ha_ulb/20-PRO.usfm

1898 lines
88 KiB
Plaintext
Raw Normal View History

2021-09-13 13:40:08 +00:00
\id PRO
\ide UTF-8
\h Littafin Misalai
\toc1 Littafin Misalai
\toc2 Littafin Misalai
\toc3 pro
\mt Littafin Misalai
\s5
\c 1
\cl Sura 1
\p
\v 1 Misalai na Suleman ɗan Dauda, sarkin Isra'ila.
\v 2 Waɗannan misalai zasu koyar da hikima da koyarwa, zasu koyar da maganganun fasaha,
\v 3 domin ka sami koyarwa domin ka rayu ta wurin yin abin da ke dai-dai, gaskiya da adalci.
\s5
\v 4 Waɗannan misalai kuma zasu bada hikima ga marar sani, su kuma bada ilimi da fahimta ga matasa.
\v 5 Bari mutane masu hikima su saurara su ƙaru a koyonsu, bari mutane masu ganewa su sami bishewa,
\v 6 su kuma fahimci misalai, karin magana, da maganganun mutane masu hikima da kacici-kacicinsu.
\s5
\v 7 Tsoron Yahweh shi ne mafarin ilimi - wawaye sukan rena hikima da koyarwa.
\v 8 Ɗana, ka kasa kunne ga koyarwar mahaifinka, kada kuma ka watsar da dokokin mahaifiyarka;
\v 9 zasu zamar maka rawani cike da alheri a kanka da abubuwan ratayawa masu kyau a wuyanka.
\s5
\v 10 Ɗana, idan masu zunubi suka jarabce ka zuwa cikin zunubinsu, kada ka bi su.
\v 11 Idan suka ce, "Ka zo tare da mu, bari mu yi fakon jinin, bari mu yi kwanto mu kai farmaƙi ga mutane marasa laifi ba tare da dalili ba.
\s5
\v 12 Bari mu haɗiye su da rai, kamar yadda Lahira take ɗauke waɗanda ke lafiyayyu, ta maishe su kamar waɗanda suka faɗa cikin rami.
\v 13 Zamu sami abubuwa iri iri masu daraja; zamu cika gidajenmu da ganimar da muka sato gun waɗansu.
\v 14 Ka haɗa kai da mu; zamu kasance dukka da ma'aji guda tare."
\s5
\v 15 Ɗana, kada ka bi wannan hanyar tare da su; kada ka yarda ƙafarka ta bi wajen da suke tafiya;
\v 16 ƙafafunsu suna gudu garin yin mugunta suna hanzari su zubda jini.
\v 17 Gama ba amfani a kafa wa tsuntsu tarko a idanunsa.
\s5
\v 18 Waɗannan mutane jininsu ne suke kafa wa tarko - suna kwanto ne su kama rayukansu.
\v 19 Haka kuma duk hanyoyin wanda ya sami arziƙi ta rashin adalci; ƙazamar riba takan ɗauke rayukan waɗanda suka riƙe ta kam-kam.
\s5
\v 20 Hikima tana kuka da ƙarfi a tituna, tana ɗaga murya a dandali;
\v 21 a karafku da ake hayaniya tana kururuwa, a ƙofofin birane tana magana,
\v 22 "Har yaushe, ku mutane marasa ganewa, zaku ƙaunaci rashin ganewa? Har yaushe, ku masu ba'a, zaku ci gaba da jin daɗin ba'a, kuma har yaushe, ku wawaye zaku ƙi ilimi?
\s5
\v 23 Ku kasa kunne ga tsautawa ta; zan faɗa maku tunanina; Zan sanar maku da maganganuna.
\v 24 Na yi kira, amma kuka ƙi ku saurara; na miƙa maku hannuna, amma ba wanda ya kula.
\v 25 Amma duk kun yi watsi da koyarwata ba ku saurara da gyaran da na yi maku ba.
\s5
\v 26 Zan yi dariya sa'ad da masifa ta zo maku, zan yi maku ba'a sa'ad da razana ta zo -
\v 27 lokacin da abin da kuke jin tsoro ya zo kamar hadari kuma bala'i ya auko kanku kamar guguwa, lokacin da azaba da damuwa suka sauko bisa kanku.
\s5
\v 28 Sa'an nan zasu kira ni, ba zan kuma amsa ba; zasu kira ni da himma, amma ba zasu same ni ba.
\v 29 Domin sun ƙi ilimi, kuma ba su zaɓi tsoron Yahweh ba,
\v 30 ba zasu bi koyarwata ba, kuma suka rena dukkan gyaran kuskurensu da na yi masu.
\s5
\v 31 Zasu ci 'ya'yan hanyoyinsu, da kuma 'ya'yan shirye shiryensu zasu ƙoshi.
\v 32 Domin a kan kashe dolaye lokacin da suka bar tafarki, wautar wawaye ta rashin kulawa zata hallaka su.
\v 33 Amma dukkan wanda ya kasa kunne gare ni zai zauna lafiya, zai huta a tsare babu tsoron masifa."
\s5
\c 2
\cl Sura 2
\p
\v 1 Ɗana, idan ka karɓi zantattukana kuma ka ajiye dokokina tare da kai kamar abu mai tamani,
\v 2 ka sa kunnenka ya maida hankali ga hikima kuma ka bada zuciyarka ga fahimta.
\s5
\v 3 Idan ka ƙwala kira domin fahimta ka ɗaga murya dominta,
\v 4 idan ka nemeta kamar yadda zaka nemi azurfa ka kuma biɗi fahimta kamar yadda zaka biɗi ɓoyayyiyar dukiya,
\v 5 sa'an nan zaka san tsoron Yahweh zaka kuma sami sanin Allah.
\s5
\v 6 domin Yahweh yana bada hikima, daga bakinsa ilimi da fahimta ke fitowa.
\v 7 Yana tanada sahihiyar hikima domin waɗanda suka gamshe shi, kuma garkuwa ne ga waɗanda suke da aminci,
\v 8 yana tsaron tafarkun adalci zai kuma kiyaye hanyoyin waɗanda suke bin sa da aminci.
\s5
\v 9 Sa'an nan ne zaka fahimci abin da ke da adalci, da, gaskiya, da kowanne tafarki mai kyau.
\v 10 Gama hikima zata shiga cikin zuciyarka, ilimi kuma zai ji wa ranka daɗi.
\s5
\v 11 Hankali zai lura da kai, fahimta kuma zata kiyaye ka.
\v 12 Zasu cece ka daga hanyar mugunta, daga kuma masu faɗar abubuwan saɓo,
\v 13 waɗanda suka yi watsi da tafarkun gaskiya suna tafiya a hanyoyin duhu.
\s5
\v 14 Suna farinciki sa'ad da suke yin mugunta, suna jin daɗi cikin aikata mugunta iri-iri.
\v 15 Suna bin karkatattun tafarku, suna amfani da ruɗu sun ɓoye manufarsu.
\s5
\v 16 Hikima da sanin dai-dai zasu cece ka daga mace mazinaciya, daga mace mai ƙazantar rayuwa daga maganganunta na zaƙin baki.
\v 17 Takan yashe da abokinta na ƙuruciya ta manta da alƙawarin Allahnta.
\s5
\v 18 Gama gidanta na bishewa zuwa mutuwa hanyoyinta zasu bishe ka zuwa gun waɗanda ke cikin kabari.
\v 19 Duk masu tafiya wurinta ba zasu sake dawowa ba kuma ba zasu sami tafarkun rai ba.
\s5
\v 20 Saboda haka zaka yi tafiya a hanyar mutanen kirki ka kuma bi tafarkun adalan mutane.
\v 21 Domin adalai zasu kafa mazauni a ƙasar, amintattu kuma za a barsu a cikinta.
\v 22 Amma za a datse mugaye daga ƙasar, marasa bangaskiya kuma za a datse su daga ita.
\s5
\c 3
\cl Sura 3
\p
\v 1 Ɗana kada ka manta da umarnaina ka riƙe koyarwata a cikin zuciyarka,
\v 2 domin za su ƙara maka tsawon kwanaki da shekarun rayuwa za su kuma ƙara maka salama.
\s5
\v 3 Kada ka bari alƙawarin aminci da dogara su taɓa barinka, ka ɗaura su tare a wuyanka, rubuta su a allon zuciyarka.
\v 4 Sa'an nan zaka sami tagomashi da suna mai kyau a gaban Allah da mutum.
\s5
\v 5 Ka dogara ga Yahweh da dukkan zuciyarka kada ka jingina ga taka fahimta;
\v 6 cikin dukkan hanyoyinka ka san da shi, shi kuwa zai maida tafarkunka miƙaƙƙu.
\s5
\v 7 Kada ka zama da hikima a naka idanu; ka ji tsoron Yahweh ka guji mugunta.
\v 8 Za ta zamar maka warkaswa ga naman jikinka da wartsakewa ga jikinka.
\s5
\v 9 Ka girmama Yahweh da dukiyarka da nunar fari na dukkan aikinka,
\v 10 sai rumbunanka su cika kuma matatsar ruwan 'ya'yan inabinka zasu yi ambaliya, su cika da ruwan inabi.
\s5
\v 11 Ɗana, kada ka rena koyarwar Yahweh kuma kada ka ƙi kwaɓarsa,
\v 12 gama Yahweh yana horon wanda ya ke ƙauna, kamar yadda mahaifi ya ke tarbiyantar da ɗansa wanda ya ke gamsarsa.
\s5
\v 13 Mai albarka ne wanda ya sami hikima; ya kuma sami fahimta.
\v 14 Ribar da ka samu daga hikima ta fi abin da azurfa zata bayar a bisani kuma ribarta tafi zinariya.
\s5
\v 15 Hikima tafi duwatsu masu ƙawa daraja kuma dukkan abin da kake marmari ba za a gwada su da ita ba a tamani.
\v 16 Tana da tsawon kwanaki cikin hannun damarta a cikin hannun hagunta akwai arziki da ɗaukaka.
\s5
\v 17 Hanyoyinta hanyoyin alheri ne kuma dukkan tafarkunta na salama ne.
\v 18 Itacen rai ce ga waɗanda suka kamata, waɗanda suka riƙe ta suna da farinciki.
\s5
\v 19 Ta wurin hikima Yahweh ya kafa duniya, ta wurin fahimta ya shimfiɗa sammai.
\v 20 Ta wurin iliminsa zurfafa suka buɗe kuma giza-gizai suka zubo da raɓarsu.
\s5
\v 21 Ɗana, ka riƙe hukuncin gaskiya da sanin dai-dai kada ka ɗauke ido daga gare su.
\v 22 Za su zama rai a rayuwarka da kayan ado na alheri da zaka rataya zagaye da wuyanka.
\s5
\v 23 Sa'an nan zaka yi tafiya a hanyarka lafiya ƙafarka ba zata yi tuntuɓe ba;
\v 24 sa'ad da ka kwanta, ba zaka ji tsoro ba; lokacin da ka kwanta, zaka yi barci mai daɗi.
\s5
\v 25 Kada ka ji tsoron masifar da zata zo farat ɗaya ko hallakarwar da mugaye suka haddasa, sa'ad da ta zo,
\v 26 domin Yahweh za ya kasance tare da kai ya tsare kafafunka daga faɗawa cikin tarko.
\s5
\v 27 Kada ka janye daga yin alheri ga waɗanda suka cancanta, yayin da kake da ikon aikatawa.
\v 28 Kada ka cewa maƙwabcinka, "Tafi ka sake dawowa, gobe zan baka," alhali kuwa da kuɗin tare da kai.
\s5
\v 29 Kada ka shirya cutar da maƙwabcinka - wanda ya ke kusa da kai ya kuma amince da kai.
\v 30 Kada ka yi jayayya da mutum ba dalili, sa'an nan bai yi komai ba don ya cuce ka.
\s5
\v 31 Kada ka ji ƙyashin ɗan ta'addar mutum ko ka zaɓi hanyoyinsa.
\v 32 Domin masu aikata mugunta abin ƙyama ne ga Yahweh, amma yana karɓar mutum mai adalci ya amince da shi.
\s5
\v 33 La'anar Yahweh tana kan gidan mugun mutum, amma yana sa albarka a gidan adalan mutane.
\v 34 Yakan yi wa masu ba'a ba'a, amma yakan bada jinƙansa ga mutane masu tawali'u.
\s5
\v 35 Mutane masu hikima sukan gãji girmamawa, amma za a ɗauke wawaye cikin kunyarsu.
\s5
\c 4
\cl Sura 4
\p
\v 1 Ku kasa kunne, 'ya'ya maza, ga koyarwar mahaifinku, ku maida hankali, domin ku san ko mene ne fahimta.
\v 2 Ina baku koyarwa mai kyau; kada ku yi banza da koyarwata.
\s5
\v 3 Sa'ad da nake ɗan yaron mahaifina, ina cikin ƙuruciya kuma ni kaɗai ne a gun mahaifiyata,
\v 4 ya koyar da ni ya ce mani, "Bari zuciyarka ta riƙe maganganuna da kirki; ka kiyaye dokokina ka rayu.
\s5
\v 5 Ka sami hikima da fahimta; kada ka manta kuma kada kuma ka ƙi maganganun bakina;
\v 6 kada ka ƙyale hikima zata tsare ka; ka ƙaunaceta zata kiyaye lafiyarka.
\s5
\v 7 Hikima ita ce mafificin abu, saboda haka ka sami hikima ka sayar da duk mallaƙarka don ka sami fahimta.
\v 8 Ka ƙaunaci hikima za ta girmamaka; zata girmama ka sa'ad da ka rungume ta.
\v 9 Zata ɗaura maka rawanin girmamawa a kanka; zata ba ka kambi mai kyau."
\s5
\v 10 Ka kasa kunne, ɗana, ka maida hankali ga maganganuna, zaka kuma sami shekaru da yawa a cikin rayuwarka.
\v 11 Ina nuna maka hanyoyin hikima; ina bishe ka a miƙaƙƙun tafarku.
\v 12 Sa'ad da kake tafiya, ba wanda zai tsaya a hanyarka in kana gudu, ba zaka yi tuntuɓe ba.
\s5
\v 13 Ka riƙe koyarwa, kada ka barta ta kubce; ka tsare ta, gama ita ce ranka.
\v 14 Kada ka bi tafarkin mugaye kuma kada ka bi hanyoyin masu aikata mugunta.
\v 15 Ka kauce mata, kada ka bi ta kanta; juya daga gare ta ka bi wata hanyar.
\s5
\v 16 Domin ba sa iya barci sai sun aikata mugunta kuma sukan rasa barci sai sun sa wani ya yi tuntuɓe.
\v 17 Domin sukan ci abincin mugunta su sha ruwan inabin ta'addanci.
\s5
\v 18 Amma tafarkin adalan mutane kamar fitowar rana ne da ke ta ƙara haskakawa; hasken yana ta ƙara girma har tsakiyar rana ta zo.
\v 19 Hanyar mugu kamar duhu take - ba su san yadda take ba suke tuntuɓe a kai.
\s5
\v 20 Ɗana, ka maida hankali ga maganganuna; ka bada kunnuwanka ga faɗata.
\v 21 Kada ka bari su guje wa idanunka; ka ajiye su a zuciyarka.
\s5
\v 22 Gama maganata rai ne ga waɗanda suka same ta lafiya ce kuma ga dukkan jikinsu.
\v 23 Ka kiyaye lafiyar zuciyarka ka tsare ta da himma, domin daga cikinta maɓuɓɓugar rai ke zubowa.
\s5
\v 24 Ka kawar da alfasha nesa daga gare ka ka kuma kawar da ruɓaɓɓar magana nesa daga gare ka.
\v 25 Bari idanunka su dubi gaba sosai ka kuma kafa ƙurawarka miƙe a gaban ka.
\s5
\v 26 Ka yi wa ƙafarka tafarkin da ke dai-dai; sa'an nan ne dukkan hanyoyinka zasu zama lafiyayyu.
\v 27 Kada ka juya zuwa dama ko hagu; ka juyar da ƙafafunka daga mugunta.
\s5
\c 5
\cl Sura 5
\p
\v 1 Ɗana, ka maida hankali ga hikimata; ka kasa kunne ga fahimtata,
\v 2 domin ka koyi sanin abin da ke dai-dai leɓunanka zasu tsare ilimi.
\s5
\v 3 Domin leɓunan mace mazinaciya suna ɗiga da zuma kuma bakinta yafi mai tabshi,
\v 4 amma a ƙarshe tana da ɗaci kamar shuwaka, tana yanka kamar takobi mai kaifi.
\s5
\v 5 Kafafunta suna gangarawa zuwa mutuwa sawunta yana tafiya har Lahira.
\v 6 Ba ta tunani game da hanyar rayuwa. Sawayenta sun ratse daga hanya; ba ta san inda zata ba.
\s5
\v 7 Yanzu dai, 'ya'yana maza, ku saurare ni; kada ku juya baya ga barin jin maganganun bakina.
\v 8 Bari tafarkinku ya yi nesa da ita kuma kada ku je kusa da ƙofar gidanta.
\s5
\v 9 Da haka ba zaka bada girmamawarka ga waɗansu ba ko shekarun rayuwarka ga mugun mutum ba;
\v 10 bãƙi ba zasu cinye dukiyarka ba; abin da ka yi wahala ka samu ba zai tafi gidan bãƙi ba.
\s5
\v 11 A ƙarshen rayuwarka zaka yi nishi sa'ad da jikinka zai lalace.
\v 12 Zaka ce, "Ai kuwa na ƙi jinin umarni kuma zuciyata ta wofintar da kwaɓa!
\s5
\v 13 Na ƙi yin biyayya da malamaina na kuma ƙi in saurari umarnansu.
\v 14 Na kusa lalacewa gaba ɗaya a tsakiyar taro, a cikin tattaruwar mutane."
\s5
\v 15 Ka sha ruwa a cikin randar da ke taka ka kuma sha ruwa mai gudana daga taka rijiyar.
\v 16 Ko ya kamata maɓuɓɓugarka ta yi ambaliya ko'ina kuma rafuffukan ruwanka su kwarara a bainar jama'a?
\v 17 Bari su zama naka kaɗai ba kuma domin bãƙin da ke tare da kai ba.
\s5
\v 18 Bari maɓuɓɓugarka ta zama da albarka kuma bari ka yi farinciki da matar kuruciyarka,
\v 19 gama ita ƙaunatacciyar barewa ce kuma kurciya cike da alheri. Bari nonnanta su ƙosar da kai koyaushe; bari ka bugu da ƙaunarta kowanne lokaci.
\s5
\v 20 Don mene ne, ɗana, zaka shaƙu da mazinaciya; donme za ka rungumi nonnan karuwar mace?
\v 21 Yahweh yana ganin dukkan abin da mutum ke yi yana kuma lura da dukkan tafarkun da ya ɗauka.
\s5
\v 22 Zunuban mugun mutum zasu cafke shi; igiyoyin zunubinsa zasu riƙe shi kam-kam.
\v 23 Zai mutu domin ya rasa umarni; an ɓadda shi ta wurin wautarsa mai girma.
\s5
\c 6
\cl Sura 6
\p
\v 1 Ɗana, idan ka ɗauki lamunin bashin da makwabcinka ya ci, idan ka yi alƙawari domin bashin wani da baka san shi ba,
\v 2 to ka kafa wa kanka tarko ta wurin alƙawarin da ka yi an kuma kama ka da maganganun bakinka.
\s5
\v 3 Sa'ad da an kama ka ta wurin maganganunka, ka yi wannan ka ceci kanka, tunda ka faɗa hannun makwabcinka; ka tafi ka ƙasƙantar da kanka ka faɗi wa makwabcinka abin da ya faru.
\s5
\v 4 Kada ka ba idonka barci ko gyangyaɗi.
\v 5 Ka tsirar da ranka kamar barewa daga hannun mafarauci, kamar tsuntsuwa daga hannun maharbi.
\s5
\v 6 Dubi tururuwa, kai ragon mutum, ka yi la'akari da hanyoyinta, ka yi hikima.
\v 7 Ba ta da hafsa, shugaba, ko mai mulki,
\v 8 duk da haka tana shirya abincinta da kaka kuma a lokacin girbi ta kan tanada abin da za ta ci.
\s5
\v 9 Har yaushe zaka yi ta barci, kai ragon mutum? Yaushe zaka tashi daga barcinka?
\v 10 "Ɗan barci kaɗan, ɗan gyangyaɗi kaɗan, ɗan naɗe hannuwa don a huta" -
\v 11 sai talaucinka ya zo maka kamar ɗanfashi buƙatunka kuma kamar jarumi mai makami.
\s5
\v 12 Wofin taliki - mugun mutum - yana rayuwa ne ta wuri karkata maganarsa,
\v 13 yana ƙifci da idanunsa, yana nuni da tafin ƙafarsa yana nuni da yatsunsa.
\s5
\v 14 Yana shirya mugunta da ruɗi a ransa; kullum yana haddasa rashin jituwa,
\v 15 Saboda haka masifarsa zata auko masa farat ɗaya; ba zato za a karairaye shi ba damar warkewa.
\s5
\v 16 Akwai abu shida da Yahweh yaƙi, har ma bakwai da ya ke ƙyamar su.
\s5
\v 17 Idanun taliki mai girman kai, harshe mai faɗar ƙarairayi, hannaye masu zub da jinin mutane marasa laifi,
\v 18 zuciya mai ƙago mugayen shirye-shirye, ƙafafu masu saurin gudu su je su yi mugunta,
\v 19 mashaidi mai furta ƙarairayi yana shuka husuma a tsakanin 'yan'uwa.
\s5
\v 20 Ɗana, ka yi biyayya da umarnin mahaifinka kada kuma ka watsar da koyarwar mahaifiyarka.
\v 21 Kullum ka ajiye su a zuciyarka; ka ɗaura su zagaye da wuyanka
\s5
\v 22 Sa'ad da kake tafiya zasu bishe ka; sa'ad da kake barci, zasu tsare ka; sa'ad da ka farka, zasu koyar da kai.
\v 23 Gama umarnai fitila ce, koyarwa kuma haske ne; tsautawa da ke zuwa daga koyarwa hanyoyin rai ne.
\s5
\v 24 Zata kiyaye ka daga muguwar mace, daga lallausar maganganun muguwar mace.
\v 25 Kada ka yi sha'awar kyanta a zuciyarka kuma kada ka bari ta cafke ka da girar idanunta.
\s5
\v 26 Kwana da karuwa tsadarsa kamar na kuɗin ɗan curin gurasa ne, amma matar wani zaka biya diyya da ranka.
\v 27 Mutum zai iya ɗaukar wuta a ƙirjinsa har da ba zata ƙona masa kayan jikinsa ba?
\s5
\v 28 Ashe mutum zai iya tafiya bisa garwashin wuta mai zafi ba tare da ya ƙona ƙafafunsa ba?
\v 29 To haka ya ke da mutumin da ya kwana da matar maƙwabcinsa; wanda ya kwana da ita ba zai kuɓuta daga hukunci ba.
\s5
\v 30 Mutane ba zasu rena ɓarawo ba idan ya yi sata domin biyan buƙatar yunwar cikinsa.
\v 31 Amma idan an kama shi, zai biya riɓi bakwai na abin da ya sata; dole ya sadaukar da dukkan abubuwa masu daraja da ke cikin gidansa.
\s5
\v 32 Wanda ya yi zina ba shi da hankali; wanda ya yi ta yana hallakar da kansa.
\v 33 Raunuka da kunya su ne sakaiyarsa kuma ƙasƙancinsa ba za a iya sharesu ba.
\s5
\v 34 Gama kishi yakan sa mutum ya husata; ba zai nuna jinƙai ba; sa'ad da zai ɗauki fansarsa.
\v 35 Ba zai karɓi wata fansa ba, kuma ba za iya ba da toshiya ba ko da an bashi kyautai da yawa.
\s5
\c 7
\cl Sura 7
\p
\v 1 Ɗana, ka adana maganganuna ka kuma ajiye dokokina a cikinka.
\v 2 Ka kiyaye dokokina ka rayu ka kiyaye koyarwata kamar ƙwayar idonka.
\v 3 Ka ɗaura su a yatsun hannunka; ka rubata su a allon zuciyarka.
\s5
\v 4 Ka ce da hikima, "Ke 'yar'uwata ce," kuma ka kira fahimi danginka,
\v 5 domin ka kiyaye kanka daga mace mazinaciya, daga karuwar mace da maganganunta masu zaƙi.
\s5
\v 6 Ta tagar ɗakina ina leƙe ta labule.
\v 7 Sai na duba wasu dolayen mutane, sai na lura cikin samari wani matashi wanda bashi da hankali.
\s5
\v 8 Saurayin ya gangara wani titi kusa da saƙonta, ya nufi wajen gidanta.
\v 9 Da maraice, wajen yammaci a ranar nan, a lokacin dare da duhu.
\s5
\v 10 A can wata mata ta gamu da shi, ta yi shigar karuwa, mai zuciyar wayo.
\v 11 Tana magana da ƙarfi da iskanci; ƙafafunta basu zauna a gida ba.
\v 12 Yanzu tana titi, an jima tana kasuwa, a kowanne saƙo takan jira ta yi kwanto.
\s5
\v 13 Sai ta kama shi kuma ta sumbace shi, da fuska mai yaudara ta ce masa,
\v 14 "Na yi baikona da salama yau, na cika wa'adina,
\v 15 shi yasa na fito in sadu da kai, da himma in biɗi fuskarka, na kuma same ka.
\s5
\v 16 Na baza shimfiɗu a kan gadona, lilin masu launuka daga Masar.
\v 17 Na fesawa gadona miyor da alos da kirfa.
\v 18 Ka zo, mu sha ƙaunarmu mu ƙoshi har safiya; bari mu ji daɗi sosai cikin ayyukan ƙauna.
\s5
\v 19 Gama mijina ba ya cikin gidansa; ya yi tafiya mai nisa.
\v 20 Ya ɗauki jakkar kuɗi tare da shi; zai dawo in wata ya raba."
\v 21 Da maganganu masu yawa ta sa shi ya ratso; da daɗin bakinta tasa shi ya karkace.
\s5
\v 22 Nan da nan ya bi ta kamar san da ake kai shi wurin yanka, kamar barewar da aka kama a tarko,
\v 23 har sai da kibiya ta tsire shi har zuwa hantarsa. Yana kama da tsuntsun da ya ke gaggautawa ya faɗa tarko. Bai san cewa zai sadaukar da ransa ba ne.
\s5
\v 24 Yanzu dai, ɗana, ka kasa kunne gare ni; ka maida hankali ga maganganun bakina.
\v 25 Kada zuciyarka ta kauce zuwa tafarkunta; kada ka bari a ɓadda kai zuwa tafarkunta.
\s5
\v 26 Ta sa mutane da yawa sun faɗi sokakku; kasassunta da suka mutu na da yawan gaske.
\v 27 Gidanta yana kan tafarkun Lahira; suna gangarawa ne zuwa ɗakunan kwanan mutuwa mai baƙin duhu.
\s5
\c 8
\cl Sura 8
\p
\v 1 Ba hikima na ƙwala kira ba? Ba fahimta na ɗaga muryarta ba?
\v 2 A kan tsaunukan dutse a gefen hanya, a mararrabar hanya, Hikima ta ɗauki matsayinta.
\v 3 A gaban ƙofofi, inda ake shiga cikin birni, a ƙofofin shiga cikin birni, tana ƙwala kira.
\s5
\v 4 A gare ku, ku mutane, nake kira; muryata domin 'yan adam.
\v 5 Ku marasa azanci, ku koyi hikima; ku kuma da kuke wauta, dole ku sami zuciya mai fahimta.
\s5
\v 6 Ku saurara, domin zan yi magana a kan mafifitan al'amura, kuma sa'ad da bakina ya buɗe zan faɗi madaidaitan al'amura.
\v 7 Gama bakina yana faɗin gaskiya, mugunta kuma abin ƙyama ce ga leɓunana.
\s5
\v 8 Dukkan maganganun bakina na adalci ne; a cikinsu ba murɗiya ko karkatarwa.
\v 9 Dukkansu miƙaƙƙu ne ga mutum mai fahimta; maganganuna dai-dai ne ga wanda ya sami ilimi.
\s5
\v 10 Ka sami koyarwata maimakon azurfa; ka sami ilimi maimakon zinariya tsantsa.
\v 11 Domin hikima tafi duwatsu masu ƙawa, ba wata dukiya da ta kai ta daraja.
\s5
\v 12 Ni Hikima ina zaune da Hankali; Na kuma mallaki ilimi da sansancewa.
\v 13 Tsoron Yahweh shi ne ƙin jinin mugunta. Na ƙi girman kai da alfarma, da muguwar hanya, da gamtsin baki, ina ƙinsu.
\s5
\v 14 Ina da shawara mai kyau; da sahihiyar hikima; ni mai gani ce; ƙarfi nawa ne.
\v 15 Ta wuri na sarakai suke sarauta, kuma masu mulki suke tsara dokoki masu adalci.
\v 16 Ta wurina mahukunta ke mulki, hakimai, da dukkan masu mulki da adalci.
\s5
\v 17 Ina ƙaunar masu ƙauna ta, kuma dukkan masu biɗata da himma, suna samu na.
\v 18 A guna akwai wadata da daraja, dawwamammar dukiya da adalci.
\s5
\v 19 'Ya'yana sun fi zinariya, koma sahihiyar zinariya ce; amfanina ya fi azurfa da aka tãce.
\v 20 Ina tafiya a hanyar adalci, cikin tsakiyar tafarkun adalci.
\v 21 Sakamakon wannan, nakan sa masu ƙaunata su gaji wadata; nakan cika rumbunansu taf.
\s5
\v 22 "Yahweh ya hallice ni tun farko, ayyukansa na farko a lokacin.
\v 23 Tun zamanun dãdã da suka wuce aka yini - daga farko, tun farkon duniya.
\s5
\v 24 Kafin tekuna su kasance, aka haife ni - kafin maɓuɓɓugai masu yawan ruwa.
\v 25 Kafin kafawar duwatsu kuma kafin tuddai, aka haife ni.
\s5
\v 26 An haife ni kafin Yahweh ya hallici duniya ko jeji, kafin ma ƙura ta farko a duniya.
\v 27 Ina nan sa'ad da ya kafa sammai, sa'ad da ya zana alamar zobe a sararin zurfi.
\s5
\v 28 Ina nan sa'ad da ya kafa giza-gizai a sama da sa'ad da maɓuɓɓugai cikin zurfi suka kafu.
\v 29 Ina nan sa'ad da ya sa wa teku iyaka, domin kada ruwaye su yi ambaliya su ƙetare umarninsa, da sa'ad da aka dasa iyakar harsashin busasshiyar ƙasa.
\s5
\v 30 Ina gefensa, kamar gwanin masassaƙi, ni abin farincikinsa ne rana bayan rana, ina farinciki a gabansa koyaushe.
\v 31 Ina ta murna da dukkan duniyarsa, kuma farincikina game da 'yan adam ne.
\s5
\v 32 Yanzu dai, 'ya'yana, ku kasa kunne gare ni, domin waɗanda suka kiyaye tafarkuna za a albarkace su.
\v 33 Ku kasa kunne ga koyarwata ku zama da hikima; kada ku ƙi ta.
\v 34 Wanda ya saurareni za a albarka ce shi. Zai yi ta tsaro a ƙofofina kowacce rana, yana ta jira a dogaran ƙofofina.
\s5
\v 35 Gama duk wanda ya same ni, ya sami rai, zai kuma sami tagomashin Yahweh.
\v 36 Amma wanda ya kãsa, yana cutar ransa ne; dukkan masu ƙina mutawa suke ƙauna."
\s5
\c 9
\cl Sura 9
\p
\v 1 Hikima ta gina gidanta; ta sassaƙa ginshiƙai bakwai daga duwatsu.
\v 2 Ta yanka dabbobinta; ta gauraya ruwan inabinta; kuma ta shimfiɗa teburinta.
\s5
\v 3 Ta aiki barorinta; tana kira daga wurare masu tsayi na birni,
\v 4 "Wane ne dolo? Bari ya ratso nan!" Tana magana da wanda ba shi da hankali.
\s5
\v 5 Kazo, ka ci abincina, kuma ka sha ruwan inabi da na gauraya.
\v 6 Ka bar ayyukan dolonci ka rayu; ka bi tafarkin fahimta.
\s5
\v 7 Duk wanda ya hori mai reni za a zage shi, kuma duk wanda ya kwaɓi mugun mutum zai sami zargi.
\v 8 Kada ka tsauta wa mai renako, domin zai ƙi jininka; ka tsauta wa mutum mai hikima, zai ƙaunace ka.
\v 9 Ka bada hikima ga mutum mai hikima, zai ƙara hikima sosai. Ka koya wa adalin mutum, zai ƙaru cikin koyonsa.
\s5
\v 10 Tsoron Yahweh shi ne mafarin hikima, kuma sanin Mai Tsarkin nan shi ne fahimta.
\v 11 Ta wurina za a tsawanta kwanakinka, shekarun rayuwa za a ƙara maka su.
\v 12 Idan kana da hikima, domin kanka kake da hikimar, idan ka yi renako, zaka ɗauka kai kaɗai."
\s5
\v 13 Wawuyar mace mai jahilci ce; ba a iya koyar da ita kuma bata san komai ba.
\v 14 Takan zauna a bakin ƙofarta, a wurare mafi tsayi a gari.
\v 15 Tana kiran masu wucewa a tituna, ga waɗanda ke tafiya a miƙe a hanyarsu.
\s5
\v 16 "Bari wani dolo ya ratso wurin," takan cewa dolaye.
\v 17 "Ruwan da aka sata ya fi daɗi, kuma abincin sirri yana da daɗi.
\v 18 Amma bai sani ba matattu na wajen, cewa gayyatattunta suna cikin zurfin Lahira.
\s5
\c 10
\cl Sura 10
\p
\v 1 Misalai na Suleman. Ɗa mai hikima yakan sa mahaifinsa ya yi farinciki amma wawan ɗa yana kawo wa mahaifiyarsa baƙinciki.
\v 2 Dukiyar da aka tara da mugunta bata da amfani, amma aikata abu nagari zai tsare ka daga mutuwa.
\v 3 Yahweh ba ya barin ran mutum mai adalci ya yunwata, amma yana kaɓar da kwaɗayin mugaye.
\s5
\v 4 Hannun da ke da ƙiyuwa sa mutum ya talauce, amma hannun ma'aikacin mutum yakan ribato arziƙi.
\v 5 Ɗa mai hikima yakan tattara amfani da kaka, amma abin kunya ne ya yi barci da kaka.
\s5
\v 6 Alheran Allah suna kan mutum mai adalci, amma bakin mugu yana cike da ta'addanci.
\v 7 Mutum mai adalci ya kan sa masu tunawa da shi su ji daɗi, amma sunayen mugaye zasu lalace.
\s5
\v 8 Mutane masu hankali suna karɓar umarni, amma wawa mai surutai zai lalace.
\v 9 Mai rayuwa cikin adalci zai yi tafiya lafiya, amma wanda ya maida tafarkunsa na maguɗi, za a kama shi.
\s5
\v 10 Mai ƙibce da ido yana kawo baƙinciki, amma wawa mai surutai za a kã da shi.
\v 11 Bakin mutum mai adalci maɓuɓɓugar ruwan rai ne, amma bakin mugu yana rufe da ta'addanci.
\s5
\v 12 ̀Ƙiyayya tana haddasa tashin hankali, amma ƙauna tana rufe dukkan laifofi.
\v 13 Hikima tana kan leɓen mutum mai basira, amma bulala domin bayan wanda ba shi da hankali ne.
\s5
\v 14 Mutane masu hikima suna tara ilimi, amma bakin wawa yana kawo hallakarwa kusa.
\v 15 Wadatar mutum attajiri shi ne tsararren birninsa; talaucin matsiyaci shi ne hallakarsa.
\s5
\v 16 Ladan mutum mai adalci yana kai ga rai; ribar mugaye takan kai su ga zunubi.
\v 17 Akwai tafarkin rai domin wanda ya ke bin tarbiya, amma wanda ya ƙi kwaɓa ya bijire ne.
\s5
\v 18 Kowanne ya ɓoye ƙiyayya yana da leɓunan ƙarya, wanda ya baza tsegumi wawa ne.
\v 19 Sa'ad da akwai maganganu dayawa, ba a rasa zunubi, amma wanda ya ke lura da abin da ya ke faɗa mai hikima ne.
\s5
\v 20 Harshen mutum mai adalci azurfa ne tsantsa; babu wani abin amfani a zuciyar mugu.
\v 21 Leɓunan mutum mai adalci sukan amfani mutane da yawa, amma wawaye sukan mutu saboda da rashin hankalinsu.
\s5
\v 22 Alheran Yahweh masu kyau sukan kawo wadata kuma ba ya sa cutarwa a ciki.
\v 23 Mugunta abu ne da wawa ya ke jin daɗi yana kuma wasa da ita, amma hikima abu ne na jin daɗi ga mutum mai fahimi.
\s5
\v 24 Abin da mugu ke jin tsoro zai auka masa, amma za a biya muraɗin adilai.
\v 25 Mugaye kamar hadari mai wargajewa ne, sai kawai ka ga basu kuma, amma adalai ginshiƙi ne da ya dawwama har abada.
\s5
\v 26 Kamar abu mai tsami a hakori koma kamar hayaƙi a idanu, haka ma rago ya ke ga waɗanda suka aike shi.
\v 27 Tsoron Yahweh ya kan tsawonta rai, amma shekarun mugaye za a gajarta su.
\s5
\v 28 Begen mutane adilai shi ne murnarsu, amma shekarun mutane mugaye zasu gajarce.
\v 29 Hanyar Yahweh ta kan tsare aminci, amma hallaka ce domin mugaye.
\v 30 Ba za a taɓa kawar da mutum mai adalci ba, amma mugu ba zai zauna a ƙasar ba.
\s5
\v 31 Daga bakin adilin mutum 'ya'yan hikima suke fitowa, amma za a sare harshe mai gatse.
\v 32 Leɓunan mutum mai adalci sun san karɓaɓɓiyar magana, amma bakin mugu, sun san abin cutarwa kawai.
\s5
\c 11
\cl Sura 11
\p
\v 1 Yahweh yana ƙin ma'aunai da ba na gaskiya ba, amma yana murna da madaidaicin nauyi.
\v 2 Sa'ad da girmankai yazo, daga nan ƙasƙanci ke zuwa, amma tare da tawali'u hikima ke zuwa.
\s5
\v 3 Mutanen kirki mutuncinsu ke bishe su, amma hanyoyin zamba kan hallaka maciya amana.
\v 4 Dukiya ba komai ba ce a ranar hukunci, amma yin abin da ke dai-dai zai hana ka mutuwa.
\s5
\v 5 Halin kirkin amintaccen mutum kansa hanyarsa ta zama a sawwaƙe, amma mugu zai faɗi saboda muguntarsu.
\v 6 Halin kirki na waɗanda suke gamsar Allah kan kiyaye su lafiya, amma marasa aminci haɗamarsu ce takan zamar masu tarko.
\s5
\v 7 Sa'ad da mugun mutum ya mutu, sa zuciyarsa takan lalace sa zuciyar kuma da ke kan ƙarfinsa takan ɓace.
\v 8 Akan kiyaye adalin mutum daga wahala kuma takan aukawa mugu a maimako.
\s5
\v 9 Marar tsoron Allah da bakinsa yakan hallaka maƙwabcinsa, amma ta wurin hikima adalai sukan sami tsaro.
\v 10 Sa'ad da adalan mutane suka azurta, birni yakan yi farinciki; sa'ad da mugu ya lalace, akwai sowa ta murna.
\v 11 Ta wurin kyautai masu kyau na waɗanda ke farantawa Allah rai, birni yakan ƙasaita; amma ta wurin maganganun mugaye, birni yakan ɓarke ƙasa.
\s5
\v 12 Mutumin da ke rena abokinsa bashi da tunani, amma mutum mai fahimta yakan yi shiru.
\v 13 Duk mai yawon yin tsegumi yakan bayyana asirai, amma amintaccen mutum yakan rufe al'amarin.
\s5
\v 14 Wurin da babu jagoranci cikin hikima al'umma takan faɗi, amma nasara takan zo ta wurin tuntuɓar mashawarta masu yawa.
\s5
\v 15 Duk wanda ya ɗaukar wa bãƙo lamuni lallai shi zai cutu, amma wanda ya ƙi bayarwa ta wurin ɗaukar alƙawari ya kuɓuta.
\v 16 Mace cike da alheri takan sami girmamawa, amma azzalumai na haɗamar dukiya.
\s5
\v 17 Mutum mai taimako yakan amfanawa kansa, amma macuci kansa ya ke cuta.
\v 18 Mugun mutum yakan kwanta ya sami ladansa, amma wanda ya shuka abin da ke dai-dai yakan girbi sakamakon gaskiya.
\s5
\v 19 Mutum mai gaskiya wanda ya yi abin da ke dai-dai zai rayu, amma wanda ke bin mugunta zai mutu.
\v 20 Yahweh yana ƙin waɗanda tunaninsu mugaye ne, amma yana murna ga waɗanda hanyoyinsu marasa aibu ne.
\s5
\v 21 Ku tabbatar da wannan - mugun mutum ba zai tafi ba tare da hukunci ba, amma zuriyar mutane masu adalci zasu zauna lafiya.
\v 22 Kome kyaun mace idan bata da tunani tana kama da zoben zinariya a hancin alade.
\s5
\v 23 Abin da adalan mutane suke so yakan jawo abu mai kyau, amma mugayen mutane zasu sa begensu ga hukunci kaɗai.
\v 24 Akwai mai warwatsawa - zai samu ma da yawa; wani kuma yakan riƙe abin da zai bayar - yakan talauce.
\s5
\v 25 Mutum mai bayarwa zai azurta kuma wanda ya ke bada ruwa ga waɗansu zai sami ruwa domin kansa.
\v 26 Mutane sukan la'anta mutumin da yaƙi sayar da hatsi, amma kyaututtuka masu kyau sukan zama kambi akan mutumin daya sayar da nasa.
\s5
\v 27 Mai la'akarin neman abu mai kyau yana neman tagomashi, amma mai neman mugunta zai same ta.
\v 28 Masu dogara ga dukiyarsu zasu faɗi, amma kamar ganye, haka adalan mutane zasu azurta.
\s5
\v 29 Wanda ya jawo wa iyalin gidansa wahala zai gãji iska wawa kuma zai zama bawan mai hikima a zuciya.
\s5
\v 30 Adalin mutum zai zama kamar itacen rai, amma tashin hankali ya kan ɗauke rayuka.
\v 31 Duba! Adalin mutum yana karɓar abin da ya dace da shi; balle ma mugu da mai zunubi!
\s5
\c 12
\cl Sura 12
\p
\v 1 Duk mai son horo yana son ilimi, amma wanda ya ke ƙin yarda da gyara wawa ne.
\v 2 Mutumin kirki yakan sami tagomashi a wurin Yahweh, amma yakan hukunta mutum mai shirya miyagun dabaru.
\s5
\v 3 Mutum ba zai kafu ta wurin mugunta ba, amma ba za a tuge adalan mutane ba.
\v 4 Mace mai tsabtar rai kambi ce ga mijinta, amma ita mai kawo kunya tana kama da cuta mai ruɓar da ƙasusuwansa.
\s5
\v 5 Shirye-shiryen adali adalci ne, amma shawarar mugu yaudara ce.
\v 6 Maganganun miyagun mutane su ne ayi kwanto a jira domin a sami zarafin yin kisa, amma maganganun adalai sukan cece su.
\s5
\v 7 Miyagun mutane ana kaɓantar da su kuma sun tafi, amma gidan adalin mutum zai tsaya.
\v 8 Akan yabi mutum bisa ga yawan hikimar da ya ke da ita, amma za a rena wanda ya ke tunanin mugunta.
\s5
\v 9 Gara baka da wani muƙami mai muhimmanci - kawai kana matsayin bawa - da kayi fankamar kai wani ne amma baka da abinci.
\v 10 Adalin mutum yakan kula da buƙatun dabbobinsa, amma ko tausayin mugu zalunci ne.
\s5
\v 11 Wanda ya yi aiki a gonarsa zai sami isasshen abinci, amma duk mai bin ayyuka marasa ma'ana ba shi da tunani.
\v 12 Mugun mutum yana marmarin abin da mugayen mutane suka sato daga wurin waɗansu, amma ribar adalai sukan zo daga gare su ne.
\s5
\v 13 Maganar mugun mutum takan zamar masa tarko, amma adalin mutum yakan kuɓuta daga wahala.
\v 14 Mutum zai ƙoshi da abubuwa masu kyau ta wurin amfanin maganganunsa, kamar yadda aikin hannuwansa zai sãka masa.
\s5
\v 15 Hanyar wawa a ganinsa dai-dai ce, amma mutum mai hikima yakan saurari shawara.
\v 16 Wawa yakan nuna fushinsa nan da nan, amma mai yin watsi da zagi yana da hikima.
\s5
\v 17 Wanda ke faɗin gaskiya yana faɗin abin da ke dai-dai, amma mai shaidar zur na faɗin ƙarairayi.
\v 18 Maganganun mai faɗin magana cikin garaje na kama da saran takobi, amma harshen mai hikima kan kawo warkarwa.
\s5
\v 19 Leɓuna masu faɗin gaskiya sukan tabbata har abada, amma harshe mai yin ƙarya na ɗan lokaci ne.
\v 20 Akwai yaudara cikin zukatan masu shirin aikata mugunta, amma murna takan zo wa masu shawarar salama.
\s5
\v 21 Ba cutar da zata sami adalin mutum, amma mugayen mutane suna cike da wahaloli.
\v 22 Yahweh yana ƙin leɓunan masu faɗar ƙarya, amma masu zama cikin aminci abin murnarsa ne.
\s5
\v 23 Mutum mai hikima yakan ɓoye abin da ya sani, amma zuciyar wawaye takan yi shelar wauta.
\v 24 Hannun mai ƙwazo zai yi mulki, amma ragayen mutane za a sa su aikin dole.
\s5
\v 25 Damuwa cikin zuciyar mutum takan nawaita masa, amma maganganu masu kyau sukan sa shi ya yi murna.
\v 26 Adalin mutum jagora ne ga abokinsa, amma hanyar miyagu takan bauɗar da su.
\s5
\v 27 Ragayen mutane ba zasu iya gasa naman farautarsu ba, amma mutum mai ƙwazo zai sami dukiya mai tamani.
\v 28 Waɗanda suka yi tafiya a hanyar da ke dai-dai sukan sami rai a cikin tafarkinsa babu mutuwa.
\s5
\c 13
\cl Sura 13
\p
\v 1 Ɗa mai hikima yakan saurari koyarwar mahaifinsa, amma shaƙiyi ba zai saurari tsautawa ba.
\v 2 Mutum zai ci moriyar abubuwa masu kyau ta wurin amfanin bakinsa, amma marmarin mayaudara ta'addanci ne.
\s5
\v 3 Mai tsaron bakinsa yana kare ransa, amma wanda ya wage bakinsa zai hallaka kansa.
\v 4 Raggayen mutane na marmarin samu, amma ba sa samun komai, amma begen mutane masu ƙwazo zai sami ƙosarwa.
\s5
\v 5 Mutum mai adalci ya kan ƙi ƙarairayi, amma mugun mutum yakan maida kansa abin ƙyama, kuma yakan yi abin kunya.
\v 6 Adalci yakan tsare kamilai a cikin tafarkinsu, amma mugunta ta kan juyar da waɗanda suka aikata zunubi.
\s5
\v 7 Akwai wani mai azurta kansa, amma ba shi da komai sam, kuma akwai wanda ba ya ba kansa komai, duk da haka yana da wadata da gaske.
\v 8 Fãnsar ran mai arzaki dukiyarsa ce, amma matalauci baya jin razanarwa.
\s5
\v 9 Hasken adalan mutane yakan yi murna, amma fitilar miyagun mutane za a ɓice ta.
\v 10 Girmankai husuma kaɗai ya ke kawowa, amma akwai hikima ga waɗanda ke karɓar shawara.
\s5
\v 11 Wadata zata ragu idan hanyar samunta ta banza ce, amma wanda ya sami kuɗi ta wurin yin aiki da hannunsa zai sa kuɗinsa su ƙaru.
\v 12 Sa'ad da aka dakatar da bege, zuciya takan karaya, amma samun abin da aka sa zuciya itacen rai ne.
\s5
\v 13 Duk wanda ya rena umarni yana jawowa kansa hallaka, amma mai mutunta doka za a sãka masa.
\v 14 Koyarwar mai hikima maɓulɓular rai ce, da zasu juyar da kai daga tarkunan mutuwa.
\s5
\v 15 Tunani mai kyau kan jawo tagomashi, amma hanyar mai cin amana bata da iyaka.
\v 16 Mutane masu hikima sukan yi aikinsu bisa ga ilimi a cikin kowacce shawara, amma wawa yakan bayyana wawancinsa.
\s5
\v 17 Mugun ɗan saƙo yakan faɗa cikin damuwa, amma amintaccen wakili yakan kawo sasanci.
\v 18 Wanda ya ƙi koyarwa zai sami talauci da kunya, amma girmamawa zata zo ga wanda ya koya ta wurin gyara.
\s5
\v 19 Samun abin da aka daɗe ana sauraro da daɗi ya ke ga rai, amma wawaye na ƙin juyawa daga mugunta.
\v 20 Ka yi tafiya da masu hikima zaka zama mai hikima, amma abokin tafiyar wawaye zai hallaka
\s5
\v 21 Bala'i na bin masu zunubi, amma adalan mutane za a saka masu da abu mai kyau.
\v 22 Nagarin mutum yakan bar gãdo domin 'ya'yan 'ya'yansa, amma a kan ajiye dukiyar mai zunubi domin adalin mutum.
\s5
\v 23 Gonar talaka da ba'a nomawa akwai abinci da yawa, amma rashin adalci yakan kawar da shi.
\v 24 Wanda baya horon ɗansa yana ƙinsa, amma mai ƙaunar ɗansa yana kula ya hore shi.
\s5
\v 25 Adalin mutum yakan ci har sai ya ƙosadda marmarinsa, amma cikin mugu koyaushe yunwa ya ke ji.
\s5
\c 14
\cl Sura 14
\p
\v 1 Mace mai hikima takan gina gidanta, amma wawar mace takan rushe shi da hannuwanta.
\v 2 Wanda ya ke tafiya cikin gaskiya yana tsoron Yahweh, amma wanda ba shi da gaskiya yana rena shi.
\s5
\v 3 Daga bakin wawa tsiron girman kansa ke fitowa, amma leɓunan masu hikima zasu tsare su.
\v 4 Wurin da babu dabbobi kwamin ciyar da dabbobi yakan zama da tsabta, amma isasshen abinci yakan zo ta wurin ƙarfin bajimi.
\s5
\v 5 Amintaccen mashaidi ba yayin ƙarya, amma mai shaidar zur ƙarairayi ya ke furtawa.
\v 6 Mai ba'a yakan nemi hikima amma ba zai samu ba, amma ilimi yakan zo a sauƙaƙe ga wanda ya ke da fahimta.
\s5
\v 7 Ka guje wa wawan mutum, domin ba zaka sami ilimi daga maganganunsa ba.
\v 8 Hikimar mutum mai fahimta shi ne ya gane hanyarsa, amma wautar wawaye itace yaudara.
\s5
\v 9 Wawaye sukan yi ba'a sa'ad da aka miƙa hadayar laifi, amma a kan raba tagomashi tsakanin kamilai.
\v 10 Zuciya tasan ɓacin ranta bata raba murnarta da bãƙo.
\s5
\v 11 Za a hallaka gidan mugayen mutane, amma rumfar masu adalci zata yi albarka.
\v 12 Akwai hanya wadda take dai-dai ga ganin mutum, amma ƙarshenta takan kai ga mutuwa kaɗai.
\s5
\v 13 Zuciya na iya dariya amma ta kuma kasance cikin damuwa murna kuma kan iya zama baƙinciki.
\v 14 Marar aminci zai sami abin da ya dace da hanyoyinsa, amma nagarin mutum zai sami abin da ke nasa.
\s5
\v 15 Marar wayo yakan gaskanta kowanne abu, amma mutum mai himma yakan yi tunani game da takawarsa.
\v 16 Mutum mai hikima yakan ji tsoro kuma ya rabu da mugunta, amma wawa da gangan yakan yi banza da gargaɗi.
\s5
\v 17 Mai saurin fushi yakan yi abubuwan wauta, kuma mutum mai tsara mugayen dabaru a na ƙinsa.
\v 18 Marasa wayo sukan gãji wauta, amma mutane masu himma a na masu kambi da ilimi.
\s5
\v 19 Mugayen mutane zasu russuna a gaban waɗanda ke nagari masu mugunta kuma zasu russuna a ƙofofin masu adalci.
\v 20 Matalauci har abokan hurɗansa ƙinsa suke, amma masu arziki suna da abokai da yawa.
\s5
\v 21 Wanda ya rena maƙwabcinsa zunubi ya ke yi, amma wanda ke taimakon matalauci mai albarka ne.
\v 22 Masu shirin mugunta ba ratse hanya suke yi ba? Amma masu shirin yin alheri zasu karɓi rabon amintacciyen alƙawari da karɓuwa.
\s5
\v 23 Ta wurin aiki tuƙuru a kan sami riba, amma wurin da taɗi ne kawai, talauci yakan zo.
\v 24 Rawanin masu hikima dukiyarsu ce, amma wautar wawaye takan ƙara kawo masu wawanci.
\s5
\v 25 Mashaidi mai gaskiya yakan ceci rayuka, amma mai shaidar zur yakan furta ƙarairayi.
\s5
\v 26 Sa'ad da wani yaji tsoron Yahweh, shi ma yana da gabagaɗi a cikinsa; waɗannan abubuwa zasu zama kamar wurin fakewa mai ƙarfi domin 'ya'yan wannan mutumin.
\v 27 Tsoron Yahweh maɓulɓula ne na rai, domin mutum ya iya juyawa daga tarkunan mutuwa.
\s5
\v 28 Ɗaukakar sarki na cikin yawan mutanensa, amma rashin mutane ke hallaka yarima.
\v 29 Mutum mai jinkirin fushi na da ganewa mai yawa, amma mutum mai garaje na ɗaukaka wauta.
\s5
\v 30 Natsattsiyar zuciya rai ce ga jiki, amma kishi yakan ruɓar da ƙasusuwa.
\v 31 Wanda ya zalunci matalauta yana la'anta Mahaliccinsa, amma wanda ya nuna tagomashi ga mabuƙata yana girmama shi.
\s5
\v 32 Akan kãda mugun mutum ƙasa ta wurin mugayen ayyukansa, amma mai adalci na da mafaka ko a cikin mutuwa.
\v 33 Hikima takan zauna cikin zuciyar mai fahimta, amma ko cikin wawaye takan bayyana kanta.
\s5
\v 34 Aikata adalci na ɗaukaka al'umma, amma zunubi abin kunya ne ga kowacce jama'a.
\v 35 Tagomashin sarki na tare da baran da ke aiki da himma, amma fushinsa na kan wanda ke aikata abin kunya.
\s5
\c 15
\cl Sura 15
\p
\v 1 Mayar da magana da taushi kan juyar da hasala, amma magana mai zafi na tada fushi.
\v 2 Harshen mutane masu hikima na yabon ilimi, amma bakin wawaye yana zuba wauta.
\s5
\v 3 Idanun Yahweh suna ko'ina, suna lura da mugaye da nagari.
\v 4 Harshe mai warkarwa Itacen rai ne, amma harshe mai yaudara na karya ruhu.
\s5
\v 5 Wawa yakan ƙi kulawa da umarnin mahaifinsa, amma wanda ke koya ta wurin gyara mai himma ne.
\v 6 A cikin gidan adalin mutum akwai dukiya mai yawa, amma dukiyar mugun mutum na ba shi damuwa.
\s5
\v 7 Leɓunan mutane masu hikima sukan baza ilimi, amma ba haka zukatan wawaye suke ba.
\v 8 Yahweh yana ƙin hadayun mugayen mutane, amma yana murna da addu'ar adalai.
\s5
\v 9 Yahweh ya ƙi hanyar mugayen mutane, amma yana ƙaunar wanda ke bin abin da ke dai-dai.
\v 10 Horo mai zafi na jiran duk wanda yabar hanyar da ke dai-dai shi kuma wanda yaƙi tsautawa zai mutu.
\s5
\v 11 Lahira da hallakarwa a buɗe suke a gaban Yahweh; to balle zukatan "yan adam?
\v 12 Mai ba'a baya son gyara; ba zai je wurin mai hikima ba.
\s5
\v 13 Zuciya mai murna takan sa fuska tayi murmushi, amma ciwon zuciya yakan karyar da ruhu.
\v 14 Zuciya mai basira takan nemi ilimi, amma bakin wawa naci daga wawanci.
\s5
\v 15 Mutanen da ke shan tsanani suna cikin takaici dukkan kwanakin ransu, amma zuciya mai farinciki zata yi buki marar matuƙa.
\v 16 Gwamma a samu kaɗan tare da tsoron Yahweh da samun dukiya da yawa cikin ruɗami.
\s5
\v 17 Cin abinci tare da 'ya'yan itatuwa a wurin da akwai ƙauna ya fi cin ɗan maraƙi mai ƙiba tare da ƙiyayya.
\v 18 Mutum mai zafin rai yakan tãda husuma, amma mai jinkirin fushi na kwantar da rigima.
\s5
\v 19 Hanyar rago na kama da wurin da aka shinge ta da ƙayayuwa, amma hanyar adali lafiyayya ce.
\v 20 Ɗa mai hikima na kawo farinciki ga mahaifinsa, amma wawa yana rena mahaifiyarsa.
\s5
\v 21 Daƙiƙai na murna da mutumin da ba shi da tunani, amma mai fahimta na tafiya a hanyar da ke dai-dai.
\v 22 Wurin da babu shawara shirye-shirye kan tafi ba dai-dai ba, amma zasu yi nasara inda akwai mashawarta da yawa.
\s5
\v 23 Mutum yakan sami farinciki sa'ad da ya bada amsar da ta dace; magana a lokacin da ya dace abu mai kyau ne!
\v 24 Tafarkin rai na kaiwa sama-sama ga mutane masu himma, domin su tsere daga Lahira ta ƙarƙashi.
\s5
\v 25 Yahweh yana rushe gidan mai girmankai, amma yana kiyaye dukiyar gwauruwa.
\v 26 Yahweh yana ƙin tunanin mugayen mutane, amma kalmomi masu daɗi tsabtatattu ne.
\s5
\v 27 Ɗan fashi na kawo masifa cikin iyalinsa, amma mai ƙin cin hanci zai rayu.
\v 28 Zuciyar adalin mutum takan yi tunani kafin ta bada amsa, amma bakin mugayen mutane na zuba dukkan muguntarsa.
\s5
\v 29 Yahweh na nesa da mugayen mutane, amma yana jin addu'ar adalan mutane.
\v 30 Fuska mai fara'a takan kawo murna ga zuciya kuma labari mai daɗi lafiya ce ga jiki.
\s5
\v 31 Idan ka maida hankali sa'ad da wani ke maka gyara yadda zaka yi rayuwa, zaka zauna cikin mutane masu hikima.
\v 32 Wanda yaƙi horo rena kansa ya ke yi, amma mai sauraron gyara zai sami fahimta.
\s5
\v 33 Tsoron Yahweh na koyar da hikima kuma tawali'u kuma na zuwa kafin girmamawa.
\s5
\c 16
\cl Sura 16
\p
\v 1 Shirye-shiryen zuciya na mutum ne, amma daga harshen Yahweh amsa ke fitowa.
\v 2 Dukkan hanyoyin mutum suna da tsarki a ganinsa, amma Yahweh ke auna ruhohi.
\s5
\v 3 Ka miƙa ayyukanka ga Yahweh shirye-shiryenka kuma zasu yi nasara.
\v 4 Yahweh ya yi kowanne abu da dalili, har da mugu domin ranar wahala.
\s5
\v 5 Yahweh na ƙin kowanne mutum mai zuciya mai fahariya, amma ku tabbatar da wannan, ba zasu kuɓuta daga hukunci ba.
\v 6 Ɗa amintaccen alƙawari da gaskatawa akan gafarta zunubi ta wurin tsoron Yahweh mutane suke juyawa daga mugunta.
\s5
\v 7 Lokacin da hanyoyin mutum suka gamshi Yahweh, zai sa maƙiyan mutumin su zauna lafiya da shi.
\v 8 Gwamma kaɗan da abin da ke na adalci, da dukiya mai yawa da ke ta rashin adalci.
\s5
\v 9 A cikin zuciya mutum ke shirya hanyarsa, amma Yahweh ke bida sawayensa.
\v 10 Ƙudurori masu zurfi na a leɓunan sarki, kada bakinsa ya munafunci adalci.
\s5
\v 11 Ma'aunai na gaskiya na zuwa ne daga Yahweh; dukkan ma'aunai cikin jakka ayyukansa ne.
\v 12 Sa'ad da sarakuna suka yi mugayen abubuwa, wannan abin ƙi ne, gama kursiyi na kafuwa ne ta wurin yin abin da ke dai-dai.
\s5
\v 13 Sarki na murna da leɓunan da ke faɗin abin da ke dai-dai kuma yana ƙaunar mai magana kaitsaye.
\v 14 Fushin sarki saƙon mutuwa ne amma mutum mai hikima zai yi ƙoƙarin kwantar da fushinsa.
\s5
\v 15 A cikin fara'ar sarki rai ne kuma tagomashinsa na kama da hadari mai kawo ruwan sama a lokacin bazara.
\v 16 Yafi kyau a sami hikima fiye da zinariya. A sami fahimta yafi neman azurfa.
\s5
\v 17 Babbar hanyar adalan mutane na kauce wa mugunta; wanda ke kãre ransa na kula da hanyarsa.
\v 18 Girmankai na zuwa kafin hallaka kuma ruhun fahariya kafin fãɗuwa.
\s5
\v 19 Ya fi kyau ka zama mai tawali'u cikin matalauta da ka zama mai raba ganima tare da masu girmankai.
\v 20 Duk wanda ke tunani a kan abin da aka koya masa zai sami abin da ke mai kyau, waɗanda kuma suka dogara ga Yahweh zasu yi albarka.
\s5
\v 21 Mai hikima cikin zuciya za a ce da shi mai sansancewa kuma zaƙin maganarsa na inganta iya koyarwa.
\v 22 Fahimta maɓuɓɓugar rai ce ga wanda ya ke da ita, amma umarnin wawaye wawancinsu ne.
\s5
\v 23 Zuciyar mutum mai hikima na bada basira ga bakinsa ta kuma ƙara ikon rinjaya ga leɓunansa.
\v 24 Kalmomi masu daɗi saƙar zuma ce - abin daɗi ga rai warkarwar kuma ga ƙasusuwa.
\s5
\v 25 Akwai hanyar da ke dai-dai ga mutum, amma ƙarshenta hanyar zuwa ga mutuwa ce.
\v 26 Marmarin ma'aikaci na yi masa aiki; yunwarsa na tura shi gaba.
\s5
\v 27 Mutum marar amfani na haƙo da damuwa maganarsa kuma na kama da wuta mai ƙuna.
\v 28 Mugun mutum na tãda tashin hankali magulmaci kuma na raba abokanai na kurkusa.
\s5
\v 29 Mutum mai ta'addanci na yin ƙarya ga maƙwabcinsa ya kuma gangara dashi ga tafarki da ba dai-dai ba.
\v 30 Mutum mai kaɗa ido abubuwan mugunta ya ke ƙullawa; waɗanda ke tsayar da leɓuna zasu kawo mugunta.
\s5
\v 31 Furfura kambin daraja ce; a na samunta ne ta yin rayuwar data dace.
\v 32 Ya fi kyau ka zama mai jinkirin fushi da ka zama jarumi kuma wanda ke mulkin ruhunsa ya fi wanda ke mamaye birni.
\s5
\v 33 Akan jefa ƙuri'a a cikin cinya, amma yanke shawara daga wurin Yahweh ne.
\s5
\c 17
\cl Sura 17
\p
\v 1 Ya fi a ci busasshiyar gurasa rai kwance da gida cike da shagali tare da tashin hankali.
\v 2 Bawa mai hikima zai yi mulki bisa ɗan da ke aikata abin kunya zai kuma sami rabon gãdo kamar ɗaya daga cikin 'yan'uwa.
\s5
\v 3 Maƙera da tanderun wuta domin tãce azurfa da zinariya ne; amma Yahweh ke tace zukata.
\v 4 Mai aikata mugunta na kasa kunne ga mugayen leɓuna; maƙaryaci na sauraren harshe mai hallakarwa.
\s5
\v 5 Duk wanda ya yi wa matalauci ba'a Mahallicinsa ya ke zagi kuma wanda ke farinciki da hasara ba zai tsira ba tare da hukunci ba.
\v 6 Jikoki kambin tsofaffi ne iyaye kuma suna kawo daraja ga 'ya'yansu.
\s5
\v 7 Yin magana da ƙwarewa bata da daɗi ga wawa; balle leɓuna masu faɗin ƙarya ba dai-dai bane da masu mulki.
\v 8 Cin hanci na kama da dutsen dabo ga wanda ya bada shi; duk inda ya juya, nasara ya ke yi.
\s5
\v 9 Duk wanda ke yafe laifi yana neman ƙauna, amma wanda ke maimaita batu yana raba abokai na kurkusa.
\v 10 Tsautawa kan shiga da zurfi cikin mutumin da ke da fahimta fiye da naushe-naushe ɗari ga jikin wawa.
\s5
\v 11 Mugun mutum tawaye kaɗai ya ke nema, don haka za a aika masa da mugun manzo ya yi gãba da shi.
\v 12 Ya fi kyau ka gamu da kerkeci wadda aka kwashe mata 'ya'yanta da ka gamu da wawa cikin wawancinsa.
\s5
\v 13 Idan wani ya maida mugunta maimakon alheri, mugunta ba zata taɓa rabuwa da gidansa ba.
\v 14 Mafarin jayayya na kama da wanda ya saki ruwa ko'ina, don haka ka kaucewa jayayya kafin ta ɓarke ko'ina.
\s5
\v 15 Mutumin da ya baratar da mugun mutum da mutumin da ya kãda adalin mutum - dukkansu abin ƙi ne ga Yahweh.
\v 16 Donme wawa zai biya kuɗi ya koyi hikima, ganin cewa ba shi da iyawar koyon ta?
\s5
\v 17 A koyaushe aboki yana nuna ƙaunarsa ɗan'uwa kuma an haife shi ne domin kwanakin damuwa.
\v 18 Sai mutum marar hankali ke ɗaukar zaunannun alƙawarai domin basusuwan maƙwabcinsa.
\s5
\v 19 Duk wanda ke ƙaunar rikici yana ƙaunar zunubi; wanda ya sa bakin ƙofarsa tayi yawan tsayi zai haifar da karyewar ƙashi.
\v 20 Mutumin da ke da gurɓatacciyar zuciya ba ya ganin abin da ke dai-dai; wanda ke da mugun harshe na faɗawa cikin bala'i.
\s5
\v 21 Mahaifin da ɗansa wawa ne yakan jawowa kansa ɓacin rai; mahaifin wawa kuma ba shi da farinciki.
\v 22 Zuciya mai farinciki magani ne mai kyau, amma karyayyen ruhu kan busar da ƙasusuwa.
\s5
\v 23 Mugun mutum yakan karɓi cin hanci a ɓoye domin ya karkatar da hanyoyin adalci.
\v 24 Mai fahimta yakan sa fuskarsa wajen hikima, amma idanun wawa a kafe suke har ga ƙarshen duniya.
\s5
\v 25 Wawan ɗa abin baƙinciki ne ga mahaifinsa abin haushi ne kuma ga matar da ta haife shi.
\v 26 Haka kuma, ba dai-dai ba ne a hukunta mutum mai adalci; kuma ba shi da kyau a bulali mutane masu daraja masu mutunci.
\s5
\v 27 Wanda ke da ilimi yakan yi amfani da kalmomi kaɗan wanda kuma ke da fahimta yana da natsuwa.
\v 28 Har wawa idan ya yi shiru za a zaci shi mai hikima ne; sa'ad da bai yi magana ba, ana masa kallon mai basira.
\s5
\c 18
\cl Sura 18
\p
\v 1 Wanda ya ware kansa muradin kansa ya ke nema yana kuma jayayya da dukkan hukunci mai kyau.
\v 2 Wawa bai da mu da ya fahimta ba, amma ya da mu kaɗai ya bayyana abin da ke cikin zuciyarsa.
\s5
\v 3 Sa'ad da mugun mutum yazo, reni yakan zo tare da shi - tare da kunya da ƙasƙanci.
\v 4 Maganganun bakin mutum ruwaye ne masu zurfi; maɓulɓular hikima rafi ne mai gudãna.
\s5
\v 5 Ba dai-dai ba ne a nuna son kai ga mugun mutum, ko a hana adalci ga mutum mai adalci.
\v 6 Maganar wawa takan jawo masa tsatsaguwa bakinsa kuma na gayyatar dũka.
\s5
\v 7 Bakin wawa ke lalatar da shi da leɓunansa kuma ya ke ɗana wa kansa tarko.
\v 8 Maganganun magulmaci na kãma da loma mai daɗi sukan kuma gangara zuwa can cikin ciki.
\s5
\v 9 Haka kuma, wanda ya yi sanyi cikin aikinsa ɗan'uwa ne da wanda ke lalatarwa sosai.
\v 10 Sunan Yahweh ƙaƙƙarfar hasumiya ne; adalan mutum yakan ruga cikinsa ya kuma tsira.
\s5
\v 11 Attajiri na zaton dukiyarsa ce zata kare shi kamar garu mai tsayi da ke kewaye da birni.
\v 12 Kafin faɗuwarsa zuciyar mutum takan kumbura, amma tawali'u yakan zo kafin girmamawa.
\s5
\v 13 Wanda ya amsa kafin ya saurara - wauta ce a gare shi da kunya.
\v 14 Ruhun mutum zai jure rashin lafiya, amma wa zai daure da karyayyen ruhu?
\s5
\v 15 Zuciyar mai ƙwazo takan sami ilimi kunnen mai hikima yana biɗarsa.
\v 16 Kyautar mutum zata bude masa hanya ta kuma kai shi gaban mutum mai muhimmanci.
\s5
\v 17 Wanda ya fara gabatar da damuwarsa za a ga shi ne da gaskiya har sai abokin ƙara ya zo ya ƙalubalance shi.
\v 18 Jefa ƙuri'a takan dai-daita jayayya ta raba tsakanin masu iko da ke jayayya.
\s5
\v 19 Ɗan'uwan da aka ɓata da shi ya fi birni mai ƙarfi wuyar shiryawa, tantankawa kuma na kama da makaran kagara.
\v 20 Cikin mutum zai ƙoshi da amfanin bakinsa; zai gamsu da amfanin leɓunansa.
\s5
\v 21 Mutuwa da rai harshe ne ke sarrafasu, waɗanda ke ƙaunar harshe zasu ci amfaninsa.
\v 22 Wanda ya sami mata abin kirki ya samu yana kuwa samun tagomashi daga wurin Yahweh.
\s5
\v 23 Fakirin mutum yakan roƙi jinƙai, amma mawadaci na amsa magana da kaushi.
\v 24 Wanda ke taƙamar yana da abokai da yawa, sukan yashe shi ta wurinsu, amma akwai abokin da ke zuwa kusa fiye da ɗan'uwa.
\s5
\c 19
\cl Sura 19
\p
\v 1 Gara matalaucin mutum mai tafiya cikin mutuncinsa da mai maganar mugunta gashi kuwa wawa.
\v 2 Kuma, ba shi da kyau a kasance da marmari ba tare da sani ba kuma wanda ke gudu da sauri yakan ɓata hanya.
\s5
\v 3 Wautar mutum takan ɓata ransa zuciyarsa kuma tana fushi gãba da Yahweh.
\v 4 Arziki na ƙara abokai da yawa, amma matalauci a ware ya ke da abokansa.
\s5
\v 5 Mai shaidar zur ba zai tserewa hukunci ba mai furta ƙarairayi ba zai kuɓuta ba.
\v 6 Mutane da yawa zasu roƙi tagomashi daga wurin mutum mai kyauta kuma kowanne mutum aboki ne ga mai bada kyautai.
\s5
\v 7 Dukkan 'yan'uwan matalauci na ƙinsa; balle ma abokansa waɗanda suka yi nisa da shi! Ya kira su, amma sun tafi.
\v 8 Wanda ya sami hikima yana ƙaunar ransa; wanda ya kiyaye fahimta zai sami abin da ya ke da kyau.
\s5
\v 9 Mai shaidar zur ba zai tsere wa hukunci ba, amma mai furta ƙarairayi zai hallaka.
\v 10 Bai dace da wawa ya zauna cikin daula ba - balle bawa ya yi mulki bisa 'ya'yan sarakuna.
\s5
\v 11 Mutum mai sanin ya kamata yakan yi jinkirin fushi kuma daraja ce a gare shi ya ƙyale laifi.
\v 12 Hasalar sarki na kama da rurin ɗan zaki, amma alherinsa na kama da raɓa a bisan ciyawa.
\s5
\v 13 Wawan ɗa masifa ce ga mahaifinsa mace mai tankiya ɗiɗɗigar ruwa ne koyaushe.
\v 14 Gida da dukiya ana gãdonsu daga iyaye, amma mace mai hankali daga wurin Yahweh take.
\s5
\v 15 Ragonci kan jefa mutum cikin barci mai zurfi, amma wanda bai son aiki zai sha yunwa.
\v 16 Wanda ya kiyaye doka ransa ya ke kiyayewa, amma mutumin da baya tunani game da al'amuransa zai mutu.
\s5
\v 17 Duk mai jin tausayin fakirai yana bada rance ga Yahweh kuma zai sãke biyansa da abin da ya yi.
\v 18 Ka hori ɗanka tun da sauran bege kuma kada ka ƙallafa ranka ga kashe shi.
\s5
\v 19 Mutum mai zafin rai za ya ɗauki alhaki; idan ka cece shi, sai ka sake yi karo na biyu.
\v 20 Ka saurari shawara ka karɓi koyarwa, domin ka iya zama mai hikima a ƙarshen rayuwarka.
\s5
\v 21 Shirye-shirye masu yawa ke a cikin zuciyar mutum, amma manufar Yahweh ce zata tabbata.
\v 22 Biyayya ce ya kamata mutum ya yi marmari kuma gara matalauci da maƙaryaci.
\s5
\v 23 Girmama Yahweh yakan jagoranci mutane ga rai; wanda ke da shi zai gamsu ba abin da zai cutar da shi.
\v 24 Rago yakan tsoma hannunsa cikin kwano; ba zai ko iya dawo da shi bakinsa ba.
\s5
\v 25 Ka bugi mai ba'a, mutum marar wayau zai zama mai tattali; ka hori mai fahimta, zai kuma ƙaru da ilimi.
\s5
\v 26 Wanda ya yi wa mahaifinsa fashi ya kuma kori mahaifiyarsa ɗa ne mai kawo kunya da zargi.
\v 27 Idan ka daina jin koyarwa, ɗana, zaka ratse daga zantattukan ilimi.
\s5
\v 28 Gurɓataccen mashaidi ya kan yi wa adalci ba'a bakin mugu yakan haɗiye laifi.
\v 29 A kan shirya hallakarwa domin masu ba'a bulala kuma domin bayan wawaye.
\s5
\c 20
\cl Sura 20
\p
\v 1 Ruwan inabi mai ba'a ne barasa kuma mai tankiya ce; duk wanda ya kauce ta wurin sha marar hikima ne.
\v 2 Tsoron sarki kamar tsoron ɗan zaki ne mai ruri; wanda yasa shi ya yi fushi zai rasa ransa.
\s5
\v 3 Abin darajantawane ga kowanne mutum da ya kauce wa husuma, amma kowanne wawa yakan yi tsalle cikin jayayya.
\v 4 Ragon mutum baya huɗa lokacin bazara; yakan nemi hatsi a lokacin girbi amma ba zai sami komai ba.
\s5
\v 5 Shawara cikin zuciyar mutum tana kama da ruwa mai zurfi, amma mutum mai fahimta zai jawo ta waje.
\v 6 Mutane da yawa suna shelar nasu alheri, amma mutum mai aminci wa ya iya samunsa?
\s5
\v 7 Mutum mai aminci wanda ke tafiya cikin mutuncinsa, 'ya'yansa da suka bishi zasu zama masu albarka.
\v 8 Sarkin da ya zauna a kan dakalin shari'a ya ke aikin alƙali da idanunsa ya ke sheƙar da dukkan muguntar da ke gabansa.
\s5
\v 9 Wane ne zai ce, "Na tsabtace zuciyata; Ni tsarkakakke ne daga zunubina"?
\v 10 Ma'auni daban-daban da mudun da ba dai-dai ba - Yahweh yaƙi su dukka.
\s5
\v 11 Ko matashi a kan sanshi ta wurin ayyukansa, ko aikinsa mai tsabta ne ko dai-dai kuma.
\v 12 Kunne mai ji da ido mai gani - Yahweh ne ya yi su dukka biyun.
\s5
\v 13 Kada kaso barci domin kada ka talauce; ka buɗe idanunka da haka zaka sami isasshen abinci ka ci.
\v 14 "Ba kyau! Ba kyau!" inji mai saye, amma sa'ad da ya tafi sai fahariya ya ke yi.
\s5
\v 15 Akwai zinariya da duwatsu masu tsada, amma leɓuna masu sani duwatsu ne masu tamani.
\v 16 Wanda ya tsayawa bãƙo ka karɓi rigarsa, ka karɓi jingina kuma daga hannun wanda ya tsayawa mace marar kintsuwa.
\s5
\v 17 Gurasar da aka samu ta wurin yaudarar ɗanɗano mai daɗi ce, amma daga baya bakinsa zai cika da tsakuwa.
\v 18 Shirye-shirye sukan kahu ta wurin shawara da jagorancin mai hikima kaɗai zaka yi yaƙi.
\s5
\v 19 Mai tsegumi yakan bayyana asirai domin haka kada kayi hurɗa tare da mutane masu yawan magana.
\v 20 Idan mutum ya la'anta mahaifinsa ko mahaifiyarsa, za a ɓice fitilarsa a cikin tsakiyar duhu.
\s5
\v 21 Gãdon da aka samu cikin gaggawa da farko amma a ƙarshe ba zai zama da kyau ba.
\v 22 Kada ka ce, "Zan rama wannan muguntar!" Ka jira Yahweh zai kuɓutar da kai.
\s5
\v 23 Yahweh yana ƙin ma'aunin algus mizanan rashin gaskiya basu da kyau.
\v 24 Al'amuran mutum Yahweh ke shugabantarsu; ta yaya zai fahimci tafarkinsa?
\s5
\v 25 Tarko ne ga mutum ya yi magana cikin sauri, "Wannan abu mai tsarki," daga nan ya fara tunanin ma'anar bayan ya yi wa'adinsa.
\v 26 Sarki mai hikima yakan sheƙe miyagu ya juyar da turmin chasa a kansu.
\s5
\v 27 Ruhun mutum fitilar Yahweh ce, tana bincike dukkan sassan ciki.
\v 28 Alƙawarin aminci da gaskiya suna tsare sarki; kursiyinsa an kintsa shi da ƙauna.
\s5
\v 29 Ɗaukakar samari ƙarfinsu ne darajar tsofaffin mutane kuma furfurarsu ce.
\v 30 Buge buge waɗanda ke sa rauni sukan tsarkake mugunta dũka kuma yakan sa sassan cikin jiki su tsarkaka.
\s5
\c 21
\cl Sura 21
\p
\v 1 Zuciyar sarki kamar tafki ce mai gudanowa a cikin hannun Yahweh kuma yana juya shi a duk inda ya ga dama.
\v 2 Kowanne mutum na ganin hanyarsa dai-dai ne a idanunsa, amma Yahweh ke auna zukata.
\s5
\v 3 Aikata abin da ke dai-dai da gaskiya abin karɓa ne ga Yahweh fiye da hadaya;
\v 4 Idanun masu fahariya da zuciya mai girman kai - fitilar mugaye - zunubi ne.
\s5
\v 5 Shirye-shiryen mai himma na kai wa ne kaɗai ga wadata, amma duk mai yawan sauri zai kai ga talauci.
\v 6 Tãra dukiya da harshe na ƙarya kamar tururi ne mai wucewa kuma tarko ne mai kashewa.
\s5
\v 7 Ta'addancin masu mugunta zai kwashe su ya tafi, domin sun ƙi aikata abin da ke dai-dai.
\v 8 Hanyar marar gaskiya karkatacciya ce, amma mai gaskiya na aikata abin da ke dai-dai.
\s5
\v 9 Ya fiye a zauna laɓe a lungun ɗaki da a zauna ɗaki ɗaya da mace mai yawan faɗace-faɗace.
\v 10 Ƙishin mugu na marmarin aikata mugunta; maƙwabtansa baya samun tagomashi a idanunsa.
\s5
\v 11 Lokacin da aka yiwa mai ba'a horo, marar wayau na samun hikima, kuma idan aka bai wa hikima umarni, yana tara ilimi.
\v 12 Mutum mai adalci na lura da gidan mutum mai mugunta; yana kawo masu mugunta zuwa ga bala'i.
\s5
\v 13 Duk wanda ya hana wa kunnensa jin kukan matalauta, haka zai yi kuka, amma ba za a amsa masa ba.
\v 14 Kyauta a ɓoye na kwantar da fushi kuma asirtacciyar kyauta na kauda hasala mai girma.
\s5
\v 15 Lokacin da aka shar'anta gaskiya, tana kawo farincikin ga mutum mai adalci, amma tana kawo fargaba ga masu aikata mugunta.
\v 16 Wanda ya kauce daga hanyar fahimta, za shi zauna a cikin taron matattu.
\s5
\v 17 Duk wanda ke ƙaunar annashuwa za shi talauce; wanda ke ƙaunar ruwan inabi da mai ba zai wadata ba.
\v 18 Mugun mutum abin fansa ne domin mai adalci, maci amana kuma abin fansa ne domin nagargarun mutane.
\s5
\v 19 Ya fiye a zauna cikin hamada da a zauna tare da mata mai yawan faɗace-faɗace da fushi.
\v 20 Zaɓaɓɓun dukiya da mai an ajiye su a mazaunin masu hikima, amma mutum marar wayo yana haɗiye su dukka.
\s5
\v 21 Wanda ke aikata adalci yana kuma kyautatawa - wannan mutum ya sami rai, da adalci, da kuma ɗaukaka.
\v 22 Mutum mai hikima na tsallake birnin masu iko, kuma yana rusar da ƙaƙƙarfan wurin da suka dogara da shi.
\s5
\v 23 Duk wanda ya kiyaye bakinsa da harshensa yana tsare kansa ne daga wahala.
\v 24 Mai girman kai da mutum mai fahariya - "Mai ba'a" ne sunansa - yana ayyukansa da girmankai na kumburi.
\s5
\v 25 Sha'awar rago tana kashe shi, gama hannunsa na ƙin yin aiki.
\v 26 Dukkan yini yana marmari yana ƙara marmari, amma mutum mai adalci yana bayarwa kuma baya hanawa.
\s5
\v 27 Hadayar mugaye ƙazanta ce; ƙazantar na yawaita idan ya kawo su da miyagun manufofi.
\v 28 Mai shaidar ƙarya zai hallaka, amma wanda ya yi sauraro za ya yi magana a dukkan lokaci.
\s5
\v 29 Mugun mutum na mai da fuskarsa da tauri, amma mai adalci na dai-daita tafarkunsa.
\s5
\v 30 Babu hikima, babu fahimta, kuma babu shawara da ke iya gãba da Yahweh.
\v 31 Ana shirya doki domin ranar yaƙi, amma nasara ta Yahweh ce.
\s5
\c 22
\cl Sura 22
\p
\v 1 Zaɓen suna mai kyau ya fi wadata mai yawa kuma tagomashi ya fi azurfa da zinariya.
\v 2 Wannan na faruwa da masu arziƙi da matalauta - Yahweh ne mahallicinsu dukka.
\s5
\v 3 Mutum mai ƙwazo na hangen wahala ya kuma ɓoye kansa, amma marasa cikakkiyar kula na wucewa har ga wahala.
\v 4 Ladan tawali'u da tsoron Yahweh arziƙi ne, da ɗaukaka, da kuma rai.
\s5
\v 5 Ƙayayuwa da tarkuna suna kan hanyar bijirarru; duk wanda ya kiyaye ransa zai yi nisa da su.
\v 6 Ka koya wa yaro hanyar da zai bi kuma idan ya manyanta ba zai kauce daga wannan umarnin ba.
\s5
\v 7 Masu arziki ne ke mulkin matalauta kuma mai cin bashi bawa ne ga mai bada bashi.
\v 8 Shi wanda ya shuka rashin adalci za shi girbi masifa kuma sandar hasalarsa zata ƙare.
\s5
\v 9 Shi wanda ke da ido na hannu sake za shi yi albarka, gama yana raba gurasarsa da talakawa.
\v 10 Ka kori mai ba'a, husuma zata fita; faɗace-faɗace da zage-zage zasu ƙare.
\s5
\v 11 Shi wanda ke ƙaunar tsabtacciyar zuciya wanda kuma kalamansa masu alheri ne, za shi zama abokin sarki.
\v 12 Idanun Yahweh na bisa ilimi, amma yana rusar da maganganun maci amana.
\s5
\v 13 Ragon mutum ya ce, "Akwai zaki a kan hanya! Za a kashe ni a buɗaɗɗun filaye."
\v 14 Bakin karuwa rami ne mai zurfi; Fushin Yahweh na gãba da duk wanda ya faɗi cikinta.
\s5
\v 15 Ana samun wawanci a zuciyar ɗan yaro, amma sandar horo na korarsa da nisa.
\v 16 Wanda ke zaluntar matalauta don ya tara dukiyarsa, ko ya baiwa mutane masu arziki, zai talauce.
\s5
\v 17 Ka kusanto da kunnuwanka ga maganganun masu hikima ka kuma miƙa zuciyarka ga ilimina,
\v 18 gama zata zamar maka abin daɗi, idan ka adana su cikinka, idan dukkansu suna shirye cikin leɓunanka.
\v 19 Domin dogararka ta kasance cikin Yahweh, na koyar da su gare ka yau - lallai a gare ka.
\s5
\v 20 Bana rubuta maka talatin maganganun na umarni da ilimi bane,
\v 21 domin na koyar da kai waɗannan amintattun maganganu, dominn ka bayar da amintattun amsoshi ga waɗanda suka aike ka ba?
\s5
\v 22 Kada ka cuci matalauci wai don shi matalauci ne, ko ka murƙushe mabuƙaci a bakin ƙofa,
\v 23 gama Yahweh zai yi magana a madadin su, kuma zai ƙwace ran wadda ya cuce su.
\s5
\v 24 Kada ka yi abokantaka da wanda fushi ke mulkinsa kuma kada ka yi tafiya da wanda ke hucin fushi,
\v 25 in ba haka ba zaka koyi halayensa da haka zaka ɗana wa ranka tarko.
\s5
\v 26 Kada ka zama wanda ke buga hannu don ɗaukar alƙawari, ko mai tsayawa a madadi na basussuka.
\v 27 Idan ka rasa hanyar biya, me zai hana wani ya ɗauke gadonka daga gare ka?
\s5
\v 28 Kada ka matsar da dutsen iyaka na dã wanda ubanninka suka sa.
\v 29 Ko ka ga mutum ƙwararre ga aikinsa? Zai tsaya a gaban sarakuna; ba zai tsaya a gaban mutane marasa daraja ba.
\s5
\c 23
\cl Sura 23
\p
\v 1 A lokacin da ka zauna cin abinci da mai mulki, ka kula da kyau abin da a ka ajiye a gaban ka,
\v 2 ka kuma sa wuƙa a maƙogwaronka idan fa kai wani ne mai yawan son cin abinci mai yawa.
\v 3 Kada ka yi marmarin kayan kwaɗayinsa, gama abincin ƙarya ne.
\s5
\v 4 Kada ka wahalar da kanka garin neman arziki; ka sami hikimar sanin lokacin da ya kamata ka huta.
\v 5 Ko zaka bar idanuwanka bisa arziki? Zai watse, gama lallai za shi ɗauki fuka-fukai kamar gaggafa ya tashi sama.
\s5
\v 6 Kada ka ci abincin wanda ke da mugun ido - kuma kada ka yi marmarin kayan kwaɗayinsa,
\v 7 gama shi irin mutum ne da ke ƙirgen farashin abincin. "Ka ci ka sha!" yana ce maka, amma zuciyarsa bata tare da kai.
\v 8 Za ka yi aman abin da ka ci kuma kalaman abokancin ka su tafi a banza.
\s5
\v 9 Kada ka yi magana a gaban wawa, gama zai rena hikimar maganganunka.
\v 10 Kada ka matsar da daɗaɗɗen dutsen iyaka ko ka shige gonar marayu,
\v 11 gama mai Fansarsu na da ƙarfi kuma zai yi magana a madadin su gãba da kai.
\s5
\v 12 Ka kafa zuciyar ka ga umarni kuma kunnuwanka ga maganganu na ilimi.
\s5
\v 13 Kada ka ƙi yiwa yaro umarni, gama idan ka yi masa horo, ba zai mutu ba.
\v 14 Kai ne ya zama dole ka doke shi da sanda ka kuma ceci ransa daga Lahira.
\s5
\v 15 Ya ɗa na, idan zuciyarka na da hikima, da haka kuma zuciyata za ta yi murna;
\v 16 can cikin zuciyata za ta yi farinciki lokacin da leɓunan ka suka furta abin da ke dai-dai.
\s5
\v 17 Kada ka bar zuciyarka ta yi kishin masu zunubi, amma ka ci gaba da tsoron Yahweh dukkan rana.
\v 18 Tabbas akwai gobe kuma ba za a datse begen ka ba.
\s5
\v 19 Ka ji - kai! - ɗa na, ka sami hikima ka kuma bida zuciyarka a hanyar.
\v 20 Kada ka yi abokantaka da mashaya, ko masu cin abinci fiye da kima,
\v 21 gama da mashayi da marar horo ga ci suna zama matalauta kuma gyangyadi za shi suturce su da tsummokara.
\s5
\v 22 Ka saurari mahaifin ka wanda ya haife ka kuma kada ka rena mahaifiyar ka sa'ad da ta tsufa.
\v 23 Ka sayi gaskiya, amma kada ka sayar da ita; sayi hikima, da umarni, da kuma fahimta.
\s5
\v 24 Mahaifin mutum mai adalci za shi yi farinciki, kuma duk wanda ya haifi yaro mai hikima za shi yi murna dominsa.
\v 25 Bari mahaifinka da mahaifiyarka su yi murna kuma bari ita da ta haife ka ta yi farinciki.
\s5
\v 26 Ɗana, ka ba ni zuciyarka kuma bari idanuwanka su kula da hanyoyi na.
\v 27 Gama karuwa rami ne mai zurfi, kuma mace mai gurɓataccen hali rijiya ce ƙuntacciya.
\v 28 Tana kwanciya kamar ɗan fashi tana kuma barbaza yawan munafunci cikin 'yan adam.
\s5
\v 29 Wa keda waiyo? Wa ke da kaito? Wa keda faɗace-faɗace? Wa ke ƙorafi? Wa keda raunuka babu dalili? Wa keda jajayen idanuwa?
\v 30 Waɗanda suka daɗe da ruwan inabi, waɗanda suka gwada gaurayayyen ruwan inabi.
\s5
\v 31 Kada ka dubi ruwan inabi sa'ad da ya yi ja, lokacin da ya ke kumfa a cikin moda yana kuma kwararowa ƙasa a hankali.
\v 32 A ƙarshe zai yi sãra kamar maciji ya kuma yi harbi kamar kãsa.
\v 33 Idanunka zasu ga baƙon abubuwa kuma zuciyarka za ta furta gurɓatattun abubuwa.
\s5
\v 34 Za ka zama kamar wanda ke kwanciya bisa tekuna ko kwantawa bisa rufin jirgi.
\v 35 "Sun buge ni," za ka ce. "amma ban ji ciwo ba. Sun buge ni, amma ban ji zafi ba. Har yaushe zan farka? Zan nemi wani abin shan."
\s5
\c 24
\cl Sura 24
\p
\v 1 Kada ka yi ƙyashin masu aikata mugunta, ko ka yi marmarin yin abokantaka da su,
\v 2 domin zuciyarsu na ƙirƙiro da ta'addanci kuma leɓunansu na zancen rigima.
\s5
\v 3 Ta wurin hikima a ke gina gida ta wurin fahimta a ke kafa shi.
\v 4 Ta wurin ilimi a ke cika ɗakunan da dukkan dukiya masu tamani da daraja.
\s5
\v 5 Jarumi mai hikima na da ƙarfi, kuma mutum mai ilimi na ƙara ƙarfinsa;
\v 6 domin ta wurin shawara na hikima zaka yi yaƙi kuma cikin shawarwari masu yawa akwai nasara.
\s5
\v 7 Hikima na da tsawo ga wawa; a bakin ƙofa ba ya buɗe bakinsa.
\s5
\v 8 Akwai wani wanda ke shirin aikata mugunta - mutane na kiransa shugaban dabaru.
\v 9 Wawan shiri zunubi ne kuma mutane na ƙyamar mai ba'a.
\s5
\v 10 Idan ka yi sanyi sabili da tsoro a ranar wahala, to ƙarfinka ƙalilan ne.
\s5
\v 11 Ka ƙwaci waɗanda aka ɗauke ga mutuwa ka kuma hana waɗanda ke gangarawa zuwa yanka.
\v 12 Idan ka ce, "Duba, ba mu san da komai game da wannan ba," shi wanda ke auna zuciya ba ya fahimci abin da kake faɗa ba? Wanda ke tsaron ranka, ba yana sane da haka ba? Allah ba zai saka wa kowanne abin da ya cancance shi ba?
\s5
\v 13 Ya ɗana, ka ci zuma domin yana da kyau, domin ɗigo-ɗigon sakar zuma na da zaƙi a bakin ka.
\v 14 Haka hikima take ga ranka - Idan ka same ta, gobe tabbas ne kuma begen ka baza a katse shi ba.
\s5
\v 15 Kada ka yi kwanto kamar mugun mutum wanda ke kai farmaki ga gidan mutum mai adalci. Kada ka lalatar da gidansa!
\v 16 Gama mutum mai adalci na faɗuwa ƙasa sau bakwai ya tashi kuma, amma ana kãda mugayen mutane ƙasa da bala'i.
\s5
\v 17 Kada ka yi farinciki sa'ad da maƙiyin ka ya faɗi kuma kada zuciyarka ta ji daɗi sa'ad da ya yi tuntuɓe,
\v 18 domin Yahweh zai gani ya kuma bayyana rashin yardarsa ya kuma juyar da hasalarsa daga gare shi.
\s5
\v 19 Kada ka da mu saboda masu aikata mugunta, kuma kada ka yi ƙyashin mugayen mutane,
\v 20 gama mugun mutum ba shi da tabbaccin gobe kuma fitilar mugaye za ta ɓice.
\s5
\v 21 Ka ji tsoron Yahweh, ka kuma ji tsoron sarki, ya ɗana; kada ka yi abokantaka da waɗanda suka tayar masu,
\v 22 gama ba zato azaba zata auko kuma wa ya sani girman lalatar da zata zo daga dukkan su biyun?
\s5
\v 23 Haka ma waɗannan maganganu ne na masu hikima. Nuna bambanci cikin shari'a ba abu ne mai kyau ba.
\s5
\v 24 Duk wanda ya cewa mugun mutum, "Kai mutum mai adalci ne," mutane zasu la'anta shi al'ummai kuma zasu ƙi shi.
\v 25 Amma waɗanda suka hori mai mugunta zasu sami jin daɗi kuma kyautai na alheri zasu zo gare su.
\s5
\v 26 Wanda ya ba da amsa mai kyau yana bada sumba ga leɓuna.
\v 27 Ka shirya aikinka na waje, ka kuma shirya wa kanka komai cikin fili; bayan haka, sai ka gina gidanka.
\s5
\v 28 Kada ka zama shaida gãba da maƙwabcinka babu dalili kuma kada ka ruɗar da leɓunanka.
\v 29 Kada ka ce, "Zan yi masa abin da ya yi mani; Zan sãka masa abin da ya yi."
\s5
\v 30 na ratsa ta cikin filin rãgo, ta gonar inabi na mutumin da ba shi da hankali.
\v 31 Duk ƙayayuwa sun rufe ko'ina, ƙasar ta cika da sarƙaƙiya, kuma ganuwarta ta dutse ta rushe.
\s5
\v 32 Sai na gani na kuma yi lura da ita; na duba na kuma karɓi umarni.
\v 33 Yin barci kaɗan, da ɗan gyangyaɗi, da ɗan naɗe-naɗen hannuwa domin hutu -
\v 34 da haka talauci za shi saukar maka, kuma buƙatarka kamar soja mai makami.
\s5
\c 25
\cl Sura 25
\p
\v 1 Waɗannan ƙarin karin magana na Suleman ne, wanda mutanen Hezekiya, sarkin Yahuda suka kwafa.
\v 2 Ɗaukaka ta Allah ce ya ɓoye zance, amma ɗaukakar sarakuna su bincike shi.
\v 3 Kamar yadda sammai suke da tsayi duniya kuma tana da zurfi, haka zuciyar sarakuna sun wuce gaban ganuwa.
\s5
\v 4 Ka sheƙe azurfa gwani kuma za shi yi amfani da azurfar ga aikinsa.
\v 5 Haka ma, ka cire mugayen mutane daga gaban sarki kursiyinsa kuma zai kafu ta wurin aikata adalci.
\s5
\v 6 Kada ka ɗaukaka kanka a gaban sarki kada kuma ka zauna a mazaunin da aka shirya wa mutane masu daraja.
\s5
\v 7 Ya fi kyau shi da kansa ya ce maka, "Hauro zuwa nan," da shi ya kunyatar da kai a gaban mutum mai daraja. Abin da ka yi shaidar sa,
\v 8 kada ka yi saurin kawo shi ga shari'a. Gama me zaka yi a ƙarshe idan maƙwabcinka yasa ka cikin kunya?
\s5
\v 9 Ka yi jayayya bisa matsala tsakaninka da maƙwabcinka da kansa kada kuma ka fallasa wani asirin,
\v 10 domin kada wanda ya ji ka yasa ka ji kunya kuma mugun rohota a kanka da ba za a iya tsayarwa ba.
\s5
\v 11 'Ya'yan itacen aful na zinariya da aka yi masu jerin azurfa kamar magana ce da aka yi ta dai-dai.
\v 12 Zobe na zinariya ko sarƙar da aka yi ta da zinariya mai kyau horo ne na hikima ga kunnuwan mai sauraro.
\s5
\v 13 Kamar yadda sanyin ƙanƙara ya ke lokacin girbi haka ɗan aike mai aminci ke ga waɗanda suka aike shi; yana dawo da ran shugabanninsa.
\v 14 Giza-gizai da iska amma babu ruwan sama ne wanda ke fahariya da kyautar da bai bayar ba.
\s5
\v 15 Cikin hakuri ake rinjayar mai mulki kuma harshe mai taushi na iya karya ƙashi.
\s5
\v 16 Idan ka sami zuma, kada kayi masa shan fitar hankali - in ba haka ba, idan ka sha dayawa, za ka amayas.
\v 17 Kada ka cika zuwa gidan maƙwabcinka, yana iya gajiya da kai ya kuma ƙi ka.
\s5
\v 18 Mutumin da ya yi shaidar ƙarya bisa maƙwabcinsa na kama da kulkin da aka yi amfani da shi a yaƙi, ko takobi, ko wani mãshi mai tsini.
\v 19 Mutum marar amincin daka amince da shi a lokacin wahala na kama da ruɓaɓɓen haƙora ko tafiya da gurguwar ƙafa.
\s5
\v 20 Kamar mutumin da ya kwaɓe rigarsa a yanayi mai tsananin sanyi, ko zuba inabi bisa ainihin gawayi na soda, haka wanda ke yin waƙoƙi ga zuciya mai nauyi.
\s5
\v 21 Idan makiyinka na jin yunwa, ba shi abinci ya ci, idan kuma yana jin ƙishi, ba shi ruwa ya sha,
\v 22 gama zaka tula masa tarin garwashin wuta a bisa kansa Yahweh kuma zai baka lada.
\s5
\v 23 Kamar yadda iskar arewa ke kawo ruwan sama, haka take da harshen da ke faɗin asirai yana hadasar da fuskoki masu fushi.
\v 24 Gara a zauna a saƙon rufin ɗaki da a zauna gida ɗaya tare da mace mai yawan faɗace-faɗace.
\s5
\v 25 Kamar yadda ruwan sanyi ke ga wanda ke ƙishi, haka ya ke ga labari mai daɗi da ke zuwa daga ƙasa mai nisa.
\v 26 Kamar ƙazantacciyar maɓuɓɓuga ko gurɓatacciyar rijiya haka ya ke da mutum adali da ya yi sanyi a gaban mugayen mutane.
\s5
\v 27 Ba shi da kyau a sha zuma da yawa; wannan kamar neman yabo ne bisa yabo.
\v 28 Mutumin da bashi da kamun kai na kama da birnin da ke a buɗe kuma bashi da ganuwa.
\s5
\c 26
\cl Sura 26
\p
\v 1 Kamar garin ƙanƙara a lokacin zafi ko ruwan sama a lokacin girbi, haka ma yabo bai dace ga wawa ba.
\v 2 Kamar tsuntsayen da ke shawagi a sama basu sauka ba, haka la'annar da ba a cancance ta ba baza ta sauka ba.
\s5
\v 3 Tsumagiya domin doki ne, linzami domin jaki sanda kuwa domin bayan wawaye.
\v 4 Kada ka bada amsa ga wawa bisa ga wawancinsa, in ba haka ba za ka zama kamar sa.
\s5
\v 5 Ka bada amsa ga wawa sai ka ƙara masa wawancinsa, domin kada ya ɗauki kansa wani mai hikima ne.
\v 6 Duk wanda ya aika da saƙo ta hannun mai wauta na datse ƙafafunsa ne yana kuma shan ta'addanci.
\s5
\v 7 Kamar ƙafafuwa shanyayyu da ke rataye da ƙasa haka karin magana ya ke a bakin wawaye.
\v 8 Kamar a gwada harba dutse a majajjawa haka ya ke a bada yabo ga wawa.
\s5
\v 9 Kamar ƙaya data shiga hannun mashayin giya haka karin magana a bakin wawaye.
\v 10 Kamar maharbin da yaji wa dukkan waɗanda ke kewaye da shi raunuka haka wanda ya yi hayar wawa ko hayar duk mai wucewa kan hanya.
\s5
\v 11 Kamar yadda kare ke komawa ga abin da ya amayas, haka wawan da ke maimaita wawancinsa.
\v 12 Ko ka ga wani wanda ke ganin kansa mai hikima ne? Ko wawa na da bege fiye da shi.
\s5
\v 13 Ragon mutum ya ce, "Akwai zaki a kan hanya! Akwai zaki a tsakanin buɗaɗɗun wurare!"
\v 14 Kamar yadda ƙofa ke juyawa a ƙyaurenta, haka ragon mutum bisa gadonsa.
\s5
\v 15 Ragon mutum na sa hannunsa cikin abinci duk da haka ba shi da ƙarfin ɗaga shi zuwa bakinsa.
\v 16 Ragon mutum a ganin sa mai hikima ne shi fiye da mazaje bakwai da suka bada dalilai masu kyau.
\s5
\v 17 Kamar wadda ya riƙe kunnuwan kare, haka mai wucewa kan hanya da ya yi fushi ga shawarwarin da basu shafe shi ba.
\s5
\v 18 Kamar mahaukacin da ke harba kibiya mai wuta,
\v 19 haka wanda ya ruɗi maƙwabcinsa yana cewa, "Ba wasa kawai nake yi ba?"
\s5
\v 20 Don rashin itace, wuta ke mutuwa; kuma duk inda babu magulmaci faɗace-faɗace na ɗaukewa.
\v 21 Kamar yadda gawayi ke ga wuta maici itace kuma ga wuta, haka ya ke da mutum mai faɗace-faɗace wurin kunna husuma.
\s5
\v 22 Maganganun magulmaci suna kama da abinci mai daɗi; suna shigewa can cikin jiki.
\v 23 Kamar kaskon da aka dalaye da azurfa haka baki mai zafi da kuma zuciya mai mugunta.
\s5
\v 24 Shi da ke ƙin mutane yana ɓoye yadda ya ke ji da leɓunansa kuma yana ajiyar munafunci cikinsa.
\v 25 Zai yi maganar alheri, amma kada ka yarda da shi, Gama akwai ƙazanta guda bakwai cikin zuciyarsa.
\v 26 Ko da ya ke rashin gaskiya ya ɓoye ƙiyayyarsa, za a bayyana muguntarsa a cikin taro.
\s5
\v 27 Duk wanda ya haƙa rami zai faɗa cikinsa kuma dutsen zai gangaro wa wanda ya turo shi.
\v 28 Maƙaryacin harshe na ƙin mutanen da ya ke murƙushewa kuma baki mai fahariya na kawo hasara.
\s5
\c 27
\cl Sura 27
\p
\v 1 Kada ka yi alfahari game da gobe, domin baka san me ranar ke iya kawo wa ba.
\v 2 Bari wani ne ya yabe ka amma ba naka bakin ba; baƙo amma ba naka leɓunan ba.
\s5
\v 3 Ka yi la'akari da yadda dutse ke da nauyi da kuma nauyin yashi - cakuna ta wawa tafi dukkansu biyu nauyi.
\v 4 Akwai rashin imanin hasala da kuma ambaliyar fushi, amma wa zai iya tsayawa a gaban kishi?
\s5
\v 5 Tsautawa a fili ta fi nuna ƙauna a ɓoye.
\v 6 Har yanzu akwai aminci a cutar da tazo daga aboki, amma maƙiyi na iya sumbatarka babu iyaka.
\s5
\v 7 Mutumin da ya ci abinci ya ƙoshi zai ƙi ko da ma saƙar zuma ne, amma ga mutum mai yunwa, kowanne abu mai ɗaci na da zaƙi.
\v 8 Kamar tsuntsun da ke yawo daga sheƙarsa haka mutumin da ya kauce daga inda ya ke zama.
\s5
\v 9 Kayan ƙamshi da turare suna sa zuciya ta yi farinciki, amma daɗin aboki na zuwa ne daga amintacciyar shawararsa.
\v 10 Kada ka yi banza da abokinka da kuma abokin mahaifinka, kuma kada ka tafi gidan ɗan'uwanka a ranar wahalar ka. Maƙwabcin da ke kusa da kai ya fiye maka da ɗan'uwanka mai nisa da kai.
\s5
\v 11 Ka zama mai hikima, ya ɗana, ka sa zuciyata ta yi farinciki; sa'an nan zan bada amsa ga wanda ke yi mani ba'a.
\v 12 Mutum mai cikakken hankali na ɓoyewa ne idan ya ga wahala, amma mutane masu halin baƙunci na tafiya kai-tsaye har su kuma shiga wahala.
\s5
\v 13 Ka karɓe mayafin wanda ya tsaya wa baƙo, ka kuma riƙe shi a matsayin alƙawari sa'ad da ya tsayawa karuwar mace.
\v 14 Duk wanda yasa wa maƙwabcinsa albarka da babbar murya da sassafe, wannan albarkar za a ganta kamar la'ana ce!
\s5
\v 15 Mace mai yawan faɗace-faɗace na kama da yayyafi a ranar ruwan sama marar tsayawa;
\v 16 hana ta na kama da hana iska ne, ko kuma yin ƙoƙarin riƙe mai cikin hannun damanka.
\s5
\v 17 Ƙarfe ke wãsa ƙarfe; haka nan kuma, mutum ke wãsa abokinsa.
\v 18 Wanda ya yi noman zaitun zai ci 'ya'yan itacensa, kuma wanda ya tsare ubangidansa za a yabe shi.
\s5
\v 19 Kamar yadda ruwa ke nuna fuskar mutum, haka zuciyar mutum ke bayyana mutumin.
\v 20 Kamar yadda Lahira da Abaddon basu ƙoshi, haka idanun mutum basu taɓa ƙoshi.
\s5
\v 21 Maƙera domin gwada azurfa ne tanderun wuta kuwa domin zinariya ne; mutum kuma ana gwada shi ne sa'ad da aka yabe shi.
\v 22 Ko da zaka daka wawa da taɓarya - harɗe da hatsi - duk da haka wawancinsa ba zai bar shi ba.
\s5
\v 23 Ka tabbatar ka san lafiyar tumakinka ka kuma nuna damuwarka ga garkenka,
\v 24 gama dukiya ba ta har abada ba ce. Ko masarauta tana dawwama dukkan tsararraki?
\v 25 Ka san lokacin da busasshiyar ciyawa ta ɗauke sabuwa kuma ta fito, da kuma lokacin da ciyawa daga bisa tuddai ke taruwa ciki.
\s5
\v 26 Waɗannan tumakai zasu yi maka tanadin tufafin sawa haka kuma ragunan zasu yi tanadin kuɗi domin filin.
\v 27 Za a sami madarar awaki domin abincinka - abinci domin iyalinka - kuma wartsakarwa domin 'yan matanka bayi.
\s5
\c 28
\cl Sura 28
\p
\v 1 Mugayen mutane na gudu babu wani mai korar su, amma masu adalci basu da tsoro kamar ɗan zaƙi.
\v 2 Saboda kurakuran ƙasa, ta sami shugabanni da yawa, amma ga mutum mai fahimta da ilimi, zata dawwama na lokaci mai tsawo.
\s5
\v 3 Matalaucin da ke zaluntar wasu matalautan mutane na kama da ruwan sama da baya bada abinci.
\v 4 Waɗanda suka yi banza da shari'a na koma wa ga yabon mugayen mutane, amma waɗanda ke bin shari'a na gãba da su.
\s5
\v 5 Mugayen mutane basu fahimtar hukunci, amma masu neman Yahweh na fahimtar komai.
\v 6 Ya fiye wa matalaucin mutum mai tafiya cikin aminci, da mai arziƙi wanda ke tafiya cikin hanyoyinsa na rashin aminci.
\s5
\v 7 Shi wanda ya kula da shari'a ɗa ne mai fahimta, amma abokin mashaya abin kunya ne ga mahaifinsa.
\v 8 Duk wanda ya tara dukiyarsa ta hanyar zamba dukiyarsa zata tafi wurin wani wanda zai tausaya wa matalauta.
\s5
\v 9 Idan wani ya juyar da kunnuwarsa daga sauraren shari'a, ko addu'arsa ma abin ƙyama ce.
\v 10 Duk wanda ya ɓatas da mai gaskiya domin aikata mugunta zai faɗa cikin ramin da ya haƙa, amma mai gaskiya zai sami gãdo mai kyau.
\s5
\v 11 Mai arziki na yi wa kansa kallon shi mai hikima ne, amma mai fahimta wanda ke matalauci zai tona masa asiri.
\v 12 Lokacin da masu adalci ke mulki, akwai babbar ɗaukaka; amma sa'ad da mugaye suka tashi, ana tone asirin mutane.
\s5
\v 13 Wanda ya ɓoye zunubansa ba za shi yi albarka ba, amma shi wanda ya furtasu ya kuma rabu da su za a yi masa jinƙai.
\v 14 Shi wanda ke rayuwa cikin girmamawa mai albarka ne, amma wanda ya taurare zuciyarsa zai abka cikin wahala.
\s5
\v 15 Kamar zaki mai ruri ko kamar dabbar kerkeci mai huci haka mugun shugaba a bisa mutane matalauta.
\v 16 Shugaban da ba shi da fahimta azzalumi ne, amma wanda ya tsani zalunci zai daɗe da kwanakinsa.
\s5
\v 17 Idan mutum ya yi laifi domin ya zubda jinin wani, zai zama mai gudun hijira har sai ya mutu kuma ba wanda zai taimake shi.
\v 18 Duk wanda ya yi rayuwa cikin gaskiya zai zauna lafiya lau, amma wanda tafarkinsa karkataccc ne zai faɗi ba zato.
\s5
\v 19 Shi wanda ya yi aiki cikin gonarsa zai sami abinci mai yawa, amma wanda ya bi wofi zai sami talauci mai yawa.
\v 20 Mutum mai aminci zai sami albarka mai girma, amma wanda ya sami wadata cikin hanzari ba zai tsira daga hukunci ba.
\s5
\v 21 Bai kamata a nuna sonkai ba, amma akan 'yar gurasa mutum kan iya aikata ba dai-dai ba.
\v 22 Mutum mai rowa na hanzarin neman arziki, amma bai san da cewar talauci na zuwa bisansa ba.
\s5
\v 23 Duk wanda ya yi ma wani horo, daga baya zai sami tagomashi daga gare shi fiye da wanda daga shi aka yi masa zaƙin baki.
\v 24 Duk wanda ya zambanci mahaifinsa da mahaifiyarsa ya kuma ce, "Wannan ba zunubi bane," shi abokin wanda ke hallakarwa ne.
\s5
\v 25 Mutum mai yawan son kansa na haddasar da rigima, amma wanda ya dangana da Yahweh zai yi albarka.
\v 26 Shi wanda ya dangana ga tasa zuciya wawa ne, amma duk wanda ya yi tafiya cikin hikima zai yi nisa daga hatsari.
\s5
\v 27 Wanda ya bayar ga matalauta ba za shi rasa komai ba, amma wanda ya rufe idanunsa gare su zai sami la'ana.
\v 28 Lokacin da miyagu suka tashi, mutane na ɓoye kansu; amma idan suka lalace, masu adalci na ƙaruwa.
\s5
\c 29
\cl Sura 29
\p
\v 1 Mutumin da ya karɓi horo dayawa amma ya taurare wuyansa za a karya shi cikin ƙanƙanen lokaci da ba za shi warke ba.
\v 2 Lokacin da masu adalci suka ƙaru, mutane na farinciki, amma lokacin da mugu ke shugabanci, mutane na ajiyar zuciya.
\s5
\v 3 Duk wanda ya ƙaunaci hikima nasa mahaifinsa ya yi farinciki, amma wanda ya yi abokantaka da karuwai na lalatar da dukiyarsa.
\v 4 Sarki na kafa ƙasar da adalci, amma wanda ya nemi cin hanci yana yayyaga ta dukka.
\s5
\v 5 Mutumin da ya yi wa maƙwabcinsa daɗin yana shinfiɗa wa sawayensa tarko ne.
\v 6 Cikin zunubin mugun mutum nan akwai tarko, amma mutum mai adalci yana waƙoƙi da farinciki.
\s5
\v 7 Mutum mai adalci na sane da yancin talakawa; mugun mutum ba shi da wannan ilimin.
\v 8 Masu ba'a sukan cinna wa birni wuta, amma waɗanda ke da hikima suna juyar da hasala.
\s5
\v 9 Lokacin da mutum mai hikima ya yi jayayya da wawa, yana fusata yana kuma dariya, ba za a kuma sami hutawa ba.
\v 10 Masu zubda jini suna tsanar masu gaskiya su kuma nemi ran kamilai.
\s5
\v 11 Wawa yana bayyana dukkan haushinsa, amma mutum mai hikima na danne shi ya kuma kãme kansa.
\v 12 Idan mai mulki ya saurari ƙarairayi, dukkan shugabanninsa zasu zama mugaye.
\s5
\v 13 Matalauci da wanda ke azzalumi sun zama ɗaya, gama Yahweh ya bada haske ga idanunsu dukka.
\v 14 Idan sarki ya shar'anta matalauta da gaskiya, kursiyinsa zai kafu har abada.
\s5
\v 15 Sanda da tsautawa na bada hikima, amma ɗan da ba ya sami horo ba na kawo wa mahaifiyarsa kunya.
\v 16 Yayin da mugayen mutane ke riƙe da iko, kurakurai na ƙaruwa, amma adalai zasu ga faduwar mugayen mutane.
\s5
\v 17 Ka hori ɗanka zai kuma baka hutu; zai kawo wa ranka jin daɗi.
\v 18 Inda babu furtacciyar ruya mutane kan yi yadda suka ga dama, amma wanda ya kula da shari'a mai albarka ne.
\s5
\v 19 Bawa ba zai tsautu da magana kawai ba, ko da ya fahimta, ba zai juya ba.
\v 20 Ko ka ga mutum mai saurin magana? Ya fiye a sa zuciya ga wawa da wannan.
\s5
\v 21 Duk wanda ya shagwaɓa bawansa tun yana matashi, a ƙarshe akwai wahala.
\v 22 Mutum mai fushi na garwaya husuma kuma mai hasala na aikata zunubai masu yawa.
\s5
\v 23 Girman kan mutum ne ke kãda shi, amma wanda ke da ruhun saukin kai za a ba shi ɗaukaka.
\v 24 Shi wanda ya yi tarayya da ɓarawo maƙiyin ransa ne; yana jin la'ana bai kuma ce komai ba.
\s5
\v 25 Tsoron mutum tarko ne, amma wanda ya dogara ga Yahweh za a kiyaye shi.
\v 26 Dayawa ne masu neman ganin fuskar mai mulki, amma daga wurin Yahweh adalci ke zuwa ga mutum.
\s5
\v 27 Mutum marar gaskiya abin ƙyama ne ga mutane masu adalci, amma wanda ke mai adalci abin ƙi ne ga mugun mutum.
\s5
\c 30
\cl Sura 30
\p
\v 1 Maganganun Agu ke nan ɗan Yãke - furcin: Wannan mutumin ya gaya wa Itiyel da Ukal:
\v 2 Tabbas ni kamar wata dabba ce ba mutum ba kuma bani da fahimta irin na mutum.
\v 3 Ban koyi hikima ba, bani kuma da ilimi game da Mai Tsarkin.
\s5
\v 4 Wane ne ya haura cikin sama ya kuma sauko? Wane ne ya tattara iska cikin hannuwansa? Wane ne ya tattara ruwaye cikin mayafi? Wane ne ya kafa iyakokin dukkan duniya? Mene ne sunansa, kuma mene ne sunan ɗansa? Tabbas ka sani.
\s5
\v 5 Kowacce maganar Allah gwadajjiya ce; garkuwa ce ga duk waɗanda ke ɓuya gare shi.
\v 6 Kada ka ƙara a bisa maganarsa, domin kada ya hore ka, kuma za a iske ka maƙaryaci.
\s5
\v 7 Abu guda biyu na tambaya gare ka, kada kuma ka hana mani kamin na mutu:
\v 8 Kada ka bar wofi da ƙarya su kusance ni. Kada ka ba ni ko talauci ko arziki, ka dai ba ni abincin da nake buƙata.
\v 9 Gama idan na samu dayawa, ina iya ƙaurace maka in ce, "Wane ne Yahweh?" Ko idan na zama matalauci, ina iya sata har in kawo reni ga sunan Allahna.
\s5
\v 10 Kada ka zargi bawa a gaban ubangidansa, don kada ya la'anta ka kuma har a kama ka da laifi.
\s5
\v 11 Akwai wata tsara da ke la'anta mahaifinsu kuma ba ta albarkatar mahaifiyarsu.
\v 12 Akwai tsarar da ke ganin kanta mai tsarki ce a gaban idanun ta, amma duk da haka basu wanku daga ƙazantarsu ba.
\s5
\v 13 Akwai tsarar da fuskarsu take ɗage sama, dubi yadda girar idanunsu ke ɗage can sama!
\v 14 Akwai wata tsara wadda haƙoransu na takobi ne, kuma mataunansu kamar wuƙaƙe, domin su hallaka matalauta daga duniya mabuƙata kuma daga cikin 'yan adam.
\s5
\v 15 Matsattsaku na da 'yan mata biyu: "Bayar kuma bayar" suke kuka. Akwai abu guda uku da basu ƙoshi, guda huɗu da basu cewa, "Ya isa":
\v 16 Lahira; da mahaifar da bata ɗaukar ciki; da ƙasar da bata ƙoshi da ruwa; da kuma wutar da bata cewa, "Ya isa!"
\v 17 Idanun da suka yi wa mahaifi ba'a ko suka rena rashin biyayya ga mahaifiya, hankakin kwari zasu ƙwaƙule idanunsa, kuma angulai zasu cinye namansa.
\s5
\v 18 Akwai abubuwa guda uku masu ban mamaki gare ni, har huɗu da ban fahimce su ba:
\v 19 hanyar gaggafa a sararin samaniya; hanyar macijiya a bisa kan dutse; hanyar jirgi a bisa kan teku; da hanyar ɗan saurayi tare da 'yar budurwa.
\s5
\v 20 Ga hanyar mazinaciya: tana cin abinci ta kuma share baki tana cewa, "Ban yi wani abin da ke ba dai-dai ba."
\s5
\v 21 A ƙarƙashin abubuwa guda uku duniya ke girgiza, kuma a ƙarƙashin guda huɗu bata iya jurewa:
\v 22 lokacin da bawa ya zama sarki; yayin da wawa ya ƙoshi da abinci;
\v 23 macen da aka ƙi lokacin data yi aure; baiwar da kuma ta gãji uwargijiyarta.
\s5
\v 24 Akwai abubuwa huɗu cikin duniya 'yan ƙanƙanana ne amma suna da hikima sosai:
\v 25 tururuwa hallitu ne marasa ƙarfi, amma suna tanadin abincinsu cikin rani;
\v 26 remaye hallitu marasa ƙarfi, amma suna gina gidajensu cikin duwatsu.
\s5
\v 27 Fãra basu da sarki, amma dukkansu suna cincirindo-cincirido.
\v 28 Haka ma ƙadangare, kana iya riƙe shi cikin hannunka biyu, duk da haka kana samun su a cikin fadodi.
\s5
\v 29 Akwai abubuwa uku suna da koƙari cikin ayyukansu haka ma huɗu da ke da takama a yadda suke tafiyarsu:
\v 30 zaki, mai ƙarfi cikin namun jeji - ba shi juya baya daga kowanne abu,
\v 31 zakara mai cara; bunsuru; da kuma sarkin da sojojinsa ke tsaye kusa da shi.
\s5
\v 32 Idan ka yi wauta, kana ɗaukaka kanka, ko idan kana shirye-shiryen mugunta - ka ɗibiya hannuwanka a bakinka.
\v 33 Kamar yadda kaɗaɗɗar madara ke fitar da mai da kuma kamar yadda hanci ke haɓo yayin da aka buge shi, haka ayyukan da aka aiwatar da su a cikin fushi.
\s5
\c 31
\cl Sura 31
\p
\v 1 Maganganun sarki Lemuwel - umarnin da mahaifiyarsa ta koya masa.
\v 2 Mene ne, ya ɗana? Mene ne, ɗan mahaifata? Me kake so, ɗan alƙawarina?
\v 3 Kada ka bada ƙarfinka ga mata, ko hanyarka ga waɗanda ke hallakar da sarakai.
\s5
\v 4 Ba girman sarakai ba ne, Lemuwel, ba girman sarakuna bane su sha giya, ko masu mulki su yi kwaɗayin abin sha mai bugarwa,
\v 5 domin lokacin da suka sha sukan manta da abin da aka umartar, su kuma juyar da yancin dukkan ƙuntattu.
\s5
\v 6 Ka bada abin sha mai bugarwa ga wanda ke hallaka inabi kuma ga waɗanda ke cikin ƙunci.
\v 7 Zaya sha ya manta da talaucinsa kuma ba za shi tuna da wahalarsa ba.
\s5
\v 8 Ka yi magana a madadin waɗanda basu iya magana, don dalilin dukkan masu hallaka.
\v 9 Ka yi magana a fili ka kuma shar'anta dai-dai da ma'aunin adalci ka kuma yi roƙo sabili da nawayar matalauta da mabuƙatan mutane.
\s5
\v 10 Wa ke iya samun mace cikakkiya? Darajarta ta fi duwatsu masu daraja.
\v 11 Zuciyar maigidanta ta yarda ya ita, kuma ba zai taɓa talaucewa ba.
\v 12 Tana yin abubuwan alheri dominsa ba mugunta ba dukkan kwanakinta.
\s5
\v 13 Takan nemi ulu da lilin, ta kuma yi aiki cikin jin daɗi da hannuwanta.
\v 14 Tana kama da fataken jirage; tana kawo abincinta daga nesa.
\v 15 Takan tashi da dare ta bai wa iyalinta abinci, tana kuma raba wa bayinta mata aikinsu.
\s5
\v 16 Takan lura da gona ta kuma saya, da ribar hannuwanta takan dasa gonar inabi.
\v 17 Tana yi wa kanta ado da ƙarfi ta kuma maida kafaɗunta ƙarfafa.
\s5
\v 18 Takan san abin da zai zama riba mai kyau gare ta; dukkan dare fitilarta ba ta mutuwa.
\v 19 Tana ɗora hannunta bisa mazarin sãƙa, kuma ta riƙe murɗaɗɗen zaren.
\s5
\v 20 Tana miƙa hannuwanta zuwa ga matalauta; tana kuma miƙa hannuwanta zuwa ga mutane mabuƙata.
\v 21 Bata tsoron sanyi ta dalilin iyalinta, gama dukkan iyalinta na sanye da kayan sanyi.
\s5
\v 22 Tana yiwa gadonta shimfiɗa, tana kuma sanye da tufafi masu kyau na lilin masu laushi na shunayya.
\v 23 Maigidanta sananne ne a ƙofofi, lokacin da ya ke zama da shugabannin ƙasar.
\s5
\v 24 Takan ɗinka riguna ta sayar, tana kuma sayar da ɗamara ga fatake.
\v 25 Tana yafe da ƙarfi da daraja, kuma tana yiwa lokaci mai zuwa dariya.
\s5
\v 26 Tana buɗe bakinta cikin hikima kuma dokar alheri na a bakinta.
\v 27 Tana lura da tafarkin iyalanta kuma bata cin abincin zaman banza.
\s5
\v 28 Yaranta na tashi su kira ta mai albarka, kuma mijinta na yabonta, cewa,
\v 29 "Mata dayawa sun aikata dai-dai, amma ke kin wuce su gaba ɗaya."
\s5
\v 30 Kayan kwalliya abin yaudara ne, kyau abin banza ne, amma mace mai tsoron Yahweh, za a yabe ta.
\v 31 Ka ba ta 'ya'yan hannuwanta kuma bari ayyukanta su yabe ta a bakin ƙofofi.