce Sheerah, wadda ta gina Runtse da Sama Bet Horon da Uzzen Sheerah.
\s5
\v 25 Ɗansa shi ne Refha. Ɗan Refha shi ne Reshef. Ɗan Reshef shi ne Tela. Ɗan Tela shi ne Tahan. Ɗan Tahan shi ne Ladan.
\v 26 Ɗan Ladan shi ne Ammihud. Ɗan Ammihud shi ne Elishama.
\v 27 Ɗan Elishama shi ne Nun. Ɗan Nun shi ne Yoshuwa.
\s5
\v 28 Mallakarsu da mazaunansu Betel ne da ƙauyukansu na kewaye. Suka miƙa ta gabashi zuwa Na'aran da yammaci zuwa Gezar da ƙauyukansu, zuwa Shekem da ƙauyukansu zuwa Ayyah da ƙauyukansu.
\v 29 Akan iyaka da Manasse su ne Bet Shan da ƙauyukansu, Ta'anak da ƙauyukansu Megiddo da ƙauyukansu, da Dor da ƙauyukansu. A cikin waɗannan garuruwa zuriyar Yosef ɗan Isra'ila suke zaune.
\s5
\v 30 'Ya'yan Asha su ne Imna, Ishba, Ishbi, da Beriya. Serah 'yar'uwar su ce.
\v 31 'Ya'yan Beriya su ne Heber da Malkiyel, shi ne mahaifin Birza'it.
\v 32 'Ya'yan Heber su ne Yaflet, Shomer da Hotman. Shuwa 'yar'uwarsu ce.
\s5
\v 33 'Ya'yan Yaflet su ne Fasak, Bimhal, da Ashbat. Waɗannan su ne 'ya'yan Yaflet.
\v 34 Shomer, ɗan'uwan Yaflet, yana da 'ya'ya kamar haka: Roga, Hubba, da Aram.
\v 35 Ɗan'uwan Shemer, wato Helem, yana da 'ya'ya kamar haka: Zofa, Imna, Shelesh, da Amal.
\s5
\v 36 'Ya'yan Zofa su ne Suwa, Harnefa, Shuwal, Beri, Imrah,
\v 37 Bezer, Hod, Shamma, Shilsha, Itran, da Beera.
\v 38 'Ya'yan Yeter su ne Yefunne, Fisfa, da Ara.
\s5
\v 39 'Ya'yan Ulla su ne Ara, Hanniyel, da Riziya.
\v 40 Duk waɗannan zuriyar Ashar ne. Su ne kakannin dangogi, shugabannin gidajen ubanninsu, fitattun mutane, mayaƙan mutane, sarakuna a cikin shugabanni. Sun kai su dubu ashirin da shida mazaje da suka cancanta domin yin hidimar aikin soja, bisa ga jerin lissafinsu.
\s5
\c 8
\cl Sura 8
\p
\v 1 'Ya'yan Benyamin biyar su ne Bela ɗan farinsa, Ashbel, Aharan,
\v 2 Nohah, da Rafa.
\v 3 'Ya'yan Bela su ne Adda, Gera, Abihud,
\v 4 Abishuwa, Na'aman, Ahowa,
\v 5 Gera, Shefufan, da Huram.
\s5
\v 6 Waɗannan su ne zuriyar Ehud shugabannin gidajen ubanninsu domin mazaunan Geba, waɗanda aka tilasta masu su tafi Manahat:
\v 7 Na'aman, Ahiyah, da Gera. Na ƙarshen, Gera, ya jagorance su cikin tafiyarsu. Shi ne mahaifin Uzza da Ahihud.
\s5
\v 8 Shaharayim ya zama mahaifni 'ya'ya cikin ƙasar Mowab, bayan ya saki matansa Hushim da Ba'ara.
\v 9 Ta wurin matarsa Hodesh, Shaharayim ya zama mahaifin Yobab, Zibiya, Mesha, Malkam,
\v 10 Yewuz, Shakiya, da Mirma. Waɗannan su ne 'ya'yansa, shugabanni cikin gidajen ubanninsu.
\v 11 Ya rigaya ya zama mahaifin Abitub da Elfa'al ta wurin Hushim.
\s5
\v 12 'Ya'yan Elfa'al su ne Eber, Misham, da Shemed (wanda ya gina Ono da Lod tare da ƙauyukan da ke kewaye da su).
\v 13 Akwai kuma Beriya da Shema. Su ne shugabannin zuriyar da suke zama cikin Aijalon, waɗanda suka kori mazaunan Gat.
\s5
\v 14 Beriya yana da waɗannan 'ya'ya: Ahio, Shashak, Yeremot,
\v 15 Zebadiya, Arad, Eder,
\v 16 Mika'el, Ishfa, da Yoha.
\v 17 Elfa'al yana da waɗannan 'ya'yan: Zebadiya, Meshullam, Hizki,
\v 18 Heber, Ishmerai, Izliya, da Yobab.
\s5
\v 19 Shimei yana da waɗannan 'ya'yan: Yakim, Zikri, Zabdi,
\v 20 Eliyenai, Zilletai, Eliyel,
\v 21 Adayiya, Berayiya, da Shimrat.
\s5
\v 22 Shashak yana da waɗannan 'ya'yan: Ishfan, Eber, Eliyel,
\v 23 Abdon, Zikri, Hanan,
\v 24 Hananiya, Elam, Antotijah,
\v 25 Ifdeyiya, da Fenuwel.
\s5
\v 26 Yeroham na da waɗannan 'ya'yan: Shamsherai, Shehariya, Ataliya,
\v 27 Ya'areshiya, Iliya da Zikri.
\v 28 Waɗannan su ne shugabannin gidajen ubanninsu da suka zauna cikin Yerusalem.
\s5
\v 29 Yeyil, mahaifin Gibiyon, sunan matarsa ita ce Ma'aka, ya zamna cikin Gibiyon.
\v 30 'Ɗan farinsa shi ne Abdon, sai Zur, Kish, Ba'al, Nadab,
\v 31 Gedor, Ahiyo, da Zeker.
\s5
\v 32 Wani daga cikin 'ya'yan Yeyil shi ne Miklot, wanda ya zama mahaifin Shimeya. Sun zauna kusa da 'yan'uwansu cikin Yerusalem.
\v 33 Ner shi ne mahaifin Kish. Kish shi ne mahaifin Saul. Saul shi ne mahaifin Yonatan, Malki-Shuwa, Abinadab, da Esh-Ba'al.
\v 34 'Ɗan Yonatan shi ne Merib-Ba'al. Merib-Ba'al shi ne mahaifin Mika.
\s5
\v 35 'Ya'yan Mika su ne, Fithon, Melek, Tareya, da Ahaz.
\v 36 Ahaz ya zama mahaifin Yehoada. Yehoada shi ne mahaifin Alemet, Azmabet da Zimri, Zimri shi ne mahaifin Moza.
\v 37 Moza shi ne mahaifin Bineya. Bineya shi ne mahaifin Rafa. Rafa shi ne mahaifin Eliyasa. Eliyasa shi ne mahaifin Azel.
\s5
\v 38 Azel yana da 'ya'ya shida: Azrikam, Bokeru, Ishmail, Sheyariya, Obadiya, da Hanan. Dukkan waɗannan 'ya'yan Azel ne.
\v 39 'Ya'yan Eshek, da ɗan'uwansa, su ne Ulam ɗan farinsa, Yewush na biyu, da Elifelet na uku.
\v 40 'Ya'yan Ulam mayaƙa ne da maharba. Suna da 'ya'ya da jikoki da yawa, jimillarsu 150. Dukkan waɗannan daga zuriyar Benyamin suke.
\s5
\c 9
\cl Sura 9
\p
\v 1 Haka dukkan Isra'ila aka rubuta su bisa ga tarihin asalinsu. An rubuta su cikin littafin sarakunan Isra'ila. Amma game da Yahuda, an ɗauke su zuwa bauta cikin Babila saboda zunubinsu.
\v 2 Na farko da suka zauna cikin biranensu su ne waɗansu Isra'ilawa, firistoci, Lebiyawa da bayin haikali.
\v 3 Waɗansu zuriyar Yahuda, Benyamin, Ifraim, da Manasse sun zauna cikin Yerusalem.
\s5
\v 4 Waɗanda suka zauna sun haɗa da Utai ɗan Ammihud ɗan Omri ɗan Imri ɗan Bani, ɗaya daga cikin zuriyar Ferez ɗan Yahuda.
\v 5 A cikin Shelonawa su ne Asayiya ɗan fari da 'ya'yansa kuma.
\v 6 A cikin zuriyar Zera akwai Yewuel. Yawan zuriyarsu ta kai 690.
\s5
\v 7 Daga zuriyar Benyamin akwai Sallu ɗan Meshullam ɗan Hodabiya ɗan Hassenuya.
\v 8 Akwai kuma Ibneyiya ɗan Yeroham; Elah ɗan Uzzi ɗan Mikri; da Meshullam ɗan Shefatiya ɗan Rewuel ɗan Ibnijah.
\v 9 'Yan'uwansu da ke rubuce cikin tarihin asalinsu sun kai 956. Dukkan waɗannan mutanen shugabanni ne cikin zuriyar kakanninsu.
\s5
\v 10 Firistoci su ne Yedayiya, Yeho'iarib, da Yakin.
\v 11 Akwai kuma Azariya ɗan Hilkiya ɗan Meshullam ɗan Zadok ɗan Meraiyot ɗan Ahitub, shugaba a cikin gidan Allah.
\s5
\v 12 Akwai Adayiya ɗan Yeroham ɗan Fashur ɗan Malkijah. Akwai kuma Ma'asai ɗan Adiyel ɗan Yahzera ɗan Meshullam ɗan Meshillemit ɗan Immer.
\v 13 'Yan'uwansu, da suke shugabanni cikin gidajen kakanninsu, sun kai 1,760. Mutane ne da suka iya aiki cikin gidan Allah.
\s5
\v 14 A wajen Lebiyawa, akwai Shemaiya ɗan Hasshub ɗan Azrikam ɗan Hashabiya, daga zuriyar Merari.
\v 15 Akwai kuma Bakbakkar, Heresh, Galal, da Mattaniya ɗan Mika ɗan Zikri ɗan Asaf.
\v 16 Akwai kuma Obadiya ɗan Shemaiya ɗan Galal ɗan Yedutun; and Berekiya ɗan Asa ɗan Elkana, wanda ya zauna a ƙauyukan Netofatawa.
\s5
\v 17 Matsaran ƙofa su ne Shallum, Akkub, Talmon, Ahiman, da zuriyarsu. Shullam shi ne shugabansu.
\v 18 Dã suna tsaro a ƙofar sarki ta wajen gabas domin sansanin zuriyar Lebi.
\v 19 Shallum ɗan Kore ɗan Ebiyasaf, wanda a matsayinsa na ɗan Kora, da 'yan'uwansa daga gidan mahaifinsa, su Korawa, suna bisa aikin hidima, su na kula da ƙofar rumfa, kamar yadda kakanninsu suka kula da sansanin Yahweh, suna kuma tsaron wurin shiga.
\s5
\v 20 Finehas ɗan Eliyeza shi ne shugabansu a dã, Yahweh kuma yana tare da shi.
\v 21 Zekariya ɗan Meshelemiya shi ne mai tsaron ƙofar shiga haikali, "rumfar taruwa."
\s5
\v 22 Dukkan waɗanda aka zaɓe su matsaran ƙofofi sun kai 212. An rubata sunayensu cikin lissafin mutane cikin ƙauyukansu. Dauda da Sama'ila mai gani sun sanya su cikin muƙamansu na amana.
\v 23 Da su da 'ya'yansu sun kula da ƙofofin gidan Yahweh, wato rumfar sujada.
\v 24 An sanya matsran ƙofofi a dukkan kusurwoyi huɗu, wajen gabas, yamma, arewa, da kudu.
\s5
\v 25 'Yan'uwansu, da ke zaune a ƙauyukansu, sun zo domin kewayawa na kwana bakwai, a juyi.
\v 26 Amma shugabannin matsara huɗu, wato Lebiyawa, an sanya su kula da ɗakuna da ɗakunan ajiya cikin gidan Allah.
\v 27 Sukan tsaya dukkan dare a wurarensu kewaye da gidan Allah. Domin suke da haƙƙin kula da shi. Za su buɗe shi kowacce safiya.
\s5
\v 28 Waɗansun su suna kula da kayan haikali; suna ƙirga su yayin da aka kawo su ko aka fitar da su.
\v 29 Waɗansu kuma an sanya su kula da abubuwa masu tsarki, kayayyaki, da kayan da aka tanada, waɗanda sun haɗa da gari mai laushi, ruwan inabi, mai, da turaren ƙonawa, da kayan yaji.
\s5
\v 30 Waɗansu 'ya'yan firistoci sukan haɗa kayan yaji.
\v 31 Mattitiya, ɗaya daga cikin Lebiyawa wanda ɗan fari ne a wurin Shallum Korahiye, shi ne ke ɗauke da nawayar shirya gurasa domin baye-baye.
\v 32 Waɗansu 'yan'uwansu, zuriyar Kohatawa, su ne masu kula da yin gurasa, su shirya kowacce Asabaci.
\s5
\v 33 Mawaƙa da shugabannin gidajen ubannin Lebiyawa sun zauna cikin ɗakuna a wuri mai tsarki lokacin da ba su da wani aiki, domin dole su aiwatar da nasu ayyuka dare da rana.
\v 34 Waɗannan shugabannin gidajen ubannin cikin Lebiyawa ne, kamar yadda ya ke a jere cikin rubutaccen tarihin asalinsu. Suna zama cikin Yerusalem.
\s5
\v 35 Mahaifin Gibiyon, Yeyiyel, sunan matarsa itace Ma'aka, ya zauna cikin Gibiyon.
\v 36 'Dan farinsa shi ne Abdon, ɗansa shi ne Zur, Kish, Ba'al, Ner, Nadab,
\v 37 Gedor Ahiyo, Zekariya da Miklot.
\s5
\v 38 Miklot shi ne mahaifin Shimeyam. Sun zauna kusa da 'yan'uwansu cikin Yerusalem.
\v 39 Ner shi ne mahaifin Kish. Kish mahaifin Saul. Saul mahaifin Yonatan, Malki-Shuwa, Abinadab, da Esh-Ba'al.
\v 40 Ɗan Yonatan shi ne Merib-Ba'al. Merib-Ba'al shi ne mahaifin Mika.
\s5
\v 41 'Ya'yan Mika su ne Fithon, Melek, Tareya, da Ahaz.
\v 42 Ahaz shi ne mahaifin Yada. Yada shi ne mahaifin Alemet, Azmabet, da Zimri. Zimri shi ne mahaifin Moza.
\v 43 Moza shi ne mahaifin Bineya. Bineya shi ne mahaifin Refayiya. Refayiya shi ne mahaifin Eliyasa. Eliyasa shi ne mahaifin Azel.
\v 44 'Ya'yan Azel shida su ne Azrikam, Bokeru, Ishma'el, Sheyariya, Obadiya, da Hanan. Waɗannan su ne 'Ya'yan Azel.
\s5
\c 10
\cl Sura 10
\p
\v 1 Yanzu fa Filistiyawa suka yi yaƙi da Isra'ila. Kowanne mutumin Isra'ila ya gudu daga gaban Filistiyawa su ka faɗi matattu a kan Tsaunin Gilbowa.
\v 2 Filistiyawa suka runtumi Saul da ɗansa kusa kusa. Filistiyawa suka kashe Yonatan, Abinadab, da Malki-Shuwa, 'ya'yansa.
\v 3 Yaƙi ya tsananta gãba da Saul ƙwarai, maharba kuma sun cim masa, kuma suka yi masa rauni.
\s5
\v 4 Daga nan sai Saul ya ceda mai ɗaukar masa makamai, "Ka zare takobinka ka kashe ni da ita. In ba haka ba, waɗannan marasa kaciyar za su zo su zage ni." Amma mai ɗaukar makamansa yaƙi, domin yana jin tsoro ƙwarai. Sai Saul ya ɗauki takobinsa ya faɗi a kanta.
\s5
\v 5 Sa'ad da mai ɗaukar makamansa ya ga Saul ya mutu, shi ma sai ya faɗi a kan takobinsa ya mutu.
\v 6 Da haka Saul ya mutu, da 'ya'yansa uku. Dukkan iyalin gidansa suka mutu tare.
\s5
\v 7 Sa 'ad da kowanne mutum a Isra'ila da ke cikin kwari yaga cewa sun gudu, kuma Saul da 'ya'yansa sun mutu, sai suka bar biranensu suka gudu. Daga nan sai Filistiyawa suka zo suka zauna cikinsu.
\v 8 Ya zama kuwa washegari, sa'ad da Filistiyawa suka zo su ɗauki kayan matattu, sun tarar da Saul da 'ya'yansa matattu a Tsaunin Gilbowa.
\s5
\v 9 Suka tuɓe shi suka ɗauki kansa da kayan yaƙinsa. Suka aikar da saƙo ko'ina cikin Filisitaya a kuma kai labarin ga gumakansu da mutane.
\v 10 Suka sa kayan yaƙinsa cikin haikalin allolinsu, suka kafe kansa a gidan Dagon.
\s5
\v 11 Sa'ad da dukkan mutanen Yabesh Giliyad suka ji dukkan abin da Filistiyawa suka yi wa Saul,
\v 12 dukkan maza mayaƙa su ka je suka ɗauki jikin Saul da na 'ya'yansa, suka kawo su Yabesh. Suka bizne ƙasusuwansu ƙarƙashin itacen rimi cikin Yabesh suka yi azumi kwana bakwai.
\s5
\v 13 Saul ya mutu saboda ya yi rashin amincin ga Yahweh. Bai yi biyayya ga umarnan Yahweh ba, amma ya nemi shawara a wurin wata mai yin magana da matattu.
\v 14 Bai nemi shawara daga wurin Yahweh ba, shi yasa Yahweh ya kashe shi ya mayar da mulkin ga Dauda ɗan Yesse.
\s5
\c 11
\cl Sura 11
\p
\v 1 Daga nan si dukkan Isra'ila suka zo wurin Dauda a Hebron suka ce, "Duba, mu ƙashinka da namanka ne.
\v 2 Cikin kwanakin dã, lokacin da Saul ya ke sarki a bisanmu, kai ne ka ke jagorancin mutanen Isra'ila. Yahweh Allahnka ya ce maka, 'Za ka yi kiwon mutanena Isra'ila, kuma zaka zama mai mulki bisan mutanena Isra'ila.""
\v 3 Dukkan dattawan Isra'ila suka zo wurin sarki a Hebron, Dauda ya yi alƙawari da su gaban Yahweh. Suka ƙeɓe Dauda sarki a bisan Isra'ila. Ta haka maganar Yahweh wadda Sama'ila ya furta ta zama gaskiya.
\s5
\v 4 Dauda da dukkan Isra'ila suka je Isra'ila (wato, Yebus). Yebusawa mazaunan ƙasar, su na can.
\v 5 Mazaunan Yebus suka ce da Dauda, "Ba za ka zo nan ba."
\v 6 Amma Dauda ya ci kagarar Sihiyona, wato, Birnin Dauda. Dauda ya ce, "Duk wanda ya fara bugun Yebusawa zai zama shugaban yaƙi." Yowab ɗan Zeruya ya fara kai hari, aka mai she shi ya zama shugaba.
\s5
\v 7 Daga nan Dauda ya fara zama cikin kagara. Sai suka kira ta birnin Dauda.
\v 8 Ya gina garu kewaye da birnin daga Millo da baya zuwa kewayan bangon. Yowab ya gina sauran birnin.
\v 9 Dauda ya zama babba ya ƙasaita saboda Yahweh mai runduna yana tare da shi.
\s5
\v 10 Wɗannan su ne shugabanni ƙarƙashin Dauda, waɗanda su ka taimaki mulkin Dauda ya zama da karfi, tare da dukkan Isra'ila, suka sa shi ya zama sarki, da biyayya da maganar Yahweh game da Isra'ila.
\v 11 Waɗannan su ne jerin ƙwararrun sojojin Dauda: Yashobeyam, ɗan Bahakmonite, shi ne hafsan ofisoshi. Ya kashe mutum ɗari uku da mashin sa a lokaci ɗaya.
\s5
\v 12 Bayan sa sai Eliyeza ɗan Dodo, Ba'ahohite, ɗaya daga cikin jarumawan nan uku.
\v 13 Yana tare da Dauda a Fas Dammim, a wurin Filistiyawa suka taru domin yaƙi, inda akwai yankin ƙasa mutane kuma suka gudu daga gaban Filistiyawa.
\v 14 Suka tsaya a tsakiyar filin. Suka kãre shi suka kuma kashe Filistiyawa da yawa Yahweh kuma ya cece su da babbar nasara.
\s5
\v 15 Daga nan mutum uku cikin talatin suka tafi wurin Dauda cikin dutse, a kogon Adullam. Mutanen Filistiyawa suka yi sansani a cikin Kwarin Refayim.
\v 16 A lokacin nan Dauda yana cikin kagara, a kogo, yayin da Filistiyawa suka kafa sansanin su a Betlehem.
\v 17 Dauda ya ji ƙishin ruwa sai ya ce, "Da ma wani zaya bani ruwa in sha daga rijiyar da ke a Betlehem, rijiyar dake a bakin ƙofa!"
\s5
\v 18 Sai jarumawan nan uku suka kụtsa cikin rundunar Filistiyawa suka ɗebo ruwa daga cikin rijiyar Betlehem, rijiyar da ke bakin ƙofa. Suka ɗauko ruwan suka kawo wa Dauda, amma yaƙi shan sa. Maimakon haka, ya tsiyaye shi ga Yahweh.
\v 19 Sai ya ce, "Yahweh, ya nisantarda wannan daga gare ni, da zan sha wannan ruwan. Zan sha jinin mutane waɗanda su ka sadaukar da rayukansu?" Saboda sun sa ran su cikin haɗari, Dauda ya ƙi shan ruwan. Wannan shi ne abin da jarumawan nan uku suka yi.
\s5
\v 20 Abishai ɗan'uwan Yowab, shugabane na jarumawan uku. Ya taɓa amfani da mãshin sa ya kashe mutum ɗari uku. An faɗe shi cikin su ukun nan.
\v 21 A cikin ukun ɗin ya sami girmamawa riɓi biyu har ya zama shugabansu. Ko da shike baya ɗaya daga cikin su.
\s5
\v 22 Benaiya ɗan Yeho'iada ya zama da ƙarfi daga Kabzeel wanda ya yi manyan abubuwa. Ya kashe 'ya'ya biyu na Ariyel mutumin Mowab. Ya kuma sauka cikin rami ya kashe zaki lokacin sanyin dusar ƙanƙara.
\v 23 Har ya kashe Bamasare, tsawon mutumin ya kai kamu biyar. Bamasaren yana da babban mãshi misalin itacen sãƙa amma ya je wurin sa da sanda kawai. Ya fizge mãshin daga hanun Bamasaren ya kashe shi da mãshinsa.
\s5
\v 24 Benaiya ɗan Yeho'iada ya yi waɗannan ayyuka, an sanya sunansa tare da jarumawan uku.
\v 25 An mutunta shi fiye da sojojin nan talatin gaba ɗaya, amma ba kamar ƙwararrun sojojin nan uku ba. Duk da haka Dauda ya sanya shi shugaba akan matsaransa.
\s5
\v 26 Jarumawan mutanen su ne: Asahel ɗan'uwan Yowab, Elhanan ɗan Dodo na Betlehem,
\v 27 Shammot Baharore, Helek Bafelone,
\v 28 Ira ɗan Ikkesh Batekoye, Abiyeza Ba'anatote,
\v 29 Sibbekai Bahushate, Ilai Ba'ahohite.
\s5
\v 30 Maharai Banetofate, Heled ɗan Baanah Banetofate,
\v 31 Ittai ɗan Ribai na Gibiya na zuriyar Benyamin, Benaiya Bafiratone,
\v 32 Hurai na kwarurrukan Ga'ash, Abiyel Ba'arbate,
\v 33 Azmabet Baharume, Eliyaba Basha'albone,
\s5
\v 34 'ya'yan Hashem Bagizoniye, Yonatan ɗan Shagi Baharare,
\v 35 Ahiyam ɗan Sakar Baharare, Elifal ɗan Ur,
\v 36 Hefar Bamekarate, Ahija Bafelone,
\v 37 Hezro Bakarmele, Na'arai ɗan Ezbai,
\s5
\v 38 Yowel ɗan'uwan Natan, Mibhar ɗan Hagri,
\v 39 Zelek Ba'moniye, Naharai Baberote (mai ɗaukar wa Yowab makamai ɗan Zeruyiya)
\v 40 Ira Ba'itriye, Gareb Ba'itriye,
\v 41 Yuriya Bahitte, Zadab ɗan Ahlai,
\s5
\v 42 Adina ɗan Shiza Barubeniye (shugaban Rubenawa) da mutum talatin tare dashi,
\v 43 Hanan ɗan Ma'aka da Yoshafat Bamitiniye,
\v 44 Uzziya Ba'ashterate, Shama da Yeyiyel 'ya'yan Hotam Ba'arowaye,
\s5
\v 45 Yediyayel ɗan Shimri, Yoha (ɗan'uwansa Batize),
\v 46 Eliyel Bamahabe, Yeribai da Yoshabiya 'ya'yan Elna'am, Itma Bamowabe,
\v 47 Eliyel, Obed, da Ya'asiel Bamezobate.
\s5
\c 12
\cl Sura 12
\p
\v 1 Waɗannan su ne waɗanda suka zo wurin Dauda a Ziklag, tun lokacin da bai iya tsayawa gaban Saul ɗan Kish ba. Suna cikin sojoji, mataimakan sa a cikin yaƙi.
\v 2 Maharban baka ne kuma sukan harba ta dama da hagu sukan jefa dutse da majaujawa wajen harbin kibiya da baka. Su mutanen Benyamin ne, mutanen kabilar Saul.
\s5
\v 3 Sarki shi ne Ahiyaza, sai Yowash, dukkan su 'ya'yan Shema'ah Bagibeyate. Akwai Yeziyel da Felet, 'ya'yan Azmebet. Akwai kuma Berakah, Yehu Ba'anatote,
\v 4 Ishmaiya Bagibiyone, sojane cikin talatin ɗin (Kuma shugaban talatin ɗin); Irmiya, Yahaziyel, Yonanan, Yozabad Bagaderate.
\s5
\v 5 Eluzai, Yerimot, Beyaliye, Shemariya, Shefatiya Baharufiye,
\v 6 Koratawa, Elkana, Isshiya, Azarel, Yoyezar, Yashobeyam, da
\v 7 Yowela da Zebadiya, 'ya'yan Yeroham na Gedor.
\s5
\v 8 Waɗansu Gadawa su ka haɗu da Dauda a kagara cikin jeji. Su jarumawa ne, Horarru domin yaƙi, waɗanda sun iya garkuwa da mashi; fuskokinsu kamar na zakuna. Sauri gare su kamar bareyi a kan duwatsu.
\s5
\v 9 Akwai Ezer shugaba, Obadiya na biyu, Eliyab na uku,
\v 10 Mishmanna na huɗu, Irmiya na biyar,
\v 11 Attai na shida, Eliyel na bakwai,
\v 12 Yonatan na takwas, Elzabad na tara,
\v 13 Irmiya na goma, Makbannai na sha ɗaya.
\s5
\v 14 Waɗannan 'ya'yan Gad shugabannin runduna ne. ƙaraminsu shi ke jagorancin ɗari, babbansu shi ke jagorancin dubbai.
\v 15 Sun ƙetare Yodan cikin wata na fari, sa'ad da ya yi ambaliya ya kori dukkan waɗanda suke zama cikin kwarurruka, dukka da na wajen gabas da na wajen yamma.
\s5
\v 16 Waɗansu mutanen Benyamin da na Yahuda suka zo kagara wurin Dauda.
\v 17 Dauda ya fita domin ya tarye su ya yi masu jawabi yace: "Idan kun zo wurina da salama ku taimakeni, za ku iya haɗa hannu da ni. Amma idan kun zo ne domin ku bashe ni ga abokan gãba ta, bari Allah na kakanninku ya gani ya tsauta maku, gama ban yi wani abin da ba dai-dai ba."
\s5
\v 18 Sa'an nan sai Ruhu ya sauko kan Amasai, wanda ya ke shugaban talatin ɗin. Amasai ya ce, "Mu na ka ne, ya Dauda. Wajen ka mu ke, ya ɗan Yesse. Salama, bari salama ta kasance ga duk wanda ya taimakeka. Bari salama ta kasance ga masu taimakonka, gama Allahnka ya na taimakonka." Daga nan Dauda ya karɓe su ya sa su zama shugabanni akan jama'arsa.
\s5
\v 19 Waɗansu daga Manasse ku ma suka koma wajen Dauda sa'ad da ya zo tare da Filistiyawa domin ya yi yaƙi da Saul. Duk da haka ba su taimaki Filistiyawa ba, saboda shugabannin Filistiyawa sun tuntuɓi junansu sa'an nan suka sallame shi. Suka ce, "Zai koma wajen ubangidansa Saul zai jawo haɗari ga rayukanmu."
\v 20 Da ya je Ziklag, mutanen Manasse da su ka haɗa hannu da su su ne Adna, Yozabad, Yediyayel, Mika'el, Yozabad, Elihu, da Zilletai, shugabanni na dubbai na Manasse.
\s5
\v 21 Sun taimaki Dauda yaƙi da taron mahara, gama su jarumawa ne. Daga baya su ka zama shugabanni cikin runduna.
\v 22 Yau da gobe, mutane suka yi ta zuwa wurin Dauda domin su taimake shi, har aka sami babbar rundunar soja, kamar rundunar sojojin Allah.
\s5
\v 23 Wannan shi ne lissafin sojoji masu makamai domin yaƙi, waɗanda suka zo wurin Dauda a Hebron, domin su juyar da mulkin Saul zuwa gare shi, domin tabbatar da maganar Yahweh.
\v 24 Daga Yahuda waɗanda suke ɗauke da garkuwa da mãshi sun kai 6,800, a shirye domin yaƙi.
\v 25 Daga zuriyar Simiyon sun kai jarumawa 7,100
\s5
\v 26 Daga zuriyar Lebiyawa sun kai mayaƙa 4,600.
\v 27 Yehoyada shi ne shugaban zuriyar 'ya'yan Haruna tare da shi akwai mutum 3,700.
\v 28 Tare da Zadok saurayi, ƙaƙƙarfa, mutum mai ƙarfin hali, sun kai shugabanni ashirin da biyu daga iyalin mahaifinsa.
\s5
\v 29 Daga Benyamin, kabilar Saul, sun kai dubu uku. Yawancinsu suka zama da biyayya ga Saul har zuwa lokacin nan.
\v 30 Daga Ifraim sun kai mayaƙa 20,800, suna cikin gidajen mahaifansu.
\v 31 Daga rabin kabilar Manasse akwai mutane dubu goma sha takwas waɗanda suka zo domin su naɗa Dauda sarki.
\s5
\v 32 Daga Issaka, akwai shugabanni ɗari biyu masu gane zamanai sun san abin da ya kamata Isra'ila su yi. Dukkan 'yan'uwansu suna ƙarƙashin mulkinsu.
\v 33 Daga Zebulun akwai mayaƙa dubu hamsin, shiryayyu domin yaƙi, da dukkan makaman yaƙi, a shirye suke suyi biyayya da zuciya ɗaya.
\s5
\v 34 Daga Naftali akwai shugabanni dubu, tare da su kuma mutum dubu talatin da bakwai tare da garkuwa da mãsu.
\v 35 Daga Danawa akwai mutane 28,600 shiryayyu domin yaƙi.
\s5
\v 36 Daga Asha akwai mutane dubu arba'in shiryayyu domin yaƙi.
\v 37 Daga ɗaya ƙetaren Yodan, daga Rubenawa, Gadawa, da rabin kabilar Manasse, akwai mutane 120,000 shirye domin kowanne irin yaƙi.
\s5
\v 38 Dukkan waɗannan sojojin, shiryayyu ne domin yaƙi, sun zo Hebron da tsayayyar manufa wato su naɗa Dauda sarki bisa Isra'ila.
\v 39 Dukkan sauran Isra'ila kuma sun amince ya zama sarki. Suna can tare da Dauda kwana uku, suna ci da sha, gama 'yan'uwansu sun aike su da guzuri.
\v 40 Har yanzu kuma, waɗanda ke kusa da su, kamar su Issaka da Zebulun da Naftali, sun kawo abinci akan jakuna da raƙuma, alfadarai, da shanu, guzurin gari, kauɗar 'ya'yan ɓaure, ruwan inabi, mai, shanu, da tumaki, gama Isra'ila tana murna.
\s5
\c 13
\cl Sura 13
\p
\v 1 Dauda ya tuntuɓi shugabanni na mutum dubbai da na ɗaruruwa, tare ta kowanne shugaba.
\v 2 Dauda ya ce da dukkan taron Isra'ila, "Idan kun ga ya yi maku kyau, idan kuma wannan ya zo ne daga wurin Yahweh Allahnmu, bari mu aika da 'yan saƙo ko'ina ga 'yan'uwanmu, waɗanda suka rage cikin dukkan lardunan Isra'ila, ga Firistoci da Lebiyawa waɗanda suke cikin garuruwansu. Bari a sanar da su cewa su haɗa kai da mu.
\v 3 Bari mu kawo akwatin Allahnmu gare mu, gama ba mu nemi nufinsa a cikin kwanakin mulkin Saul ba."
\v 4 Dukkan taron jama'a suka yarda da waɗannan abubuwa, saboda ya yi dai-dai a idanun dukkan mutane.
\s5
\v 5 Dauda fa ya tara dukkan Isra'ila tare, daga Shihor Kogi a cikin Masar zuwa Lebo Hamat, domin kawo akwatin Allah daga Kiriyat Yeyarim.
\v 6 Dauda da dukkan Isra'ila suka hau zuwa Baalah, wato Kiriyat Yeyarim, wanda ke na Yahuda, domin daga can za a ɗauko akwatin Allah, wanda ake kira da sunan Yahweh, wanda ya ke zaune yana mulki akan Kerubim
\s5
\v 7 Sai suka sanya akwatin Allah akan sabon keken shanu. Sun fito da shi daga gidan Abinadab. Uzza da Ahiyo suna kula da keken shanun.
\v 8 Dauda da dukkan Isra'ila suna murna a gaban Allah da dukkan ƙarfinsu. Suna waƙa da garayu da molaye, kugenni, da kakaki
\s5
\v 9 Sa'ad da suka zo masussukar Kidon, Uzza ya miƙa hannunsa domin ya riƙe akwatin, saboda shanun sun yi tuntuɓe.
\v 10 Daga nan fushin Yahweh ya yi ƙuna akan Uzza, Yahweh ya kashe shi domin Uzza ya miƙa hannunsa ya taɓa akwatin. Ya mutu a wurin a gaban Allah.
\v 11 Dauda ya yi fushi saboda Yahweh ya abkawa Uzza. Ana kiran wannan wurin Ferez Uzza har wa yau.
\s5
\v 12 Dauda ya ji tsoron Allah a wannan rana. Ya ce, "Ya ya zan kawo akwatin Allah in dawo da shi gidana?"
\v 13 Dauda bai gusar da akwatin zuwa birnin Dauda ba, amma ya sa shi a gefe cikin gidan Obed Idom Bagittiye.
\v 14 Akwatin Allah ya kasance cikin gidan Obed Idom har wata uku. Yahweh ya albarkaci gidansa da dukkan abin da ya mallaka.
\s5
\c 14
\cl Sura 14
\p
\v 1 Daga nan Hiram sarkin Taya ya aika da 'yan saƙo wurin Dauda, da itatuwan Sida, kafintoci da magina. Su ka gina masa gida.
\v 2 Dauda kuwa ya sa ni Yahweh ya tabbatar da shi zama sarki akan Isra'ila, kuma mulkinsa zai ɗaukaka sama domin taimakon mutanensa Isra'ila.
\s5
\v 3 A cikin Yerusalem, Dauda ya auri waɗansu mata, ya zama mahaifin waɗansu 'ya'ya maza da 'ya'ya mata.
\v 4 Waɗannan su ne 'ya'yan da aka haifa masa cikin Yerusalem: Shammuwa, Shobab, Natan, Solomon,
\v 5 Ibha, Elishuwa, Elfelet,
\v 6 Noga, Nefeg, Yafiya,
\v 7 Elishama, Biliyada, da Elifelet.
\s5
\v 8 Sa'ad da Filistiyawa su ka ji cewa an keɓe Dauda ya zama sarki bisa Isra'ila, dukka suka fita suna neman sa. Amma Dauda ya ji labarin sai ya fita ya yi yaƙi da su.
\v 9 Filistiyawa sun rigaya sun kawo hari cikin kwarin Refayim.
\s5
\v 10 Daga nan Dauda ya nemi taimako a wurin Allah. Ya ce, "Ko zan iya kai wa Filistiyawa hari? Za ka bani nasara akan su?" Yahweh ya ce masa, "Kai masu hari, gama lallai zan ba she su gare ka."
\v 11 Sai suka zo Ba'al Ferazim, a can ya yi nasara da su. Ya yaba ya ce, "Yahweh ya fasa abokan gãbata ta hannuna, kamar fasuwar ambaliyar ruwa." Sunan wannan wurin ya zama Ba'al Ferazim.
\v 12 Filistiyawa suka bar allolinsu a wurin, Dauda kuma ya umarta a ƙone su.
\s5
\v 13 Filistiyawa suka sake kai hari a cikin kwari.
\v 14 Dauda ya sake neman taimako a wurin Allah. Allah ya ce masa, ba za ka kai hari ta gabansu ba, amma ka kewaye su ta itatuwan balsam sai ka kai masu hari ta baya."
\s5
\v 15 Sa'ad da ka ji motsin tafiya cikin iska ta itatuwan balsam, daga nan sai ka kai hari da ƙarfi. Ka yi haka gama Allah ya rigaya ya tafi a gabanka domin ya bugi rundunar Filistiyawa."
\v 16 Dauda ya yi kamar yadda Allah ya umarce shi. Ya ci nasara da rundunar Filistiyawa tun daga Gibiyon har zuwa Gezar.
\v 17 Daga nan sunan Dauda ya bazu zuwa ko'ina cikin dukkan ƙasashe, Yahweh kuma ya sa dukkan ƙasashe su ji tsoron sa.
\s5
\c 15
\cl Sura 15
\p
\v 1 Dauda ya gina wa kansa gidaje a cikin birnin Dauda. Ya shirya rumfa saboda akwatinin Yahweh inda a ka ajiye shi.
\v 2 Sa'an nan Dauda yace, "Lebiyawa ne kaɗai za su ɗauki akwatin Yahweh, domin su aka zaɓa su ɗauki akwatin Yahweh, su yi masa hidima har abada."
\v 3 Sa'an nan Dauda ya tattara dukkan Isra'ila a Yerusalem domin a kawo akwatin Yahweh wurin da ya shirya masa.
\s5
\v 4 Dauda ya tattara zuriyar Haruna da Lebiyawa.
\v 5 Daga zuriyar Kohat akwai shugaba wato Yuriyel, da 'yan'uwansa mutum 120.
\v 6 Daga zuriyar Merari akwai shugaba wato Asayiya, da 'yan'uwansa mutum 220.
\s5
\v 7 Daga zuriyar Geshon akwai shugaba wato Yowel, da 'yan'uwansa mutum 130.
\v 8 Daga zuriyar Elizafan, akwai shugaba wato Shemaiya, da 'yan'uwansa mutum 200.
\v 9 Daga zuriyar Hebron akwai shugaba wato Eliyel, da 'yan'uwansa mutum tamanin.
\v 10 Daga zuriyar Yuziyel akwai shugaba wato Amminadab da 'yan'uwansa mutum 112.
\s5
\v 11 Dauda ya kira Zadok da Abiyata firistoci da Lebiyawa wato su, Yuriyel da Asayiya da Yowel da Shemaiya da Eliyel da Amminadab.
\v 12 Ya ce da su, "Ku ne shugabannin Lebiyawa. Ku tsarkake kanku, ku da 'yan'uwanku domin ku kawo akwatin Yahweh, Allah na Isra'ila a wurin da na shirya domin sa.
\s5
\v 13 Ba ku ne ku ka ɗauke shi da farko ba. Shi ya sa Ubangiji Yahweh ya yi fushi da mu domin ba mu bi farillansa ba."
\v 14 Sai firistoci da Lebiyawa suka tsarkake kansu domin su iya ɗauko akwatin Yahweh, Allah na Isra'ila.
\v 15 Haka Lebiyawa suka ɗauko akwatin Yahweh, Allah na Isra'ila, a bisa kafaɗunsu da sandunan, kamar yadda Musa ya umurta - suna bin ka'idojin da aka shimfiɗa a maganar Yahweh.
\s5
\v 16 Dauda ya yi magana da shugabannin Lebiyawa su sa 'yan'uwansa su zama mawaƙa, da kayan waƙoƙi, wato su garayu da molaye da kugenni, suna kaɗa su da ƙara sosai suna tada muryoyinsu suna murna.
\v 17 Sai Lebiyawa suka naɗa Heman ɗan Yowel da wani cikin 'yan'uwansa, wato Asaf ɗan Berekiya. Daga cikin 'yan'uwansu, wato daga zuriyar Merari suka naɗa Itam ɗan Kushaiya.
\v 18 Tare da su akwai 'yan'uwansu aji na biyu: wato su Zekariya da Ya'aziyel da Shemiramot da Yehiyel da Unni da Eliyab da Benaiya da Ma'aseiya da Mattitiya da Elifelehu da Miknaiya da Obed Idom da Yehiyel masu tsaron ƙofa.
\s5
\v 19 Mawaƙan suka zaɓi Heman da Asaf da Itam su zama masu kaɗa kugenni masu ƙara na tagulla.
\v 20 Zekariya da Aziyel, Shemiramot, Yehiyel, Unni, Eliyab, Ma'sseiya da Benaiya su ne masu kiɗan girayu, da aka shirya wa Alamot.
\v 21 Mattitiya da Elifelehu da Mikneiya, Obed Idom, Yeyiyel da Azaziya suka bi da hanya tare da kiɗin girayu da aka shirya wa Sheminit.
\s5
\v 22 Kenaniya, shugaban Lebiyawa shi ne kuma shugaban mawaƙa saboda shimai koyar da waƙa ne.
\v 23 Berekiya da Elkana su ne masu tsaron akwati.
\v 24 Shebaniya, Yoshafat, Netanel, Amasai, Zekariya, Benaiya da Eliyeza, firistoci, su ne masu busa ƙaho a gaban akwatin Yahweh. Obed Idom da Yehiyel kuma su ne masu tsaron akwatin Yahweh.
\s5
\v 25 Sai Dauda da dattawan Isra'ila da shugabannin dubbai suka tafi don su ɗauko akwatin alƙawarin Yahweh daga gidan Obed Idom da murna.
\v 26 Sa'an nan, Yahweh ya taimaki Lebiyawan da suka ɗauko akwatin alƙawarin Yahweh, suka miƙa hadaya ta bijimai bakwai da raguna bakwai.
\s5
\v 27 Dauda ya sa riga ta linin, haka kuma Lebiyawan da suka ɗauki akwatin da mawaƙa da Kenaniya shugaban mawaƙan. Dauda kuma yana saye da falmara ta linin.
\v 28 Haka dukkan Isra'ila suka kawo akwatin alƙawarin Yahweh da shewa ta farinciki, da ƙarar ƙahonni da kugenni da girayu da molaye.
\s5
\v 29 Amma sa'ad da akwatin alƙawarin Yahweh ya shigo birnin Dauda, Mika'el ɗiyar Saul ta leƙa ta taga. Sai ta ga sarki Dauda yana rawa yana jin daɗi. Sai ta rena shi a cikin zuciyarta.
\s5
\c 16
\cl Sura 16
\p
\v 1 Su kawo akwatin Yahweh suka sa shi a tsakiyar rumfar da Dauda ya kafa domin sa. Sa'an nan suka yi baye-baye na ƙonawa da baye-baye na zumunta a gaban Yahweh.
\v 2 Sa'ad da Dauda ya gama yin hadayu na ƙonawa da baye - baye na zumunta, ya sa wa mutanen albarka a cikin sunan Yahweh.
\v 3 Ya ba kowanne mutum namiji da mace dunƙulen gurasa da yankan nama da curin kauɗar inabi.
\s5
\v 4 Dauda ya sa waɗansu cikin Lebiyawa su yi hidima a gaban akwatin Yahweh, su yi farinciki da godiya su yi yabo ga Yahweh, Allah na Isra'ila.
\v 5 Waɗannan Lebiyawa su ne Asaf, shi ne shugabansu da Zekariya, Yaaziyel, Shemiramot, Yehiyel, Mattitiya, Eliyab, Benaiya, Obed Idom da Yeyiyel. Waɗanna su ne za su kiɗa girayu da molaye. Asaf shi ne zai kiɗa kugenni da ƙara sosai.
\v 6 Benaiya da Yahaziyel firistoci su ne za su yi ta busa ƙahonni, a gaban akwatin alƙawari na Allah.
\s5
\v 7 A wannan rana Dauda ya fara sa Asaf da 'yan'uwansa su rera wannan waƙa ta godiya ga Yahweh.
\v 8 Ku yi godiya ga Yahweh, ku kira bisa sunansa, ku sanar da ayyukansa a cikin al'ummai.
\v 9 Ku rera gare shi, ku rera yabbai gare shi, ku faɗi dukkan ayyukansa na mamaki.
\s5
\v 10 Ku yi fahariya cikin sunansa mai tsarki; bari zuciyar waɗanda suke neman Yahweh ta yi murna.
\v 11 Ku nemi Yahweh da ƙarfinsa; ku nemi kasancewarsa a kullun.
\s5
\v 12 Ku tuna aiyukan ban mamakin da ya yi, da al'ajibansa da dokokin bakinsa,
\v 13 ku zuriyar Isra'ila bayinsa da ku mutanen Yakubu, zaɓaɓɓunsa.
\v 14 Shi ne Yahweh, Allahnmu, dokokinsa suna cikin dukkan duniya.
\s5
\v 15 Ku tsare alƙawarinsa a zukatanku har abada da maganar da ya umurta ga dubun tsararraki.
\v 16 Yakan tuna alƙawarin da ya yi da Ibrahim da wa'adin da ya yi wa Ishaku.
\v 17 Wannan shi ne ya tabbatar wa Yakubu ya zama ka'ida, ga Isra'ila kuma alƙawari na har abada.
\v 18 Ya ce, "Zan ba ku ƙasar Kan'ana a matsayin rabonku na gădo."
\s5
\v 19 Lokacin da ba su da yawa, 'yan ƙalilan, kuma baƙi a cikin ƙasar.
\v 20 Suka yi yawo daga wannan al'umma zuwa waccan, daga wannan mulki zuwa wani.
\v 21 Bai yarda wani ya tsanance su ba; ya ma hori sarakuna saboda su.
\v 22 Ya ce, "Kada ku taɓa shafaffuna, kada ku cuci annabawana."
\s5
\v 23 Ku rera ga Yahweh, ku duniya dukka, ku yi shelar cetonsa kowacce rana.
\v 24 Ku shaida ɗaukakarsa a cikin al'ummai, ayyukansa na mamaki a cikin dukkan al'immai.
\s5
\v 25 Gama Yahweh mai girma ne, a yabe shi ƙwarai, a ji tsoron sa fiye da dukkan alloli.
\v 26 Gama dukkan alloli na al'ummai gumaka ne, Amma Yahweh, shi ne ya hallicci sammai.
\v 27 Daraja da martaba na tare da shi. Iko da farinciki na wurinsa.
\s5
\v 28 Ku bayar ga Yahweh, ku kabilun duniya, ku bayar da daraja da iko ga Yahweh!
\v 29 Ku ba Yahweh darajar da ta dace da sunansa. Ku kawo masa baiko ku zo gabansa. Ku durƙusa ga Yahweh a cikin martabarsa mai tsarki.
\s5
\v 30 Ku yi rawar jiki a gabansa ku duniya dukka. Duniya ta kahu, ba za ta iya girgiza ba.
\v 31 Bari sammai su yi murna, bari duniya ta yi farinciki, a cikin al'ummai bari su ce, "Yahweh ne ya ke mulki."
\s5
\v 32 Bari teku ya yi ruri, abin da ya ke cika shi kuma ya yi sowa ta farin ciki. Bari filaye su yi farinciki tare da dukkan abin da ke cikin su.
\v 33 Bari itatuwan da ke cikin jeji su yi sowa ta farinciki a gaban Yahweh, gama yana zuwa domin ya hukunta duniya.
\s5
\v 34 A yi godiya ga Yahweh, gama nagari ne shi, alƙawarinsa na jinƙai ya tabbata har abada.
\v 35 Sai ku ce, "Ka cece mu, ya Allah na cetonmu. Ka tattara mu, ka kuɓutar da mu daga sauran al'ummai, domin mu ba da godiya ga sunanka mai tsarki da ɗaukaka cikin yabonka."
\s5
\v 36 A yi yabo ga Yahweh, Allah na Isra'ila har abada abadin. Dukkan mutane suka ce, "Amin" yabo ga Yahweh.
\s5
\v 37 Sai Dauda ya bar Asaf da 'yan'uwansa a gaban akwatin alƙawari na Yahweh, su yi ta yin hidima a gaban akwatin, dai-dai da buƙatar kowacce rana.
\v 38 Obed Idom haɗe da 'yan'uwan nan sittin da takwas. Obed Idom ɗan Yedutun tare da Hosah su ne masu tsaron ƙofa.
\v 39 Zadok da abokan aikinsa firistoci kuma suka yi hidima a rumfar Yahweh a can tudun Gibiyon.
\s5
\v 40 Su riƙa miƙa baye-baye na ƙonawa a kan bagadi babu fasawa safe da yamma, bisa ga abin da ke rubuce a cikin shari'ar Yahweh, wadda ya ba Isra'ila umarni.
\v 41 Heman da Yedutun su na tare da su da kuma waɗanda a ka kira sunayensu a ka zaɓe su, su ba da godiya ga Yahweh saboda alƙawarinsa da amincinsa sun tabbata har abada.
\s5
\v 42 Heman da Yedutun su ne za su lura da waɗanda za su busa ƙahonni da kugenni da sauran kayan kiɗin da a ke amfani da su lokacin da a ke rera waƙoƙi na saduda. 'ya'yan Yedutun su na tsaron ƙofa.
\v 43 Daga nan dukkan jama'a su ka koma gidajensu, Dauda kuma ya koma gida domin ya sa wa mutanensa albarka.
\s5
\c 17
\cl Sura 17
\p
\v 1 Ya zama bayan da sarki ya kimtsa a gidansa, sai ya ce da annanbi Natan, "Duba ni ina zaune a cikin gidan sida, amma akwatin alƙawarin Yahweh yana zaune a rumfa."
\v 2 Natan yace da Dauda, "Ka yi abin da ya ke a zuciyarka, gama Yahweh yana tara da kai."
\s5
\v 3 Amma a wannan daren maganar Yahweh ta zo wurin Natan, cewa,
\v 4 "Je ka, ka gaya wa Dauda bawana, 'ga abin da Yahweh ya ce: 'Kai ba za ka gina mani gidan da zan zauna ba.
\v 5 Gama ba a gida ni ke zama ba tun daga ran da na kawo Isra'ila har zuwa yau. Sai dai a rumfa na ke zama da rumfar sujada a wurare dabam-daban.
\v 6 A cikin dukkan wuraren da na zaga cikin Isra'ila, na taɓa yi wa wani cikin shugabannin da na sa, cewa, "Me ya sa ba ka gina mani gida na sida ba?""'
\s5
\v 7 To yanzu, ka gaya wa bawana Dauda, 'Ga abin da Yahweh mai Runduna ya ce: Na ɗauko ka daga wurin kiwo, daga bin tumaki, domin ka yi mulkin jama'ata Isra'ila.
\v 8 Ina tare da kai dukkan inda ka tafi, na kuma datse dukkan maƙiyanka daga gabanka, kuma zan sa ka yi suna, kamar sunan waɗanda suke manya a duniya.
\s5
\v 9 Zan zaɓi wuri domin jama'ata Isra'ila, domin su zauna a wuri na kansu, don kada su ƙara samun tashin hankali. Mutane masu mugunta ba za su ƙara musguna masu yadda suka yi a dã ba,
\v 10 kamar yadda su ka yi sa'ad da na umurci alƙalai su shugabanci jama'ata Isra'ila. Zan ladabtar da dukkan maƙiyanka. Har yanzu, ina gaya ma ka, Ni Yahweh, zan gina maka gida.
\s5
\v 11 Za ya zama idan kwankinka suka cika da za ka tafi wurin ubanninka, zan tada zuriyarka a bayanka, wani daga cikin zuyarka, zan kafa masarautarsa.
\v 12 Shi zai gina mani gida, kuma zan kafa kursiyinsa har abada.
\s5
\v 13 Zan zama uba a gare shi, shi kuma zai zama ɗana. Ba zan ɗauke alƙawarin amincina daga gare shi ba kamar yadda na ɗauke daga wurin Saul, wanda ya yi mulki kafin ka.
\v 14 Zan ɗora shi bisa gidana cikin masarautata har abada, kursiyinsa kuma zai tabbata har abada.'"
\v 15 Natan ya yi magana da Dauda, ya baiyana masu dukkan waɗannan maganganu, ya kuma gaya masa game da wahayin gabaɗaya.
\s5
\v 16 Sai Dauda ya shiga ciki ya zauna a gaban Yahweh; ya ce, "Wanene ni, Ubangiji Yahweh, menene kuma iyalina, da ka kawo ni a wannan matsayi?
\v 17 Gama wannan ƙaramin abu ne a wurin ka Yahweh. Ka yi magana a kan iyalin bawanka game da babban lokaci mai zuwa, ka kuma nuna wa bawanka tsararraki na gaba, Allah Yahweh.
\v 18 Ni Dauda, me kuma zan ce da kai? Ka ɗaukaka bawanka. Gama ka darajanta bawanka sosai.
\s5
\v 19 Yahweh, saboda bawanka, kuma domin ka cika nufinka, ka yi wannan babban abu na baiyana ayyukanka masu girma.
\v 20 Yahweh, ba wani kamar ka, kuma ba wani Allah ban da kai, kamar yadda mu ke ji koyaushe.
\v 21 Gama ina wata al'umma kamar jama'arka Isra'ila, waɗanda ka kuɓutar daga Masar domin su zama mutanenka, su yi suna domin ka ta wurin aiyukanka masu girma da ban razana? Ka kori al'ummai daga gaban mutanenka, waɗanda ka kuɓutar daga Masar.
\s5
\v 22 Ka sa Isra'ila sun zama mutanenka har abada, kuma kai, Yahweh ka zama Allahnsu.
\v 23 To yanzu, Yahweh, ka bari alƙawarin da ka yi game da bawanka da iyalinsa ya tabbata har abada. Ka yi kamar yadda ka ce.
\v 24 Sunanka ya tabbata har abada ya yi girma domin mutane su ce, 'Yahweh mai Runduna shi ne Allah na Isra'ila,' gidana kuma ni, Dauda ya tabbata a gabanka har abada.
\s5
\v 25 Gama kai, Allahna, ka baiyanawa bawanka za ka gina gida domin sa. Shi ya sa ni bawanka, na sami ƙarfin in yi addu'a zuwa gare ka.
\v 26 To yanzu, Yahweh, kai Allah ne, ka kuma yi wannan kyakkyawan alƙawari ga bawanka:
\v 27 Gama ya gamshe ka, ka albarkaci gidan bawanka ya kasance a gabanka har abada. Kai Yahweh, kai ne ka albarkace shi, kuma zai zama mai albarka har abada."
\s5
\c 18
\cl Sura 18
\p
\v 1 Bayan wannan sai Dauda ya kai wa Filistiyawa hari kuma ya yi nasara a kan su. Ya ƙwace Gat da ƙauyukanta daga ƙarƙashin mulkin Filistiyawa.
\v 2 Daga nan ya yi nasara da Mowab, Mowabawa suka zama bayin Dauda suka biya haraji gare shi.
\s5
\v 3 Sa'an nan Dauda ya yi nasara da Hadadezer sarkin Zoba a Hamat, sa'ad da Hadadezer ya ke tafiya domin ya kafa mulkinsa a Kogin Yuferatis.
\v 4 Dauda ya ƙwace masa karusai dubu da mahaya dawaki dubu bakwai da sojojin ƙasa dubu ashirin. Dauda ya yaiyanke jijiyoyin gwuiwoyin dukkan dawakan da ke jan karusai, amma ya rage waɗanda za su ja karusai ɗari.
\s5
\v 5 Sa'ad da Aramiyawan Damaskus suka zo domin su taimaki Hadadezar sarkin Zoba, Dauda ya kashe mutanen Aramiyawa dubu ashirin da biyu.
\v 6 Sai Dauda ya kafa zangon sojoji a Aram ta Damaskus. Aramiyawa suka zama bayinsa suka kawo masa gaisuwa. Dukkan inda Dauda ya je, Yahweh yana ba shi nasara.
\s5
\v 7 Dauda ya ɗauko garkuwowin zinari waɗanda bayin Hadadezar ke ɗauke da su ya kawo su Yerusalem.
\v 8 Dauda ya ɗauko tagulla da yawa daga Tibhat da Kun biranen Hadadezar. Da wannan tagullar ne Suleman ya yi "Teku" na tagulla da ginshiƙai da sauran kayan aiki na tagulla.
\s5
\v 9 Sa'ad da Tou sarkin Hamat ya ji labarin Dauda ya yi nasara da dukkan sojojin Hadadeza sarkin Zoba,
\v 10 Sai Tou ya aika ɗansa Hadoram ya je ya gaida sarki Dauda ya sa masa albarka, saboda Dauda ya yi yaƙi da Hadadeza kuma ya yi nasara da shi, saboda Tou ya yi yaƙi da Hadadeza. Kuma Tou ya aika Dauda abubuwa daban-daban na zinariya da azurfa da tagulla.
\v 11 Sarki Dauda ya keɓe waɗannan kaya ga Yahweh tare da dukkan azurfa da zinariyar da ya samo daga dukkan al'ummai: wato Idom, Mowab, da mutanen Ammon da Filistiyawa da Amelikawa.
\s5
\v 12 Abishai ɗan Zeruyiya ya kashe Idomawa dubu goma sha takwas a Kwarin Gishiri.
\v 13 Ya kafa zangon sojoji a Idom, dukkan Idomawa suka zama bayin Dauda. Yahweh ya ba Dauda nasara a dukkan inda ya je.
\s5
\v 14 Dauda ya yi mulkin dukkan Isra'ila, kuma ya yi gaskiya da adalci ga dukkan mutane.
\v 15 Yowab ɗan Zeruyiya shi ne shugaban sojoji, Yehoshafat ɗan Ahilud kuma shi ne marubuci.
\v 16 Zadok ɗan Ahitub da Ahimelek ɗan Abiyata su ne firistoci, Shabsha ne marubuci.
\v 17 Benaiya ɗan Yehoiada shi ne shugaban Keretawa da Feletiyawa, 'ya'yan Dauda kuma su ne manyan masu ba da shawara.
\s5
\c 19
\cl Sura 19
\p
\v 1 Daga baya sai Nahash, sarkin mutanen Amon, ya mutu, ɗansa ya gaje shi.
\v 2 Dauda yace, "Zan yi mutunci ga Hanum ɗan Nahash, saboda mahaifinsa ya nuna mutunci gare ni." Sai Dauda ya aika manzanni su yi masa gaisuwa game da mahaifinsa. Bayin Dauda suka shiga ƙasar Ammoniyawa suna je wurin Hanum domin su yi masa gaisuwa.
\v 3 Amma sarakunan Ammoriyawa suka ce da Hanum, "Ka na tsammani Dauda girmama mahaifinka ya ke yi da ya aiko mutane su yi maka gaisuwa? Ba leƙen asiri ya kawo su domin su duba ƙasar nan da nufin su kaɓantar da ita ba?"
\s5
\v 4 Sai Hanun ya kama bayin Dauda ya yi masu aski, ya yayyanke rigunansu har zuwa kwankwaso sa'an nan ya sallame su.
\v 5 Sa'ad da suka yi wa Dauda bayani ya aika a ka tarbe su, saboda sun kunyata ƙwarai. Sarki yace da su, "Ku tsaya a Yeriko sai gemunanku sun fito, sa'an nan ku dawo."
\s5
\v 6 Da Ammoniyawa suka ga sun maida kansu abin ƙyama ga Dauda, Hanun da Ammoniyawa suka aika da dubban awon azurfa domin su gaiyato karusan Arameyawa da mahaya dawaki daga Nahariyam da Ma'aka da Zoba.
\v 7 Su ka gaiyato karusai dubu talatin da biyu tare da sarkin Ma'aka da mutanensa, waɗanda suka zo suka yi zango kusa da Medeba. Ammoniyawa suka tattaro daga biranensu, suka fito domin a yi yaƙi.
\s5
\v 8 Da Dauda ya ji haka, sai ya aiki Yowab tare da dukkan sojojinsa su je su same su.
\v 9 Mutanen Ammon su ka fito suka ja layi a ƙofar birni domin yaƙi, su kuma sarakunan da suka zo suka zauna cikin fili su kaɗai.
\s5
\v 10 Lokacin da Yowab ya ga layin yaƙi na fuskantar sa gaba da baya, daga cikin mutanen Isra'ila ya zaɓi waɗansu gwanayen yaƙi ya shirya su, domin su kara da Arameyawa.
\v 11 Sauran sojojin kuma ya ba da su ga Abishai ɗan'uwansa, domin ya sa su kara da sojojin Ammon.
\s5
\v 12 Yowab yace, "Idan Arameyawa suka fi ƙarfi na, to kai Abishai, sai ka kuɓutar da ni. Amma idan sojojin Ammoniyawa suka fi ƙarfin ka to, ni zan zo in kuɓutar da kai.
\v 13 Ka ƙarfafa, bari mu yi ƙarfin hali saboda mutanenmu kuma saboda biranen Allahnmu, gama Yahweh zai yi abin da ya gamshe shi."
\s5
\v 14 Sai Yowab da sojojinsa suka nausa domin su yi yaƙi da sojojin Arameyawa, waɗanda aka tilasta wa su gudu a gaban sojojin Isra'ila.
\v 15 Sa'ad da sojojin Ammon suka ga Arameyawa sun gudu, suma sai suka gudu daga wurin Abishai ɗan'uwan Yowab suka koma cikin birni. Daga nan Yowab ya koma daga wurin mutanen Ammon ya kuma koma Yerusalem.
\s5
\v 16 Lokacin da Arameyawa suka ga Isra'ilawa sun yi nasara a kansu, sai suka nemi taimako daga ƙetaren Kogin Yuferatis, tare da Shofak shugaban sojojin Hadadeza.
\v 17 Sa'ad da Dauda ya ji haka, sai ya tattara dukkan Isra'ila, suka haye Yodan, suka je wurin su. Ya shirya sojoji domin su yi yaƙi da Arameyawa, suka kuwa yi faɗa da shi.
\s5
\v 18 Arameyawa suka gudu daga gaban Isra'ila, Dauda kuwa ya kashe sojojin karusan Arameyawa dubu bakwai da sojojin ƙasa dubu arba'in. Ya kuma kashe Shofak shugaban sojojin.
\v 19 Da dukkan sarakuna, wato bayin Hadadeza suka ga Isra'ila sun ci nasara a kan su, suka nemi salama da Dauda suka bauta masa. Sai ya zama mutanen Aram ba su ƙara marmarin su taimaka wa Amoniyawa ba.
\s5
\c 20
\cl Sura 20
\p
\v 1 Da lokaci ya yi sa'ad da sarakuna su kan tafi yaƙi, sai Yowab ya jagoranci sojoji suka je suka ragargaza ƙasar Amoniyawa. Ya ja daga a Rabba. Dauda kuma na Yerusalem. Yowab ya kai wa Rabba hari, ya yi nasara a kanta.
\s5
\v 2 Dauda ya ɗauke rawanin sarkinsu daga kansa, sai ya tarar ya kai nauyin awo ɗaya na zinariya, kuma da duwatsu masu daraja a cikin sa. A ka ɗora rawanin a kan Dauda, kuma ya kawo ganima mai yawa daga birnin.
\v 3 Ya fito da mutanen daga cikin birni ya tilasa su yi aiki da zartuna da ƙarafa masu tsini na aiki da gatura. Dauda ya sa dukkan mutanen da ke cikin biranen Ammon su yi wannan aikin. Daga nan Dauda da dukkan sojojin suka dawo Yerusalem.
\s5
\v 4 Bayan wannan sai ya zama yaƙi ya ɓarke a Gezer da Filistiyawa. Sibbekai Bahushate ya kashe Siffai, wani daga cikin kabilar Refiyam, daga nan sai a ka ladabtar da Filistiyawa.
\v 5 Sai ya zama a wani yaƙi kuma da Filistiyawa a Gob, Elhanan ɗan Ya'ir mutumin Betlehem ya kashe Lahmi ɗan'uwan Goliya mutumin Gat, wanda makamin mãshinsa ya yi kamar turken masaƙa.
\s5
\v 6 A wani yaƙin kuma a Gat, a ka sami wani mutum mai tsawo ƙwarai, wanda ya ke da yatsu shida a kowanne hannunsa da kuma yatsu shida a kowacce ƙafarsa. shi ma daga Refiyam ya ke.
\v 7 Da ya yi wa sojojin Isra'ila ba'a, Yehonadab ɗan Shemiya ɗan'uwan Dauda ya kashe shi.
\v 8 Waɗannan zuriyar Refiyam na Gat ne, suka kashe su da hannuwan Dauda da sojojinsa.
\s5
\c 21
\cl Sura 21
\p
\v 1 Wani magafcin Isra'ila ya taso ya iza Dauda ya ƙidaya mutanen Isra'ila.
\v 2 Sai Dauda yace da Yowab da manyan sojoji, "Ku je ku ƙidaya mutanen Isra'ila tun daga Biyasheba har zuwa Dan, ku kawo mani rahoto, domin in san yawansu."
\v 3 Sai Yowab ya ce, "Dama Yahweh ya sa sojojinsa su fi haka yawa sau ɗari. Amma shugabana sarki, dukkan su ba bauta maka su ke yi ba? Me ya sa shugabana ya ke so a yi haka? Yaya za a kawo laifi a Isra'ila?"
\s5
\v 4 Amma maganar sarki ta rinjayi Yowab. To, sai Yowab ya fita ya zagaya dukkan Isra'ila. Daga nan ya dawo Yerusalem.
\v 5 Yowab ya kawo wa Dauda rahoton yawan sojoji. A Isra'ila masu zarar takobi su ne 1,100,000. A Yahuda kaɗai akwai sojoji 470,000.
\s5
\v 6 Amma ba a ƙidaya Benyamin da Lebi tare da su ba, saboda Yowab bai ji daɗin maganar da sarki ya yi ba.
\v 7 Yahweh bai ji daɗin wannan aikin ba, saboda haka sai ya buga Isra'ila.
\v 8 Dauda ya ce da Yahweh, "Na yi zunubi mai girma da na yi haka. Yanzu, ka ɗauke zunubin bawanka gama na yi wauta ƙwarai."
\s5
\v 9 Yahweh yace da Gad, annabin Dauda,
\v 10 "Je ka ka ce da Dauda, 'Ga abin da Yahweh yace, ina ba ka zaɓi guda uku, sai ka zaɓi ɗaya daga cikin su."
\s5
\v 11 Sai Gad ya je wurin Dauda ya ce da shi, "Ga abin da Yahweh ya ce, 'Ka zaɓi ɗaya cikin waɗannan:
\v 12 yunwa ta shekaru uku ko wata uku na ƙanƙanci a hannun abokan gãbarka ko kuwa Yahweh ya bi ka da takobinsa har kwana uku, wato annoba ta afko cikin ƙasar, mala'ikan Yahweh ya bi ko'ina cikin ƙasar Isra'ila yana ta hallaka mutane.' To yanzu, sai ka yi tunani ka ba ni amsar da zan kai wa wanda ya aiko ni."
\s5
\v 13 Sai Dauda yace da Gad, "Ina cikin babbar damuwa! Gara in faɗa cikin hannun Yahweh da in faɗa cikin hannun mutum, gama jinƙansa yana da yawa ƙwarai."
\v 14 Sai Yahweh ya aiko da annoba a ƙasar Isra'ila, har mutum dubu saba'in suka mutu.
\v 15 Sa'an nan Yahweh ya aiko mala'ika ya hallaka Yerusalem. Yana kusa da ya hallaka ta, sai Yahweh ya canza niyyarsa. Ya ce da mala'ikan mai hallakarwa, "Ya isa! Ka mayar da hannunka."A wannan lokacin, mala'ikan Yahweh yana tsaye masussukar Ornan Bayebushe.
\s5
\v 16 Dauda ya tada ido, ya ga mala'kan Yahweh yana tsaye tsakanin sama da ƙasa, da takobi a zare cikin hannunsa ya ɗaga shi a kan Yerusalem. Sai Dauda ya ce da dattawa, ku sa tufafin makoki, ku kwanta da fuskokinku a ƙasa.
\v 17 Dauda ya ce da Yahweh, "Ba ni ne na ba da umarnin a ƙidaya sojoji ba? Ni ne na yi wannan aikin mugunta, amma waɗannan tumaki, me suka yi? Yahweh Allahna! Ka sa hannunka ka buga ni, ni da iyalina, amma kada ka bari annobar ta zauna a kan mutanenka."
\s5
\v 18 Sai mala'ikan Yahweh ya umurci Gad ya ce da Dauda, Dauda ya je ya ginawa Yahweh bagadi a masussukar Ornan Bayebushe.
\v 19 Sai Dauda ya tafi ya yi kamar yadda Gad ya dokace shi a cikin sunan Yahweh.
\v 20 Lokacin da Ornan ke sussukar alkama, sai ya juya ya ga mala'ikan. Sai shi da 'ya'yansa su huɗu, suka ɓoye kansu.
\s5
\v 21 Lokacin da Dauda ya zo wurin Ornan, sai Ornan ya duba ya ga Dauda. Sai ya bar wurin sussukar ya faɗi da fuskarsa a ƙasa a gaban Dauda.
\v 22 Sa'an nan Dauda ya ce da Onan, "Ka sayar mani da wannan masussuka domin in gina wa Yahweh bagadi. Zan biya gaba ɗaya domin a cire annobar daga cikin jama'a."
\s5
\v 23 Ornan ya ce da Dauda, "Ka ɗauke ta kamar taka ce, ya shugabana sarki. Ka yi abin da ka ga dama da ita. Duba, zan ba ka bijimaina domin hadaya ta ƙonawa, sandunan fyaɗi kuma ka yi makamashi da su, alkama kuma domin hadaya ta tsaba, zan ba ka su dukka."
\v 24 Sarki Dauda yace da Ornan, "A'a gara dai in saya in biya. Ba zan ɗauki kayanka in yi hadaya ta ƙonawa ga Yahweh ba, ba tare da ya shafe ni da komi ba."
\s5
\v 25 Sai Dauda ya sayi wurin a bakin zinariya awo ɗari shida.
\v 26 Sai Dauda ya gina wa Yahweh bagadi a wurin, ya miƙa baye-baye na ƙonawa da baye-baye na zumunta. Ya yi kira ga Yahweh, ya kuwa amsa masa da wuta daga sama a kan baye-baye na ƙonawar.
\v 27 Sa'an nan Yahweh ya umurci mala'ikan, mala'ikan kuma ya mayar da takobinsa cikin kubenta.
\s5
\v 28 Da Dauda ya ga Yahweh ya amsa masa a masussukar Ornan Bayebushe, sai ya yi hadayar a wurin nan take.
\v 29 A wannan lokaci wurin taruwa na Yahweh wanda Musa ya yi a cikin Jeji da bagadi domin baye-baye na ƙonawa suna can kan tudun Gibiyon.
\v 30 Duk da haka, Dauda ba zai iya zuwa can domin ya nemi nufin Yahweh ba, saboda yana jin tsoron takobin mala'kan Yahweh.
\s5
\c 22
\cl Sura 22
\p
\v 1 Sai Dauda yace, "A nan gidan Yahweh Allah zai kasance, tare da bagadin ƙona baye-baye na Isra'ila."
\v 2 Sai Dauda ya umurci bayinsa su tattaro baƙin da ke zaune a ƙasar Isra'ila. Ya sa su zama masu sassaƙo duwatsu, su sassaƙo tubulan duwatsu waɗanda za a gina gidan Yahweh da su.
\s5
\v 3 Dauda kuma ya ba da ƙarafa masu tarin yawa domin a yi ƙusoshi saboda ƙofofi da ƙyamarensu da tagulla. Ya kuma ba da tagulla mai yawan da ba za a iya aunawa ba,
\v 4 da itacen sida fiye da yadda za a iya ƙirgawa. (Sidoniyawa da mutanen Taya suka kawo wa Dauda gumaguman sida da yawa domin ya ƙidaya.)
\v 5 Dauda ya ce ɗana Suleman yaro ne, bai ƙware ba tukuna, kuma gidan da za a gina wa Yahweh dole ne ya zama mai daraja sosai, domin ya zama da daraja ya yi suna a dukkan ƙasashe. Saboda haka zan yi shiri domin gininsa." Saboda haka, Dauda ya yi gagarimin shiri kafin mutuwarsa.
\s5
\v 6 Sai ya kira Suleman ɗansa ya umurce shi ya gina gida saboda Yahweh, Allah na Isra'ila.
\v 7 Dauda yace da Suleman, "Ɗana, na yi niyya ni da kaina in gina gida saboda sunan Yahweh, Allahna.
\v 8 Amma Yahweh ya zo wuri na ya ce, 'Ka yi yaƙe-yaƙe da yawa ka zubar da jini. Ba za ka gina gida domin sunana ba, domin ka zubar da jini da yawa bisa ƙasa a idanuna.
\s5
\v 9 Duk da haka, za ka sami ɗa wanda zai zama mutum mai salama. Zan ba shi hutawa daga dukkan maƙiyansa a kowanne sashi. Sunansa zai zama Suleman, kuma zan ba da salama da kwanciyar rai ga Isra'ila a kwanakinsa.
\v 10 Shi ne zai gina mani gida, zai zama ɗa a gare ni, ni kuma zan zama mahaifinsa. Zan tabbatar da kursiyin mulkinsa bisa Isra'ila har abada.'
\s5
\v 11 To yanzu, ɗana, Yahweh ya kasance tare da kai ya ba ka nasara. Za ka ginawa Yahweh Allahnka gida kamar yadda ya ce.
\v 12 Bari Yahweh ya ba ka fahimi da hangen gaba, domin ka yi biyayya da dokar Yahweh Allahnka, sa'ad da ya ɗora ka bisa shugabancin Isra'ila.
\v 13 Za ka yi nasara idan ka lura ka yi biyayya da farillai da dokokin da Yahweh ya ba Musa game da Isra'ila. Ka ƙarfafa, ka yi ƙarfin zuciya, kada ka karaya.
\s5
\v 14 Yanzu ka duba, na yi baban ƙoƙari, na yi tanaji domin gidan Yahweh, zinariya awo 100,000, azurfa awo milyan ɗaya, da tagulla da ƙarafa masu tarin yawa. Na kuma tanaji katako da dutse. Na sani dole sai ka ƙara a kan su.
\s5
\v 15 Kana da ma'aikata da yawa: masu sassaƙar dutse da magina da kafintoci da ƙwararru ga aikin hannu da yawa a kowanne fanni,
\v 16 waɗanda za su iya yin aiki da zinariya da azurfa da tagulla da ƙarafa. Sai ka fara aiki, Yahweh ya kasance tare da kai."
\s5
\v 17 Dauda kuma ya dokaci dukkan dattawan Isra'ila su taimaki ɗansa Suleman, da cewa,
\v 18 "Yahweh Allahku yana tare da ku, kuma ya ba ku salama a kowanne sashi, ya ba da mazauna yankin cikin hannuna. An ladabtar da yankin a gaban Yahweh da mutanensa.
\v 19 Sai ku nemi Yahweh Allah da dukkan zuciyarku da ranku. Sai ku tashi tsaye ku gina wuri mai tsarki na Yahweh Allah. Sa'an nan ne za ku iya kawo akwatin alƙawari na Yahweh tare da abubuwan da ke na Yahweh a cikin gidan da a ka gina domin sunan Yahweh."
\s5
\c 23
\cl Sura 23
\p
\v 1 Sa'ad da Dauda ya tsufa, yana kusa da ƙarshen rayuwarsa, sai ya naɗa ɗansa Suleman ya zama sarkin Isra'ila.
\v 2 Ya tattara dukkan shugabannin Isra'ila, tare da firistoci da Lebiyawa.
\v 3 Lebiyawa kuwa masu shekaru talatin da ma sama da haka, aka kidaya su, sun kai jimillar dubu talatin da takwas.
\s5
\v 4 '"Dubu ashirin da huɗu daga cikin su za su yi hidimar gidan Yahweh, sai kuma dubu shida za su zama ma'aikata da alƙalai.
\v 5 Dubu huɗu kuwa za su zama matsara ƙofofi da dubu huɗu kuma za su zama masu yabon Yahweh da kayayyakin bushe-bushe da kaɗe-kaɗe waɗanda za su yi yabo," Dauda ya ce.
\v 6 Ya raba su kashi kashi bisa ga 'ya'yan Lebi: Geshon, da Kohat da Merari.
\s5
\v 7 Daga zuriyar kabilar Geshon, akwai Ladan da Shimei.
\v 8 Akwai 'ya'ya maza uku na Ladan: su ne Yehiyel shi ne shugaba da Zetam da Yowel.
\v 9 Akwai 'ya'ya uku maza na Shimei, su ne Shelomit da Heziyel da Haran. Waɗannan su ne shugabannin kabilar Ladan.
\s5
\v 10 Akwai 'ya'ya huɗu maza na Shimei, su ne Yahat, Ziza, Yewush da Beriya.
\v 11 Yahat shi ne babba, Ziza shi ne na biyu, amma Yewush da Beriya ba su da 'ya'ya maza da yawa, saboda haka sai aka ɗauke su a matsayin kabila ɗaya tare da yin ayyuka iri ɗaya.
\s5
\v 12 Akwai 'ya'ya maza huɗu na Kohat su ne Amram, Izhar, Hebron da Uzziyel.
\v 13 Waɗannan 'ya'ya maza na Amram su ne Haruna da Musa. Haruna aka zaɓa aka kuma ƙeɓe shi domin ya tsarkake abubuwa mafi tsarki, shi da kabilarsa su riƙa ƙona turare a gaban Yahweh, su yi masa hidima, su riƙa sa albarka da sunansa har abada.
\v 14 Amma Musa mutumin Allah, da 'ya'yansa maza aka ɗauke su a matsayin Lebiyawa.
\s5
\v 15 'Ya'yan Musa maza kuwa su ne Geshon da Eliyeza.
\v 16 A zuriyar Geshon Shebayel ne babban ɗansa.
\v 17 Zuriyar Eliyeza Rehabiya ne ɗansa. Eliyeza ba shi da 'ya'ya maza, amma Rehabiya na da zuriya mai yawa.
\v 18 Ɗan Izhar shi ne Shelomit na shugaba.
\s5
\v 19 Zuriyar Hebron su ne Yeriya, babbansu, Amariya na biyu, Yahaziyel na uku da kuma Yekameyam na huɗu.
\v 20 'Ya'yan Uzziyel maza kuwa su ne Mika ne babban da Ishija na biyu.
\s5
\v 21 'Ya'yan Merari maza su ne Mali da Mushi. 'Ya'yan Mali maza su ne Eliyeza da Kish.
\v 22 Eliyeza kuwa ya rasu ba shi da ko 'ya'ya maza. Yana da 'ya'ya mata ne kaɗai.
\v 23 'Ya'ya maza na Kish ne suka aure su. 'Ya'yan Mushi uku maza su ne Mali, Eder da Yerimot.
\s5
\v 24 Waɗannan su ne zuriyoyin Lebiyawa bisa ga dangoginsu. Su ne shugabannin, da aka lasafta aka jera su bisa ga sunaye, su ne dangogin da suka yi hidimar aiki a cikin gidan Yahweh, daga shekaru ashirin zuwa gaba.
\v 25 Gama Dauda ya ce, '"Yahweh, Allah na Isra'ila, ya ba da hutu ga sauran mutanensa. Ya mai da gidansa a Yerusalem har abada.
\v 26 Lebiyawa ba sauran bukatar ɗauka rumfar sujada tare da kayayyakin yin aiki a cikinta."
\s5
\v 27 Gama bisa ga maganar Dauda ta ƙarshe aka kiɗaya Lebiyawa, daga mai shekaru ashirin zuwa gaba.
\v 28 Aikinsu kuwa shi ne su taimaki zuriyar Haruna gudanar da aiki cikin gidan Yahweh. Su kula da farfajiyoyi da ɗakuna, da tsabtace tsarkakan dukkan abubuwa da su ke na Yahweh, da sauran ayyuka a cikin gidan Allah.
\v 29 Za su kuma ɗauki nauyin kula da wajen gurasar ajiyewa da lallausan gari na baiko na gari, da waina marar gami da soyayyun baye-baye, baye-bayen da ka gauraya da mai, da dukkan ma'aunan nauyi da girma abubuwa.
\s5
\v 30 Suna kuma tsaye a kowacce safiya don su yi godiya da yabon Yahweh. Suna riƙa yin wannan da maraice
\v 31 da duk lokacin baikon ƙonawa suna miƙa wa Yahweh, a ranakun Asabaci da lokacin tsayuwar sabon wata da bikin ƙayyadaddun idodi. Akwai adadin lambar da za a sa bisa ga ka'ida, kullum za su bayyana a gaban Yahweh.
\s5
\v 32 Su ne za su riƙa lura da rumfar taruwa, da wuri mai tsarki, za su kuma taimaki abokansu, zuriyar Haruna hidima cikin gidan Yahweh.
\s5
\c 24
\cl Sura 24
\p
\v 1 Ga yadda aka raba aiki bisa ga zuriyar Haruna su ne: Nadab, Abihu, Eliyeza da kuma Itama.
\v 2 Nadab da Abihu sun riga mahaifinsu mutuwa. Ba su da 'ya'ya, saboda haka Eliyeza da Itama suka shiga aikin firistoci.
\v 3 Dauda, tare da Zadok, zuriyar Eliyeza da Ahimelek, da zuriyar Itama, sun karkasa su bisa ga ayyukansu na matsayin firistoci.
\s5
\v 4 Akwai manyan mutane da yawa a zuriyar Eliyeza fiye da zuriyar Itama, sai suka karkasa zuriyar Eliyeza zuwa kashi goma sha shida. Sun yi wannan bisa ga shugaban dangogi da kuma bisa ga zuriyar Itamar. Waɗannan rabe rabe guda takwas ne adadinsu, bisa ga dangoginsu.
\v 5 Suka karkasa su ta hanyar ƙuri'a, domin akwai ma'aikatan wuri mai tsarki da kuma ma'aikata na Allah daga zuriyar Eliyeza da kuma zuriyar Itama.
\s5
\v 6 Shemaiya ɗan Netanel marubuci, Balabe, ya rubuta sunayensu a gaban sarki da ma'aikata, Zadok firist, da Ahimelek ɗan Abiyata, da shugabannin firistoci da iyalan Lebiyawa. An sami dangi ɗaya ta wurin ƙuri'a daga zuriyar Eliyeza, an sake samun ɗaya daga zuriyar Itama.
\s5
\v 7 Ƙuri'a ta farko ta je ga Yehoyarib, ta biyu ga Yedayiya,
\v 8 ta uku ga Harim, ta huɗu ga Seyorim,
\v 9 ta biyar ga Malkija, ta shida ga Mijamin,
\v 10 ta bakwai ga Hakkoz, ta takwas ga Abija,
\s5
\v 11 Na tara Yeshuwa, ta goma ga Shekaniya,
\v 12 ta goma sha ɗaya ga Eliyashib, ta goma sha biyu ga Yakim,
\v 13 ta goma sha uku ga Huffa, ta goma sha huɗu ga Yeshebeyab,
\v 14 Ta goma sha biyar ga Bilga, ta goma sha shida ga Immer,
\s5
\v 15 Ta goma sha bakwai ga Hezir, ta goma sha takwas ga Haffizzez,
\v 16 ta goma sha tara ga Fetahiya, ta ashirin ga Yehezkel,
\v 17 ta ashirin da ɗaya ga Yakin, ta ashirin da biyu ga Gamul,
\v 18 ta ashirin da uku ga Delaiya, da kuma ta ashirin da huɗu ga Ma'aziya.
\s5
\v 19 Wannan shi ne tsarin aikinsu, idan sun zo hidima cikin gidan Yahweh, bisa ga ka'idar da kakansu Haruna ya ba su, kamar yadda Yahweh, Allah na Isra'ila ya umarce shi.
\s5
\v 20 Waɗannan su ne sauran Lebiyawa, 'ya'ya maza na wajen Amram, shi ne Shubawel; 'Ya'ya maza na Shubawel da Yedaiya.
\v 21 'Ya'ya maza na Rehabiya shi ne Ishija shugaba.
\v 22 Na wajen Izharawa: shi ne Shelomit; na wajen Shelomit: shi ne Yahat.
\s5
\v 23 'Ya'ya maza na wajen Hebron Yeriya ne shugaba, Amariya na biyu, da Yahaziyel na uku, da Yekameyam na huɗu.
\v 24 'Ya'ya maza zuriyar Uzziyel ya haɗa da Mika. Zuriyar Mika ta haɗa da Shamir.
\v 25 Ɗan'uwan Mika shi ne Ishija. 'Ya'ya maza ya haɗa da Zekariya.
\s5
\v 26 'Ya'ya maza na Merari su ne Mali da Mushi. Ɗan Yaaziya shi ne Beno.
\v 27 'Ya'ya maza na Merari su ne Yaaziya: Beno, Shoham, Zakkur da Ibri.
\v 28 'Ya'ya maza na Mali su ne Eliyeza, wanda ba shi da 'ya'ya maza.
\s5
\v 29 'Ya'ya maza na Kish, ɗan Kish, shi ne Yerameyel.
\v 30 'Ya'ya maza na Mushi su ne Mali, Eder da Yerimot. Waɗannan su ne Lebiyawa bisa ga iyalansu.
\v 31 Waɗannan mutane su ne ke shugabatar kowanne gidan uba da kowane ɗan 'yan'uwansu, aka jefa ƙuri'a a gaban sarki Dauda da Zadok da kuma Ahimelek, tare da shugabanni na kowanne iyalan firistoci da Lebiyawa. Suka jefa ƙuri'a kamar yadda zuriyar Haruna suka yi.
\s5
\c 25
\cl Sura 25
\p
\v 1 Dauda da shugabannin Lebiyawa sun zaɓi waɗansu don aiki suna cikin 'ya'yan Asaf maza da na Heman da na Yedutun. Waɗannan mutane za su yi annabci da waɗannan kayayyakin bushe bushe irin su garayu da molaye da kuge. A nan ga adadin mutanen da suka yi wannan aikin:
\v 2 Daga 'ya'yan Asaf maza, su ne Zakkur, Yosef, Netaniya da Asharela, Asaf mahaifinsu ne ya ke bi da su, shi ne kuma wanda ya ke waƙa a ƙarƙashin sarki.
\v 3 Daga 'ya'yan Yedutun maza su ne Gedaliya, Zeri da Yeshayiya, Shimei, Hashabiya da Mattitiya, dukka su shida ne, mahaifinsu Yedutun ne ke kula da su, shi ne kuma mai raira waƙoƙi da garaya don godiya da yabon Yahweh.
\s5
\v 4 Daga 'ya'yan Heman maza kuwa akwai Bukkiya, Mattaniya, Uzziyel, Shebuwel, Yerimot, Hananiya, Hanani, Eliyata, Giddalti, Romamti-Ezer, Yoshbekasha, Malloti, Hotir da kuma Mahaziyot.
\v 5 Dukkan waɗannan 'ya'ya maza ne na Heman annabin sarki. Allah ya ba Heman 'ya'ya maza goma sha huɗu da kuma 'ya'ya mata uku don ya girmama shi.
\s5
\v 6 Dukkan waɗannan suna ƙarƙashin mahaifinsu. Su mawaƙan gidan Yahweh ne, tare da kaɗa kuge da molaye da garayu kamar yadda suke aiki cikin gidan Allah. Asaf da Yedutun da Heman suna ƙarƙashin umarnin sarki.
\v 7 Su da 'yan'uwansu maza horarru ne sun kuma ƙware da mawaƙa ga Yahweh jimillarsu kuwa ita ce 288.
\v 8 Suka jefa ƙuri'u don ayyukansu, dukka suna kama da juna, haka ma ya ke ga yaro da babba da malami da ɗalibi.
\s5
\v 9 Yanzu game da 'ya'yan Asaf maza; ƙuri'a ta farko ta faɗa a kan iyalin Yosef; ta biyu ga iyalin Gedaliya, jimilla mutane goma sha biyu ne;
\v 10 ta uku ta faɗa a kan Zakkur, da 'ya'yansa da danginsa, jimilla mutane goma sha biyu ne,
\v 11 ta hudu ta faɗa ga Izri, 'ya'yansa da danginsa jimilla mutane goma sha biyu ne;
\v 12 ta biyar ta faɗa ga Netaniya, 'ya'yansa maza da danginsa jimilla mutane goma sha biyu ne;
\s5
\v 13 ta shida ta faɗa ga Bukkiya, 'ya'yansa maza da danginsa, jimilla mutane goma sha biyu ne;
\v 14 ta bakwai ta faɗa ga Yesarela, 'ya'yansa maza da danginsa jimilla mutane goma sha biyu na;
\v 15 ta takwas ta faɗa ga Yeshayiya, 'ya'yansa dandinsa, jimilla mutane goma sha biyu ne;
\v 16 ta tara ta faɗa ga Mattaniya, 'ya'yansa maza da danginsa, jimilla mutane goma sha biyu ne;
\s5
\v 17 ta goma ta fada ga Shimei, 'ya'yansa maza da danginsa, jimilla mutane goma sha biyu ne;
\v 18 ta goma sha ɗaya ta faɗa ga Azarel, 'ya'yansa maza da danginsa, jimilla mutane goma sha biyu ne;
\v 19 ta goma sha biyu ta faɗa ga Hashabiya, 'ya'yansa maza da danginsa, jimilla mutane goma sha biyu ne;
\v 20 ta goma sha uku ta faɗa ga Shubayel, 'ya'yansa maza da danginsa, jimilla mutane goma sha biyu ne;
\s5
\v 21 ta goma sha hudu ta faɗa ga Mattitiya, 'ya'yansa maza da danginsa, jimilla mutane goma sha biyu ne;
\v 22 ta goma sha biyar ta faɗa ga Yerimot, 'ya'yansa maza da danginsa, jimilla mutane goma sha biyu ne;
\v 23 ta goma sha shida ta faɗa ga Hananiya, 'ya'yansa maza da danginsa, jimilla mutane goma sha biyu ne;
\v 24 ta goma sha bakwai ta faɗa ga Yoshbekasha, 'ya'yansa maza da danginsa, jimilla mutane goma sha biyu ne;
\s5
\v 25 ta goma sha takwas ta faɗa ga Hanani, 'ya'yansa maza da danginsa, jimilla mutane goma sha biyu ne;
\v 26 ta goma sha tara ta faɗa ga Malloti, 'ya'yansa da danginsa, jimilla mutane goma sha biyu ne;
\v 27 ta ashirin ta faɗa ga Eliyata, 'ya'yansa maza da danginsa, jimilla mutane goma sha biyu ne;
\v 28 ta ashirin da ɗaya ta faɗa ga Hotir, 'ya'yansa maza da danginsa, jimilla mutane goma sha biyu ne;
\s5
\v 29 ta ashirin da biyu ta faɗa ga Giddalti, 'ya'yansa maza da danginsa, jimilla mutane goma sha biyu ne;
\v 30 ta ashirin da uku ta faɗa ga Mahaziyot, 'ya'yansa maza da danginsa, jimilla mutane goma sha biyu ne;
\v 31 sai ta ashirin da huɗu ta faɗa ga Romamti-Ezer, 'ya'yansa maza da danginsa, jimilla mutane goma sha biyu ne.
\s5
\c 26
\cl Sura 26
\p
\v 1 A nan ga yadda aka raba masu tsaron ƙofofi: Daga Koratawa, Meshelemiah ɗan Kore ne, zuriyar Asaf.
\v 2 Meshelemiya yana da 'ya'ya maza: Zekariya ne ɗan fari, Yediyayel ne na biyu, Zebadiya na uku, Yatniyel na huɗu,
\v 3 Elam na biyar, Yehohanan na shida, Eliyehoyenai ne ɗa na bakwai.
\s5
\v 4 Obed Idom da 'ya'ya maza su ne, na fari shi ne Shemaiya, na biyu Yehozabad, na uku Yowa, na huɗu Sakar, na biyar Netanel, shida
\v 5 Ammiyel, na bakwai Issaka, na takwas Fiyuletai, gama Allah ya sa wa Obed Idom albarka.
\v 6 Shemaiya shi ne ɗan farin Obed Idom ya haifi 'ya'ya maza waɗanda suka yi shugabancin iyalansu; su jarumawan mutane ne.
\s5
\v 7 'Ya'yan Shemaiya maza su ne Otni, Refayel, Obed, Elzabad. Danginsa Elihu da Shemakiya suma jaruman mutane ne.
\v 8 Dukkan waɗannan kabilun Obed Idom. Su da 'ya'yansu maza da dangoginsu jarumai ne masu ƙarfi da gwaninta na yin hidima. Akwai mutane sittin da biyu da suke da dangantaka da Obed Idom.
\v 9 Meshelemiya yana da 'ya'ya maza da 'yan'uwa, mutane ne masu ƙarfi da gwaninta, su dukka goma sha takwas ne.
\s5
\v 10 Hosa, yana cikin zuriyar Merari, yana da 'ya'ya maza, Shimri shugaba (ko da ya ke ba shi ne ɗan fari ba, duk da haka maihaifinsa ya maishe shugaba).
\v 11 Hilkiya shi ne na biyu, da Tabaliya na uku da Zekariya na huɗu. Dukkan 'ya'yan Hosa maza da 'yan'uwansa su goma sha uku ne.
\s5
\v 12 Waɗannan su ne rabe rabe na masu tsaron ƙofa, bisa ga shugabanninsu, da ayyuka, kamar iyalansu, da za su yi hidima a gidan Yahweh.
\v 13 Sai suka jefa kuri'a yaro da babba bisa ga iyalansu, don kowacce ƙofa.
\v 14 Sai ƙuri'ar ƙofar gabas, ta faɗo a kan Shelemiya. Suka kuma jefa ƙuri'a don ɗansa Zekariya, mai ba da shawara mai ma'ana, sai ƙuri'arsa ta fito don ƙofar arewa.
\s5
\v 15 An sa Obed Idom ƙofar kudu, an kuma sa 'ya'yansa maza lura da ɗakunan ajiya.
\v 16 Shuffin da Hosa an sa su a ƙofa ta yamma tare da Shalleket, a kan hanyar da ta haura. Aka tabbatar da masu tsaron kowanne iyali.
\s5
\v 17 A gefen gabas akwai Lebiyawa shida, a gefen arewa a rana ta huɗu, a gefen kudu a rana ta huɗu, an kuma sa biyu biyu a ɗakunan ajiya.
\v 18 A ɗakin shari'a da ke yamma akwai masu tsaro huɗu, a hanya guda huɗu, biyu kuma a ɗakin shari'a.
\v 19 Yadda aka raba masu tsaron ƙofofin kenan. Suna cike da zuriyoyin Kora da Merari.
\s5
\v 20 A cikin Lebiyawa, Ahijah ne mai kula da ma'ajin gidan Allah, da ma'ajin abubuwa da ke na Yahweh.
\v 21 Zuriyar Ladan, daga zuriyar Geshon ta wurinsa da waɗanda suke shugabannin iyalan Ladan Bageshone, su ne Yehiyeli,
\v 22 da 'ya'yansa maza Zetam da Yowel ɗan'uwansa, su ne ke kula da ɗakunan ajiyar gidan Yahweh.
\s5
\v 23 Akwai kuma masu tsaro da aka ɗauko daga kabilar Amram, da Izhar da Hebron da kuma Uzziyel.
\v 24 Shubayel ɗan Geshom ɗan Musa, shi ne babban jami'in ɗakunan ajiya.
\v 25 Danginsa daga kabilar Eliyeza su ne ɗansa Rehabiya, Yeshayiya ɗan Rehabiya, Yoram ɗan Yeshabiya, Zikri ɗan Yoram, da kuma Shelomit ɗan Zikri.
\s5
\v 26 Shelomit da 'yan'uwansa ne ke lura da dukkan gidajen ajiya da abubuwan da ke na Yahweh, wanda Dauda sarki, da iyalin shugabanni, da shugabannin sojoji na dubu dubu na ɗari ɗari da kuma shugabannin sojojin da aka keɓe.
\v 27 Su ne kuma aka keɓe don kula da ganimar yaƙe-yaƙe domin kuma gyaran gidan Yahweh.
\v 28 Su ne kuma masu lura da kowane irin abubuwa da aka keɓe ga Yahweh ta wurin annabi Sama'ila, da Saul ɗan Kish da Abner ɗan Ner da Yowab ɗan Zeruyiya. Kowanne abu da aka keɓe ga Yahweh yana ƙarƙashin kulawar Shelomit da 'yan'uwansa.
\s5
\v 29 Zuriyar Izhar da Kenaniya tare da 'ya'yansa maza su ne aka danƙa wa al'amuran sasantawa na Isra'ila. Su ne shugabanni da alƙalai.
\v 30 Zuriyar Hebron da Hashabiya haɗe da 'yan'uwansa, 1700 gwanayen mutane ne, su ne masu lura da ayyukan Yahweh da na sarki. Suna wajen yammacin Yodan.
\s5
\v 31 Daga zuriyar Hebron, Yeriya shi ne shugaban zuriyarsa, bisa ga asalin iyalansu. A shekara ta arba'in ta sarautar Dauda sun bincika, aka tarar akwai ƙarfafan mutane, jarumawa a Yazer ta Giliyad.
\v 32 Yeriya yana da 'yan'uwa har 2,700, waɗanda suke gwanaye shugabannin iyali. Dauda ya maida su masu lura da kabilar Ruben da ta Gad da kuma rabin kabilar Manasse, domin kowane abu da ke na Allah da kuma al'amuran sarki.
\s5
\c 27
\cl Sura 27
\p
\v 1 Wannan shi ne lissafin iyalin shugabannin Isra'ila, shugabannin sojoji na dubu dubu da ɗari ɗari, har da rudunar sojoji waɗanda suke yi wa sarki aiki ta hanyoyi dabam dabam. Kowace runduna za ta yi aiki wata wata har ƙarshen shekara. Kowanne kashi na da mutane dubu ashirin da huɗu.
\v 2 A kowane kashi a wata na farko, shi ne na Yashobeyam ɗan Zabdiyel. A cikin kashinsa akwai mutane dubu ashirin da huɗu.
\v 3 Yana cikin zuriyar Pezer, shi ne kuma mai lura da dukkan shugabannin sojoji a watan farko.
\s5
\v 4 Bisa ga kashi wata na biyu shi ne Dodai, daga kabilar zuriya daga Ahoya. Miklot shi ne na biyu a jerin. A cikin rabonsa akwai mutane dubu ashirin da huɗu.
\v 5 Shugaban ruduna a wata na uku shi ne Benaiya ɗan Yehoiada, firist ne kuma shugaba. A cikin rabonsa akwai mutane dubu ashirin da huɗu.
\v 6 Wannan shi ne Benaiya wanda shi ne shugaba a cikin talatin, da kuma bisa ga talatin. Ammizabad ɗansa mana cikin rabonsa.
\s5
\v 7 Shugaban sojoji a wata na huɗu shi ne ɗan'uwan Asahel Yowab. Ɗansa Zebadiya ya zama shugaba a madadinsa. A cikin rabonsa akwai mutane dubu ashirin da huɗu.
\v 8 Shugaba na watan biyar shi ne Shamhut, a zuriyar Izra. A cikin rabonsa akwai mutane dubu ashirin da huɗu.
\v 9 Shugaba na watan shida shi ne Ira ɗansa Ikesh, daga Tekowa. A cikin rabonsa akwai mutane dubu ashirin da huɗu.
\s5
\v 10 Shugaba na watan bakwai shi ne Helez Bafelone, daga mutanen Ifraim. Rabonsa mutane dubu ashirin da huɗu ne.
\v 11 Shugaba na watan takwas shi ne Sibbekai Bahushate, daga kabilar zuriya daga Zera. Rabonsa mutane dubu ashirin da huɗu ne.
\v 12 Shugaba na watan tara shi ne Abiyeza Ba'anatot, daga kabilar Benyamin. Rabonsa mutane dubu ashirin da huɗu ne.
\s5
\v 13 Shugaba na watan goma shi ne Maharai daga birnin Netofa, daga dangin zuriya daga Zera. Rabonsa mutane dubu ashirin da huɗu ne.
\v 14 Shugaba na watan goma sha ɗaya shi ne Benaiya daga birnin Firaton, daga kabilar Ifraim. Rabonsa mutane dubu ashirin da huɗu ne.
\v 15 Shugaba na watan goma sha biyu shi ne Heldai daga birnin Netofa, daga dangin zuriya daga Otniyel. Rabonsa mutane dubu ashirin da huɗu ne.
\s5
\v 16 Waɗannan su ne shugabannin kabilun Isra'ila: Ga kabilar Ruben, Eliyeza ɗan Zikri shi ne shugaba. Ga kabilar Simiyonn, Shefatiya ɗan Ma'aka shi ne shugaba.
\v 17 Ga kabilar Lebi, Hashabiya ɗan Kemuwel shi ne shugaba, Zadok shi ne jagora na zuriyar Haruna.
\v 18 Ga kabilar Yahuda, Elihu, ɗaya daga cikin 'yan'uwan Dauda, shi ne shugaba. Ga kabilar Issaka, Omri ɗan Mika'el shi ne shugaba.
\s5
\v 19 Ga kabilar Zebulun, Ishamaiya ɗan Obadiya shi ne shugaba. Ga kabilar Naftali, Yerimot ɗan Azriyel shi ne shugaba.
\v 20 Ga kabilar Ifraim, Hosheya ɗan Azaziya shi ne shugaba. Ga rabin kabilar Manasse, Yowel ɗan Fedaiya shi ne shugaba.
\v 21 Ga rabin kabilar Manasse a Gileyad, Iddo ɗan Zekariya shi ne shugaba. Ga kabilar Benyamin, Ya'asiyel ɗan Abner shi ne shugaba.
\v 22 Ga kabilar Dan, Azarel ɗan Yeroham shi ne shugaba. Waɗannan su ne shugabannin kabìlun Isra'ila.
\s5
\v 23 Dauda bai ƙidaya waɗanda shekarunsu ba su kai ashirin ba ko kuma yara, gama Yahweh ya yi alƙawarin zai sa mutanen Isra'ila su yi yawa kamar taurarin sammai.
\v 24 Yowab ɗan Zeruya ne ya fara ƙidayar mutanen nan, amma bai gama ba. Sai hukunci mai zafi ya sami Isra'ila saboda wannan. Wannan ƙidayar ba a rubuta ta ba cikin Tarihin Sarki Dauda ba.
\s5
\v 25 Azmabet ɗan Adiyel shi ne mai lura da ma'ajin sarki. Yonatan ɗan Uzziya shi ne mai kula da ɗakin ajiya a filaye da kuma cikin birane, har da ƙauyuka da kagaran hasumiyoyi.
\v 26 Ezri ɗan Kelub shi ne mai lura da gonaki, da waɗanda suke huɗa a ƙasar.
\v 27 Shimei Baramate shi ne mai kula da gonakin inabi da Zabdi Bashifime shi ne mai lura da itatuwan zaitun da inda ake ajiye kwalaben shaye-shaye.
\s5
\v 28 Ga itatuwan zaitun da na ɓaure waɗanda suke a kwari shi ne Ba'al-Hanan daga Geder, kuma ɗakin ajiyar man shi ne Yowash.
\v 29 Bisa ga garken shanu a Sharon shi ne Shitrai, daga Sharon kuma bisa ga garken shanu da ke cikin kwari shi ne Shafat ɗan Adlai.
\s5
\v 30 Bisa ga rakuma shi ne Obil Ba'isma'ile, kuma bisa ga jakuna mata shi ne Yedaiya daga Meronot. Bisa ga tumaki shi ne Yaziz Bahagire.
\v 31 Yazia Bahagire shi ne mai lura da garken. Dukkan waɗannan su ne masu lura da dukiyar sarki Dauda.
\s5
\v 32 Yonatan, kawun Dauda, shi ne mai ba da shawara, tun da shi mutum ne mai ganewa shi ne kuma magatakarda. Yehiyel ɗan Hakmoni shi ne mai kula da 'ya'yan sarki.
\v 33 Ahitofel shi ne mai ba sarki shawara, Hushai daga mutanen Arkite su ne masu shawara na jikin sarki.
\v 34 Ahitofel ɗan Benaiya an ba da makaminsa ga Yehoiada ɗan Benaiya ta wurin Abiyata. Yowab shi ne babban shugaban sojojin sarki.
\s5
\c 28
\cl Sura 28
\p
\v 1 Dauda ya tara dukkan shugabannin Isra'ila a Yerusalem: shugabannin kabilu da shugabannin kungiyoyi da ke yi wa sarki hidima a cikin shirin aikinsa, shugabannin dubu dubu da ɗari ɗari da manajoji bisa dukkan dukiya da mallakar sarki da 'ya'yansa da kuma fãdawa da mutane mayaƙa, tare da waɗanda suka zama mafiya fasaha.
\s5
\v 2 Sai sarki Dauda ya mike tsaye ya ce, "Ku saurare ni, 'yan'uwana da jama'ata. Na yi niyya in gina haikalin akwatin alƙawari na Yahweh; wurin zaman zatin Allahnmu, na kuma riga na yi shirin ginin.
\v 3 Amma Allah ya ce da ni, 'Ba za ka gina mani haikali da sunana ba, domin kai mutum ne mayaƙi, ka kuma zubar da jini.'
\s5
\v 4 Duk da haka Yahweh, Allah na Isra'ila, ya zaɓe ni daga dukkan iyalin mahaifina, in zama sarkin Isra'ila har abada. Shi ne ya zaɓi kabilar Yahuda da kuma gidan mahaifina, daga cikin dukkan 'ya'ya maza na mahaifina, shi ne ya zaɓe ni in zama sarkin Isra'ila.
\v 5 Daga 'ya'ya maza da yawa Yahweh ya ba ni, ya zaɓe Suleman, ɗana, ya zauna a kan gãdon sarautar mulkin Yahweh, bisa Isra'ila.
\s5
\v 6 Ya ce da ni, 'Suleman ɗanka ne zai gina mani gida da farfajiyoyina, gama na zaɓe shi ya zama ɗa a gare ni, ni kuwa zan zama uba a gare shi.
\v 7 Zan tabbatar da mulkinsa har abada, idan ya tsaya da gaske ya yi biyayya da dokokina da kuma ka'idodina.'
\s5
\v 8 Saboda haka yanzu, a gaban dukkan Isra'ila, wannan taron Yahweh, da kuma gaban Allahnmu, dukkan ku dole ku kiyaye kuma yi ƙoƙari ku bi dukkan umarnan Yahweh Allahnku. Ku yi wannan don ku mallaki wannan ƙasar mai kyau, ku zauna a cikin ta a matsayin gãdo ga 'ya'yanku a bayanku har abada.
\s5
\v 9 Amma kai, ɗana Suleman, ka yi biyayya da Allah na mahaifinka, ka bauta masa da dukkan zuciyarka da kuma yardar rai. Ka yi wannan gama Yahweh mai binciken dukkan zukata ne, ya kuma san kowanne irin nufi da tunanin kowanne mutum. Idan ka neme shi, zaka same shi, amma idan ka rabu da shi, shi ma zai yi watsi da kai har abada.
\v 10 Ka lura da cewa Yahweh ya zaɓe ka domin ka gina wannan rumfa mai tsarki. Ka yi ƙarfi, ka kama yi aiki."
\s5
\v 11 Sa'an nan Dauda ya ba ɗansa Suleman tsarin ginshiƙan ƙofar haikalin, da gine-ginen haikali da ɗakunan ajiya da benaye da ɗakunan ciki da ɗakunan inda ake gafarta zunubi.
\v 12 Ya ba shi tsarin da ya zãna domin farfajiyoyin gidan Yahweh, da dukkan kewayen ɗakunan, da ɗakunan ajiya na gidan Allah, da ma'ajiyai domin abubuwan da ke na Yahweh.
\s5
\v 13 Ya kuma ba shi ƙa'idodin domin rarraba firistoci da Lebiyawa, da dukkan hidimar da za a yi a gidan Yahweh, domin kowanne aiki na cikin gidan Yahweh.
\v 14 Ya fayyace nauyin santulan zinariya domin kowanne irin aiki, nauyin santulan azurfa domin kowanne irin aiki.
\v 15 Nauyin zinariya domin dukkan kayayyakin zinariya, sun haɗa da kowanne alkuki da fitilunsa da fitilar zinariya, nauyin ma'aunin kowacce fitila da maɗori, nauyin ma'aunin kowacce azurfa domin kowanne maɗorin fitila, bisa ga yadda za'a yi amfani da kowanne maɗorin fitila a cikin sujada.
\s5
\v 16 Ya ba da ma'aunin zinariya da za a yi teburorin gurasar ajiyewa don kowanne teburi, da kuma ma'aunin azurfa don teburorin azurfa.
\v 17 Ya bada ma'aunin zinariya tsantsa wadda za a yi cokula masu yatsu domin nama da daruna da kofuna da kwanoni da da ma'auni na yawan azurfa da za a yi kwanoni da ita.
\s5
\v 18 Ya bada ma'aunin zinariya tsantsa wadda za a yi bagaden ƙona turare da ita, da kuma zinariya da za a yi tsarin kerubobin da za su miƙa fikafikansu su rufe akwatin alƙawarin Yahweh.
\v 19 Dauda ya ce, "Na sa dukkan wannan a rubuce ne kamar yadda Yahweh ya umarce ni, ya kuma ba ni don in fahimci fasalin aikin filla-filla."
\s5
\v 20 Dauda ya ce da ɗansa Suleman, "Ka yi ƙarfi da jaruntaka. Ka yi aikin. Kada ka ji tsoro ko ka karai, gama Yahweh Allah, Allahna, na tare da kai. Ba zai bar ka ba ko ya ƙyale ka har sai ka gama dukkan aikin hidimar haikalin Yahweh.
\v 21 Duba ga, karkasuwar firistoci da Lebiyawa na nan domin yin dukkan hidima a haikalin Allah. Za su kasance tare da kai, tare kuma da dukkan gwanayen mutanen da suka yarda su taimake ka a cikin aikin da yadda za a yi hidimar. Shugabanni da dukkan mutane na shirya su bi umarninka."
\s5
\c 29
\cl Sura 29
\p
\v 1 Sarki Dauda yace da dukkan taron, "Ɗana Suleman, wanda shi kaɗai Allah ya zaɓa, sai dai saurayi ne, kuma ba shi da ƙwarewa, kuma aikin babba ne. Gama haikalin ba na mutum ba ne, amma na Yahweh Allah ne.
\v 2 A halin yanzu dai na riga na yi iyakacin ƙoƙarina, har na tanada waɗannan abubuwa saboda haikalin Allahna. Na ba da zinariya saboda abubuwa na zinariya, azurfa saboda abubuwa na azurfa, tagulla saboda abubuwa na tagulla, ƙarfe saboda abubuwa na ƙarfe, itace kuwa saboda na itace. Na kuma ba da duwatsu da yawa masu daraja, da masu launi iri-iri -da kowaɗanne irin duwatsu masu daraja - da duwatsu a yalwace.
\s5
\v 3 Yanzu, saboda ƙaunar da na ke da ita ta gidan Allahna, shi ya sa na bada zinariyata da azurfata don wannan aiki. Ina ƙara yin wannan dukka don in shirya wannan haikali mai tsarki,
\v 4 na bada zinariya tsantsa talanti dubu uku daga Ofir, azurfa tsantsa talanti dubu bakwai, domin yin ado a bangon ginin.
\v 5 Na bada zinariya saboda abubuwa da abin da za ayi da zinariya, azurfa saboda abubuwan da za a yi na azurfa, da dukkan irin abubuwa da kafintoci za su yi. Wane ne kuma ya ke da niyyar bayarwa domin Yahweh yau, ya kuma ba da kansa gare shi?
\s5
\v 6 Sai aka yi bayarwar yardar rai bisa ga shugabannin iyalan kakanni da shugabannin kabilun Isra'ila da shugabannin dubbai da ɗaruruwa da kuma shugabannin da suke yi wa sarki aiki.
\v 7 Suka bada saboda hidimar gidan Allah talanti dubu biyar da darik dubu goma na zinariya, da talanti dubu goma na azurfa da dubu goma sha takwas na tagulla da kuma talanti 100,000 na ƙarfe.
\s5
\v 8 Waɗanda suke da duwatsu masu daraja sun bada su cikin taskar gidan Yahweh, a ƙarƙashin kulawar Yehiyel, zuriyar Gashon.
\v 9 Mutane suka yi murna domin waɗannan baye-baye na yardar rai, gama sun bayar da zuciya ɗaya ga Yahweh. Sarki Dauda kuma ya yi murna ƙwarai.
\s5
\v 10 Dauda ya albarkaci Yahweh a gaban dukkan taron, ya ce, "Yabo naka ne, Yahweh, Allah na kakanmu Isra'ila, har abada abadin.
\v 11 Naka ne, Yahweh, girma da iko da daraja da nasara da ɗaukaka. Gama dukkan abin da ke cikin sammai da duniya naka ne. Naka ne mulki, Yahweh, kai ne maɗaukaki mai mulki a bisa komai.
\s5
\v 12 Dukkan wadata da ɗaukaka suna zuwa daga gare ka, kai ka ke mulki bisa dukkan mutane. A hannunka iko da ƙarfi su ke. Kai ne ka ke da ƙarfi da iko ka sa mutane su yi girma, ka kuma bada ƙarfi ga kowane mutum.
\v 13 Yanzu, ya Allahnmu, muna gode maka muna kuma yabon sunanka mai daraja.
\s5
\v 14 Amma wãne ni, ko kuma mutanena da za mu iya kawo waɗannan abubuwa da yardar rai? Gama dukkan abubuwan nan sun zo daga gare ka ne, mu kuma muka ba ka abin da ke naka.
\v 15 Gama mu bãƙi ne, matafiya kuma a gabanka, kamar kakanninmu. Kwanakinmu a duniya kamar inuwa ne, ba mu da begen dauwama a duniya.
\s5
\v 16 Yahweh Allahnmu, dukkan wannan dukiya da muka tattara domin mu gina haikali saboda ɗaukakar sunanka mai tsarki - sun zo daga gare ka ne kuma naka ne. Na kuma sani, ya Allahna, ka kan gwada zuciya, kana jin daɗin abin da ke nagari.
\v 17 Amma ni, bisa ga amincewar zuciyata, da yardar rai, na miƙa maka dukkan waɗannan abubuwa, yanzu ina dubawa da murna ganin mutanenka waɗanda suke nan da yardar su suka kawo maka kyautai.
\s5
\v 18 Yahweh, Allah na Ibrahim da Ishaku da Isra'ila-kakanninmu - ka ajiye wannan har abada a cikin tunanin zukatan mutanenka. Ka bi da zukatansu zuwa gare ka.
\v 19 Ka ba ɗana Suleman cikakkiyar zuciyar sha'awar kiyaye umarnanka da alƙawarin ka'idodi da dokokinka, domin ya aikata dukka waɗannan shirye-shirye na gina haikali wanda na riga na yi tanaji dominsa."
\s5
\v 20 Dauda ya ce da dukkan taron, "Yanzu sai ku albarkaci Yahweh, Allahnku." Dukkan taron kuwa suka albarkaci Yahweh, Allah na kakaninsu, suka rusuna da kawunsu suka yi sujada ga Yahweh suka kuma sunkuyar da kansu a gaban sarki.
\v 21 Washegari, sai suka miƙa wa Yahweh hadayu da hadayun ƙonawa gare shi. Sun miƙa bijimai dubu ɗaya, da raguna dubu ɗaya da kuma 'ya'yan tumakai dubu ɗaya, tare da hadayunsu na sha da hadayu masu yawan gaske domin dukkan Isra'ila.
\s5
\v 22 A wannan rana, sun ci, sun sha a gaban Yahweh tare da bayyana murna da yabo. Sai suka sake naɗa Suleman ɗan Dauda, sarki a karo na biyu, suka shafa masa man keɓewa tare da ikon Yahweh ya zama mai mulki. Suka kuma keɓe Zadok don ya zama firist.
\v 23 Sai Suleman ya zauna a kan gadon sarauta na Yahweh maimakon Dauda mahaifinsa. Ya yi wadata, kuma dukkan Isra'ila suka yi biyayya da shi.
\s5
\v 24 Dukkan shugabanni da sojoji da 'ya'yan sarki suka yi alƙawari za su yi wa sarki Suleman biyayya.
\v 25 Yahweh kuwa ya ɗaukaka Suleman ƙwarai da gaske a gaban dukkan Isra'ila, ya ba shi babban iko fiye da wani sarki kafin shi a Isra'ila.
\s5
\v 26 Dauda ɗan Yesse ya yi mulki bisa dukkan Isra'ila.
\v 27 Dauda ya yi mulki a Isra'ila har shekaru arba'in. Ya yi mulki a Hebron shekaru bakwai, sa'an nan ya yi mulki shekaru talatin da uku a Yerusalem.
\v 28 Ya rasu da kyakkyawan tsufa, bayan ya ji daɗin rayuwa mai tsawo, da arziki da daraja. Suleman ɗansa ya gaje shi.
\s5
\v 29 Abubuwan da sarki Dauda ya yi suna rubuce a cikin tarihin annabi Sama'ila, da annabi Natan da annabi Gad.
\v 30 Abubuwan da ke rubuce su ne ayyukansa da mulkinsa, abubuwan da ya kammala da kuma waɗanda suka shafe shi da Isra'ila da dukkan mulkokin sauran ƙasashe.