ha_ulb/24-JER.usfm

2670 lines
220 KiB
Plaintext
Raw Normal View History

2021-09-13 13:40:08 +00:00
\id JER
\ide UTF-8
\h Littafin Irmiya
\toc1 Littafin Irmiya
\toc2 Littafin Irmiya
\toc3 jer
\mt Littafin Irmiya
\s5
\c 1
\cl Sura 1
\p
\v 1 Waɗannan su ne kalmomin Irmiya ɗan Hilkiya, ɗaya daga cikin firistocin Anatot cikin ƙasar Benyamin.
\v 2 Maganar Yahweh ta zo gare shi a kwanakin Yosiya ɗan Amon, sarkin Yahuda, cikin shekara ta goma sha uku ta mulkinsa.
\v 3 Ta kuma zo cikin kwanakin Yehoyakim ɗan Yosiya, sarkin Yahuda, har sai watan biyar na shekara goma sha ɗaya ta Zedekiya ɗan Yosiya, sarkin Yahuda, lokacin da aka kwashe mutanen Yerusalem a matsayin 'yan fursuna.
\s5
\v 4 Maganar Yahweh tazo gare ni, cewa,
\v 5 "Kafin In sifanta ka a cikin ciki, Na zaɓe ka; kafin ka fito daga cikin ciki Na keɓe ka; Na sa ka zama annabi ga al'ummai."
\v 6 Sai na ce, "Ah, Ubangiji Yahweh!" Na ce, "Ni ban san yadda zan yi magana ba, gama ni yaro ne."
\s5
\v 7 Amma Yahweh yace mani, "Kada ka ce 'Ni ƙaramin yaro ne.' Dole ka tafi duk inda Na aike ka, kuma ɗole ka faɗi duk abin da Na umarce ka!
\v 8 Kada ka ji tsoron su, gama Ina tare da kai domin in cece ka - wannan furcin Yahweh ne."
\s5
\v 9 Daga nan sai Yahweh ya miƙa hanunsa ya taɓa bakina, yace mani, "Yanzu, Nasa maganata a cikin bakinka.
\v 10 Yau na sanya ka bisa kan al'ummai da kan mulkoki, ka tunɓuke ka kuma rushe, ka hallakar, ka kuma juyar, ka gina ka dasa."
\s5
\v 11 Sai maganar Yahweh ta zo wurina, cewa, "Me ka gani, Irmiya?" Na ce, "Na ga reshen almond."
\v 12 Yahweh yace mani, "Ka gani da kyau, gama ina kiyaye maganata domin in cika ta."
\s5
\v 13 Maganar Yahweh ta sake zuwa wuri na karo na biyu, cewa, "Me ka gani? Na ce, "Na ga tukunya mai zafi, wadda fuskarta na ɓullowa, tana kaucewa daga arewa.
\v 14 "Yahweh ya ce mani, "Bala'i zai fito daga arewa akan dukkan mazaunan ƙasar nan.
\s5
\v 15 Gama ina kiran dukkan kabilun mulkokin arewa, inji Yahweh. Zasu zo, kowanne ɗayan su zai kafa kursiyin sa a ƙofofin shiga Yerusalem, gãba da dukkan ganuwar da ta kewaye ta, kuma gãba da dukkan biranen Yahuda.
\v 16 Zan furta hukunci gãba da su domin dukkan muguntarsu cikin yãshe ni, ta wurin ƙona turare ga waɗansu alloli, cikin kuma yin sujada ga abubuwan da suka ƙera da hannuwansu.
\s5
\v 17 Ka shirya kanka! Ka tashi ka faɗa masu duk abin da na umarce ka. Kada ka firgita a gaban su, ko in firgitar da kai a gabansu!
\v 18 Duba! Yau, na maishe ka tsararren birni, ginshiƙin ƙarfe, da bangaye na tagulla gãba da dukkan ƙasar - gãba da sarakunan Yahuda, da hakimansu, firistocinsu, da mutanen ƙasar.
\v 19 Zasu yi yaƙi gãba da kai, amma ba zasu yi nasara da kai ba, gama zan kasance tare da kai in cece ka - wannan furcin Yahweh ne."
\s5
\c 2
\cl Sura 2
\p
\v 1 Maganar Yahweh tazo gare ni, cewa,
\v 2 "Kaje ka yi shela ga kunnuwan Yerusalem. Ka ce, 'Yahweh ya faɗi wannan: Na tuna a madadin ki da alƙawarin aminci cikin ƙuruciyarki, ƙaunarki a lokacin da muna tashe, lokacin da kika bi ni cikin jeji, ƙasar da ba'a taɓa shuka ba.
\v 3 An keɓe Isra'ila ga Yahweh, nunan farin girbinsa! Dukkan waɗanda suka ci daga nunan farin sun ɗauki laifinsu; bala'i ya afko masu - wannan furcin Yahweh ne."'
\s5
\v 4 Kuji maganar Yahweh, ya gidan Yakubu, dukkanku iyalin gidan Isra'ila.
\v 5 Yahweh ya faɗi haka, "Wanne laifi ubanninku suka iske tare da ni, da suka yi nisa daga bi na? Da suka bi alloli marasa amfani su kansu kuma suka zama marasa amfani?
\v 6 Basu ce, "Ina Yahweh, wanda ya fito da mu daga ƙasar Masar ba? Ina Yahweh, wanda ya bishe mu cikin jeji, zuwa cikin ƙasar Araba da ramummuka, a cikin ƙasar fari da duhu mai zurfi, ƙasa wadda ba wanda ke ratsawa ba kuma wanda yake zama ciki?'
\s5
\v 7 Amma na kawo ku cikin ƙasar Kamel, domin ku ci 'ya'yan itatuwanta, da sauran abubuwa masu kyau! amma da kuka zo, kuka ƙazantar da ƙasata, kun maida abin gãdona ya zama abin ƙyama!
\v 8 Firist bai ce, 'Ina Yahweh ba?' masanan shari'a kuma basu da mu da ni ba! Makiyaya sun yi mani laifi. Annabawa suka yi annabci domin Ba'al suka kuma bi al'amura marasa amfani.
\s5
\v 9 Saboda haka har yanzu zan zarge ku - wannan furcin Yahweh ne - kuma zan zargi 'ya'yan 'yayanku.
\v 10 Domin ƙetarewa zuwa gaɓar Kittim ku kuma duba. Ku aika da manzanni zuwa Kedar ku bincika ku gani ko an taɓa yin wani abu irin wannan.
\v 11 Ko al'umma ta musanya allolinta, ko da shike su ba alloli ba ne? Amma mutane na sun musanya darajarsu da abin da ba zai taimakesu ba.
\s5
\v 12 Ku girgiza, sammai, saboda wannan! ku yi rawar jiki ku kuma firgita - wannan furcin Yahweh ne.
\v 13 Gama mutanena sun aikata mugayen abubuwa biyu gãba da ni: Sun yi watsi da maɓuɓɓugan ruwayen rai, sun gina wa kansu randuna, hudaddun randuna waɗanda ba zasu iya riƙe ruwa ba.
\s5
\v 14 Ko Isra'ila bawa ne? An haife shi a gidan ubangidansa? To don me ya zama abin washewa?
\v 15 'Yan zakuna sun yi masa ruri. Suna surutai da yawa sun kuma mai da ƙasarsu wurin tsoratarwa. An lalatar da biranensu ba sauran mazauna a ciki.
\v 16 Kuma, mutanen Memfis da Tafanhes zasu aske ƙoƙon kanku.
\v 17 Ba ku ne kuka yi wa kanku wannan ba lokacin da kuka yashe da Yahweh Allahnku, yayin da yake bishe ku a hanya?
\s5
\v 18 Yanzu fa, me ya kai ku hanyar Masar kuka kuma sha ruwayen Shihor? Don me kuka bi hanyar zuwa Asiriya kuma kuka sha ruwayen kogin Yufiratis?
\v 19 Muguntarku ta tsauta maku, rashin bangaskiyarku kuma ya hore ku. Don haka ku yi tunani akai, kuma ku fahimci cewa mugunta ce kuma da ɗaci idan kuka yashe da Yahweh Allahnku, kuma baku da tsoro na - wannan furcin Ubangiji Yahweh mai runduna ne.
\s5
\v 20 Gama na karye karkiyar da kake da ita tun zamanin dã; na yanke sarƙƙoƙinka. Duk da haka ka ce, 'Ba zan yi bauta ba!' da shike ka russuna wa kowanne tudu mai tsawo da gindin kowanne itace mai ganye, kai mazinaci.
\v 21 Na dasa ka a matsayin zaɓaɓɓen inabi, cikakke daga iri marar aibi. Amma ta yaya ka canza kan ka zuwa gurɓatacce, inabi marar amfani.
\v 22 Gama ko da ka wanke kanka cikin kogi ko ka wanke da sabulu mai ƙarfi, zunubinka ya ɓata ka a gaba na - wannan furcin Ubangiji Yahweh ne.
\s5
\v 23 Ta yaya zaka ce, 'Ban ƙazantu ba! Ban bi Ba'aloli ba?' Dubi abin da ka yi a cikin kwarurruka! Yi la'akari da abin da kayi, kai raƙumi ne mai gaggawar tafiya mai gudu nan da can,
\v 24 jakar jeji wadda ta saba da zaman jeji, a cikin zuffarta tana numfasa iska! Wa zai tsai da sha'awarta? Babu daga cikin mazajen da ke buƙatar ya gajiyar da kansa wajen binta; a lokacin barbararsu zasu same ta.
\v 25 Dole ka tsaida ƙafafunka daga zama marar takalmi kuma maƙogwaronka daga jin ƙishi! Amma ka ce, 'Ba bege! A'a, Ina ƙaunar bãƙi kuma zan bi su!'
\s5
\v 26 Kamar yadda ɓarawo yake jin kunya idan an kama shi, haka gidan Isra'ila zai ji kunya - su, da sarakunansu, hakimansu, da firistocinsu da annabawa!
\v 27 Waɗannan su suke cewa itace, 'Kai ubana ne,' ga dutse kuma, 'Kai ka haife ni.' Gama bayansu ke fuskanta ta ba fuskokinsu ba. Duk da haka a kwanakin matsaloli zasu ce 'Ka tashi ka cece mu!'
\v 28 Duk da haka ina allolin da kuka yi wa kanku? Bari su tashi in sun ga dama su cece ku a lokacin damuwarku, gama yawan allolinku yawan biranenku, ya Yahuda!
\s5
\v 29 To don me kuke zargi na a kan yi ba dai-dai ba? Dukkan ku kun yi mani zunubi - wannan furcin Yahweh ne.
\v 30 A banza na hukunta mutanenku. Ba zasu karɓi horo ba. Takobinku ya cinye annabawanku kamar zaki mai hallakarwa!
\v 31 Ku 'yan wannan tsara! Ku saurari maganata, maganar Yahweh! Na zama jeji ga Isra'ila? Ko ƙasa mai baƙin duhu? Don me mutanena zasu ce, 'Bari mu yi yawo mu zagaya, ba zamu ƙara zuwa wurin ka ba?'
\s5
\v 32 Zai yiwu budurwa ta manta da kayan adonta na zinariya ko amarya da kayan lulluɓin ta? Duk da haka mutanena sun manta da ni kwanaki ba iyaka!
\v 33 kin shirya hanyarki da kyau don ki nemi ƙauna. Kin koyar da halayenki ga mugayen mata.
\v 34 A cikin tufafinki an iske jinin ran marasa laifi, mutane talakawa. Waɗannan mutane ba a same su cikin ayyukan sata ba.
\s5
\v 35 Amma kin ce, 'Ni mara laifi ce; lallai fushinsa ya juya daga gare ni.' Amma duba! zan kawo hukunci a kan ki domin kin ce, 'Ban yi zunubi ba.'
\v 36 Don me kike ɗauka da sauƙi haka batun canza hanyoyinki? Masar zata kunyatar da ke kamar yadda Asiriya ta yi maki.
\v 37 Kema za ki fita daga can a wulaƙance, da hannayen ki a kanki, gama Yahweh ya ƙi waɗanda kika dogara gare su, don haka ba za ki sami taimako daga gare su ba."
\s5
\c 3
\cl Sura 3
\p
\v 1 "Idan mutum ya saki matarsa, ta fita daga wurinsa ta kuma zama matar wani, zai sake komawa wurinta kuma? Ƙasar ba zata ƙazantu ba gaba ɗaya? Kin zama kamar karuwa mai masoya da yawa; yanzu kuma kina so ki sake dawowa wurina? - wannan furcin Yahweh ne.
\v 2 Ki ɗaga idanun ki sama ki duba tsaunuka! ko akwai wurin da ba kiyi lalata ba? A bakin hanya kin zauna kina jiran masoyanki, kamar Balarabe cikin jeji. Kin ƙazantar da ƙasar da karuwancinki da kuma mugunta.
\s5
\v 3 Don haka an hana ruwan bazara ruwan kaka kuma bai zo ba. Amma fuskar ki akwai girmankai, kamar fuskar karuwa. Ba ki jin kunya.
\v 4 Ba yanzu kika kira gare ni ba: 'Ubana! Abokina na kurkusa tun daga ƙuruciyata!
\v 5 Koyaushe zai yi ta fushi? Kullum zai riƙe fushinsa har ƙarshe?' Duba! Wannan shi ne abin da kika ce, amma kin yi dukkan muguntar da kika iya yi!"
\s5
\v 6 A kwanakin sarki Yosiya sai Yahweh ya ce mani, "Ka ga abin da Isra'ila marar amana ta aikata? Ta hau bisa kan kowanne tudu mai tsawo ƙarƙashin kowanne itace mai ganyaye, a can ta zama kamar karuwa.
\v 7 Na ce, 'Bayan ta yi dukkan waɗannan al'amura, zata koma wurina,' amma bata komo ba. Daga nan sai 'yar uwarta mai cin amana Yahuda ta ga waɗannan abubuwa.
\s5
\v 8 Sai na ga haka, Isra'ila maci amana ta aikata zina na kore ta na bata takardar kisan aure, 'yar uawrta maci amana Yahuda bata ji tsoro ba; ita ma ta fita ta aikata kamar karuwa.
\v 9 Karuwancinta ba wani abu ba ne a gare ta; ta ƙazantar da ƙasa, ta kuma aikata zina da duwatsu da itatuwa.
\v 10 Daga nan bayan dukkan waɗannan, 'yaruwarta maci amana Yahuda ta komo wurina, amma ba da dukkan zuciyarta ba, amma da ƙarya - wannan furcin Yahweh ne."
\s5
\v 11 Daga nan sai Yahweh ya ce mani, "Adalcin Isra'ila ya fi na Yahuda maci amana!
\v 12 Ka je kayi shelar waɗannan maganganu zuwa ga arewa. 'Ki dawo, ya Isra'ila mai cin amana! - wannan furcin Yahweh ne - ba kulluyaumin zan yi fushi da ke ba. Tun da ni mai aminci ne-wannan furcin Yahweh ne - ba zan zauna cikin fushi ba har abada.
\s5
\v 13 Ki yarda da zunubinki, gama kin aikata laifuffuka gãba da Yahweh Allahnku; kin raba hanyoyin ki da bãƙi ƙarƙashin kowane itace mai duhuwa! Gama baki saurari muryata ba! - wannan furcin Yahweh ne.
\v 14 Ku juyo, mutane maciya amana! - wannan furcin Yahweh ne - mijinki ne! zan ɗauke ki, ɗaya daga cikin birni, biyu daga cikin iyali, zan kawo ki Sihiyona!
\v 15 Zan baku makiyaya gwargwadon zuciyata, kuma zasu yi kiwon ku da sani da fahimta.
\s5
\v 16 Sa'annan zai kasance a sa'ad da zaku riɓanɓanya ku bada 'ya'ya a waɗannan kwanaki - wannan furcin Yahweh ne - daga nan ba zasu ƙara cewa, "Sanduƙin akwatin alƙawari na Yahweh ba!" Wannan al'amarin ba zai ƙara zuwa cikin zuciyarsu ba, gama ba zasu ƙara tunawa ko su yi kewarsa ba. Kuma ba za a ƙara yin wani ba.'
\s5
\v 17 A lokacin nan za su yi shela game da Yerusalem, 'Wannan shi ne kursiyin Yahweh,' daga nan sauran al'ummai za su taru a Yerusalem a cikin sunan Yahweh. Ba za su ƙara yin tafiya cikin taurin kai da muguntar zuciyar su ba.
\v 18 Cikin kwanakin nan, gidan Yahuda zai yi tafiya da gidan Isra'ila. Tare za su zo daga kasar arewa zuwa ƙasa wadda na ba kakannin ku a matsayin gãdo.
\s5
\v 19 Amma ni, Nace, Yadda nake so in girmamaku a matsayin ɗa in baku ƙasa mai daɗi abin gãdo wanda ya fi kyau fiye da wanda ke cikin sauran al'ummai!' Da sai in ce, 'Zaku kira ni "baba na". 'Ba zaku juya daga bina ba.
\v 20 Amma kamar mace mai cin amanar mijinta, kun yashe ni, ku gidan Isra'ila - wannan furcin Yahweh ne."
\s5
\v 21 An ji murya bisan filaye, kuka da godon mutanen Isra'ila! Gama sun canza hanyoyinsu; sun manta da Yahweh Allahnsu,
\v 22 "Ku juyo, ku mutane maciya amana! Zan warkar da yaudarar ku!" Duba!! Zamu zo wurin ka, gama kai ne Yahweh Allahnmu!
\s5
\v 23 Hakika ƙarairayi sun zo daga tuddai, muryoyi masu ruɗar wa daga duwatsu; hakika Yahweh Allahnmu shi ne ceton Isra'ila.
\v 24 Duk da haka gumaka abin kunya sun cinye abin da kakanninmu suka yi wahalarsa - garkunansu na shanu da na awaki, 'ya'yansu maza da mata!
\v 25 Bari mu kwanta cikin kunya. Bari kunyar mu ta rufe mu, gama mun yi zunubi ga Yahweh Allahnmu! Mu da kakanninmu, tun daga lokacin ƙuruciyar mu har zuwa yau, bamu saurara ga muryar Yahweh Allahnmu ba!"
\s5
\c 4
\cl Sura 4
\p
\v 1 Idan kuka juyo, Isra'ila - wannan furcin Yahweh ne - zai zama gare ni zaku juyo. Idan kuka kawar da ƙazantattun abubuwa daga gabana kuma baku ƙara bari na ba,
\v 2 Dole ku zama da gaskiya, marasa aibi, da masu adalci lokacin da kuke rantsuwa, 'Da ran Yahweh.' Sa'annan ne al'ummai za su albarkaci kansu a cikinsa, kuma a cikinsa zasu yi ɗaukaka."
\v 3 Gama Yahweh ya faɗi haka ga kowanne mutum da ke cikin Yahuda da Yerusalem: 'Ku yi huɗar ƙasarku, kada kuma ku yi shuka cikin ƙayayuwa.
\s5
\v 4 Kuyi wa kanku kaciya ga Yahweh, ku cire loɓar zuciyarku, mazajen Yahuda da mazaunan Yerusalem, in ba haka ba fushina zai fita kamar wuta, ya ƙone har ba wanda zai kashe shi, saboda muguntar ayyukanku.
\v 5 Ka sanar cikin Yahuda, bari a ji a Yerusalem. Ka ce, "A busa ƙaho cikin ƙasar." Ayi shela a ce, "Mu taru. Bari mu shiga zuwa birane masu kagara."
\v 6 A ɗaga alamar tuta kuma ta fuskanci wajen Sihiyona, ku gudu don ku tsira! kada ku tsaya, gama zan kawo bala'i daga arewa da babbar faɗuwa.
\s5
\v 7 Zaki yana zuwa daga cikin kurminsa wani kuma wanda zai hallakar da al'ummai yana shirin fita. Zai bar wurinsa ya kawo tsoratarwa a ƙasarku, zai mai da biranenku su zama kangaye, inda ba mai zama ciki.
\v 8 Saboda haka, ku yi ɗammara da tsummoki, ku yi makoki kuna kururuwa. Gama ƙarfin fushin Yahweh bai juya daga gare mu ba.
\s5
\v 9 Zai zama kuma a ranar nan - wannan furcin Yahweh ne. a ranar nan, zuciyar sarki da hakimansa zata mutu. Firistoci zasu tsorata annabawa kuma zasu razana."
\v 10 Sai nace, "Ah! Ubangiji Yahweh. Lallai ka ruɗi waɗannan mutane da Yerusalem ta wurin cewa, 'Zaku sami salama.' Duk da haka takobi tana sara gãba da ransu."
\s5
\v 11 A wannan lokaci za'a ce da waɗannan mutane da Yerusalem, "Iska mai ƙuna daga wajen filayen hamada, zata yi wajen ɗiyar mutanena. Ba zata sheƙe ba ko kuwa ta tsarkake su.
\v 12 Iska da ta fi wannan ƙarfi zata zo bisa ga umarni na, yanzu kuma zan furta shari'a a kansu.
\s5
\v 13 Duba, yana kai hari kamar giza-gizai, karusansa kuma suna kamar hadari. Dawakansa sunfi gaggafa sauri. Kaiton mu, gama zamu zama hallakakku!
\v 14 Ki wanke zuciyar ki daga mugunta ya Yerusalem, domin ki tsira. Har yaushe zuzzurfan tunaninki zai kasance yadda za a yi zunubi?
\v 15 Gama murya na kawo labari daga Dan, an ji zuwan masifa daga tuddan Ifraim.
\s5
\v 16 Kasa al'ummai su yi tunani akan wannan: Duba, ka sanar da Yerusalem cewa magewaya suna zuwa daga ƙasa mai nisa su tada muryar yaƙi akan biranen Yahuda.
\v 17 Zasu zama kamar masu tsaron nomammiyar gona gãba da ita kewaye, domin tayi mani tayaswa wannan shi nefurcin Yahweh -
\v 18 halinki da ayyukanki ne suka yi maki waɗannan abubuwa. Wannan zai zama hukuncinki. Zai zama da muni! Zai buga har zuciyarki.
\s5
\v 19 Ya zuciyata! Zuciyata! Ina cikin baƙin ciki a zuciyata, zuciyata tana binbini a cikina. Ba zan iya yin shiru ba, gama na ji ƙarar ƙaho, gangamin yaƙi.
\v 20 Bala'i na bin bala'i; gama dukkan ƙasar ta zama kango. Farat ɗaya rumfunana an hallaka su, labulena kuwa nan da nan.
\s5
\v 21 Har yaushe zan ga tutar? Zan ji ƙarar ƙaho?
\v 22 Saboda wautar mutanena - basu sanni ba. Mutane ne masu halin wauta basu da fahimta. Masu azanci ne wajen mugunta, amma basu da sanin yin abu mai kyau.
\s5
\v 23 Na duba ƙasar. Duba! ta zama wofi da fanko. Gama babu haske domin sammai.
\v 24 Na duba duwatsu. Duba, suna rawar jiki dukkan tsaunuka suna girgiza.
\v 25 Na duba. Duba, babu ko ɗaya, kuma dukkan tsuntsayen sammai sun gudu.
\v 26 Na duba. Duba, fadamun sun zama jeji dukkan biranenta sun rurrushe a gaban Yahweh, da zafin fushinsa."
\s5
\v 27 Ga abin da Yahweh yace, "Dukkan ƙasar zata zama kango, amma ba zan hallakar da ita dungum ba.
\v 28 Saboda wannan dalili, ƙasar zata yi makoki, sammai daga bisa kuma zasu duhunta. Gama na sanar da manufofi na; ba zan sake nufi na ba; ba kuwa zan juya ga barinsa ba.
\v 29 Kowanne birni zai gudu daga ƙarar mahayan dawakai da maharba; zasu ruga cikin kurmi. Kowanne birni zai hau sama cikin wurare masu duwatsu. Za a bar biranen, ba za a sami wanda zai zauna cikinsu ba.
\s5
\v 30 Yanzu da kika zama kango, me za ki yi? Ko da kike sa tufafi na mulufi, kike ado da kayan zinariya, kina sa idanunki su zama manya saboda shafe shafe, mazan da suka yi sha'awar ki yanzu sun yashe ki. Maimakon haka, suna ƙoƙarin ɗaukar ranki.
\v 31 Na ji sautin baƙin ciki, wahala kamar a lokacin haihuwar ɗan fari, sautin muryar ɗiyar Sihiyona. Tana haki. Ta baza hannayenta, ta ce, 'Kaitona! Ina suma saboda waɗannan masu kisan kai."
\s5
\c 5
\cl Sura 5
\p
\v 1 "Yi gudu ta titunan Yerusalem; yi bincike cikin dandalin birninta, kuma. Daga nan ka duba kayi tunani akan wannan: Ko za a sami mutum ɗaya ko akwai wanda ya ke aikata adalci yana ƙoƙarin aikata aminci, daga nan zan yafewa Yerusalem.
\v 2 Kodashike suna cewa, 'Mun rantse da ran Yahweh,' duk da haka suna rantsuwa kan ƙarya."
\v 3 Yahweh, idanunka ba aminci suke kallo ba? Ka bugi mutanen, duk da haka basu ji zafi ba, ka hallaka su gaba ɗaya, amma duk da haka sunƙi kaɓar horo. Sun sa fuskokinsu sun taurare fiye da dutse, gama sun ƙi tuba.
\s5
\v 4 Sa'annan nace, "Hakika waɗannan mutane talakawa ne. Su wawaye ne, gama basu san tafarkun Yahweh ba, ko umarnan Allahnsu ba.
\v 5 Zan tafi wurin muhimman mutane domin in sanar da saƙonnin Allah gare su. Gama sun san hanyoyin Yahweh, da umarnan Allahnsu." Amma dukkan su sun karya karkiyarsu tare, sun tsintsinke sarƙoƙin da suka ɗaure su ga Allah.
\v 6 Domin wannan zaki daga cikin kurmi zai kai masu hari. Kyarkeci daga Araba zai lalata su. Damisa za ta zo gãba da biranensu. Duk wanda ya fita daga cikin birninsa za a yayyage shi. Gama laifofinsu sun ƙaru. Ayyukan rashin amincinsu kuwa basu da iyaka.
\s5
\v 7 Don me zan gafarta wa waɗannan mutane? 'Ya'yansu sun yashe ni kuma sunyi rantsuwa ga waɗanda ba alloli ba ne. Na ciyar dasu sun ƙoshi, amma sun aikata zina, sun riƙa tafiya suna cincirindo zuwa gidajen karuwai.
\v 8 Dawakai ne su cikin zafi. Suna yawo suna jira a haɗu, kowanne mutum yana neman matar maƙwabcinsa.
\v 9 Don haka ba zan hukunta su ba? - wannan furcin Yahweh ne - kuma ba zan ɗaukar wa kai na fansa a kan irin wannan al'ummar ba?
\s5
\v 10 Ku hau sama gun garkunan inabinta ku gano ku hallaka. Amma kada ku hallakar da ita duka. Ku gyara inabinsu, gama waɗannan inabin ba daga Yahweh suke ba.
\v 11 Gama gidajen Isra'ila dana Yahuda sun bashe ni gaba ɗaya - wannan furcin Yahweh ne.
\v 12 Sun faɗi ƙarya game da Yahweh kuma suka ce, "Ba zai yi kome ba; ba wata cuta da zata zo kanmu, ba kuwa zamu ga takobi ko yunwa ba.
\v 13 Annabawa zasu zama iska, maganar bata cikin su, bari duk abin da suka faɗi ayi masu."
\s5
\v 14 Yahweh, Allah mai runduna ya faɗi wannan, "Saboda ka faɗi haka, duba, duba zansa maganata cikin bakinka. Zata zama kamar wuta, mutanen nan kuma zasu zama kamar itace! Gama zata cinyesu.
\v 15 Duba!! zan kawo wata al'umma daga nesa, ya gidan Isra'ila - wannan furcin Yahweh ne - al'ummace wadda ta wanzu, kuma daɗaɗɗiyar al'umma! Al'umma ce wadda baka san yaren su ba, ba kuwa zaka fahimci abin da suke faɗi ba.
\s5
\v 16 Kwarinsu kamar buɗaɗɗen kabari ne. Dukkansu sojoji ne.
\v 17 Zasu cinye amfanin da ka girbe, haka 'ya'yanka maza da mata, da abincinka. Zasu cinye garken tumakinku da na awaki da kuma garken shanunku; zasu cinye kuringar anab naka dana ɓaure. Zasu rurrushe biranenka masu ganuwa da takobi waɗanda ka dogara gare su.
\s5
\v 18 Amma ko a cikin waɗancan kwanaki - wannan furcin Yahweh ne - bani da nufin in hallakar da ku baki ɗaya.
\v 19 Zai faru idan ku, Isra'ila da Yahuda, kun ce, 'Don me Yahweh Allahnmu ya yi mana dukkan waɗannan abubuwa?' Sai kai, Irmiya, kace masu, 'Kamar yadda kuka yashe da Yahweh kuka yi sujada ga baƙin alloli a cikin ƙasarku, haka kuma dole ku bauta wa baƙi a cikin ƙasar da ba taku bace.
\s5
\v 20 Ka sanar da wannan a gidan Yakubu bari a ji a gidan Yahuda. Kace,
\v 21 'Ku ji wannan ku wawayen mutane waɗanda basu da fahimta; kuna da idanu amma baku gani, kuna da kunnuwa amma ba ku ji.
\v 22 Baku ji tsoro na ba - wannan furcin Yahweh ne - ko kuyi rawar jiki a fuskata ba? Na sa yashi ya zama iyakar teku, bisa madauwamin umarni wanda ba zai ƙetare ba - koda shike teku yana tashi ya na faɗuwa, duk da haka bai karya shi ba, ko da sun yi ruri ba zasu ƙetare ba.
\s5
\v 23 Amma waɗannan mutane suna da kangararriyar zuciya. Sun yi tayarwa sun tafi abinsu.
\v 24 Gama a cikin zuciyarsu ba su ce, "Bari mu ji tsoron Yahweh Allahnmu, wanda yake bada ruwa na farko da na ƙarshe a lokacinsu ba, ya ke tabbatar mana da makonnin girbl." Laifofinku sun hana waɗannan faruwa.
\v 25 Zunubanku sun hana abubuwa masu kyau su zo gare ku.
\s5
\v 26 Gama an sami miyagun mutane tare da mutanena. Suna fako kamar yadda wani ke laɓewa ya kama tsuntsaye; suna ɗana tarko su kama mutane.
\v 27 Kamar yadda keji yake cike da tsuntsaye, haka gidajensu suke cike da ha'inci da ruɗi. Don haka sun yaɗu sun zama masu arzaki.
\v 28 Sun yi ƙiba; suna ƙyalli da lafiyarsu. Suna keta haddin kowacce mugunta. Basu sauraron roƙon mutane ko dalilin marayu. Sun azurta duk da ba sa nuna adalci ga masu bukata.
\v 29 Bazan hukunta su saboda waɗannan abubuwa ba - wannan furcin Yahweh ne - kuma ba zan ɗaukar wa kaina fansa a kan al'umma irin wannan ba?
\s5
\v 30 Abubuwan banƙyama da tsoratarwa sun faru a cikin ƙasar.
\v 31 Annabawa suna anabci da ha'inci, firistoci suna mulki da ikonsu. Mutanena kuma suna son haka, amma me zai faru a ƙarshe?"'
\s5
\c 6
\cl Sura 6
\p
\v 1 Ku nemi mafaka, mutanen Benyamin, ta wurin fita daga Yerusalem. Ku busa ƙaho cikin Tekowa. Ku tada tuta kan Bet Hakkerem, tun da mugunta tana bayyana daga arewa; babbar hallakarwa na zuwa.
\v 2 Za a hallaka ɗiyar Sihiyona, kyakkyawar mace 'yar lele.
\v 3 Makiyaya da garkunansu zasu tafi wurinsu; zasu kafa rumfunansu kewaye dasu; ko wannen su zai yi kiwo tare da hannunsa.
\s5
\v 4 Ka miƙa kanka ga allolin domin yaƙin. Mu tashi, bari mu kai hari da rana. Bashi da kyau gama hasken rana yana dushewa, inuwoyin yamma suna faɗuwa.
\v 5 Amma bari mu tashi da dare mu kai hari mu hallaka matsaranki."
\s5
\v 6 Gama Yahweh mai runduna ke faɗar haka: Ku sare itatuwanta, ayi tudu da aikin kewaye gãba da Yerusalem. Wannan shi nebirnin daya cancanci a kai wa hari, domin cike yake da zalunci.
\v 7 Kamar yadda rijiya take bada ruwa, haka birnin yake sarrafa mugunta. Ana jin tashin hankali da rashin lafiya a cikinta, cuta da rauni kullum suna gabana.
\v 8 Ki karɓi horo ya Yerusalem ko in juya daga gareki in sa ki cikin hallaka, ƙasar da babu mai zama ciki.
\s5
\v 9 Yahweh mai runduna ya faɗi wannan, "Hakika zasu yi kalar waɗanda suka ragu a Isra'ila kamar kuringar inabi. Ka sake sa hanunka ka tsinki inabi daga kuringa.
\v 10 Ga wa zan sanar in kuma yi gargaɗi domin su ji? Duba! Kunnuwansu marasa kaciya ne; ba su iya saurarawa! Duba! Maganar Yahweh tazo gare su domin ta kwaɓesu, amma basu so ba."
\s5
\v 11 Amma na cika da hasalar Yahweh. Na gaji da daurewa a cikinta, Yace mani, "Ka zuba ta kan yara cikin tituna, da kan taron majiya ƙarfi. Gama kowanne miji za a ɗauke shi da matarsa; da kowanne tsoho mai yawan shekaru.
\v 12 Za a ɗauki gidajensu aba waɗansu, gonakinsu da matansu gaba ɗaya. Gama zan kai hari ga mazaunan ƙasar da hannuna - wannan furcin Yahweh ne.
\s5
\v 13 Yahweh ya furta cewa daga ƙaraminsu zuwa babbansu, dukkansu suna haɗama wajen cin ƙazamar riba.
\v 14 Daga annabi zuwa Firist, kowannensu yana aikata yaudara. Sun warkar da raunukan mutane na sama sama, suna cewa, 'Salama, Salama,' alhali kuwa ba salamar.
\v 15 Suna jin kunya lokacin da suka aikata abin ƙyama? Basu jin kunya; basu san yadda zasu juye ba, Don haka zasu faɗi cikin masu faɗowa; za a kawo su ƙasa lokacin hukuncinsu, inji Yahweh.
\s5
\v 16 Yahweh yace, "Ka tsaya a mararrabar hanya ka duba, ka tambayi daɗaɗɗun tafarkun hanyoyi. 'Ina wannan hanya mai kyau take?' kayi tafiya kanta ka samarwa kanka wurin hutu. Amma mutane suka ce, 'Ba zamu je ba'
\v 17 Na sa maku matsara ku saurari muryar ƙaho. Amma suka ce, 'Ba zamu saurara ba.'
\v 18 Don haka ku saurara, al'ummai! ku duba, ku zama shaidar abin da zai same su.
\v 19 Ki ji, ke duniya! Zan kawo masifa kan mutanen nan - 'ya'yan tunaninsu. Ba su saurari maganata ko dokata ba, amma sun ƙi ta."
\s5
\v 20 "Mene ne ma'anar wannan turare mai ƙanshi na lubban da ake kawowa daga sheba a gare ni? ko wannan ƙanshi mai daɗi daga ƙasa mai nisa? ƙonannun hadayunku ba abin karɓa ba ne a gareni ko sadakokinku.
\v 21 Domin wannan Yahweh yace, 'Duba, zan sa sanadin tuntuɓe akan waɗannan mutane. Za suyi tuntuɓe a kan sa - Ubanni da 'ya'ya maza tare. Mazaunan tare da maƙwabtansu kuma zasu hallaka.'
\v 22 Yahweh yace, 'Duba, al'umma tana zuwa daga ƙasar arewa. Za a zuga babbar al'umma su taso daga ƙasa mai nisa.
\s5
\v 23 Zasu ɗauki kibau da mãsu. Masu mugunta ne basu da tausayi. Ƙararsu na ruri kamar teku, suna kuma hawan dawakai, sun fita a jere kamar mayaƙan mutane, gãba da ke, ɗiyar Sihiyona.'"
\v 24 Mun ji rahotanni game dasu hannuwanmu kuma sun yi sanyi cikin azaba. Azaba ta kama mu kamar mace mai naƙuda.
\s5
\v 25 Kada ku fita zuwa filaye, kada ku yi tafiya kan hanyoyi, gama takubban abokan gaba da tsoratarwa suna koina.
\v 26 Ɗiyar mutanena, ki sanya tsummoki ki kuma yi birgima cikin toka; ki yi makoki da kuka mai zafi kamar na tilon ɗa, gama mai hallakarwar zai zo kanmu ba zato.
\s5
\v 27 "Irmiya, Na maishe ka mai gwada mutanena, kamar mai gwada ƙarfe, zaka duba suka auna hanyoyinsu.
\v 28 Mutane ne da suka fi kowa rashin ji, suna yawon ɓata waɗansu. Dukkansu jan karfe da baƙin ƙarfe suke, masu aikata cin hanci.
\v 29 Mazuga suna zuga da wutar dake ƙonesu; dalma tana cinyewa cikin harshen wuta. Tacewar ta ci gaba tsakaninsu, amma bashi da amfani, saboda ba a kawar da muguntar ba.
\v 30 Za a kira su azurfar da aka ƙi, gama Yahweh ya ƙi su."
\s5
\c 7
\cl Sura 7
\p
\v 1 Maganar da ta zo ga Irmiya daga Yahweh, cewa,
\v 2 Ka tsaya a ƙofar gidan Yahweh ka shaida wannan maganar! Kace, 'Ji maganar Yahweh, dukkan kuna Yahuda, ku da kuke shiga waɗannan ƙofofin kuyi ma Yahweh sujada.
\s5
\v 3 Yahweh mai runduna, Allah na Isra'ila, ya faɗa haka: Ku gyara hanyoyinku da ayyukanku da kyau, haka kuwa zan ƙyale ku ku ci gaba da zama a nan wurin.
\v 4 Kar ku miƙa kanku ga maganganun ƙarya ku kuma ce, "Haikalin Yahweh! Haikalin Yahweh! Haikalin Yahweh!"
\s5
\v 5 Gama idan kun tabbatar da ayyukanku da hanyoyinku da kyau; idan kun aiwatar da adalci da gaskiya tsakanin mutum da makwabcinsa -
\v 6 idan baku zalunci wanda ke zaune a ƙasar ba, da maraya da gwauruwa kuma baku zubar da jini a banza a nan wurin ba, kuma baku bi waɗansu allolin da zasu yi maku illa ba -
\v 7 sa'annan zan ƙyale ku ku zauna a nan wurin, a ƙasar dana bayar ga kakanin ku daga zamanin zamanai da zuwa har abada.
\s5
\v 8 Duba!! kun amince da maganganu na ruɗami da ba zasu taimake ku ba.
\v 9 Kuna sata da kisan kai da zina? kuna rantsuwar ƙarya da kuma miƙa turare ga Baal kuma kuna bin waɗansu allolin da baku sani ba?
\v 10 Sa'annan sai kuzo ku tsaya a gabana a wannan gidan da ake kira da sunana kuma a ce, "An cece mu," saboda kawai kuyi dukkan waɗannan abubuwan banƙyama?
\v 11 Wannan gidan dake ɗauke da sunana, ya zama ƙogon mafasa a idanunku? Amma duba, Na gani - wannan furcin Yahweh ne.'
\s5
\v 12 Saboda haka ku je wuri na dake shiloh, inda na bar sunana ya zauna nan da farko, kuma duba abin da nayi da ita saboda muguntar mutanena Isra'ila.
\v 13 Don haka yanzu, ta dalilin yin waɗannan ayyuka - wannan furcin Yahweh ne - Nayi magana da ku lokuta zuwa lokuta, amma baku ji ba. Na kira ku amma baku amsa ba.
\v 14 Saboda haka, abin da nayi a Shilo, Zan kuma yi ma gidan nan da ake kira da sunana, gidan da kuka amince, wannan wuri da na baku da kakaninku.
\v 15 Gama zan aikar da ku waje daga gare ni kamar yadda na aikar da dukkan 'yan uwanku, dukkan zuriyar Ifraim.'
\s5
\v 16 Kai kuwa, Irmiya, kar ka yi wa mutanen nan addu'a, kuma kar ka ɗaga muryar makoki ko ka faɗi addu'a a madadinsu, kuma kada ka roƙe ni, gama ba zan ji ka ba.
\v 17 Baka ga abin da suke yi a biranen Yahuda da titunan Yerusalem ba?
\v 18 Yaran na tattara katako kuma Ubanin na kunna wuta! Matayen na ƙwaba ƙullu don yin gurasa domin sarauniyar sammai kuma suna zubo da hadayun ruwan inabi ga waɗansu alloli domin su tsokane ni.
\s5
\v 19 Da gaske tsokana ta suke yi? - wannan furcin Yahweh ne - ba kansu suke tsokana ba, har kunya ta kasance a kansu?
\v 20 Hakika Ubangiji Yahweh ya faɗi wannan, 'duba, fushina da hasalata zasu kwararo a wannan wurin, a kan mutum da dabba, a itatuwa na fili da 'ya'yan itace na ƙasa. Zata ƙone kuma ba za a ɓice ta ba.'
\s5
\v 21 Yahweh mai runduna, Allahn Isra'ila ya faɗi haka, 'Ku ƙara baye -bayen ƙonawa akan hadayarku da naman daga garesu.
\v 22 Gama sa'adda na fito da kakaninku daga ƙasar Masar, ban nemi komai daga gare su ba. Ban basu ko umurni a kan zancen baye - baye na ƙonawa da hadayu ba.
\v 23 Na basu wannan umurnin ne, "Ku saurare muryata, sai in zama Allahnku ku kuma ku zama mutanena. Saboda haka kuyi tafiya a hanyoyin da nake umurtar ku, don ya tafi maku dai-dai."
\s5
\v 24 Amma basu saurara ko su kula ba. Sun rayuwa ta bishewar shirye-shiryen taurin zuciyarsu, saboda haka suka koma baya, maimakon gaba.
\v 25 Tun daga ranar da kakaninku suka fito daga ƙasar Masar har zuwa wannan ranar, Na aike kowanne ɗaya daga cikin barorina da annabawa na a gare ku. Nayi naciya yayin da nake aikar da su.
\v 26 Amma basu saurare ni ba. Basu kula ba. Maimako, suka taurare wuyansu. Sun ma fi kakanninsu mugunta.'
\s5
\v 27 Saboda haka ka sanar da waɗannan maganganun gare su, amma ba zasu saurare ka ba. Faɗi waɗannan abubuwan a gare su, amma ba zasu ba ka amsa ba.
\v 28 Kace masu Wannan ce al'ummar da ba zata saurari muryar Yahweh Allahnta ba kuma bata karɓi horaswa ba. An hallaka an datse gaskiya daga bakunansu.
\s5
\v 29 Ku yanke gashinku ku kuma yi wa kanku aski, ku kuma zubar da gashin kanku. Ku raira waƙar jana'iza a kan buɗaɗɗun wurare. Gama Yahweh ya ƙi kuma ya watsar da wannan tsara a cikin hasalarsa.
\v 30 Gama 'ya'ya maza na Yahuda sun yi mugunta a idona - wannan furcin Yahweh ne - Sun sa abubuwan ƙyamarsu a cikin gidan da ake kira da sunana, domin su ƙazamtar dashi.
\s5
\v 31 Sa'annan suka gina babban wurin Tofet wanda ke cikin kwarin Ben Hinom. Sun yi haka don su ƙone 'ya'yansu maza da mata a wuta - abin da ban umurta ba, ko ya shiga zuciyata ba,
\v 32 Saboda haka duba, rana na zuwa - Wannan furcin Yahweh ne - yayin da ba za'a ƙara kiran wurin Tofet ko kwarin Ben Hinnom ba. Zai zama kwarin yanka; za a binne jikkuna a Tofet har sai babu wurin da ya rage.
\s5
\v 33 Gawawwakin waɗannan mutanen zasu zama abincin tsuntsayen sararin sama da dabbobin duniya, kuma babu wanda zai tsoratar da su.
\v 34 Zansa ƙarshen titunan Yahuda da na Yerusalem, ƙarar murna da ƙarar farin ciki, ƙarar ango da amarya, gama ƙasar zata zama lalatacciya."
\s5
\c 8
\cl Sura 8
\p
\v 1 Wannan ne furcin Yahweh - a lokacin nan zasu fitar da kasusuwan sarakunan Yahuda da ofisoshinsu, kasusuwan firistoci da annabawa, da kasusuwan mazaunan Yerusalem daga kaburbura.
\v 2 Sa'annan zasu shimfiɗa su a waje a hasken rana da wata da dukkan tauraron sararin sammai; waɗannan abubuwan na sararin sama da suka bi suka kuma bauta masu, da suka kuma bisu suka nemesu, kuma suka yi masu sujada. Baza a binne ko a tattara kasusuwan kuma ba, zasu zama kamar kashin dabba a fili.
\v 3 A dukkan ragowar wuraren da na kore su zuwa, zasu zaɓi mutuwa a maimakon rai domin kansu, dukkan waɗanda aka bar su daga wannan muguwar al'umma - Wannan ne furcin Yahweh mai runduna.
\s5
\v 4 Saboda haka ka faɗa masu, 'Yahweh yace haka: Akwai wanda ya faɗi kuma bai tashi ba? Akwai wanda ya ɓace da bai yi ƙoƙarin dawowa ba?
\v 5 Meyasa waɗannan mutanen, Yerusalem, suka juya baya da daɗewa cikin rashin bangaskiya? Sun rungume yaudara kuma sun ƙi su tuba.
\s5
\v 6 Na kula na kuma saurara, amma basu yi maganan dai - dai ba; ba wanda ke nadama da muguntarsa, ba wanda yace, "Mene ne na yi?" Dukkansu sun tafi wurin da suke so, kamar dokin da ke sauri zuwa fagen fama.
\v 7 Ko shamuwar sama ma ta san lokutan da suka dace; kurciyoyi kuma, da dila da zalɓe. Suna kiyaye lokacin ƙaurarsu, amma mutanena ba su san dokokin Yahweh ba.
\s5
\v 8 Yaya zaku ce, "Mu masu hikima ne, don umurnin Allah na tare da mu"? Hakika ku duba! alƙalamin ƙarya na magatakarda ya ƙirƙiro ƙarya.
\v 9 Mutane masu hikima zasu ji kunya. Zasu tsorata su kuma cafku. Duba! Sun ƙi maganar Yahweh, to mene ne amfanin hikimarsu?
\v 10 Saboda haka zan bada matayensu ga waɗansu, filayensu kuma ga waɗansu su mallaka, don daga mafi ƙanƙantarsu zuwa babbansu, kowannensu ya na haɗamar cin ƙazamar riba! Daga annabi zuwa firist, dukkansu suna aikata ha'inci.
\s5
\v 11 Sun warkar da raunin mutanena sama - sama, suna cewa, "Salama, Salama," sa'adda babu salama.
\v 12 basu ji kunya ba ne a sa'adda suke ayyukan banƙyama? Basu ji kunya ba; basu san yadda zasu kunyata ba! Saboda haka zasu faɗi cikin faɗaɗɗu; za a kawo su ƙasa sa'adda ake horar da su, inji Yahweh.
\v 13 Zan tuge su kakaf - wannan furcin Yahweh ne - baza a sami inabi a itacen inabi ba, ko 'ya'ya a itacen ɓaure ba, gama ganyen zai bushe, kuma abin da na basu zai ƙuɓuce masu.
\s5
\v 14 Me yasa muke zama a nan? kuzo mu taru; bari mu je garuruwa masu garu, kuma mu yi shiru a can cikin mutuwa. Gama Yahweh Allahnmu zai sa muyi tsit. Zai sa mu sha guba, tunda mun yi masa laifi.
\v 15 Muna fatan salama, amma babu wani abu mai kyau. Muna fatan lokacin warkarwa, amma duba, za a sami razana.
\s5
\v 16 Firjin dawakansa aka ji daga Dan. Dukkan duniya ta girgiza saboda haniniyar ingarmun ƙarfafan dawakansa. Gama zasu zo su cinye ƙasar da wadatarta, birni da masu zama cikinsa.
\v 17 Gama ku duba! Ina aikar da macizai a cikinku, kãsayen da ba zaku samu makarinsu ba. Zasu cije ku -Wannan furcin Yahweh ne."'
\s5
\v 18 Baƙincikina ba shi da ƙarshe, kuma zuciyata na ciwo.
\v 19 Duba!! Muryar ihun ɗiyar mutanena daga ƙasa mai nisa! Babu Yahweh a Sihiyona ne? Ko ba sarkin a cikinta? Me ya sa suke cakuna ta zuwa fushi da sassaƙaƙƙun sifofinsu da banzayen bãƙin gumakansu?
\s5
\v 20 Girbi ya ƙare, damuna kuma ta wuce. Amma ba a cece mu ba.
\v 21 Na raunana saboda raunin ɗiyar mutanena. Nayi makokin a kan abubuwan tsoron da suka same ta; Na tsorata.
\v 22 Babu wani magani a Giliyad ne? Babu mai warkarwa a can ne? Me zai hana warkarwar ɗiyar mutanena ta faru?
\s5
\c 9
\cl Sura 9
\p
\v 1 Da ma kaina zai ɓullo da ruwa, kuma idanuna su zama maɓuɓɓular hawaye! Gama ina tunanin yin kuka rana da dare domin waɗanda ke cikin ɗiyar mutanena da aka kashe.
\v 2 Da ma wani zai bani wuri domin matafiya a hamada su zauna, inda zan je in rabu da mutanena. Da ma zan iya barin su, tunda dukkansu mazinata ne, ƙungiyar maciya amana!
\v 3 Yahweh ya furta, "Sun tanƙwasa bakkunan ƙarerayinsu da na harsunansu, amma ba don wani amincinsu ne ya sa suka yi ƙarfi a duniya ba. Suna ta ci gaba daga aikin mugunta ɗaya bayan ɗaya. Basu san ni ba."
\s5
\v 4 Kowannen ku, yayi hankali da maƙwabcinsa kuma kada ya amince da kowanne irin ɗan'uwa. Gama kowanne ɗan'uwa hakika mayaudari ne, kuma kowanne maƙwabci mai kushe ne.
\v 5 Kowanne mutum yana yiwa maƙwabcisa ba a kuma ba ya faɗin gaskiya. Harsunansu na koyar da abubuwan ƙarya. Sun rafke daga aikata laifi.
\v 6 Zamanku na cikin ruɗu; a cikin yaudararsu sun ƙi su shaida ni - Wannan furcin Yahweh ne."
\s5
\v 7 Yahweh mai runduna ya faɗi haka, "Duba, Ina gab da tsabtace su in kuma gwada su, gama me zan iya yi, saboda abin da mutanena suka yi?
\v 8 Harsunansu kibiyoyi masu kaifi ne; suna faɗin abubuwan rashin aminci. Da bakunansu suna shaida salama ga maƙwabtansu, amma da zukatansu suna shirya masu maƙarƙashiya.
\v 9 Ba zan hukuntasu saboda waɗannan abubuwan ba - wannan shi ne furcin Yahweh - kuma ba zan rama wa al'umma irin wannan ba?
\s5
\v 10 Zan raira waƙar makoki da kururuwa saboda duwatsu, kuma za a raira wakar jana'iza domin wuraren kiwo. Gama an ƙone su don kar kowa ya wuce ta wurinsu. Ba zasu ji kukan wata dabba ba. Tsuntsaye da namomin daji sun gudu sun tafi.
\v 11 Saboda haka Zan maida Yerusalem tsibin kufai, maɓoyar diloli. Zan maida biranen Yahuda kufai inda ba mazauna."
\v 12 Wanne mutum ne ke da isasshiyar hikima ya gane wannan? Ga wane ne bakin Yahweh yayi magana, kuma zai faɗe shi? Me yasa ƙasar ta lalace an kuma hallakar da ita kamar hamadar da ba wanda zai iya wucewa ta cikinta?
\s5
\v 13 Sai Yahweh yace, "Saboda sun ƙi dokokin da na shirya a gare su, saboda basu saurari muryata ko su yi aiki da ita ba.
\v 14 Saboda sun yi tafiya da taurarrar zuciyarsu suka kuma bi Ba'aloli kamar yadda ubanninsu suka koya masu suyi.
\s5
\v 15 Saboda haka Yahweh mai runduna, Allah na Isra'ila, ya faɗi haka, 'Duba, Ina gab da sa mutanen nan suci abinci mai ɗaci da ruwan dafi.
\v 16 Sa'annan zan watsar dasu cikin al'ummar da basu sani ba da su da kakaninsu. Zan aikar da takobi ya bi su har sai na hallaka su kakaf."'
\s5
\v 17 Yahweh mai runduna ya faɗi haka, "Kuyi tunani a kan wannan: Ku kira masu waƙar jana'iza; bari su zo. Ku aiko a kira matayen da suka ƙware a makoki; bari suzo.
\v 18 Bari su yi sauri su raira waƙar makoki a kanmu, saboda idanuwanmu su iya zubar da hawaye kuma girar idanuwanmu ta malalo da ruwa.
\s5
\v 19 Gama an jin muryar kuka a Sihiyona, 'Yaya muke lalacewa. Mun ji kunya sosai, gama mun yi watsi da ƙasar tun da suka rurrushe gidajenmu.'
\v 20 Saboda haka ku mataye, ku ji maganar Yahweh; ku kula da saƙonni dake zuwa daga bakinsa. Sa'annan ku koyar da 'ya'yanku mata waƙar makoki, kuma kowacce mace maƙwabciya waƙar jana'iza.
\s5
\v 21 Gama mutuwa ta iso ta tagoginmu; ta shigo cikin fãdodinmu. Ta hallaka yara daga waje, da 'yan maza a dandalin biranen.
\v 22 Ka faɗi haka, 'Wannan furcin Yahweh ne - gawawwakin mutane zasu faɗo kamar kashin dabbobi a gonaki, kuma kamar dammunan masu girbi, kuma babu wanda zai tara su."'
\s5
\v 23 Yahweh ya faɗi haka, "Kada ka bar mutum mai hikima yayi taƙama da hikimarsa, ko jarumi a cikin ƙarfinsa. Kada ka bar mai arziki yayi taƙama da arzikinsa.
\v 24 Gama idan mutum yayi taƙama da wani abu, bari ya zama a wannan, cewa yana da fahimta kuma ya san ni. Gama ni ne Yahweh, wanda yake aiki da alƙawarin aminci da adalci da ayyukan adalci a duniya. Gama a cikin waɗannan ne nake murna - wannan furcin Yahweh ne."
\s5
\v 25 Duba, kwanaki na zuwa - wannan furcin Yahweh ne - sa'adda zan horar da dukkan masu kaciya a jiki kawai.
\v 26 Zan horar da Masar da Yahuda da Idom da mutanen Ammon da Mowab da dukkan mutanen da ke yanke gashin kansu suna sanƙo. Domin dukkan waɗannan al'umman marasa kaciya ne, kuma dukkan gidan Isra'ila suna da zuciya marar kaciya."
\s5
\c 10
\cl Sura 10
\p
\v 1 "Ku ji maganar da Yahweh yake sanar daku, ya gidan Isra'ila.
\v 2 Yahweh ya faɗi haka, 'Kar ku koyi hanyoyin al'ummai, kuma kada ku da mu da alamun cikin sammai, domin al'ummai na damuwa da waɗannan ne.
\s5
\v 3 Gama al'adun addinin mutanen nan na banza ne. Suna sare itace a cikin jeji, kuma gwanayen sassaƙa na sassaƙa katako.
\v 4 Sa'annan suka ƙayata shi da azurfa da zinari. Sun inganta ƙarfin shi da guduma da ƙusa don kada ya faɗo.
\v 5 abin da suka yi da hanuwansu yana kama da mutummutumi a gonar kukumba, saboda su, ma, ba zasu iya cewa komai ba, kuma ɗaukarsu ake yi domin ba zasu iya tafiya ba. Kada ku ji tsoronsu, gama ba zasu iya jawo mugunta, ko kuma su iya yin wani abu maiƙyau ba."'
\s5
\v 6 Babu wani kamarka, Yahweh. Kai mai girma ne, kuma sunanka na da girma cikin iko.
\v 7 Wane ne ba ya jin tsoron ka, sarkin al'ummai? Don ka cancanci haka, gama babu wani kamar ka a cikin dukkan mazaje masu hikima na al'ummai ko dukkan mulkokinsu masu martaba.
\s5
\v 8 Dukkansu iri ɗaya ne, su daƙiƙai da wawaye ne, almajiran gumaka da ba kome ba ne sai itace.
\v 9 Suna kawo sarafaffiyar azurfa daga Tarshish da zinariya daga Ufaz waɗanda ƙwararru suka yi, da hannuwan maƙera. Tufafinsu na mulifi da shunayya ne. Gwanayensu ne suka yi dukkan waɗannan abubuwan.
\v 10 Amma Yahweh shi ne Allah na gaskiye. Shi ne Allah mai rai da madawamin sarki. Fushinsa yakan girgiza duniya, kuma al'ummai ba zasu jure fushinsa ba.
\s5
\v 11 Zaka yi magana da su kamar haka, "Allolin da basu yi sammai da duniya ba zasu lalace daga duniya kuma daga ƙarƙashin waɗannan sammai."
\v 12 Amma shi ne wanda yayi duniya ta ikonsa, ya kuma kafa ta ta wurin hikimarsa, kuma ta fahimtarsa ya miƙar da sammai.
\v 13 Muryarsa ta yi ƙugin ruwa a sammai, ya kuma kawo hayaƙi daga kurewar duniya. Yakan yi walƙiyoyi domin ruwan sama ya kuma aikar da iska daga taskokinsa.
\s5
\v 14 Kowanne mutum ya zama jahili da marar ilimi. Kowanne maƙerin zinariya zai sha kunya ta dalilin gumakansa. Gama ƙerarrun siffofinsu ƙarya ne; Babu rai a cikinsu.
\v 15 Basu da amfani, aikin masu ba'a; zasu lalace a lokacin horonsu.
\v 16 Amma Allah, madogarar Yakubu, ba haka yake ba, gama shi ne yayi dukkan abubuwa. Isra'ila kabilar gãdonsa ne; Yahweh mai runduna ne sunansa.
\s5
\v 17 Ku tattara kayayyakinku ku bar ƙasar, ku mutanen dake zaune a wuraren dake kewaye da yaƙi.
\v 18 Gama Yahweh ya faɗi haka, "Duba, Ina gab da jefar da mazaunan ƙasar waje a wannan lokacin. Zan kawo masu ƙunci, kuma zasu kuwa same shi a hakan."
\s5
\v 19 Kaito na! Saboda karyayyun ƙasusuwana, raunina ya sami lahani. Saboda haka na ce, "Tabbas wannan azaba ce, amma zan jure."
\v 20 An lalatar da rumfata, kuma dukkan igiyoyin rumfata an yanke su biyu. An ɗauke 'ya'yana daga gare ni, saboda haka basu nan. Babu wanda zai yi shimfiɗa a rumfata ko mai ɗaga labulolin rumfata.
\s5
\v 21 Gama makiyayan wawaye ne kuma ba sa biɗar Yahweh; saboda haka basu wadata ba, kuma dukkan garkensu an warwatsar.
\v 22 Rohotonin labarai sun iso, "Duba! Tana zuwa, babbar girgizar ƙasa tana zuwa daga ƙasar arewaci ta sa biranen Yahuda su zama kufai, maɓuya domin diloli."
\s5
\v 23 Na sani, Yahweh, cewa hanyar mutun ba daga kansa take fitowa ba. Babu mutumin dake jagorar tafiyarsa da takawar kansa.
\v 24 Ka tsauta mani, Yahweh, da adalci, ba a cikin fushinka ba domin kada ka hallaka ni.
\v 25 Ka kwarara hasalarka ga al'umman da basu san ka ba, da iyalan da basu kira bisa sunanka. Gama sun cinye Yakubu sun kuma haɗiye shi saboda su hallakar da shi kakaf su kuma rushe mazauninsa.
\s5
\c 11
\cl Sura 11
\p
\v 1 Maganar da tazo ga Irmiya daga Yahweh, cewa,
\v 2 "Ka saurari maganganun wannan alƙawari, kuma ka furta su ga kowanne mutum a Yahuda da kuma ga mazaunan Yerusalem
\s5
\v 3 Ka ce masu, 'Yahweh, Allah na Isra'ila ya faɗi haka: La'ananne ne duk wanda ba ya sauraron maganganun wannan alƙawari.
\v 4 Wannan shi nealƙawarin da na umurci kakaninku su cika a ranar dana fito da su daga ƙasar Masar, Daga tanderun sarrafa ƙarfe. Nace, "Ku saurari muryata ku kuma yi dukkan waɗannan abubuwan kamar yadda na umurce ku, gama zaku zama mutane na ni kuma In zama Allahnku."
\v 5 Kuyi mani biyayya saboda in cika rantsuwar da na yi ma kakaninku, rantsuwar cewa zan ba su ƙasar dake kwararo da madara da zuma, inda kuke zama a yau." Sa'annan Ni Irmiya, na amsa nace, "I, Yahweh!"
\s5
\v 6 Yahweh yace mani, "Kayi shelar waɗannan abubuwan a cikin biranen Yahuda da titunan Yerusalem. Kace, Ku saurari maganganun wannan alƙawari ku kuma aikata su.
\v 7 Gama na yi ta bayar da tsarkakan umarnai na ga kakaninku daga ranar da na fitar dasu daga ƙasar Masar har zuwa wannan lokacin, nayi ta faɗakar da su cewa, "Ku saurari muryata."
\v 8 Amma basu saurara ko su kula ba. Kowanne mutum yana tafiya a cikin taurarriyar muguntar zuciyarsa. Saboda haka na kawo dukkan la'anonin cikin wannan alƙawarin da na umurta su zo gare su. Amma mutanen basu yi biyayya ba duk da haka."
\s5
\v 9 Biye da haka Yahweh yace mani, "An gano tawaye a cikin mutanen Yahuda da mazunan Yerusalem.
\v 10 Sun juya zuwa zunuban kakaninsu na farko, waɗanda sun ƙi su saurari maganata, maimakon haka suka bi waɗansu alloli suka bauta masu. Gidan Yahuda da na Isra'ila sun karya alƙawarina da na kafa da kakaninsu.
\s5
\v 11 Saboda haka Yahweh ya faɗi haka, 'Duba, Ina gab da kawo bala'i a kansu, bala'in da ba zasu iya kuɓutar da kansu ba. Sa'annan zasu yi kira gare ni, amma ba zan saurare su ba.
\v 12 Biranen Yahuda da mazaunan Yerusalem zasu je su yi kira ga allolin da suka bada baye-baye gare su, amm hakika ba zasu sami ceto ta wurinsu a lokacin bala'insu ba.
\v 13 Gama ke Yahuda, allolinki sun ƙaru dai - dai da yawan biranenki. Kin yi yawan bagadanki masu ban kunya a Yerusalem, da turaren bagadai domin Ba'al, dai - dai da yawan titunanta.
\s5
\v 14 Saboda haka kai kanka, Irmiya, kada kayi wa mutanen nan addu'a. Kada kayi kuka ko addu'a a madadin su. Gama ba zan saurara ba sa'adda suka kira ni a lokacin bala'insu.
\v 15 Me ya sa ƙaunatacciyata, wadda take da mugayen ƙudurori da yawa, take ta aikata su a gidana? Naman hadayunki ba zasu iya taimakonki ba. Kina farinciki saboda mugayen ayyukanki.
\v 16 A baya Yahweh ya kira ki itacen zaitun mai duhuwa, kyakyawa mai 'ya'yan da ake so. Amma zai cinna wuta a kanta wadda zata yi ƙara kamar iskar guguwa; rassanta zasu kakkarye.
\s5
\v 17 Gama Yahweh mai runduna, shi wanda ya dasa ku, ya furta bala'i gãba da ku saboda mugayen ayyukan da gidan Isra'ila da na Yahuda suka yi - sun sa na husata ta wurin yiwa Ba'al baye-baye."'
\s5
\v 18 Yahweh ya sa na san waɗannan abubuwan, saboda haka na sansu. Kai, ya Yahweh, ka sa na ga ayyukansu.
\v 19 Ina kama da ɗan rago mai sauƙin kai wanda ake ja zuwa mayanka. Ba ni da sanin cewa sun yi maƙarƙashiya gãba da ni, "Bari mu lalatar da itacen da 'ya'yansa! Bari mu datse shi daga ƙasar masu rai saboda kada a sake tunawa da sunansa."
\v 20 Duk da haka Yahweh mai runduna Mai yin shari'ar adalci ne wanda yake bincike zuciya da tunani. Zan shaidi sakayyarka game da su, gama na danƙa maganata a gare ka.
\s5
\v 21 Saboda haka Yahweh ya faɗi haka game da mutanen Anatot dake biɗar ranka, "Suka ce, 'Kada ka kuskura kayi annabci da sunan Yahweh, ko ka mutu ta hannun mu.'
\v 22 Domin haka Yahweh mai runduna ya faɗi haka, 'Duba, Ina gab da hukunta su. Samarinsu masu ƙarfi zasu mutu ta takobi. 'Ya'yansu maza da mata zasu mutu saboda yunwa.
\v 23 Babu waninsu wanda za a bari, domin Ina tahowa da masifa gãba da mutanen Anatot, a shekarar hukuncinsu."'
\s5
\c 12
\cl Sura 12
\p
\v 1 Kai adali ne, Yahweh, duk lokacin dana kawo rashin jituwata a gare ka. Hakika zan faɗa maka dalilin ƙarata: Me yasa hanyoyin mugaye suke yin nasara? Dukkan marasa bangaskiya suna cin nasara?
\v 2 Ka dasa su kuma suka yi saiwa. Sun ci gaba da bada 'ya'ya. Kana kusa da su a cikin bakunansu, amma nesa daga zuciyarsu.
\s5
\v 3 Duk da haka kai, Yahweh, ka san ni. Kana gani na kuma kana gwada zuciyata gare ka. Ka ɗauke su kamar tunkiyar da ake kaiwa mayanka, ka ware su domin ranar yanka!
\v 4 Yaushe ƙasar zata ci gaba da bushewa, kuma tsire-tsiren kwace gona ke yaushi saboda muguntar mazaunanta? Dabbobi da tsuntsaye an ɗauke. Hakika, mutanen sun ce, "Allah ba zai ga abin da zai faru da mu ba."
\s5
\v 5 Yahweh yace, "hakika, idan kai, Irmiya, kayi tsere da sojojin ƙafa suka kuma gajiyar da kai, to yaya zaka yi gasa gãba da dawakai? Idan ka faɗi a lafiyayyar karkara, ƙaƙa zaka yi a kurmin Yodan.
\v 6 Gama ko 'yan'uwanka da gidan mahaifinka sun basheka sun kuma ƙi ka ƙiri-ƙiri. kada ka amince da su, ko sun faɗi maka abubuwa masu daɗi.
\s5
\v 7 Na yashe da gidana; Na rabu da gãdona. Na bada ƙaunatacciyata cikin hannuwan maƙiyanta.
\v 8 Abar gãdona ta zamar mani kamar zaki a kurmi; ta kafa kanta gãba da ni da muryarta, saboda na ƙi jininta.
\v 9 Ashe mallakar da nake ji da ita ta zama dabbare-dabbaren tsuntsu, wacce manyan tsuntsaye ke farauta gãba da ita a kewaye? Tafi ka tattaro dukkan namomin jeji ka kuma kawo su su lanƙwameta.
\s5
\v 10 Makiyaya da yawa sun lalatar mani da garkar inabi. Sun tattake kan dukkan nawa rabon ƙasar; sun maida kyakkyawan rabona hamada da kufai.
\v 11 Sun maida ita ba komai. Ina makoki domin ta; ba ta da komai. Dukkan ƙasar an maida ita kango, gama ba wanda ya ɗauke abin a zuciya.
\s5
\v 12 Masu hallakarwa sun zo gãba da dukkan tsaunukan cikin hamada, gama takobin Yahweh tana hallakarwa daga wannan iyakar ƙasa zuwa waccan. Babu kwanciyar hankali a ƙasar domin kowacce hallita mai rai.
\v 13 Sun shuka alkama sun girbi ƙayayuwa. Sun gaji da aiki amma basu samu ribar komai ba. Saboda haka ku ji kunyar ribarku saboda fushin Yahweh."
\s5
\v 14 Yahweh ya faɗi haka a kan dukkan maƙwabtana, mugayen da suka taɓa mallakar dana sa mutanena Isra'ila suka gada, "Duba, Nine wanda ke gab da tumɓuke su daga ƙasarsu, kuma zan jawo gidan Yahuda daga cikinsu.
\v 15 Sa'annan bayan na tumɓuke waɗancan al'ummai, zai zamana zan sake jin tausayinsu in kuma komo da su; Zan komar da su - kowanne mutum ga gãdonsa da ƙasarsa.
\s5
\v 16 Zai kuwa zamana idan waɗancan al'umman zasu himmantu su koyi hanyoyin mutanena, su yi rantsuwa da sunana 'In dai Yahweh na raye' kamar dai yadda suka koya ma mutanena suyi rantsuwa da Ba'al, to su ma zasu ginu a cikin mutanena.
\v 17 Amma idan ba wanda ya saurara, sai in tumɓuke wannan al'ummar. Hakika za a tumɓuke ta a kuma hallakata - wannan furcin Yahweh ne."
\s5
\c 13
\cl Sura 13
\p
\v 1 Yahweh yace da ni haka, "Jeka ka sayi lilin na yin ɗamara kuma ka sa shi kewaye da kwankwasonka, amma kar ka sa shi a ruwa da farko"
\v 2 Saboda haka na sayi ɗamarar kamar yadda Yahweh ya jagorance ni, sai na rataya kewaye da kwankwasona.
\v 3 Daga nan maganar Yahweh ta zo a gare ni karo na biyu, cewa,
\v 4 "Ka ɗauki ɗamarar da ka saya wadda ke kewaye da kwankwasonka, ka tashi ka tafi yanzu zuwa Ferat. Ka ɓoye ta nan a ƙogon tsaguwar dutse."
\v 5 Sai na tafi na ɓoye ta a Ferat, kamar yadda Yahweh ya umarce ni.
\s5
\v 6 Bayan kwanaki da yawa, Yahweh yace mani, "Tashi ka koma Ferat. Ka ɗauki ɗamarar da na ce ka ɗauka daga wurin da ka ɓoye."
\v 7 Sai na koma Ferat na kuma haƙo ɗamarar a inda na ɓoye ta, kuma duba, ta lalace dukka kuma babu amfani.
\s5
\v 8 Sai maganar Yahweh tazo gare ni, cewa,
\v 9 Yahweh ya faɗi haka: Ta dai wannan hanyar zan hallakar da gagarumin kumbura kan Yahuda a Yerusalem.
\v 10 Waɗannan miyagun mutanen da suka ƙi su raurari maganata, waɗanda ke tafiya a cikin taurin zuciyarsu, waɗanda ke bin bayan waɗansu alloli suyi masu sujada suka kuma russuna masu - zasu zama kamar wannan ɗamarar da ba ta da amfani.
\v 11 gama kamar yadda ɗamarar nan ta ke manne wa ƙwanƙwason wani, haka na maida gidan Isra'ila da dukkan gidan Yahuda su manne mani - wannan furcin Yahweh ne - su zama mutanena, su kawo mani shahara, a ko'ina da yabo, da girmamawa. Amma ba su saurare ni ba.
\s5
\v 12 Saboda haka, dole ka faɗa masu wannan magana, 'Yahweh, Allah na Isra'ila, yace: Za a cika kowanne gora da ruwan inabi.' Zasu ce da kai, "Ashe bamu sani hakika cewa kowanne gora za a cika shi da ruwa ba?'
\v 13 Sai kace da su, Yahweh ya faɗi haka: Duba, Ina gab da cika dukkan mazaunan wannan ƙasa da buguwa, sarakunan dake zaune a kursiyin Dauda da firistoci da annabawa da mazaunan Yerusalem.
\v 14 Sa'annan zan sa su kara da junansu, iyaye maza da 'ya'yansu tare - wannan shi ne furcin Yahweh - Ba zan ji tausayinsu ko juyayinsu ba, kuma ba zan kiyaye su daga hallaka ba."'
\s5
\v 15 Ku saurara ku kuma natsu. Kada ku kumbura kai, gama Yahweh yayi magana.
\v 16 Ku girmama Yahweh Allahnku kafin ya kawo duhu, kafin kuma yasa ƙafafunku su yi tuntuɓe akan duwatsu da hasken asuba. Gama kuna begen haske, amma zai maishe da wurin duhu baƙƙi ƙirin, zuwa baƙin girgije.
\v 17 Saboda haka idan ba zaku saurara ba, zan yi kuka ni kaɗai saboda kumbura kanku. idanuwa na zasu yi kuka ƙwarai kuma su zub da hawaye, domin an ɗauke garken Yahweh zuwa bauta.
\s5
\v 18 Kace da sarki da kuma mahaifiyar sarki, 'Ku sauko daga bisa kursiyoyinku, gama rawwunanku masu daraja sun faɗi daga kawunanku.'
\v 19 Biranen cikin Negeb za a rufe su, kuma babu wanda zai buɗe su. Za a ɗauke Yahuda zuwa bauta, dukkan ƙasar zuwa bauta.
\s5
\v 20 Ku ta da idanuwanku ku ga waɗanda ke tahowa daga arewa. Ina garken da ya baku, garken dake kyakkyawa a gare ku?
\v 21 Me zaku ce sa'adda Allah ya naɗa a kanku shugabanin da kuka koyar su zama muhimman aminanku? Ashe ba waɗannan ba ne mafarin zafin azabai da zasu mamaye ku kamar mace mai naƙuda?
\s5
\v 22 Sa'annan zaku iya cewa a zuciyarku, 'Me yasa waɗannan abubuwan suke faruwa da ni?' Zai zama domin yawan zunubanku ne shi yasa an ɗaga ɗantofinku kuma an wulaƙanta ku.
\v 23 Mutanen Kush zasu iya sake launin fatarsu, ko kuwa damisa zata iya sake dabbare-dabbarenta? Idan haka ne, to ku kanku, duk da dai kun saba da yin mugunta, zaku iya yin nagarta.
\v 24 Saboda haka zan watsar da su kamar ƙaiƙayi da kan lalace a iskar hamada.
\s5
\v 25 Wannan shi ne abin da na baku, rabon da nayi doka dominku - wannan Furcin Yahweh ne - saboda kun mance da ni kun dogara ga ruɗu.
\v 26 Saboda haka kuma Ni kaina zan kware ɗantofinku, kuma za a ga tsiraicinku.
\v 27 Na ga zinarki da haniniyarki, da muguntar karuwancinku akan tuddai da cikin gonaki, na kuma ga waɗannan abubuwa masu ban ƙyama! kaiton ki, Yerusalem! Har tsawon wanne lokaci ne zaki sake wankuwa kuma?"
\s5
\c 14
\cl Sura 14
\p
\v 1 Wannan ita ce maganar Yahweh da tazo wurin Irmiya game da fari,
\v 2 "Bari Yahuda ta yi makoki; bari ƙofofinta su lalace. Suna kuka domin ƙasar; kukansu domin Yerusalem ta hau sama.
\v 3 Manyansu sun aiki barorinsu su ɗebo ruwa. Da suka je maɓuɓɓuga, sun tarar ba ruwa. Sai dukkansu suka koma ba tare da samun kome ba, sun lulluɓe kawunansu don kunya da ƙasƙanci.
\s5
\v 4 Domin wannan ƙasar ta tsage, domin babu ruwan sama a ƙasar. Manoma sun sha kunya har sun lulluɓe kawunansu.
\v 5 Ko dama barewa ma a saura ta kan gudu ta bar 'ya'yanta sabuwar haihuwa, don ba ciyawa.
\v 6 Jakunan jeji sukan tsaya akan huntun sararinsu na haki kamar diloli. Idanuwansu ba sa gani, domin ba abinci."
\s5
\v 7 Ko da yake zunubanmu suna shaida gãba da mu, Yahweh, kayi taimako saboda sunanka. Gama rashin amincinmu yayi yawa; mun yi maka zunubi.
\v 8 Kai ne begen Isra'ila, mai cetonta a lokacin wahala, ƙaƙa zaka zama kamar baƙo a ƙasar, kamar mai tafiyar yawon buɗe ido wanda ya kwanta a gefen hanya don ya kwana ɗaya?
\v 9 Ƙaƙa zaka zama kamar jarumin da ya kãsa iya ceton kowa? Duk da haka kana nan a tsakiyarmu, Yahweh, da sunanka ake kiranmu. Kada ka barmu!
\s5
\v 10 Yahweh yace wannan akan waɗannan mutanen: "Tun da suna ƙaunar yawace-yawace, basu iya daina wa ba."
\v 11 Yahweh ba ya jin daɗinsu. Yanzu zai tuna da laifofinsu ya kuma hukunta zunubansu. Yahweh yace mani, "Kada kayi addu'a domin lafiyar waɗannan mutane.
\v 12 Ko da sun yi azumi, ba zan saurare kukansu ba, kuma ko da sun mika hadaya ta ƙonawa da hadayar abinci, ba zan karɓe su ba. Amma zan kawo ƙarshensu da takobi, yunwa, da annoba."
\s5
\v 13 Sai na ce, "Ah, Ubangiji Yahweh! Duba!! Annabawa suna gayawa mutane, 'Ba zaku ga takobi ba; babu yunwa domin ku, amma zan baku dawwamammen tsaro a wannan wuri.'"
\v 14 Yahweh yace mani, "Annabawa suna annabcin ƙarya da sunana. Ban aike su ba, ko kuwa in basu wani umarni ko kuma in yi magana da su. Amma ƙarairayi da wahayin ƙarya ne, ƙaryar duba da suke yi marar amfani suna fitowa daga tunaninsu waɗanda suke annabcin ƙarya ne."
\s5
\v 15 Saboda haka ga abin da Yahweh yace, "Akan annabawan da suke yin annabci da sunana amma ba ni ne na aikesu ba - waɗanda suka ce baza a yi takobi ko yunwa ba a ƙasar. Waɗannan annabawa zasu hallaka da takobi da yunwa.
\v 16 Kuma mutanen da suka yi wa annabci za a jefar dasu waje cikin titunan Yerusalem domin yunwa da takobi, har ma babu wanda zai binne su - su, da matayensu da 'ya'yansu maza da mata - don zan sa muguntarsu a kansu.
\s5
\v 17 Faɗa masu wannan magana: 'Bari idanuna suyi ta zub da hawaye, dare da rana. Kada su daina, saboda akwai babbar aukawar budurwa 'yar mutane na -babban rauni marar warkewa.
\v 18 Idan na tafi cikin saura, akwai su da yawa da aka kashe da takobi! Idan kuma na shiga cikin birni, akwai cututtukan da yunwa ta kawo. Gama annabi da firist yawace-yawace suke ta yi a ƙasar, kuma basu sani ba.'"
\s5
\v 19 Ka ƙi Yahuda kenan dungum? Kana ƙin Sihiyona ne? Me yasa zaka azabtar da mu sa'adda babu warkarwa domin mu? Muna begen salama, amma ba wani abin kirki - don lokacin warkewa, amma ku gani, sai dai tsoro kaɗai.
\v 20 Mun yarda, Yahweh, laifofinmu da muguntarmu da ta kakanninmu, gama mun yi maka zunubi.
\s5
\v 21 Kada ka ƙi mu! Saboda darajar sunanka, kada kuma ka ƙasƙantar da darajar kursiyinka. Ka tuna kada kuma ka karya alƙawarinka da mu.
\v 22 A cikin gumakan al'ummai marasa amfani akwai mai iya sa sammai su bada ruwa? Ba kai kaɗai ba ne, Yahweh Allahnmu, wanda yayi wannan? Mun sa bege a gare ka, gama kai ne mai yin waɗannan abubuwa dukka.
\s5
\c 15
\cl Sura 15
\p
\v 1 Sai Yahweh yace da ni, "Ko da Musa ko Sama'ila zasu tsaya a gabana, duk da haka ba zan nuna wa waɗannan mutanen tagomashi ba. Ka kore su daga gabana, don su yi tafiyarsu.
\v 2 Zaya zama sa'ad da suka ce da kai, 'Ina zamu tafi?' Sai ka faɗa masu, Yahweh ya faɗi wannan: Waɗanda an ƙaddara su mutu su tafi ga mutuwa; waɗanda suke na takobi su tafi ga takobi. Waɗanda suke na yunwa su tafi ga yunwa; kuma waɗanda suke na bauta su tafi ga bauta.'
\s5
\v 3 Zansa su kasance kashi huɗu - wannan furcin Yahweh ne - takobi na kisan wasu ne, karnuka su yayyaga wasu, tsutsaye sararin sama da dabbobin duniya don su cinye su kuma hallakar da wasu.
\v 4 Zan kuma sa su zama abin banƙyama ga dukkan mulkokin duniya, saboda abin da Manassa ɗan Hezekiya, sarkin Yahuda, ya aikata a Yerusalem.
\s5
\v 5 Amma wa zai ji tausayinki, Yerusalem? Wa zai yi baƙinciki domin ki?
\v 6 Kun yashe ni - wannan furcin Yahweh ne - kun koma baya daga gare ni. Saboda haka zan buge ku da hannuna in kuma hallaka ku. Ni na gaji da nuna maku jinƙai.
\v 7 Saboda haka zan sheƙe su da abin shiƙa a ƙofofin garuruwan ƙasar. Zansa su makoki. Zan hallaka mutanena tun da ba zasu juyo daga mugayen hanyoyinsu ba.
\s5
\v 8 Zan yawaita gwaurayensu fiye da yashi a bakin teku. Game da uwayen samari zan aika da hallakarwa da tsakar rana. Zan sa azaba da razana su auko masu farat ɗaya.
\v 9 Uwar da ta haifi 'ya'ya baƙwai zata yi yaushi ta suma. Faɗuwar ranarta zata zo tun da rana. Zata ji kunya da wulaƙanci, don zan bada waɗanda suka ragu ga takobi a gaban abokan gãbarsu -wannan furcin Yahweh ne."
\s5
\v 10 Kaito na, mahaifiyata! Domin ke kika haife ni, ni ne mutum mai jayayya da gardama cikin dukkan ƙasar. Ban bada rance ba, ko wani ya bani rance, duk da haka dukkansu suna zagina.
\v 11 Yahweh yace: "Ba zan ceto ka domin alheri ba? Babu shakka zansa abokan gãbarka su roƙi taimako a lokacin bala'i da masifa.
\v 12 Wani zai iya karya ƙarfe? Musamman ƙarfe daga arewa wanda aka haɗa da tagulla?
\s5
\v 13 Zan bada wadatarku da dukiyarku ganima kyauta ga abokan gãbarku. Zan yi wannan saboda dukkan zunubanku da kuka aikata a dukkan iyakarku.
\v 14 Zansa ku bautawa abokan gãbarku a cikin ƙasar da ba ku sani ba, gama wuta zata kama, zata kunnu a cikin fushina gãba da ku."
\s5
\v 15 Yahweh, ka sani! Ka tuna da ni ka kuma taimake ni. Ka kawo mani fansa ka kuma sãka wa waɗanda suke tsananta mani. Kai mai haƙuri ne, amma kada ka bar su su tafi da ni; ka sani na sha wahala saboda kai.
\v 16 An sami magangaanunka, na kuwa cinyesu. Maganganunka sun zamar mani abin murna da farincikin zuciyata, gama ana kira na da sunanka, Yahweh, Allah mai runduna.
\s5
\v 17 Ban zauna cikin ƙungiyar waɗanda suke annashuwa ko murna ba. Na zauna ni kaɗai saboda hannunka mai iko, gama ka sa na cika da haushi.
\v 18 Me yasa azabata ta ƙi ƙarewa kuma raunukana ba sa warkewa? Zaka yaudare ni kamar ruwaye, ruwaye masu ƙafewa?
\s5
\v 19 Domin wannan ga abin da Yahweh yace, "Idan ka tuba, Irmiya, sai in komo da kai, sa'annan zaka tsaya a gabana ka kuma bauta mani. Gama idan ka ware abubuwan dake banza daga abubuwa masu daraja, zaka zama kamar bakina. Sai mutanen su dawo wurinka, amma kai ba zaka koma wurinsu ba.
\v 20 Zan maishe ka kamar garun tagulla da ba za a iya hudawa ba ga waɗannan mutane, zasu yi yaƙi da kai. Amma ba zasu yi nasara a kanka ba, gama ina tare da kai don in cece ka kuma in kuɓutar da kai -wannan furcin Yahweh ne -
\v 21 gama zan kuɓutar da kai daga hannun mugaye kuma zan fanshe ka daga hannun marasa tausayi."
\s5
\c 16
\cl Sura 16
\p
\v 1 Sai maganar Yahweh tazo gare ni, cewa,
\v 2 "Kada ka auri mata domin kanka, kuma kada ka sami 'ya'ya maza da 'ya'ya mata domin kanka a wannan wuri.
\v 3 Gama Yahweh yace waɗannan 'ya'ya maza da mata waɗanda za a haifa a wannan wuri, da kuma iyayensu mata waɗanda zasu haife su, da iyayensu maza da zasu sa a haife su a wannan ƙasa,
\v 4 'Zasu mutu da muguwar cuta. Baza a yi makoki ko a bisne su ba. Zasu zama kamar juji a ƙasa. Gama ƙarshe zai kasance ta wurin takobi da yunwa, kuma gawarwakinsu zasu zama abincin tsuntsayen sararin sama da nanamomin ƙasar.'
\s5
\v 5 Gama maganar Yahweh ta zo gare ni, cewa, 'Kada ka shiga gidan da ake makoki. Kada kayi makoki ko ka nuna damuwa dominsu, gama na ɗauke salamata daga waɗannan mutanen, da ƙaunata da jinƙaina - wannan furcin Yahweh ne.
\v 6 Babba da yaro zasu mutu a wannan ƙasa. Baza a bizne su ba kuma ba wanda zai yi makoki domin su ko su tsattsage jikinsu ko su aske kansu ƙwal domin su.
\s5
\v 7 Tilas kada wani ya raba abinci a cikin makoki don ya ta'azantar da su saboda matattu, tilas kuma kada wani ya bada ƙoƙon ta'aziya ga mahaifinsa ko mahaifiyarsa don ya ta'azantar da su.
\v 8 Tilas kada kuma ka shiga gidan da ake biki ka zauna don ka ci ka sha tare da su.'
\v 9 Gama Yahweh mai runduna, Allah na Isra'ila, ya faɗi wannan, 'Duba, a gaban idanunka, da zamaninka a kuma wannan wuri, na kusa kawo ƙarshen muryar murna da muryar farinciki, data ango data amarya.'
\s5
\v 10 Zai kasance idan ka bayyana dukkan waɗannan maganganu ga waɗannan mutane, zasu kuwa ce maka, 'Me yasa Yahweh ya furta dukkan wannan babbar masifa a kanmu? Mene ne laifinmu da zunubin da muka yi wa Yahweh Allahnmu?'
\v 11 Sai kace da su, 'Domin kakanninku sun rabu da ni - wannan furcin Yahweh ne - sun bi wasu alloli har sun bauta masu sun kuma sunkuya sun yi masu sujada. Sun rabu da ni, kuma basu kiyayye dokokina ba.
\s5
\v 12 Gama ku kuma kun kawo mugunta fiye da ta kakanninku, ku gani, kowannenku yana tafiyar taurinkai da mugun nufi a zuciyarsa; ba wanda yake saurare na.
\v 13 Saboda haka zan jefar da ku daga wannan ƙasa zuwa wata ƙasa wadda ku ko kakanninku baku sani ba, a can zaku bauta wa wasu alloli dare da rana, gama ba zan nuna maku wani tagomashi ba.'
\s5
\v 14 Saboda haka, duba, kwanaki suna zuwa - wannan furcin Yahweh ne - da baza a ƙara cewa, 'Na rantse da ran Yahweh, wanda ya fito da mutanen Isra'ila daga ƙasar Masar ba.'
\v 15 amma, 'Na rantse da ran Yahweh, wanda ya fito da mutanen Isra'ila daga ƙasar arewa kuma daga ƙasashen da ya warwatsa su.' Gama zan komo da su zuwa ƙasar da na ba kakanninsu.
\s5
\v 16 Duba!! Zan aika domin masunta da yawa - wannan furcin Yahweh ne - zasu kuwa kama mutane su fitar waje. Bayan wannan zan aika domin mafarauta da yawa don su farauto su daga dukkan tsaunuka da tuddai, da cikin kogunan dutse.
\v 17 Gama idona yana dukkan hanyoyinsu; ba a ɓoye suke ba a gare ni. Muguntarsu kuma ba a ɓoye take ba daga idanuwana.
\v 18 Zan fara saka masu ruɓi biyu domin laifinsu da zunubi domin sun ƙazantar da ƙasata da ƙazantattun siffofin gunkinsu, kuma domin sun cika gãdona da gumakansu na banƙyama."
\s5
\v 19 Yahweh, kai ne kagarata da mafakata, wurin tsarona a ranar wahala. Al'ummai zasu zo gunka daga ƙurewar duniya za a kuma ce, "Babu shakka kakanninmu sun gãji yaudara. Su fanko ne; babu riba a cikinsu.
\v 20 Mutane zasu iya yiwa kansu alloli?' amma su ba alloli ba ne."
\v 21 Saboda haka duba!! Zansa su sani a wannan lokacin, zansa su san hannuna da ikona, don haka zasu sani cewa sunana Yahweh ne.
\s5
\c 17
\cl Sura 17
\p
\v 1 "Zunubin Yahuda a rubuce yake da alƙalamin ƙarfe mai bakin lu'u-lu'u. An zana shi a allon zuciyarsu da ƙahon bagadinku.
\v 2 Har 'ya'yansu masu na tunawa da bagadansu da sandunan Ashtarot ɗinsu a gindin itatuwa shimfiɗe akan kuma tuddai masu tsayi.
\s5
\v 3 Dutsena a buɗaɗɗiyar ƙasar, dukiyarku da dukkan wadatarku zan bada su ganima, tare da wuraren tsaunukanku, saboda zunubin da kuka aikata a dukkan ƙasashen.
\v 4 Zaku rasa gãdon da na baku. Zansa ku bautawa abokan gãbarku a ƙasar da baku sani ba, gama kun kunna wuta cikin fushina, wadda zata yi ta ci har abada."
\s5
\v 5 Yahweh yace, "Mutumin dake dogara ga ɗan adam la'ananne ne; wanda ya maida jiki ƙarfinsa wanda ya juya zuciyarsa daga Yahweh.
\v 6 Gama zai zama kamar ƙaramin jeji a Hamada ba kuma zai ga wani abu mai kyau yana zuwa ba. Zai zauna a wurare masu duwatsu a cikin daji, ƙeƙasarshiyar ƙasar da ba mazauna.
\s5
\v 7 Amma mai albarka ne mutumin da yake dogara ga Yahweh, gama Yahweh ne dalilin madogararsa.
\v 8 Domin yana kamar itacen da aka dasa gefen rafi, wanda saiwoyinsa suka bazu zuwa cikin rafin. Ba zai ji tsoron zafi ba a duk lokacin da yazo, domin kullum ganyensa kore ne. Ba zai da mu da shekarar fari ba, ba kuma zai fasa yin 'ya'ya ba.
\s5
\v 9 Zuciya ta fi kome rikici. Cuta gare ta matuka; wa zai iya gane ta?
\v 10 Ni ne Yahweh, wanda yake binciken tunani, wanda yake gwada zukata. Ina ba kowane mutum gwargwadon al'amuransa, da kuma gwargwadon ayyukansa.
\v 11 Makwarwar da ta ƙwanta kan ƙwan da ba ita ta saka ba. Mutum zai iya zama mai arzaƙi ta rashin gaskiya, amma lokacin da yayi rabin shekarunsa sun yi, wannan arzaƙin zai bar shi, a ƙarshe zai zama wawa."
\s5
\v 12 "Wurin haikalinmu kursiyi ne mai daraja, an ɗaukaka shi tun daga farko.
\v 13 Yahweh shi ne begen Isra'ila. Dukkan waɗanda suka rabu da kai zasu ji kunya. Waɗanda suke cikin ƙasar waɗanda suka juya daga gare ka za a rubuta su akan ƙura. Domin sun rabu da Yahweh, maɓuɓɓugar ruwan rai.
\v 14 Warkar da ni, Yahweh, zan kuwa warke! Ka cece ni, zan kuwa cetu. Gama kai ne waƙar yabona.
\s5
\v 15 Duba!, suna ce mani, 'Ina maganar Yahweh take? Tazo mana!'
\v 16 Amma ni, ban gudu daga zama makiyayi da yake binka ba. Ban kuma so zuwan ranar bala'i ba. Ka kuwa san abin da ya fito daga leɓunana. An yi su a gabanka.
\s5
\v 17 Kada ka zamar mani abin ban razana. Kai ne mafakata a ranar masifa.
\v 18 Bari waɗanda suke runtumata su kunyata, amma kada ka barni in kunyata. Bari su karaya, amma kada ka bar ni in karaya. Ka aika masu da ranar masifa gãba da suka kuma rugurkujesu da hallaka riɓi biyu."
\s5
\v 19 Yahweh ya faɗa mani wannan: "Ka tafi ka tsaya a ƙofar jama'a wadda sarakunan Yahuda suke shiga da fita ta cikinta, ka kuma tafi dukkan ƙofofin Yerusalem.
\v 20 Ka ce da su, 'Ku ji maganar Yahweh, ku sarakunan Yahuda da dukkan ku mutanen Yahuda, da kowanne mazaunin Yerusalem waɗanda ke shiga ta waɗannan ƙofofi.
\s5
\v 21 Yahweh ya faɗi wannan: "Kuyi hankali saboda rayukanku kada ku kuma ɗauki kaya a ranar Asabar ku kawo su ta ƙofofin Yerusalem.
\v 22 Kada ku kawo kaya daga gidajen ku a ranar Asabar. Kada ku yi kowanne irin aiki, sai dai ku kiyaye ranar Asabar da tsarki, kamar yadda na umarce kakanninku su yi.'"
\v 23 Basu saurara ba ko su mai da hankali, amma suka taurare wuyansu don kada su ji ni ko su karɓi horaswa.
\s5
\v 24 Zai kasance idan dai kun saurare ni - wannan furcin Yahweh ne - kada ku kawo kaya ta ƙofofin wannan birni a ranar Asabar amma maimako ku tsarkake ranar Asabar ta Yahweh kada kuma ku yi kowanne irin aiki a cikinta,
\v 25 sa'an nan ne sarakuna, da 'ya'yan sarakuna, da waɗanda ke zaune akan kursiyin Dauda za su shiga ta ƙofofin wannan birni su na hawan karusai da dawakai, su da shugabaninsu, da mutanen Yahuda da mazauna Yerusalem, wannan birni kuma za a zauna cikinsa har abada.
\s5
\v 26 Zasu zo daga biranen Yahuda daga kuma dukkan kewayen Yerusalem, daga ƙasar Benyamin da ta kwarurruka, daga duwatsu, da ta Negeb, suna kawo baye-bayen na ƙonawa da hadayu, baye-bayen hatsi da na turare, baye-bayen godiya ga gidan Yahweh.
\v 27 Amma idan baku saurare ni ba - ku kiyaye ranar Asabar ba kuma ku ka ɗauki kaya masu nauyi kuka shiga ta ƙofofin Yerusalem a ranar Asabar ba - sai in cinna wa ƙofofin wuta, zata kuwa cinye tsararrun wurare na Yerusalem, ba kuwa zata kasu ba."
\s5
\c 18
\cl Sura 18
\p
\v 1 Maganar da ta zo ga Irmiya daga Yahweh, cewa,
\v 2 "Tashi ka tafi gidan maginin tukwane, domin a can zaka ji maganata.
\v 3 Sai na gangara zuwa gidan maginin tukwanen, duba yana aikin tukwane akan na'urar ginin tukwanen.
\v 4 Amma abin da yake mulmulawa da yunɓu ya lalace a hannunsa, sai ya canja tunaninsa ya sake wani abu dabam wanda yake gani yana da kyau a idanunsa.
\s5
\v 5 Sa'annan maganar Yahweh tazo gare ni, cewa,
\v 6 "Ba zan iya yin haka da ku ba kamar wannan maginin tukwanen, gidan Isra'ila? -wannan furcin Yahweh ne. Duba! Kamar yadda yumɓu yake a hannun maginin tukwane - haka nan kuke a hannuna, gidan Israi'la.
\v 7 A lokaci ɗaya, zan iya yin shela wani abu akan al'umma ko mulki, cewa zan kora ta, in kakkaryata, ko hallaka ta.
\v 8 Amma idan al'umma wadda na yi magana a kanta ta juyo daga muguntarta, sai in janye masifar da nayi niyyar kawo mata.
\s5
\v 9 A wani lokaci, zan iya yin shelar wani abu akan wata al'umma ko mulki, cewa zan gina ko in kafa ta.
\v 10 Amma idan ta aikata mugunta a idanuna ta wurin rashin sauraron muryata, daga nan zan janye abu mai kyau da na ce zan yi domin su.
\s5
\v 11 To yanzu, yi magana da jama'ar Yahuda da mazaunan Yerusalem ka ce, 'Yahweh ya faɗi wannan: Duba, ina gab da shirya masifa gãba da ku. Ina gab da tsara wata dabara gãba da ku. Ku tuba, kowanne mutum daga muguwar hanyarsa, da haka hanyoyinku da ayyukanku zasu kawo maku alheri.
\v 12 Amma zasu ce, 'Wannan bashi da amfani. Zamu yi kamar yadda muka tsara. Kowanne ɗayan mu zai yi bisa ga muguntarsa, da tattaurar zuciyarsa take marmari.'
\s5
\v 13 Saboda haka Yahweh ya faɗi wannan, 'Tambayi al'ummai, wane ne ya taɓa jin irin wannan? Budurwa Isra'ila ta yi mugun abu ƙwarai.
\v 14 Dusar ƙanƙara Lebanon ta taɓa rabuwa da tsaunuka a gefenta? Ko rafuffukan duwatsu masu gangarowa daga nesa sun taɓa lalacewa, waɗannan rafuffuka masu sanyi?
\s5
\v 15 Duk da haka mutanena sun manta da ni. Suna baye-baye ga gumaka marasa amfani waɗanda aka sasu tuntuɓe a cikin tafarkunsu; sun bar tsofaffin tafarku don suyi tafiya a tafarku masu sauƙi.
\v 16 Ƙasarsu zata zama abar banƙyama, ta zama abin tsaki har abada. Duk wanda ya wuce ta wurin zai razana ya kuma kaɗa kansa.
\v 17 Zan warwatsa su gaban maƙiyansu kamar iskar gabas. Zan nuna masu bayana, amma ba fuskata ba, a ranar masifarsu.'"
\s5
\v 18 Sai mutanen suka ce, "Kuzo, mu shirya maƙarƙashiya akan Irmiya, tun da yake shari'a bata lalace daga wurin firist ba, ko shawara daga mutane masu hikima ba, ko maganganu daga annabawa ba. Kuzo, mu kai ƙararsa ta wurin maganarmu kada mu yarda ko mu kula da duk wani abin da zai faɗa."
\v 19 Ka saurare ni, Yahweh, ka saurari murya abokan gãbata.
\v 20 Lallai ne masifa daga gare su ta zama ladana don yin abin kirki gare su? Duk da haka sun gina rami domina. Ka tuna yadda na tsaya a gabanka na yi magana akan lafiyarsu, da zai sa a janye fushinka daga gare su.
\s5
\v 21 Saboda haka ka miƙa 'ya'yansu ga yunwa, ka kuma bashe su a hannun masu amfani da takobi. Bari matansu su zama masu makoki da gwauraye, mazajensu a kashe su, samarinsu a kashe su da takobi a yaƙi.
\v 22 Bari a ji kururuwa daga gidajensu, don maharan da ka aika masu farat ɗaya. Gama sun haƙa rami don su kama ni sun kuma kafa wa ƙafafuna tarkuna.
\v 23 Amma kai, Yahweh, ka san dukkan maƙarshiyarsu a kaina don su kashe ni. Kada ka gafarta masu muguntarsu da zunubansu. Kada kuma ka shafe zunubansu daga gabanka. A maimakon haka, bari a jefar da su a gabanka. Ka yi gãba dasu a lokacin fushinka.
\s5
\c 19
\cl Sura 19
\p
\v 1 Yahweh ya faɗi wannan, "Tafi ka sayo tulun yumɓu a wurin maginin tukwane sa'ad da kana tare da dattawan mutane da kuma firistoci.
\v 2 Sai ku tafi Kwarin Ben Hinnom na ƙofar Kasko, a wurin zaka yi shelar maganar da zan faɗa maka.
\v 3 Ka ce, 'Ku ji maganar Yahweh, sarakunan Yahuda da mazaunan Yerusalem! Yahweh mai runduna, Allah na Isra'ila, ya faɗi wannan, "Ku gani, na kusa kawo masifa akan wannan wuri, duk kuma kunuwan kowanne da zai ji zai karkaɗa.
\s5
\v 4 Zan yi wannan domin mutanen sun rabu da ni sun ƙazantar da wannan wuri. A wannan wuri sun miƙa hadayu ga wasu alloli da basu san su ba. Kakaninsu, da sarakunan Yahuda sun cika wannan wuri da jinin marasa laifi.
\v 5 Sun ginawa Ba'al bagadi don su ƙona 'ya'yansu maza a matsayin baye-bayen ƙonawa gare shi - abin da ban umarta ba, ko in furta, ban ma yi tunanin haka ba.
\s5
\v 6 Saboda haka, ku gani, rana tana zuwa - wannan furcin Yahweh ne - wadda wannan wuri baza a ƙara kiransa Tofet, Kwarin Ben Hinnom ba, domin zai zama Kwarin Yanka.
\v 7 A wannan wuri zan wofinta shirin Yahuda da na Yerusalem. Zansa a kashe su da takobi a gaban abokan gãbarsu ta hannun waɗanda suke neman ransu. Sa'annan zan ba da gawawwakinsu su zama abincin tsutsayen sammai da na namomin jeji.
\v 8 Zan mai da wannan birni kango da kuma abin tsaki, domin duk wanda ya wuce wurin zai yi mamaki da tsaki, akan dukkan annobar.
\v 9 Zansa su ci naman 'ya'yansu maza da mata; kowanne mutum zai ci naman maƙwbcinsa cikin damuwa da azaba akan abin da ya faru da su daga wurin abokan gãbarsu da waɗanda suke neman ransu.'"
\s5
\v 10 Sa'annan sai ka fasa tulun yumɓun a gaban mutanen da suka tafi tare da kai.
\v 11 Ka kuwa ce masu, 'Yahweh mai runduna yace wannan: Haka zan yi wannan abu ga waɗannan mutane na wannan birni - wannan furcin Yahweh ne - kamar yadda Irmiya ya fashe tulun yumɓun yadda ba wanda zai iya gyara shi kuma. Mutane zasu bizne matattu a Tofet har sai an rasa wurin da ya rage da za a sake bizne matattu kuma.
\s5
\v 12 Wannan shi ne abin da zan yi da wannan wuri da mazaunansa idan na maida wannan birni kamar Tofe -wannan furcin Yahweh ne -
\v 13 saboda haka gidajen Yerusalem da na sarakunan Yahuda zasu zama kamar Tofet - dukkan gidajen waɗanda akan rufinsu ne ƙazaman mutane suke sujada ga dukkan taurarin sararin sama da suke zuba abin sha na baye baye ga wasu alloli.'"
\s5
\v 14 Sai Irmiya ya komo daga Tofet, inda Yahweh ya aike shi don yayi annabci. Ya tsaya a filin gidan Yahweh, yace da dukkan mutane.
\v 15 "Yahweh mai runduna, Allah na Isra'ila, y faɗi wannan, 'Ku gani, na kusa auka wa wannan birni da dukkan garuruwansa da dukkan masifu da na ambata gãba da shi, tun da sun taurare wuyansu sun kuma ƙi jin maganganuna.'"
\s5
\c 20
\cl Sura 20
\p
\v 1 Fashur ɗan Immer firist - shi babban jami'i ne - ya ji Irmiya yana annabcin waɗannan maganganu a gaban gidan Yahweh.
\v 2 Saboda haka Fashur ya bugi annabi Irmiya sa'annan ya sa shi cikin turu wanda ke ƙofar bisa ta Benyamin a gidan Yahweh.
\s5
\v 3 Ya zamana kashegari sa'adda Fashhur ya fitar da Irmiya daga turun. Sai Irmiya yace da shi, "Yahweh bai kira sunanka Fashhur ba, amma ya baka suna Magor Missabib.
\v 4 Domin Yahweh ya faɗi wannan, 'Duba, zan maishe ka abin tsoro, kai da dukkan waɗanda kake ƙauna, amma zasu mutu da takobi ta wurin abokan gãbarsu idanunka kuma zasu gani. Zan kuma bada dukkan jama'ar Yahuda a hannun sarkin Babila. Shi kuwa zai maida dasu bayi a Babila ko kuwa ya kai masu hari da takobi.
\s5
\v 5 Zan ba shi dukkan dukiyar wannan birni da kuma dukkan arzikinta da dukkan abubuwa masu tamani da dukkan dukiyar sarakunan Yahuda. Zan miƙa waɗannan abubuwa a hannun abokan gãbarsu zasu kuma washe su. Zasu ɗauke su su kuma kai su Babila.
\v 6 Amma kai, Fashhur, da dukkan mazauna gidanka zasu tafi bauta. Kai zaka tafi Babila a can zaka mutu. Kai da dukkan waɗanda kake ƙauna kuma kayi masu annabcin ƙaryar waɗannan abubuwa a wurin za a bizne ka.'"
\s5
\v 7 Yahweh, ka ruɗe ni, na kuwa ruɗu. Ka fi ni ƙarfi, ka kuma rinjaye ni. Na zama abin dariya dukkan yini, kowa yana ta yi mani ba'a.
\v 8 Amma duk lokacin da zan yi magana, na kan kira da murya in yi magana da ƙarfi, 'Hargitsi da hallakarwa.' Sai maganar Yahweh ta zama abin zargi da abin ba'a a dukkan yini.
\v 9 Idan na ce, 'Ba zan ƙara yin tunani akan Yahweh ba. Ba kuwa zan ƙara yin magana da sunansa ba.' Sai in ji kamar wuta a cikin zuciyata, an sa ta a cikin ƙasusuwana. Sai in yi ƙoƙarin danne ta amma ba zan iya jurewa ba.
\s5
\v 10 Na kan ji jita-jita ta banrazana daga wurin mutane da yawa a dukkan kewaye. 'Dole mu bada rahoto!' Waɗanda ke kusa da ni su dubawa su gani ko zan faɗi. 'Watakila za a ruɗe shi. Idan haka ne, sa'annan ma iya rinjayarsa har mu ɗauki fansarmu a kansa.'
\v 11 Amma Yahweh yana tare da ni kamar jarumi mai iko, don haka masu runtumata zasu yi tangaɗi. Baza su ci nasara da ni ba. Zasu ji kunya ƙwarai domin ba zasu yi nasara ba. Ba zasu daina jin kunya ba, kuma ba za a manta ba.
\s5
\v 12 Amma kai, Yahweh mai runduna, mai gwada adali wanda yake ganin zuciya da tunani. Bari in ga sakayyar da zaka yi masu tun da na kawo ƙarata a gare ka.
\v 13 Raira waƙa ga Yahweh! A yabi Yahweh! Gama ya kuɓutar da rayukan waɗanda ake zalunta daga hannun mugaye.
\s5
\v 14 Bari ranar da aka haife ni ta zama la'ananniya. Kada ka bar ranar da uwata ta haife ni ta yi albarka.
\v 15 Bari mutumin da ya kai wa mahaifina labari ya zama la'annane, wanda yace, An haifa maka ɗa namiji,' don yasa ka farin ciki.
\s5
\v 16 Bari wannan mutum ya zama kamar biranen da Yahweh ya kaɓantar ba tare da ya ji tausayinsu ba. Bari ya ji kuka don neman taimako da wayewar gari, da rana kuma ya ji gangamin yaƙi,
\v 17 domin bai kashe ni tun ina ciki ba, ya sa uwata ta zama kabarina, cikin mahaifar da zata dawwama har abada.
\v 18 Me yasa na fito daga cikin mahaifa in ga damuwa da azaba, don kwanakina su cika da kunya?"
\s5
\c 21
\cl Sura 21
\p
\v 1 Wannan ita ce maganar da ta zo wa Irmiya daga Yahweh lokacin da sarki Zadakiya ya aiki Fashhur ɗan Malkiya da Zafaniya ɗan Ma'aseya firist gare shi. Suka ce da shi,
\v 2 "Nemi shawara daga Yahweh a madaddin mu, don Nebukadnezza sarkin Babila yana kawo ma na yaƙi. Me yiwuwa Yahweh zai yi abin ban al'ajabi domin mu, kamar yadda ya saba a lokatan baya, wanda ya sa shi ya janye daga wurin mu."
\s5
\v 3 Sai Irmiya ya ce da su, "Wannan shi ne abin da dole za ku ce da Zadakiya,
\v 4 Yahweh, Allah na Israila, ya faɗi wannan: Duba, zan juya baya ga kayan yaƙin da su ke hannunka, waɗanda ka ke yaƙi da su gãba da sarkin Babila da Kaldiyawa waɗanda suke kusa da ku daga wajen garun! Gama zan tara su a cikin tsakiyar wannan birnin.
\v 5 Ni kaina zan yi faɗa da kai da duk ƙarfina, da kuma hasalata da zafin fushina.
\s5
\v 6 Gama zan faɗawa mazaunan wannan birnin, mutum da dabba. Za su mutu da babbar annoba.
\v 7 Bayan wannan - wannan shi ne furcin Yahweh - Zadakiya sarkin Yahuda, da bayinsa da mutanen, da duk wanda ya rage a cikin wannan birni bayan annoba, da takobi da kuma yunwa, zan bashe su dukka a hannun Nebukadnezza sakin Babila, da kuma hannun abokan gãbarsu, da hannun waɗanda suke neman rayukansu. Daga nan shi kuma zai kashe su da kaifin takobi. Ba zai ji tausayinsu ba, ko ya rage su, ko kuma ya yi juyayinsu ba.'
\s5
\v 8 Game da waɗannan mutane dole ka ce, 'Yahweh ya faɗi wannan: Duba ina kusa da sa hanyar rai da hanyar mutuwa a gabanku.
\v 9 Shi wanda ya zauna a wannan birnin zai mutu da takobi, da yunwa da kuma annoba; amma shi wanda ya fita zai ba da kansa ga Kaldiyawa waɗanda suka kewaye ku gãba da ku zai rayu. Zai tserar da ransa.
\v 10 Gama na ƙudura zan yi gãba da wannan birni in kuma kawo masa masifa ba alheri ba - wannan furcin Yahweh ne. An ba da shi a hannun sarkin Babila, shi kuwa zai ƙone shi da wuta.'
\s5
\v 11 A game da gidan sarkin Yahuda kuwa, ku ji maganar Yahweh.
\v 12 Ya gidan Dauda, Yahweh ya ce, 'Ku aikata adalci kowace safiya. Ku ceci wanda aka yi masa ƙwace daga hannun mai tsananta masa, ko kuma hasalata ta fita kamar wuta ta yi ƙuna, harma ba mai iya kashe ta, saboda mugayen ayyukanku.
\s5
\v 13 Duba, mazaunan kwari! Ina gãba da ku, dutsen da ya ke a fili - wannan furcin Yahweh ne - ina gãba da wanda yake cewa, "Wane ne zai iya saukowa ƙasa don ya yi gãba da mu?" Ko kuwa "Wane ne zai iya shiga gidajenmu?"
\v 14 Na sa sakamakon ayyukanku su yi gãba da ku - wannan furcin Yahweh ne - kuma zan kunna wuta a cikin kurmin, za ta cinye duk abin da ya ke kewaye da ita.'"
\s5
\c 22
\cl Sura 22
\p
\v 1 Wannan shi ne abin da Yahweh ya ce, "Ka gangara zuwa gidan sarkin Yahuda ka faɗa ma sa wannan magana a can.
\v 2 Ka ce, 'Sarkin Yahuda, ka saurari maganar Yahweh - kai da ke zaune akan gadon sarautar Dauda - da kai, da barorinka, da mutanenka da ke shigowa ta waɗannan ƙofofi.
\v 3 Yahweh ya faɗi wannan, "Ku aikata gaskiya da adalci, kuma duk wanda aka yi masa ƙwace - ku cece shi daga hannun masu zalumtarsa. Kada ku wulaƙanta wani baƙon da ke ƙasarku, ko maraya ko kuwa gwauruwa. Kada a yi ta'addanci ko a zubar da jinin marar laifi a wannan wurin.
\s5
\v 4 Domin idan hakika ku ka yi waɗannan abubuwa, sarakunan da ke zaune kan kursiyin Dauda za su shiga cikin ƙofofin gidan nan haye cikin karusa da dawakai, shi, da barorinsa, da jama'arsa!
\v 5 Amma idan ba ku kasa kunne ga waɗannan zantattuka waɗanda na yi shelar su ba - wannan furcin Yahweh ne - to wannan masarauta za ta zama kufai.'"
\s5
\v 6 Gama Yahweh ya faɗi wannan game da gidan sarkin Yahuda, 'Kai kamar Giliyad ka ke, kamar ƙolƙolin Lebanon ka ke a gare ni. Duk da haka zan maisheka jeji, da kuma birane da ba mazauna.
\v 7 Gama zan ƙaddara masu lalatarwa su tashi gãba da ku! Mutane da makamansu za su daddatse itatuwan sidarku mafi kyau su kuma zuba su a wuta.
\s5
\v 8 Sa'annan al'ummai da yawa za su shige ta wannan birni. Kowanne mutum zai ce wa na kusa da shi, "Me ya sa Yahweh ya yi haka game da wannan babban birni?"
\v 9 Sa'annan ɗayan zai amsa, "Saboda sun yi watsi da alƙawarin Yahweh Allahnsu suka russuna wa waɗansu alloli suka yi masu sujada."
\s5
\v 10 Kada ku yi kuka domin wanda ya mutu ko ku yi makoki dominsa; amma ku yi kuka mai zafi sabili da wanda ya kusa tafiya, domin ba zai ƙara dawowa ya ga ƙasar asalinsa ba.'
\s5
\v 11 Domin Yahweh ya faɗi haka game da Yehoahaz ɗan Yosiya sarkin Yahuda, wanda ya gaji sarauta a madadin ubansa Yosiya, 'Ya tafi daga nan wurin ba zai sake komowa ba.
\v 12 Zai mutu a can inda suka kai shi zaman talala, kuma ba zai ƙara ganin wannan ƙasa ba.'
\s5
\v 13 Kaiton wanda ya gina gidansa ta hanyar rashin adalci, benayensa kuma ta hanyar rashin gaskiya, ya sa makwabcinsa ya yi masa aiki a banza, bai kuma bashi al'bashinsa ba;
\v 14 yana cewa, 'Zan gina wa kaina babban gida mai manyan ɗakuna a sama.' Sai ya sa masu manyan tagogi, ya kuma rufe su da itacen sida, ya kuma yi masu jan shafe.
\s5
\v 15 Wannan ne zai maishe ka sarki mai adalci, da ka ke son ka sami katakan sida? Ko mahaifinka bai ci ya sha ba, duk da haka ya yi gaskiya da adalci? Sai komai ya tafi dai - dai da shi.
\v 16 Ya shari'anta da alheri ga matalauta da fakirai. Ya yi kyau a lokacin nan. Wannan ba shi ne ma'anar sanina ba? - wannan ne furcin Yahweh.
\s5
\v 17 Amma ba kome a zuciyarka da idanunka sai dai damuwa domin muguwar ribarka da kuma domin zubar da jinin marasa laifi, da aikata danniya da murƙushe waɗansu.
\v 18 Sabili da wannan Yahweh ya faɗi haka game da Yehoiyakim ɗan Yosiya, sarkin Yahuda: Ba za su yi makoki domin sa ba, suna cewa, 'Kaito, ɗan'uwana!' ko, 'Kaito, 'yar'uwata!' Ba za su yi makoki dominsa ba, suna cewa, 'Kaito, ubangida!' ko, 'Kaito, mai martaba!'
\v 19 Za a binne shi kamar yadda ake binne jaki, a janye shi a jefar nesa da ƙofofin Yerusalem.
\s5
\v 20 Ku haura kan duwatsun Lebanon ku yi ihu. Ku tada muryarku a Bashan. Ku yi ihu daga duwatsun Abarim, gama duk abokanku za a hallaka su.
\v 21 Na yi maku magana sa'ad da ku ke zaune lafiya, amma kun ce, 'Ba za mu kasa kunne ba.' Al'adarku ce wannan tun kuna samari, gama ba ku saurari muryata ba.
\s5
\v 22 Iska za ta kora dukkan makiyayanku, abokanku kuma za su tafi bautar talala. Sa'annan lallai za ku kunyata ku ƙasƙantu ta wurin miyagun ayyukanku. Ku da kuke zaune cikin 'Lebanon,'
\v 23 ku da ku ke shaƙatawa cikin ginin itatuwan sida, za ku zama abin tausayi sa'ad da azabar naƙuda ta afko maku, azaba kamar ta mace mai naƙudar haifuwa!"
\s5
\v 24 "Na rantse da zatina - wannan furcin Yahweh ne - ko da kai, Yehoiyacin ɗan Yehoiyakim, sarkin Yahuda, zoben hannun damana ne, zan cire ka.
\v 25 Gama na bashe ka a hannun masu neman ranka da kuma hannun waɗanda ka ke jin tsoro a gabansu, wato hannun Nebukaneza sarkin Babila da Kaldiyawa.
\v 26 Zan jefar da kai da mahaifiyarka wadda ta haife ka cikin wata ƙasa, ƙasar da ba nan aka haife ka ba, kuma can za ka mutu.
\s5
\v 27 Game da ƙasar nan da suke so su koma, ba za su dawo nan ba.
\v 28 Wannan ita ce tukunyar da aka rena aka kuma farfasa? Wannan shi ne mutumin nan Yehoiyacin tukunyar da ba ta gamshi kowa ba? Me ya sa suka jefar da shi waje da shi da zuriyarsa, kuma suka zubar da su cikin ƙasar da ba su santa ba?
\s5
\v 29 Ƙasa, Ƙasa, ƙasa! Ki ji maganar Yahweh!
\v 30 Yahweh ya faɗi wannan, "Rubuta akan mutumin nan Yehoiyacin: Ba zai haifu ba. Ba zai yi albarka ba a kwanakinsa, ba kuma wani a zuriyarsa da zai ci nasara ko kuma ya ƙara zama a kursiyin Dauda ya yi mulki bisa Yahuda ba."
\s5
\c 23
\cl Sura 23
\p
\v 1 "Kaiton makiyayan da ke lalatarwa suke kuma warwatsar da tumakin makiyayata - wannan furcin Yahweh ne."
\v 2 Saboda haka Yahweh, Allah na Isra'ila, ya faɗi wannan game da makiyayan da ke kiwon mutanensa, "Kun warwatsar da garkena kun kore su nesa. Ba ku lura da su ba. Sabili da haka na kusa in hukunta ku saboda muguntar da ku ka aikata - wannan ne furcin Yahweh.
\s5
\v 3 Ni da kaina zan tattara ragowar garkena daga dukkan ƙasashen da na kora su, zan kuma dawo da su wurin kiwo, inda za su hayayyafa su kuma ƙaru.
\v 4 Sa'anna zan tanada makiyaya bisansu waɗanda za su yi kiwon su domin kada su ƙara tsorata ko su zama karyayyu. Ba za a rasa ko ɗayansu ba - wannan furcin Yahweh ne.
\s5
\v 5 Duba, kwanaki suna zuwa - wannan ne furcin Yahweh - da zan tada wa Dauda reshe mai adalci. Shi zai yi mulki kamar sarki; zai yi aiki da hikima ya sa gaskiya da adalci su kasance a ƙasar.
\v 6 A kwanakinsa Yahuda zai tsira, Isra'ila zai zauna lafiya. Ga sunan da za a kira shi da shi: Yahweh shi ne adalcinmu.
\s5
\v 7 Saboda haka duba, kwanaki suna zuwa - wannan ne furcin Yahweh - da ba za su ƙara cewa, "Na rantse da ran Yahweh wanda ya fito da mutanen Isra'ila daga ƙasar Masar ba.'
\v 8 Maimakon haka za su ce, 'Na rantse da ran Yahweh, wanda ya fitar ya kuma dawo da zuriyar gidan Isra'ila daga ƙasar arewa da dukkan ƙasar da aka kora su.' Sa'annan za su zauna a ƙasar da ke tasu."
\s5
\v 9 A game da annabawan, zuciyata ta karai, dukkan ƙasusuwana su na kaɗuwa, na zama kamar bugaggen mutum, kamar mutumin da ruwan inabi ya rinjaye shi, saboda Yahweh da kuma zantattukansa masu tsarki.
\v 10 Domin ƙasar ta cika da mazinata. Sabili da waɗannan ne ƙasar ta bushe. Wuraren kiwo a jeji sun ƙeƙashe. Tafarkun annabawan nan mugaye ne; ba su mori ikonsu yadda ya kamata ba.
\s5
\v 11 Gama da annabawan da firstocin dukka biyu sun ƙazamtu. Har ma na ga muguntarsu a cikin gidana! - wannan ne furcin Yahweh -
\v 12 Sabili da haka tafarkinsu zai zama kamar wuri mai santsi cikin duhu. Za a ture su ƙasa. Za su faɗa a cikinta. Gama zan aiko da masifa găba da su a shekarar da zan hukunta su - wannan ne furcin Yahweh.
\s5
\v 13 Gama na ga annabawan da ke cikin Samariya su na yin abin kyama: sun yi annabci da Ba'al sun karkatar da jama'ata Isra'ila.
\v 14 A cikin annabawan da ke Yeruselem na ga mugayen abubuwa: Su na yin zina su na aikata ƙarya. Su na ƙarfafa hannun miyagu; ba wanda yake juyowa daga muguntarsa. Dukkan su sun zama kamar Soduma a gareni, mazamnan su kuma kamar Gwamarata!"
\v 15 Saboda haka Ubangiji mai runduna ya faɗi wannan game da annabawan, "Duba, na kusa in sa su su ci abu mai ɗaci su sha ruwa mai dafi, gama ƙazamta ta bazu daga annabawa da ke cikin Yeruselem har zuwa dukkan ƙasar."
\s5
\v 16 Ubangiji mai runduna ya ce, "Kada ku saurari maganganun annabawan da ke yi maku annabci. Sun zurma ku! Suna sanar da wahayi daga nasu tunani, ba daga bakin Yahweh ba.
\v 17 Kullum su na faɗa wa waɗanda su ka rena ni, 'Yahweh ya ce akwai salama dominku,' Gama kowanne mai tafiya a cikin tattaurar zuciyarsa ya kan ce, 'Masifa ba za ta auko kanmu ba.'
\v 18 Duk da haka wa ya tsaya a majalisar Yahweh? Wa ya gani ya kuma ji maganarsa? Wa ya natsu ya kasa kunne ya saurari maganarsa?
\s5
\v 19 Duba, akwai hadarin da ke dannowa daga Yahweh! Hasalar sa na fita, guguwa kuma na juyawa ko'ina. Tana zagayawa kewaye da kan mugaye.
\v 20 Fushin Yahweh ba zai huce ba sai ya gama aiwatawa da cika nufin zuciyarsa. A ƙarshen kwanaki, za ku gane shi.
\s5
\v 21 Ban aiki waɗannan annabawan ba. Haka kawai su ka bayyana. Ban shaida masu kome ba, amma duk da haka su ka yi annabci.
\v 22 Inda sun kasance a majalisar shawarata, da sun sa jama'ata su ji maganata; da sun sa su su juyo daga mugayen maganganunsu da kuma mugayen ayyukansu.
\s5
\v 23 Ni Allah ne na kusa kaɗai - wannan ne furcin Yahweh - ba kuma Allah na nesa ba?
\v 24 Akwai wani da zai iya ɓoye wa a wurin da ba zan ganshi ba? - wannan ne furcin Yahweh - ko ni ban cika sammai da ƙasa ba? - wannan ne furcin Yahweh.
\s5
\v 25 Na ji abin da annabawan su ka faɗi, waɗanda suke annabcin ƙarya cikin sunana. Sukan ce, 'Na yi mafarki! 'Na yi mafarki!
\v 26 Har yaushe za a ci gaba da haka, annabawa masu annabcin ƙarya daga tunaninsu, da kuma annabci daga ruɗun da ke cikin zuciyarsu?
\v 27 Su na shirin sa mutanena su manta da sunana ta wurin mafarkan da su ka sanar, kowanne ga maƙwabcinsa, kamar dai yadda kakaninsu su ka manta da sunana su ka so sunan Ba'al.
\s5
\v 28 Annabin da ya ke da mafarki, bari ya sanar da mafarkin. Amma ga wanda na sanar da shi wani abu, bari ya sanar da maganata da gaskiya. Me ya haɗa ciyawa da al'kama? - wannan ne furcin Yahweh - Maganata ba kamar wuta ta ke ba? - wannan ne furcin Yahweh -
\v 29 kuma kamar guduma mai farfasa duwatsu gutsu - gutsu?
\v 30 To ku duba, ina găba da annabawan - wannan ne furcin Yahweh - da kowanne ɗayan da ya saci magana daga wani mutum ya kuma ce maganar ta zo daga gareni.
\s5
\v 31 Duba, ina găba da annabawan - wannan ne furcin Yahweh - masu amfani da harshensu su yi shelar annabci.
\v 32 Duba, ina găba da annabawa da ke mafarkan ƙarya - wannan ne furcin Yahweh - sa'annan su yi shela da haka su ke ɓad da mutanena da ƙarairayinsu da kuma fariya. Ina găba da su, gama ban aike su ba ko in ba su umarni. Saboda haka lallai, ba za su taimaki mutanen nan ba - wannan ne furcin Yahweh.
\s5
\v 33 Lokacin da waɗannan mutane, ko annabi, ko firist ya tambayeku, 'mene ne nawaiyar Yahweh?' za ka ce masu, 'Ku ne nawaiyar, kuma zan jefar da ku - wannan ne furcin Yahweh.
\v 34 Game da annabawan, da firistoci, da kuma mutanen da ke cewa, 'Wannan shi ne nawaiyar Yahweh' zan hukunta wannan mutum da gidansa.
\s5
\v 35 Kuna ci gaba da cewa, kowanne mutum ga makwabcinsa da kuma kowanne mutum ga ɗan'uwansa, 'Me Yahweh ya amsa?' kuma 'Me Yahweh ya furta?
\v 36 Amma ka da ku ƙara yin magana akan 'nawayar Yahweh,' gama nawaiyar ita ce maganar kowanne mutum, kuma kun karkatar da maganganun Allah mai rai, Ubangiji mai runduna, Allahnmu.
\s5
\v 37 Ga abin da za ku ce wa annabi, 'Wace amsa ce Yahweh ya ba ku? ko kuma, 'Me Yahweh ya ce?'
\v 38 Amma idan kun ce, 'Nawaiyar Yahweh,' wannan shi ne abin da Yahweh ya ce: 'Sabili da kun faɗi wanɗannan maganganu, 'Nawaiyar Yahweh,' lokacin da na aika maku, cewa, 'Ba za ku ce, "Nawaiyar Yahweh,"' ba.
\v 39 saboda haka, duba, na kusa ɗaukar ku in jefar da ku nesa da ni, tare da birnin dana ba ku da kakanninku.
\v 40 Sa'annan zan sa maku madawwamiyar kunya da zargi a kanku wanda ba za a taɓa mantawa ba.'"
\s5
\c 24
\cl Sura 24
\p
\v 1 Yahweh ya nuna mani wani abu. Duba, ga kwanduna biyu na 'ya'yan baure a gaban haikalin Yahweh. (Wannan wahayi ya faru bayan da Nebukadnezza, sarkin Babila, ya kai waɗannan mutane bautar talala: Yehoyacin ɗan Yehoyakim, sarkin Yahuda, da shugabannin Yahuda, da masassaƙa, da masu ƙira da kwasao daga Yerusalem ya kawo su Babila.)
\v 2 Ɗaya kwandon ɓauren na da ƙyau sosai, kamar nunar fari na ɓaure, amma ɗaya kwandon ɓauren ba shi da kyau ko kaɗan har ma ba za a iya cin su ba.
\v 3 Yahweh ya ce mani, "Me ka gani, Irmiya?" Na ce, '"Ya'yan ɓaure. 'Ya'yan ɓaure masu kyau sosai da marasa kyau har ma ba za a iya cinsu ba."
\s5
\v 4 Sai maganar Yahweh ta zo gareni, cewa,
\v 5 "Yahweh, Allah na Isra'ila, ya faɗi wannan: Zan dubi 'yan bautar talala na Yahuda da tagomashi, kamar kyawawan 'ya'yan ɓauren nan, 'yan bautar talala waɗanda na kore su daga nan zuwa ƙasar Kaldiya.
\v 6 Zan kafa idanuna a kansu domin in yi masu alheri, in kuma dawo da su wannan ƙasar. Zan gina su, ba zan rushe su ba. Zan dasa su, ba zan tumbuƙe su ba.
\v 7 Sa'annan zan ba su zuciyar da za su sanni, gama ni ne Yahweh. Za su zama mutanena, zan kuma zama Allahnsu, haka za su juyo gareni da dukkan zuciyarsu.
\s5
\v 8 Amma kamar 'ya'yan ɓauren nan marasa kyau har da ba za a iya cinsu ba-ga abin da Yahweh ya ce - Zan yi haka da Zedekiya, sarkin Yahuda, da shugabanninsa, da kuma sauran da ke a Yerusalem waɗanda suka rage a cikin ƙasar nan ko kuwa su ka tafi su zauna cikin ƙasar Masar.
\v 9 Zan maishe su abin tsoro, abin masifa, a idanun dukkan mulkokin duniya, abin kunya abin zargi da karin magana, da dariya, da la'ana a duk wuraren da na warwatsa su.
\v 10 Zan aika da takobi, yunwa, da annoba găba da su, har sai an hallakasu daga ƙasar da na basu da kakanninsu."
\s5
\c 25
\cl Sura 25
\p
\v 1 Wannan ita ce maganar da ta zo wurin Irmiya game da dukkan mutanen Yahuda. Ya zo ne a shekara ta huɗu ta Yehoyakim ɗan Yosiya, sarkin Yahuda. Wannan ita ce shekara ta fari ta Nebukadnezza, sarkin Babila.
\v 2 Annabi Irmiya ya yi shelar wannan ga dukkan mutanen Yahuda da dukkan mazaunan Yerusalem.
\s5
\v 3 Ya ce, "Shekaru ashirin da uku, tun daga shekara ta sha uku ta Yosiya ɗan Amon, sarkin Yahuda, har zuwa yau, maganar Yahweh ta na ta zuwa gare ni, ni kuma na yi maku magana akai-akai, amma ba ku kasa kunne ba.
\v 4 Yahweh ya aika maku dukkan bayinsa annabawa akai-akai, amma ba ku saurare su ba ko ku kasa kunne.
\s5
\v 5 Waɗannan annabawa sun ce, 'Bari kowanne mutum ya juyo daga hanyar muguntarsa da lalatattun ayyukansa ya dawo ƙasar da Yahweh ya bayar a zamanin dã ga kakanninku da ku kuma, a matsayin madawwamiyar kyauta.
\v 6 Saboda haka kada ku bi waɗansu alloli ku yi masu sujada ko ku russuna masu, kuma kada ku cakune shi da ayyukan hannuwanku domin kada ya azabtar da ku.'
\s5
\v 7 Amma ba ku saurare ni ba - wannan ne furcin Yahweh - haka ku ka cakune ni da aikin hannuwanku in cutar da ku.
\v 8 Domin haka Ubangiji mai ruduna ya faɗi wannan, 'Saboda ba ku saurari maganganuna ba,
\v 9 duba, ina gaf da aiko da umarni domin a tara dukkan mutanen arewa - wannan ne furcin Yahweh - da Nebukadnezza bawana, sarkin Babila, zan kawo su gãba da ƙasar nan da mazaunanta, gãba kuma da dukkan al'umman da ke kewaye da ku. Gama zan keɓe su domin halakarwa. Zan mai da su abin tsoro, abin yi wa tsaki, da kuma kufai har abada.
\s5
\v 10 Zan kawo ƙarshen ƙarar murna da ƙarar farinciki, ƙarar ango da ƙarar amarya, ƙarar dutsen niƙa da hasken fitila.
\v 11 Sa'annan dukkan wannan ƙasa za ta zama kufai da abin tsoro, kuma waɗannan al'ummai za su bauta wa sarkin Babila shekaru saba'in.
\s5
\v 12 Za ya zama kuwa bayan shekaru saba'in sun cika, zan hukunta sarkin Babila da al'umman nan, ƙasar Kaldiyawa - wannan ne furcin Yahweh - saboda kurakuransu in maishe ta kango marar matuƙa.
\v 13 Sa'anan kuma zan yi wa ƙasar nan abin gãba bisa ga dukkan maganar da na faɗi, da kuma dukkan abin da aka rubuta a cikin wannan littafi wanda Irmiya ya yi annabci gãba da dukkan al'ummai.
\v 14 Kuma wasu al'umman da yawa da manyan sarakuna za su bautar da waɗannan al'ummai. Zan sãka masu bisa ga abin da su ka aikata da kuma ayyukan hannuwansu."'
\s5
\v 15 Gama Yahweh, Allah na Isra'ila, ya faɗa mani wannan, "Ka ƙarɓi wannan ƙoƙon ruwan inabi na hasalata daga hannuna ka sa dukkan al'umman da na aike ka gun su su sha shi.
\v 16 Gama za su sha sa'anan su yi tuntuɓe ko ina su sheƙa da gudu daga takobin da nake aikowa cikinsu."
\s5
\v 17 Sai na ƙarɓi ƙoƙon daga hannun Yahweh, na kuma să dukkan al'umman da Yahweh ya aike ni su sha shi:
\v 18 Yerusalem, biranen Yahuda da sarakunanta da shugabanninta-a maida su kufai da abin tsoro, da kuma abin tsaki da la'antarwa, kamar yadda suke a yau.
\s5
\v 19 Sauran al'ummai dole su sha shi: Fir'auna Sarkin Masar da barorinsa; shugabanninsa da dukkan mutanensa;
\v 20 dukkan baƙin mutane ruwa biyu da dukkan sarakunan da ke ƙasar Uz; dukkan sarakunan da ke ƙasar Filistiya - Ashkelon, Gaza, Ekron, da ragowar Ashdod;
\v 21 Idom da Mowab da mutanen Ammon.
\s5
\v 22 Sarakunan Taya da Sidon, sarakunan gãɓar tsallaken teku,
\v 23 Dedan, Tema, da Buz da dukkan waɗanda suke aske gashin gefen kawunansu suma sai da suka sha shi.
\s5
\v 24 Waɗannan mutanen suma dole suka sha shi: dukkan sarakunan Arebiya da dukkan sarakunan mutane masu ruwa biyu da ke zaune a jeji;
\v 25 dukkan sarakunan Zimri, da dukkan sarakunan Elam, da dukkan sarakunan Madayana;
\v 26 dukkan sarakunan arewa, waɗanda suke kusa da waɗanda suke nesa - kowanne da ɗan'uwansa da dukkan masarautar da ke duniya da ke a fuskar ƙasa. A ƙarshe, sarkin Babila zai sha a bayansu.
\s5
\v 27 Yahweh ya ce mani, "Yanzu dole ka faɗa masu, 'Yahweh mai runduna, Allah na Isra'ila, ya faɗi wannan: Ku sha ku bugu, sa'anan ku haras, ku faɗi ƙasa, kada ku tashi kafin in aiko da takobi a tsakanin ku.'
\v 28 Idan kuwa sun ƙi su ƙarɓi ƙoƙon daga hannunka su sha, za ka ce masu, 'Yahweh mai runduna ya faɗi wannan, Dole ne lallai ku sha shi.
\v 29 Ku duba, na kusa kawo masifa akan birnin da ake kira da sunana, to ku da kanku ya kamata a tsirar da ku daga horo ne? Ba za ku tsira ba, gama ina kawo takobi gãba da dukkan mazaunan ƙasar! - wannan ne furcin Yahweh mai runduna.'
\s5
\v 30 Dole ka yi annabcin dukkan waɗannan maganganu gãba da su, kuma ka ce masu, 'Yahweh zai yi ruri daga sammai zai yi ihu da muryarsa daga wurin zamansa mai tsarki, zai yi ruri da ƙarfi gãba da nasa; kuma zai yi ihu, kamar waɗanda suke matse 'ya'yan inabi gãba da dukkan mazaunan duniya.
\v 31 Zizar yaƙi zata buga ta kai dukkan bangon duniya, gama Yahweh yana kawo ƙara gãba da dukkan al'ummai, zai kuma kawo hukunci kan dukkan talikai. Zai ba da mugaye ga takobi - wannan ne furcin Yahweh.'
\s5
\v 32 Ubangiji mai runduna ya faɗi wannan, 'Duba, masifa tana tasowa daga al'umma zuwa al'umma, kuma babban hadari ya danno daga manisantan wurare na duniya.
\v 33 Sa'anan waɗanda Yahweh ya kashe za su zama daga wannan bangon duniyan zuwa wan can; ba kuma za a yi makokinsu ba, ko a tattarasu, ko kuma a binne su. Za su zama kamar taki a ƙasa.
\s5
\v 34 Ku yi makoki, makiyaya, ku yi ihu domin taimako! Ku yi birgima a cikin ƙura, ku iyayengijin garke, gama ranar da za a yanka ku ta zo; za a warwatsa ku sa'ad da ku ka faɗi kamar kyawawan tukwane.
\v 35 Babu mafaka domin makiyaya, ba sauran mafita domin iyayengijin garke.
\v 36 Ku ji koke-koken makiyaya da makokin iyayengijin garke, gama Yahweh yana lalatar da makiyayarsu.
\s5
\v 37 Haka makiyayarsu mai salama za a lalatar da ita sabili da zafin fushin Yahweh.
\v 38 Kamar ɗan zaki, da ya baro maɓuyarsa, gama ƙasarsu zata zama abin ban tsoro saboda fushin mai tsanantawa, saboda kuma zafin fushinsa.'"
\s5
\c 26
\cl Sura 26
\p
\v 1 A farkon mulkin Yehoyakim ɗan Yosiya, wannan maganar ta zo daga Yahweh cewa,
\v 2 "Yahweh ya faɗi wannan: Ka tsaya a filin haikalina ka yi magana akan dukkan biranen Yahuda waɗanda suke zuwa su yi sujada a gidana. Yi shelar dukkan maganganun da na umarce ka ka faɗa masu. Kada ka rage ko wata kalma!
\v 3 Mai yiwuwa su kasa kunne, har kowanne mutum ya juyo ya bar mugayen hanyoyinsa, nima in janye masifar da nake niyyar saukar masu saboda mugayen ayyukansu.
\s5
\v 4 Saboda haka dole ka ce masu, 'Yahweh ya faɗi wannan: Idan baku kasa kunne gare ni kun yi biyayya da dokokina da na sa agabanku ba -
\v 5 Idan baku kasa kunne da maganar bayina annabawa waɗanda na ke aiko maku-amma ba ku ji ba! -
\v 6 to zan maida gidan nan kamar Shiloh; zan maida birnin nan la'ana a idanun dukkan al'umman da ke a duniya.'"
\s5
\v 7 Da firistoci, da annabawa da dukkan jama'a sun ji annabi Irmiya yana shelar waɗannan maganganu a haikalin Yahweh.
\v 8 Ananan da Irmiya ya gama shelar dukkan maganar da Yahweh ya umarce shi ya faɗa wa dukkan mutane, sai firistoci, da annabawa da dukkan mutane suka kama shi suka ce, "Zaka mutu lallai!
\v 9 Me yasa ka yi annabci a cikin sunan Yahweh ka ce wannan gida zai zama kamar Shiloh kuma wannan birni zai zama kufai, har ba mazauna?" Gama dukkan mutanen sun tada tarzoma gãba da Irmiya a cikin haikalin Yahweh.
\s5
\v 10 Daganan sai shugabannin Yahuda suka ji waɗannan maganganu suka tashi daga gidan sarki su ka tafi gidan Yahweh. Su ka zauna a ƙofa a Sabuwar Ƙofa ta haikalin Yahweh.
\v 11 Sai firistoci da annabawa suka yi wa shugabanni da dukkan mutane magana. Suka ce, "Dai-dai ne mutumin nan ya mutu, domin ya yi annabci gãba da birnin nan, kamar yadda kuka ji da kunnuwanku!"
\v 12 Sai Irmiya ya yi magana da dukkan shugabanni da dukkan mutane yace, "Yahweh ya aiko ni in yi annabci gãba da haikalin nan da kuma birnin nan, in faɗi dukkan maganganun nan da kuka ji.
\s5
\v 13 Saboda haka yanzu fa, sai ku gyara al'amuranku da kuma ayyukanku, ku saurari muryar Yahweh Allahnku domin ya janye masifar da ya yi shela gãba da ku.
\v 14 Ni da kaina-ku dube ni! - ina hannunku. Ku yi mani abin da kuka ga yayi dai-dai a idanunku.
\v 15 Amma lallai ya kamata ku sani idan ku ka kashe ni, kuna jawo wa kanku al'hakin jinin marar laifi da kuma wannan birni da mazaunan da ke a cikinsa, gama lallai Yahweh ya aiko ni wurinku in yi shelar waɗannan maganganu a kunnuwanku."
\s5
\v 16 Daga nan shugabannin da dukkan mutane suka cewa firistoci da annabawa, "Ba dai-dai ba ne mutumin nan ya mutu, gama ya yi mana shelar abubuwa a cikin sunan Yahweh Allahnmu."
\v 17 Sai wasu maza suka tashi daga cikin dattawan ƙasar suka yi wa dukkan taron mutanen magana.
\s5
\v 18 Suka ce, "Mika Ba-morashe ya yi annabci a zamanin Hezekiya sarkin Yahuda. Ya yi wa dukkan mutanen Yahuda magana yace, 'Yahweh mai runduna yace: Za a huɗa Sihiyona kamar gona, Yerusalem za ta zama tsibin juji, dutsen haikali zai zama dutsen da ciyayi suka sha kansa.'
\v 19 To, Hezekiya sarkin Yahuda da dukkan Yahuda sun kashe shi ne? Ashe bai ji tsoron Yahweh ya nemi alheri a fuskar Yahweh domin Yahweh ya janye masifar da ya faɗa masa ba? Ko dai-dai ne muyi mugunta mafi girma gãba da rayyukanmu?"
\s5
\v 20 Ananan wani mutum kuma ya yi annabci cikin sunan Yahweh - Yuriya ɗan Shemaya daga Kiriyat Yarim-shi ma ya yi annabci gãba da birnin nan da kuma ƙasannan, ya amince da dukkan maganganun Irmiya.
\v 21 Amma da sarki Yehoyakim da dukkan sojojinsa da shugabanninsa suka ji maganarsa sai sarki ya yi ƙoƙari ya kashe shi, amma da Yuriya ya ji sai ya tsorata, ya gudu ya tafi Masar.
\s5
\v 22 Sai sarki Yehoyakim ya aiki mutane su tafi Masar - Elnatan ɗan Akbor da waɗansu mutanen aka aike su su bi Yuriya zuwa Masar.
\v 23 Suka ɗauko Yuriya daga Masar suka kawo shi wurin sarki Yehoiyakim. Sai Yehoiyakim ya kashe shi da takobi ya aika gawarsa makabartar da ke waje inda ake rufe mutane marasa galihu.
\v 24 Amma hannun Ahikam ɗan Shafan yana tare da Irmiya, saboda haka ba a bada shi ga hannun mutane su kashe ba.
\s5
\c 27
\cl Sura 27
\p
\v 1 A farkon sarautar Zedekiya ɗan Yosiya, sarkin Yahuda, wannan magana ta zo ga Irmiya daga Yahweh.
\v 2 Wannan shi ne abin da Yahweh ya faɗa mani, "Ka yiwa kanka karkiyar itace. Ka sa su a wuyanka.
\v 3 Sa'annan ka aika su wurin sarkin Idom, sarkin Mowab, sarkin mutanen Ammon, sarkin Taya, da kuma sarkin Sidon. Ka aika da su ta hannun jakadun sarki da suka zo Yerusalem gun Zedekiya sarkin Yahuda.
\v 4 Ka ba su umarni domin iyayengijinsu ka ce, 'Ubangiji mai runduna, Allah na Isra'ila ya ce: Wannan shi ne abin da zaku ce da iyayengijinku,
\s5
\v 5 Ni da kaina na yi duniya ta wurin ƙarfina mai girma da miƙaƙƙen hannuna. Ni ne nayi mutane da dabbobi a kan fuskar duniya, nakan kuma ba da ita ga wanda na ga ya dace a idanuna.
\v 6 Saboda haka yanzu, ina bada dukkan ƙasar nan a cikin hannun bawana, Nebukadnezza, sarkin Babila. Kuma ina bada abubuwa masu rai na jeji su bauta masa.
\v 7 Gama dukkan al'ummai za su bauta masa, da ɗansa da kuma jikokinsa, har sai lokaci domin ƙasarsa ya zo. Sa'annan al'ummai da yawa da manyan sarakuna za su ci ƙarfinsa.
\s5
\v 8 Saboda haka duk al'umma da mulkin da bai bauta wa Nebukadnezza, sarkin Babila ba, bai kuma ba da wuyansa ya yi karkiya da sarkin Babila ba-zan hukunta wannan al'umma da takobi, yunwa, da annoba - wannan furcin Yahweh ne-har sai na hallaka ta ta hannunsa.
\s5
\v 9 Saboda haka kada ku saurari annabawanku, da masu mafarkanku, masu dubanku, masu sihiri, da matsubbata, waɗanda suke ta yi maku magana suna cewa, 'Kada ku bauta wa sarkin Babila,'
\v 10 Gama suna yi maku annabcin ƙarya domin su kora ku nesa da ƙasarku, gama zan kore ku, zaku kuma mutu.
\v 11 Amma al'ummar da ta bada wuyanta ta yi karkiya da sarkin Babila, ta kuma bauta masa, zan bar su su huta a ƙasarsu - wannan furcin Yahweh ne-zasu kuma noma ta su gina mazauninsu a ciki.""'
\s5
\v 12 Sai na yi magana da Zedekiya sarkin Yahuda na ba shi wannan saƙon, 'Ku ba da wuyanku ku yi karkiya da sarkin Babila ku bauta masa da shi da mutanensa, zaku kuwa rayu.
\v 13 Donmi zaku mutu-da kai da mutanenka-da takobi, yunwa da annoba, kamar yadda na faɗa game da al'ummar da ta ƙi ta bauta wa sarkin Babila?
\s5
\v 14 Kada ku saurari maganganun annabawan da suka ce maku, 'Kada ku bauta wa sarkin Babila,' gama suna yi maku annabcin ƙarya ne.
\v 15 Gama ni ban aikesu ba-wannan furcin Yahweh ne - gama annabcin ƙarya suke yi cikin sunana domin in kore ku ku tafi ku hallaka, da ku da annabawan da suke maku annabci."
\s5
\v 16 Na yi shelar wannan ma firistoci da dukkan mutane na ce, "Yahweh ya faɗi wannan yace: Kada ku kasa kunne ga maganganun annabawaku da su kayi maku annabci suka ce, 'Duba! ana dawo da kayayyakin gidan Yahweh daga Babila yanzu!' Annabcin ƙarya suke yi maku,
\v 17 Kada ku saurare su. Ku bauta wa sarkin Babila ku rayu. Don me wannan birni zai zama kufai?
\v 18 Idan su annabawa ne, kuma idan lallai maganar Yahweh ta zo gare su, to su roƙi Yahweh mai runduna kada ya aika kayan haikalinsa da suka rage, na gidan sarkin Yahuda, da na Yerusalem zuwa Babila.
\s5
\v 19 Yahweh mai runduna ya faɗi haka game da ginshiƙai da babban daro da aka sani a matsayin "Tekun" da mazauninta, da sauran kayayyakin da suka rage a wannan birni -
\v 20 kayayyakin da Nebukadnezza sarkin Babila bai ɗauka ba lokacin da ya tafi da Yehoyacin ɗan Yehoiyakim, sarkin Yahuda bautar talala daga Yerusalem zuwa Babila tare da dukkan hakiman Yahuda da na Yerusalem.
\s5
\v 21 Yahweh mai runduna, Allah na Isra'ila, ya faɗi wannan game da kayayyakin da suka rage a gidan Yahweh, da gidan sarkin Yahuda da Yerusalem,
\v 22 'Za a kawo su Babila, kuma za su kasance a can har sai ranar da na aza a zo domin su - wannan ne furcin Yahweh - sa'annan zan komo da su in maido su a wannan wuri."'
\s5
\c 28
\cl Sura 28
\p
\v 1 Sai ya kasance a cikin shekarar nan, a farkon mulkin Zedekaya sarkin Yahuda, a shekara ta huɗu kuma a wata na biyar, Annabi Hananiya ɗan Azzur, wanda ya fito daga Gibiyon, yayi magana da ni a gidan Yahweh a gaban firistoci da dukkan mutane. Yace,
\v 2 "Yahweh Mai runduna, Allah na Isra'ila, Ya faɗi wannan: Na karya karkiyar da sarkin Babila ya ɗora maku.
\s5
\v 3 A cikin shekara biyu a wannan wuri zan maido da dukkan kayayyakin gidan Yahweh wanda Nebukadnezza sarkin Babila ya ɗauke daga wannan wuri ya tafi dasu Babila.
\v 4 Daga nan kuma a wannan wurin zan maido da Yehoiyacin ɗan Yehoiyakim, sarkin Yahuda, da dukkan kamammun Yahuda waɗanda aka aika Babila - wannan furcin Yahweh ne - Gama zan karya karkiyar sarkin Babila."
\s5
\v 5 Sai Annabi Irmiya yayi magana da Annabi Hananiya a gaban firistoci da dukkan mutanen dake tsaye a gidan Yahweh.
\v 6 Irmiya Annabi yace, "Bari Yahweh yayi haka! bari Yahweh ya tabbatar da maganganun daka anabta a wannan wuri ya maido da kayayyakin gidan Yahweh, da dukkan kamammu daga Babila.
\v 7 Duk da haka, ka saurari maganar da nake shelarwa a kunnuwanka da kunnuwan dukkan mutane.
\s5
\v 8 Annabawan da suka wanzu da daɗewa kafin ni da kai sunyi anabci game da al'ummai masu yawa gãba da manyan masarautu, game da yaƙi, da yunwa, da annoba.
\v 9 Hakanan Annabin da yayi anabcin za a yi salama - Idan maganarsa ta tabbata, to za a sani cewa lallai annabi ne wanda Yahweh ya aiko."
\s5
\v 10 Amma annabi Hananiya ya tashi ya ɗauki karkiyar dake wuyan annabi Irmiya ya karya ta.
\v 11 Daga nan sai Hananiya yayi magana a gaban dukkan mutanen yace, "Yahweh ya faɗi haka: kamar dai haka, cikin shekara biyu zan karya kowace karkiya daga wuyan dukkan al'ummai wanda Nebukadnezza sarkin Babila ya ɗora masu." Daga nan annabi Irmiya yayi tafiyarsa.
\s5
\v 12 Bayan da annabi Hananiya ya karya karkiyar dake wuyan annabi Irmiya, sai maganar Yahweh tazo ga Irmiya, cewa,
\v 13 "Kaje kayi magana da Hananiya kace, 'Yahweh ya faɗi haka: ka karya karkiyar itace, a maimako zan yi karkiyar ƙarfe.'
\v 14 Gama Yahweh Mai runduna, Allah na Isra'ila, ya faɗi haka: na ɗora karkiyar ƙarfe a bisa wuyan dukkan waɗannan al'ummai domin su bauta wa Nebukadnezza sarkin Babila, kuma zasu bauta mashi. Na kuma bashi bisashen jeji dake cikin gonaki domin yayi mulki a kansu."
\s5
\v 15 Kuma annabi Irmiya ya cewa annabi Hananiya, "Ka saurara Hananiya! Yahweh bai aiko ka ba, amma kai da kanka kasa mutanen nan su gaskata ƙarya.
\v 16 Saboda haka Yahweh ya faɗi wannan: duba, ina gab da aika ka daga wannan duniya. A wannan shekarar zaka mutu, tunda kayi shelar tawaye ga Yahweh."
\v 17 A cikin watan bakwai na wannan shekara, annabi Hananiya ya mutu.
\s5
\c 29
\cl Sura 29
\p
\v 1 Waɗannan ne maganganun dake cikin littafin da annabi Irmiya ya aika daga Yerusalem zuwa ga ragowar dattawan daga cikin kamammun da kuma firistoci, da annabawa, da dukkan mutanen da Nebukadnezza ya tura bauta daga Yerusalem zuwa Babila.
\v 2 Wannan ya faru ne bayan da aka aika da sarki Yehoyacin, da mahaifiyar sarki, da manyan dagatai, da shugabannin Yahuda da Yerusalem, da masu sana'o'in hannu daga Yerusalem.
\v 3 Ya aika da wannan littafi ne ta hannun Elasa ɗan shafan da Gemariya ɗan Hilkiya waɗanda Hezekaya, sarkin Yahuda, ya aika ga Nebukadnezza sarkin Babila.
\s5
\v 4 Littafin yace, "Yahweh Mai runduna, Allah na Isra'ila, ya faɗi wannan ga dukkan kamammu waɗanda nasa suka tafi bauta daga Yerusalem zuwa Babila,
\v 5 'Ku gina gidaje ku zauna a cikinsu. Ku shuka gonaki kuci amfaninsu.
\s5
\v 6 Ku auri mataye ku haifi 'ya'ya maza da mata. Ku aurowa 'ya'yanku maza mataye, ku aurar da 'ya'yanku mata ga mazaje. Bari su haifi 'ya'ya maza da mata kuma ku ƙaru ta haka ba zaku zama 'yan kaɗan ba.
\v 7 Ku biɗi salamar birnin da na aika daku bauta, ku yi roƙo gare ni a madadinsa tunda zaku kasance da salama idan yana cikin salama.'
\s5
\v 8 Gama Yahweh Mai runduna, Allah na Isra'ila, Ya faɗi wannan, 'Kada ku bar annabawanku dake zaune a tsakaninku da masu sihirinku su ruɗe ku, kada kuma ku saurari mafarke-mafarken da ku da kanku kuke yi.
\v 9 Gama suna ruɗin ku cikin anabcin da suke yi a cikin sunana. Ban aike su ba - wannan furcin Yahweh ne.'
\s5
\v 10 Gama Yahweh ya faɗi wannan 'Idan Babila ta yi mulkinku har shekaru saba'in, zan taimake ku in aiwatar da maganata mai nagarta game da ku in sake maido da ku a wannan wuri.
\v 11 Gama ni da kaina na san irin shirye-shiryen da nake da su dominku - wannan furcin Yahweh ne- shirye-shirye na salama ba na bala'i ba, domin in baku gaba mai kyau da bege.
\s5
\v 12 Daga nan zaku yi kira a gare ni, zaku je ku yi addu'a a gare ni, zan kuma saurare ku.
\v 13 Gama zaku neme ni ku kuma same ni, tunda zaku neme ni da dukkan zuciyarku.
\v 14 Daga nan zan samu gare ku - wannan furcin Yahweh ne - zan kuma maido da kadarorinku; zan tattaro ku daga cikin dukkan al'ummai da wuraren da na warwatsar da ku - wannan furcin Yahweh ne - gama zan maido da ku wannan wuri daga inda nasa kuka tafi bauta.'
\s5
\v 15 Tunda kunce Yahweh ya tado maku da annabawa a Babila,
\v 16 Yahweh ya faɗi wannan game da wanda ke zaune bisa kursiyin Dauda da dukkan mutanen da ke zaune a cikin birnin, 'yan'uwanku waɗanda basu tafi tare da ku cikin bauta ba -
\v 17 Yahweh Mai runduna ya faɗi haka, 'Duba, ina gab da aiko da takobi, da yunwa da cuta a kansu. Gama zan maishe su kamar ruɓaɓɓen ɓauren da ba a iya ci.
\s5
\v 18 Daga nan zan runtume su da takobi, da yunwa, da annoba in maida su abin tsoratarwa ga dukkan mulkokin duniya.-abin ƙyama, abin la'ana da tsãki, abin kunya cikin dukkan al'ummai inda na warwatsa ta.
\v 19 Wannan saboda basu saurari maganata ba ne - wannan furcin Yahweh ne-wanda na aika masu ta wurin bayina annabawa. Na aike su sau da yawa, amma baku saurara ba-wannan furcin Yahweh ne.'
\s5
\v 20 Domin wannan ku da kanku ku saurari maganar Yahweh, dukkanku 'yan bautar da ya kora daga Yerusalem zuwa Babila,
\v 21 Yahweh Mai runduna, Allah na Isra'ila, ya faɗi wannan game da Ahab ɗan Kolaiya da Zedekaya ɗan Ma'ãseya, waɗanda suke yi maku anabcin ƙarya a cikin sunana: Duba, ina gab da sanya su cikin hannun Nebukadnezza sarkin Babila. Zaya kashe su a kan idanun ku.
\s5
\v 22 Daga nan za a furta la'ana game da waɗannan mutane daga bakin ɗaurarrun Yahuda da ke Babila. La'anar zata ce: Dãma Yahweh ya maida kai kamar Zedekaya da Ahab, waɗanda sarkin Babila ya gashe cikin wuta.
\v 23 Wannan zaya faru ne saboda abubuwan kunya da suka aikata a Isra'ila da suka yi zina da matayen maƙwabtansu suka kuma furta maganganun ƙarya a cikin sunana, abubuwan da ban taɓa umurtar su ba su faɗa. Gama Ni ne na sani; Ni ne shaida-wannan furcin Yahweh ne."'
\s5
\v 24 Game da Shemaiya Nehelamiye, ka faɗi wannan:
\v 25 Yahweh Mai runduna, Allah na Isra'ila, ya faɗi wannan: Domin ka aika da wasiƙu a cikin sunanka zuwa ga dukkan mutanen Yerusalem, zuwa ga Zefaniya ɗan Ma'ãseiya firist, da dukkan firistoci, kãce,
\v 26 Yahweh ya maida kai firist a maimakon Yehoaida firist, domin kayi shugabancin gidan Yahweh. Kai ne ke mulkin dukkan mutanen dake girgije-girgije suna maida kansu annabawa. Sai ka sanya su a turu da sarƙoƙi.
\s5
\v 27 To yanzu, me yasa baka tsautawa Irmiya na Anatot ba, wanda ya maida kansa annabi mai tsayayya da kai?
\v 28 Gama ya aika mana a Babila yana cewa, 'Lokaci ne mai tsawo za ayi. Ku gina gidaje ku zauna a ciki, ku shuka gonaki ku ci amfaninsu.""'
\v 29 Zefanaya firist ya karanta wannan wasiƙa a kunnen annabi Irmiya.
\s5
\v 30 Sai maganar Yahweh tazo ga Irmiya, cewa,
\v 31 "Ka aika magana ga dukkan 'yan bauta kace, 'Yahweh ya faɗi wannan game da Shemaiya Nehelamiye: Saboda Shemaiya yayi maku anabci wanda Ni da kaina ban aike shi ba, kuma yasa kun gaskata ƙarya,
\v 32 Domin wannan Yahweh ya faɗi haka: Duba, Ina gab da horon Shemaiya Nehelamiye da zuriyarsa. Ba za a sami wani mutum da zaya tsaya masa ba a cikin mutanen nan. Ba zai ga alherin da zan yiwa mutanena ba - wannan furcin Yahweh ne - Gama yayi shelar tawaye gãba da Yahweh."'
\s5
\c 30
\cl Sura 30
\p
\v 1 Maganar da ta zo wa Irmiya daga Yahweh, cewa,
\v 2 "Ga abin da Yahweh, Allah na Isra'ila, yace, 'Ka rubutawa kanka a littafi dukkan maganganun dana furta maka a littafi.
\v 3 Gama duba, kwanaki suna zuwa - wannan ne furcin Yahweh - da zan maido da kaddarorin mutanena, Isra'ila da Yahuda. Ni, Yahweh, Na faɗi wannan. Gama zan maido da su ƙasar da na ba kakanninsu, zasu kuma mallake ta."'
\s5
\v 4 Waɗannan ne maganganun da Yahweh ya furta game da Isra'ila da Yahuda,
\v 5 "Gama Yahweh ya faɗi wannan, 'Munji muryar rawar jiki da fargaba bata salama ba.
\s5
\v 6 Ku yi tambaya ku ji ko Namiji na haihuwar ɗa. To yaya naga kowanne mutum mai ƙuruciya da hannu a kwankwaso kamar macen da zata haihu? Yaya fuskokinsu suka koɗe?
\v 7 Kaito! Gama wannan rana babba ce, babu wata kamar ta. Zata zama lokacin fargaba domin Yakubu, amma za a cece shi daga ita.
\s5
\v 8 Gama zaya kasance a wannan rana - wannan furcin Yahweh ne Mai runduna - zan karya karkiyar daga wuyan ku, zan ɓalle sarƙoƙinku, domin bãƙi ba zasu sake bautar da ku ba.
\v 9 Amma zasu yi sujada ga Yahweh Allahnsu su kuma bautawa Dauda sarkinsu, wanda zan naɗa sarki a kansu.
\s5
\v 10 To kai, Yakubu bawana, kada kaji tsoro - wannan furcin Yahweh ne - kada kuma ka firgita, Isra'ila. Gama duba, Ina gaf da maido da kai daga nesa, Zuriyarka kuma daga ƙasar bauta. Yakubu zai dawo ya zauna cikin salama; za a kãre shi, kuma babu sauran tsoratar wa.
\v 11 Gama ina tare da ku - wannan furcin Yahweh ne - domin in cece ku. Daga nan zan kawo cikakken ƙarshen dukkan al'ummai inda na warwatsar da ku. Amma tabbas bazan kawo ƙarshenku ba, koda yake na horar da ku bisa adalci kuma tabbas bazan barku babu horo ba.'
\s5
\v 12 Gama Yahweh ya faɗi wannan, 'Rauninku ba ya warkuwa; rauninku ya sami lahani.
\v 13 Babu wanda za yayi roƙo domin ku; babu wani magani da zai warkar da rauninku.
\s5
\v 14 Masoyanku dukka sun manta da ku. Ba zasu neme ku ba, gama na yi maku rauni da raunin maƙiyi da kuma horon ubangida mai mugunta saboda kurakuranku masu yawa da zunubanku marasa ƙirguwa.
\v 15 Me yasa kuke neman taimako domin rauninku? zafinku baya warkuwa. Saboda kurakuranku masu yawa da zunubanku marasa ƙirguwa, na yi maku waɗannan abubuwa.
\s5
\v 16 Domin wannan duk waɗanda ke cinye ku za a cinye su, kuma dukkan magabtanku zasu tafi cikin bauta. Domin dukkan waɗanda suka washe ku za su zama abin washewa, kuma dukkan waɗanda suka maida ku ganima zan maida su ganima.
\v 17 Gama zan kawo warkarwa gare ku; zan warkar da ku daga raunukanku - wannan furcin Yahweh ne - zan yi wannan saboda sun kira ku: Yasassu. Babu wanda ya kula da wannan Sihiyonar."'
\s5
\v 18 Yahweh ya faɗi wannan, "Duba, Ina gab da maido da kaddarorin rumfunan Yakubu in kuma ji tausayin gidajensu. Daga nan za a gina birni a bisa rusassun wurarensu, mafaka mai ƙarfi kuma zata kasance inda take a dã.
\v 19 Daganan waƙar yabo da ƙarar shagulgula zasu fito daga gare su, gama zan ƙãra su ba kuma zan rage su ba; zan darjanta su domin kada su wulaƙanta.
\s5
\v 20 Daga nan mutanensu zasu zama kamar dã, taronsu kuma zaya tabbata a gabana yayin da zan horar da masu tsananta masu a yanzu.
\v 21 Shugabansu zaya fito daga cikin su. Zaya ɓullo daga cikin su yayin da zan jawo shi kusa yayin da kuma ya matso gare ni. Idan ban yi haka ba wane ne zai iya zuwa kusa da ni? - wannan furcin Yahweh ne.
\v 22 Daganan zaku zama mutanena, ni kuma in zama Allahnku.
\s5
\v 23 Duba, iskar fushin Yahweh, da hasalarsa, tana fita waje. Iska ce marar tsaitsayawa. Zata yi guguwa bisa kawunan mutane masu mugunta.
\v 24 Fushin Yahweh ba zai dawo ba har sai ya aiwatar kuma ya haifar da nufe-nufen zuciyarsa. A ranakun ƙarshe, zaku fahimci wannan."
\s5
\c 31
\cl Sura 31
\p
\v 1 "A wannan lokaci - wannan furcin Yahweh ne- Zan zama Allahn dukkan iyalan Isra'ila, su kuma zasu zama mutanena."
\v 2 Yahweh ya faɗi wannan, "Mutanen da zuka tsira daga takobi sun sami tagomashi a jeji; zan fita in bayar da hutawa ga Isra'ila."
\v 3 Yahweh ya bayyana gare ni a baya kuma yace, "Na ƙaunace ka, Isra'ila, da madawwamiyar ƙauna. Saboda haka na jawoka zuwa gare ni da amintaccen alƙawari.
\s5
\v 4 Zan sake gina ki domin ki ginu, budurwa Isra'ila. Zaki sake ɗaukar tamburanki ki fita da raye-rayen murna.
\v 5 Zaki sake dasa gonakin inabi a tsaunukan samariya; manoman zasu dasa kuma suyi amfani da 'ya'yan.
\v 6 Gama rana tana zuwa wadda masu tsaron tsaunukan Ifraim zasu yi shela, 'Ku tashi, mu tafi Sihiyona ga Yahweh Allahnmu.'
\s5
\v 7 Gama Yahweh ya faɗi wannan, "Ku yi sowa ta farinciki game da Yakubu! Ku yi sowa cikin jindaɗi game da manyan mutanen al'ummai! Bari aji yabo. Ku ce, 'Yahweh ya ceci mutanensa, ragowar Isra'ila.'
\s5
\v 8 Duba, ina gab da kawo su daga ƙasashen arewa. Zan tattaro su daga sassan duniya mafi nisa. Makaho da gurgu zasu kasance a cikin su; Mataye masu ciki da waɗanda ke kusa da haihuwa zasu kasance tare da su. Babban taro ne zaya dawo a nan.
\v 9 Za su zo da kuka; zan bishe su yayin da sukeyin roƙo. Zansa suyi tafiya zuwa maɓulɓulan ruwa a bisa miƙaƙƙiyar hanya. Ba zasu yi tuntuɓe akai ba, gama zan zama Uba ga Isra'ila, Ifraim kuma zaya zama ɗan farina."
\s5
\v 10 Ku saurari maganar Yahweh, al'ummai. Ku yi rahoto har ga ƙasashen kurmi dake nesa. Ku al'ummai dole ku ce, 'Wanda ya warwatsa Isra'ila yana tattara ta kuma yana tsaronta kamar yadda makiyayi ke tsaron tumakinsa.'
\v 11 Gama Yahweh ya ceto Yakubu ya kuma fanso shi daga hannun wanda yafi ƙarfinsa sosai.
\s5
\v 12 Daga nan zasu zo su yi farinciki bisa tuddan Sihiyona. Fuskokinsu zasu haskaka saboda alherin Yahweh, bisa hatsi da ruwan inabi, bisa mai da 'ya'yan garken awakinsu da na tumaki da kuma na shanu. Gama rayuwarsu zata zama kamar fadamar da ake yiwa banruwa, ba kuma zasu ƙara jin baƙinciki ba daɗai.
\s5
\v 13 Daga nan budurwai zasu yi farinciki da rawa, samari kuma da tsofaffi zasu kasance tare. Domin zan canza makokinsu zuwa bukukuwa. Zan ji tausayin su insa su yi farinciki a maimakon baƙinciki.
\v 14 Daga nan zan mamaye rayuwar firistoci da yalwa. Mutanena zasu cika kansu da nagartata-wannan ne furcin Yahweh."
\s5
\v 15 Yahweh ya faɗi wannan: "An ji murya a Ramah, kururuwa da kuka mai ɗaci. Rahila ce ke kukan 'ya'yanta. Taƙi ta ta'azantu game da su, gama basu a raye."
\s5
\v 16 Yahweh ya faɗi wannan, "Ki tsai da muryarki daga kuka idanunki kuma daga hawaye; gama akwai sakamako game da aikinki - wannan ne furcin Yahweh - 'ya'yanki zasu dawo daga ƙasar maƙiya.
\v 17 Akwai bege domin gabanki - wannan furcin Yahweh ne- zuriyarki zasu dawo cikin kan iyakokinsu."
\s5
\v 18 Babu shakka naji bakincikin Ifraim, 'Ka horar da ni, kuma na horu kamar maraƙin da ba horarre ba. Ka maido da ni kuma zan sami maiduwa, gama kai ne Yahweh Allahna.
\v 19 Gama bayan na juyo zuwa gare ka, nayi nadama; bayan na horu, na mari cinyata. Na ji kunya kuma na ƙasƙantu, gama na ɗauki tsarguwar ƙuruciyata.'
\v 20 Ifraimu ba ɗa na ne mai daraja ba? Ba ƙaunataccena ba ne, ɗan da nake jin daɗinsa? Gama duk sa'ad da na yi maganar tsayayya da shi, babu shakka ina tunawa da shi a raina da ƙauna. Ta haka zuciyata ke marmarin sa. Babu shakka zanji tausayin sa - wannan furcin Yahweh ne."
\s5
\v 21 Ku kafawa kanku alamun hanya. Ku sanyawa kanku alamun jagora. Ku shirya tunaninku a tafarki mai kyau, hanyar da zaku bi. Ku dawo, budurwan Isra'ila! Ku dawo cikin waɗannan biranen naku.
\v 22 Har yaushe zaki ci gaba da shakka, ɗiya marar aminci? Gama Yahweh ya halicci wani sabon abu a duniya - mace ta kewaye namiji maji ƙarfi.
\s5
\v 23 Yahweh Mai runduna, Allah na Isra'ila, ya faɗi wannan, "Idan na maido da mutanen zuwa cikin ƙasarsu, zasu faɗi wannan cikin ƙasar Yahuda da kuma biranenta, 'Bari Yahweh ya albarkace ka, kai wuri mai adalci inda ya ke zaune, kai dutse mai tsarki.'
\v 24 Gama Yahuda da biranenta zasu zauna tare a wurin, kamar yadda manoma da waɗanda suka fita da garkunansu.
\v 25 Gama zan bada ruwa ga gajiyayyu domin su sha, kuma zan cika dukkan sumammu."
\v 26 Bayan wannan sai na farka, sai na lura da cewa barcina ya wartsakar da ni.
\s5
\v 27 Duba, ranaku suna zuwa - wannan ne furcin Yahweh - Inda zan shuke gidajen Isra'ila dana Yahuda da zuriyoyin mutane dana bisashe.
\v 28 A baya, Na keɓe su ciki tsaro domin in tunɓuke su in yage su, in tuntsurar, in lalatar, in kuma kawo masu bala'i. Amma a kwanaki masu zuwa, zan lura da su, domin in gina su in kuma dasa su - wannan furcin Yahweh ne.
\s5
\v 29 A cikin waɗannan kwanaki babu wanda zaya sake cewa, 'Ubanni sun ci inabi masu tsami, amma haƙoran 'ya'ya ne suka dãsashe.'
\v 30 Gama kowane mutum zaya mutu cikin kurakuransa; Duk wanda ya ci inabi masu tsami, haƙoransa ne zasu dãsashe.
\s5
\v 31 Duba, kwanaki suna zuwa - wanna furcin Yahweh ne - inda zan kafa sabon alƙawari tare da gidan Isra'ila da kuma gidan Yahuda.
\v 32 Ba zaya zama kamar alƙawarin dana kafa da Ubanninsu ba a kwanakin da na ɗauko su na kamo hannusu na fito da su daga ƙasar masar. Waɗannan kwanakin ne inda suka karya alƙawarina, duk da cewa ni miji ne a gare su - wannan furcin Yahweh ne.
\s5
\v 33 Amma wannan ne alƙawarin da zan kafa da gidan Isra'ila bayan waɗannan kwanaki - wannan furcin Yahweh ne: Zan sanya shari'ata a cikinsu in rubuta ta a zukatansu, gama zan zama Allahnsu, zasu kuma zama mutanena.
\v 34 Daganan babu sauran wani mutum ya koyawa maƙwabcinsa, ko wani mutum ya koyawa ɗan'uwansa ya ce, 'Ka san Yahweh!' gama dukkan su, daga mafi ƙanƙantarsu har ya zuwa mafi girmansu, zasu san ni - wannan furcin Yahweh ne - Gama zan gafarta kurakuransu ba kuma zan sake tunawa da zunubansu ba."
\s5
\v 35 Yahweh ya faɗi wannan - shi ne wanda yake sanya rana ta haskaka da rana ya kuma jejjera wata da taurari su haskaka da dare. Shi wanda ke sanya teku na motsi raƙuman ruwanta kuma na ruri. Sunansa Yahweh Mai runduna.
\v 36 Sai idan waɗannan dawwamammun abubuwan sun ɓace daga gare ni - wannan furcin Yahweh ne- ko zuriyar Isra'ila zasu daina zama al'umma a gabana."
\s5
\v 37 Yahweh ya faɗi wannan, "Sai idan za a iya ɗaukar gwajin sammai dake nesa, sai kuma idan za a iya gano harsashin duniya dake can ƙasa, shi ne zan iya yashe da dukkan zuriyar Isra'ila saboda dukkan abin da suka yi - wannan furcin Yahweh ne."
\s5
\v 38 Duba, kwanaki suna zuwa - wannan furcin Yahweh ne - sa'ad da za a sake gina birnin domina, daga hasumiyar Hananel zuwa Ƙofar kwana.
\v 39 Daga nan layin gwajin zai fita ya ƙara nisa, zuwa tuddun Gerab da kewayen Goya.
\v 40 Dukkan kwarin gawawwaki da tokarsu, da dukkan filayen kurmi har ya zuwa Kwarin Kidron har zuwa kwanar Ƙofar Doki da ke gabas, za a keɓe domin Yahweh. Ba za a sake rusarwa ko tuntsurar da birnin ba, har abada."
\s5
\c 32
\cl Sura 32
\p
\v 1 Wannan ce maganar da ta zo wa Irmiya daga Yahweh a shekara ta goma ta sarautar sarki Zedekiya na Yahuda, a shekara ta sha takwas ta Nebukadnezza.
\v 2 A wannan lokaci, sojojin sarkin Babila sun yi wa Yerusalem sansani, Annabi Irmiya kuma yana cikin kurkukun harabar 'yan tsaro dake cikin gidan sarkin Yahuda.
\s5
\v 3 Zedekiya sarkin Yahuda ya sanya shi cikin kurkuku ya kuma ce, "Me yasa kake anabci kana cewa, 'Yahweh ya faɗi wannan: Duba, ina gab da miƙa wannan birni cikin hannun sarkin Babila, kuma zaya ci shi da yaƙi.
\v 4 Zedekiya sarkin Yahuda ba zai kubce ba daga hannun Kaldiyawa, gama babu shakka za a miƙa shi cikin hannun sarkin Babila. Bakinsa kuma za ya yi magana da bakin sarkin, idanunsa kuma zasu ga idanun sarkin.
\v 5 Za ya ɗauki Zedekiya zuwa Babila, zaya zauna a can har sai na gama horar da shi - wannan furcin Yahweh ne. Koda yake za ka yi yaƙi da Kaldiyawa, ba zaka yi nasara ba."'
\s5
\v 6 Irmiya ya ce, "Maganar Yahweh tazo gare ni, tana cewa,
\v 7 'Duba, Hanamel ɗan Shallum kawunka na zuwa wurin ka kuma zai ce, "Ka saiwa kanka gonata da ke Anatot, domin kai ne ka ke da 'yancin sayen ta.""'
\s5
\v 8 Daga nan, kamar yadda Yahweh ya furta, Hanamel, ɗan-ɗan kawuna, Yazo wuri na a harabar 'yan tsaro, sai ya ce da ni, "Ka sayi gonata dake a Anatot cikin ƙasar Benyamin, domin kai ne ke da 'yancin gãdo, kuma 'yancin saye na gare ka. Ka sai wa kanka." Daga nan na sani cewa wannan maganar Yahweh ce.
\v 9 Sai na sayi gonar da ke Anatot daga wurin Hanamel, ɗan-ɗan kawuna, sai na gwada mashi azurfar, shekel sha bakwai a nauyi.
\s5
\v 10 Sai na rubuta a takarda na hatimce ta, na kuma kawo shaidu su shaida. Sai na gwada mashi azurfar a ma gwaji.
\v 11 Sai na ɗauki takardar kammala saye da aka hatimce, bisa ga shari'a da ka'idoji, da kuma takardar kammala saye da ba a hatimce ba.
\v 12 Sai na bada hatimtacciyar takardar ga Baruk ɗan Neriya ɗan Masiyya a gaban Hanamel, ɗan kawuna, da kuma shaidun da suka sa hannu a hatimtacciyar takardar, a kuma gaban Yahudawan da ke zaune a harabar 'yan tsaron.
\s5
\v 13 Sai na bada umarni ga Baruk a gaban su. Nace,
\v 14 Yahweh Mai runduna, Allah na Isra'ila, ya faɗi wannan: Karɓi takardunnan, dukkan takardun kammala sayen da wannan da aka hatimce da waɗannan da ba a hatimce ba, sai ka sanya su a cikin tukunyar ƙasa domin suyi ƙarko na dogon lokaci.
\v 15 Gama Yahweh Mai runduna, Allah na Isra'ila, ya faɗi wannan: Za a sake sayen gidaje, da gonaki, da garkunan inabi a cikin wannan ƙasar."
\s5
\v 16 Bayan da na bada rasiɗin saye ga Baruk ɗan Neriya, sai nayi addu'a ga Yahweh nace,
\v 17 Kaito, Ubangiji Yahweh! Duba! Kai ka ɗai ka halitta Sammai da duniya ta wurin babban ƙarfinka da ɗagaggen hannunka. Babu abin da ka faɗa wanda zai gagare ka ka yi.
\v 18 Kana nuna amintaccen alƙawarinka ga dubbai kana kuma zubo da tsarguwar mutane bisa cinyoyin 'ya'yansu bayansu. Kai ne mai girma Allah mai iko kuma; Yahweh Mai runduna ne sunanka.
\s5
\v 19 Kai babba ne a hikima mai girma kuma cikin ayyuka, idanunka a buɗe suke ga dukkan hanyoyin mutane, domin kaba kowanne mutum abin da ya cancanci halinsa da ayyukansa.
\v 20 Ka yi alamu da al'ajibai a ƙasar Masar. Har yazuwa yau a nan ƙasar Isra'ila da kuma cikin dukkan 'yan adam, kasa sunanka ya zama sananne.
\v 21 Gama ka fito da mutanenka Isra'ila daga ƙasar Masar da alamu da al'ajibai, da hannu mai ƙarfi, da ɗagaggen hannu, da kuma babbar razana.
\s5
\v 22 Daga nan ka basu wannan ƙasar - wanda ka rantsewa Ubanninsu zaka basu - ƙasar dake zubo da madara da zuma.
\v 23 Sai suka shiga suka mallake ta. Amma ba su yi biyayya da muryarka ba ko suka zauna cikin biyayya da shari'arka ba. Ba su yi komai ba game da abin da ka umarce su su yi, sai ka kawo dukkan wannan bala'i a kansu.
\s5
\v 24 Duba! Tarin sansanin ya kai har birnin domin ya ci shi da yaƙi. Gama saboda Takobi, da yunwa, da annoba, an bayar da birnin cikin hannun Kaldiyawa da suke yaƙi da shi. Gama abin da kace zaya faru yana faruwa, kuma duba, kana kallo.
\v 25 Daga nan kai da kanka kace mani, "Ka sai wa kanka gona da azurfa kuma ka kawo shaidu su shaida, duk da cewar ana bayar da wannan birni a hannun Kaldiyawa."
\s5
\v 26 Maganar Yahweh ta zo ga Irmiya, tana cewa,
\v 27 Duba! Ni ne Yahweh, Allahn dukkan 'yan adam. Akwai abin da ya gagare ni in yi?
\v 28 Saboda haka Yahweh ya faɗi wannan, "Duba, ina gab da bayar da wannan birni cikin hannun Kaldiyawa da Nebukadnezza, sarkin Babila. Za ya ci shi da yaƙi.
\s5
\v 29 Kaldiyawan da ke yaƙi da birnin nan za su zo su cinna mashi wuta su ƙone shi, tare da gidajen da ke kan rufin wuraren da mutane ke yiwa Ba'al sujada suke kuma zuba baye-bayen shayarwa ga wasu alloli domin su cakune ni.
\v 30 Gama mutanen Isra'ila da Yahuda babu shakka mutane ne da ke ta aikata mugunta a gaban idanuna tun daga ƙuruciyarsu. Babu shakka mutanen Isra'ila sun ɓata mani rai ta wurin ayyukan hannuwansu - wannan furcin Yahweh ne.
\s5
\v 31 Yahweh ya furta cewa wannan birni na tunzura fushina da hasalata tun daga ranar da aka gina shi. Haka yake har zuwa wannan rana. To zan kawar da shi daga fuskata
\v 32 saboda dukkan muguntar mutanen Isra'ila da ta Yahuda, abubuwan da suka yi domin su cakune ni - su, da sarakunansu, da dagatansu, da firistocinsu, da annabawansu, da kuma kowane mutum a Yahuda da dukkan mazaunan Yerusalem.
\s5
\v 33 Sun juya mani bayansu a maimakon fuskokinsu, koda yake da ɗoki na koyar da su. Nayi ƙoƙari in koyar da su, amma babu wani cikinsu da ya saurara domin ya ɗauki gyara.
\v 34 Suka jera haramtattun gumakansu a cikin gidan da ake kira da sunana, suka gurɓata shi.
\v 35 Suka gina dogayen wurare domin Ba'al a kwarin Ben Hinnom domin su sanya 'ya'yansu maza da mata cikin wuta domin Molek. Ban umarcesu ba. Bai taɓa shiga tunanina ba cewa zasu aikata wannan abin ƙyama su sa Yahuda ya yi zunubi.'
\s5
\v 36 To saboda haka yanzu, Ni, Yahweh, Allah na Isra'ila, Na faɗi wannan game da birnin, birnin da kuke cewa, 'An bayar da shi cikin hannun sarkin Babila ta wurin takobi, da yunwa, da annoba.
\v 37 Duba, ina gab da tattaro su daga kowace ƙasa inda na kora su cikin fushina, da hasalata, da babban jin haushina, Ina gab da maido su cikin wannan wuri in kuma sa su iya zama cikin tsaro.
\s5
\v 38 Daga nan zasu zama mutanena, Ni kuma in zama Allahnsu.
\v 39 Zan basu zuciya ɗaya da hanya ɗaya na girmama ni kullum domin ya zama alheri a gare su da kuma zuriyarsu bayansu.
\v 40 Daga nan tare da su zan kafa madawwamin alƙawari, cewa bazan juya daga yi masu alheri ba. Zan sa girmamawa domi na a zukatansu, ta haka ba zasu sake juyawa daga gare ni ba.
\s5
\v 41 Daga nan zan yi farinciki wurin yi masu alheri. Da aminci zan dasa su cikin ƙasar nan da dukkan zuciyata da dukkan raina.
\v 42 Gama Yahweh ya faɗi wannan, 'Kamar yadda na kawo dukkan wannan babban bala'i a bisa mutanen nan, haka zan kawo masu dukkan abubuwan alherin da nace zan yi domin su.
\s5
\v 43 Daga nan za a sayi gonaki a cikin wannan ƙasar, wadda kuke cewa, "Wannan busasshiyar ƙasa ce, wadda babu mutum balle dabba. An bayar da ita cikin hannun Kaldiyawa."
\v 44 Za su sayi gonaki da azurfa su kuma rubuta cikin hatimtattun takardu. Zasu tattara shaidu a cikin ƙasar Benyamin, a dukkan kewayen Yerusalem da biranen Yahuda, a cikin birane a cikin garuruwan tudu da kuma ƙasashen kwari, da kuma biranen Negeb. Gama zan maido da kaddarorinsu - wannan furcin Yahweh ne."'
\s5
\c 33
\cl Sura 33
\p
\v 1 Daga nan maganar Yahweh ta zo ga Irmiya karo na biyu, yayin da yake kulle a harabar 'yan tsaro, cewa,
\v 2 "Yahweh mahalicci, ya faɗi wannan - Yahweh, wanda yake halittawa domin ya tabbatar-Yahweh ne sunansa,
\v 3 Ku kira gare ni, Ni kuma zan amsa maku. Zan nuna manyan abubuwa a gare ku, asirai da baku fahimta ba.'
\s5
\v 4 Gama Yahweh, Allah na Isra'ila, ya faɗi wannan game da gidajen da ke cikin wannan birni da gidajen sarakunan Yahuda waɗanda suka rushe saboda mamayewar sansani da takobi,
\v 5 Kaldiyawa suna zuwa su yi yaƙi su kuma cika waɗannan gidaje da gawawwakin mutane waɗanda zan kashe cikin fushina da hasalata, yayin da na ɓoye fuskata daga wannan birni saboda dukkan muguntarsu.
\s5
\v 6 Amma duba, Ina gab da kawo warkarwa da lafiya, zan warkar da su in kawo masu yalwa, salama da aminci.
\v 7 Gama zan maido da kaddarorin Yahuda da Isra'ila; Zan kuma gina su kamar da farko.
\v 8 Daga nan zan tsarkake su daga dukkan kurakuran da suka yi a gare ni. Zan gafarta dukkan kurakuran da suka yi a gare ni, da kuma dukkan hanyoyin da suka yi tsayayya a gare ni.
\v 9 Gama wannan birni zai zame mani abin farinciki, waƙar yabo da girmamawa daga dukkan al'umman duniya waɗanda zasu ji dukkan abubuwan alheri da zan yi domin shi. Daga nan zasu ji tsoro su girgiza saboda dukkan abubuwan alheri da salama da zan bayar a gare su.
\s5
\v 10 Yahweh ya faɗi wannan, 'A wannan wurin wanda yanzu kuke cewa, "Kufai ne, wurin da babu mutum balle dabba," a biranen Yahuda da kuma titunan Yerusalem waɗanda suke kufai babu mutum balle dabba, da za a sake ji a ciki
\v 11 Ƙarar farinciki da ƙarar murna, ƙarar ango, da ƙarar amarya, ƙarar waɗanda suka ce, yayin da suke kawo baye-bayen godiya ga gidan Yahweh, "Ku bada godiya ga Yahweh Mai runduna, gama Yahweh nagari ne, kuma ƙaunarsa marar kasawa ta dawwama har abada!" Gama zan maida kaddarorin ƙasar nan kamar yadda suke a dã,' inji Yahweh.
\s5
\v 12 Yahweh Mai runduna ya faɗi wannan: 'A wannan kufan wuri, inda yanzu babu mutum balle dabba-a dukkan biranen za a sami saura inda makiyaya zasu hutar da garkunansu.
\v 13 A cikin biranen da ke ƙasar tudu, da kwari, da kuma Negeb, a cikin ƙasar Benyamin da dukkan kewayen Yerusalem, da kuma cikin biranen Yahuda, garkuna kuma zasu sake bi ta ƙarƙashin hannuwan masu ƙirga su,' inji Yahweh.
\s5
\v 14 Duba! kwanaki na zuwa - wannan furcin Yahweh ne-inda zan aikata abin da na yi alƙawari game da gidan Isra'ila da kuma gidan Yahuda.
\v 15 A cikin waɗannan kwanaki da kuma cikin wannan lokaci zan sa reshen adalci ya tsiro domin gidan Dauda, zaya aiwatar da hukunci da kuma adalci a cikin ƙasar.
\v 16 A waɗannan kwanaki za a ceci Yahuda, Yerusalem kuma zata zauna cikin tsaro, gama ga yadda za a kira ta, "Yahweh ne adalcinmu."'
\s5
\v 17 Gama Yahweh ya faɗi wannan: 'Daga zuriyar gidan Dauda ba za a taɓa rasa mutum da zaya zauna a kursiyin gidan Isra'ila ba,
\v 18 ko kuwa a rasa mutum daga Lebiyawa firistoci da zaya tsaya a gabana ya ɗaga baye-baye na ƙonawa ba, ya ƙona baye-bayen abinci ba, ya kuma aiwatar da baye-baye na hatsi a dukkan lokaci."'
\s5
\v 19 Maganar Yahweh ta zo ga Irmiya, cewa,
\v 20 Yahweh ya faɗi wannan: 'Idan zaku iya karya alƙawarina da rana da dare yadda ba za a sake yin rana ko dare ba a lokuttansu,
\v 21 to zaku iya karya alƙawarina da Dauda bawana, yadda ba za a sake samun ɗan da zai zauna a kursiyinsa ba, da kuma alƙawarina da Lebiyawa Firistoci bayina.
\v 22 Kamar yadda baza a iya ƙirga rundunar sama ba, ko kuma a iya gwada yashin da ke bakin teku, hakanan zan kawo ƙaruwa ga zuriyar Dauda bawana da kuma Lebiyawa da ke bauta a gabana."'
\s5
\v 23 Maganar Yahweh ta zo ga Irmiya, cewa,
\v 24 "Ba ku yi la'akari da abin da mutanen nan suka furta ba da suka ce, 'Iyalai biyu da Yahweh ya zaɓa, yanzu ya watsar da su'? Ta wannan hanya sun wulaƙanta mutanena, suna cewa ba al'umma ba ce kuma a gaban mu.
\s5
\v 25 Ni, Yahweh, Na faɗi wannan, 'Idan da ban kafa alƙawarin rana da dare ba, ban kuma kafa dokokin sama da duniya ba,
\v 26 to shi ne zan watsar da zuriyar Yakubu da Dauda bawana, har da ba zan kawo wani daga gare su ba da za ya yi mulki bisa zuriyar Ibrahim, da Ishaku, da Yakubu ba. Gama zan maido da kaddarorinsu in nuna masu jinƙai."'
\s5
\c 34
\cl Sura 34
\p
\v 1 Maganar da ta zo wurin Irmiya daga Yahweh, lokacin da NebuKadnezza sarkin Babila da dukkan rundunarsa, tare da dukkan sarakunan duniya, su harabobin da ke a ƙarkashin ikonsa, kuma dukkan mutanensu suna zuwa yaƙi gãba da Yerusalem da dukkan biranenta, cewa:
\v 2 'Yahweh, Allah na Isra'ila, ya faɗi wannan: Jeka ka yi magana da Zedekiya sarkin Yahuda ka kuma ce masa, 'Yahweh ya faɗi wannan: Duba, ina gab da miƙa wannan birni cikin hannun sarkin Babila. Zai ƙone shi.
\v 3 Ba zaka tsira daga hannunsa ba, gama lallai za a kama ka a miƙa ka a cikin hannunsa. Idanunka za su dubi idanun sarkin Babila; zai yi magana da kai fuska da fuska yayin da kake tafiya zuwa Babila.'
\s5
\v 4 Saurari maganar Yahweh, Zedekiya sarkin Yahuda! Yahweh ya faɗi wannan game da kai, 'ba za ka mutu ta hanyar takobi ba.
\v 5 Za ka mutu cikin salama. Kamar yadda aka yi wa kakanninka jana'izar ƙonawa, sarakuna magabatan ka, haka za su ƙone jikinka. Za su ce, "kaito, shugaba!" Za su yi maka makoki. Yanzu dai na faɗi_ wannan furcin Yahweh ne."
\s5
\v 6 Sai Irmiya annabi ya furta wa Zedekiya sarkin Yahuda dukkan waɗannan maganganu a Yerusalem.
\v 7 Rundunar sarkin Babila suka yi yaƙi da Yerusalem da dukkan sauran biranen Yahuda: Lakish da Azeka. Waɗannan biranen Yahuda sun kasance kamar birane masu tsaro mai ƙarfi.
\s5
\v 8 Maganar da ta zo ga Irmiya daga wurin Yahweh bayan da Zedekiya sarki ya yi alƙawari da dukkan mutanen Yerusalem, domin ya furta 'yanci gare su da
\v 9 cewa bari kowane ya 'yantar da bawansa Bayahude, namiji da ta mace, wato mutum na iya ɗaukan bawa Ba-yahude, wanda ya ke ɗan uwansa.
\s5
\v 10 Sai dukkan shugabanni da mutanen suka ɗauki alƙawari kowannensu da cewa su 'yantar bayinsu maza da mata domin kada su sake zama bayi. Suka yi biyayya su ka 'yantar su.
\v 11 Amma bayan haka sai suka canza zuciyarsu. Suka dawo da bayin da suka 'yantar. Suka tilasta masu su sake zama bayi.
\s5
\v 12 Sai maganar Yahweh ta zo ga Irmiya, cewa,
\v 13 "Yahweh, Allah na Isra'ila, yana cewa, 'Ni da kaina na yi alƙawari da ubanninku a ranar da na fito da su daga ƙasar Masar, daga gidan bauta. A wannan lokaci ne na ce,
\v 14 A duk ƙarshen kowacce shekara bakwai, kowanne mutum dole ya 'yantar da ɗan'uwansa, BaIbrane wanda ya sayar da kansa gare ka ya kuma yi maka bauta na shekaru shida. Ka sake shi ya tafi cikin 'yanci." Amma ubanninku ba su saurare ni ba ko su ba da kunnuwansu gare ni.
\s5
\v 15 Yanzu ku da kanku kuka tuba ku ka fara ayyukan da ke dai-dai a gabana. Ku ka furta yanci, kowanne mutum ga maƙwabcinsa, kuma ku ka yi alƙawari a gabana a wannan gida da ake kiransa da sunana.
\v 16 Amma kuka juya ku ka ƙazamtar da sunana; kuka sa kowanne mutum ya dawo da bayinsa maza da mata, waɗanda kuka 'yantar domin su tafi inda ransu ke so. Ku ka tilasta masu su sake zama bayinku.'
\s5
\v 17 Saboda haka Yahweh ya faɗi wannan, 'Ku da kanku ba ku saurare ni ba. Dama kun furta 'yanci, kowannen ku, zuwa ga 'yan'uwanku da dangi Isra'ilawa. Don haka duba! Ina dab da furta 'yanci gare ku--- wannan furcin Yahweh ne- 'yanci ga takobi, ga annoba, da yunwa, gama zan maishe ku abin tsoro a fuskar kowacce masarauta a duniya.
\v 18 Sa'an nan zan hori mutanen da suka karya alƙawarina, waɗanda suka ƙi su kiyaye maganganun wannan alƙawari wanda suka ɗauka a gabana a lokacin da suka yanka bajimi kashi biyu suka kuma ratsa tsakanin kason,
\v 19 daga nan sai shugabannin Yahuda da na Yerusalem, da bãbãnni da kuma firistoci, da kuma dukkan mutanen ƙasar suka ratsa tsakanin bajimin.
\s5
\v 20 Zan ba da su cikin hannun maƙiyansu da kuma cikin hannun waɗanda suke neman rayukansu. Jikkunansu zasu zama abinci ga tsuntsayen sama da kuma namomin jeji a duniya.
\v 21 Haka zan ba da Zedekiya sarkin Yahuda da shugabanninsa cikin hannun makiyansu da kuma cikin hannun waɗanda suke neman ransu, da kuma cikin hannun rundunar sarkin Babila da ya tashi tsaye gãba da ku.
\v 22 Duba, ina dab da bãda ummarni--- wannan furcin Yahweh ne-- kuma zan dawo da su zuwa ga wannan birni su kuma yaƙe shi su kuma karɓe shi, su kuma ƙona shi. Gama zan juyar da birnin Yahuda zuwa yasassun kufai inda ba za a sami mazauna cikinsa ba."
\s5
\c 35
\cl Sura 35
\p
\v 1 Maganar da ta zo wurin Irmiya daga wurin Yahweh a kwanakin Yehoiyakim ɗan Yosiya sarkin Yahuda, cewa,
\v 2 "Jeka wurin iyalin Rekabawa ka yi magana da su. Sai ka kawo su zuwa gidana, cikin ɗaya daga cikin ɗakunan da ke can, sai ka ba su inabi su sha."
\s5
\v 3 Sai na ɗauki Ya'azaniya ɗan Irmiya ɗan Habazziniya tare da 'yan'uwansa, dukkan 'ya'yansa, da dukkan iyalin Rekabawa.
\v 4 Sai na kawo su zuwa gidan Yahweh, zuwa cikin ɗakunan 'ya'yan Hanan ɗan Igdaliya, mutumin Allah. Waɗannan ɗakunansu na kurkusa da ɗakunan shugabanni, wanda ke sama da ɗakin Ma'aseiya ɗan Shallum, mai tsaron ƙofa.
\s5
\v 5 Sai na ajiye kwanuka da kofuna cike da inabi a gaban Rekabawa na ce masu, "Ku sha inabi."
\v 6 Amma suka ce, "ba za mu sha inabi ba, gama kakanmu, Yonadab ɗan Rekab, ya umurcemu, 'Kada ku sha kowanne inabi, ko ku ko zuriyarku, har abada.
\v 7 Kuma, kada ku gina gidaje, ko ku shuka iri, ko ku shuka gonakin inabi; wannan ba na ku ba ne. Gama dole ku zauna cikin bukkoki dukkan kwanakinku, domin ku rayu da kwanaki masu yawa a cikin ƙasar da kuke zaman baƙunci.'
\s5
\v 8 Mun yi biyayya da muryar Yonadab ɗan Rekab, kakanmu, cikin dukkan abin da ya umurce mu, da kada mu sha inabi a duk kwanakinmu, mu, da matayenmu, da 'ya'yanmu, da kuma 'ya'ya matanmu.
\v 9 Ba zamu taɓa gina gidaje mu zauna ciki ba, ko mu yi gonar inabi, ko fili, ko mu ajiye iri wurinmu.
\v 10 Mun daɗe da zama a cikin bukkoki kuma mun yi biyayya mun kuma aiwatar da dukkan abin da Yonadab kakanmu ya umurce mu.
\v 11 Amma da Nebukadnezza sarkin Babila ya kawo farmaki ga ƙasar, muka ce, 'Zo, dole ne mu je Yerusalem domin mu tsira daga rundunar Kaldiyawa da Aremiyawa.' Shi ya sa mu ke zama a Yerusalem."
\s5
\v 12 Sai maganar Yahweh ta zo ga Irmiya, cewa,
\v 13 "Yahweh mai runduna, Allah na Isra'ila, ya faɗi haka, 'Ka je ka ce da jama'ar Yahuda da mazauna Yerusalem, "Ba za ku karɓi gyara ku kuma saurari maganata ba?--- wannan shi ne furcin Yahweh.
\v 14 Maganganun Yonadab ɗan Rekab da ya yi wa 'ya'yansa a matsayin umurni, kada su sha kowanne inabi, an yi la'akari da haka har zuwa yau. Sun yi biyayya da umurnin kakansu. Amma a nawa, Ni da kai na ina ta naciya wurin shaida maku, amma ba ku saurare ni ba.
\s5
\v 15 Na aika zuwa gare ku dukkan bayina, su annabawa. Na yi naciya da aiken su su ce, 'Bari kowanne mutum ya juyo ga barin muguwar hanyarsa ya kuma aikata ayyuka na gari; kada wani ya sake yin tafiya bisa ga tafarkin wasu alloli ko ya kuma yi masu sujada. A maimakon haka, ku dawo zuwa ga ƙasar da na ba ku da kuma kakanninku.' Duk da haka ku ka ƙi ku saurare ni ko ku bada hankalinku gare ni.
\v 16 Domin zuriyar Yonadab ɗan Rekab sun kula da umurnin kakansu da ya ba su, amma waɗannan jama'a suka ƙi su saurare ni."
\s5
\v 17 Sai Yahweh, Allah mai runduna da kuma Allah na Isra'ila, ya faɗi haka, 'Duba, Ina kawo masifa bisa Yahuda da kuma bisa kowanne mai zama cikin Yerusalem, dukkan masifar da na furta game da su domin na yi magana da su, amma ba su saurara ba; Na yi kira gare su, amma ba su amsa ba."'
\s5
\v 18 Irmiya ya cewa iyalin Rekabawa, "Yahweh mai runduna, Allah na Isra'ila, na faɗin haka: Kun saurari umurnan Yonadab kakanku kuka kuma yi biyayya da su dukka- kun yi biyayya da dukkan abin da ya dokace ku ku yi-
\v 19 sai Yahweh mai runduna, Allah na Isra'ila, ya faɗi wannan, 'A kullum za a sami wani daga zuriyar Yonadab ɗan Rekab da zai bauta mani."'
\s5
\c 36
\cl Sura 36
\p
\v 1 Sai ya kasance a cikin shekara ta huɗu ta Yehoyakim ɗan Yosiya sarkin Yahuda, da wannan maganar ta zo ga Irmiya daga Yahweh, ya kuma ce,
\v 2 "Ka ɗaukar wa kanka naɗaɗɗen littafi ka rubuta dukkan maganar da na faɗa maka game da Is'raila da Yahuda, da kowacce al'umma. Ka yi haka da duk abin da na faɗa tun daga zamanin Yosiya har zuwa yau.
\v 3 Watakila jama'ar Yahuda za su saurara da dukkan masifar da na yi niyyar kawo wa bisan su. Watakila kowanne zai juyo daga barin muguwar hanyarsa, da haka zan gafarta kurakuransu da zunubansu."
\s5
\v 4 Sai Irmiya ya kira Baruk ɗan Neriya, sai kuma Baruk ya yi rubutu cikin naɗadɗen littafi, sa'ada da Irmiya ya ke magana, dukkan maganganun Yahweh da aka faɗa masa.
\v 5 Bayan wannan Irmiya ya bada umurni ga Baruk. Ya ce, "Ina cikin kurkuku kuma ba zan iya zuwa gidan Yahweh ba.
\v 6 Saboda haka sai ka tafi ka karanta daga cikin naɗaɗɗen littafin da ka rubuta daga maganar da na faɗa. A ranar azumi, dole ne ka karanta maganganun Yahweh jama'a suna sauraro cikin gidansa, haka kuma a cikin kunnuwan dukkan Yahuda waɗanda suka fito daga birane. Furta waɗannan maganganu a gare su.
\s5
\v 7 Wataƙila roƙonsu na jinkai kai zuwa ga Yahweh. Wataƙila kowannen su zai juyo daga muguwar hanyarsa, da yake fushi da hasalar da Yahweh ya furta game waɗannan mutane masu zafi ne."
\v 8 Sai Baruk ɗan Neriya ya aiwatar da dukkan abin da Irmiya annabi ya doka ce shi ya yi. Ya karanta maganganun Yahweh da babbar murya a cikin gidan Yahweh.
\s5
\v 9 Sai ya zama kuma a cikin shekara ta biyar ga watan tara na Yehoiyakim ɗan Yosiya, sarkin Yahuda, sai dukkan jama'ar Yerusalem da kuma mutanen da suka zo Yerusalem daga biranen Yahuda suka yi shelar azumi don girmama Yahweh.
\v 10 Sai Baruk ya karanta maganganun Irmiya da ƙarfi a cikin gidan Yahweh, daga cikin ɗakin Gemariya ɗan Shafan marubuci, a cikin harabar da ke bisa, dab da mashigin ƙofa ta gidan Yahweh. Ya yi wannan a kunnuwan dukkan jama'a.
\s5
\v 11 Yanzu Mikaiya ɗan Gemaraya ɗan Shafan ya ji dukkan maganganun Yahweh daga cikin naɗaɗɗen littafi.
\v 12 Ya gangara zuwa gidan sarki, zuwa ga ɗakin sakatare. Duba, dukkan shugabanni na nan zaune: Elishama sakatare, da Delaya ɗan Shemaya, da Elnatan ɗan Akbor, da Gemaraya ɗan Shafan, da kuma Zedekiya ɗan Hananiya, da dukkan shugabanni.
\s5
\v 13 Sai Mikaiya ya kawo masu rahoton dukkan maganganun da ya ji Baruk ya karanta da ƙarfi jama'a suna saurare.
\v 14 Sai dukkan shugabanni suka aiki Yehudi ɗan Netanaya ɗan Shelemaya ɗan Kushi, zuwa ga Baruk. Yehudi ya ce wa Baruk, "Ɗauki naɗaɗɗen littafin cikin hannunka, naɗaɗɗen littafin da ka karanta ga sauraron jama'a, ka kuma zo." Sai Baruk ɗan Neraya ya ɗauki naɗaɗɗen littafin cikin hannunsa ya tafi wurin shugabannin.
\v 15 Sai suka ce masa, "Zauna ka kuma karanta muna jinka." Sai Baruk ya karanta naɗaɗɗen littafin.
\s5
\v 16 Sai ya zama sa'ad da suka ji dukkan waɗannan maganganu, kowanne mutum ya juya yana kallon na kusa da shi cikin tsoro suka ce wa Baruk, "Dole ne mu kai rohoton dukkan waɗannan maganganu ga sarki."
\v 17 Sai su ka tambayi Baruk, "Gaya mana, ta yaya ka rubuta dukkan waɗannan maganganu daga bakin Irmiya?
\v 18 Baruk ya ce masu, "Ya furta dukkan maganganun gare ni, ni kuma na rubuta su da tawada cikin wannan naɗaɗɗen littafi."
\v 19 Sai shugabannin su ka cewa Baruk, "Ka tafi, ka ɓoye kanka, da Irmiya, kuma. Kada ka bar wani ya san inda ku ke."
\s5
\v 20 Sai su ka ajiye naɗaɗɗen littafin a cikin ɗakin Elishama sakatare, kuma suka tafi wurin sarki cikin haraba suka kuma faɗawa sarki komai.
\v 21 Sa'annan sarki ya aiki Yehudi ya kawo naɗaɗɗen littafin. Yehudi ya ɗauko shi daga ɗakin Elishama sakatare. Sa'annan ya karanta wa sarki da dukkan shugabanni da suke tsayawa kusa da shi.
\v 22 Yanzu sarki na zama a gida lokacin hunturu a cikin wata na tara, kuma wutar kasko na ci a gaban shi.
\s5
\v 23 Ya zama kuwa da Yehudi ya karanta shafi uku ko huɗu, sarkin za ya datse su da wuƙa ya jefa cikin wuta cikin kaskon wuta har dukkan naɗaɗɗen littafin ya ƙare.
\v 24 Amma babu wani ko sarki ko wani daga cikin bayinsa da ya ji dukkan waɗannan maganganun ya kuma tsorata, basu kuma yayyage tufafinsu ba.
\s5
\v 25 Elnatan, da Delaya, da kuma Gemariya sun riga sun roƙi sarki da kada ya ƙona naɗaɗɗen littafin, amma ya ƙi ya sauraren su.
\v 26 Sai sarkin ya umarci Yeramil, na dangi, da Seraya ɗan Aziriyel, da kuma Shelemiya ɗan Abdil domin su damƙe Baruk sakatare da kuma Irmiya annabi, amma Yahweh ya riga ya ɓoye su.
\s5
\v 27 Sai maganar Yahweh ta zo wa Irmiya bayan sarki ya ƙona naɗaɗɗen littafin da kuma maganganun da Baruk ya rubuta daga furcin bakin Irmiya, cewa,
\v 28 "Ka koma, ka ɗaukar wa kanka wani naɗaɗɗen littafi, ka kuma rubuta cikin sa dukkan maganganun da suke a cikin naɗaɗɗen littafin na farko, wanda Yehoyakim sarkin Yahuda ya ƙona.
\v 29 Sa'annan dole ka faɗi wannan ga Yehoyakim sarkin Yahuda: 'Ka ƙona wannan naɗaɗɗen littafi, kana cewa, 'Don me ka yi rubutu a cikinsa, 'Sarkin Babila lallai zai zo ya hallakar da wannan ƙasar, gama za ya hallakar da mutum da kuma dabba a cikinta'?""'
\s5
\v 30 Saboda haka Yahweh ya faɗi wannan game da kai, Yehoiyakim sarkin Yahuda: "Babu zuriyarka da za ta taɓa zama a kan kursiyin Dauda. Game da kai, gawarka za a jefa ta a waje cikin zafin rana da kuma cikin sanyin dare.
\v 31 Gama zan yi maka horo, da zuriyarka, da kuma bayinka domin kurakuranku duka. Zan kawo a bisanka, da bisan dukkan mazamnan Yerusalem, da kuma a bisa kowanne mutum cikin Yahuda dukkan masifun da na tsoratar daku da su, amma baku ba da hankali ga wannan ba."
\s5
\v 32 Sai Irmiya ya ɗauko wani naɗaɗɗen littafi ya kuma miƙa shi ga Baruk ɗan Neriya marubuci. Baruk ya rubuta ciki daga bakin Irmiya dukkan maganganun da suka kasance a cikin naɗaɗɗen littafin da Yehoyakim sarkin Yahuda ya ƙona. Bugu da ƙari kuma, aka ƙara maganganu da yawa makamantan waɗannan cikin wannan naɗaɗɗen littafin.
\s5
\c 37
\cl Sura 37
\p
\v 1 Yanzu Zedekiya ɗan Yosiya ya yi sarauta a madadin Yehoiyacin ɗan Yehoyakim. Nebukadnezza sarkin Babila ya naɗa Zedekiya sarki bisa ƙasar Yahuda.
\v 2 Amma Zedekiya, da bayinsa, da mutanen ƙasa ba su saurari maganganun Yahweh da ya furta ta hannun Irmiya annabi ba.
\s5
\v 3 Sai sarki Zedekiya, da Yehukal ɗan Shelemiya, da kuma Zefanaya ɗan Maseya firist ya aika saƙo zuwa ga Irmiya annabi. Su ka ce, "Yi addu'a a madadinmu ga Yahweh Allahnmu."
\v 4 Yanzu Irmiya na shigowa da fitowa a cikin mutanen, gama ba a rigaya an saka shi cikin kurkuku ba.
\v 5 Rundunar Fir'auna suka fito daga Masar, sai kuma Kaldiyawa waɗanda suke kafa wa Yerusalem sansani suka ji labari game da su sai kuma su ka bar Yerusalem.
\s5
\v 6 Sai maganar Yahweh ta zo ga Irmiya annabi, cewa,
\v 7 "Yahweh, Allahn Isra'ila, ya faɗi wannan: Ga abin da za ka faɗi wa sarkin Yahuda, domin ya aike ka neman shawara wurina, 'Duba, rundunar Fir'auna, wacce ta kawo maku taimako, tana dab da komawa Masar, ƙasarta.
\v 8 Su Kaldiyawa za su dawo. Za su yaƙi wannan birni, su karɓe shi, su kuma ƙona shi.'
\s5
\v 9 Yahweh ya faɗi wannan: Kada ku ruɗi kanku kuna cewa, 'Hakika Kaldiyawan na tafiya suna barin mu,' domin ba za su tafi ba.
\v 10 Ko da ace kun ci dukkan rundunar Kaldiyawan da yaƙi da ke yaƙi da ku da har ace raunannun mutane ne aka bari cikin runfunansu, za su tashi sama su kuma ƙone wannan birnin."
\s5
\v 11 Haka ya zama lokacin da rundunan Kaldiyawa su ka bar Yerusalem lokacin da rundunar Fir'auna ke gabatowa,
\v 12 sai Irmiya ya fito Yerusalem domin ya tafi kasar Beyamin. Ya bukaci ya mallaki wani ɗan fili a nan a tsakanin mutanensa.
\v 13 Sa'ad da ya ke a bakin Ƙofar Benyamin, wani shugaban matsara na wurin. Sunansa Iriya ɗan Hananiya. Ya riƙe annanbi Irmiya gama kuma ya ce, "Kana zanzarewa zuwa ga Kaldiyawa."
\s5
\v 14 Amma Irmiya ya ce, "Wannan ba gaskiya ba ne. Ba zanzarewa na ke yi ba zuwa ga Kaldiyawa." Amma Iriya ya ƙi ya saurare shi. Ya ɗauki Irmiya ya kawo shi wurin shugabanni.
\v 15 Shugabannin suka ji haushin Irmiya. Suka yi ma sa duka suka sa shi cikin kurkuku, wanda ya ke cikin gidan Yonatan marubuci, gama sun maishe shi kurkuku.
\s5
\v 16 Sai aka sa ka Irmiya cikin kurkuku na ƙarƙashin ƙasa, inda ya zauna ranaku da yawa.
\v 17 Sai sarki Zedekiya ya aika da wani wanda ya kawo shi zuwa ga fada. A gidansa, sarkin ya tambaye shi a asirce, "Akwai wata magana daga Yahweh?" Irmiya ya amsa, "Akwai magana: Za a miƙa ka cikin hannun sarkin Babila."
\s5
\v 18 Sai Irmiya ya ce wa sarki Zedekiya, "Ta yaya na yi maka zunubi, ko bayinka, ko waɗannan mutane da har ka saka ni cikin kurkuku?
\v 19 Ina annabawanka, waɗanda suka yi maka anabci kuma suka ce sarkin Babila ba zai zo gãba da kai ko gãba da wannan birnin ba?
\v 20 Amma ka saurara yanzu, shugabana sarki! Bari roƙona shi zo gare ka. Kada ka maida ni zuwa ga gidan Yonatan marubuci, don kada in mutu a can."
\s5
\v 21 Sai sarki Zedekiya ya ba da umarni. Bayinsa suka tsare Irmiya cikin harabar matsara. Aka ba shi curin gurasa kowace rana daga layin matoya, har sai da dukkan gurasar ta ƙare cikin birnin. Haka Irmiya ya zauna cikin harabar matsaran.
\s5
\c 38
\cl Sura 38
\p
\v 1 Shefatiya ɗan Matan, da Gedaliya ɗan Fashhur, da Yehukal ɗan Shelemiya, da kuma Fashhur ɗan Malkiyah su ka ji maganganun da Irmiya ya ke furtawa ga dukkan mutanen. Yana cewa,
\v 2 "Yahweh ya faɗi haka: Duk mai zama cikin wannan birni za a kashe shi da takobi, da yunwa, da kuma annoba. Amma kowanne da ya fita zuwa ga Kaldiyawa za shi rayu. Zai tsira da ransa, shi rayu.
\v 3 Yahweh ya faɗi wannan: Wannan birni za a ba da shi ga hannun rundunar sarkin Babila, kuma za ya karɓe shi."
\s5
\v 4 Sai shugabannin suka ce wa sarkin, "Bari wannan mutum shi mutu, gama ta wannan hanya yana raunanar da hannuwan mazaje mayaƙa waɗanda suka rage a wannan birni, da kuma hannun dukkan mutane. Ya na furta waɗannan maganganu, gama wannan mutum bai kula da lafiyar waɗannan mutane ba, sai dai bala'i."
\v 5 Sai sarki Zedekiya ya ce, "Duba, yana cikin hannunku da shi ke babu sarkin da ya isa shi yi tsayayya da ku."
\s5
\v 6 Sai su ka ɗauki Irmiya su ka jefa shi cikin ramin Malkiyah, ɗan sarki. Ramin na cikin harabar masu tsaro. Suka zurara Irmiya ƙasa da igiyoyi. Babu ruwa cikin ramin, amma taɓo ne, sai kuma ya nutse ƙasa cikin taɓon.
\s5
\v 7 Yanzu Ebed Melek Ba-Kushi yana cikin ubanni na gidan sarki. Ya ji cewa an jefa Irmiya cikin rami. Yanzu sarkin yana zama a Kofar Benyamin.
\v 8 Sai Ebed Melek ya tafi daga gidan sarki ya yi magana da sarki. Ya ce,
\v 9 "Shugabana sarki, waɗannan mutane sun aikata mugunta ta yadda suka yi da Irmiya annabi. Sun jefar da shi cikin rami domin ya mutu cikinsa da yunwa, tun da babu wani abincin da ya rage cikin birnin."
\s5
\v 10 Sai sarkin ya bada umurni ga Ebed Melek Ba-Kushe. Ya ce, "Ka ɗauki shugabancin mutane talatin daga nan ka kuma ciro annabi Irmiya daga ramin kamin ya mutu."
\v 11 Sai Ebed Melek ya ɗauki shugaban waɗannan mutanen ya tafi gidan sarki, zuwa ga ɗakin ajiyar kaya na ƙarƙashin gidan. Daga nan ne ya ɗauko tsummokara da kuma koɗaɗɗun kaya sai kuma ya zurara su da igiyoyi ga Irmiya cikin ramin.
\s5
\v 12 Ebed Melek mutumin Kush ya cewa Irmiya, "Sanya tsummokaran da koɗaɗɗun kayan a ƙarƙashin hannunka da kuma bisa igiyoyin." Irmiya kuwa ya yi haka.
\v 13 Sai suka jawo Irmiya da igiyoyin. Da haka suka fito da shi daga cikin ramin. Irmiya kuma ya zauna cikin harabar masu tsaro.
\s5
\v 14 Sai sarki Zedekiya ya aika magana ya kuma kawo Irmiya annabi wurin sa, zuwa cikin mashigi na uku cikin gidan Yahweh. Sarkin ya cewa Irmiya, "Ina so in tambaye ka wani abu. kada ka hana mani amsar."
\v 15 Irmiya ya ce da Zedekiya, "Idan na amsa maka, lallai ba za ka kashe ni ba? Amma idan na ba ka shawara, ba za ka saurare ni ba."
\v 16 Amma sarki Zedekiya ya rantse wa Irmiya a asirce ya kuma ce, "Na rantse ga Yahweh mai rai, wanda ya yi mu, ba zan kashe ka ba ko in miƙa ka cikin hannuwan waɗannan mutanen nan da suke neman ranka ba."
\s5
\v 17 Sai Irmiya annabi ya cewa sarki Zedekiya, "Yahweh, Allah mai runduna, Allah na Isra'ila, ya faɗi haka: Idan ka fita zuwa ga shugabannin Babila za ka rayu kuma ba za a kone wannan birni ba. Kai da iyalin ka za ku rayu.
\v 18 Amma idan ka ƙi fita zuwa ga shugabannin sarkin Babila, to za a miƙa wannan birnin cikin hannun Kaldiyawa. Za su kona shi, kai kuma ba za ka tsira daga hannun su ba."
\s5
\v 19 Sarki Zedekiya ya cewa Irmiya, "Amma ina jin tsoron mutanen Yahuda waɗanda suka ƙaurace zuwa ga sansanin Kaldiyawa domin ana iya miƙa ni cikin hannuwansu, domin su wulaƙanta ni sosai."
\s5
\v 20 Irmiya ya ce, "Ba zasu miƙa ka cikin hannuwansu ba. Kai dai ka yi biyayya da saƙon Yahweh da nake faɗa maka, domin komai ya zamar maka lafiya lau, domin kuma ka rayu.
\v 21 Amma idan ka ƙi ka fita, wannan shi ne abin da Yahweh ya nuna mani.
\s5
\v 22 Duba! Dukkan matayen da aka rage a gidanka, sarkin Yahuda, za a fito da su zuwa ga shugabannin sarkin Babila. Waɗannan matayen za su ce maka, 'Abokananka sun ruɗe ka; sun rusar da kai. Ƙafafunka yanzu sun nutse cikin taɓo, kuma abokanka za su gudu.'
\v 23 Gama dukkan matayen ko da 'ya'yanka ma za a fito da su zuwa ga Kaldiyawa, kai kuma da kanka ba za ka tsira daga hannunsu ba. Za a kama ka ta hannun sarkin Babila, kuma za a ƙona wannan birnin."
\s5
\v 24 Sai Zedekiya ya cewa Irmiya, "Kada ka sanar da kowa game da wannan maganganu, don kada ka mutu.
\v 25 Idan shugabannin suka ji labari na yi magana da kai, idan kuma suka zo su ka ce maka, "Ka faɗi mana abin da ka faɗi wa sarki kuma kada ka ɓoye mana, ko mu kashe ka,
\v 26 sa'annan dole za ka amsa masu da cewa, na yi roƙo ne da zuciya ɗaya ga sarki da kada ya komar da ni gidan Yonatan don kada in mutu a can."
\s5
\v 27 Sai dukkan shugabannin suka zo wurin Irmiya suka tambaye shi abin da ya gaya wa sarki, shi kuma sai ya amsa masu yadda sarki ya umarce shi da ya faɗi. Sai suka daina magana da shi, domin ba su ji tattaunawar da aka yi tsakanin Irmiya da sarkin ba.
\v 28 Sai Irmiya ya zauna a cikin harabar masu tsaro har zuwa ranar da aka karɓe Yerusalem.
\s5
\c 39
\cl Sura 39
\p
\v 1 A shekara ta tara na watan goma na Zedekiya sarkin Yahuda, Nebukadnezza sarkin Babila ya zo da dukkan rundunarsa gãba da Yerusalem ya kuma kafa mata sansani.
\v 2 A shekara ta sha ɗaya da kuma wata na huɗu na Zedekiya, a rana ta tara ga wata, aka rusar da birnin.
\v 3 Sai dukkan shugabannin sarkin Babila suka zo suka zauna a ƙofa ta tsakiya: Nagal Shareza, da Samgar Samgal Nebo, da kuma Sarsekim, shugaba mai muhimmanci. Nagal Shareza shugaba ne babba kuma dukkan sauran sun zama shugabannin sarkin Babila.
\s5
\v 4 Sai ya zamana da Zedekiya sarkin Yahuda, da dukkan mayaƙan sa suka gan su, suka gudu. Suka fita da dare daga birnin ta hanyar gonar gidan sarki, ta cikin ƙofa ta tsakanin ganuwa biyun. Sarkin ya fita ta bangon hanyar Araba.
\v 5 Amma rundunar Kaldiyawa suka runtume su suka kuma cimma Zedekiya a cikin filin Kogin Yodan kwari kusa da Yeriko. Sai suka cafko shi suka kawo shi wurin Nebukadnezza, sarkin Babila, a Ribla cikin ƙasar Hamat, inda Nebukadnezza ya yanke masa hukunci.
\s5
\v 6 Sarkin Babila ya kashe 'ya'yan Zedekiya a fuskarsa a Ribla. Ya kuma kashe dukkan muhimman mutanen Yahuda.
\v 7 Sai ya cire idanuwan Zedekiya ya kuma ɗaure shi da sarƙoƙin jan karfe domin ya tafi da shi Babila.
\s5
\v 8 Sai Kaldiyawan suka ƙone gidan sarki da gidajen mutane. Suka kuma rushe ganuwar Yerusalem.
\v 9 Nebuzaradan, hafsan masu tsaron sarki, ya kwashe sauran mutanen waɗanda aka rage cikin birnin zuwa bauta. Wannan ya haɗa har da waɗanda suka yi ƙaura zuwa ga Kaldiyawa da kuma sauran mutanen waɗanda aka rage cikin birnin.
\v 10 Amma Nebuzaradan babban hafsan masu tsaron sarki ya bar sauran mutanen waɗanda suke fakirai waɗanda basu da wani abu na kansu su zauna a cikin Yahuda. Ya kuma ba su gonakin inabi da filaye a wannan rana.
\s5
\v 11 Nebukadnezza sarkin Babila ya ba da umarni game da Irmiya ga Nebuzaradan hafsan masu tsaron sarki. Ya riga ya ce,
\v 12 "Ka ɗauke shi ka kula da shi. Kada ka ji ma sa rauni. Yi ma sa duk abin da ya ce ma ka.
\v 13 Sai Nebuzaradan hafsan masu tsaron sarki, Nebushazban babban bãbãn, Nagal Shareza babban shugaba, da dukkan muhimman shugabannin sarkin Babila su ka aiki mutane waje.
\v 14 Mutanensu su ka ɗauki Irmiya daga harabar masu tsaro su ka miƙa shi cikin hannun Gedaliya ɗan Ahikam ɗan Shafan, ya kai shi gida, sai Irmiya ya zauna a tsakanin mutanen.
\s5
\v 15 Yanzu dai maganar Yahweh ta zo ga Irmiya tun ya na a tsare a cikin harabar masu tsaro, cewa,
\v 16 "Yi magana da Ebed Melek mutumin Kush ka ce, "Yahweh mai runduna, Allah na Isra'ila, ya faɗi wannan: Duba, ina dab da cika maganganuna da na furta game da wannan birni bala'i kuma ba alheri ba. Gama za su faru dukka a idanunka a wannan rana.
\s5
\v 17 Amma zan cece ka a wannan rana- wannan ne furcin Yahweh- kuma ba za a bashe ka cikin hannun mutanen da ka ke jin tsoronsu ba.
\v 18 Gama babu shakka zan tsirar da kai. Ba za ka faɗi ga takobi ba. Za ka tsira da ranka, tun da ka yarda da ni- wannan shi ne furcin Yahweh."
\s5
\c 40
\cl Sura 40
\p
\v 1 Maganar ta zo wurin Irmiya daga wurin Yahweh bayan da Nebuzaradan babban hafsan masu tsaron sarki ya sa ke shi a Rama. Ya sami Irmiya a ɗaure da sarƙoƙi a tsakiyar dukkan 'yan sarƙar Yerusalem da Yahuda waɗanda aka kwashe zuwa ga ƙasar bauta a Babila.
\v 2 Shugaban matsara ya ɗauki Irmiya ya kuma ce ma sa, "Yahweh Allahnka ya umarta wannan masifar domin wannan wurin.
\s5
\v 3 Don haka Yahweh ya kawo hakan. Ya aikata kamar yadda ya umarta, tun da ku mutanen nan kun yi ma sa zunubi kuma ba ku yi biyayya da muryar sa ba. Shi ya sa wannan abu ya faru da ku mutanen nan.
\v 4 Amma yanzu duba! Na sa ke ka yau daga sarƙokin da ke hannuwanka. Idan ka ga ya dace a idanunka ka bi ni zuwa Babila, sai ka bi ni, ni kuwa zan kula da kai. Amma idan ba ya dace a idanunka ba da ka biyo ni zuwa Babila, to kada ka yi haka. Duba dukkan ƙasar da ke a gabanka. Ka tafi duk inda ya ke da kyau da kuma dai - dai a idanunka ka tafi."
\s5
\v 5 Da Irmiya ba ya amsa ba, Nebuzaradan ya ce, "Tafi wurin Gedaliya ɗan Ahikam ɗan Shafan, wanda sarkin Babila ya ɗora wa haƙin kula da biranen Yahuda. Ka zauna da shi a tare da sauran mutanen ko ka tafi ko inda da ya yi ma ka kyau a idanunka ka tafi." Sai hafsan masu tsaron sarki ya bashi abinci da 'yar kyauta, daga nan ya sallame shi.
\v 6 Sai Irmiya ya tafi wurin Gedaliya ɗan Ahikam, a Mizfa. Ya zauna tare da shi a tsakiyar mutanen da aka bari cikin kasar.
\s5
\v 7 Yanzu wa su hafsoshin Yahuda waɗanda har yanzu su na a cikin harabar-- su da mutanensu-- su ka ji cewa sarkin Babila ya ɗora Gedaliya ɗan Ahikam, gwamna bisa ƙasar. Sun kuma sa ke ji cewa ya sa shi a matsayin mai kula da mazajen, mataye, da yara waɗanda su ne fakiran mutane a cikin ƙasar, waɗanda ba a kwashe ga hijira zuwa ƙasar Babila ba.
\v 8 Sai su ka tafi wurin Gedaliya a Mizfa. Waɗannan mutane su ne Ishmayel ɗan Netaniya; Yohanan da Yonatan, 'ya'yan Kariya; da Seraya ɗan Tanhumet; su 'ya'yan Ifai mutumin Netofatiyawa; da Ya'azaniya ɗan Ma'akatiyawa-- su da mutanensu.
\s5
\v 9 Gedaliya ɗan Ahikam ɗan Shafan ya ɗauki alƙawari da su da 'ya'yansu ya ce masu, "Ka da ku ji tsoro da za ku bauta wa shugabannin Kaldiyawa. Ku zauna a cikin ƙasar ku kuma bauta wa sarkin Babila, da haka komai zai yi maku dai - dai.
\v 10 Duba, ina zama a Mizfa domin in sami ganin Kaldiyawa da su ka zo gare mu. Sai ku girbe inabi, da kayan itatuwa na damuna, da kuma mai ku adana su a cikin dururruka. Ku zauna a biranen da ku ka mallaka."
\s5
\v 11 Sai dukkan mutanen Yahuda da ke a Mowab, a tsakanin mutanen Ammon, da kuma cikin Idom, da kuma a kowacce ƙasa su ka ji cewa sarkin Babila ya bar ragowar Yahuda su zauna, har ya aza Gedaliya ɗan Ahikam ɗan Shafan bisan su.
\v 12 Saboda haka dukkan mutanen Yahuda su ka dawo daga dukkan wuraren da aka tarwatsa su. Su ka dawo zuwa ga ƙasar Yahuda, zuwa ga Gedaliya a Mizfa. Su ka girbe inabi da amfanin itatuwa na damina mai yawan gaske.
\s5
\v 13 Yohanan ɗan Kareya da dukkan shugabannin rundunar da su ke baje cikin ƙasar su ka zo wurin Gedaliya a Mizfa.
\v 14 Su ka ce ma sa, "Ko ka sa ni da cewa Balis sarkin mutanen Ammon ya aiko Ishmel ɗan Netaniya da ya kashe ka?" Amma Gedaliya ɗan Ahikim bai yarda da su ba.
\s5
\v 15 Sai Yohanan ɗan Kareya ya yi magana a asirce da Gedaliya a Mizfa kuma ya ce, "Ka bar ni in tafi in kashe Ismayel ɗan Netaniya. Babu wanda zai sani. Don me za shi kashe ka? Don me za a bar Yahuda da aka tara maka su wartwatsu kuma ragowar Yahuda su hallaka?
\v 16 Amma Gedaliya ɗan Ahikam ya ce wa Yohanan ɗan Kareya, "Kada ka aikata wannan abu, gama ka na faɗin ƙarya ne bisa Ismayel."
\s5
\c 41
\cl Sura 41
\p
\v 1 Amma ya kasance a wata na bakwai Ismayel ɗan Netaniya ɗan Elishama, daga gidan sarauta, da waɗansu shugabanni na sarki, su ka zo su goma tare da shi wurin Gedaliya ɗan Ahikam, Mizfa. Su ka ci abinci tare a can Mizfa.
\v 2 Amma Ismayel ɗan Netaniya da mutanen nan goma da ke tare da shi su ka tashi suka farmaki Gedaliya ɗan Ahikam ɗan Shafan da takobi. Ismayel ya kashe Gedaliya, wanda sarkin Babila ya sa ya mulki ƙasar.
\v 3 Daga nan sai Ismayel ya kashe dukkan mutanen Yahudiya da ke goyon bayan Gedaliya a Mizfa da mayaƙan Kaldiyawan da ya samu a can.
\s5
\v 4 To a rana ta biyu bayan kisan Gedaliya, amma ba wanda ya sani.
\v 5 Waɗansu mutane su ka zo daga Shekem, da kuma Shilo, da Samariya su tamanin waɗanda su ka aske gemunsu, su ka kuma kece tufafinsu, su ka yayyanka jikkunansu - ɗauke da baye - baye na abinci da turaren itacen lubban a hannuwansu don su je gidan Yahweh.
\s5
\v 6 Sai Ismayel ɗan Netaniya ya tafi daga Mizfa don ya sadu da su akan hanyarsu ta komawa, suna tafe su na kuka. A lokacin da ya gansu sai ya ce da su, "Ku zo wurin Gedaliya ɗan Ahikam!"
\v 7 Sai ya zamana bayan sun zo birnin, sai Ismayel ɗan Netaliya ya yayyanka su ya zura su cikin rami, tare da mutanen da ke tare da shi.
\s5
\v 8 Amma akwai mutane goma daga cikinsu da su ka ce da Ismayel," kada ka kashe mu, don muna da tanaji a filin: da alkama, da sha'ir da mai da ruwan zuma." Don haka bai kashe su tare da abokan tafiyarsu ba.
\v 9 Rijiyar da Ismayel ya zuba gawawwakin waɗanda ya kashe ta na da girma ita ce rijiyar da sarki Asa ya haƙa don kariya daga sarkin Ba'asha na Isra'ila. sai Ismayel ɗan Netaniya ya cikata da gawawwaki.
\s5
\v 10 Abu na gaba shi ne Ismayel ya kame dukkan mutanen da ke a Mizfa, da 'ya'yan sarki 'yan mata da duk sauran mutanen da su ka ragu a Mizfa waɗanda Nebuzzradan shugaban masu tsaro ya ba Gedaliya ɗan Ahikam. To sai Ismayel ɗan Netaniya ya kame su ya tafi ya ƙetare da suzuwa wurin mutanen Ammon.
\s5
\v 11 Amma Yohannan ɗan Kareya da dukkan hafsoshin da ke tare da shi suka ji dukkan muguntar da Ismayel ɗan Netaniya ya yi.
\v 12 To sai su ka kwashi dukkan mutane don su yaƙi Ismayel ɗan Netaniya. su ka same shi a babban kwarin Gibeyon.
\s5
\v 13 Sai ya zamana a lokacin da dukkan mutanen da ke tare da Ismayel su ka ga Yohanan ɗan Kareya da dukkan hafsoshin da ke tare da shi, sai suka yi murna.
\v 14 Sai dukkan mutanen da Ismayel ya kame a mizfa su ka juya suka koma ga Yohannan ɗan Kareya.
\s5
\v 15 Amma Ismayel ɗan Netaniya ya gudu tare da mutane takwas daga Yohannan. Ya je wurin mutanen Ammon.
\v 16 Sai Yohannan ɗan Kareya da dukkan hafsoshin da ke tare da shi su ka kwashe mutanen daga Mizfa, suka kuɓutar da su daga Ismayel ɗan Netaniya. Hakan ya faru ne bayan Ismayel ya kashe Gedaliya ɗan Ahikan. Yohannan da abokan tafiyarsa su ka ɗauki ƙarfafan mazaje, da mayaƙa, da mata da yara, da bãbãnni waɗanda aka kuɓutar a Gibeyon.
\s5
\v 17 Daga nan sai su ka je su ka ɗan tsaya a Gerut Kimham, wanda ke kusa da Betelehem. Su na tafiya don su je Masar
\v 18 saboda Kaldiyawa. Suna tsoron su tunda yake Ismayel ɗan Netaniya ya kashe Gedaliya ɗan Ahikam, wanda sarkin Babila ya sa ya yi mulkin ƙasar.
\s5
\c 42
\cl Sura 42
\p
\v 1 Daga nan dukkan hafsoshin da Yohanan ɗan Keriya, da Yezaniya ɗan Hoshayiya, da dukkan mutanen tun daga ƙanana ya zuwa manya suka zo wurin annabi Irmiya.
\v 2 Su ka ce da shi, "bari kukanmu ya zo gareka.
\v 3 Kayi addu'a zuwa ga Yahweh Allahnka a madadinmu da muka ragu tun da ya ke ba mu da yawa, kamar yadda ka gani. Ka roƙi Yahweh Allahnka ya faɗa mana abin da za mu yi da kuma hanyar da za mu bi"
\s5
\v 4 Annabi Irmiya ya ce da su, "Na ji ku. Duba, zan yi addu'a ga Yahweh Allahnku kamar yadda ku ka bukata. Kuma duk amsar da Yahweh ya bayar zan faɗa muku. Ba zan ɓoye muku komai ba."
\v 5 Su ka cewa Irmiya, "Dama Yahweh ya zama amintaccen shaida na gaskiya a tsakaninmu, idan ba mu yi duk abin da Yahweh Allahn ka ya ce mu yi ba.
\v 6 Ko da mai kyau ne ko kuma mara kyau, za mu yi biyayya da muryar Yahweh Allahnmu, wanda mu ke aiken ka wurinsa, don komai ya yi mana dai - dai a lokacin da muka yi biyayya da muryar Yahweh Allanmu."
\s5
\v 7 Bayan kwana goma, maganar Yahweh ta zo wurin Irmiya.
\v 8 Sai Irmiya ya kira Yohanan ɗan Kareya da dukkan hafsoshin da ke tare da shi, da kuma dukkan mutane daga ƙanana zuwa manya.
\v 9 Sai ya ce da su, "Wannan shi ne abin da Yahweh Allah na Isra'ila - wanda ku ka aike ni wurin sa don in kai roƙonku gare shi - ya ce,
\v 10 Idan kun koma wannan ƙasar ku ka zauna to zan gina ku ba zan keta ku ba; Zan dasa ku ba zan tuge ku ba, don zan kawar da masifar da na aukar a kan ku.
\s5
\v 11 Kada ku ji tsoron sarkin Babila, wanda ku ke jin tsoro. Kada ku ji tsoron sa - wannan shi ne abin da yahweh ya furta - da shi ke Ina tare da ku don in cece ku in kuma kuɓutar da ku daga hannunsa.
\v 12 Gama zan yi maku jinkai. Zan kuma ji tausayinku, zan kuma dawo da ku ƙasarku.
\s5
\v 13 Amma in kun ce "ba za mu zauna a wannan ƙasa ba" - in ba ku saurari muryata ba, muryar Yahweh Allanku.
\v 14 In kun ce, "A a! Za mu je ƙasar Masar, inda ba za mu ga wani yaƙi ba, inda ba za mu ji ƙarar ƙaho ba, kuma ba zamu ji yunwa domin abinci ba, can za mu zauna."
\s5
\v 15 Yanzu sai ku saurari muryar Yahweh, ku da ku ka rage a Yahuda. Yahweh mai runduna, Allah na Isra'ila, Ya faɗi wannan, 'In dai har ku ka je Masar, don ku je ku zauna a can,
\v 16 To takobin da ku ke jin tsoro za ta kashe ku a can ƙasar Masar. Yunwar da ku ke damuwa a kanta yanzu za ta kora ku zuwa Masar, kuma za ku mutu a can.
\v 17 Don haka duk waɗanda su ka gudu Masar don su zauna a can za su hallaka ta wurin takobi, da yunwa, ko annoba. Kuma ba wanda zai tsira daga wannan masifar da zan aukar masu.
\s5
\v 18 Domin Yahweh mai runduna, Allah na Isra'ila, ya faɗi wannan: Kuma kamar yadda fushina ya yi ƙuna a kan mazauna Yeruselem, hakanan zan saukar da matsanancin fushina a kanku in ku ka je Masar. Za ku zama abin la'ana da reni, abin la'antawa, da abin ƙasƙantarwa, kuma ba za ku ƙara ganin wannan wurin ba.'"
\v 19 Sai Irmiya ya ce,'" Yahweh ya faɗi wannan a kanku - ku da ku ka rage a Yahuda. Kada ku je Masar! Don tabbas kun san ni sheda ne a kanku a yau.
\s5
\v 20 Domin kun yaudari kanku sosai a lokacin da ku ka aike ni ga Yahweh Allahnku ku ka ce, ka yi addu'a ga Yahweh Allahnmu dominmu. Duk abin da Yahweh Allahnmu ya ce, ka faɗa mana, za mu yi shi.'
\v 21 Domin yau na ba ku rahoto, amma ba ku saurari muryar Yahweh Allahnku ko kuma duk abin da ya aiko ni wurinku.
\v 22 To yanzu sai ku san cewa tabbas zaku mutu ta wurin takobi, da yunwa, da annoba, a wurin da kuke son ku tafi ku zauna."
\s5
\c 43
\cl Sura 43
\p
\v 1 Sai ya zamana bayan Irmiya ya gama shaidawa mutane dukkan maganar Yahweh Allahnsu wadda Yahweh Allahnsu ya faɗi masa ya faɗa.
\v 2 Azariya ɗan Hosheya, Yohanan ɗan Kareya, da dukkan mutane kangararru su ka ce da Irmiya, '"ƙarya ka ke faɗi. Yahweh Allanhmu bai aiko ka ka faɗi cewa kada ku je Masar ku zauna a can ba'
\v 3 Domin Baruk ɗan Neriya ya na zuga ka ka bada mu a hannun Kaldiyawa, don kaima ka jawo mana mutuwa ka kuma mai da mu kamammu a Babila."
\s5
\v 4 Domin haka Yohannan ɗan Kareya, da dukkan shugabannin mayaƙa da dukkan mutane su ka ƙi sauraron muryar Yahweh da ta ce su zauna a Yahuda.
\v 5 Yohanan ɗan Kareya da shugabannin mayaƙa su ka kwashe dukkan waɗanda su ka rage a Yahuda waɗanda su ka dawo daga dukkan al'uman da aka warwatsa su su zauna a cikin ƙasar Yahuda.
\v 6 Su ka kwashe maza da mata, da yara da 'ya'ya mata na sarki, da duk wanda Nebuzaradan, hafsan sarki da matsaran sarki, ya sa suka kasance tare da Gedeliya ɗan Ahikam ɗan Shafan. Hakannan su ka ɗauki Annabi Irmiya da Baruk ɗan Neriya.
\v 7 Su ka tafi zuwa ƙasar Masar, a Tafenhes, saboda ba su saurari muryar Yahweh ba.
\s5
\v 8 To sai maganar Yahweh ta zo ga Irmiya a Tafanhes, cewa,
\v 9 "Ka ɗauki manyan duwatsu a hannunka, da kuma a gaban mutanen Yahuda, ka ɓoye su a kankare a gefen hanyar zuwa ƙofar gidan Fir'auna a Tafanhes."
\v 10 Daga nan sai ka ce da su, Yahweh mai runduna, Allah na Isra'ila ya faɗi wannan, 'Duba ina gab da aika manzannina zuwa Babila a matsayin bayina. Zan kafa mulkinsa akan waɗannan duwatsu wanda kai Irmiya ka binne. Nebukadzza zai kafa daularsa a kansu.
\s5
\v 11 Domin zai zo ya kawo hari ga ƙasar Masar. Duk wanda aka ƙaddara ga mutuwa zai mutu. Duk wanda aka ƙaddara ga bauta za a ɗauke shi zuwa bauta. Duk wanda aka ƙaddara ga takobi za a bada shi ga takobi.
\v 12 Daga nan zan kunna wuta a haikalun allolin Masar. Nebukadnezza zai ƙone su ko kuma ya kwashe su. Zai tsarkake ƙasar Masar kamar yadda makiyaya ke tsabtace tufafinsu. Zai fita daga wurin nan da ɗaukaka.
\v 13 Zai karye ginshiƙan nan na dutse na Heliyofolis a ƙasar Masar. Zai ƙone haikalun allolin Masar.'"
\s5
\c 44
\cl Sura 44
\p
\v 1 Maganar ta zo ga Irmiya game da dukkan mutanen Yahudiya da ke zaune a ƙasar Masar, waɗanda ke zaune a Migdol, da Tafenhas, da Memfis, da ƙasar Fatros.
\v 2 Yahweh mai runduna, Allah na Isra'ila, ya faɗi wannan: Ku da kan ku kun ga duk waɗannan masifu da na aukar a Yeruselem da dukkan biranen Yahuda. Duba, yau sun zama kangaye. Ba wanda zai zauna a cikinsu.
\v 3 Wannan saboda miyagun abubuwan da su ka yi domin su yi mani laifi ta wurin zuwa su ƙona turare da kuma bautawa waɗansu alloli. Waɗannan alloli ne da ko su da kansu, ko ku, ko kakanninku ba su sani ba.'
\s5
\v 4 Don haka na dinga aikawa da dukkan bayina annabawa gare su. Na aike su su ce, 'Ku dena aikata abubuwan ban ƙyamar da na ke ƙi.' ba su saurara ba.
\v 5 Amma sun ƙi saurare. Suka ƙi maida hankali ko su juyo daga muguntarsu ta wurin ƙona turare ga wasu alloli.
\v 6 Sai razanata da fushina su ka yi ƙuna a kan biranen Yahuda da titunan Yerusalem. Don haka suka zama kango da abin banzatarwa, kamar yadda ya ke a yau'
\s5
\v 7 To yanzu Yahweh, Allah mai runduna Allah na Isra'ila, ya faɗi wannan, "Don me ku ke aikata babbar mugunta gãba da kanku? Don me ku ke jawowa kanku abin da zai sa a datse ku daga cikin Yahuda - mazaje da mataye, yara da jarirai? Ba za a rage ko ɗayanku ba.
\v 8 Ta wurin aikin muguntarku kun yi ma ni laifi ta wurin ayyukan hannuwanku, ta ƙona turare ga waɗansu alloli a ƙasar Masar, inda ku ka je ku zauna. Kun je can ne don a hallaka ku, don ku zama la'antattu da abin reni a cikin dukkan al'umman duniya.
\s5
\v 9 Kun manta da ayyukan muguntar da kakanninku su ka yi da muguntar da sarakunan Yahuda da matansu su ka yi? Kun manta da muguntar da ku da kanku da matanku ku ka aikata a cikin ƙasar Yahuda da titunan Yerusalem?
\v 10 Har ya zuwa yau, ba su yi tawa'li'u ba. Ba su girmama shari'una ba ko dokokina da na sanya a gabansu ba, su da kakanninsu, ba su kuma yi tafiya a cikinsu ba.'
\s5
\v 11 Don haka Yahweh mai runduna, Allah na Isra'ila, ya faɗi wannan, "Duba, ina gab da sa fuskata gãba da ku don in kawo muku masifa in kuma hallakar da dukkan Yahuda.
\v 12 Don zan kwashe sauran mutanen Yahuda waɗanda su ka je Masar su zauna a can. Zan yi wannan don dukkan su su hallaka a ƙasar Masar. Za su faɗi ta wurin takobi da yunwa. Tun daga ƙaraminsu har zuwa babbansu za su faɗi ta wurin takobi da yunwa. Za su mutu su kuma zama abin reni da abin ƙyama.
\s5
\v 13 Don zan hori mutanen dake zaune a ƙasar Masar kamar yadda na hori mutanen Yeruselem da takobi, da yunwa. da annoba,
\v 14 yadda ba wani ragowar Yahuda waɗanda su ka tafi su zauna a cikin ƙasar Masar da zai kucce ko ya tsira ko ya dawo ƙasar Yahuda, wadda su ke marmari su dawo su zauna; Ba waninsu da zai dawo, sai dai 'yan kima da su ka kutto a nan.'"
\s5
\v 15 Daga nan duk waɗanda su ka san matansu na ƙona turare ga waɗansu alloli, da kuma dukkan matayen da ke a babbar taruwa, da dukkan mutanen da ke zaune a ƙasar Masar ta kwari da tudu, a Fatros su ka amsa wa Irmiya.
\v 16 Su ka ce, "Game da maganar da ka faɗa, mana a cikin sunan Yahweh ba za mu saurare ka ba.
\v 17 Don hakika za mu yi duk abin da mu ka ce za mu yi - ƙona turare ga sarauniyar sama da zuba baye - baye na sha a gabanta Kamar yadda kakanninmu, da sarakunanmu, da shugabanninmu su ka yi a titunan Yerusalem. Daga nan za mu ƙoshi da abinci mu wadatu, ba tare da fuskantar wata masifa ba.
\s5
\v 18 Sa'ad da mu ka dena yin waɗannan wato ƙin miƙa baiko ga sarauniyar sama da kuma ƙin miƙa baye - baye na sha a gare ta, duk za mu talauce mu kuma mutu ta wurin takobi da yunwa."
\v 19 Sai matayen suka ce, "lokacin da mu ke yin baye - baye na turare a gaban sarauniyar sama da zuba baye - baye na sha a gare ta, ashe saɓawa mazanmu muka yi da muka aikata waɗannan abubuwa, yin waina a cikin siffarta da kuma zuba baye - baye na sha gare ta?"
\s5
\v 20 Daga nan sai Irmiya ya ce da dukkan mutanen -ga maza da mata, kuma dukkan mutanen da su ka amsa masa - ya yi shela ya ce,
\v 21 "Ashe Yahweh bai tuna da turaren da ku ka ƙona a biranen Yahuda da titunan Yerusalem - ku da kakanninku, da sarakunanku da shugabanninku, da kuma mutanen ƙasar ba? Domin Yahweh ya tuna da wannan; ya fãɗo cikin tunaninsa.
\s5
\v 22 Daga nan ba zai ƙara jurewa da shi ba saboda miyagun ayyukanku da ku ka yi, saboda ayyukan ban ƙyamar da ku ka aikata. Sai ƙasarku ta zama yassashiya, da abin reni, da la'anta ta zama ba wanda ke zaune a cikinta har ya zuwa yau.
\v 23 Saboda kun ƙona turare kun kuma yi zunubi ga Yahweh, don kun ƙi sauraron muryarsa, da shari'unsa ba da kuma ƙa'idojinsa ba, ko alƙawaransa ba, da dokokinsa ba shi ya sa wannan masifar ta same ku kamar yadda ya ke a yau."
\s5
\v 24 Sai Irmiya ya ce da dukkan taron mutanen da kuma dukkan matayen, "Ku ji maganar Yahweh, dukkan mutanen Yahuda da ke ƙasar Masar.
\v 25 Yahweh mai runduna, Allah na Isra'ila ya faɗi wannan, 'Ku da matayenku duk kun furta da bakinku kun kuma ɗauki duk abin da ku ka ce,"Hakika za mu aiwatar da alƙawuran da mu ka yi cewa za mu yi sujada ga sarauniyar sama, mu kuma zuba baye-baye na sha a gareta." Yanzu sai ku cika alƙawuranku, ku kuma aikatasu.'
\s5
\v 26 Don haka ku ji maganar Yahweh, ku dukkan mutanen Yahuda da ke a ƙasar Masar, duba na rantse da sunana mai girma - in ji Yahweh. Ba za a sa ke kiran sunana ta bakin wani daga cikin mutanen Yahuda ba a dukkan ƙasar Masar, ku da yanzu ke cewa, "Na rantse da ran Ubangiji Yahweh."
\v 27 Duba, ina lura da su don in aukar masu da masifa ba abu na gari ba. Duk wani mutumin Yahuda da ke a Masar zai hallaka ta wurin takobi da yunwa har sai dukkan su sun ƙare.
\v 28 Daga nan sai waɗanda su ka tsira daga takobin su dawo daga ƙasar Masar zuwa ƙasar Yahuda, 'yan kimansu kawai. Da haka dukkan waɗanda su ka ragu a Yahuda da suka je Masar don su zauna a can za su san ko maganar waye zata zama gaskiya - tawa ko tasu.
\s5
\v 29 Wannan zai zamar maku alama - wannan shi ne furcin Yahweh - da na ke shirya maku a wannan wurin, don ku san cewa maganata tabbas za ta hare ku tare da masifa.'
\v 30 Yahweh ya faɗi wannan, duba ina gab da in bada Fir'auna Hofra sarkin Masar ga hannun maƙiyansa da kuma hannun masu so su hallaka shi. Zai zama kamar yadda na ba da Zedekiya sarkin Yahuda ga sarki Nebukadnezza sarkin Babila, maƙiyinsa wanda ya biɗi ransa.'"
\s5
\c 45
\cl Sura 45
\p
\v 1 Wannan ita ce maganar annabi Irmiya da ya faɗawa Baruk ɗan Neriya. Wannan ya faru a lokacin da ya rubuta a cikin naɗaɗɗen littafi wanda Irmiya ya yi masa shifta - wannan ya faru a watan huɗu na sarautar Yahoaikim ɗan Yosiya sarkin Yahuda, sai ya ce,
\v 2 Yahweh Allah na Isra'ila, ya faɗi wannan a gareku, ina faɗa maka wannan Baruk:
\v 3 Ku ka ce, 'Kaito na, domin Yahweh ya ƙara ƙunci ga raɗaɗina. Da nishe - nishena sun gajiyar da ni; ban sami hutu ba.'
\s5
\v 4 Wannan shi ne abin da tilas za ka faɗa masa; Dubi abin da na gina, yanzu ina rushewa. Abin da na dasa, yanzu ina tumɓukewa - Zan yi wannan a dukkan duniya.
\v 5 Amma ko kana begen manyan abubuwa domin kanka? Kada ka yi begen haka. Don duba, masifa za ta aukowa dukkan mutane - wannan furcin Yahweh ne - amma zan ba ka ranka a matsayin ganimarka a duk inda ka je.'"
\s5
\c 46
\cl Sura 46
\p
\v 1 Wannan ita ce maganar Yahweh da ta zo wurin Irmiya annabi game da al'ummai.
\v 2 Game da Masar: "Wannan game da sojan Fir'auna Neko ne, sarkin Masar da ke Karkemish a wajan kogin Yuferetis. Wannan shi ne sojan Nebudkadnezza sarkin Babila ya cinye a yaƙi a shekara ta huɗu ta mulkin Yehoyakim ɗan Yosiya, sarkin Yahuda:
\v 3 A sami ƙananan garkuwoyi da manyan garkuwoyi a shirya su ka fita ka yi yaƙi.
\v 4 Ka sa linzamin doki; Ka ɗaura sirdi ka kuma sa hular kwano; ka wasa mãshi ka ɗaura kayan yaƙi.
\s5
\v 5 Me nake gani a nan? sun cika da fargaba suna kuma guduwa, don an yi nasara da sojojinsu. Suna gudu don neman tsira basa kuma waigen baya. Fargaba na ko'ina - wannan shi ne abin da Yahweh ya furta -
\v 6 masu hanzari baza su iya gudu ba, sojojin kuma ba za su tsira ba. Sun yi tuntuɓe a arewa suka faɗi a gefen Kogin Yuferetis.
\s5
\v 7 Wane ne wannan da ya tashi kamar Nilu, wanda ruwayensa ke tunbatsa sama da ƙasa kamar koguna?
\v 8 Masar na tashi kamar Nilu, kamar kogunan da suke tumbatsa sama da ƙasa. Masar ta ce Zan tashi in rufe duniya. Zan hallakar da birane da mazaunansu.
\v 9 Ku dawakai ku hau sama ku yi fushi, ku karusai. Bari sojoji su fita waje, Kush da Fut, mutanen da ke fasaha da garkuwa, da mutanen Ludim, mutanen da suka shahara a tanƙwara bakkunansu.'
\s5
\v 10 Wannan ranar zata zama ranar ramako ce ga Ubangiji Yahweh mai runduna, zai kuma sakawa kansa akan magaftansa. Takobi za ta ci ta ƙoshi. zata ƙoshi da jininsu. Don za a yi hadaya ga Yahweh Ubangiji mai runduna a arewacin ƙasar a gefen Kogin Yuferetis.
\s5
\v 11 Ku je Gileyad ku sami magani, budurwan Masar. A banza kuke sawa kanku magani mai yawa. Ba za ku warke ba.
\v 12 Al'ummai sun ji labarin kunyarku. Duniya ta cika da makokinku, don sojoji suna tuntuɓe da juna, dukkansu su ka fãɗi tare."
\s5
\v 13 Wannan ita ce maganar da Yahweh ya faɗawa annabi Irmiya bayan Nebukadnezza sarkin Babila ya kawo wa Masar hari:
\v 14 "Ka sanar a Masar, ka kuma yi shela a Migdol, da Memfis, da Tafanhes. Ku sami wurinku ku shirya kanku, don takobi zai haɗiye waɗanda ke kewaye da ku.'
\s5
\v 15 Don me jarumawanki fuskarsu a sunkuye ƙasa? Ba za su tsaya ba, saboda Ni, Yahweh, na ture su ƙasa.
\v 16 Ya ƙara yawan waɗanda su ka yi tuntuɓe. Kowanne soja ya fãɗi kusa da ɗan uwansa. Su na cewa, 'Ku tashi. Bari mu tafi gida. Bari mu koma wurin mutanenmu, zuwa ainahin ƙasarmu. Bari mu bar wannan takobin da ya ke doddoke mu ƙasa.'
\v 17 Su ka yi shela a can, 'Fir'auna sarkin Masar mai kwakazo ne kawai, wanda ya bar zarafinsa ya sille.'
\s5
\v 18 Na rantse da zatina inji Sarki, wanda sunansa shi ne Yahweh mai runduna - wani zai zo mai kama da Dutsen Tabor da Dutsen Karmel na bakin teku.
\v 19 Ku kwaso wa kanku jakkuna don za ku tafi hijira, ku da ku ke zaune a Masar. Domin Memfis zata zama wofi, zata zama kango, ba kuma wanda zai zauna a can.
\s5
\v 20 Masar kyakkyawar maraƙa ce, amma ƙwaro mai harbi na zuwa daga arewa. Yana zuwa.
\v 21 Sojojin hayar da ke cikinta kamar bijimi mai ƙiba suke, amma su ma za su juya su gudu. Ba za su iya tsayuwa tare ba, don ranar masifarsu na zuwa gãba da su, lokacin horonsu ne.
\v 22 Masar ta fito kamar maciji tana kuma rarrafawa, don maƙiyanta suna tattaki gãba da ita. Suna tunkararta kamar masu yankan katako da gatura.
\s5
\v 23 Za su sassare dazuzzuka - wannan shi ne abin da Yahweh ya furta-duk da yake abin ya na da ban razana. Domin magabta za su zama da yawa sosai fiye da fara ba za su ƙidayu ba.
\v 24 Za a kunyatar da Masar. Za a miƙa ta ga hannun mutane daga arewa."
\s5
\v 25 Yahweh mai runduna, Allah na Isra'ila, ya ce, "Duba, ina gab da in hori Amon na Tebes, da Fir'auna, da Masar da allolinta, da sarakunanta wato masu mulkinta, da masu dogara da su.
\v 26 Zan miƙa su ga wanda ke neman rayukansu, da kuma hannun Nebukadnezza sarkin Babila da bayinsa. Daga nan bayan wannan za a sake zama a Masar kamar a kwanakinta na can baya - wannan furcin Yahweh ne
\s5
\v 27 Amma kai, bawana Yakubu, kada ka ji tsoro. Kada ka razana, Isra'ila, don duba, Ina gab da in komo da ku daga manisanta wurare, zuriyarku kuma daga ƙasar bautarsu. Daga nan sai Yakubu ya dawo, ya sami salama, ya kuma sami tsaro, kuma ba sauran wanda zai razana shi.
\v 28 Kai, bawana Yakubu, kada ka ji tsoro - wannan shi ne furcin Yahweh - don ina tare da kai, kuma zan halakar da dukkan al'ummai a inda na warwatsa ku. Amma ba zan hallaka ku dukka ba. Duk da haka zan hore ku da adalci hakika ba zan bar ku ba horo ba."
\s5
\c 47
\cl Sura 47
\p
\v 1 Wannan ita ce maganar Yahweh da ta zo ga annabi Irmiya game da Filistiyawa. Wannan maganar ta zo gare shi kafin Fir'auna ya kai wa Gaza hari.
\v 2 Yahweh ya faɗi wannan: Duba, tunbatsar ruwa na tasowa daga arewa. Zai zama kamar ambaliyar koguna! Daga nan za su share ƙasar da duk abin da ke cikinta, da biranenta da mazaunanta! Saboda haka kowa zai yi kukan neman taimako, kuma dukkan mazaunan ƙasar za su yi makoki.
\s5
\v 3 Da jin motsin sawayen ƙarfafan dawakansu 'kofatansu na ruri akan karusansu da kuma ƙarar gargarensu, ubanni ba za su taimaki 'ya'yansu ba saboda rashin ƙarfinsu.
\v 4 Domin rana na zuwa da zata warwatsa dukkan Filistiyawa, ta datse daga Taya da kuma Sidom da kuma daga duk wanda ya tsira ya ke kuma so ya taimake su. Don Yahweh yana warwatsa Filistiyawa, waɗanda su ka ragu a tsibirin Kafto.
\s5
\v 5 Saiƙo zai aukawa Gaza. Ashkelon kuma mutanen da aka bari a kwarurrukansu za a sa su su yi shiru. Makokinku zai kai wanne lokaci?
\v 6 Kaito, takobin Yahweh! Har yaushe za ta kasance har sai kun yi shiru? Ku koma ga watsewarku! Ku dena ku yi shiru.
\v 7 Ta yaya zai huta, sa'ad da Yahweh ya umarce shi. Sa'ad da ya umarta a kaiwa Ashkelon hari da kuma ƙasashen da ke gefen teku?"
\s5
\c 48
\cl Sura 48
\p
\v 1 Ga Mowab, Yahweh mai runduna, Allah na Isra'ila, ya faɗi wannan, "Kaiton Nebo, domin an warwatsa ta. An cinye KIriyata an ƙasƙantar da ita. An ɓalle hasumiyarta an wulaƙanta ta.
\v 2 Mowab ba ta da sauran wata daraja. Maƙiyansu a Heshbon sun shirya mata masifa. Sun ce Ku zo mu hallakar da ita a matsayinta na ƙasa. Mahaukatanta suma za su hallaka - takobi za ta bi bayanku.'
\s5
\v 3 Ku saurara! Ƙarar kururuwa na tafe daga Horoniyam, inda akwai kango da kuma babbar hallakarwa.
\v 4 An hallakar da Mowab. 'Ya'yanta sun yi kuka har aka ji su.
\v 5 Sun je kan tsaunukan Luhit suna kuka, Domin akan hanya zuwa Horoniyam, an ji ƙara mai ban razana saboda hallakarwa.
\s5
\v 6 Tsere! Ku ceci rayukanku ku zama kamar dajin yunifa a jeji.
\v 7 Domin saboda dogararku ga ayyukanku da dukiyarku, kuma za a kame ku. Daga nan sai Kemosh ya tafi zaman bauta, tare da firistocinsa da shugabanninsa.
\s5
\v 8 Domin mai hallakarwa zai zo kowanne birni; ba birnin da zai tsira. Don haka kwari zai lalace, filin ƙasa kuma za a ɓaɓɓata shi, Kamar yadda Yahweh ya faɗa.
\v 9 Ku bada fukafukai ga Mowab, don tilas ne ta tashi ta gudu. Biranenta za su zama ɓatattun ƙasashe, inda ba mai zama a cikinsu.
\v 10 Dama duk wanda ke ragwanci cikin aikin Yahweh ya zama la'ananne! Dama duk wanda ya janye takobinsa daga zubar da jini ya zama la'annanne!
\s5
\v 11 Mowab tana jin tana da tsaro tun tana matashiya. Ta zama kamar ruwan inabin da ba a taba canja masa gora ba. Ba ta taɓa zuwa bauta ba. Don haka yana jin komai dai - dai ne kamar dã; ɗanɗanonsa bai canza ba.
\v 12 To duba, ranaku na zuwa - wannan shi ne abin da Yahweh ya furta - lokacin da zan aika masa da waɗanda za su juye shi su kuma juye dukkan tukwanensa su kuma farfasa butocinsa.
\s5
\v 13 Daga nan sai Mowab su ji kunyar Kemosh kamar yadda ya faru ga gidan Isra'ila, yadda su ka ji kunyar Betel, abin dogararsu.
\v 14 Yaya za ku ce 'Mu sojoji ne, jarumawan yaƙi'?
\s5
\v 15 Za a washe Mowab za kuma a kai wa biranenta hari. Don kyawawan matasanta sun gangara mayanka. Wannan furcin sarki ne! Sunansa Yahweh mai runduna ne.
\v 16 Masifar Mowab na gab da auko mata; bala'i ya kusa sauka da sauri.
\v 17 Dukkan ku da ke kewaye da Mowab, ku yi kuka; da ku da kuka san ƙarfinta, ku yi sowar wannan, Kaiton, sanda mai ƙarfi, sandar daraja, an karye ta.'
\s5
\v 18 Sauko daga wurinki mai daraja ki zauna a busasshiyar ƙasa, ke ɗiya mai zama a Dibon. Domin wanda zai hallaka Mowab yana kawo ma ki hari, wanda zai hallakar da madogaranki.
\v 19 Ku tsaya akan hanya ku yi tsaro, ku mutanen da ke a Arowa. Ku yi tambaya ga wanda ya ga wanda ke gudu don ya tsira. ku ce Me ya faru?'
\v 20 Mowab ta kunyata, don an warwatsa ta. Ku kaɗa kai ku yi makoki; Ku yi ihun neman taimako. Ku faɗawa mutanen yankin kogin Arnon cewa an hallakar da Mowab.
\s5
\v 21 Yanzu horo ya sauko kan ƙasa mai duwatsu, ga Holon, da Jakza, da Mefat,
\v 22 ga Dibon, ga Nebo, da Bet diblataim,
\v 23 ga Kiriyataim, da Bet Gamul, da Bet Meyon,
\v 24 ga Keriyot da Bozra, da kuma ga dukkan biranen da ke ƙasar Mowab - da manisanta, da biranen da ke nesa da kusa.
\v 25 An kawar da ƙahon Mowab; an karya damtsenta - wannan furcin Yahweh ne.+
\s5
\v 26 Ka sa ya bugu, don ya yi girman kai gãba da Yahweh. Bari Mowab ta yi birgima a kan hararwarta, ka sa ta zama abin ba a.
\v 27 Domin ko Isra'ila bata zama abin dariya a gare ku ba? An same shi cikin ɓarayi, saboda haka ku ka kaɗa kanku gare shi ku ka yi kuma ta yin magana a kansa?
\s5
\v 28 Ku yi watsi da birane ku tattaru a gefen gari, ku mazaunan Mowab. Ku zama kamar kurciyar da ke sheƙa a bakin rami a cikin duwatsu.
\v 29 Mun ji labarin girman kan Mowab - da tayarwarta, da kumbura kanta, yadda ta ke ɗaukaka kanta da mugayen tunane tunanenta na zuciya.
\s5
\v 30 Wannan furcin Yahweh ne - Ni da kaina na san maganganunsa na banza, waɗanda ba komai ba ne, kamar ayyukansa.
\v 31 Don haka zan kawo makoki ga Mowab, zan kuma tada muryar makoki ga dukkan Mowab zan yi makoki saboda mutanen Kir Hareset.
\v 32 Zan yi kuka dominku fiye da yadda na yi don Yazer, da kuringar Sibmah! Rassanki sun zarce ƙetaren Tekun Gishiri sun kai har Yazer. masu hallakarwa sun kawo hari ga 'ya'yan itatuwan inabinki na damina.
\s5
\v 33 Don an kawar da biki da farinciki daga 'ya'yan itace da kuma ƙasar Mowab. Na kawo ƙarshen ruwan inabi daga wurin matsawarsu. Ba zasu matse su da sowace - sowacen farinciki ba. Duk wani sowace - sowace ba zai zama sowace - sowacen murna ba.
\s5
\v 34 Daga sowace - sowace a Heshbon tun daga can Eleyele, an jiwo ƙararsu a Yahaz, daga Zowar har zuwa Horoniyaim da Eglat Shelishiya, tun daga ma can rafuffukan Nimrim da suka bushe.
\v 35 Don zan kawo ƙarshen kowa a Masar wanda ke miƙa hadayu a manyan wurare da ƙona turare ga allolinsa - wannan furcin Yahweh ne.
\s5
\v 36 Don haka zuciyata tana makoki domin Mowab kamar sarewa. Zuciyata tana makoki kamar gungume saboda mutanen Kir Hereset. Dukiyar da suka ribato ta ƙare.
\v 37 Don dukkan kawuna sun yi saiƙo an kuma aske duk wani gemu. Tsage - tsage yana a kowanne hannu, sun kuma yafa tufafin makoki a kwankwasonsu
\s5
\v 38 A kwai makoki a ko'ina, a cikin dukkan gine-ginen Mowab da kuma Cibiyoyin kasuwancin Mowab. Don na hallakar da Mowab kamar tukwanen da ba wanda ke so - wannan furcin Yahweh ne.
\v 39 Yadda aka farfasa su! Yadda su ka yi ruri cikin makokinsu! Mowab ta juya bayanta cikin kunya! Don haka Mowab zata zama abin ba a da firgita ga dukkan waɗanda suka kewaye shi."
\s5
\v 40 Gama Yahweh ya faɗi wannan, "Duba, maƙiyi zai zo yana jewa kamar gaggafa, yana buɗe fuka-fukansa a kan Mowab.
\v 41 An kame Keriyot da dukkan hasumiyoyinta an ƙwance su. Don a waccan ranar zukatan sojojin Mowab za su zama kamar na zukatan matan da ke naƙuda a lokacin haihuwa.
\s5
\v 42 Don haka za a hallakar da Mowab ta zama ba sauran mutane, don ya mai da kansa ya zama babba gãba da yahweh.
\v 43 Masifa da rami, da tarko suna zuwa kanku, ku mazauna Mowab - wannan furcin Yahweh ne.
\v 44 Duk wanda ya gudu saboda firgita zai faɗa rami, kuma duk wanda ya fito daga rami tarko zai kama shi, don zan aukar masu da wannan a shekarar fushina na ramako a kansu - wannan furcin Yahweh ne.
\s5
\v 45 Waɗanda su ka tsere za su tsaya a inuwar Heshbon ba tare da wani ƙarfi, ba don wuta za ta tashi daga Heshbon, da harshen wuta daga tsakiyar Sihon. Zata cinye goshin Mowab da tsakiyar kawunan mutane masu ɗaga kai.
\s5
\v 46 Kaiton ki, Mowab! an hallakar da mutanen Kemosh, Don an kwashe 'ya'yanki maza a matsayin bayi, 'yan matanki kuma zuwa bauta.
\v 47 Amma zan dawo da nasarar Mowab a kwanaki masu zuwa - wannan furcin Yahweh ne." Hukuncin Mowab ya ƙare a nan.
\s5
\c 49
\cl Sura 49
\p
\v 1 Ga abin da Yahweh ya ce, game da mutanen Ammon, Isra'ila ba ta da 'ya'ya ne? Babu wanda zai gãji wani abu a Isra'ila? Me ya sa Molek ya ke zaune a Gad, mutanen sa kuma su na zaune a cikin biranen sa?
\v 2 To duba, kwanaki su na zuwa - wannan furcin Yahweh ne - sa'ad da zan ba da alamar yaƙi gãba da Rabbah a cikin mutanen Ammon, za ta zama yasasshen tsibi kuma a ƙone ƙauyukanta da wuta. Gama Isra'ila zai mallaki waɗanda su ka mallake shi." cewar Yahweh.
\s5
\v 3 Yi ruri cikin makoki, da Heshbon, gama za a ragargaza Ai! Ɗiyar Rabba, ki yi kururuwa! Sa kayan makoki. Yi makoki da kai da kawowa a wofi, gama Molek zai tafi bauta, tare da firistocinsa da shuganninsa.
\v 4 Me ya sa ki ke fahariya da kwarurrukanki, kwarurrukan masu ba da 'ya'ya sosai, ke kangararriyar ɗiya? Ke da ki ke dogara da dukiyarki kuma kin ce, "wane ne za ya iya zuwa ya yi gãba da ni?'
\s5
\v 5 Duba, na kusa kawo maki tsoro, wannan shi ne furcin Ubangiji Yahweh Mai Runduna - wannan abin tsoro zai zo daga dukkan waɗanda su ke maƙwabtanki. Zai watsar da kowanne ɗayan ku. Ba wanda zai tattaro waɗanda suka gudu.
\v 6 Amma bayan haka zan dawo da kaddarorin mutanen Ammon - wannan shi ne furcin Yahweh."
\s5
\v 7 A kan Idom, Yahweh mai runduna ya ce haka, "Ba sauran hikimar da za a samu a Teman? Shawara mai amfani ta ƙare daga masu fahimta? Hikimar su ta lalace?
\v 8 Ku gudu! Ku koma baya! Ku jira cikin ramummuka cikin ƙasa, mazauna Dedan. Gama zan kawo hallaka ga Isuwa, a kan shi lokacin da zan hore shi.
\s5
\v 9 Idan masu girbin inabi su ka zo wurin ku, ba za su rage kaɗan ba? Idan ɓarayi ne da daddare, ba za su saci abin da su ke so ba?
\v 10 Amma na tuɓe Isuwa ya zama huntu, na tono wuraren ɓoyon sa domin kada ya ƙara ɓoye wa. 'ya'yansa da 'yan uwansa da maƙwabtansa an hallakar da su, shi kuma ya tafi.
\v 11 Ku bar marayunku, zan lura da su rayukansu, gwaurayenku su dogara gare ni."
\s5
\v 12 Gama Yahweh ya faɗi haka, "Duba waɗanda ba su cancanta ba tabbas za su sha daga cikin ƙoƙon. Kai da kanka, ka na tsammani za ka tafi ba tare da horo ba? Ba zai yi wu ba, domin tabbas zaka sha.
\v 13 Gama na rantse da kaina, wannan furcin Yahweh ne - Bozra za ta zama abin tsoro, abin reni, lalatatta, da abin la'antarwa. Dukkan biranenta za su lalace har abada.
\s5
\v 14 Na ji magana daga wurin Yahweh, an aika da manzo zuwa ga al'ummai, 'ku taru ku kai mata hari, ku yi shiri domin yaƙi.'
\v 15 Duba, idan an gwada da sauran al'ummai na mai da ke 'yar ƙarama, abin reni ga mutane.
\s5
\v 16 Saboda tsoron ka, girman kan zuciyarka ya ruɗe ka, mazauna can ƙoli, ku da ku ke a can bisa tsaunuka masu tsawo domin ka sa sheƙar ka can sama kamar gaggafa. Zan dawo da kai ƙasa daga can - wannan ne furcin Yahweh.
\s5
\v 17 Idom za ta zama abin tsoro ga dukan mai wuce ta. Kowanne mutum zai yi rawar jiki da tsaki saboda dukkan masifunta.
\v 18 Kamar yadda aka kaɓantar da Sodom da Gomora da maƙwabtansu," Yahweh ya faɗi, "ba wanda zai zauna a can; ba wanda zai tsaya a can.
\s5
\v 19 Duba, zai tashi kamar zaki daga jejin Yodan zuwa wuraren kiwo masu kyau. Domin nan da nan zan sa Idom ta gudu daga wurin ta, zan sa wani zaɓaɓɓe ya lura da ita. Gama wanene kama da ni, wane ne kuma zai yi mani sammaci? Akwai makiyayin da zai iya yin tsayayya da ni?"
\s5
\v 20 Ji shirye-shiryen da Yahweh ya yi gãba da Idom, shirye-shiryen da ya yi gãba da mazaunan Teman. Ba shakka za a janye su har ɗan ƙaramin garken dabbobi. Wuraren kiwon su za su zama rusasssun wurare.
\s5
\v 21 Duniya za ta girgiza da ƙarar faɗuwar su. An ji sowace - sowacen ƙunci daga Tekun Iwa.
\v 22 Duba, wani zai kawo hari kamar gaggafa, ya kawo su-ra ya buɗe fuka-fukansa a kan Bozra. Daga nan a wannan rana zuciyar sojojin Idom za ta zama kamar zuciyar macen da ke cikin naƙuda."
\s5
\v 23 Game da Damaskus: "Hamat da Arfad za su ji kunya, saboda sun ji labarin hallaka. Sun narke! hankalin su ya ta shi kamar tekun da ya kasa kwantawa.
\v 24 Damaskus ta raunana ƙwarai, ta juya ta gudu; tsoro ya kama ta. Ƙunci da ciwo ya kama ta kamar mace mai hafuwa.
\v 25 Yaya birnin yabo ba a yashe shi ba, garin farincikina?
\s5
\v 26 Saboda haka samarinta za su faɗi a wuraren cinikaiyarsu, jarumawanta za su hallaka a rannar- wannan shi ne furcin Yahweh mai runduna"
\v 27 "Gama zan kunna wuta a kan ganuwar Damsakus, za ta cinye kagara mai ƙarfi ta Ben Hadad."
\s5
\v 28 Game da Kedar da mulkokin Hazor, ga abin da Yahweh ya ce da Nebukadnezza, (gama Nebukadnezza sarkin Babila zai kai wa waɗannan wurare hari): "Tashi ka kai wa Kedar hari ka hallaka waɗannan mutanen na gabas.
\v 29 Za a kwashe bukkokinsu da garkunansu, duk da labulen bukkokinsu da kayan aikinsu; za a kore raƙumansu daga wurinsu, mazaje za su yi masu ihu su ce, "Ga abin tsoro a kowanne gefe!"
\s5
\v 30 Ku gudu! Ku yi ragaita can nesa! Ku tsaya a cikin ramuka a ƙasa ku mazauna Hazor - wannan furcin Yahweh ne. Gama Nebukadnezza sarkin Babila ya ƙulla shiri gãba da ku. Ku gudu! Ku koma baya!
\v 31 Tashi ka kai wa al'ummar da ke zaune lafiya hari cikin sauƙi, "Yahweh ya ce" Ba su da ƙofofi ko makarai, mutanen hakanan suke zaune su kaɗai.
\s5
\v 32 Gama raƙumansu za su zama ganima, kayansu masu yawa za su zama ganimar yaƙi. Sa'annan zan sa iska ta watsar da su, su waɗanda ke aske gefen gashinsu, zan kawo masu hallaka daga kowanne gefe - haka Yahweh ya furta.
\v 33 Hazor za ta zama wurin kwanciyar diloli, ta lalace har abada. Ba wanda zai zauna a wurin, ba mutumin da zai tsaya a can.
\s5
\v 34 Wannan ce maganar Yahweh da ta zo ta wurin Irmiya annabi game da Elam. Wannan ya faru a farkon mulkin Zedekiya sarkin Yahuda, ya ce,
\v 35 "Yahweh Mai runduna ya faɗi wannan: Duba, na kusa karya 'yan baka na Elam, a karfinsu mafi yawa.
\v 36 Gama zan kawo iskoki huɗu daga kusurwoyi huɗu na sammai, zan watsar da mutanen Elam ga dukkan waɗannan iskokin. Waɗanda su ka watse daga Elam babu al'ummar da za su je.
\s5
\v 37 Zan ragargaza Elam a gaban abokan gãbar su da waɗanda ke neman ransu. Domin zan kawo masu hallaka da zafin fushina - haka Yahweh ya furta - Zan aika takobi a bayansu har sai na hallakar da su.
\v 38 Sa'annan zan kafa kursiyina a Elam in hallakar da sarkinta da shugabanninta daga can - abin da Yahweh ya furta kenan -
\v 39 Zai zama a cikin kwanaki masu zuwa zan dawo da martabar Elam - abin da Yahweh ya furta kenan."
\s5
\c 50
\cl Sura 50
\p
\v 1 Ga abin da Yahweh ya furta game da Babila, ƙasar Kaldiyawa, ta hannun Irmiya annabi,
\v 2 "Faɗawa al'ummai kuma ka sa su, su saurara. Ka sa alama kuma ka sa su saurara. kada ka rufe ta. Ka ce, 'An ɗauke Babila, an kuyatar da Bel. Marduk ta razana, an sa gumakanta cikin kunya; siffofinta sun razana.
\s5
\v 3 Wata al'umma daga arewa zata taso mata, domin ta mayar da ƙasarta kango. Ba wanda zai zauna cikinta ko mutum ko dabba, duk za su gudu.
\v 4 Ga abin da Yahweh ya furta a cikin waɗannan kwanaki da wannan lokaci, mutanen Isra'ila da na Yahuda - zasu taru su je suna neman Yahweh Allahnsu da kuka.
\v 5 Za su tambayi hanyar zuwa Sihiyona su nufi wurin ta suna cewa, za mu je mu haɗa kanmu da Yahweh da dauwamamman alƙawarin da ba za a manta ba."
\s5
\v 6 Mutane na sun zama garken da ya ɓace, makiyayansu sun bauɗar da su cikin duwatsu; suna juya su daga wannan tudu zuwa wancan. Sun tafi sun mance wurin da suka fito.
\v 7 Kowa ya je wurin su yana cinye su. Abokan gãbar suna cewa, 'Ba mu yi zunubi ba gama sun yi zunubi ga Yahweh, gidansu na gaskiya -Yahweh begen kakanninsu.
\s5
\v 8 Ku fita daga tsakiyar Babila; ku fice daga ƙasar Kaldiyawa; ku zama kamar dan akuyan da ya tafi kafin sauran garke.
\v 9 Duba, na kusa ta da ruɗami, in tada wata ƙungiya ta manyan al'ummai daga arewa su yi gãba da Babila. za su haɗa kan su gãba da ita. Za a ci Babila da yaƙi daga can. Kibiyoyinsu kamar na babban maharbin da ba ya dawowa hakanan.
\v 10 Kaldiya za ta zama ganima. Dukkan waɗanda suka washe ta za su gamsu - haka Yahweh ya furta.
\s5
\v 11 Kun yi farinciki, kun yi shagali sa'ad da aka washe abin gãdona, kun yi tsalle kamar ɗan maraki a wurin kiwonsa, kun yi haniniya kamar ƙaƙƙarfan doki.
\v 12 Saboda haka mahaifiyarku zata ji kunya ƙwarai; za a ƙasƙantar da wadda ta haife ku. Zata zama mafi ƙanƙanta cikin al'ummomi, ta zama jeji ta zama busasshiyar ƙasa ta zama hamada.
\v 13 Saboda Yahweh ya yi fushi, Babila za ta zama kufai mai zama a cikinta, za ta lalace sarai. Dukkan wanda ya wuce zai yi mamakin lalacewar Babila, ya yi tsaki saboda dukkan raunukanta.
\s5
\v 14 Ku da ke kewaye da ita, ku shirya ku kai wa Babila hari. Dukkan wanda ya ɗana baka dole ya harbe ta, kada ku mayar da kibiyoyinku, gama ta yi wa Yahweh zunubi.
\v 15 Ku yi mata ihu a ko'ina! Ta ba da kai, hasumiyoyinta sun faɗi; an rushe ganuwoyinta, wannan fansa ce da Yahweh ya ɗauka. Ku ɗauki fansa a kanta! Ku yi mata kamar yadda ta yi.
\s5
\v 16 Ku hallaka manoma, da wanda ya shuka iri da wanda ya yi amfani da lauje a lokacin girbi cikin Babila. Bari kowanne mutum ya koma wurin mutanensa ya gudu daga takobin mai azabtarwa; bari su gudu su koma ƙasarsu.
\s5
\v 17 Isra'ila tumaki ne da suka watse zakuna suka kore su. Da farko sarkin Asiriya ya cinye shi; sa'annan Nebukadnezza sarkin Babila ya karya ƙasusuwansa.
\v 18 Saboda haka Yahweh Mai Runduna, Allah na Isra'ila, ya faɗi haka: Duba, na kusa in hori sarkin Babila da ƙasarsa, kamar yadda na hori sarkin Asiriya.
\s5
\v 19 Zan dawo da Isra'ila ƙasarsa; zai yi kiwo a Karmel da Bashan. Sa'annan za ya ƙoshi a ƙasar kan tudu ta Ifraim da Giliyad.
\v 20 Yahweh ya ce, a cikin waɗanan kwanaki da wannan lokaci, za a nemi laifi a Isra'ila, amma ba za a samu ba. Zan biɗi zunubi game da Yahuda, amma ba zan samu ba, gama zan gafartawa waɗanda na keɓe."
\s5
\v 21 "A tasar wa ƙasar Meratayim, gãba da ita da mazaunan Fekod. Sa masu takobi, kuma a keɓe su domin hallakarwa - abin da Yahweh ya furta kenan-- ku yi dukkan abin da nake umurtarku.
\v 22 Zizar yaƙi da mummunar hallakarwa suna cikin ƙasar.
\s5
\v 23 Yadda aka datse gudumar dukkan ƙasashe kuma aka hallakar. Yadda Babila ta zama rusasshen wuri cikin al'ummai.
\v 24 Na ɗana maki tarko kuma kin kamu, ke Babila, kuma baki sani ba! An same ki kuma an kama ki, domin kin yi tsayayya da Yahweh.
\s5
\v 25 Yahweh ya buɗe wurin ajiyar kayan yaƙinsa kuma yana fito da kayan yaƙin domin aiwatar da fushinsa. Akwai aiki domin Ubangiji Yahweh mai runduna a ƙasar Kaldiyawa.
\v 26 Ku kai ma ta hari daga nesa. Ku buɗe rumbunanta ku tara ta kamar tsibin hatsi. Ku keɓe ta domin hallakarwa. kada ku rage ma ta komi.
\s5
\v 27 Ku kashe dukkan bijimanta, ku kai su wurin yankawa. Kaiton su, ranarsu ta zo - lokacin horonsu.
\v 28 Akwai motsin waɗanda suke gujewa, waɗanda suka rage, daga ƙasar Babila. Waɗannan za su ba da labarin ɗaukar fansa da Yahweh Allahnmu ya yi domin Sihiyona, da ɗaukar fansa domin haikalinsa."
\s5
\v 29 A kira maharba gãba da Babila - dukkan waɗanda su ka ɗana bakkunansu. Ku yi zango gãba da ita, kuma kada kowa ya tsira. Ku sãka mata kamar yadda ta yi. ku yi mata bisa ga ma'aunin da ta yi amfani da shi. Gama ta rena Yahweh, Mai Tsarki na Isra'ila.
\v 30 Haka samarinta za su faɗi a cikin dandalin birni, kuma dukkan mayaƙanta zasu hallaka a wannan rana - Wannan shi ne furcin Yahweh."
\s5
\v 31 Duba, Ina gãba da ke, ke mai takama - wannan shi ne furcin Ubangiji Yahweh mai runduna - gama ranarki ta zo, ke mai taƙama, lokacin da zan hore ki.
\v 32 Domin masu taƙama su yi tuntuɓe su faɗi. Ba wanda zai tashe su. Zan kunna wuta a cikin biranensu; za ta cinye komi da komi da ke kewaye da shi.
\s5
\v 33 Yahweh mai runduna ya ce wannan: An tsanantawa mutanen Isra'ila, tare da mutanen Yahuda. Dukkan waɗanda suka kamasu su na riƙe da su; sun hana su su tafi.
\v 34 Mai kuɓutar da su mai ƙarfi ne. Yahweh mai runduna ne sunansa. Lallai zai duba matsalar su da gaskiya, domin ya kawo hutu a ƙasar, ya kuma kawo husuma ga mazaunan Babila.
\s5
\v 35 Takobi na gãba da Kaldiyawa, haka Yahweh ya furta, da kuma Babila da mazaunanta da shuganninta da masu hikimarta.
\v 36 Takobi na gãba da masu faɗar maganganun banza! Za su zama wawaye! Takobi na gãba da sojojinta! za su cika da tsoro.
\v 37 Takobi yana zuwa gãba da dawakansu, da karusansu da dukkan mutane mazauna cikin tsaƙiyar Babila, domin su zama kamar mataye. Takobi ya na zuwa gãba da ɗakunan ajiyarta, kuma za a washe su.
\s5
\v 38 Fari ya na zuwa kan ruwayenta domin su bushe. Domin ta zama ƙasar gumaka lalatattu, sun yi kamar mutane marasa hankali ta wurin gumakansu.
\v 39 Ta zama hamada inda namun daji za su zauna da diloli da 'ya'yan jimina su zauna a cikinta. Ba lokacin da za a ƙara zama a cikinta. Ba za a ƙara zama cikinta ba daga tsara zuwa tsara.
\v 40 Kamar yadda Yahweh ya kaɓantar da Sodom da Gomora da maƙwabtansu - abin da Yahweh ya furta ke nan - ba wanda zai zauna a can; ba mutumin da zai tsaya cikinta."
\s5
\v 41 Duba, wasu mutane suna zuwa daga arewa; babbar al'umma da sarakuna masu yawa an izo su daga manisantan wuraren duniya.
\v 42 Zasu ɗauko bakkuna da mãsu. Su masu masifa ne ba su da tausayi. Tafiyar su tana kama da rurin teku, sun haye bisa dawakai, a jere bisa layi kamar mutane domin yaƙi, gaba da ke, ɗiyar Babila.
\s5
\v 43 Sarkin Babila ya ji rahoto game da su, sai hannayensa suka yi sanyi cikin ƙunci. Azaba ta kama shi kamar mace mai haihuwa.
\s5
\v 44 Duba! Ya fito kamar zaki daga tuddan Yodan zuwa wuraren kiwo. Gama nan da nan zan sa su gudu daga wurin, kuma zan sa wani zaɓaɓɓe ya lura da wurin. Gama wane ne kama da ni, kuma wa za ya ba ni sammaci? Wanne makiyayi ne zai iya tsayayya da ni?
\s5
\v 45 To saurari shirye-shiryen da Yahweh ya yi gãba da Babila, shirye-shiryensa da ya shirya gãba da ƙasar Kaldiyawa. Lallai za a janye su, har ma da ɗan karamin garke. Wuraren kiwon su za su zama kango.
\v 46 Duniya za ta girgiza da rurin yaƙin yin nasara da Babila, al'ummai za su ji kukansa na ƙunci."
\s5
\c 51
\cl Sura 51
\p
\v 1 Ga abin da Yahweh ya faɗi: Duba, na kusa tado da iskar mai hallakaswa a kan Babila da mazauna cikin Leb Kamai.
\v 2 Zan aika da baƙi ga Babila, za su warwatsar da ita su lalata kasarta, gama za su auko mata ta kowanne gefe a ranar hallakarwa.
\s5
\v 3 Kada ku bari maharba su ɗana bakkunansu; kada ku bari su sa kibiya. Kada ku ƙyale samarinta, ku keɓe dukkan sojojinta domin hallakarwa.
\v 4 Gama mutanen da suka sami rauni za su faɗi a ƙasar Kaldiyawa; matattu za su faɗi a cikin titunanta.
\s5
\v 5 Gama Isra'ila da Yahuda Allah bai yashe su ba, Yahweh mai runduna, ko da yake ƙasar ta na cike da laifofin da a ka yi wa Mai Tsarki na Isra'ila.
\v 6 Ku gudu daga cikin Babila, kowa ya tsira da kansa. Kada ku hallaka cikin muguntarta. Gama lokacin ɗaukar fansar Yahweh ne. Zai rama komai a kanta.
\s5
\v 7 Dã Babila ƙoƙon zinari ce a hannun Yahweh wadda ta sa dukkan duniya suka bugu; dukkan al'ummai suka sha ruwan inabinta suka sami taɓin hankali.
\v 8 Ba da jimawa ba Babila za ta fadi za a hallaka ta. Ku yi makoki dominta! Ku ba ta magani domin ciwonta; ko ƙila zata warke.
\s5
\v 9 Mun so mu warkar da Babila, amma ba ta warke ba. Bari mu barta, mu tafi kasarmu. Gama muguntarta ta kai har sama, ta taru a cikin giza-gizai.
\v 10 Yahweh ya ce mu ba mu da laifi. Ku zo, mu faɗi ayyukan Yahweh Allahnmu a cikin Sihiyona.'
\s5
\v 11 Ku wãsa kibiyoyi ku kuma ɗauki garkuwoyi. Yahweh ya na zuga ruhun sarkin Medes a kan shirin hallaka Babila. Wannan fansa ce ta Yahweh, fansa saboda hallaka haikalinsa.
\v 12 Ku tada tuta a kan ganuwoyin Babila, ku tsananta tsaro; ku sa masu tsaro ku shirya kwanton ɓauna; gama UBANGIJI zai aikata abin da ya ce game da mazaunan Babila.
\s5
\v 13 Ku mutanen da ke zaune a bakin rafuka masu ruwa da ku mutane masu arzikin dukiya, ƙarshenku ya zo. An rage tsawon zaren rayuwarku.
\v 14 Yahweh mai ruduna ya rantse da ran sa, ' zan cika ku da mutane, kamar cincirindon fara, za kuma su tãda muryar yaƙi gãba da ku.'
\s5
\v 15 Ya yi duniya ta wurin ikonsa; ya kafa duniya ta wurin hikimarsa. Ta wurin fahiminsa ya shimfiɗa sammai.
\v 16 Idan ya yi tsawa, sai ruwaye su yi ruri a cikin sammai, gama ya kan kawo turiri daga ƙarshen duniya. Ya kan yi walƙiya domin ruwa ya kuma aiki iska daga cikin taskokinsa.
\s5
\v 17 Kowanne mutum ya zama marar fahimi, marar sani. Kowanne maƙerin tama gumakansa sun kunyatar da shi. Gama sifofinsa na zubi ƙarya ce kawai babu rai a cikin su.
\v 18 Ba su da amfani, aikin ruɗi ne kawai, za su lalace a ranar horonsu.
\v 19 Amma Yahweh, rabon Yakubu ba kamar waɗannan ya ke ba, gama shi ne ya cura dukkan abu. Isra'ila ne harshen gãdonsa; Yahweh mai runduna ne sunansa.
\s5
\v 20 Kai ne gudumata da kayan yaƙina. Da kai zan ragargaza al'ummai in hallaka mulkoki.
\v 21 Da kai zan ragargaza dawakai da mahayansu; da kai zan ragargaza karusai da masu tuƙa su.
\s5
\v 22 Da kai zan ragargaza kowanne mutum da kowacce mace. Da kai zan ragargaza tsoho da yaro. Da kai zan ragargaza samari da budurwai.
\v 23 Da kai zan ragargaza makiyayi da garkensa. Da kai zan ragargaza manoma da ƙungiyarsu, Da kai zan ragargaza gwamnoni da jami'ansu.
\s5
\v 24 Kana gani zan sakawa Babila da dukkan mazauna Kaldiya, bisa ga dukkan muguntar da suka yi a cikin Sihiyona - abin da Yahweh ya furta kenan.
\s5
\v 25 Duba, ina gãba da kai, dutsen hallakarwa - abin da Yahweh ya furta kenan - wanda ke hallaka dukkan duniya. Zan miƙa hannuna gãba da kai in gangarar da kai daga can ƙoli, in mai da kai ƙonannen dutse.
\v 26 Yadda ba za su ɗauki wani dutse daga wurinka su kafa tushen gini da shi ba. Za ka lalace sarai har abada - haka Yahweh ya furta.
\s5
\v 27 A kafa tuta bisa duniya. A busa ƙaho bisa al'ummai, a kira al'ummai su kai mata hari: Ararat, Minni da Ashkenaz. A sa wani jarumi ya kai mata hari, a zo da dawakai kamar cincirindon fãri.
\v 28 A shirya al'ummai su kai mata hari: Sarkin Medes da gwamnoninsa, da dukkan jami'ansa da dukkan ƙasashen da ke ƙarƙashin mulkinsa.
\s5
\v 29 Gama ƙasar za ta girgiza ta kasance cikin azaba, tun da shirye - shiryen Yahweh ya ci gaba a kan Babila, domin ya maida ƙasar Babila lalatacciyar ƙasa inda ba mazauna.
\s5
\v 30 Sojojin da ke Babila sun dena faɗa; sun koma cikin maɓoyarsu. Ƙarfinsu ya ƙare; sun zama mata - gidajenta suna cin wuta, an kakkarya makaran ƙofofinta.
\v 31 Wani manzo ya tafi ya yi shela ga wani manzo, wani mai gudu ya tafi ya gaya wa wani mai gudu ya kai wa sarkin Babila rahoton an ƙwace birninsa tun daga ƙarshe har zuwa ƙarshe.
\v 32 An ƙwace magangarin rafi an ƙone ciyawar fadamu, kuma mayaƙan Babila sun rikice.
\s5
\v 33 Gama Yahweh mai runduna, Allah na Isra'ila, ya faɗi haka: Ɗiyar Babila ta zama kamar masussuka. Lokaci ya yi da za a tattake ta ƙasa. Da jimawa kaɗan lokacin girbi zai zo mata.
\s5
\v 34 Nebukadnezza sarkin Babila ya lanƙwame ni; ya kore ni cikin ruɗami ya kuma maishe ni tukunyar da ba komi a ciki. Ya haɗiye ni kamar dodo, ya cika cikinsa da abinci na mai kyau, ya share ni sarai.'
\v 35 Shi wanda ya ke zaune a Sihiyona zai ce, 'Ta'addancin da a ka yi mani da jikina ya koma kan Babila.'Yerusalem za ta ce, ' Bari jinina ya zauna a kan Kaldiya.'
\s5
\v 36 Saboda haka ga abin da Yahweh ya ce: Duba, ina kusa da goya ma ki baya cikin matsalar ki in ɗauki fansa domin ki. Duba zan busar da ruwayen Babila, in sa mabulbulolinta su ƙafe.
\v 37 Babila za ta zama juji, kogunan diloli, wurin jin tsoro, abin tsãki, inda ba kowa a ciki.
\s5
\v 38 Mutanen Babila za su yi ruri tare kamar 'yan zakoki. Za su yi ƙara kamar 'ya'yan zaki.
\v 39 Sa'ad da su ka ji zafi saboda haɗama, zan shirya masu liyafa; zan sa su bugu domin su yi murna, sa'annan su yi barci wanda ba za su ƙara tashi ba - abin da Yahweh ya furta kenan -
\v 40 Zan tura su kamar ragunan yanka, kamar raguna da bunsura.
\s5
\v 41 An ci Babila da yaƙi! An kame yabon dukkan duniya. Abin da mamaki yadda Babila ta zama kango a cikin al'ummai.
\v 42 Teku ya zo kan Babila! Rurin balalloƙan ruwa ya cika ta.
\s5
\v 43 Biranenta sun zama lalatattu, ƙasa busasshiya da kuma jeji, ƙasar da babu mai zama a ciki, ba talikin da ke wucewa ta wurin.
\v 44 Saboda haka zan hori Bel cikin Babila; zan fitar daga bakinsa abin da ya haɗiye, al'ummai ba za su ƙara gangarowa wurinsa da baye - bayensu ba. Ganuwoyin Babila za su faɗi.
\s5
\v 45 Mutanena, ku fice daga cikin tsakiyarta. Bari kowanne ɗayanku ya tsira da ransa daga fushin hasalata.
\v 46 Kada ku bari zuciyarku ta yi suwu saboda labarin da ku ka ji cikin ƙasar, gama labaran za su zo shekara ɗaya. Bayan wannan shekara mai zuwa akwai labarai, tashin hankali zai zo cikin ƙasar. Mai mulki zai yi gãba da mai mulki.
\s5
\v 47 Saboda haka, duba, kwanaki za su zo inda zan hori sassaƙaƙƙun gumaka na Babila. Dukkan ƙasarta za ta ji kunya, dukkan waɗanda a ka yanka za su faɗi cikin tsakiyarta.
\v 48 Sa'annan sama da ƙasa, da dukkan abin da ke cikin su za su yi farin ciki a kan Babila. Gama masu hallakarwa za su zo dominta daga arewa - haka Yahweh ya furta.
\v 49 Kamar yadda Babila ta kashe mutane su ka faɗi a Isra'ila, haka kuma za a kashe mutane su faɗi a cikin tsakiyar Babila.
\s5
\v 50 Masu tsira daga takobi, ku tafi! Kada ku tsaya cik. Ku tuna da Yahweh daga nesa; bari Yerusalem ta zo cikin lamirinku.
\v 51 Mun ji kunya, domin mun ga wulaƙanci; kunya ta rufe fuskokinmu, gama bãƙi sun shiga wurare masu tsarki na gidan Yahweh.
\s5
\v 52 Domin haka, duba, kwanaki suna zuwa - haka Yahweh ya furta - sa'ad da zan hukunta sassaƙaƙƙun gumakanta, waɗanda suka ji rauni zasu yi nishi cikin ƙasarta dukka.
\v 53 Ko da Babila zata hau cikin sammai ta inganta hasumiyarta, masu hallakarwa zasu auko mata daga wurina - haka Yahweh ya furta.
\s5
\v 54 Kukan baƙinciki ya fito daga Babila, babbar ribɗewa ta fito daga ƙasar Kaldiyawa.
\v 55 Gama Yahweh ya na hallakar da Babila. Yana sa muryarta mai ƙara ta lalace. Abokan gabarsu su na ruri kamar balalloƙan ruwaye masu yawa; ƙarar su ta yi ƙarfi ƙwarai.
\v 56 Gama masu hallakarwa sun zo kanta - a kan Babila! - kuma an kama jarumawanta. An kakkarya bakkunansu, gama Yahweh Allah ne mai ɗaukar fansa; ba shakka zai ɗauki fansa.
\s5
\v 57 Zan sa hakimanta da masu mulkinta da sojojinta su bugu, su yi barcin da ba za su tashi ba - wannan furcin sarki ne: Yahweh mai runduna ne sunansa.
\v 58 Yahweh mai runduna ya faɗi haka: Ganuwar Babila mai kauri za a rushe ta sarai, za a ƙone dogayen ƙofofinta. Sa'annan mutane masu kawo mata ɗauki za su yi aikin wofi; dukkan abin da al'ummai su ka yi ƙoƙarin yi mata za a ƙone shi."
\s5
\v 59 Wannan ita ce maganar da Irmiya annabi ya umurtawa Seraya dan Neriya dan Maseya, sa'ad da ya tafi da Zedekiya sarkin Yahuda zuwa Babila a cikin shekara ta hudu ta mulkinsa. A lokacin Seriya shi ne babban jami'i.
\v 60 Irmiya ya riga ya rubuta a cikin naɗaɗɗen littafi dukkan hallakar da za ta zo a kan Babila - dukkan waɗannan maganganu da aka rubuta game da Babila.
\s5
\v 61 Irmiya ya ce da Seraiya, "Sa'ad da ka je Babila za ka gani kuma za ka karanta waɗannan maganganu da ƙarfi.
\v 62 Sa'annan za ka ce, 'Yahweh, kai da kanka ka furta cewa za ka hallaka wannan wuri, kuma ba mutum ko dabba da zai zauna a cikinta, za ta zama lalatacciya har abada.'
\s5
\v 63 Sa'ad da ka gama karanta wannan naɗaɗɗen littafi, ka ɗaura masa dutse ka jefa shi cikin tsakiya Ifratis.
\v 64 Ka ce, 'Haka Babila zata nitse. Ba zata tashi ba saboda bala'in da na ke aiko wa gãba da ita, kuma za su faɗi."' Nan maganganun Irmiya suka tsaya.
\s5
\c 52
\cl Sura 52
\p
\v 1 Zedekiya yana da shekara ashirin da ɗaya sa'ad da ya fara mulki; ya yi mulki a Yerusalem shekara goma sha ɗaya. Sunan mahaifiyarsa Hamutal ne; ita ɗiyar Irmiya ce daga Libna.
\v 2 Ya yi mugunta a gaban Yahweh; ya yi dukkan abin da Yohoaikim ya yi.
\v 3 Ta wurin fushin Yahweh dukkan waɗannan abubuwa suka faru a Yerusalem da Yahuda, har sai lokacin da ya kore su daga gabansa. Sa'annan Zedekiya ya yi wa sarkin Babila tawaye.
\s5
\v 4 Ya zama a cikin shekara ta tara ta mulkin Zedekiya, a cikin wata na goma, a cikin rana ta goma ga watan, Nebukadnezza sarkin Babila, ya zo da dukkan mayaƙansa gãba da Yerusalem. Suka yi zango daura da ita, suka kafa sansanin yaƙi kewaye da ita.
\v 5 Suka kewaye birnin ba shiga ba fita, har shekara ta goma sha ɗaya ta mulkin Zedekiya.
\s5
\v 6 A cikin wata na hudu, a kan rana ta tara ga watan yunwa ta yi tsanani a cikin birnin har ma ba abin da mutane za su ci a ƙasar.
\v 7 A ka ɓalle birnin aka shiga, dukkan mayaƙa su ka gudu su ka fice daga cikin birnin ta hanyar da ke tsakanin ganuwa biyu a cikin dare, ta lambun sarki, duk da ce wa Kaldiyawa su na kewaye da birnin. Su ka tafi wajen Arabah.
\v 8 Amma sojojin Kaldiyawa su ka bi sarki su ka cimma Zedekiya a filin Kogin Yodan kusa da sararin kwarin Yariko. Dukkan mayaƙansa su watse daga wurinsa.
\s5
\v 9 Suka kama sarki suka kawo shi wurin sarkin Babila a Riblah cikin ƙasar Hamat, inda ya yanke ma sa hukunci.
\v 10 Sarkin Babila ya yanka 'ya'yan sarki Zedekiya maza ya na gani, kuma a Riblah ya yanka dukkan shugabannin Yahuda.
\v 11 Sa'annan ya ƙwaƙule idanun Zedekiya, ya ɗaure shi da sarƙa ta jan ƙarfe ya kawo shi Babila. Sarkin Babila ya sa shi a kurkuku har zuwa ranar mutuwarsa.
\s5
\v 12 To, a cikin wata na biyar, a kan rana ta goma ga wata, a shekara ta goma sha tara ta mulkin Nebukadnezza sarki, sarkin Babila, Nebuzaradan ya zo Yeruselem. Shi ne jami'in masu tsaron sarki, shi kuma bawan sarkin Babila ne.
\v 13 Ya ƙone gidan Yahweh, da fadar sarki da dukkan gidajen Yerusalem; ya kuma ƙone kowanne gini mai mahimmanci.
\v 14 Ganuwar da ta kewaye Yerusalem kuma, mayaƙan Babiloniyawa da ke tare da jami'in masu tsaron sarki suka rushe su.
\s5
\v 15 Su marasa galihu da sauran mutanen da su ka ragu a cikin birni, waɗanda su ka bijire su ka tafi wurin sarkin Babila da sauran masu aikin hannu - Nebuzaradan jami'in masu tsaron sarki ya kwashe su ya kai su bauta.
\v 16 Amma Nebuzaradan jimi'in masu tsaron sarki ya bar waɗansu cikin marasa galihu a ƙasar domin su yi aiki a garkar inabi da gonaki.
\s5
\v 17 Game da ginshikai na tagulla da ke na gidan Yahweh kuwa, da diraku, da babban bangaji na tagulla da ake kira "Teku" da su ke cikin gidan Yahweh, Kaldiyawa su ka kakkarya su gutsu - gutsu suka kwashe dukkan tagullan suka koma da su Babila.
\v 18 Tukwanen, da ceburan, da tsinkunan gyara fitilu, da bangazai, da dukkan kayan aikin na tagulla waɗanda firistoci suka yi hidima da su a haikali - Kaldiyawa suka kwashe su dukka suka tafi da su.
\v 19 Daruka da tasoshin ƙona turare, da bangazai, da tukwane, da maɗorin fitilu, da kaskuna, da darurruka da aka yi da su zinariya da waɗanda aka yi su da azurfa - jami'in masu tsaron sarki ya kwashe su dukka.
\s5
\v 20 Ginshiƙai guda biyu, da babban bangajin tagulla da aka sa ni da "Teku," da bijimai guda goma sha biyu na tagulla da su ke karkashin dirakun, abubuwan da Sulaiman ya yi domin gidan Yahweh, ɗauke da tagulla da ta wuce gaban aunawa.
\v 21 Ginshikan kamu sha takwas ne kowannen a tsayi, da layikan da su ke kewaye da su kuma kowanne kamu goma sha biyu ne. Kowannen su kaurin yatsu hudu ne masu rami.
\s5
\v 22 Akwai gammon tagulla a bisan sa. Gammon tsawon kamu biyar ne, an yi masa aikin dajiya da siffofin 'ya'yan manta'uwa waɗanda a ka yi da tagulla. Ɗaya ginshikin da nashi 'ya'yan manta uwar dai - dai su ke da na farin.
\v 23 Don haka akwai manta'uwa tasa'in da shida bisa gefen gammunan, da manta'uwa guda ɗari a bisa kewayen aikin dajiyar.
\s5
\v 24 Jami'in masu tsaron sarkin ya dauki Seraiya babban firist tare da Zafaniya da firist na biyu da masu tsaron ƙofa su uku a matsayin 'yan kurkuku.
\v 25 Daga cikin birni kuwa ya kama jami'in da ke kula da sojoji da mutane bakwai masu ba sarki shawara, waɗanda suke cikin birni har wannan lokaci. Ya kuma kama jami'in sojojin sarki wanda shi ne ke shigar da mutane aikin soja, tare da waɗansu mahimmam mutane guda sittin waɗanda su ke cikin birni.
\s5
\v 26 Sai Nebuzaradan jami'in masu tsaron sarki ya ɗauko su ya kawo su wurin sarkin Babila a Ribla.
\v 27 Sarkin Babila ya kashe su a Ribla cikin ƙasar Hamat. Ta haka Yahuda ta fita daga ƙasarta ta tafi bauta.
\s5
\v 28 Waɗannan su ne mutanen da Nebukadnezza ya kai bauta cikin shekara ta bakwai, mutanen Yahuda su 3,023.
\v 29 A cikin shekara ta takwas ta Nebukadnezza, ya ɗauki mutane 832 daga Yerusalem.
\v 30 A cikin shekara ta ashirin da uku ta Nebukadnezza, Nebuzaradan, jami'in masu tsaron sarki ya ɗauki mutum 745 cikin mutanen Yahudiya ya kai su bauta. Dukkan waɗanda a ka kai bauta su ne mutum 4,600.
\s5
\v 31 Ya zama kuma a cikin shekara ta talatin da bakwai ta hijira Yehoyacin, sarkin Yahuda, a cikin wata na goma sha biyu, a kan rana ta ashirin da biyar ga wata, sai Awel-Marduk, sarkin Babila ya saki Yehoyacin sarkin Yahuda daga kurkuku. Wannan ya faru ne a cikin shekarar da Awel-Marduk ya fara mulki.
\s5
\v 32 Ya yi masa maganar alheri, ya ba shi wurin zama da ya fi na sauran sarakunan da suke tare da shi daraja a Babila.
\v 33 Awel-Marduk ya cire wa Yehoiyacin kayan 'yan sarƙa. Yehoyacin ya yi ta cin abinci a teburin sarki dukkan sauran rayuwarsa,
\v 34 a kan ba shi kuɗin cin abinci kullum har mutuwarsa.