ha_ulb/50-EPH.usfm

297 lines
17 KiB
Plaintext
Raw Permalink Normal View History

2021-09-13 13:40:08 +00:00
\id EPH
\ide UTF-8
\h Afisawa
\toc1 Afisawa
\toc2 Afisawa
\toc3 eph
\mt Afisawa
\s5
\c 1
\p
\v 1 Bulus, manzon Yesu Almasihu ta wurin nufin Allah, zuwa ga kebabbu na Allah da ke a Afisa wanda suke aminci cikin Yesu.
\v 2 Bari alheri ya kasance da ku, da salama daga wurin Allah Ubanmu da Ubangijinmu Yesu Almasihu.
\s5
\v 3 Yabo ya tabbata ga Allah Uban Ubangijinmu Yesu Almasihu. Shine ya albarkace mu da kowanne albarku na ruhaniya da ke cikin sammai cikin Almasihu.
\v 4 Kafin halitar duniya, Allah ya zabe mu da muka ba da gaskiya cikin Yesu. Ya zabe mu domin mu yi zaman tsarki da rayuwar da babu aibu a gabansa.
\s5
\v 5 Cikin kauna Allah ya kaddara ya dauke mu mu zama yayansa ta wurin Yesu almasihu. Ya yi wannan domin ya gamshe shi ya yi abin da ya ke so.
\v 6 Sakamakon shine Allah ya karbi yabo domin daukakan alherinsa. Wannan shine abinda ya ba mu hannu sake ta wurin kaunataccensa.
\s5
\v 7 Gama cikin kaunataccensa aka fanshe mu ta wurin jininsa, da gafarar zunubai ta wurin wadataccen alherinsa.
\v 8 Ya ba da wannan alherin a yalwace cikin dukan hikima da fahimta.
\s5
\v 9 Allah ya bayyana mana gaskiyar al'amarin da aka boye na shirinsa, ta wurin abin da yake so ya nuna cikin Almasihu.
\v 10 Idan lokaci ya yi na kammala shirinsa, Allah zai kawo dukan abubuwan da ke sama da kasa cikin Yesu.
\s5
\v 11 An zabe mu cikin Almasihu mu zama abin gado na Allah. Ya yi mana wannan shirin tun da cikin shirin sa, shi mai yin dukan abu ta dalilin nufinsa.
\v 12 Allah ya yi haka saboda mu rayu domin yabon daukakarsa. Mune na farko da muka sami bege cikin Almasihu.
\s5
\v 13 A cikin Almasihu ne kuma kuka samu jin maganar gaskiya, bisharan cetonku ta wurin Yesu. A cikinsa ne kuka bada gaskiya aka hatimce ku da Ruhu Mai Tsarki wanda aka alkawarta.
\v 14 Ruhun shine tabbacin gadonmu kafin mu kai ga samunsa. Wannan don yabon daukakarsa ne.
\s5
\v 15 Sabo da haka, tun lokacin da na ji labarin bangaskiyarku cikin Ubangiji Yesu da kaunar ku zuwa dukan wadanda aka kebe dominsa.
\v 16 Ban fasa tunawa da ku ba ina addu'a saboda ku cikin addu'o'ina.
\s5
\v 17 Ina addu'a da cewa Allah Ubangijinmu Yesu Almasihu, Uban daraja, ya ba ku ruhun basira da wahayin saninsa.
\v 18 Ina addu'a idanun zuciyarku su bude domin ku san tabacin kiranku. Ina addu'a dominku san arzikin mulkin gadonsa cikin wadanda aka kebe dominsa.
\s5
\v 19 Ina addu'a ku san ikon nan nasa mai girma mara iyaka da ke cikin mu da muka ba da gaskiya. Wannan girman yana ta wurin aikin karfin ikonsa ne.
\v 20 Wannan shine ikon da ya yi aiki cikin Almasihu lokacin da Allah ya tashe shi daga matattu ya sa shi a hannun damansa cikin sammai.
\v 21 Ya sanya shi bisa birbishin dukan sarauta, iko, mulki, karfi, da kowanne irin suna. Ya sanya Almasihu ba a wannan zamanin kadai ba, amma da zamani mai zuwa.
\s5
\v 22 Allah ya saka dukan abubuwa a karkashin kafafun Almasihu. Ya sa shi shugaban dukan abubuwa a cikin ikilisiya.
\v 23 Ikilisiya jikinsa ne, cikarsa wanda ya cika dukan abubuwa cikin kowacce hanya.
\s5
\c 2
\p
\v 1 Amma da ku matattu ne cikin zunubanku da laifofinku.
\v 2 A cikinsu kuka yi rayuwa bisa ga al'amuran duniyan nan. Kuka biye wa mai sarautar ikokin sararin sama, wannan ruhun ne da ke aiki cikin kangararrun 'ya'ya.
\v 3 Da can dukanmu muna cikin wadannan marasa bada gaskiya. Muka biye wa mugun burin jikinmu. Muna aikata halin mutuntaka da na tunaninmu. Bisa ga dabi'a 'ya'ya ne wadanda sun cancanci fushin Allah, kamar wadansu.
\s5
\v 4 Amma Allah mai yalwar jinkai ne, sabili da matukar kauna da ya kaunace mu.
\v 5 Sa'anda muke matattu cikin zunubai, ya kawo mu cikin sabon rai tare da Almasihu. Ta wurin alheri aka cece mu.
\v 6 Allah ya tashe mu tare ya kuma sa muka zauna tare a matsayi guda cikin Almasihu Yesu.
\v 7 Ya yi wannan domin a zamanai masu zuwa ya nuna mana matukar yalwar arzikin alherinsa ta wurin Yesu. Yana nuna mana wannan ta wurin alherinsa.
\s5
\v 8 Domin ta wurin alheri aka cece ku ta wurin bangaskiya, wannan ba daga gare ku ba ne, kyauta ce ta Allah.
\v 9 Ba daga ayyuka ba, Saboda wannan dalili kada kowa ya yi fahariya.
\v 10 Gama mu aikin hannuwansa ne, halitattu cikin Almasihu Yesu domin mu yi kyawawan ayyuka, wadanda tun da Allah ya tanada, mu yi rayuwa a cikinsu.
\s5
\v 11 Saboda haka ku tuna da ku al'ummai ne a dabi'ar jiki. Ana kiranku "marasa kaciya", abin da ake kira kaciya cikin jiki wadda hannayen mutane ke yi.
\v 12 Gama a lokacin nan a rabe kuke da Almasihu. Ku bare ne ga mutanen Isra'ila. Ku baki ne ga wa'adodi na al'kawarai. Ba ku da tabbaci a kan gobe. Ba ku da Allah a cikin duniya.
\s5
\v 13 Amma yanzu a cikin Almasihu Yesu ku da da kuke nesa da Allah, an kawo ku kusa da shi ta wurin jinin Almasihu.
\v 14 Gama shine salamar mu. Domin ya mai da biyun daya. Cikin jikinsa ne ya rushe katangar gaba da ta raba mu da juna.
\v 15 Wato ya kawar da shari'a mai umarnai da sharudda, domin ya halitta sabon mutum daya a cikinsa. Yin haka ya kawo salama.
\v 16 Ya yi haka domin ya sulhunta mutum biyu cikin jiki daya ga Allah ta wurin gicciye. Ta wurin gicciye ya kashe gabar da ke tsakaninsu.
\s5
\v 17 Yesu ya zo ya yi maku shelar salama ku da kuke nesa da ku na kusa.
\v 18 Domin ta wurin Yesu dukanmu biyu cikin Ruhu daya muna da hanya zuwa wurin Uba.
\s5
\v 19 Sabo da haka yanzu ku al'ummai, ko daya, ba bare ba ne. Maimakon haka ku abokai ne tare da kebabbun Allah, abokan aiki.
\v 20 Wadanda an gina su bisa tushen manzanni da annabawa. Almasihu Yesu da kansa shine mafificin dutsen ginin.
\v 21 A cikinsa dukan ginin ya hade tare, suna kuma girma kamar haikali cikin Ubangiji.
\v 22 A cikinsa ne kuma ake gina ku gaba daya kun zama mazaunin Allah a cikin Ruhu.
\s5
\c 3
\p
\v 1 Saboda haka, ni Bulus, dan sarka sabili da Almasihu dominku al'ummai.
\v 2 Ina zaton kun ji a kan aiki mai girma na alherin Allah da ya ba ni dominku.
\s5
\v 3 Ina rubuto maku bisa ga wahayin da aka sanashe ni. Wannan ita ce boyayyar gaskiya da na rubuta a takaice a cikin wata wasikar.
\v 4 Sa'adda kuka karanta a kan wannan, za ku iya fahimtar basira ta cikin boyayyar gaskiya a kan Almasihu.
\v 5 Wanda a zamanun da ba a bayyana wa mutane ba. Amma yanzu an bayyana shi ga manzanni da annabawa kebabbu a cikin Ruhu.
\s5
\v 6 Wannan boyayyar bishara ita ce al'ummai ma abokan gado ne tare da mu, gabobi ne cikin jiki daya. Abokan tarayya ne kuma cikin alkawaran Almasihu Yesu ta wurin bishara.
\v 7 Domin wannan na zama bawa ta wurin baiwar alherin Allah da ya bani ta wurin karfin ikonsa.
\s5
\v 8 Allah ne ya ba ni wannan baiwa. Ko da shike nine mafi kankanta cikin kebabbun Allah, in yi shelar bishara ga al'ummai akan wadatar Almasihu marar matuka.
\v 9 In kuma fahimtar da dukan mutane a kan shirin Allah, wannan boyayyar gaskiya wadda tun zamanai da suka wuce Allah ya boye, shi da ke mahallicin dukan abubuwa.
\s5
\v 10 Saboda haka, ta wurin ikilisiya, masu iko da masu mulkin sararin sama za su san hikimar Allah ta fuskoki daban daban.
\v 11 Wannan ya kasance bisa ga dawwamammen nufi da ya zartar cikin Almasihu Yesu Ubangijinmu.
\s5
\v 12 Gama a cikin Almasihu muna da gabagadi, da dama, da amincewa sabili da gaskiyar mu a cikinsa.
\v 13 Saboda haka ina rokon ku kada ku karaya da wahalar da na sha domin ku wadda ta zama daukakar ku.
\s5
\v 14 Saboda haka nake durkusawa da gwiwa ta a gaban Uba,
\v 15 wanda ta wurinsa ake kiran kowanne iyali na sama da na kasa.
\v 16 Ina addu'a ya amince maku bisa ga yalwar wadatar daukakarsa, ku karfafa matuka da iko ta wurin Ruhunsa, da yake cikinku.
\s5
\v 17 Ina addu'a Almasihu ya zauna a cikin zuciyar ku ta wurin bangaskiya. Ina kuma addu'a ku kafu ku kuma ginu da zurfi kwarai cikin kaunarsa.
\v 18 Ku kasance cikin kaunarsa domin ku gane, tare da dukan masu bi, menene zurfi, da fadi, da tsawon kaunar Almasihu.
\v 19 Ina addu'a domin ku san mafificiyar kaunar Almasihu da ta wuce sani. Ku yi wannan domin a cika ku da dukan cikar Allah.
\s5
\v 20 Yanzu ga wanda yake da ikon aikata dukan abu fiye da abin da muke roko ko tunani, bisa ga ikonsa da ke aiki a cikinmu,
\v 21 daukaka ta tabbata a gare shi a cikin ikilisiya ta wurin Almasihu Yesu har ya zuwa zamanun zamanai har abada abadin. Amin.
\s5
\c 4
\p
\v 1 Saboda haka a matsayi na na dan sarka saboda Ubangiji; ina rokon ku ku yi zaman rayuwa da ta cancanci kiran da Allah ya kiraye ku.
\v 2 Ku zamna da matukar tawali'u da sahihanci da hakuri. Ku karbi juna cikin kauna.
\v 3 Ku yi kokarin zaman dayantaka cikin Ruhu kuna hade cikin salama.
\s5
\v 4 Akwai jiki daya da kuma Ruhu daya, kamar yadda aka kira ku a kan begen nan daya.
\v 5 Ubangiji daya, bangaskiya daya, da kuma baftisma daya.
\v 6 Allah daya ne da Uban duka. Shine bisa duka, ta wurin duka, da kuma cikin duka.
\s5
\v 7 Ko wannenmu an ba shi baiwa bisa ga awon baiwar Almasihu.
\v 8 Kamar yadda nassi ya ce, "Da ya haye zuwa cikin sama, ya bi da bayi cikin bauta. Ya kuma yi wa mutane baye baye.
\s5
\v 9 Menene ma'anar, "Ya hau?" Ana cewa kenan ya sauka har cikin zurfin kasa.
\v 10 Shi da ya sauka shine kuma wanda ya hau birbishin sammai. Ya yi wannan domin ya cika dukan abubuwa.
\s5
\v 11 Almasihu ya ba da baye baye kamar haka: manzanni, annabawa, masu shelar bishara, makiyaya, da masu koyarwa.
\v 12 Ya yi haka domin ya shiryar da masu bi saboda hidima, domin gina jikin Almasihu.
\v 13 Ya yi haka har sai mun kai dayantakar bangaskiya da sanin Dan Allah. Ya yi haka har sai mun kai ga manyanta, kamar wadanda suka kai cikakken matsayin nan na falalar Almasihu.
\s5
\v 14 Wannan ya zamanto haka domin kada mu kara zama kamar yara. Kada a yi ta juya mu. Wannan haka yake domin kada mu biye wa iskar kowacce koyarwa ta makirci da wayon mutane masu hikimar yin karya.
\v 15 Maimakon haka za mu fadi gaskiya cikin kauna domin mu yi girma cikin dukan tafarkun da ke na sa, shi da yake shugaba, Almasihu.
\v 16 Almsihu ya hada dukan jikin masu ba da gaskiya. Jikin yana hade ta wurin kowanne gaba, domin jikin ya yi girma ya gina kansa cikin kauna.
\s5
\v 17 Saboda haka ina yi maku gargadi cikin Ubangiji cewa, kada ku sake yin rayuwa irin ta al'ummai da suke yi cikin azancin wofi marar amfani.
\v 18 Sun duhunta cikin tunaninsu. Bare suke da rai irin na Allah, ta wurin jahilcin da ke cikinsu da ta wurin taurare zukatansu.
\v 19 Basa jin kunya. Sun mika kansu ga mutumtaka ta yin kazamtattun ayyuka da kowacce zari.
\s5
\v 20 Amma ba haka kuka koyi al'amuran Almasihu ba.
\v 21 Ina zaton kun rigaya kun ji a kansa. Ina zaton an koyar da ku cikinsa, kamar yadda gaskiyar Yesu ta ke.
\v 22 Dole ku yarda halin ku na da, wato tsohon mutum. Tsohon mutumin ne ya ke lalacewa ta wurin mugun buri.
\s5
\v 23 Ku yarda tsohon mutum domin a sabonta ku cikin ruhun lamirinku.
\v 24 Ku yi haka domin ku yafa sabon mutum, mai kamanin Allah. An hallitta shi cikin adalci da tsarki da gaskiya.
\s5
\v 25 Saboda haka ku watsar da karya. "Fadi gaskiya ga makwabcin ka", domin mu gabobin juna ne.
\v 26 "Ku yi fushi, amma kada ku yi zunubi." Kada ku bari rana ta fadi kuna kan fushi.
\v 27 Kada ku ba shaidan wata kofa.
\s5
\v 28 Duk mai yin sata, kada ya kara yin sata kuma. Maimakon haka, ya yi aiki. Ya yi aiki da hannuwan sa domin ya sami abin da zai taimaka wa gajiyayyu.
\v 29 Kada rubabbun maganganu su fito daga cikin bakinku. Maimakon haka, sai ingantattu da za su ba da alheri ga masu ji.
\v 30 Kada ku bata wa Ruhu Mai Tsarki na Allah rai domin ta wurin sa ne aka hatimce ku domin ranar fansa.
\s5
\v 31 Sai ku watsar da dukan dacin rai, da hasala, da fushi, da tankiya, da reni tare da dukan mugunta.
\v 32 Ku yi wa juna kirki, ku zama da taushin zuciya. Ku yafe wa juna, kamar yadda Allah cikin Almasihu ya gafarta maku.
\s5
\c 5
\p
\v 1 Saboda haka ku zama masu koyi da Allah, kamar kaunatattun 'ya'yansa.
\v 2 Ku yi zama cikin kauna kamar yadda Almasihu ya kaunace mu, ya kuma mika kansa sadaka da hadaya ga Allah dominmu, hadaya mai kanshi abin karba ga Allah.
\s5
\v 3 Fasikanci ko kowacce irin kazamta, ko kazamar lalata kada a ambace su a tsakaninku, don haka ya dace ga masu bi.
\v 4 Kada a ambaci batsa, maganar wauta ko alfasha wadanda ba su dace ba. Maimakon haka, mu zama masu godiya.
\s5
\v 5 Domin wannan kun sani cewa ba fasiki, ko mara tsarki, ko mai hadama wato mai bautar gumaka zai sami gado cikin mulkin Almasihu da Allah.
\v 6 Kada kowa ya rude ku da maganganun wofi. Saboda wadannan abubuwa ne fushin Allah ke zuwa kan kangararrun 'ya'ya.
\v 7 Kada ku yi tarayya tare da su.
\s5
\v 8 Domin da ku duhu ne, amma yanzu ku haske ne cikin Ubangiji. Sai ku yi tafiya kamar 'ya'yan haske.
\v 9 Saboda amfanin haske shine dukan alheri, adalci da gaskiya.
\v 10 Kuna bidar abin da Ubangiji ke murna da shi.
\v 11 Kada ku sa hannu ga ayyuka marasa amfani da ayyukan duhu amma gara a tone su.
\v 12 Don abubuwan da suke yi a boye abin kunya ne a bayyana su.
\s5
\v 13 Dukan abu, idan haske ya bayyana su, za a gan su.
\v 14 Domin duk abin da aka bayyana ya zama haske. Saboda haka aka ce, "Ka farka, kai mai barci, ka tashi daga cikin matattu; Almasihu kuwa zai haskaka bisanka".
\s5
\v 15 Saboda haka, ku maida hankali yadda kuke rayuwar ku, ba kamar mutane marasa hikima ba amma kamar masu hikima.
\v 16 Ku yi lura yadda kuke amfani da lokaci don kwanakin miyagu ne.
\v 17 Kada ku zama wawaye. Maimakon haka, ku fahimci ko menene nufin Ubangiji.
\s5
\v 18 Kuma Kada ku bugu da ruwan inabi, don yana iya lalata rayuwa. Maimakon haka, ku cika da Ruhu Mai Tsarki.
\v 19 Kuna magana da junanku cikin zabura da wakoki da wakokin ruhaniya, kuna rairawa da yabo da zuciyarku ga Ubangiji.
\v 20 Kullum kuna ba da gaskiya domin dukan abubuwa cikin sunan Ubangiji Yesu ga Allah Uba.
\v 21 Kuna sarayadda kanku ga juna cikin girmama Almasihu.
\s5
\v 22 Mata, ku yi biyayya ga mazan ku kamar ga Ubangiji.
\v 23 Domin miji shine shugaban matarsa kamar yadda Almasihu yake shugaban ikilisiya. Shine kuma mai ceton jiki.
\v 24 Amma kamar yadda ikilisiya take biyayya ga Almasihu, haka kuma dole mata suyi ga mazajen su cikin kowanne abu.
\s5
\v 25 Mazaje, ku kaunaci matanku kamar yadda Almasihu ya kaunaci ikilisiya har ya ba da kansa dominta,
\v 26 Ya yi wannan domin ya tsarkake ta. Ya wanke mu da ruwan wanki ta wurin kalma.
\v 27 Ya yi wannan domin ya mika ma kansa ikilisiya mai daraja, ba tare da tabo ko cikas ko wani abu kamar wadannan, amma ta zama da tsarki da kuma mara aibi.
\s5
\v 28 Hakannan kuma, mazaje su kaunaci matansu kamar jikunnansu. Wanda yake kaunar matarsa yana kaunar kansa.
\v 29 Ba wanda ya taba kin jikinsa. Amma, yakan ciyadda shi yana kaunarsa, kamar yadda Almasihu ya kaunaci ikilisiya.
\v 30 Domin mu gabobin jikinsa ne.
\s5
\v 31 "Domin wannan mutum zai rabu da ubansa da uwarsa ya manne wa matarsa, su biyu su zama nama daya".
\v 32 Wannan asirin gaskiyar, da girma yake, amma ina magana ne game da Almasihu da ikilisiyarsa.
\v 33 Duk da haka, kowannenku dole ya kaunaci matarsa kamar kansa, matar kuma dole ta girmama mijinta.
\s5
\c 6
\p
\v 1 'Ya'ya, ku yi biyayya ga iyayenku chikin Ubangiji, domin wannan daidai ne.
\v 2 "Ka girmama mahaifinka da mahaifiyarka" (Doka ta fari kenan da alkawari),
\v 3 "ta haka za ku yi albarka, domin kwanakinku su yi tsawo a duniya".
\s5
\v 4 Hakanan, ku ubanni kada ku cakuni 'ya'yan ku har su yi fushi, amma ku goye su cikin horon Ubangiji da gargadinsa.
\s5
\v 5 Bayi, ku yi biyayya ga iyayengijinku na duniya tare da girmamawa da tsoro da zuciya mai gaskiya. Ku yi masu biyayya kamar ga Almasihu.
\v 6 Ku yi masu biyayya ba don lallai suna kallonku ba domin ku faranta masu rai. Maimakon haka, ku yi biyayya kamar bayi ga Almasihu. Ku yi nufin Allah daga zuciya.
\v 7 Ku yi hidima da dukan zuciya, kamar kuna bautar Ubangiji ba mutane ba.
\v 8 Sai ku sani cewa duk abinda mutum ya yi zai karbi sakamako daga wurin Ubangiji, ko shi bawa ne ko 'yantacce.
\s5
\v 9 Ku kuma iyayengiji, ku yi irin wannan ga barorin ku. Kada ku razana su. Kun sani shi wanda ke Ubangijinsu da ku daya ne yana sama. Kun sani tare da shi baya nuna tara.
\s5
\v 10 A karshe, ku karfafa cikin Ubangiji da cikin karfin ikonsa.
\v 11 Ku dauki dukan makamai na Allah, domin ku iya dagewa gaba da dabarun shaidan.
\s5
\v 12 Gama yakinmu ba da nama da jini bane. Amma, da ikoki da mulkoki da mahukuntan wannan zamani mai duhu da rundunai masu duhu na mugunta cikin sammai.
\v 13 Don haka ku dauki dukan makamai na Allah, domin ku iya tsayawa da karfi cikin muguwar rana. Bayan kun yi komai za ku tsaya da karfi.
\s5
\v 14 Saboda haka ku tsaya da karfi. Ku yi wannan bayan kun yi damara cikin gaskiya kuna yafa sulke na adalci.
\v 15 Ku yi wannan bayan kun daure kafafunku da shirin kai bisharar salama.
\v 16 Cikin dukan abu ku dauki garkuwar bangaskiya, wadda za ku kashe dukan kibau masu wuta na mugun.
\s5
\v 17 Ku dauki kwalkwalin ceto da takobin Ruhu, wanda shine maganar Allah.
\v 18 Tare da kowacce irin addu'a da roko kuna addu'a kullum cikin Ruhu. Da wannan lamiri, kuna tsare wannan da iyakacin kula da dukan juriya da roko saboda dukan masu bi.
\s5
\v 19 Ku yi mani addu'a, domin in karbi sako duk sa'adda na bude bakina. Ku yi addu'a in sami gabagadin bayyana boyayyar gaskiyar bishara.
\v 20 Saboda bishara nake jakada cikin sarkoki, yadda a cikinta zan yi magana gabagadi yadda takamata.
\s5
\v 21 Amma domin ku san rayuwa ta, da yadda nake, Tikikus, dan'uwa kaunatacce da amintaccen bawa cikin Ubangiji, zai sanar da ku dukan abu.
\v 22 Saboda wannan dalili na aiko shi gare ku, domin ku san al'amuran mu, kuma domin ku sami ta'aziya a zukatan ku.
\s5
\v 23 Bari salama ta kasance tare da 'yan'uwa, kauna da bangaskiya daga wurin Allah Uba da Ubangiji Yesu Almasihu.
\v 24 Alheri ya kasance tare da wadannan da suke kaunar Ubangijinmu Yesu Almasihu tare da kauna mara mutuwa.