ha_ulb/67-REV.usfm

839 lines
61 KiB
Plaintext
Raw Normal View History

2021-09-13 13:40:08 +00:00
\id REV
\ide UTF-8
\h Wahayin Yahaya
\toc1 Wahayin Yahaya
\toc2 Wahayin Yahaya
\toc3 rev
\mt Wahayin Yahaya
\s5
\c 1
\p
\v 1 Wannan shine wahayin Yesu Almasihu da Allah ya bashi ya nuna wa bayinsa abinda zai faru ba da dadewa ba. Ya bayyana wannan ta wurin aiko da mala'ikansa ga bawansa Yahaya.
\v 2 Yahaya yayi shaida akan abinda ya gani game da maganar Allah da kuma shaidar da aka bayar game da Yesu Almasihu.
\v 3 Mai albarka ne wanda ke karanta littafin nan da murya mai karfi, da kuma wadanda ke sauraron kalmomin wannan annabci kuma suke biyayya da abinda aka rubuta a ciki, domin kuwa lokaci ya kusato.
\s5
\v 4 Ni Yahaya, zuwa ga ikilisiyoyi bakwai na kasar Asiya: alheri zuwa gare ku da salama daga wanda ke yanzu, wanda ya kuma kasance a da, shi ne kuma mai zuwa nan gaba, kuma daga ruhohin nan bakwai da ke gaban kursiyinsa,
\v 5 kuma daga Yesu Almasihu, wanda ke amintaccen mashaidi, dan fari na tashi daga cikin matattu, kuma mai mulkin sarakunan duniya. Ga wanda ya ke kaunar mu ya kuma kwance mu daga daurin zunubanmu ta wurin jininsa,
\v 6 ya maishe mu masu mulki, firistoci na Allahnsa da Ubansa - daukaka da iko su tabbata gare shi har abada abadin, Amin.
\s5
\v 7 Duba yana zuwa tare da gizagizai, kowane ido zai gan shi, har ma da wadanda suka soke shi. Haka kuma dukkan kabilun duniya za su yi makoki saboda da shi. I, Amin.
\v 8 "Nine na farko da na karshe", in ji Ubangiji Allah, "Wanda yake shine a yanzu, shine wanda ya kasance a da, kuma shi ne mai zuwa nan gaba, Mai iko duka."
\s5
\v 9 Ni, Yahaya- dan'uwan ku da wanda ke tarayya daku cikin shan wahala, da mulki da tsawon jimrewa wadanda ke cikin Yesu - ina tsibirin da ake kira Batmusa saboda maganar Allah da kuma shaida game da Yesu.
\v 10 Ina cikin Ruhu a ranar Ubangiji. Sai naji wata murya mai karfi a baya na kamar ta kaho.
\v 11 Ta ce, "Rubuta abinda ka gani a cikin littafi, ka kuma aika wa ikilisiyoyin nan bakwai - ga Afisus, ga Simirna, ga Birgamas, ga Tayatira, ga Sardisu, ga Filadalfiya, da kuma ga Laudikiya."
\s5
\v 12 Na juya don in ga wanda muryarsa ke magana da ni, da na juya sai na ga fitilu bakwai akan madorin su
\v 13 A tsakiyar fitilun akwai wani mai kama da dan mutum, yana sanye da doguwar tufa har tafin sawunsa, da damara ta zinariya kewaye a kirjinsa.
\s5
\v 14 Kansa da gashinsa fari fat kamar auduga - kamar dusar kankara, kuma idanun sa kamar harshen wuta.
\v 15 Kafaffunsa kamar gogaggiyar tagulla, kamar tagullar da aka tace da wutar makera, muryar sa kuma kamar kugin ambaliyar ruwan teku ne.
\v 16 A hannunsa na dama yana rike da taurari bakwai, daga bakinsa kuma kakkaifan takobi mai kaifi biyu ke fitowa. Fuskarsa tana haskakawa kamar sa'adda rana ke haskakawa kwarai.
\s5
\v 17 Lokacin da na gan shi, na fadi kamar mataccen mutum a kafaffunsa. Ya dora hannunsa na dama a kaina ya ce, "Kada ka ji tsoro. Nine na farko da na karshe,
\v 18 da kuma wanda ke raye. Na mutu, amma duba ina raye har abada! Kuma ina da mabudin mutuwa da na hades.
\s5
\v 19 Domin haka ka rubuta abinda ka gani, abin da ke yanzu, da abin da zai faru bayan wanan.
\v 20 Akan boyayyar ma'ana game da taurari bakwai da ka gani a hannun dama na, da madorin fitilu bakwai na zinariya: Taurarin nan bakwai mala'iku ne na ikilisiyoyi bakwai, kuma madorin fitilun nan bakwai ikilisiyoyi ne bakwai.
\s5
\c 2
\p
\v 1 "Zuwa ga mala'ikan dake ikilisiyar Afisus, ka rubuta: 'Wadannan sune kalmomin wanda ke rike da taurari bakwai a cikin hannun damarsa. wanda yake tafiya a tsakanin zankayen fitilun zinari bakwai,
\v 2 "Na san abubuwan da ka yi, da famar ka, da hakurinka da jimirinka. Na sani ba ka jimrewa miyagun mutane, na sani ka gwada wadanda suka ce da kansu, su manzanni ne, amma ba haka ba, ka tarar da su makaryata.
\s5
\v 3 Na san kana da tsawon jimrewa, kuma ka sha wahala sosai sabili da sunana, kuma baka gaji ba.
\v 4 Amma ga rashin jin dadi na da kai, ka bar kaunar ka ta fari.
\v 5 Domin haka ka tuna daga inda ka fadi. Ka tuba ka yi abubuwan da ka yi da fari. Sai fa ka tuba, zan zo maka in kuma cire fitilar ka daga mazauninta.
\s5
\v 6 Amma kana da wannan: Ka tsani abubuwan da Nikolatawa suka yi, wanda nima na tsana.
\v 7 wanda yake da kunnen ji ya saurari abinda Ruhu yake fada wa ikilisiyoyi. Ga wanda yayi nasara zan bashi dama ya ci daga itacen rai, wanda ke cikin firdausin Allah.""
\s5
\v 8 Zuwa ga mala'ikan da ke Ikilisiliyar Samirna rubuta: 'Wadannan su ne kalmomin wanda yake shine farko shine karshe, wanda ya mutu ya sake rayuwa kuma.
\v 9 "Na san wahalun ka da talaucin ka amma kana da arziki. Nasan masu bata suna wadanda suke cewa su Yahudawa ne, amma ba haka suke ba. Su majami'ar Shaidan ne.
\s5
\v 10 Kada ka ji tsoron wahalar da zaka fuskanta nan gaba. Duba! Shaidan yana gab da jefa wadansun ku cikin kurkuku, domin a gwada ku, kuma zaku sha wahala ta kwana goma. Kuyi aminci har ga mutuwa zan baku rawanin rai.
\v 11 wanda yake da kunne ya saurari abinda Ruhu yake fada wa ikilisiyoyi. Shi wanda yayi nasara ba zai cutu a mutuwa ta biyu ba.""
\s5
\v 12 "Zuwa ga mala'ikan dake ikilisiyar Burgamas rubuta: 'Wadannan ne kalmomin wanda ya ke da takobi mai kaifi biyu;
\v 13 "Na san inda kake zama can inda kursiyin shaidan yake. Duk da haka ka rike sunana da karfi, na sani baka yi musun bangaskiyar ka da ni ba, ko a lokacin Antifas mashaidina, amintaccena, wanda aka kashe a tsakaninku, can inda shaidan yake zama.
\s5
\v 14 Amma ga rashin jin dadi na kadan da kai: Kana da wadansu da suke rike da koyarwar Bil'amu kamkam, wanda ya koya wa Balak ya sa abin tuntubi gaban 'ya'yan Isra'ila, domin su ci abincin da aka mika wa gumaka kuma suyi fasikanci.
\v 15 Hakannan kuma wasunku sun rike koyarwar Nikolatawa kamkam.
\s5
\v 16 Sabili da haka ka tuba! Idan ka ki zan zo gare ka da sauri, kuma in yi yaki gaba da su da takobi dake cikin bakina.
\v 17 Bari wanda yake da kunne ya sauriri abin da Ruhu yake fadawa ikilisiyoyi. Ga wanda yayi nasara zan bada wata boyayyar manna, kuma zan bashi farin dutse da sabon suna a rubuce a kan dutsen, suna wanda ba wanda ya sani, sai shi wanda ya karbe shi.""
\s5
\v 18 Zuwa ga mala'ikan ikilisiyar Tiyatira rubuta: 'Wadannan sune kalamomin Dan Allah, wanda yake da idanu kamar harshen wuta; sawayen kamar gogaggiyar tagulla:
\v 19 "Na san abin da ka yi, kaunar ka, da bangaskiya da hidima da tsawon jimrewar ka. Na san abinda ka yi bada dadewa ba ya fi abinda ka yi da fari.
\s5
\v 20 Amma ga rashin jin dadi na da kai: Kana hakurce wa matar nan Yezebel, wadda take kiran kanta annabiya. Ta wurin koyarwarta, ta rudi bayina suyi fasikanci kuma su ci abincin da aka mika wa gumaka sadaka.
\v 21 Na bata lokaci domin ta tuba amma bata so ta tuba da fasikancin ta.
\s5
\v 22 Duba! zan jefa ta a kan gadon jinya, wadanda kuma suka yi zina da ita za su shiga babbar wahala, sai dai in sun tuba daga ayukan ta.
\v 23 Zan buga 'ya'yanta da mutuwa, kuma dukan ikilisiyoyi zasu san cewa nine wanda nake bincike tunani da zukata. Zan ba kowanen ku bisa ga ayyukansa.
\s5
\v 24 Amma ga sauran ku dake cikin Tayatira, ga kowanen ku wanda bai rike wannan koyarwar ba, kuma bai san abinda wadansu suke kira zurfafan abubuwan Shaidan ba--ga ku na ce ban sa muku wata nawaya ba.'
\v 25 Duk da haka dole ku tsaya da karfi har in zo.
\s5
\v 26 Wanda yayi nasara da wanda ya yi abin da na yi har karshe, a gareshi zan bada iko akan al'ummai
\v 27 Zai yi mulkin su da sandar karfe, zai farfasa su kamar randunan yumbu."
\v 28 Kamar yadda na karba daga wurin Ubana, ni kuma zan bashi tauraron asubahi.
\v 29 Bari wanda yake da kunne ya saurari abinda Ruhu yake fadawa ikilisiyioyi.""
\s5
\c 3
\p
\v 1 "Zuwa ga mala'ikan ikilisiyar Sardisu rubuta: 'Wadannan ne kalmomin wanda yake rike da ruhohi bakwai na Allah da taurari bakwai. "Na san abin da ka aikata. Ka yi suna cewa kana raye amma kai mattacce ne.
\v 2 Ka farka ka karfafa abin da ya rage amma ya kusan mutuwa, domin ban sami ayyukanka cikakku a gaban Allahna ba.
\s5
\v 3 Domin haka sai ka tuna, da abubuwan da ka karba kuma kaji. Ka yi biyayya da su, ka kuma tuba. Amma idan baka farka ba, zan zo maka kamar barawo, kuma ba zaka farga da sa'ar da zan zo gaba da kai ba.
\v 4 Amma akwai sunayen mutane kadan a Sardisu wadanda basu kazantar da tufafinsu ba. Za su yi tafiya tare da ni sanye da fararen tufafi domin sun cancanta.
\s5
\v 5 Wanda ya yi nasara za a sanya mashi fararen tufafi, kuma ba zan taba share sunansa ba daga Littafin Rai, kuma zan fadi sunansa a gaban Ubana, da kuma gaban mala'ikunsa.
\v 6 Bari wanda yake da kunne ya saurari abin da Ruhu ke fadawa ikilisiyoyi."'"
\s5
\v 7 Zuwa ga mala'ikan ikilisiyar cikin Filadelfiya rubuta: kalmomin wanda yake maitsarki ne kuma mai gaskiya - yana rike da mabudin Dauda, yana budewa babu mai rufewa, kuma inda ya rufe ba mai budewa.
\v 8 Na san abin da ka aikata. Duba, na sa budaddiyar kofa a gabanka wanda ba mai iya rufewa. Na san kana da karamin karfi, duk da haka ka yi biyayya da maganata kuma baka yi musun sunana ba.
\s5
\v 9 Duba! Wadanda ke na majami'ar Shaidan, wadanda suke cewa su Yahudawa ne; amma maimakon haka karya suke yi. Zan sa su zo su rusuna a kafafunka, kuma za su san cewa ina kaunarka.
\v 10 Tun da ka jure cikin hakuri ka kiyaye dokoki na, ni ma zan kiyaye ka daga sa'a ta gwaji da zata sauko kan dukan duniya, domin a gwada mazauna duniya.
\v 11 Ina zuwa da sauri. Ka rike abin da kake da shi kamkam domin kada wani ya dauke maka rawani.
\s5
\v 12 Zan sa wanda ya yi nasara ya zama ginshiki a haikalin Allahna, kuma ba zai taba fita daga cikin sa ba. Zan rubuta sunan Allahna a kansa, sunan birnin Allahna (sabuwar Urushalima, mai saukowa daga sama daga wurin Allahna), da kuma sabon sunana.
\v 13 Bari wanda yake da kunne ya ji abin da Ruhu ke gayawa ikilisiyoyi."
\s5
\v 14 "Zuwa ga mala'ikan ikilisiyar da ke Lawudikiya rubuta: 'Wadannan sune kalmomin Amin, madogara da mai shaidar gaskiya, mai mulki bisa hallittar Allah.
\v 15 Na san abin da ka aikata, ba ka sanyi ko zafi. Naso ko da kana sanyi ko zafi!
\v 16 Amma saboda kai tsaka-tsaka ne - ba zafi ba sanyi - na kusa tofar da kai daga bakina.
\s5
\v 17 Domin ka ce, "Ni mai arziki ne, na mallaki kadarori da yawa, ba na bukatar komai." Amma ba ka sani ba kana cike da takaici ne, abin tausayi, matalauci, makaho kuma tsirara kake.
\v 18 Saurari shawara ta: Ka sayi zinariya a wuri na wadda aka goge da wuta domin ka zama mai arziki, domin ka suturta kanka da fararen tufafi masu kyalli domin kada ka nuna kunyar tsiraicin ka, da mai domin ka shafa wa idanunka ka sami gani.
\s5
\v 19 Ina horar da duk wanda nake kauna, ina kuma koya masu yadda za su yi rayuwa. Saboda haka, ka himmatu ka tuba.
\v 20 Duba, ina tsaye a bakin kofa ina kwankwasawa. Idan wani ya ji muryata ya bude kofar, zan shigo cikin gidansa, in ci tare da shi, shi kuma tare da ni.
\s5
\v 21 Wanda ya ci nasara, zan bashi dama ya zauna tare da ni bisa kursiyina, kamar yadda nima na ci nasara kuma na zauna da Ubana a kan kursiyinsa.
\v 22 Bari wanda yake da kunne ya saurari abin da Ruhu yake fadawa wa ikilisiyoyi."
\s5
\c 4
\p
\v 1 Bayan wadannan abubuwa na duba, sai ga budaddiyar kofa a sama. Muryar fari da na ji kamar kakaki, na cewa hauro in nuna maka abubuwan da dole za su faru bayan wadannan al'amura."
\v 2 Nan da nan ina cikin Ruhu, sai na ga wani kursiyin da aka ajiye shi a sama, da wani zaune bisansa.
\v 3 Shi da ke zaune a kan tana da kamanin yasfa da yakutu. Akwai Bakangizo kewaye da kursiyin kamanin bakangizon kuwa zumurudu.
\s5
\v 4 A kewaye da kursiyin kuwa akwai kursiyoyi ashirin da hudu, masu zama bisa kursiyoyin nan kuwa dattawa ne ashirin da hudu, sanye da fararen tufafi, da kambunan zinariya bisa kawunansu.
\v 5 Daga kursiyin walkiya na ta fitowa, cida, da karar aradu. Fitilu bakwai na ci a gaban kursiyin, fitilun sune ruhohin Allah guda bakwai.
\s5
\v 6 Gaban kursiyin akwai tekun gilashi, mai haske kamar karau. A tsakiyar kursiyin da kewayen kursiyin akwai rayayyun hallitu guda hudu cike da idanu gaba da baya.
\s5
\v 7 Rayayyen hallitta na farko na da kamanin zaki, rayayyen hallitta na biyun kamanin dan maraki ne, rayayyen hailitta na uku fuskar sa kamar dan adam, kuma rayayyen hallitta ta hudu na da kamanin gaggafa mai tashi.
\v 8 Dukan rayayyun hallittan nan hudu na da fukafukai shida shida, cike da idanu a bisa da karkashin fukafukan. Dare da rana ba sa daina cewa, Mai Tsarki, Mai Tsarki, Mai Tsarki ne Ubangiji Allah, mai iko duka, shine da shine yanzu shine mai zuwa."
\s5
\v 9 A dukan lokacin da rayayyun hallittun nan suke ba da girma, daukaka, da godiya ga shi da ke zaune bisa kursiyin, wanda ke raye har abada abadin,
\v 10 sai dattawan nan ashirin da hudu suka fadi da fuskokinsu a kasa gaban shi da ke zaune bisa kursiyin. Suka yi sujada ga shi da ke rayuwa har abada abadin, suna jefar da kambinsu a gaban kursiyin, suna cewa,
\v 11 "Ka cancanta, ya Ubangijinmu da Allahnmu, ka karbi yabo da daukaka da iko. Domin kai ka hallicci dukan komai, da kuma nufinka ne, suka kasance aka kuma hallicce su.
\s5
\c 5
\p
\v 1 Sa'annan na ga a cikin hannun daman wanda ke zaune a kan kursiyin, na ga littafi wanda ke da rubutu ciki da waje, an kuma hatimce shi da hatimai bakwai.
\v 2 Na kuma ga wani kakkarfan mala'ika na shela da murya mai karfi, "Wa ya isa ya bude littafin ya kuma bambare hatimin?"
\s5
\v 3 Ba wani a sama ko a kasa ko karkashin kasa da ya iya ya bude littafin ko ya karanta abin da ke cikinsa.
\v 4 Na yi kuka mai zafi saboda ba wani da ya cancanta da zai bude littafin ko ya karanta abin da ke cikinsa.
\v 5 Amma daya daga cikin dattawan nan ya ce mani, "Kada ka yi kuka. Duba! Zaki na kabilar Yahuza, Tushen Dauda, ya yi nasara. Ya cancanci bude littafin da kuma hatimansa bakwai."
\s5
\v 6 Na ga Dan Rago yana tsaye tsakanin kursiyin da rayayyun halittun nan guda hudu a cikin dattawa. Yana kama da wanda aka kashe. Yana da kafonni bakwai da idanuwa bakwai; wadannan sune ruhohin Allah bakwai da aka aiko zuwa dukan duniya.
\v 7 Ya tafi ya karbi littafin daga hannun daman wanda ke zaune bisa kursiyin.
\s5
\v 8 Lokacin da Dan Ragon ya dauki littafin, rayayyun halittun nan hudu da dattawan nan ashirin da hudu suka fadi har kasa a gaban Dan ragon. Kowannen su na dauke da molo da tasar zinariya cike da kayan kamshi, wadanda kuwa sune addu'o'in masu ba da gaskiya.
\s5
\v 9 Suka raira sabuwar waka: "Ka cancanta ka dauki littafinka kuma bude hatimansa. Domin an yanka ka, da jininka ka saya wa Allah mutane daga kowacce kabila, harshe, jama'a da al'umma.
\v 10 Ka maishe su mulki da firistoci su bauta wa Allanmu, kuma za su yi mulki a duniya."
\s5
\v 11 Da na duba sai na ji karar mala'iku masu yawa kewaye da kursiyin da rayayyun halitu da kuma dattawa. Jimillarsu ya kai dubbai goma, sau dubbai goma, da dubun dubbai.
\v 12 Suka tada murya da karfi suka ce, "Macancanci ne Dan Ragon da aka yanka ya karbi iko, wadata, hikima, karfi, girma, daukaka da yabo."
\s5
\v 13 Na ji kowanne halittaccen abu da ke cikin sama da kasa da karkashin kasa da cikin teku - dukan abubuwan da ke cikinsu - na cewa, "Ga shi wanda ke zaune a kan kursiyin da kuma Dan Ragon, yabo, girma, daraja, da kuma ikon yin mulki, har abada abadin.
\v 14 Sai rayayyun halittun nan hudu suka ce, "Amin!" dattawan nan kuma suka fadi da fuskokinsu suka yi sujada.
\s5
\c 6
\p
\v 1 Na duba lokacin da Dan Ragon ya bude daya daga cikin hatiman bakwai, sai na ji daya daga cikin rayayyun halittattun hudu ya fada da murya kamar tsawa, "Zo!"
\v 2 Sai Na duba sai ga wani farin doki, mahayinsa na rike da baka, kuma an bashi rawani. Ya fito a matsayin mai nasara domin ya yi nasara.
\s5
\v 3 Sa'anda Dan Ragon ya bude hatimi na biyu, sai na ji rayayyen halitta na biyu ya ce, "Zo!"
\v 4 Sai wani doki ya fito waje - jawur. Ga mahayin aka bashi dama ya dauke salama daga duniya, domin mutanen ta su karkashe juna. Wannan mahayin an bashi babbar takobi.
\s5
\v 5 Sa'anda Dan Ragon ya bude hatimi na uku, sai na ji rayayyen halita na uku ya ce, "Zo!" Na ga bakin doki, mai hawanta na rike da ma'auni a cikin hannunsa.
\v 6 Sai na ji kamar wata murya daga cikin rayayyun halittattun nan hudu ta ce, "Mudun alkama guda a kan albashin yini, kuma mudun sha'ir uku. Amma kar ka bata mai da kuma ruwan inabi."
\s5
\v 7 Da Dan Ragon ya bude hatimi na hudu, na ji muryar rayayyen halitta na hudu ya ce, "Zo!"
\v 8 Sai na ga wani doki ruwan toka. Mai hawansa an bashi suna mutuwa, hades kuma tana biye da shi. An basu iko bisa kashi hudu na duniya su kashe da takobi, yunwa, cututtuka, da kuma namomin jeji na duniya.
\s5
\v 9 Da Dan Ragon ya bude hatimi na biyar, a karkashin bagadi sai na ga rayukan wadanda aka kashe saboda maganar Allah, da kuma shaidar da suka rike.
\v 10 Suka yi kuka da babban murya, "Sai yaushe ya mai iko duka, Mai Tsarki da gaskiya, zaka shari'anta mazaunan duniya, ka kuma dauki fansar jininmu?
\v 11 Sai kowanne dayan su aka bashi farar tufa aka kuma fada masu su kara jira na lokaci kadan har sai adadin abokan bautar su da kuma 'yan'uwansu maza da mata wadanda aka kashe ya cika, kamar yadda aka kashe su.
\s5
\v 12 Da Dan Ragon ya bude hatimi na shidan, ina kallo sai ga babbar girgizar kasa. Rana ta zama baki kirin kamar bakar tufa, wata kuma ya zama kamar jini.
\v 13 Taurarin sama suka fado kasa, kamar yadda itacen baure ke karkade 'ya'yansa da basu nuna ba, yayin da babbar iska ta kada.
\v 14 Sama kuma ta bace kamar takardar da aka nannade. Kowanne dutse da tsibiri aka kau da shi daga wurinsa.
\s5
\v 15 Sai sarakan duniya da muhimman mutane da sarakunan yaki, attajirai, da masu iko, tare da kowanne mutum, bawa da 'yantacce suka boye cikin duwatsu da tsaunuka.
\v 16 Suka ce wa tsaunuka da duwatsu, "Ku fado bisan mu! Ku boye mu daga fuskar wanda yake zaune bisa kursiyin da kuma fushin Dan Ragon.
\v 17 Domin babban ranar fushin sa ta zo. Wa zai iya tsayawa?"
\s5
\c 7
\p
\v 1 Bayan wannan sai na ga mala'iku hudu suna tsaye bisa kusurwoyi hudu na duniya, suka rike iskoki hudu na duniya kamkam domin kada iska ta hura a kan duniya, a kan teku, ko wani itace.
\v 2 Sai na ga wani mala'ika na zuwa daga gabas, wanda yake da hatimin Allah mai rai. Ya yi kira da babbar murya da mala'ikun nan hudu da aka basu dama su azabtar da duniya da teku:
\v 3 "Kada ku azabtar da duniya, da teku, da itatuwa har sai mun sa hatimi bisa goshin bayin Allahnmu."
\s5
\v 4 Sai naji yawan wadanda aka hatimce: 144, 000, wadanda aka hatimce daga kowacce kabilar mutanen Isra'ila:
\v 5 dubu goma sha biyu aka hatimce daga kabilar Yahuza, dubu goma sha biyu daga kabilar Ra'ubainu, dubu goma sha biyu daga kabilar Gad,
\v 6 dubu goma sha biyu daga kabilar Ashiru, dubu goma sha biyu daga kabilar Naftali, dubu goma sha biyu daga kabilar Manassa.
\s5
\v 7 Dubu goma sha biyu daga kabilar Saminu, dubu goma sha biyu daga kabilar Lawi, dubu goma sha biyu daga kabilar Issaka,
\v 8 dubu goma sha biyu daga kabilar zabaluna, dubu goma sha biyu daga kabilar Yusufu, sai kuma dubu goma sha biyu daga kabilar Bilyaminu aka hatimce.
\s5
\v 9 Bayan wadannan abubuwa na duba, sai ga wani babban taro wanda ba mai iya kirgawa daga kowacce al'umma, kabila, mutane da harsuna tsaye a gaban kursiyin da gaban Dan Ragon. Suna sanye da fararen tufafi da ganyen dabino a hannuwansu,
\v 10 kuma suna kira da murya mai karfi: "Ceto ya tabbata ga Allahnmu wanda ke zaune bisa kursiyi, da kuma Dan Ragon!"
\s5
\v 11 Dukan mala'iku suna tsaitsaye kewaye da kursiyin kuma kewaye da dattawan nan da kuma rayayyun halittun nan hudu, suka kwanta rib da ciki da fuskokinsu a gaban kursiyin. Suka yi sujada ga Allah,
\v 12 suna cewa, "Amin! yabo, daukaka, hikima, godiya, girma, iko, da karfi su zama na Allahnmu har abada abadin! Amin!"
\s5
\v 13 Sai daya daga cikin dattawan ya tambaye ni, "Su wanene wadannan, da suke sanye da fararen tufafi, kuma daga ina suka fito?"
\v 14 Sai nace masa, "Ya shugaba, "Ka sani," sai ya ce mani, "Wadannan sune suka fito daga babban tsanani. Sun wanke tufafin su sun maida su farare cikin jinin Dan Ragon.
\s5
\v 15 Domin wannan dalili, suke gaban kursiyin Allah, kuma suna masa sujada dare da rana cikin haikalinsa. Shi wanda ke zaune bisa kursiyin zai zama runfa a bisan su.
\v 16 Ba za su kara jin yunwa ba, ko kishin ruwa ba. Rana ba zata buge su ba, ko kowanne zafi mai kuna.
\v 17 Domin Dan Ragon dake tsakiyar kursiyin zai zama makiyayin su, kuma zai bishe su zuwa mabulbulan ruwan rai, kuma Allah zai share dukan hawaye daga idanuwansu."
\s5
\c 8
\p
\v 1 Lokacin da Dan Ragon nan ya bude hatimi na bakwai, sai aka yi shiru a sama na kimanin rabin sa'a.
\v 2 Sa'anan na ga mala'iku bakwai wadanda ke tsaye a gaban Allah, aka kuma basu kahonni bakwai
\s5
\v 3 Wani mala'ika ya zo, rike da tasar turaren konawa na zinariya, a tsaye gaban bagadi. Turaren konawa mai yawa aka bashi saboda ya mika su tare da adu'o'in dukan masu bada gaskiya akan bagadin kona turare na zinariya a gaban kursiyin.
\v 4 Hayakin turaren konawa, da adu'o'in masu bada gaskiya, suka tashi sama a gaban Allah daga hanun mala'ikar.
\v 5 Mala'ikan ya dauki tasar turaren konawa ya cika ta da wuta daga bagadin. Sa'annan ya wurgo ta kasa zuwa duniya, sai ga tsawar aradu, da cida, da walkiya mai haske, da kuma girgizar kasa.
\s5
\v 6 Mala'ikun nan bakwai wadanda suke da kahonni bakwai suka yi shirin busa su.
\v 7 Mala'ika na fari ya hura kahonsa, sai ga kankara da wuta a garwaye da jini. Aka jeho shi kasa zuwa duniya sai kashi daya cikin uku na duniya ya kone, daya cikin uku na itatuwa suka kone, da duk danyar ciyawa suka kone kaf.
\s5
\v 8 Mala'ika na biyu ya busa kahonsa, sai wani abu mai kama da babban dutse mai cin wuta aka jefo shi cikin teku. Kashi daya cikin uku na tekun ya zama jini,
\v 9 daya cikin uku na rayayyun halittu da ke cikin ruwa suka mutu, sai daya bisa uku na jiragen ruwa aka hallaka.
\s5
\v 10 Mala'ika na uku ya busa kahonsa, sai gagarumin tauraro ya fado daga sama, yana ci kamar cocila, bisa kashi daya cikin uku na koguna da mabulbulan ruwa.
\v 11 Sunan tauraron Daci. Kashi daya cikin uku na ruwaye suka yi daci, sai jama'a da yawa suka mutu domin ruwayen sun yi daci.
\s5
\v 12 Mala'ika na hudu ya busa kahonsa, sai daya cikin kashi uku na rana ya harbu, da daya cikin kashi uku na wata da kuma daya cikin kashi uku na taurari. Sai daya cikin kashi uku nasu duka suka duhunce; daya cikin kashi uku na yini da daya cikin uku na dare suka rasa hasken su.
\s5
\v 13 Da na duba sai na ji gaggafa da take shawagi a tsakiyar sararin sama tana kira da babban murya, "Kaito, kaito, kaito, ga mazaunan duniya sabili da sauran karar kahonni na mala'ikun nan uku da za su busa."
\s5
\c 9
\p
\v 1 Sa'annan mala'ika na biyar ya busa kahonsa. Na ga tauraro daga sama da ya fado zuwa duniya. An ba tauraron nan mabudin hanyar rami marar iyaka.
\v 2 Ya bude hanyar rami marar iyaka, sai hayaki ya fito daga kofar kamar hayaki daga babban ramin wuta. Rana da iska suka juya duhu, sabili da hayakin da ke fitowa daga kofar ramin.
\s5
\v 3 Daga cikin hayakin kuwa sai ga fari sun fito zuwa duniya, aka ba su iko kamar na kunamai cikin duniya.
\v 4 Aka gaya masu kada su yi wa ciyayi da kowanne koren ganye ko itace illa, sai dai mutanen da basu da hatimin Allah a goshinsu.
\s5
\v 5 Ba a basu izini su kashe wadannan mutane ba, sai dai su azabtar da su na watani biyar. Zafinsu kuwa zai zama kamar na cizon kunama idan ta harbi mutum.
\v 6 A kwanakin nan mutane za su nemi mutuwa, amma ba za su same ta ba. Za su yi marmarin mutuwa, amma mutuwa za ta guje su.
\s5
\v 7 Farin kuwa suna kama da dawakai da aka shirya domin yaki. A bisa kansu akwai wani abu kamar rawanan zinariya, fuskokinsu kuma kamar na 'yan adam.
\v 8 Gashinsu kuma kamar na mata yake, hakoransu kamar hakoran zaki.
\v 9 Sulkunansu kuma kamar na karfe, karar fikafikansu kuma kamar karar kekunan dawakin yaki masu yawa da dawakai da aka shirya domin zuwa yaki.
\s5
\v 10 Suna da wutsiya da kari kamar kunamai; A wutsiyar su kuma suna da ikon da zai azabtar da mutane na tsawon wata biyar.
\v 11 Suna da wani kamar sarki a kansu, mala'ikan rami marar iyaka. Sunansa da Ibraniyanci Abadon, da Helenanci kuma Afoliyon.
\v 12 Bala'i na fari ya wuce. Duba! Bayan wannan akwai masifu guda biyu masu zuwa.
\s5
\v 13 Mala'ika na shida ya busa kahonsa, sai na ji murya daga kahonin bagadin zinariya da ke gaban Allah.
\v 14 Muryar ta ce wa mala'ika na shida da ke rike da kahon, "Kwance mala'ikun nan hudu da ke daure a babban kogin Yufiretis,"
\v 15 Mala'iku hudun da aka shirya domin wannan sa'a, da wannan rana, da wannan wata, da kuma wannan shekara, aka sake su su kashe daya bisa uku na 'yan adam.
\s5
\v 16 Yawan sojoji da ke kan dawakai shine 200, 000, 000. Na ji adadin su.
\v 17 Haka na ga dawakan a cikin wahayina da mahayansu: Sulkunansu jawur kamar wuta, bakin shudi, da kuma ruwan doruwa. Kawunan dawakan suna kama da na zakuna, daga bakunansu kuma wuta, da hayaki da farar wuta suka fito.
\s5
\v 18 Aka kashe daya bisa uku na mutane ta annoban nan uku: wuta, hayaki da farar wuta da suka fito daka bakunansu.
\v 19 Domin iko na dawakan na bakunansu da wutsiyoyinsu - domin wutsiyoyinsu suna kama da macizai, kuma suna da kawuna wadanda dasu suke ji wa mutane rauni.
\s5
\v 20 Sauran 'yan adam, da ba a kashe su ta wannan annoba ba, basu tuba daga ayyukan da suka yi ba. Basu kuma daina bautar aljanu da gumakan zinariya, da azurfa, da tagulla, da dutse, da itace ba - abubuwan da ba su gani, ji, ko tafiya.
\v 21 Basu kuma tuba ba daga kisan kai, sihiri, fasikanci, ko kuma ayyukansu na sata ba.
\s5
\c 10
\p
\v 1 Sa'anan na ga wani babban mala'ika yana zuwa daga sama. Yana lullube cikin girgije, a bisa kansa akwai bakangizo. Fuskarsa kamar rana, kafafunsa kamar ginshikan wuta.
\v 2 Yana rike da karamin littafi a hannunsa, da aka bude, sai ya sa kafarsa ta dama a bisa teku, kafarsa ta hagu kuma a kan kasa.
\s5
\v 3 Sai yayi ihu da babbar murya kamar zaki mai ruri. Lokacin da ya yi ihu, tsawan nan bakwai suka yi magana da karar su.
\v 4 Da tsawan nan bakwai suka yi magana, ina dab da rubutu, amma na ji wata murya daga sama cewa, "Ka rike asirin abin da tsawan nan bakwai suka fada. Kada ka rubuta shi."
\s5
\v 5 Sai mala'ikan da na gani tsaye bisa teku da kasa, ya daga hannun damarsa sama.
\v 6 Sai ya rantse da wannan da ke raye har abada abadin - wanda ya halicci sama da duk abinda ke cikinsa, da duniya da duk abin da ke a kanta, da teku da dukan abin da ke cikinsa, sai mala'ikan ya ce, "Babu sauran jinkiri.
\v 7 Amma a ranar da mala'ika na bakwai yana dab da busa kahonsa, a lokacin ne asirin Allah zai cika, daidai da yadda ya sanar wa bayinsa annabawa."
\s5
\v 8 Muryar da na ji daga sama ta sake magana da ni: "Tafi, ka dauki budadden littafin da ke hannun mala'ikan da ke tsaye bisa teku da kan kasa."
\v 9 Sai na tafi wurin mala'ikan na ce da shi ka bani karamin littafin. Yace dani, "Dauki littafin ka ci. Zai sa cikinka ya yi daci, amma a bakinka zai yi zaki kamar zuma."
\s5
\v 10 Na dauki karamin littafin daga hannun mala'ikan na ci. Ya yi zaki sosai a bakina kamar zuma, amma da na ci, sai cikina ya zama da daci.
\v 11 Wani yace mani, "Dole ka sake yin annabci kuma game da mutane masu yawa, da al'ummai, da harsuna da sarakuna."
\s5
\c 11
\p
\v 1 Aka bani sanda in yi amfani da ita kamar sandar awo. Aka ce mani, "Tashi ka auna haikalin Allah da bagadi, da wadanda ke sujada a cikinsa.
\v 2 Amma kada ka auna harabar haikalin, domin an ba da shi ga Al'ummai. Za su tattake birnin mai tsarki har wata arba'in da biyu.
\s5
\v 3 Zan ba shaidu na biyu iko su yi anabci na kwanaki dubu daya da dari biyu da sittin, sanye da tsummoki.
\v 4 Wadannan shaidu sune itatuwan zaitun biyu da kuma fitilu biyu da suke tsaye a gaban Ubangijin duniya.
\v 5 Idan wani ya yi niyyar cutar da su, wuta na fitowa daga bakinsu ta lashe makiyansu. Duk mai son cutar da su, dole a kashe shi ta wannan hanya.
\s5
\v 6 Wadannan shaidu suna da iko su kulle sama domin kada a yi ruwa a lokacin da suke anabci. Suna da iko su juya ruwaye su zama jini, su kuma bugi duniya da kowacce irin annoba duk lokacin da suka ga dama.
\v 7 Sa'adda suka gama shaidarsu, dabban da ke fitowa daga rami marar iyaka zai yi yaki da su. Zai ci nasara da su ya kashe su.
\s5
\v 8 Gawawwakinsu zasu kwanta kan hanyar babban birnin nan (wanda ma'anar sa ake kira Saduma da Masar) inda aka gicciye Ubangijinsu.
\v 9 Wajen kwana uku da rabi wadansu daga dukan mutane, da kabila, da harshe, da al'umma za su yi kallon gawawwakinsu. Za su ki yarda a sa su cikin kabari.
\s5
\v 10 Mazaunan duniya zasu yi murna da biki a kansu. Har za su aika wa juna kyautai saboda annabawan nan biyu da suka azabtar da mazaunan duniya.
\v 11 Amma bayan kwana uku da rabi, numfanshin rai daga wurin Allah zai shiga cikinsu sa'annan za su tsaya a kan kafafunsu. Matsanancin tsoro zata fado kan wadanda za su gansu.
\v 12 Sa'annan zasu ji murya mai kara daga sama tana ce masu, "Ku hauro nan!" Sa'annan za su tafi sama cikin gajimarai, makiyansu suna kallo.
\s5
\v 13 A waccan sa'a za a yi babbar girgizar kasa, sai kashi daya cikin goma na garin ya fadi. Mutane dubu bakwai za su mutu a girgizar kasar, wadanda suka tsira kuwa za su tsorata su ba da daukaka ga Allah na sama.
\v 14 Annoba ta biyu ta wuce. Duba! Annoba ta uku tana zuwa nan da nan.
\s5
\v 15 Sa'annan mala'ika na bakwai ya busa kahonsa, sai muryoyi masu kara suka yi magana cikin sama cewa, "Mulkin duniya ya zama mulkin Ubangijinmu da na Almasihunsa. Zai yi mulki har abada abadin."
\s5
\v 16 Sa'annan dattawan nan ashirin da hudu da ke zaune a kursiyoyinsu a gaban Allah, suka fadi fuskokinsu na kasa. Suka yi wa Allah sujada.
\v 17 Suka ce, "Mun yi maka godiya, Ubangiji Allah, Madaukaki, wanda yake yanzu da wanda yake a da, saboda ka dauki ikonka mai girma ka fara mulki.
\s5
\v 18 Al'ummai suka fusata, amma hasalar ka ta zo. Lokaci ya zo da za a yi wa mattatu sharia, da zaka ba da sakamako ga bayinka annabawa, da masu ba da gaskiya, da wadanda suka ji tsoron sunanka, karami da babba. Lokaci kuma ya yi da za ka hallaka wadanda ke hallakar da duniya."
\s5
\v 19 Sa'annan aka bude haikalin Allah da ke sama, sai aka ga akwatin alkawarinsa a cikin haikalinsa. Sai ga hasken walkiya, da rugugi, da aradu, da girgizar kasa, da manyan duwatsun kankara.
\s5
\c 12
\p
\v 1 Aka ga wata babbar alama a sama: wata mace ta yi lullubi da rana, kuma wata na karkashin kafafunta; rawanin taurari goma sha biyu na bisa kanta.
\v 2 Tana da ciki, tana kuma kuka don zafin nakuda - a cikin azabar haihuwa.
\s5
\v 3 Sai aka ga wata alama cikin sama: Duba! Akwai wani katon jan maciji mai kawuna bakwai da kahonni goma, sai kuma ga kambi guda bakwai bisa kawunansa.
\v 4 Wutsiyarsa ta share daya bisa uku na taurari a sama ta zubo su kasa. Diragon nan ya tsaya a gaban matar da ta kusan haihuwa, domin lokacin da ta haihu ya lankwame yaronta.
\s5
\v 5 Sai ta haifi da, namiji, wanda zai yi mulkin dukan al'ummai da sandar karfe. Aka fizge yaron ta zuwa ga Allah da kursiyinsa,
\v 6 matar kuwa ta gudu zuwa jeji inda Allah ya shirya mata domin a iya lura da ita kwanaki 1, 260.
\s5
\v 7 A lokacin sai yaki ya tashi a sama. Mika'ilu da mala'ikunsa suka yi yaki da diragon, sai diragon da nasa mala'iku suka yake su su ma.
\v 8 Amma diragon ba shi da isashen karfin da zai ci nasara. Don haka, shi da mala'ikunsa ba su kara samun wuri a sama ba.
\v 9 Sai aka jefa katon diragon nan tare da mala'ikunsa kasa, wato tsohon macijin nan da ake kira Iblis ko Shaidan wanda ke yaudarar dukan duniya.
\s5
\v 10 Sai na ji wata murya mai kara a sama: "Yanzu ceto ya zo, karfi, da mulkin Allahnmu, da iko na Almasihunsa. Gama an jefar da mai sarar 'yan'uwanmu a kasa - shi da yake sarar su a gaban Allah dare da rana.
\s5
\v 11 Suka ci nasara da shi ta wurin jinin Dan Ragon da kuma shaidar maganarsu, gama ba su kaunaci ransu ba, har ga mutuwa.
\v 12 Don haka, yi farinciki, ya ku sammai da duk mazauna da ke cikinsu. Amma kaito ga duniya da teku saboda iblis ya sauko gare ku. Yana cike da mummunan fushi, domin ya san lokacin sa ya rage kadan.
\s5
\v 13 Da diragon ya ga an jefar da shi kasa, sai ya fafari matar nan da ta haifi da namiji.
\v 14 Amma aka ba matar nan fukafukai biyu na babbar gaggafa domin ta gudu zuwa inda aka shirya mata a jeji. A wannan wuri ne za a lura da ita na dan lokaci, da lokatai, da rabin lokaci - a lokacin da babu macijin.
\s5
\v 15 Macijin ya kwararo ruwa daga bakin sa kamar kogi, don ya kawo ambaliyar da zai kwashe ta.
\v 16 Amma kasa ta taimaki matar. Kasa ta bude bakinta ta hadiye kogin da diragon ya kwararo daga bakinsa.
\v 17 Sai diragon ya fusata da matar, sai ya tafi ya yi yaki da sauran zuriyarta, wadanda suka yi biyayya da umarnan Allah suna kuma rike da shaida game da Yesu.
\v 18 Sai diragon ya tsaya a kan yashi, a gaban teku.
\s5
\c 13
\p
\v 1 Sai na ga wani dabba yana fitowa daga teku. Yana da kahonni goma da kawuna bakwai. A kan kahonninsa akwai kambi goma, a kan kowanne kansa akwai suna na sabo.
\v 2 Wannan dabban da na gani yana kama da damisa, kafafunsa kuma kamar na beyar, bakinsa kuma kamar na zaki. Wannan diragon ya ba shi karfinsa, da kursiyinsa da ikonsa mai girma na sarauta.
\s5
\v 3 Daya daga cikin kawunan dabban ya yi kamar an kashe shi, amma rauninsa mai tsanani ya warke. Sai dukan duniya ta yi mamaki a yayin da suke bin dabban.
\v 4 Su ma suka yi wa diragon sujada, domin ya ba dabban ikonsa. Suka yi wa dabban sujada suna ta cewa, "Wanene kamar dabban? Wa kuma zai iya yin fada da shi?"
\s5
\v 5 Aka ba dabban baki da zai iya fadin kalmomin fahariya da sabo. Ya sami izini na zartar da iko har wata arba'in da biyu.
\v 6 Sai dabban ya bude bakinsa yana maganganun sabo ga Allah: yana sabon sunansa, da mazauninsa, da kuma wadanda ke zaune a sama.
\s5
\v 7 Aka yarje wa dabbar ya yi yaki da masu bi ya kuma yi nasara da su. An kuma ba shi iko bisa kowacce kabila, da jama'a, da harshe, da al'umma.
\v 8 Dukan wadanda ke zaune a duniya za su yi masa sujada, dukan wadanda tun hallitar duniya ba a rubuta sunayensu a littafin rai na Dan Rago ba, wanda aka yanka.
\s5
\v 9 Idan wani yana da kunne, bari ya ji. Duk wanda za a dauke shi zuwa bauta, ga bauta zai tafi.
\v 10 Duk wanda za a kashe da takobi, da takobi za a kashe shi. Wannan kira ne na dauriya, hakuri da bangaskiya ga wadanda suke da tsarki.
\s5
\v 11 Sai na ga wani dabban na fitowa daga cikin kasa. Yana da kahonni biyu kamar na dan rago, ya kuma yi magana kamar maciji.
\v 12 Ya zartar da dukan ikon dabban na farko a gabansa, ya kuma sa duniya da duk mazaunanta su yi wa dabban nan na farko sujada, wanda aka warkar masa da rauni mai kamar na ajali.
\s5
\v 13 Ya yi manyan al'ajibai. Har ya sa wuta ta sauko kasa daga sama a gaban mutane.
\v 14 Ta wurin alamu da aka yarje masa ya yi, ya yaudari mazaunan duniya. Ya ce masu su yi wata siffa don girmama dabban da yake da raunin takobi, amma duk da haka ya rayu.
\s5
\v 15 Aka yarje masa ya ba da numfashi ga siffar dabban domin siffar ta yi magana, ta kuma sa a kashe duk wadanda suka ki yin sujada ga dabban.
\v 16 Ya kuma tilasta kowa, kanana da manya, mawadata da matalauta, masu yanci da bayi, su karbi alama a hannun dama ko kuma a goshi.
\v 17 Ba shi yiwuwa wani ya saya ko ya sayar sai dai yana da alamar dabban, wato lambar nan da ke wakiltar sunansa.
\s5
\v 18 Wannan na bukatar hikima. Idan wani yana da hikima, sai ya kididdige lambar dabban nan. Gama lambar ta mutum ce. Lambarta itace 666.
\s5
\c 14
\p
\v 1 Sai na duba na ga Dan Ragon yana tsaye a kan Dutsen Sihiyona. Tare da shi akwai mutum dubu dari da arba'in da hudu wadanda aka rubuta sunansa da sunan Ubansa a goshinsu.
\v 2 Na ji wata murya daga sama mai kara kamar kogin ruwa mai gudu da kuma aradu mai kara. Muryar da na ji ta yi kama da masu molo suna kada molonsu.
\s5
\v 3 Suka raira sabuwar waka a gaban kursiyin da kuma gaban rayayyun halittun nan hudu, da kuma dattawan. Ba mai iya koyon wakar nan sai dai mutum 144, 000 nan wadanda aka fanso daga duniya.
\v 4 Wadannan sune wadanda basu kazantar da kansu da mata ba, gama sun kebe kansu da tsarki daga halin jima'i. Wadannan ne ke bin Dan Ragon duk inda ya tafi. Aka fanso su daga cikin mutane domin su zama nunan fari domin Allah da Dan Ragon.
\v 5 Ba a iske karya a bakinsu ba; ba su da aibi.
\s5
\v 6 Na ga wani mala'ika na firiya a tsakiyar sararin sama, wanda yake da madawwamin sako na labari mai dadi domin a sanar da ita ga mazaunan duniya - ga kowacce al'umma, da kabila, da harshe, da kuma jama'a.
\v 7 Yayi kira da babbar murya, "Ku ji tsoron Allah, ku daukaka shi. Gama sa'arsa ta hukunci ta yi. Yi masa sujada, shi wanda ya yi sama da kasa, da teku, da kuma mabulbular ruwa."
\s5
\v 8 Sai wani malai'ka, malaika na biyu, ya biyo yana cewa, "Ta fadi, Babila mai girma ta fadi, wadda ta rinjayi dukan al'ummai su sha ruwan inabin fasikancinta."
\s5
\v 9 Wani mala'ika - na uku - ya biyo su da murya mai karfi yana cewa, "Duk wanda ya yi sujada ga dabban da kuma siffarsa, ya karbi alama a goshinsa ko a hannunsa,
\v 10 shi ma zai sha daga ruwan inabin fushin Allah, ruwan inabi da aka zuba tsantsa cikin kokon fushinsa. Wanda ya sha shi za a azabtar da shi da wuta, da farar wuta, a gaban tsarkakan mala'ikun Allah da kuma Dan Ragon.
\s5
\v 11 Hayaki daga azabarsu yana tashi sama har abada abadin, kuma ba su da hutu dare ko rana - wadannan masu sujada ga dabban da siffarsa da kuma dukan wadanda suka karbi alamar sunansa.
\v 12 Wannan shine kira domin hakurin jimrewa na wadanda ke da tsarki, wadanda suke biyayya ga dokokin Allah da bangaskiya cikin Yesu."
\s5
\v 13 Na ji murya daga sama cewa, "Rubuta wannan: Masu albarka ne matattu da suka mutu cikin Ubangiji." Ruhu yace, 'I' domin sun huta daga wahalarsu, gama ayyukansu na biye da su."
\s5
\v 14 Na duba sai ga farin gajimare. Zaune a kan gajimaren akwai wani kamar Dan Mutum. Yana da kambin zinariya a kansa da lauje mai kaifi a hannunsa.
\v 15 Sai wani malaika ya fito daga haikalin, ya yi kira da murya mai karfi ga wanda ke zaune kan gajimare: "Dauki laujenka ka fara girbi, domin lokacin girbin duniya ya yi."
\v 16 Sai wanda ke zaune a kan gajimaren ya wurga laujensa bisa kan duniya, aka kuma girbe duniya.
\s5
\v 17 Wani mala'ika ya fito daga haikali a sama, shi ma yana da kakkaifan lauje.
\v 18 Sai wani mala'ika ya fito daga bagadin kona turare, wanda yake da iko kan wutar. Ya yi kira da murya mai karfi ga wanda yake rike da kakkaifan lauje, "Ka dauki kakkaifan laujenka ka tattara nonnan innabi daga itacen inabin na duniya, gama inabin ya nuna."
\s5
\v 19 Mala'ikan ya jefa laujensa duniya ya tattara girbin inabin duniya. Ya zuba shi a cikin babbar taskar wurin matsar ruwan inabi na fushin Allah.
\v 20 Aka tattake wurin matsar inabin a bayan birni, jini ya yi ta gudu daga wurin matsar inabin, ya kai kamar tsawon linzami a bakin doki, har mil dari biyu.
\s5
\c 15
\p
\v 1 Sai na ga wata alama cikin sama, babba mai ban mamaki: Akwai mala'iku bakwai rike da annobai bakwai, wadanda sune annobai na karshe domin da su ne fushin Allah zai cika.
\s5
\v 2 Na ga wani abin da da ya bayyana mai kama da tekun gilashi mai haske garwaye da wuta. Tsaye a gefen tekun sune wadanda suka ci nasara a kan dabban da siffarsa, da kuma lambar da ke wakiltar sunansa. Suna rike da molayen da Allah ya ba su.
\s5
\v 3 Suna rera wakar Musa, bawan Allah, da wakar Dan Rago: "Ayyukan ka manya ne da ban mamaki, Ubangiji Allah, Mai iko duka. Adalci da gaskiya hanyoyinka ne, Sarkin al'ummai.
\v 4 Wanene ba zai ji tsoron ka ba, Ubangiji, ya kuma daukaka sunanka? Domin kai kadai ne mai tsarki. Dukan al'ummai za su zo su yi sujada a gabanka domin an bayyana ayyukan ka na adalci."
\s5
\v 5 Bayan wadannan abubuwa na duba, kuma aka bude haikalin alfarwar shaida a cikin sama.
\v 6 Daga wuri mafi tsarki mala'iku bakwai masu rike da annobai bakwai suka zo. Suna sanye da tufafi masu tsabta, da lallausar linin mai haske, suna kuma da damarar zinariya a kirjinsu.
\s5
\v 7 Daya daga cikin rayyayun halitu hudu ya ba mala'iku bakwai tasoshin zinariya bakwai cike da fushin Allah wanda yake raye har abada abadin.
\v 8 Haikalin ya cika da hayaki daga daukakar Allah da kuma ikonsa. Ba wanda ya iya shigarsa har sai da annoban nan bakwai na mala'ikun nan bakwai suka cika.
\s5
\c 16
\p
\v 1 Na ji babban murya na kira daga cikin haikali tana ce wa malai'iku bakwai, "Ku je ku zuba tasoshi bakwai na fushin Allah a kan duniya."
\s5
\v 2 Mala'ika na fari ya je ya zuba tasarsa a kan duniya; munanan gyambuna masu zafi suka fito wa mutane wadanda suke da alamar dabbar, wadanda suka bauta wa siffarsa.
\s5
\v 3 Mala'ika na biyu ya zuba tasarsa cikin teku. Ya zama jini, kamar jinin wanda ya mutu, kuma kowane abu mai rai da ke cikin tekun ya mutu.'
\s5
\v 4 Malaika na uku ya zuba tasarsa a cikin rafuffuka da mabulbulan ruwa, sai suka zama jini.
\v 5 Na ji mala'ikan ruwaye ya ce, "Kai mai adalci ne - wanda ya ke yanzu wanda yake kuma a da, Mai Tsarkin nan, domin ka shari'anta wadannan abubuwa.
\v 6 Domin sun zubar da jinin masu ba da gaskiya da annabawa, ka basu jini su sha; shine abinda da ya dace da su.
\v 7 Na ji bagadi ya amsa, "I, Ubangiji Allah Mai iko duka, shari'un ka gaskiya ne da adalci."
\s5
\v 8 Mala'ika na hudu ya zuba tasarsa a kan rana, kuma aka ba shi izini ya kone jama'a da wuta.
\v 9 Suka kone da zafi mai tsanani, kuma suka sabi sunan Allah, wanda ke da iko akan annobai. Ba su tuba ba ko su daukaka shi.
\s5
\v 10 Sai malaika na biyar ya zuba tasarsa a kan kursiyin dabban, sai duhu ya rufe mulkinsa. Suka cicciji harsunansu saboda zafi.
\v 11 Suka yi sabon Allah na sama domin zafi da gyambunansu, suka kuma ki su tuba daga abin da suka yi.
\s5
\v 12 Mala'ika na shida ya zuba tasarsa cikin babban rafi, Yufiretis. Ruwansa ya bushe domin a shirya hanya da sarakuna za su zo daga gabas.
\v 13 Na ga kazamun ruhohi uku suna kama da kwadin da ke fitowa daga bakin diragon, da makaryacin annabi.
\v 14 Gama su ruhohin aljanu ne masu aikata alamun ban mamaki. Sun fita za su wurin sarakunan dukan duniya domin su tattaro su wuri daya saboda yaki a babbar ranar Allah Mai iko duka.
\s5
\v 15 ("Duba! Ina zuwa kamar barawo! Mai albarka ne wanda ke zaune a fadake, wanda ke sanye da tufafinsa domin ba zai fita tsirara a ga tsiraicin sa ba.")
\v 16 Aka kawo su tare a wurin da ake kira Armagiddon da Ibraniyanci.
\s5
\v 17 Mala'ika na bakwai ya zuba tasarsa cikin iska. Sa'annan babbar murya ta fito daga cikin haikali da kuma kursiyin, cewa, "An gama!"
\v 18 Aka yi walkiya, da kararraki masu tsanani, da aradu da babbar girgizar kasa - girgizar da ta fi kowacce da aka taba yi tun da 'yan adam suke a duniya, girgizar da girma ta ke.
\v 19 Babban birnin ya rabu kashi uku, kuma biranen al'ummai suka fadi. Sai Allah ya tuna da Babila mai girma, sai ya ba wancan birnin koko cike da ruwan innabi wanda aka yi daga fushinsa mai tsanani.
\s5
\v 20 Kowanne tsibiri ya bace, sai ba a kara ganin duwatsun ba.
\v 21 Manyan duwatsun kankara, masu nauyin talanti, suka fado daga sama kan mutane. Suka zagi Allah domin annobar kankarar saboda annobar ta yi tsanani.
\s5
\c 17
\p
\v 1 Daya daga cikin mala'ikun nan bakwai wanda ke rike da tasoshi bakwai ya zo ya ce mani, "Zo, zan nuna maka hukuncin babbar karuwarnan da ke zaune a kan ruwaye masu yawa.
\v 2 Da ita ce sarakunan duniya suka yi fasikanci. Da ruwan inabinta na fasikanci marar dacewa ta sa mazaunan duniya suka bugu."
\s5
\v 3 Sai mala'ikan ya dauke ni cikin Ruhu ya tafi da ni jeji, sai na ga mace zaune bisa jan dabba cike da sunayen sabo. Dabbar tana da kawuna bakwai da kahonni goma.
\v 4 Matar kuwa tana sanye da tufafi na shunayya da kuma jar garura, ta kuma ci ado da kayan zinariya da duwatsu masu tamani da lu'u-lu'ai. Tana rike da kokon zinariya a hannunta cike da abubuwan kyama da na kazantar fasikancinta marar dacewa.
\v 5 Bisa goshinta an rubuta wani suna mai boyayyar ma'ana: "Babila mai girma, uwar karuwai da na kazamtattun abubuwan duniya."
\s5
\v 6 Sai na ga matar a buge da jinin masu ba da gaskiya da kuma jinin wadanda aka kashe su domin Yesu. Da na gan ta, na yi mamaki kwarai da gaske.
\v 7 Amma mala'ikan ya ce mani, "Don me kake mamaki? Zan bayyana maka ma'anar matar da kuma na dabbar da ke dauke da ita, dabban nan da ke da kawuna bakwai da kahonni goma.
\s5
\v 8 Dabban da ka gani da, yanzu ba ta, amma ta na kusan hawowa daga rami marar iyaka. Sa'annan za ta je hallaka. Wadanda ke zaune a duniya, wadanda ba a rubuta sunayensu cikin littafin rai ba tun kafuwar duniya - za su yi mamaki idan suka ga dabbar da da ta kasance, ba ta nan yanzu, amma ta kusa zuwa.
\s5
\v 9 Wannan al'amari na bukatar hikima. Kawunnan bakwai, tuddai ne bakwai da macen ke zaune a kai.
\v 10 Su kuma sarakuna ne bakwai. Sarakuna biyar sun fadi, daya na nan, amma dayan bai zo ba tukuna; sa'anda ya zo zai kasance na dan lokaci kadan.
\s5
\v 11 Dabban da ya kasance a da, amma yanzu ba shi, shi ma sarki ne na takwas; amma shi daya ne cikin sarakunan nan bakwai, kuma zai tafi hallaka.
\s5
\v 12 Kahonnin nan goma da ka gani sarakuna goma ne wadanda ba a nada su ba tukuna, amma za su karbi iko kamar na sarakai na sa'a daya tare da dabban.
\v 13 Ra'ayinsu daya ne, za su ba da sarautarsu da ikon su ga dabban.
\v 14 Za su yi yaki da Dan Rago. Dan Ragon zai ci nasara a kansu domin shi Ubangijin iyayengiji ne da Sarkin sarakuna - kuma tare da shi sune kirayayyun, zababbun, amintattun."
\s5
\v 15 Mala'ikan ya ce mani, "Ruwayen da ka gani, inda karuwar ke zaune, jama'a ce, da taro masu dumbin yawa, da al'ummai da harsuna.
\s5
\v 16 Kahonnin nan goma da ka gani - su da dabban za su ki karuwar. Za su washe ta su tsiranceta, za su lankwame namanta, za su kone ta gaba daya da wuta.
\v 17 Gama Allah ya sa a zukantansu su yi nufinsa ta wurin amincewarsa, su sadaukar da ikonsu na yin mulki ga dabban har sai maganar Allah ta cika.
\s5
\v 18 Matar da ka gani ita ce babban birnin nan da ke mulki bisa sarakunan duniya."
\s5
\c 18
\p
\v 1 Bayan wadannan abubuwa sai na ga wani mala'ika yana saukowa daga sama. Yana da babban iko sosai, duniya kuwa ta haskaka da daukakarsa.
\v 2 Ya yi kira da kakkarfar murya cewa, "Ta fadi, Babila mai girma ta fadi! Ta zama mazaunin aljannu, da matattarar kowanne kazamin ruhu da kuma mazaunin kowanne kazami da kyamataccen tsuntsu.
\v 3 Gama dukan al'ummai sun sha ruwan innabin fasikancinta. Sarakunan duniya sun aikata fasikanci da ita. Attajiran duniya sun arzuta da ikon rayuwar annashuwarta."
\s5
\v 4 Sai na ji wata murya daga sama ta ce, "Ku fito daga cikinta, mutanena, domin kada kuyi zunubi irin na ta, domin kuma kada bala'inta ya auko maku.
\v 5 Zunubanta sun taru sun yi tsayi har sama. Allah kuma ya tuna da miyagun ayyukanta.
\v 6 Ku saka mata gwargwadon yadda ta saka wa wadansu, ku biya ta ninki biyu na abin da ta yi; a cikin kokon da ta dama, ku dama mata ninki biyu.
\s5
\v 7 Kamar yadda ta daukaka kanta ta yi ta annashuwa, ku wahalsheta da azaba da bakin ciki haka. Domin ta ce a zuciyarta, 'Ina zaune kamar sarauniya; ni ba gwauruwa ba ce, kuma ba zan taba yin makoki ba,'
\v 8 Saboda haka a rana daya bala'inta zai auko mata; mutuwa, makoki da kuma yunwa. Wuta za ta kona ta kurmus, domin Ubangiji Allah mai iko ne, kuma shine mai hukuntata."
\s5
\v 9 Sarakunan duniya da suka yi fasikanci, har suka baude tare da ita, za su yi kuka da kururuwa domin ta sa'adda suka ga hayakin kunarta.
\v 10 Za su tsaya can nesa suna tsoron azabarta, suna cewa, "Kaito, kaiton babban birni, Babila, birni mai iko! Domin cikin sa'a guda hukuncinta ya zo."
\s5
\v 11 Manyan 'yan kasuwan duniya za su yi kuka da bakin ciki dominta, da shike ba wanda ke sayan kayanta kuma -
\v 12 kayan zinariya, azurfa, da duwatsun alfarma, da lu'u-lu'u, da lilin mai laushi, da hajja mai ruwan jar garura, da siliki, da jar alharini da itacen kamshi iri iri, da kayan da aka sassaka da itace mai tsada, da na tagulla, da na bakin karfe, da na dutse mai sheki,
\v 13 da kirfa, da kayan yaji, da turaren wuta, da mur da lubban, da ruwan innabi, da mai, da garin alkama, da alkama, da shanu, da tumaki, da dawakai, da kekunan doki, da bayi, da rayukan 'yan adam.
\s5
\v 14 Amfanin da kika kwallafa rai da duk karfinki sun fice daga gareki. Duk annashuwarki da darajarki sun bace, ba za a kara samunsu ba kuma.
\s5
\v 15 Manyan 'yan kasuwa na wadannan kaya da suka azurta ta wurinta, za su tsaya can nesa da ita, sabili da tsoron azabarta, kuka da kururuwar bakin ciki.
\v 16 Za su ce, "Kaito, kaito ga babban birni da take sanye da lilin mai laushi da tufafi masu jar garura da kuma jan alharini, da ta ci ado da kayan zinariya, da duwatsu masu daraja da lu'u-lu'u!
\v 17 A cikin sa'a guda duk dukiyan nan ta lallace. Kowanne matukin jirgin ruwa, da fasinjoji, da masu tuki da duk wadanda suke samun biyan bukatun rayuwarsu daga ruwa, suka tsaya can nesa.
\s5
\v 18 Suka yi kuka sa'anda suka ga hayakin kunarta. Suka ce, "Wanne birni ne ya yi kama da babban birnin?"
\v 19 Suka watsa kura a kawunansu, suka yi kuka da karfi, da kururuwa da bakin ciki, "Kaito, kaiton babban birnin nan inda duk masu jiragen ruwa suka azurta daga dukiyarta. Domin a sa'a guda an hallakar da ita."
\v 20 "Ku yi murna a kanta, sama, ku masu ba da gaskiya, manzanni, da annabawa, domin Allah ya kawo hukuncinku a kanta!"
\s5
\v 21 Wani kakkarfan mala'ika ya dauki wani dutse mai kama da dutsen nika, ya jefa shi cikin teku yana cewa, "Ta wannan hanya, Babila, babban birnin, za a jefar da ita kasa da karfi, ba za a kara ganinsa ba.
\v 22 Muryar masu kidar molaye, mawaka, masu busa sarewa, da na masu busa algaita, ba za a kara ji a cikinta ba. Babu wani mai kowanne irin sana'a da za a samu a cikinta. Ba za a kara jin karar nika a cikinta ba.
\s5
\v 23 Hasken fitila ba za ya kara haskakawa a cikin ki ba. Ba za a kara jin muryoyin ango da na amarya a cikinki ba, domin attajiranki sune 'ya'yan masu mulki a duniya, kuma ta wurin sihirinki kika yaudari al'ummai.
\v 24 A cikinta aka sami jinin annabawa da na masu ba da gaskiya, da jinin duk wadanda aka kashe a duniya."
\s5
\c 19
\p
\v 1 Bayan wadannan abubuwa na ji wata karar da ta yi kamar muryar mutane masu yawa a sama suna cewa, "Halleluya. Ceto, daukaka da iko sun tabbata ga Allahnmu.
\v 2 Hukunce - hukuncensa gaskiya ne da adalci, domin ya hukunta babbar karuwan nan wadda ta kazamtar da duniya da fasikancinta. Ya dauki fansar jinin bayinsa, wadda ita da kanta ta zubar."
\s5
\v 3 Suka yi magana a karo na biyu: "Halleluya! Hayaki na tasowa daga wurinta har abada abadin."
\v 4 Dattawan nan ashirin da hudu da rayayyun halittun nan hudu, suka fadi suka yi wa Allah sujada shi da yake zaune a kan kursiyin. Suna cewa, "Amin. Halleluya!"
\s5
\v 5 Sai wata murya ta fito daga kursiyin tana cewa, "Ku yabi Allahnmu, dukanku bayinsa, ku da kuke tsoronsa, da duk marasa iko da masu iko."
\s5
\v 6 Sai na ji murya kamar na kasaitaccen taron mutane, kamar rurin kogi na ruwaye masu yawa, kuma kamar tsawar aradu, cewa, "Halleluya! Gama Ubangiji yana mulki, Allah mai iko duka.
\s5
\v 7 Bari mu yi murna, mu yi farinciki matuka mu kuma ba shi daukaka domin bikin auren Dan Ragon ya zo, amaryarsa kuma ta shirya kanta.
\v 8 An yardar mata ta sa kaya masu haske da tsabta na lilin mai laushi" (domin lilin mai laushi shine ayyukan adalci na tsarkaka).
\s5
\v 9 Mala'ika ya ce mani, "Rubuta wannan: Masu albarka ne wadanda aka gayyace su zuwa bikin auren Dan Ragon." Ya kuma ce mani, "Wadannan kalmomin Allah na gaskiya ne."
\v 10 Na fadi a gaban kafafunsa domin in yi masa sujada, amma ya ce mani, "Kada ka yi haka! Ni ma abokin bauta ne tare da kai da 'yan'uwanka wadanda ke rike da shaida game da Yesu. Yi wa Allah sujada, domin shaida game da Yesu shine ruhun annabci."
\s5
\v 11 Sai na ga sama a bude, na kuma duba sai ga wani farin doki. Mahayinsa ana kiransa amintacce da gaskiya. Yana shari'a da adalci yana yaki.
\v 12 Idanunsa kamar harshen wuta suke, a kansa akwai kambuna da yawa. Yana da suna a rubuce a jikinsa wanda ba wani da ya sani sai dai shi da kansa.
\v 13 Yana sanye da riga da aka tsoma a cikin jini, kuma ana kiran sunansa Kalmar Allah.
\s5
\v 14 Rundunonin sama suna biye da shi a kan fararen dawakai, suna sanye da lilin mai laushi, fari mai tsabta.
\v 15 Daga cikin bakinsa takobi mai kaifi na fitowa, da ita yake sarar al'ummai, zai kuma mulke su da sandar karfe. Yana tattake wurin matsar ruwan inabi da matsananciyar fushin Allah Mai iko duka.
\v 16 Yana da suna a rubuce a rigarsa da cinyarsa: "Sarkin sarakuna da Ubangijin iyayengiji."
\s5
\v 17 Na ga mala'ika tsaye a rana. Yayi kira da murya mai karfi ga dukan tsuntsaye da ke firiya a sama.
\v 18 "Ku zo, ku tattaru saboda babban bukin Allah. Ku zo ku ci naman sarakuna, da naman sarakunan yaki, da naman manyan mutane, da naman dawakai, da na mahayansu, da naman dukan mutane, yantattu da bayi, marasa iko da masu iko."
\s5
\v 19 Na ga dabban da sarakunan duniya da rundunoninsu. Suna tattaruwa domin su yi yaki da wanda ke bisa doki da rundunarsa.
\v 20 Aka kama dabban tare da makaryatan annabawa da suka yi ayyukan al'ajibai a gabansa. Da wadannan alamu ya yaudari wadanda suka karbi alamar dabbar da wadanda suka yi wa siffarta sujada. Aka jefa dukansu biyu da rai cikin tafkin farar wuta mai ci.
\s5
\v 21 Sauran aka karkashe su da takobin da ke fitowa daga bakin mahayin dokin. Dukan tsuntsaye suka ci gawarwakinsu.
\s5
\c 20
\p
\v 1 Sai na ga mala'ika na saukowa daga sama. Yana da makullin rami marar iyaka, yana kuma da babar sarka a hannunsa.
\v 2 Sai ya dauki tsohon macijin, wanda shine iblis, ko shaidan, ya daure shi shekaru dubu.
\v 3 Ya jefa shi cikin rami marar iyaka, ya rufe shi ya kuma sa hatimi a bisansa. Hakan ya faru ne domin kada ya kara yaudarar al'ummai har sai bayan shekaru dubu. Bayan wannan, dole a sake shi na dan lokaci.
\s5
\v 4 Sa'annan na ga kursiyoyi. Wadanda ke zaune a bisansu sune wadanda aka ba ikon hukunci. Na kuma ga rayukan wadanda aka fille wa kai saboda shaidar Yesu da maganar Allah. Ba su yi wa dabban sujada ba ko siffarsa, suka ki su karbi alamar a goshinsu ko a hannu. Sun sake rayuwa, suka yi mulki tare da Kristi shekaru dubu.
\s5
\v 5 Sauran matattun basu sake dawowa da rai ba har sai da shekaru dubu din suka cika. Wannan shine tashin matattu na fari.
\v 6 Mai albarka ne mai tsarki ne kuma wanda yake da rabo cikin tashin matattu na fari! Mutuwa ta biyu ba ta da iko akan wadannan. Za su zama firistocin Allah da na Almasihu za su kuma yi mulki tare da shi shekaru dubu.
\s5
\v 7 Sa'adda shekaru dubu suka zo ga karshe, za a saki shaidan daga kurkukunsa.
\v 8 Za ya fito domin ya yaudari al'ummai da ke kursuyoyi hudu na duniya, Gog da Magog ya tattara su domin yaki. Yawan su zai zama kamar yashin teku.
\s5
\v 9 Suka bazu a fuskar duniya suka kuma kewaye sansanin masu ba da gaskiya, kaunataccen birni. Amma wuta ta sauko daga sama ta lankwame su.
\v 10 Shaidan, wanda ya yaudare su, aka jefa shi cikin korama ta farin wuta mai ci, inda aka jefa dabban da makaryacin annabin. Za su sha azaba dare da rana har abada abadin.
\s5
\v 11 Sai na ga babban kursiyi da wanda ke zaune a kansa. Duniya da sama suka guje wa fuskarsa, amma babu wurin da za su tafi.
\v 12 Na ga matattu manya da kanana- suna tsaye gaban kursiyin, aka bude litattafai. Sai aka bude wani littafi - Littafin rai. Aka yi wa matattu shari'a bisa ga abinda aka rubuta cikin litattafan, gwargwadon ayyukansu.
\s5
\v 13 Teku ta ba da matattun dake cikinta. Mutuwa da hades suka ba da matattun da ke cikinsu, aka yi masu shari'a gwargwadon abin da suka yi.
\v 14 Aka jefa mutuwa da hades cikin tafkin wuta. Wannan shine mutuwa ta biyu - tafkin wuta.
\v 15 Duk wanda ba a sami sunansa a rubuce cikin littafin rai ba, aka jefar da shi cikin tafkin wuta.
\s5
\c 21
\p
\v 1 Sai na ga sabuwar sama da sabuwar duniya, domin sama ta fari da duniya ta fari sun shude, ba kuma teku.
\v 2 Na ga birni mai tsarki, sabuwar Urushalima, wadda ta sauko kasa daga sama wurin Allah, shiryayya kamar amaryar da aka yi wa ado domin mijinta.
\s5
\v 3 Na ji babbar murya daga kursiyinta na cewa, "Duba! Mazaunin Allah yana tare da 'yan adam, zai zauna tare da su. Za su zama mutanensa, Allah kuma da kansa zai kasance tare da su ya kuma zama Allahnsu.
\v 4 Zai share dukan hawaye daga idanunsu, kuma babu sauran mutuwa, ko bakinciki, ko kuka, ko azaba. Abubuwan da sun shude.
\s5
\v 5 Shi wanda yake zaune a kan kursiyin ya ce, "Duba! Na maida kome ya zama sabo." Ya ce, "Ka rubuta wannan domin wadannan kalmomi amintattu ne da gaskiya".
\v 6 Ya ce mani, "Wadannan abubuwan an gama! Ni ne Alpha da Omega, farko da karshe. Ga mai jin kishi, zan bashi kyauta daga mabulbular ruwan rai.
\s5
\v 7 Wanda ya ci nasara, zai gaji wadannan abubuwa, ni kuma zan zama Allahnsa, shi kuma ya zama da na.
\v 8 Amma ga matsorata, da marasa bangaskiya, da masu kazanta, da masu kisan kai, da fasikai, da masu sihiri, da masu bautar gumaka, da dukan makaryata, mazaunin su zai kasance cikin tafki mai ci da farar wuta. Mutuwa ta biyu kenan."
\s5
\v 9 Daya daga cikin mala'ikun bakwai ya zo wurina, wanda yake dauke da tasoshi bakwai cike da annobai bakwai na karshe, yace, "Zo nan. Zan nuna maka amarya, matar Dan Rago".
\v 10 Sai ya dauke ni cikin Ruhu zuwa wani babban dutse mai tsawo ya nuna mani birni mai-tsarki, Urushalima, tana saukowa daga cikin sama daga wurin Allah.
\s5
\v 11 Urushalima tana da daukakar Allah, shekinta yana kama da dutse mai tamani, sai kace dutsen yasfa, garau kamar karau.
\v 12 Tana da babban garu mai tsawo, da kofofi goma sha biyu, da mala'iku goma sha biyu a kofofin. Akan kofofin an rubuta sunayen kabilu sha biyu na 'ya'yan Isra'ila.
\v 13 A gabas akwai kofofi uku, a arewa kofofi uku, a kudu kofofi uku, da kuma yamma kofofi uku.
\s5
\v 14 Garun birnin yana da harsashin gini goma sha biyu, a bisansu akwai sunaye goma sha biyu na manzanni goma sha biyu na Dan Rago.
\v 15 Shi wanda yayi magana dani yana da sandan awo na zinariya domin ya auna birnin, da kofofinsa, da garunsa.
\s5
\v 16 Birnin; da tsawonsa da fadinsa iri daya ne. Ya gwada birnin da sandar awo, mil dubu sha biyu a tsaye (fadinsa, da tsawonsa, da tsayinsa duka daya ne)
\v 17 Ya kuma gwada garunsa, kamu 144, bisa ga gwajin 'yan adam (wanda shine ma'aunin mala'ika).
\s5
\v 18 An gina garun da Yasfa birnin kuma da sahihiyar zinariya, mai kama da madubi mai kyalli.
\v 19 An kawata harsashin garun da kowanne irin dutse mai tamani. Na fari yasfa, na biyu saffir, na uku agat, na hudu emerald,
\v 20 na biyar Onis, na shida sardiyus, na bakwai kirisolat, na takwas beril, na tara tofaz, na goma kirisofaras, na sha daya yakinta, na sha biyu kuma ametis.
\s5
\v 21 Kofofi goma sha biyu lu'u-lu'ai ne goma sha biyu; kowacce daya a cikin kofofin daga lu'u-lu'u daya aka yi shi. Titunan birnin kuwa zinariya ce sahihiya, sai kace madubi garau.
\v 22 Ban ga haikali a cikin birnin ba, gama Ubangiji Allah Mai iko duka da Dan Ragon su ne haikalinsa.
\s5
\v 23 Birnin ba ya bukatar rana ko wata su haskaka shi gama daukakar Allah ta haskaka shi, kuma fitilarsa Dan Rago ne.
\v 24 Al'ummai za su yi tafiya cikin hasken birnin. Sarakunan duniya kuma za su kawo daukakarsu cikinsa.
\v 25 Kofofinsu kuma ba za a rufe su da rana ba, babu dare kuma a can.
\s5
\v 26 Za su kawo daukaka da darajar al'ummai a cikinsa,
\v 27 babu wani abu mai kazanta da zai taba shiga cikinsa. Ko wanda yake aikata abin kunya da karya, sai wadanda an rubuta sunayensu a cikin littafin rai na Dan Rago kadai.
\s5
\c 22
\p
\v 1 Sai mala'ika ya nuna mani kogin ruwan rai, ruwa mai tsabta. Yana fitowa daga cikin kursiyin Allah da na Dan-Rago
\v 2 ta tsakiyar titin birnin. A kowanne gefen kogin akwai itacen rai, mai ba da 'ya'ya iri goma sha biyu, kowanne wata. Ganyayen itacen kuma domin warkar da al'ummai ne.
\s5
\v 3 Babu sauran la'ana nan gaba. Kursiyin Allah da na Dan Rago za su kasance a cikin birnin, bayinsa kuma za su yi masa bauta.
\v 4 Za su ga fuskarsa, sunansa kuma zai kasance a goshinsu.
\v 5 Babu sauran dare; ba za su bukaci hasken fitila ko hasken rana ba gama Ubangiji Allah zai haskaka su. Za su yi mulki har abada abadin.
\s5
\v 6 Mala'ika ya ce mani, "Wadannan kalmomi amintattu ne da gaskiya. Ubangiji, Allah na ruhohin annabawa, ya aiki mala'ikansa ya nuna wa bayinsa abin da lallai zai faru ba da dadewa ba".
\v 7 "Duba! Ina zuwa ba da dadewa ba! Mai albarka ne wanda ya yi biyayya da kalmomin littafin nan."
\s5
\v 8 Ni, Yahaya, nine na ji na kuma ga wadannan abubuwa. Sa'adda na ji na gan su, sai na fadi gaban kafaffun mala'ikan da ya nuna mani wadannan abubuwa domin in yi masa sujada.
\v 9 Ya ce mani, "Kada ka yi haka! Ni abokin bauta ne tare da kai, tare da 'yan'uwanka annabawa, da wadanda ke biyayya da kalmomin littafin nan. Yi sujada ga Allah!"
\s5
\v 10 Ya ce mani, "Kada ka rufe kalmomin anabcin littafin nan, gama lokaci ya kusa.
\v 11 Wanda yake mara adalci, bari ya cigaba da yin rashin adalci. Wanda yake mai kazanta bari ya cigaba da kazantar da kansa. Wanda yake mai adalci bari ya cigaba da yin adalci. Wanda yake mai-tsarki, bari yaci gaba da tsarki."
\s5
\v 12 "Duba! Ina zuwa ba da dadewa ba. Sakamakona na tare da ni, zan saka wa kowa gwargwadon aikin da ya yi.
\v 13 Nine Alpha da Omega, farko da karshe, mafarin abu da karshensa.
\s5
\v 14 Masu albarka ne wadanda suka wanke rigunansu domin su sami izini su ci daga itacen rai su kuma shiga birnin ta kofofinsa.
\v 15 A waje akwai karnuka, masu sihiri, masu bautar gumaka, fasikai, masu kisan kai, da duk wanda yake kaunar aikata rashin gaskiya.
\s5
\v 16 Ni, Yesu na aiko mala'ikana ya shaida maku wadannan abubuwa saboda ikilisiyoyi. Nine tushe da zuriyar Dauda, tauraron asubahi mai-haske."
\s5
\v 17 Ruhu da Amarya suka ce, "Zo!" Bari wanda ya ji ya ce, "Zo!" Kowanne mai jin kishi, da kowanne mai bukatar ta, bari ya sami ruwan rai kyauta.
\s5
\v 18 Ina shaida wa duk mai jin kalmomin anabcin wannan littafi: Idan wani ya kara a kansu, Allah zai kara masa annoban da ke rubuce a cikin littafin.
\v 19 Idan wani ya rage daga kalmomin wannan littafin anabci, Allah zai rage rabonsa daga cikin itacen rai daga cikin birni mai-tsarki, wadanda aka rubuta cikin wannan littafi.
\s5
\v 20 Shi wanda ya shaida wadannan abubuwa ya ce, "I! Ina zuwa ba da dadewa ba." Amin! Zo, Ubangiji Yesu!
\v 21 Alherin Ubangiji Yesu ya kasance tare da kowanne dayanku. Amin.