2281 lines
163 KiB
Plaintext
2281 lines
163 KiB
Plaintext
|
\id EXO
|
|||
|
\ide UTF-8
|
|||
|
\h Littafin Fitowa
|
|||
|
\toc1 Littafin Fitowa
|
|||
|
\toc2 Littafin Fitowa
|
|||
|
\toc3 exo
|
|||
|
\mt Littafin Fitowa
|
|||
|
|
|||
|
\s5
|
|||
|
\c 1
|
|||
|
\cl Sura 1
|
|||
|
\p
|
|||
|
\v 1 Ga sunanyen 'ya'yan Isra'ila da suka zo cikin Masar tare da Yakubu, kowannen su tare da iyalansa:
|
|||
|
\v 2 Ruben, da Simiyon, da Lebi, da kuma Yahuda,
|
|||
|
\v 3 da Issaka, da Zebulun da kuma Benyamin,
|
|||
|
\v 4 da Dan, da Naftali, da Gad, da Asha.
|
|||
|
\v 5 Dukkan zuriyar Yakubu su saba'in ne. Yosef yana nan a Masar.
|
|||
|
|
|||
|
\s5
|
|||
|
\v 6 Sai Yosef, dukkan 'yan uwansa, da duk wannan tsãra suka mutu.
|
|||
|
\v 7 Isra'ilawa suka yi albarka, suka riɓaɓɓanya, da kuma ƙara ƙarfi sosai; ƙasar kuma ta cika da su.
|
|||
|
|
|||
|
\s5
|
|||
|
\v 8 Yanzu dai sai wani sabon sarki ya taso a Masar, wanda bai san da Yosef ba.
|
|||
|
\v 9 Ya cewa mutanensa, "Ku duba, Isra'ilawan sun fi mu yawa da kuma ƙarfi.
|
|||
|
\v 10 Ku zo, bari mu bi da su cikin hikima, idan ba haka ba za su ci gaba da haɓɓaƙa, idan yaƙi ya taso, za su haɗa kai da maƙiyanmu, su yaƙe mu, su kuma bar ƙasar."
|
|||
|
|
|||
|
\s5
|
|||
|
\v 11 Sai suka ɗora shugabannin aikin tilas a bisansu domin su wahalshe su da bauta mai zafi. Isra'ilawan suka gina wa Fir'auna biranen ajiya: Fitom da Ramesis.
|
|||
|
\v 12 Amma sa'ad da Masarawan suke ƙuntata masu, da haka Isra'ilawa ke ƙaruwa suna kuma yaɗuwa. Don haka Masarawan suka fara tsorata da Isra'ilawa.
|
|||
|
|
|||
|
\s5
|
|||
|
\v 13 Masarawan suka sa Isra'ilawa su yi aiki mai tsanani.
|
|||
|
\v 14 Suka sa rayukan su suka yi ɗaci cikin hidimarsu a kwaɓa ƙasa da ginin tubali, da kuma dukkan ayyuka a cikin filaye. Dukkan aikin da ake so suyi masu wuya ne.
|
|||
|
|
|||
|
\s5
|
|||
|
\v 15 Sai sarkin Masar ya yi magana da mataye unguwarzoma na Ibraniyawa; ɗaya sunanta Shifra, ɗayan kuma Fuwa.
|
|||
|
\v 16 Ya ce, "Lokacin da kuke taimaka wa matan Ibraniyawa a kujeran haihuwa, ku kula da lokacin da suka haihu. Idan ɗa namiji ne, to sai ku kashe shi; amma idan mace ce, to tana iya rayuwa."
|
|||
|
\v 17 Amma matan unguwarzoma suka ji tsoron Allah ba su kuma aikata yadda sarkin Masar ya umarce su ba; a maimakon haka, suka bar 'ya'ya maza su rayu.
|
|||
|
|
|||
|
\s5
|
|||
|
\v 18 Sarkin Masar ya kirawo mataye unguwarzoman ya ce masu, "Don me kuka yi haka, da kuka bar 'ya'ya maza su rayu?"
|
|||
|
\v 19 Unguwarzoman suka ce wa Fir'auna, "Matayen Ibraniyawa ba kamar matayen Masar ba ne. Suna da ƙarfi kuma kamin mu iso gare su sun rigaya sun haihu."
|
|||
|
|
|||
|
\s5
|
|||
|
\v 20 Allah kuma ya tsare waɗannan mata unguwarzoma. Mutanen kuma suka riɓaɓanya suka zama da ƙarfi sosai.
|
|||
|
\v 21 Domin mataye unguwarzoman sun ji tsoron Allah, sai ya ba su iyalai.
|
|||
|
\v 22 Sai Fir'auna ya ba dukkan mutanensa doka, "Dole ku jefa kowanne ɗan da aka haifa cikin kogi, amma kowacce ɗiya ku bar ta da rai."
|
|||
|
|
|||
|
\s5
|
|||
|
\c 2
|
|||
|
\cl Sura 2
|
|||
|
\p
|
|||
|
\v 1 To akwai wani mutum daga kabilar Lebi wanda ke auren wata mace mutumiyar Lebi.
|
|||
|
\v 2 Macen ta yi juna biyu ta kuma haifi ɗan yaro. Da ta ga cewa yaron lafiyayye ne, sai ta ɓoye shi har wata uku.
|
|||
|
|
|||
|
\s5
|
|||
|
\v 3 Amma da ya kai wani lokacin da ta ga ba za ta iya ɓoye shi ba, sai ta ɗauki kwandon iwa ta dalaye shi da katsi da ƙaro. Sai ta sanya jaririn ciki ta kuma saka shi cikin ruwan a cikin ciyayin bakin teku.
|
|||
|
\v 4 'Yar'uwarsa na tsaye daga nesa don ta ga abin da zai faru da shi.
|
|||
|
|
|||
|
\s5
|
|||
|
\v 5 Ɗiyar Fir'auna ta gangaro zuwa kogin domin ta yi wanka yayin da kuyanginta na tafiya a gefen kogin. Sai ta hango kwandon cikin ciyayi sai ta aika kuyanginta su kawo shi.
|
|||
|
\v 6 Da ta buɗe, sai ta ga jaririn. Duba, jaririn na kuka. Sai ta yi juyayinsa ta kuma ce, "Wannan lallai ɗaya daga cikin 'ya'yan Ibraniyawa ne."
|
|||
|
|
|||
|
\s5
|
|||
|
\v 7 Sai 'yar uwar jaririn ta ce ma ɗiyar Fir'auna, "In je in nemo maki mai reno daga cikin matan Ibraniyawa?"
|
|||
|
\v 8 Sai ɗiyar Fir'auna ta ce ma ta, "Je ki." Sai yarinyar ta tafi ta kuma samo uwar jaririn.
|
|||
|
|
|||
|
\s5
|
|||
|
\v 9 Sai ɗiyar Fir'auna ta cewa uwar jaririn, "Ɗauki jaririn nan ki yi mani renon sa, ni kuma zan biya ki albashi." Sai matar ta ɗauki jaririn ta yi renon sa.
|
|||
|
\v 10 Da jaririn ya yi girma, sai ta kawo shi wurin ɗiyar Fir'auna, sai ya zama ɗanta. Ta raɗa masa suna Musa ta kuma ce, "Domin na tsamo shi daga ruwa."
|
|||
|
|
|||
|
\s5
|
|||
|
\v 11 Da Musa ya yi girma, ya tafi wurin mutanensa ya kuma lura da nawayarsu. Sai ya ga wani Bamasare na bugun Ba'ibrane, ɗaya daga cikin mutanensa.
|
|||
|
\v 12 Sai ya waiga nan da can, da ya ga babu kowa a wurin, sai ya kashe Bamasaren ya kuma binne jikinsa cikin yashi.
|
|||
|
|
|||
|
\s5
|
|||
|
\v 13 Washegari ya sake fita, kuma, gashi kuwa, biyu daga cikin mazajen Ibraniyawa suna faɗa da juna. Ya cewa wanda shi ke da rashin gaskiya, "Me ya sa kake dukan ɗan'uwan ka?"
|
|||
|
\v 14 Amma mutumin yace, "Waye ya sanya ka shugaba da mai shari'a bisanmu? Ko kana shirin kashe ni kamar yadda ka kashe wancan Bamasaren?" Sai Musa ya ji tsoro ya kuma ce, "Abin da na yi tabbas ba a ɓoye yake ga sauran ba."
|
|||
|
|
|||
|
\s5
|
|||
|
\v 15 Ya zama kuma da Fir'auna ya ji abin da ya faru, sai ya yi ƙoƙarin kashe Musa. Amma Musa ya tsere daga gaban Fir'auna zuwa ƙasar Midiyan. A nan ya zauna a bakin wata rijiya.
|
|||
|
\v 16 Ya zama cewa firist na Midiyan na da 'yan mata guda bakwai. Suka zo, su ɗebi ruwa, su cika kwamayensu don su shayar da garkunan mahaifinsu.
|
|||
|
\v 17 Sai wasu makiyaya suka zo suka yi ƙoƙarin korar su, amma Musa ya tashi ya taimake su. Sai kuma ya shayar da dabbobinsu.
|
|||
|
|
|||
|
\s5
|
|||
|
\v 18 Da 'yan matan suka komo wurin Ruwel mahaifinsu, ya ce, "Me ya sa kuka yi saurin dawo wa gida yau?"
|
|||
|
\v 19 Suka ce, "Wani Bamasare ne ya kuɓutar da mu daga hannun makiyayan. Har ma ya jawo mana ruwa ya shayar da garken."
|
|||
|
\v 20 Sai ya ce da 'yan matansa, "To ina yake? Don me kuka bar mutumin? Ku kira shi domin ya ci abinci tare da mu."
|
|||
|
|
|||
|
\s5
|
|||
|
\v 21 Sai Musa ya yarda da ya zauna tare da mutumin, shi ma sai ya ba shi ɗiyarsa Ziffora ya aura.
|
|||
|
\v 22 Ta haifa masa ɗan yaro, sai Musa ya kira shi da suna Gashom; yana cewa, "Na zama mai baƙonci a cikin baƙuwar ƙasa."
|
|||
|
|
|||
|
\s5
|
|||
|
\v 23 Bayan lokaci mai tsawo, sai sarkin Masar ya mutu. Isra'ilawa suka yi nishi saboda aikin bautarsu. Suka yi kukan neman taimako, sai kuma roƙon su ya kai ga Allah saboda bautarsu.
|
|||
|
\v 24 Sa'ad da Allah ya ga ƙuncinsu, Allah ya tuna da alƙawarinsa da Ibrahim, da Ishaku, da kuma Yakubu.
|
|||
|
\v 25 Allah ya ga Isra'ilawa, ya kuma fahimci matsalarsu.
|
|||
|
|
|||
|
\s5
|
|||
|
\c 3
|
|||
|
\cl Sura 3
|
|||
|
\p
|
|||
|
\v 1 Yanzu dai Musa yana ta kiwon garken Yetro surukinsa, firist na Midiyan. Musa ya kai garken har iyakar sashen hamada ya kuma iso Horeb, tsaunin Allah.
|
|||
|
\v 2 A nan mala'ikan Yahweh ya bayyana gare shi cikin harshen wuta mai ci a kurmi. Sai Musa ya duba, ga shi, kurmin na ci da wuta, amma kurmin bai ƙone sarai ba.
|
|||
|
\v 3 Sai Musa yace, "Zan juya nan inga wannan abin ban mamaki, don me kurmin bai cinye ƙurmus da wutar ba."
|
|||
|
|
|||
|
\s5
|
|||
|
\v 4 Sa'ad da Yahweh ya ga cewa ya juya garin ya duba, sai Allah ya yi kira gare shi daga cikin kurmin ya ce, "Musa, Musa." Musa yace, "Ga ni nan."
|
|||
|
\v 5 Allah yace, "Kada ka iso nan! Ka kwaɓe takalmanka daga kafafun ka, gama inda kake tsaye ƙasa ce keɓaɓɓiya a gare ni."
|
|||
|
\v 6 Ya kuma ce, "Ni ne Allahn mahaifinka, Allahn Ibrahim, da na Ishaku, da kuma na Yakubu." Sai Musa ya rufe fuskarsa, gama yana tsoron duban Allah.
|
|||
|
|
|||
|
\s5
|
|||
|
\v 7 Yahweh yace, "Na ga azabar mutanena da suke a Masar. Na ji kururuwarsu sabili da shugabanninsu na aikin tilas, gama ina sane da wahalarsu.
|
|||
|
\v 8 Na sauko domin in kuɓutar da su daga ikon Masarawa in kuma fito da su daga wannan ƙasa zuwa ƙasa mai kyau, mai girma, ƙasa mai ɓulɓulo da madara da zuma; zuwa ƙasashen Kan'aniyawa, da Hittiyawa, da Amoriyawa, da Ferizziyawa, da Hibiyawa, da kuma Yebusiyawa.
|
|||
|
|
|||
|
\s5
|
|||
|
\v 9 Yanzu dai kururuwar mutanen Isra'ila ta hau zuwa gare ni. Fiye da haka, na ga zaluncin da Masarawa suke gwada masu.
|
|||
|
\v 10 Ga shi yanzu, zan aike ka wurin Fir'auna domin ka fito da mutanena, Isra'ilawa, daga cikin Masar."
|
|||
|
|
|||
|
\s5
|
|||
|
\v 11 Amma Musa ya cewa Allah, "Ni, wane ne, har da zan tafi wurin Fir'auna in kuma fito da Isra'ilawa daga cikin Masar?"
|
|||
|
\v 12 Allah ya amsa, "Ni zan kasance tare da kai tabbas. Wannan zai zama maka alama da cewa Ni na aike ka. Yayin da ka fito da mutanen daga Masar, za ku yi mani sujada a kan wannan n."
|
|||
|
|
|||
|
\s5
|
|||
|
\v 13 Sai Musa ya cewa Allah, "Sa'ad da na tafi wurin Isra'ilawa na kuma ce masu, 'Allah na kakanninku ya aiko ni gare ku,' in kuma suka ce mani, 'Mene ne sunansa?' to me zan amsa masu?"
|
|||
|
\v 14 Sai Allah ya cewa Musa, "NI NE DA NAKE NI NE." Allah yace, "Dole ka faɗi wa Isra'ilawa, 'NI NE ya aiko ni gare ku."'
|
|||
|
\v 15 Allah ya kuma ce wa Musa, "Dole ka gaya wa Isra'ilawa, 'Yahweh, Allah na kakanninku, Allah na Ibrahim, Allah na Ishaku, da Allah na Yakubu, ya aiko gare ku. Wannan ne sunana har abada, kuma da haka za a tuna da ni cikin dukkan tsararraki.
|
|||
|
|
|||
|
\s5
|
|||
|
\v 16 Ka tafi ka tara shugabannin Isra'ila tare. Ka ce masu, 'Yahweh, Allah na kakanninku, Allah na Ibrahim, na Ishaku, kuma da na Yakubu, ya bayyana gare ni ya ce, "Lallai na kula da ku na kuma ga abin da aka yi maku a Masar.
|
|||
|
\v 17 Na yi alƙawarin in fito da ku daga zaluncin Masar zuwa ƙasar Kan'aniyawa, da Hittiyawa, da Amoriyawa, da Feriziyawa, da Hibiyawa, da kuma Yebusiyawa, ƙasa mai zubo da madara da kuma zuma."'
|
|||
|
\v 18 Za su saurare ka. Da kai da shugabannin Isra'ila dole ku je wurin sarkin Masar, dole kuma ku faɗi masa, 'Yahweh, Allah na Ibraniyawa, ya gamu da mu. Saboda haka yanzu bari mu yi tafiyar kwana uku cikin jeji, domin mu yi hadaya ga Yahweh Allahnmu.'
|
|||
|
|
|||
|
\s5
|
|||
|
\v 19 Amma na san da cewa sarkin Masar ba zai bar ku ku tafi ba, sai in an tilasta hannunsa.
|
|||
|
\v 20 Zan miƙa hannuna in kuma kai wa Masarawa farmaki da dukkan al'ajiban da zan aikata a tsakaninsu. Bayan haka, zai ƙyale ku ku tafi.
|
|||
|
\v 21 Zan bai wa mutanen nan tagomashi daga Masarawa, don haka lokacin da kuka fito, ba za ku fita hannu wofi ba.
|
|||
|
\v 22 Kowacce mace za ta roƙi ƙarafan azurfa da zinariya da kuma tuffafi daga maƙwabtansu Masarawa da kuma kowacce mace dake zama gidan maƙwabtanta. Za ku sanya su bisa 'ya'yanku maza da mata. Da haka za ku washe Masarawa."
|
|||
|
|
|||
|
\s5
|
|||
|
\c 4
|
|||
|
\cl Sura 4
|
|||
|
\p
|
|||
|
\v 1 Sai Musa ya amsa, "Amma idan basu gaskata da ni ko su saurare ni ba amma suka ce a maimako, 'Yahweh bai bayyana gare ka ba'?"
|
|||
|
\v 2 Yahweh yace masa, "Menene wannan a hannunka?" Musa yace, "Sanda ce.
|
|||
|
\v 3 Yahweh yace, "Jefa ƙasa." Sai Musa ya jefar da ita ƙasa, sai ta zama maciji. Sai Musa ya guje masa.
|
|||
|
|
|||
|
\s5
|
|||
|
\v 4 Yahweh ya cewa Musa, "Ka miƙa hannu ka riƙe wutsiyar." Sai ya miƙa hannu ya kuma kama macijin. Sai ta sake zama sanda cikin hannunsa.
|
|||
|
\v 5 "Wannan ya faru domin su gaskata da Yahweh, Allahn kakanninsu, Allah na Ibrahim, da Allah na Ishaku, da kuma Allah na Yakubu, ya bayyana gare ka."
|
|||
|
|
|||
|
\s5
|
|||
|
\v 6 Yahweh ya sake ce masa, "Yanzu ka sanya hannun ka cikin rigarka." Sai Musa ya sanya hannunsa a cikin rigarsa. Da ya fito da shi, gashi kuwa, hannunsa ya kama kuturta, fari fat kamar ƙanƙara.
|
|||
|
\v 7 Yahweh yace, "Ka sake maida hannunka cikin riga, kuma da ya fito da shi, sai ya ga cewa an maido da lafiyarsa kuma, kamar sauran sashen fatarsa.
|
|||
|
|
|||
|
\s5
|
|||
|
\v 8 Yahweh yace, "Idan basu gaskanta da kai ba - idan har basu kula da alama ta ikona na farko ba ko su gaskanta da ita ba, to za su gaskanta da alama ta biyun.
|
|||
|
\v 9 Idan kuma basu gaskanta da dukka waɗannan alamu biyu na ikona ba, ko su saurare ka, sai ka ɗebo ruwa daga kogi ka kuma tsiyaye shi a busasshiyar ƙasa. Ruwan daka ɗebo zai zama jini a bisa busasshiyar ƙasar."
|
|||
|
|
|||
|
\s5
|
|||
|
\v 10 Sai Musa ya cewa Yahweh, "Ubangiji, ban taɓa iya magana da kyau ba, ko a dã ko tun lokacin daka yi magana da bawanka. Ni ba mai magana da sauri ba ne kuma harshena mai nauyi ne."
|
|||
|
\v 11 Yahweh yace dashi, "Wanene ya yi bakin mutum? Wa ke maida mutum bebe ko kurma ko mai gani ko makaho? Ba Ni ba ne, Yahweh?
|
|||
|
\v 12 Saboda haka yanzu ka tafi, Ni kuma zan kasance da kai in kuma koya maka abin da za ka faɗi."
|
|||
|
\v 13 Amma Musa yace, "Ubangiji, na roƙe ka ka aika da wani, duk wanda ka so ka aika."
|
|||
|
|
|||
|
\s5
|
|||
|
\v 14 Sai Yahweh ya yi fushi da Musa. Yace, "To Haruna fa, ɗan'uwanka, Ba'lebi? Na san da cewar ya iya magana da kyau. Ga shi ma, yana fitowa don ya tarye ka, kuma sa'ad da ya ganka, zai yi murna cikin zuciyarsa.
|
|||
|
\v 15 Za ka yi magana dashi ka kuma sanya maganganun da zai faɗi a bakinsa. Zan kasance da bakinka da kuma bakin sa, kuma zan bayyana maku ku biyun abin da za ku yi.
|
|||
|
\v 16 Shi za ya yi magana ga mutanen a madadin ka. Zai zama bakinka, kai kuma za ka zama gareshi kamar ni, Allah.
|
|||
|
\v 17 Za ka ɗauki wannan sanda a hannunka. Da ita za ka aiwatar da alamun."
|
|||
|
|
|||
|
\s5
|
|||
|
\v 18 Sai Musa ya komo wurin Yetro surukinsa ya kuma ce dashi, "Bari in tafi domin in koma ga dangina da su ke a Masar in kuma ga ko suna nan da rai." Sai Yetro ya cewa Musa, "Ka tafi cikin salama."
|
|||
|
\v 19 Yahweh ya cewa Musa cikin Midiyan, "Tafi, ka koma Masar, gama dukkan mazajen dake neman su ɗauke ranka sun mutu."
|
|||
|
\v 20 Musa ya ɗauki matarsa da 'ya'yansa ya ɗora su bisa jaki. Ya dawo zuwa ƙasar Masar, ya kuma ɗauki sandar Allah cikin hannunsa.
|
|||
|
|
|||
|
\s5
|
|||
|
\v 21 Yahweh ya cewa Musa, "Lokacin da ka iso Masar, ka tabbata ka aikata a gaban Fir'auna dukkan abubuwan banmamaki da na sanya cikin ikonka. Amma zan taurare zuciyarsa, ba kuwa zai bar mutanen su tafi ba.
|
|||
|
\v 22 Dole ka cewa Fir'auna, 'Ga abin da Yahweh yace: Isra'ila ɗana ne, ɗan fãrina,
|
|||
|
\v 23 kuma ina ce maka, "Ka bar ɗana ya tafi, domin ya yi mani sujada." Amma tunda ka ƙi ka bar shi ya tafi, lallai zan kashe ɗanka, ɗanka na fãri.'"
|
|||
|
|
|||
|
\s5
|
|||
|
\v 24 Yayin da suke kan hanya, da suka tsaya don su kwana a daren nan, Yahweh ya gamu da Musa ya kuma yi ƙoƙarin ya kashe shi.
|
|||
|
\v 25 Sai Ziffora ta ɗauki wuƙa mai kaifi ta yanke loɓar fatar ɗanta, ta taɓa shi da ita ga sawayensa. Sai ta ce, "Tabbas kai ango ne a gare ni ta wurin jini."
|
|||
|
\v 26 Sai Yahweh ya ƙyale shi. Ta ce, "Kai angon jini ne" sabili da kaciyar.
|
|||
|
|
|||
|
\s5
|
|||
|
\v 27 Yahweh yace da Haruna, "Tafi cikin jeji ka gamu da Musa." Haruna ya tafi, ya gamu dashi a tsaunin Allah, ya yi masa sumba.
|
|||
|
\v 28 Sai Musa ya faɗa wa Haruna dukkan maganganun Yahweh da ya aike shi ya faɗi da dukkan alamu na ikon Yahweh da ya umarce shi ya aikata.
|
|||
|
|
|||
|
\s5
|
|||
|
\v 29 Sai Musa da Haruna suka tafi suka tãra dukkan dattawan Isra'ila.
|
|||
|
\v 30 Haruna ya faɗi dukkan maganganun da Yahweh ya faɗa wa Musa. Ya kuma yi alamun na ikon Yahweh a gaban mutanen.
|
|||
|
\v 31 Mutanen suka gaskanta. Lokacin da suka ji cewa, Yahweh ya lura da Isra'ilawa kuma da cewa ya ga ƙuncinsu, sai suka sunkuyar da kansu suka kuma yi masa sujada.
|
|||
|
|
|||
|
\s5
|
|||
|
\c 5
|
|||
|
\cl Sura 5
|
|||
|
\p
|
|||
|
\v 1 Bayan waɗannan abubuwan sun faru, sai Musa da Haruna suka je wurin Fir'auna suka kuma ce, "Ga abin da Yahweh, Allah na Isra'ila, yace: 'Ka bar mutane na su tafi, domin suyi ma ni biki a cikin jeji.'"
|
|||
|
\v 2 Fir'auna yace, "Wane ne Yahweh? Don me zan saurari muryarsa har da zan bar Isra'ila ya tafi? Ban san Yahweh ba; don haka, ba zan bar Isra'ila ya tafi ba."
|
|||
|
|
|||
|
\s5
|
|||
|
\v 3 Suka ce, "Allah na Ibraniyawa ya gamu da mu. Ka bar mu mu yi tafiyar kwana uku cikin jeji mu kuma yi hadaya ga Yahweh Allahnmu domin kada ya kawo mana farmaki da annoba ko takobi."
|
|||
|
\v 4 Amma sarkin Masar yace ma su, 'Musa da Haruna, don me kuke ɗauke mutanen nan daga aikinsu? Ku koma ga aikinku."
|
|||
|
\v 5 Ya kuma ce, "Gashi yanzu akwai mutane Ibraniyawa dayawa a cikin ƙasarmu, kuma kuna sasu su daina aikinsu."
|
|||
|
|
|||
|
\s5
|
|||
|
\v 6 A wannan ranar, Fir'auna ya bada umarni ga shugabannin aikin tilas da masu jagorar mutanen. Ya ce,
|
|||
|
\v 7 Ba kamar dã ba, ba za ku bada tattaka ga mutanen ba domin yin tubula. Bari su tafi su tarawa kansu budu.
|
|||
|
\v 8 Duk da haka, za ka buƙaci tubula daga garesu dai dai kamar yadda ka buƙata a dã. Kada ku karɓi abin da ya gaza yadda aka sãba, domin ƙyuya gare su. Shi yasa suke kira da cewar, 'Bari mu je mu yi hadaya ga Allahnmu.'
|
|||
|
\v 9 Ku ƙara wa mazajen aiki don su duƙufa cikinsa har da ba za su saurari maganganun yaudara ba."
|
|||
|
|
|||
|
\s5
|
|||
|
\v 10 Sai shugabannin aikin tilas da masu jagorar mutanen suka fita suka yi magana da mutane. Suka ka ce, "Ga abin da Fir'auna yace: 'Ba zan ƙara baku wani budu ba.
|
|||
|
\v 11 Ku da kanku dole ku je ku kuma samo budu duk inda ake samunsa, amma aikin ku ba zai ragu ba.'"
|
|||
|
|
|||
|
\s5
|
|||
|
\v 12 Don haka sai mutanen suka barbazu a ko'ina cikin ƙasar Masar domin su tãra yayi don budu.
|
|||
|
\v 13 Sai 'yan gandu suka ci gaba da tsananta masu suna cewa, "Ku gama aikin ku, kamar yadda dã ake baku tattaka."
|
|||
|
\v 14 Shugabannin aikin tilas na Fir'auna suka dinga bugun masu jagorar Isra'ilawa, waɗanda aka sanya bisa sauran ma'aikata. Shugabannin aikin tilas suka dinga tambayarsu, "Don me yasa baku yi dukkan ãdadin tubula da ake buƙata ba, ko na jiya da kuma na yau, kamar yadda kuka sãba a baya?"
|
|||
|
|
|||
|
\s5
|
|||
|
\v 15 Sai masu jagora na Isra'ilawa suka shiga wurin Fir'auna da kuka gare shi. Suka ce, "Meyasa kake yi da bayinka haka?
|
|||
|
\v 16 Babu wata tattakar da ake ba bayin ka kuma, duk da haka suna ce mana, 'Ku yi tubula!' Mu ma, bayin ka, yanzu bugun mu ake yi, duk da haka laifin mutanen ka ne."
|
|||
|
\v 17 Amma Fira'auna yace, "Kuna da ƙyuya! Kuna da ƙyuya! Kun ce, 'Ka barmu mu je mu yi hadaya ga Yahweh.'
|
|||
|
\v 18 Saboda haka yanzu ku koma ga aiki. Ba za a ba ku tattaka ba, amma dole ne ku cika ãdadin tubulan ku."
|
|||
|
|
|||
|
\s5
|
|||
|
\v 19 Sai masu jagorar Isra'ilawa suka ga cewa suna cikin matsala lokacin da aka ce da su, "Ba za ku rage tubula na kowace rana ba."
|
|||
|
\v 20 Sai suka sami Musa da Haruna, a wannan lokaci suna tsaye a wajen fãdar, sa'ad da suke fitowa daga wurin Fir'auna.
|
|||
|
\v 21 Suka cewa Musa da Haruna, 'Bari Yahweh ya dube ku ya kuma hore ku, domin kunsa mun zama abin kyama a gaban Fir'auna da kuma bayinsa. Kun sanya takobi a hannunsu don su kashe mu."
|
|||
|
|
|||
|
\s5
|
|||
|
\v 22 Sai Musa ya komo ga Yahweh ya kuma ce, "Ubangiji, meyasa ka kawo wahala ga mutanenka? Meyasa ka aiko ni tun da farko?
|
|||
|
\v 23 Tun lokacin da na iso wurin Fir'auna domin in yi magana da shi a sunanka, ya jawo wa mutanen nan wahala, kuma baka ƙubutar da mutanenka ba sam-sam."
|
|||
|
|
|||
|
\s5
|
|||
|
\c 6
|
|||
|
\cl Sura 6
|
|||
|
\p
|
|||
|
\v 1 Daga nan Yahweh ya cewa Musa, "Yanzu ne za ka ga abin da zan yi wa Fir'auna. Za ka ga wannan, gama zai barsu su tafi sabili da hannuna mai ƙarfi. Sabili da hannuna mai ƙarfi, zai kore su daga ƙasarsa."
|
|||
|
|
|||
|
\s5
|
|||
|
\v 2 Allah ya yi magana da Musa ya kuma ce masa, "Ni ne Yahweh.
|
|||
|
\v 3 Na bayyana ga Ibrahim, ga Ishaku, ga Yakubu kuma a matsayin Allah Mai Iko Dukka; amma da sunana, Yahweh, basu san Ni ba.
|
|||
|
\v 4 Na kuma kafa alƙawari na da su, domin in ba su ƙasar Kan'ana, ƙasar da suka zauna a matsayin baƙi, ƙasar da suka yi yawo a ciki.
|
|||
|
\v 5 Bugu da ƙari, na ga ƙuncin 'ya'yan Isra'ila waɗanda Masarawa suka bautar, kuma na tuna da alƙawarina.
|
|||
|
|
|||
|
\s5
|
|||
|
\v 6 Saboda haka, ka gaya wa Isra'ilawa, 'Ni ne Yahweh. Zan fito da ku daga bautar Masarawa, kuma zan fishe su daga ƙarƙashin ikon su. Zan kuɓutar da ku ta wurin nuna ikona, tare da manyan ayyukan hukunci.
|
|||
|
\v 7 Zan ɗauke ku a gare ni a matsayin mutane na, zan kuma zama Allahnku. Za ku sani Ni ne Yahweh Allahnku, wanda ya fito da ku daga bautar Masarawa.
|
|||
|
|
|||
|
\s5
|
|||
|
\v 8 Zan kawo ku cikin ƙasar da na rantse in ba Ibrahim, da Ishaku, da kuma Yakubu. Zan bada ita gareku abin mallaka. Ni ne Yahweh."'
|
|||
|
\v 9 Da Musa ya faɗi wannan ga Isra'ilawa, sai suka ƙi su saurare shi saboda karayar zucinsu sabili da bautarsu mai zafi.
|
|||
|
|
|||
|
\s5
|
|||
|
\v 10 Sai Yahweh ya yi magana da Musa, cewa,
|
|||
|
\v 11 "Tafi ka faɗi wa Fir'auna, sarkin Masar, ya bar mutanen Isra'ila su tafi daga ƙasarsa."
|
|||
|
\v 12 Sai Musa ya cewa Yahweh, "To idan har Isra'ilawa ba su saurare ni ba, don me Fir'auna zai saurare ni, tunda ban ƙware a magana ba?"
|
|||
|
\v 13 Yahweh ya yi magana da Musa da kuma Haruna. Ya ba su umarni domin Isra'ilawa domin kuma Fir'auna, sarkin Masar, su fito da Isra'ilawa daga ƙasar Masar.
|
|||
|
|
|||
|
\s5
|
|||
|
\v 14 Waɗannan su ne shugabannin gidajen kakanninsu: 'Ya'yan Ruben, ɗan fari na Isra'ila, su ne Hanok, da Fallu, da Hezron, da kuma Karmi. Waɗannan su ne kakannin kabilar Ruben.
|
|||
|
\v 15 'Ya'yan Simiyon su ne Yemuwel, da Yamin, da Ohad, da Yakin, da Zohar, da kuma Shawul - ɗan wata mace Bakan'aniya. Waɗannan su ne kakannin kabilar Simiyon.
|
|||
|
|
|||
|
\s5
|
|||
|
\v 16 Ga jerin sunayen 'ya'yan Lebi, tare da zuriyarsu. Sune Gashon, da Kohat, da kuma Merari. Lebi ya yi rayuwa har shekaru 137.
|
|||
|
\v 17 'Ya'yan Gashon su ne Libni da Shimei.
|
|||
|
\v 18 'Ya'yan Kohat su ne Amram, da Izhar, da Hebron, da kuma Uzziyel. Kohat ya yi rayuwa har ya kai shekaru 133.
|
|||
|
\v 19 'Ya'yan Merari su ne Mahli da Mushi. Waɗannan suka zama kakannin kabilar Lebiyawa, tare da zuriyarsu.
|
|||
|
|
|||
|
\s5
|
|||
|
\v 20 Amram ya auri Yokebeb, 'yar'uwar mahaifinsa. Ta haifar masa Haruna da Musa. Amram ya yi rayuwa har tsawon shekaru 137 sai kuma ya mutu.
|
|||
|
\v 21 'Ya'yan Izhar su ne Korah, da Nefeg, da Zikri.
|
|||
|
\v 22 'Ya'yan Uzziyel su ne Mishyel, da Elzafan, da kuma Sitri.
|
|||
|
|
|||
|
\s5
|
|||
|
\v 23 Haruna ya auri Elisheba, ɗiyar Amminadab, 'yar uwar Nahshon. Ta haifar masa Nadab da Abihu, da Eliyeza da kuma Itamar.
|
|||
|
\v 24 'Ya'yan Kora su ne Assir, da Elkana, da kuma Abiyasaf. Waɗannan su ne kakannin kabilar Korahawa.
|
|||
|
\v 25 Eliyeza, ɗan Haruna, ya auri ɗaya daga cikin 'ya'ya matan Futiyel. Ta haifa masa Finehas. Waɗannan su ne shugabannin gidajen ubanni a cikin Lebiyawa, tare da zuriyarsu.
|
|||
|
|
|||
|
\s5
|
|||
|
\v 26 Waɗannan mutanen biyu su ne Haruna da Musa a gare su ne Yahweh yace, "Ku fito da 'ya'yan Isra'ilawa daga ƙasar Masar, bisa ga ƙungiyoyinsu na mayaƙa."
|
|||
|
\v 27 Sai Haruna da Musa suka yi magana da Fir'auna, sarkin Masar, da ya barsu su fito da Isra'ilawa daga Masar. Waɗannan dai Musa da Harunan ne.
|
|||
|
|
|||
|
\s5
|
|||
|
\v 28 Da Yahweh ya yi magana da Musa a cikin ƙasar Masar,
|
|||
|
\v 29 ya ce masa, "Ni ne Yahweh. Ka ce wa Fir'auna, sarkin Masar, dukkan abin da zan faɗa maka."
|
|||
|
\v 30 Amma Musa ya cewa Yahweh, "Ban ƙware ba wurin magana, don haka ta yaya Fir'auna zai saurare ni?"
|
|||
|
|
|||
|
\s5
|
|||
|
\c 7
|
|||
|
\cl Sura 7
|
|||
|
\p
|
|||
|
\v 1 Yahweh ya cewa Musa, "Duba, Na maishe ka kamar wani allah ga Fir'auna. Haruna ɗan'uwanka zai zama annabi dominka.
|
|||
|
\v 2 Za ka faɗi dukkan abin da na dokace ka ka faɗa. Haruna ɗan'uwanka zai yi magana da Fir'auna don ya bar mutanen su tafi daga ƙasarsa.
|
|||
|
|
|||
|
\s5
|
|||
|
\v 3 Amma zan taurare zuciyar Fir'auna, kuma zan bayyana alamu masu yawa na iko na, abubuwa masu ban mamaki, cikin ƙasar Masar.
|
|||
|
\v 4 Amma Fir'auna ba zai saurare ku ba, saboda haka zan saukar da hannuna bisa Masar in kuma kawo ƙungiyoyin mayaƙana, mutanena, zuriyar Isra'ila, daga cikin ƙasar Masar da manyan ayyuka na shara'antawa.
|
|||
|
\v 5 Masarawa zasu sani Ni ne Yahweh sa'ad da na miƙa hannuna bisa Masar na kuma fito da Isra'ilawa daga cikin su."
|
|||
|
|
|||
|
\s5
|
|||
|
\v 6 Sai Musa da Haruna suka aikata haka; suka yi dai-dai kamar yadda Yahweh ya dokace su.
|
|||
|
\v 7 Musa yana da shekara tamanin, Haruna kuma yana da shekara tamanin da uku a lokacin da suka yi magana da Fir'auna.
|
|||
|
|
|||
|
\s5
|
|||
|
\v 8 Yahweh ya cewa Musa da Haruna,
|
|||
|
\v 9 "Idan Fir'auna yace maku, 'Ku yi abin al'ajibi,' sai ka ce wa Haruna, 'Ka ɗauki sandarka ka kuma jefa ta ƙasa a gaban Fir'auna, domin ta zama maciji.'"
|
|||
|
\v 10 Sai Musa da Haruna suka tafi wurin Fir'auna, sai kuma suka yi kamar yadda Yahweh ya umarce su. Haruna ya jefar da sandarsa ƙasa a gaban Fir'auna da bayinsa, sai ta zama maciji.
|
|||
|
|
|||
|
\s5
|
|||
|
\v 11 Sai Fir'auna shima ya kira masu hikimarsa da masu duba. Sai su ma suka yi haka ta wurin sihiri.
|
|||
|
\v 12 Kowanne mutum ya jefar da sandarsa ƙasa, sai sandunan suka zama macizai. Amma sai macijin Haruna ya haɗiye macizansu.
|
|||
|
\v 13 Amma zuciyar Fir'auna ta taurare, bai kuwa saurara ba, kamar yadda Yahweh ya faɗa tun dã.
|
|||
|
|
|||
|
\s5
|
|||
|
\v 14 Yahweh ya cewa Musa, "zuciyar Fir'auna ta yi tauri, kuma ya ƙi ya bar mutanen su tafi.
|
|||
|
\v 15 Ka tafi wurin Fir'auna da safe lokacin da ya fita wurin ruwan. Ka tsaya daga bakin kogin don ka tarye shi, ka kuma ɗauki sandarka a hannunka sandar da ta zama maciji.
|
|||
|
|
|||
|
\s5
|
|||
|
\v 16 Ka ce masa, 'Yahweh, Allah na Ibraniyawa, ya aike ni gare ka in ce maka, "Ka bar mutanena su tafi, don su yi mani sujada cikin jeji. Har yanzu baka saurara ba."
|
|||
|
\v 17 Yahweh ya faɗi wannan: "Ta haka zaka sani Ni ne Yahweh. Zan bugi ruwa na Kogin Nilu da sandar dake a hannuna, sai kuma ruwan ya zama jini.
|
|||
|
\v 18 Kifayen da suke a cikin kogin za su mutu, kuma kogin zai yi ɗoyi. Masarawa ba za su iya shan ruwa daga kogin ba.'""
|
|||
|
|
|||
|
\s5
|
|||
|
\v 19 Sai Yahweh yace da Musa, "Ka ce wa Haruna, 'Ka ɗauki sandarka ka miƙa ta zuwa ga ruwayen Masar, da kuma zuwa ga kogunansu, da rafufukansu, da kududdufansu, da kuma dukkan tafkunansu, domin ruwayensu sun zama jini. Ka yi wannan domin a sami jini cikin dukkan ƙasar Masar, har ma da randunan itace da na duwatsu.'"
|
|||
|
|
|||
|
\s5
|
|||
|
\v 20 Sai Musa da Haruna suka yi kamar yadda Yahweh ya umarta. Haruna ya miƙa sandar ya kuma bugi ruwan kogin, a gaban Fir'auna da bayinsa. Sai dukkan ruwaye na kogunan suka zama jini.
|
|||
|
\v 21 Kifayen kogin suka mutu, sai kogin ya fara ɗoyi. Masarawa ba su iya shan ruwa daga kogin ba, kuma sai jinin ya bazu ko'ina a cikin ƙasar Masar.
|
|||
|
\v 22 Amma masu sihiri na Masar suka yi haka dai-dai da dabonsu. Amma zuciyar Fir'auna an taurare, sai kuma ya ƙi ya saurari Musa da Haruna, kamar yadda Yahweh ya faɗi zai faru.
|
|||
|
|
|||
|
\s5
|
|||
|
\v 23 Sai Fir'auna ya juya ya koma gidansa. Bai ma ba da hankalinsa ga wannan ba.
|
|||
|
\v 24 Dukkan Masarawa suka haƙa rami a gefen kogin don su sami ruwa su sha, amma ba su iya shan ruwan kogin da kansa ba.
|
|||
|
\v 25 Kwana bakwai suka wuce bayan da Yahweh ya kai farmaƙi ga kogin.
|
|||
|
|
|||
|
\s5
|
|||
|
\c 8
|
|||
|
\cl Sura 8
|
|||
|
\p
|
|||
|
\v 1 Sai Yahweh ya yi magana da Musa, "Ka tafi wurin Fir'auna ka kuma ce masa, 'Yahweh ya faɗi wannan: "Ka bar mutanena su tafi domin suyi mani sujada.
|
|||
|
\v 2 Idan ka ƙi ka barsu su tafi, zan azabtar da dukkan ƙasarka da ƙwaɗi.
|
|||
|
\v 3 Kogunan za su cika da kwaɗi. Za su fito su shiga gidajenku, da ƙuryar ɗakinku, da kan gadonku. Za su shiga cikin gidajen bayinku. Za su kai ga mutanenka, cikin murhunka, da kuma cikin makwaɓan ƙullunka.
|
|||
|
\v 4 Kwãɗin za su hau kanka, da mutanenka, da kuma dukkan bayinka.""'
|
|||
|
|
|||
|
\s5
|
|||
|
\v 5 Yahweh ya cewa Musa, "Ka ce wa Haruna, 'Miƙa hannun ka tare da sandarka bisa kogunan, da rafufuka, da kuma kududdufai, ka kawo kwãɗi bisa ƙasar Masar."'
|
|||
|
\v 6 Sai Haruna ya miƙa hannunsa bisa ruwayen Masar, sai kwãɗin suka zo suka rufe dukkan ƙasar Masar.
|
|||
|
\v 7 Amma bokayen suka aikata irin haka da dabonsu; suka kawo kwãɗi bisa ƙasar Masar.
|
|||
|
|
|||
|
\s5
|
|||
|
\v 8 Sai Fir'auna ya kirawo Musa da Haruna ya kuma ce, "Ku yi addu'a ga Yahweh don ya kawar da kwãɗin daga gare ni da mutanena. Sa'an nan zan bar mutanen su tafi, domin su yi masa hadaya."
|
|||
|
\v 9 Musa ya cewa Fir'auna, "Kana iya samun zarafin gaya mani in yi maka addu'a, da bayinka, da kuma mutanenka, don a kawar da kwãɗin daga gare ku da gidajenku su kuma tsaya a cikin kogin kawai."
|
|||
|
|
|||
|
\s5
|
|||
|
\v 10 Fir'auna yace, "Gobe." Musa yace, "Bari shi zama yadda ka faɗa, don ka san cewa babu wani kamar Yahweh, Allahnmu.
|
|||
|
\v 11 Kwãɗin za su bar ka, da gidajenka, da bayinka, da kuma mutanenka. Za su tsaya cikin kogi ne kawai."
|
|||
|
\v 12 Sai Musa da Haruna su ka fito daga gaban Fir'auna. Sai Musa ya yi kuka ga Yahweh game da kwãɗin da ya kawo bisa Fir'auna.
|
|||
|
|
|||
|
\s5
|
|||
|
\v 13 Yahweh ya aikata kamar yadda Musa ya roƙa: Sai kwãɗin suka mutu cikin gidajen, daga shirayi, da filaye.
|
|||
|
\v 14 Sai mutanen suka tara su tuli-tuli, sai kuma ƙasar ta yi ɗoyi.
|
|||
|
\v 15 Amma da Fir'auna ya ga cewa akwai sauƙi, sai ya taurare zuciyarsa bai kuma saurari Musa da Haruna ba, kamar yadda Yahweh yace zai yi.
|
|||
|
|
|||
|
\s5
|
|||
|
\v 16 Yahweh ya cewa Musa, "Ka ce da Haruna, 'Ka miƙa sandarka ka bugi ƙurar ƙasa, don ta zama kwarkwata cikin dukkan ƙasar Masar."'
|
|||
|
\v 17 Suka aikata haka: Haruna ya miƙa hannunsa da sandarsa. Ya bugi ƙura a ƙasa. Sai kwarkwata masu yawa suka zo bisa mutum da dabba. Dukkan ƙurar ƙasa ta zama kwarkwata cikin dukkan ƙasar Masar.
|
|||
|
|
|||
|
\s5
|
|||
|
\v 18 Sai bokayen su ma suka gwada da sihirinsu domin su fito da kwarkwata, amma ba su iya yin haka ba. Aka sami kwarkwata a bisa mutane da kuma dabbobi.
|
|||
|
\v 19 Sai bokayen suka ce wa Fir'auna, "Wannan yatsan Allah ne." Amma zuciyar Fir'auna ta taurare, don haka bai saurare su ba. Dai-dai ne ga yadda Yahweh ya faɗi cewa Fir'auna zai yi.
|
|||
|
|
|||
|
\s5
|
|||
|
\v 20 Yahweh ya cewa Musa, "Ka tashi da sauri da safe ka kuma tsaya a gaban Fir'auna yayin da ya fito zuwa kogi. Ka ce da shi, 'Yahweh ya faɗi wannan: "Ka bar mutanena su tafi don suyi mani sujada.
|
|||
|
\v 21 Amma idan baka bar su sun tafi ba, zan aiko da cin-cirindon ƙudaje gareka, zuwa ga bayinka, da kuma mutanenka, da kuma cikin gidajenka. Gidajen Masarawa za su cika da cin-cirindon ƙudaje, har ma da ƙasar da suke tsayawa za ta cika da ƙudaje.
|
|||
|
|
|||
|
\s5
|
|||
|
\v 22 Amma a wannan ranar zan bambanta ƙasar Goshen, ƙasar da mutanena suke zama, don kada a sami wani cin-cirindon ƙudaje a nan. Wannan zai faru domin ka san cewa Ni ne Yahweh da nake tsakiyar wannan ƙasa.
|
|||
|
\v 23 Zan bambanta tsakanin mutanena da mutanenka. Wannan alama ce ta ikona zai faru gobe.""'
|
|||
|
\v 24 Yahweh ya yi haka, sai kuma cin-cirindon ƙudaje mai kauri suka aukawa gidan Fir'auna da kuma gidajen bayinsa. Cikin dukkan ƙasar Masar, ƙasar ta lalace ta dalilin cin-cirindon ƙudajen.
|
|||
|
|
|||
|
\s5
|
|||
|
\v 25 Sa'an nan Fir'auna ya kira Musa da Haruna yace, "Ku tafi, ku yi hadaya ga Allahnku a cikin ƙasarmu."
|
|||
|
\v 26 Musa yace, "Bai yi dai-dai ba muyi haka, gama hadayar da muke yi ga Yahweh Allahnmu abar ƙyama ce ga Masarawa. Idan muka miƙa hadayar suna gani abin ƙyama ga Masarawa, ba zasu jejjefemu ba?
|
|||
|
\v 27 Ba haka ba, tafiyar kwana uku ce cikin jeji da ya kamata muyi, domin muyi hadaya ga Yahweh Allahnmu, kamar yadda ya umurce mu."
|
|||
|
|
|||
|
\s5
|
|||
|
\v 28 Fir'auna yace, "Zan bar ku don ku tafi ku yiwa Allahnku hadaya cikin jeji. Sai dai kada ku tafi da nisa sosai. Ku yi mani addu'a.
|
|||
|
\v 29 Musa yace, "Da zarar na fita daga gare ka, zan yi roƙo ga Yahweh domin cin-cirindon ƙudaje su bar ka, Fir'auna, da bayinka da kuma mutanenka gobe. Amma kada ka ƙara yin yaudara ta wurin ƙin barin mutanenmu su tafi su yiwa Yahweh hadaya."
|
|||
|
|
|||
|
\s5
|
|||
|
\v 30 Sai Musa ya fita daga gaban Fir'auna ya kuma yi roƙo ga Yahweh.
|
|||
|
\v 31 Yahweh ya yi yadda Musa ya roƙa; ya kuma janye cin-cirindon ƙudaje daga Fir'auna, da bayinsa, da mutanensa. Babu wanda ya rage
|
|||
|
\v 32 Amma Fir'auna ya taurare zuciyarsa wannan lokaci kuma, ya kuma ƙi barin mutanen su tafi.
|
|||
|
|
|||
|
\s5
|
|||
|
\c 9
|
|||
|
\cl Sura 9
|
|||
|
\p
|
|||
|
\v 1 Sa'an nan Yahweh yace da Musa, "Jeka wurin Fir'auna ka ce masa, 'Yahweh, Allah na Ibraniyawa, ya faɗi wannan: "Bar mutanena su tafi domin suyi mani sujada."
|
|||
|
\v 2 Amma idan baka yarda ka bar su ba, idan ka hana su,
|
|||
|
\v 3 daganan hannun Yahweh zai kasance bisa garken shanunka cikin filaye da kuma bisa dawakai, da jakuna, da raƙuma, garkunan dabbobi, da garkunan tumaki da awaki, kuma zai yi sanadiyar cuta mai banrazana.
|
|||
|
\v 4 Yahweh zai bambanta garken Isra'ilawa da ta Masarawa kuma babu dabbar dake ta Isra'ilawa da za ta mutu.
|
|||
|
|
|||
|
\s5
|
|||
|
\v 5 Yahweh ya tsayar da lokaci; ya riga yace, "Gobe ne zan aikata wannan abin cikin ƙasar.""'
|
|||
|
\v 6 Yahweh ya yi wannan washegari: Dukkan garkunan shanun Masar suka mutu, amma babu dabbar da ke ta Isra'ila da ta mutu, ko dabba ɗaya.
|
|||
|
\v 7 Fir'auna ya yi bincike, kuma, duba, ko da ɗaya na dabbar Isra'ilawa bata mutu ba. Amma zuciyarsa ta taurare, don haka bai yadda mutanen su tafi ba.
|
|||
|
|
|||
|
\s5
|
|||
|
\v 8 Sai Yahweh ya cewa Musa da Haruna, "Ku ɗebo toka daga murhu. Kai, Musa, dole ka watsa tokar sama cikin iska yayin da Fir'auna na gani.
|
|||
|
\v 9 Za su zama ƙura mai laushi bisa dukkan ƙasar Masar. Za su yi sanadiyar gyambuna da kuma marurai su addabi mutane da dabbobi cikin dukkan ƙasar Masar."
|
|||
|
\v 10 Sai Musa da Haruna suka ɗebo toka daga murhu suka kuma tsaya a gaban Fir'auna. Sai Musa ya watsar da tokar cikin iska. Tokar ta yi sanadiyar gyambuna da marurai da suka addabi mutane da dabbobi.
|
|||
|
|
|||
|
\s5
|
|||
|
\v 11 Bokayen ba su iya tsayayya da Musa ba sabili da gyambunan, domin gyambunan sun kama su da sauran Masarawa.
|
|||
|
\v 12 Yahweh ya taurare zuciyar Fir'auna, don haka Fir'auna bai saurari Musa da Haruna ba. Wannan kamar yadda Yahweh ya riga ya gaya wa Musa ne cewa Fir'auna zai yi.
|
|||
|
|
|||
|
\s5
|
|||
|
\v 13 Sai Yahweh yace wa Musa, "Ka tashi da sassafe, ka tsaya a gaban Fir'auna, ka kuma ce masa, 'Yahweh, Allah na Ibraniyawa, ya faɗi wannan: "Ka bar mutanena su tafi domin suyi mani sujada.
|
|||
|
\v 14 Gama a wannan karon zan aiko da dukkan annobaina a kanka, a bisa bayinka da mutanenka. Zan aikata wannan domin ka san cewa babu wani mai kama da ni cikin dukkan duniya.
|
|||
|
|
|||
|
\s5
|
|||
|
\v 15 Ko a yanzu da na miƙa hannuna in kai maka farmaki da mutanenka da cuta, kuma da yanzu an kawar da kai daga ƙasar.
|
|||
|
\v 16 Amma sabili da wannan dalili ne na bar ka ka tsira: Domin in nuna maka ikona, domin a shaida sunana a cikin dukkan duniya.
|
|||
|
\v 17 Har yanzu kana ɗaukaka kanka gãba da mutanena da har yanzu baka barsu su tafi ba.
|
|||
|
|
|||
|
\s5
|
|||
|
\v 18 Ka saurara! Gobe warhaka zan kawo ruwa da ƙanƙara mai ƙarfi, irin wadda ba a taɓa gani ba a cikin ƙasar Masar ba tun lokacin da aka kafa ta zuwa yau.
|
|||
|
\v 19 Yanzu dai, ku aika mazaje su dawo da garken ku da dukkan abin da kuke da shi a cikin gonaki zuwa ga mafaka. Kowanne mutum da dabba dake a gona da ba a shigo da su gida ba - ƙanƙarar zata faɗo masu, za su kuma mutu.""'
|
|||
|
|
|||
|
\s5
|
|||
|
\v 20 Sa'an nan wasu daga cikin bayin Fir'auna waɗanda suka gaskanta da saƙon Yahweh suka yi hanzari suka dawo da bayinsu da kuma garkensu cikin gidaje.
|
|||
|
\v 21 Amma waɗanda ba su ɗauki maganar Yahweh da wani mahimmanci ba suka bar bayinsu da garken su cikin gonaki.
|
|||
|
|
|||
|
\s5
|
|||
|
\v 22 Sai Yahweh yace wa Musa, "Miƙa hannunka zuwa sararin sama don a yi ƙanƙara cikin dukkan ƙasar Masar, bisa mutane, bisa dabbobi, da kuma dukkan itatuwan cikin gonaki a dukkan ƙasar Masar."
|
|||
|
\v 23 Sai Musa ya miƙa sandarsa zuwa sararin sama, sai Yahweh ya aiko da aradu, ƙanƙara, da walkiya a ƙasar. Ya kuma kwararo ruwan ƙanƙara a bisa ƙasar Masar.
|
|||
|
\v 24 Saboda haka aka yi ƙanƙara da walƙiya gauraye da ƙanƙarar, mai tsananin gaske, irin da ba a taɓa yi ba cikin dukkan ƙasar Masar tun lokacin da ta zama al'umma.
|
|||
|
|
|||
|
\s5
|
|||
|
\v 25 A dukkan ƙasar Masar kuwa, ƙankaran ta bugi kowanne abu cikin gonaki, da mutane da kuma dabbobi. Ta bugi kowacce shuka dake a gonaki ta kuma karya kowanne itace.
|
|||
|
\v 26 A ƙasar Goshen ne kaɗai, inda Isra'ilawa ke zama, babu ƙanƙara.
|
|||
|
|
|||
|
\s5
|
|||
|
\v 27 Daga nan sai Fir'auna ya aika da mutane su kawo Musa da Haruna. Ya ce masu, "Na yi zunubi dai yanzu. Yahweh mai adalci ne, ni kuwa da mutanena mugaye ne.
|
|||
|
\v 28 Ku yi addu'a ga Yahweh, domin waɗannan tsawa mai ƙarfi da kuma ƙanƙara sun yi yawa. Zan barku ku tafi, ba kuma zaku zauna nan ba."
|
|||
|
|
|||
|
\s5
|
|||
|
\v 29 Musa yace masa, "Da zarar na fita daga birnin, zan buɗe hannuwana ga Yahweh. Tsawar aradun zata tsaya, kuma babu sauran ƙanƙara. Ta haka zaka sani cewa duniyar ta Yahweh ce.
|
|||
|
\v 30 Amma game da kai da bayinka, Na san da cewa har yanzu baka rigaya ka girmama Yahweh Allah ba da gaske."
|
|||
|
|
|||
|
\s5
|
|||
|
\v 31 Yanzu dai da hatsi da kuma riɗi an lallatar da su, gama riɗi ta yi ido, hatsi kuma tana fidda kai.
|
|||
|
\v 32 Amma alkama da gero ba a ji masu rauni ba domin ba su yi girma ba tukuna.
|
|||
|
\v 33 Bayan da Musa ya bar Fir'auna da kuma birnin, ya miƙa hannuwansa ga Yahweh; tsawa da ƙanƙara suka tsaya, sai kuma ruwan sama bai sake saukowa ba.
|
|||
|
|
|||
|
\s5
|
|||
|
\v 34 Sa'ad da Fir'auna ya ga cewa ruwan sama ya tsaya, da ƙanƙarar, da tsawar aradun sun tsaya, sai ya sake yin zunubi ya taurare zuciyarsa, duk da bayinsa.
|
|||
|
\v 35 Zuciyar Fir'auna ta taurare, don haka bai bar mutanen Isra'ila su tafi ba. Yadda Yahweh ya riga ya faɗa wa Musa cewa Fir'auna zai aikata.
|
|||
|
|
|||
|
\s5
|
|||
|
\c 10
|
|||
|
\cl Sura10
|
|||
|
\p
|
|||
|
\v 1 Yahweh ya cewa Musa, "Ka tafi wurin Fir'auna, gama na taurare zuciyarsa da zuciyar bayinsa. Na yi haka ne domin in nuna waɗannan alamun ikon ƙarfina a cikin su.
|
|||
|
\v 2 Na kuma yi haka ne domin ku gaya wa 'ya'yanku da jikokinku abubuwan dana yi, yadda na fusata bisa Masar, da kuma yadda na nuna alamu daban-daban na ƙarfin ikona a tsakaninsu. Da haka zaku sani Ni ne Yahweh."
|
|||
|
|
|||
|
\s5
|
|||
|
\v 3 Sai Musa da Haruna suka tafi wurin Fir'auna suka kuma ce masa, "Yahweh, Allah na Ibraniyawa, ya faɗi wannan: 'Har yaushe zaka ƙi ka ƙasƙantar da kanka a gabana? Ka bar mutanena su tafi domin suyi mani sujada.
|
|||
|
\v 4 Amma idan ka ƙi ka bar mutanena su tafi, ka saurara, gobe zan kawo fãri cikin ƙasarka.
|
|||
|
|
|||
|
\s5
|
|||
|
\v 5 Za su rufe fuskar ƙasa har babu wanda zai iya ganin ƙasa. Za su chinye kowanne abin da ya tsira daga ƙanƙara. Za su kuma cinye kowanne itacen da ya tsiro domin ka cikin gonaki.
|
|||
|
\v 6 Za su cika gidajenka, da na bayinka, da na dukkan Masarawa - abu ne wanda mahaifinka da kakanka basu taɓa gani ba, abin da ba a taɓa gani ba tun daga ranar da suke cikin duniya har wa yau.'" Daga nan Musa ya fita ya kuma bar Fir'auna.
|
|||
|
|
|||
|
\s5
|
|||
|
\v 7 Sai bayin Fir'auna suka ce masa, "Har yaushe wannan mutum zai zama mana bala'i? Ka bar Isra'ilawan su tafi domin su yi wa Yahweh Allahnsu sujada. Ko ba ka fahimci cewa an hallakar da Masar ba?"
|
|||
|
\v 8 Aka kawo Musa da Haruna kuma a gaban Fir'auna, sai yace masu, "Ku tafi ku yiwa Yahweh Allahnku sujada. Amma waɗanne mutane ne za su tafi?"
|
|||
|
|
|||
|
\s5
|
|||
|
\v 9 Musa yace, "Za mu tafi tare da ƙanananmu da kuma tsofofinmu, tare da 'ya'yanmu maza da 'ya'ya mata. Zamu tafi da tumakanmu da garkenmu, gama dole ne muyi buki ga Yahweh."
|
|||
|
\v 10 Fir'auna yace masu, "Bari Yahweh lallai ya kasance tare da ku, idan har na barku ku tafi tare da 'yan ƙanananku. Duba, kana da wata mugunta a cikin zuciya.
|
|||
|
\v 11 Ba haka ba! Ku tafi, mazaje kawai na cikinku, ku yiwa Yahweh sujada, gama abin da kuke so kenan." Sa'an nan aka kori Musa da Haruna daga fuskar Fir'auna.
|
|||
|
|
|||
|
\s5
|
|||
|
\v 12 Sai Yahweh ya cewa Musa, "Ka miƙa hannunka bisa ƙasar Masar zuwa ga fãrin, domin su abko wa ƙasar Masar su kuma cinye dashe-dashen cikin ta, dukkan sauran abubuwan da ƙanƙara ta rage."
|
|||
|
\v 13 Musa ya miƙa sandarsa bisa Masar, Yahweh kuwa ya aiko da iskar gabas bisa ƙasar dukkan wannan rana da dare. Sa'ad da safiya ta yi, iskar gabas ta riga ta kawo fãrin.
|
|||
|
|
|||
|
\s5
|
|||
|
\v 14 Fãrin suka shiga dukkan ƙasar Masar suka kuma cutar da dukkan sassanta. Ba a taɓa yin irin wannan cin-cirindon fãri cikin ƙasar ba, ba kuma za a sake mai kamannin haka ba.
|
|||
|
\v 15 Suka rufe fuskar dukkan ƙasa har wuri ya yi duhu. Suka cinye dukkan dashe-dashe da ke cikin ƙasa da dukkan 'ya'yan itatuwan da ƙanƙara ta rage. A cikin dukkan ƙasar Masar, babu koren tsiro mai rai da ta ragu, ko wani itace ko dashe a cikin gonaki.
|
|||
|
|
|||
|
\s5
|
|||
|
\v 16 Sa'an nan Fir'auna ya kirawo Musa da Haruna ya kuma ce, "Na yi zunubi ga Yahweh Allahnku, da gare ku kuma.
|
|||
|
\v 17 Yanzu dai, ku gafarta zunubi na wannan kãron, kuyi addu'a ga Yahweh Allahnku don ya ɗauke wannan mutuwa daga gare ni."
|
|||
|
\v 18 Don haka Musa ya fita daga gaban Fir'auna ya yi addu'a ga Yahweh.
|
|||
|
|
|||
|
\s5
|
|||
|
\v 19 Yahweh ya kawo babbar iskar yamma mai ƙarfi da ta kwashe fãrin ta kora su cikin Jan Teku; babu fãrar da ta rage cikin dukkan lardunan Masar.
|
|||
|
\v 20 Amma Yahweh ya taurare zuciyar Fir'auna, kuma Fir'auna bai bar Isra'ilawa su tafi ba.
|
|||
|
|
|||
|
\s5
|
|||
|
\v 21 Sai Yahweh ya cewa Musa, "Ka miƙa hannunka zuwa sararin sama, don a yi duhu bisa ƙasar Masar, duhun da za a iya taɓawa."
|
|||
|
\v 22 Sai Musa ya miƙa hannunsa zuwa sama, sai aka yi wani gaggarumin duhu bisa dukkan ƙasar Masar har na kwana uku. Babu wanda ya iya ganin wani;
|
|||
|
\v 23 Babu wanda ya bar gidansa har kwana uku. Duk da haka, dukkan Isra'ilawa suna da haske a wurin da suke zaune.
|
|||
|
|
|||
|
\s5
|
|||
|
\v 24 Sai Fir'auna ya aika aka kawo Musa sai yace, "Ku tafi ku yi wa Yahweh sujada. Har da iyalanku na iya tafiya tare da ku, amma garkunan ku na tumaki dole ku bar su nan."
|
|||
|
\v 25 Amma Musa yace, "To dole ka ba mu dabbobin da zamu yi hadaya ga Yahweh Allahnmu.
|
|||
|
\v 26 Garkunan mu dole mu tafi da su; babu ko ƙofaton su da zai rage a baya, gama dole ne mu tafi da su domin yin sujada ga Yahweh Allahnmu. Gama ba mu san da mene ne za mu yi sujada ga Yahweh ba, sai mun isa can."
|
|||
|
|
|||
|
\s5
|
|||
|
\v 27 Amma sai Yahweh ya taurare zuciyar Fir'auna, har da ba zai bar su su tafi ba.
|
|||
|
\v 28 Fir'auna ya cewa Musa, "Ka fita daga gare ni! Kayi hankali da abu ɗaya, cewa kada ka ƙara gani na, gama duk ranar da ka ga fuskata, za ka mutu."
|
|||
|
\v 29 Sai Musa yace masa, "Kai da kanka ka faɗa. Ba zan ƙara ganin fuskarka ba."
|
|||
|
|
|||
|
\s5
|
|||
|
\c 11
|
|||
|
\cl Sura 11
|
|||
|
\p
|
|||
|
\v 1 Daga nan Yahweh ya cewa Musa, "Akwai sauran annoba guda ɗaya da zan kawo bisa Fir'auna da Masar. Bayan wannan, zai barku ku tafi daga nan. Sa'ad da a ƙarshe ya barku kuka tafi, zai kore ku gaba ɗaya.
|
|||
|
\v 2 Ka umarci mutanen cewa kowanne mutum da kowacce mace su roƙi maƙwabcinsa ko maƙwabciyarta kayayyakin azurfa da kayayyakin zinariya."
|
|||
|
\v 3 Yanzu dai Yahweh ya sa Masarawa suyi ɗokin farantawa Isra'ilawa rai. Bugu da ƙari, mutumin nan Musa ya birge sosai a gaban barorin Fir'auna da mutanen Masar.
|
|||
|
|
|||
|
\s5
|
|||
|
\v 4 Musa yace, "Yahweh ya faɗi wannan: 'Wajen tsakar dare zan ratsa cikin dukkan Masar.
|
|||
|
\v 5 Dukkan 'ya'yan fãri cikin ƙasar Masar za su mutu, daga ɗan fãrin Fir'auna, wanda ke zaune bisa kursiyinsa, zuwa ɗan fãrin baiwa wanda ke bayan dutsen niƙa tana niƙa, da dukkan 'ya'yan fãrin dabbobi.
|
|||
|
|
|||
|
\s5
|
|||
|
\v 6 Daga nan za a yi babban makoki cikin dukkan ƙasar Masar, irin wanda ba a taɓa yi ba kuma ba za a ƙara yi ba.
|
|||
|
\v 7 Amma babu ko kare da zai yi haushi ga ko ɗaya daga cikin mutanen Isra'ila, ko ga mutum ko dabba. Ta wannan hanya za ku sani cewa ina nuna bambanci tsakanin Masarawa da Isra'ilawa.'
|
|||
|
\v 8 Dukkan waɗannan bayin naka, Fir'auna, za su sauko zuwa gare ni su rusuna mani. Za su ce, 'Ka tafi, kai da dukkan mutanen da suka biyo ka!' Bayan wannan zan fita." Daga nan ya fita daga wurin Fir'auna da babban fushi.
|
|||
|
|
|||
|
\s5
|
|||
|
\v 9 Yahweh ya cewa Musa, "Fir'auna ba zai saurare ka ba. Wannan ya zama haka ne domin in aiwatar da abubuwan ban mamaki masu yawa a cikin ƙasar Masar."
|
|||
|
\v 10 Musa da Haruna suka yi dukkan waɗannan al'ajibai a gaban Fir'auna. Amma Yahweh ya kangarar da zuciyar Fir'auna, Fir'auna kuma bai bar mutanen Isra'ila suka fita daga ƙasarsa ba.
|
|||
|
|
|||
|
\s5
|
|||
|
\c 12
|
|||
|
\cl Sura 12
|
|||
|
\p
|
|||
|
\v 1 Yahweh ya yi magana da Musa da Haruna a cikin ƙasar Masar. Ya ce,
|
|||
|
\v 2 "Game da ku, wannan wata zai zama farawar watanni, watan farko na shekara a gare ku.
|
|||
|
|
|||
|
\s5
|
|||
|
\v 3 Ka faɗa wa taron Isra'ila, 'A ranar goma ga wannan watan dole ne kowannen su ya ɗauki ɗan rago ko ɗan akuya domin kansu, kowanne iyali na yin wannan, ɗan rago domin kowanne gida.
|
|||
|
\v 4 Idan gidan ya yi ƙanƙanta sosai domin ɗan rago, mutumin da makwabcinsa zasu ɗauki naman ɗan rago ko ɗan akuya wanda zai isa domin adadin mutanen. Ya kasance ya isa domin kowanne mutum ya ci, saboda haka dole su ɗauki isasshen nama domin dukkan su su ci.
|
|||
|
|
|||
|
\s5
|
|||
|
\v 5 Ɗan ragonku ko ɗan akuyan dole ya zama marar aibi, ɗan shekara ɗaya m. Kuna iya ɗaukar ɗaya daga cikin tumaki ko awaki.
|
|||
|
\v 6 Tilas ku ajiye ta har sai ranar sha huɗu ga wata. Daga nan dukkan taron Isra'ila tilas su yanka waɗannan dabbobi da hasken asuba.
|
|||
|
\v 7 Tilas ku ɗiba daga cikin jinin ku kuma sanya a dokin ƙofa gefe biyu da saman ginshiƙan ƙofofin gidajen inda zaku ci naman.
|
|||
|
\v 8 Tilas ku ci naman a wannan daren, bayan an gasa da farko a bisa wuta. A ci shi da gurasa da akayi ba da gami ba, tare da ganye mai ɗaci.
|
|||
|
|
|||
|
\s5
|
|||
|
\v 9 Kada ku ci shi ɗanye ko dafaffe cikin ruwa. A maimako, ku gasa shi bisa wuta tare da kansa, kafafunsa da kayan cikinsa.
|
|||
|
\v 10 Tilas ba za ku bar wani daga cikinsa ba ya rage har safiya. Tilas ku ƙone duk abin da ya rage har safiya.
|
|||
|
\v 11 Ga yadda tilas zaku ci shi: tare da ɗamararku a ɗaure, takalmanku bisa tafin ƙafarku, da sandarku a hannunku. Tilas ku ci shi da hanzari. Ƙetarewa ne na Yahweh.
|
|||
|
|
|||
|
\s5
|
|||
|
\v 12 Yahweh ya faɗi wannan: zan ratsa ta cikin ƙasar Masar a wannan dare zan kuma kai hari ga dukkan 'ya'yan fãri na mutum da na dabba a cikin ƙasar Masar. Zan kawo horaswa ga dukkan allolin Masar. Ni ne Yahweh.
|
|||
|
\v 13 Jinin zai zama alama ne bisa gidajenku domin zuwa na a gare ku. Idan naga jinin, Zan ƙetare ku sa'ad da na kai hari ga ƙasar Masar.
|
|||
|
\v 14 Wannan annoba ba za ta zo bisan ku ba ta kuma hallaka ku. Wannan rana zata zama abar tunawa domin ku, wadda tilas ku kiyaye a matsayin bikin Yahweh. A koyaushe zai kasance shari'a a gare ku, cikin dukkan tsararrakin mutanenku, cewa tilas ku kiyaye wannan rana.
|
|||
|
|
|||
|
\s5
|
|||
|
\v 15 Zaku ci gurasa ba tare da gami ba a lokacin kwanakin bakwai. A rana ta farko zaku cire gami daga gidajenku. Duk wanda yaci gurasa mai gami daga ranar farko zuwa rana ta bakwai, wannan taliki tilas a datse shi daga Isra'ila.
|
|||
|
\v 16 A rana ta farko za ayi taro da za a keɓe a gare ni, a rana ta bakwai kuma za a sake yin wani irin wannan taron. Babu wani aikin da za ayi a cikin waɗannan kwanaki, sai dai girki domin kowa ya ci. Wannan ne kaɗai aikin da tilas ya zama mai yiwuwa a gare ku.
|
|||
|
|
|||
|
\s5
|
|||
|
\v 17 Tilas ku kiyaye wannan biki na gurasa marar gami saboda a wannan rana ce na fito da mutanenku, ƙungiya, ƙungiya na mayaƙa, daga cikin ƙasar Masar. Saboda haka tilas ku kiyaye wannan rana cikin dukkan tsararrakin mutanenku. Wannan a koyaushe zai zama shari'a a gare ku.
|
|||
|
\v 18 Tilas ku ci gurasa marar gami tun daga hasken asuba na ranar sha huɗu ga watan farko na shekara, har zuwa hasken asuba na ranar ashirin da ɗaya ga watan.
|
|||
|
|
|||
|
\s5
|
|||
|
\v 19 A lokacin waɗannan kwanaki bakwai, tilas kada a sami wani gami cikin gidajenku. Duk wanda ya ci gurasa da aka yi da gami tilas a datse shi daga cikin gundumar Isra'ila, koda wannan taliki baƙo ne ko kuma wanda aka haifa a cikin ƙasar.
|
|||
|
\v 20 Tilas ba zaku ci wani abin da akayi da gami ba. Duk inda kuka zauna, tilas ku ci gurasa da akayi ba tare da gami ba."'
|
|||
|
|
|||
|
\s5
|
|||
|
\v 21 Daga nan Musa ya yi sammace ga dukkan dattawan Isra'ila ya kuma ce masu, "Kuje ku zaɓi 'yan raguna ko 'yan awaki waɗanda za su isa ku ciyad da iyalanku sai ku kuma yanka su a matsayin ɗan ragon Ƙetarewa.
|
|||
|
\v 22 Daga nan sai ku ɗauki curin soso ku tsoma cikin jinin da zai kasance cikin kwano. Sai ku shafa jinin a bisa ginshiƙin ƙofa da dokin ƙofofi biyu. Kada waninku ya fita daga ƙofar gidansa har sai da safe.
|
|||
|
|
|||
|
\s5
|
|||
|
\v 23 Domin Yahweh zai ratsa ta ciki ya kai hari ga Masarawa. Idan yaga jinin a bisa ginshiƙin ƙofar da dokin ƙofa biyun, zai ƙetare ƙofarku kuma ba zai bada izini ga mai lalatarwa ba ya shigo cikin gidajenku ya kawo maku hari.
|
|||
|
|
|||
|
\s5
|
|||
|
\v 24 Tilas ku kiyaye wannan al'amari. Wannan a koyaushe zai zama shari'a domin ku da zuriyarku.
|
|||
|
\v 25 Idan kuka shiga ƙasar da Yahweh zai baku, kamar yadda ya yi alƙawari zai yi, tilas ku kiyaye wannan aikin sujada.
|
|||
|
|
|||
|
\s5
|
|||
|
\v 26 Idan 'ya'yanku suka tambaye ku, 'Mene ne ma'anar wannan aikin sujada?'
|
|||
|
\v 27 daganan tilas ku ce, 'hadayar Ƙetarewa ce ta Yahweh, saboda Yahweh ya ƙetare gidajen Isra'ilawa a Masar sa'ad da ya kai hari ga Masarawa. Ya 'yantar da gidajenmu."' Daga nan mutanen suka rusuna suka kuma yi sujada ga Yahweh.
|
|||
|
\v 28 Isra'ilawa suka tafi suka yi dai-dai yadda Yahweh ya umarci Musa da Haruna.
|
|||
|
|
|||
|
\s5
|
|||
|
\v 29 Ya kuwa faru a tsakar dare Yahweh ya kai hari ga dukkan 'ya'yan fãri dake cikin ƙasar Masar, daga ɗan fãrin Fir'auna, wanda ya zauna bisa kursiyi, har ya zuwa ɗan fãrin talikin dake cikin kurkuku da dukkan 'ya'yan fãrin dabbobi.
|
|||
|
\v 30 Fir'auna ya tashi da dare - shi, dukkan bayinsa, da dukkan masarawa. Akwai makoki mai ƙara a Masar, domin babu wani gida inda ba wanda ba a rasa wani da ya mutu ba.
|
|||
|
|
|||
|
\s5
|
|||
|
\v 31 Fir'auna ya yi sammace ga Musa da Haruna da dare ya kuma ce, "Ku tashi, ku fita daga cikin mutanena, ku da Isra'ilawa. Ku tafi, kuyi sujada ga Yahweh, kamar yadda kuka ce kuna so kuyi.
|
|||
|
\v 32 Ku ɗauki garken tumakinku dana awakinku da garken shanunku, kamar yadda kuka ce, ku kuma tafi, sai ku kuma albarkace ni."
|
|||
|
\v 33 Masarawa suna cikin babban hanzari su fitar dasu daga ƙasar, gama sun ce, "Dukkanmu zamu mutu."
|
|||
|
|
|||
|
\s5
|
|||
|
\v 34 Sai mutanen suka ɗauki ƙullinsu ba tare da sun ƙara wani gami ba. Kwanonin markaɗensu sun riga sun ɗaure cikin kayansu da bisa kafaɗunsu.
|
|||
|
\v 35 Yanzu mutanen Isra'ila sun yi yadda Musa yace masu. Suka roƙi Masarawa domin kayayyakin azurfa, da kayayyakin zinariya, da sutura.
|
|||
|
\v 36 Yahweh yasa Masarawa ɗokin farantawa Isra'ilawa rai. Sai masarawa suka basu komai game da abin da suka roƙa. Ta wannan hanyar, Isra'ilawa suka washe Masarawa.
|
|||
|
|
|||
|
\s5
|
|||
|
\v 37 Isra'ilawa suka yi tafiya daga Remasis zuwa Sukkot. Lissafinsu kimanin mazaje 600,000, baya ga ƙarin mataye da yara.
|
|||
|
\v 38 Gaurayen taron waɗanda ba Isra'ilawa ba ma suka tafi tare da su, tare da garkunan tumaki da awaki da na shanu, babban lissafin dabbobi.
|
|||
|
\v 39 Suka gasa gurasa marar gami daga cikin ƙullin da suka kawo daga Masar. Ya zama marar gami ne saboda an kore su daga Masar ba zasu kuma yi jinkirin shirya abinci ba.
|
|||
|
\v 40 Isra'ilawa sun yi zama a cikin Masar har shekaru 430.
|
|||
|
|
|||
|
\s5
|
|||
|
\v 41 A ƙarshen shekaru 430, a dai-dai wannan rana, dukkan ƙungiyoyin mayaƙan Yahweh suka fita daga ƙasar Masar.
|
|||
|
\v 42 Wannan dare ne na tsayawa a faɗake, domin Yahweh ya fito da su daga ƙasar Masar. Wannan daren Yahweh ne da za a kiyaye ga dukkan Isra'ilawa cikin dukkan tsararrakin mutanensu.
|
|||
|
|
|||
|
\s5
|
|||
|
\v 43 Yahweh ya cewa Musa da Haruna, "Wannan ne ka'ida domin Ƙetarewa: babu wani bare da mai yiwuwa yaci daga cikin sa.
|
|||
|
\v 44 Duk da haka, kowanne bawan Ba-isra'ile, da aka sawo da kuɗi, yana iya ci bayan kun yi masa kaciya.
|
|||
|
|
|||
|
\s5
|
|||
|
\v 45 Bare da bayin haya tilas ba za su ci wani daga cikn abincin ba.
|
|||
|
\v 46 Tilas a ci abincin cikin gida ɗaya. Tilas ba za ku ɗauki wani daga cikin abincin ba ku fita da shi waje, tilas kuma ba za ku karya wani ƙashi ba daga cikin sa.
|
|||
|
|
|||
|
\s5
|
|||
|
\v 47 Dukkan gundumar Isra'ila tilas su kiyaye wannan biki.
|
|||
|
\v 48 Idan bare yana zaune tare daku kuma yana so ya kiyaye Ƙetarewar ga Yahweh, dukkan danginsa maza tilas a yi masu kaciya. Daga nan zai yiwu su zo su kuma kiyaye shi. Zai zama kamar mutanen da aka haifa cikin ƙasar, Duk da haka, babu wani taliki marar kaciya da mai yiwuwa ya ci wani abu daga cikin abincin.
|
|||
|
|
|||
|
\s5
|
|||
|
\v 49 Wannan irin dokar za a zartar ga haifaffen garin da kuma bare dake zaune cikin ku.
|
|||
|
\v 50 Sai dukkan Isra'ilawa suka yi dai-dai yadda Yahweh ya umarci Musa da Haruna.
|
|||
|
\v 51 Sai ya kasance a dai-dai wannan rana ce Yahweh ya fito da Isra'ila daga ƙasar Masar a ƙungiyoyin mayaƙansu.
|
|||
|
|
|||
|
\s5
|
|||
|
\c 13
|
|||
|
\cl Sura 13
|
|||
|
\p
|
|||
|
\v 1 Yahweh ya yi magana da Musa ya kuma ce,
|
|||
|
\v 2 "Ka keɓe mani dukkan 'ya'yan fãri, kowanne ɗan fãri namiji daga cikin Isra'ilawa, duk da na mutane da dabbobi. 'Ya'yan fãrin nawa ne."
|
|||
|
|
|||
|
\s5
|
|||
|
\v 3 Musa ya cewa mutanen, "Ku tuna da wannan rana, ranar da kuka fito daga Masar, daga gidan bauta, domin ta hannun Yahweh mai ƙarfi ya fito daku daga nan wurin. Babu wata gurasa mai gami da zai yiwu a ci.
|
|||
|
\v 4 Za ku fita daga Masar a wannan ranar, a cikin watan Abib.
|
|||
|
\v 5 Sa'ad da Yahweh ya kawo ku cikin ƙasar Kan'aniyawa, da Hittiyawa, da Amoriyawa, da Hibbiyawa, da kuma Yebusiyawa, ƙasar da ya rantse wa kakanninku zai baku, ƙasar dake malala da madara da zuma - daganan tilas ku kiyaye wannan aikin sujada a cikin wannan watan.
|
|||
|
|
|||
|
\s5
|
|||
|
\v 6 Gama kwanaki bakwai tilas za ku ci gurasa marar gami; a ranar kwana na bakwai za ayi bikin girmama Yahweh.
|
|||
|
\v 7 Gurasa marar gami tilas za a ci cikin dukkan kwanakin bakwai; babu wata gurasa mai gami da zai yiwu a gani a cikin ku. Babu wani gami da zai yiwu a gani tare daku a cikin kowanne kan iyakokinku.
|
|||
|
|
|||
|
\s5
|
|||
|
\v 8 A wannan rana zaku cewa 'ya'yanku, 'Wannan saboda abin da Yahweh ya yi domina ne sa'ad da na fito daga Masar.'
|
|||
|
\v 9 Wannan zai zama abin tunawa domin ka a bisa hannu, abin tunawa kuma a bisa goshi. Wannan saboda shari'ar Yahweh ta kasance a bakinka, domin tare da hannu mai ƙarfi Yahweh ya fito da kai daga Masar.
|
|||
|
\v 10 Saboda haka tilas ka kiyaye wannan shari'a a lokacin da aka zaɓa daga shekara zuwa shekara.
|
|||
|
|
|||
|
\s5
|
|||
|
\v 11 Sa'ad da Yahweh ya kawo ku cikin ƙasar Kan'aniyawa, kamar yadda ya rantse maku da kakanninku zai yi, kuma sa'ad da ya bayar da ƙasar a gare ku,
|
|||
|
\v 12 tilas ku keɓe ga Yahweh kowanne yaro ɗan fãri da ɗan farko na dabbobinku. Mazajen dukka za su zama na Yahweh.
|
|||
|
\v 13 Kowanne ɗan fãrin jaki tilas ku saye shi da ɗan rago. Idan baku saye shi ba, daga nan tilas ku karya wuyansa. Amma kowanne ɗan fãri namiji daga cikin dukkan 'ya'yanku maza - tilas ku sake sayen su.
|
|||
|
|
|||
|
\s5
|
|||
|
\v 14 Idan ɗan ka yayi maka tambaya daga bisani, 'Mene ne ma'anar wannan?' Daga nan sai ka gaya ma shi, 'Ta wurin hannun Yahweh mai ƙarfi ne aka fito damu daga Masar, daga gidan bauta.
|
|||
|
\v 15 Sa'ad da Fir'auna da taurin kai ya ƙi ya bar mu mu tafi, Yahweh ya kashe dukkan 'ya'yan fãri na ƙasar Masar, duk da 'ya'yan fãrin mutane da 'ya'yan fãrin dabbobi. Shi ya sa nake hadaya ga Yahweh na ɗan fãri namiji na kowacce dabba, shi yasa kuma nake sake sayen 'ya'yan fãri na mazaje.'
|
|||
|
\v 16 Wannan zaya zama abin tunawa a hannunku, abin tunawa kuma a bisa goshinku, domin ta hannu mai ƙarfi Yahweh ya fito damu daga Masar."
|
|||
|
|
|||
|
\s5
|
|||
|
\v 17 Sa'ad da Fir'auna ya bar mutanen su tafi, Allah bai bida su ta hanyar ƙasar Filistiyawa ba, koda yake wannan ƙasar tana kurkusa. Domin Allah yace, "Watakila mutanen za su canza ra'ayinsu sa'ad da suka fuskanci yaƙi daganan kuma su koma Masar."
|
|||
|
\v 18 Sai Allah ya bi da mutanen su kewaya ta cikin jeji zuwa Tekun Iwa. Isra'ilawa suka fita daga ƙasar Masar shirye domin yaƙi.
|
|||
|
|
|||
|
\s5
|
|||
|
\v 19 Musa ya ɗauki ƙasusuwan Yosef tare da shi, domin Yosef yasa Isra'ilawa suka yi rantsuwa ya kuma ce, "Babu shakka Allah zai ceto ku, kuma tilas ku ɗauke ƙasusuwana tare daku."
|
|||
|
\v 20 Isra'ilawa suka yi tafiya daga Sukkot suka kuma yi sansani a Itam a bisa gaɓar jeji.
|
|||
|
\v 21 Yahweh ya shiga gabansu da rana ta inuwar girgije domin ya bida su ta hanyar da zasu bi. Da dare ya tafi ta inuwar wuta domin ya basu haske. Ta wannan hanyar suna iya tafiya da rana da kuma dare.
|
|||
|
\v 22 Yahweh bai ɗauke kuma daga gaban mutanen da rana inuwar girgije ba da dare kuma inuwar wuta ba.
|
|||
|
|
|||
|
\s5
|
|||
|
\c 14
|
|||
|
\cl Sura 14
|
|||
|
\p
|
|||
|
\v 1 Daga nan Yahweh ya yi magana da Musa, cewa,
|
|||
|
\v 2 "Ka gaya wa Isra'ilawa cewa su juya su kuma yi sansani kafin Fi Hahirot, tsakanin Magdol da teku, kafin Ba'al Zifon. Za ku yi sansani a gefen teku akasi da Fi Hahirot.
|
|||
|
\v 3 Fir'auna zai ce game da Isra'ilawa, 'Su na yawo a cikin ƙasar. Jeji ya rufe bisan su.'
|
|||
|
|
|||
|
\s5
|
|||
|
\v 4 Zan taurare zuciyar Fir'auna, kuma zai runtume su. Zan sami girmamawa saboda Fir'auna da dukkan mayaƙansa. Masarawa zasu sani cewa Ni ne Yahweh." Sai Isra'ilawa suka yi sansani kamar yadda aka umarce su.
|
|||
|
\v 5 Sa'ad da aka gaya wa sarkin Masar cewa Isra'ilawa sun tsere, sai ra'ayin Fir'auna da bayinsa suka juya gãba da mutanen. Suka ce, "Me muka yi? Mun saki Isra'ila daga bauta ma na?"
|
|||
|
|
|||
|
\s5
|
|||
|
\v 6 Daga nan sai Fir'auna ya shiryo karusansa ya kuma ɗauki mayaƙansa tare da shi.
|
|||
|
\v 7 Ya ɗauki zaɓaɓɓun karusai ɗari shidda da dukkan sauran karusan Masar, da shugabanni a bisa dukkansu.
|
|||
|
\v 8 Yahweh ya taurare zuciyar Fir'auna, sarkin Masar, sarkin kuma ya runtumi Isra'ilawa. Yanzu dai Isra'ilawa sun yi tafiyarsu cikin nasara.
|
|||
|
\v 9 Amma Masarawa suka runtume su, tare da dukkan dawakansa da karusai, mahayan dawakansa, da mayaƙansa. Suka sha kan Isra'ilawa da suka yi sansani a gefen teku a gefen Fi Hahirot, kafin Ba'al Zifon.
|
|||
|
|
|||
|
\s5
|
|||
|
\v 10 Sa'ad da Fir'auna ya iso kusa, Isra'ilawa suka duba sama suka kuma yi mamaki. Masarawa suna tattaki bayan su, suka kuma firgita. Isra'ilawa suka yi kuka ga Yahweh.
|
|||
|
\v 11 Suka ce wa Musa, "Saboda babu kaburbura ne a Masar, shi yasa ka ɗauko mu domin mu mutu a jeji? Meyasa ka yi haka da mu, ka fito da mu daga Masar?
|
|||
|
\v 12 Ba wannan muka gaya maka ba a Masar? Muka ce maka, 'Ka ƙyale mu, domin mu yiwa Masarawa aiki.' Ya gwammace mana muyi aiki domin su maimakon mu mutu cikin jeji."
|
|||
|
|
|||
|
\s5
|
|||
|
\v 13 Musa ya cewa mutanen, "Kada kuji tsoro. Ku tsaya cik ku kuma ga ceton da Yahweh zai wadata domin ku a yau. Domin ba zaku sake ganin Masarawan da kuka gani ba a yau.
|
|||
|
\v 14 Yahweh zai yi yaƙi domin ku, kuma tsayawa kawai za kuyi cik."
|
|||
|
|
|||
|
\s5
|
|||
|
\v 15 Daga nan Yahweh ya cewa Musa, "Meyasa kai, Musa, ka ke ci gaba da kira a gare ni? Ka gaya wa Isra'ilawa su tafi gaba.
|
|||
|
\v 16 Ka ɗaga sandarka, ka miƙa hannunka bisa tekun ka kuma raba ta biyu, saboda mutanen Isra'ila su bi ta tekun bisa busasshiyar ƙasa.
|
|||
|
\v 17 Ka sani cewa zan taurare zukatan Masarawa saboda su biyo bayansu. Zan sami daraja saboda Fir'auna da dukkan mayaƙansa, karusansa, da mahaya dawakansa.
|
|||
|
\v 18 Daga nan Masarawa zasu sani cewa Ni ne Yahweh sa'ad da Na samo daraja saboda Fir'auna, karusansa, da mahaya dawakansa."
|
|||
|
|
|||
|
\s5
|
|||
|
\v 19 Mala'ikan Allah, wanda ya tafi gaban Isra'ilawa, ya matsa ya kuma je bayansu. Inuwar girgijen ta matsa daga gabansu ta kuma koma ta tsaya bayansu.
|
|||
|
\v 20 Girgijen ya zo tsakanin sansanin Masar da sansanin Isra'ila. Girgije mai duhu ne ga Masarawa, amma ya haska daren domin Isra'ilawa, sai gefe ɗaya basu zo kusa da ɗayan ba dukkan dare.
|
|||
|
|
|||
|
\s5
|
|||
|
\v 21 Musa ya miƙar da hannunsa bisa tekun. Yahweh ya maida tekun baya da babbar iskar gabas dukkan wannan dare ya kuma maida tekun zuwa busasshiyar ƙasa. Ta haka ruwayen suka rabu.
|
|||
|
\v 22 Isra'ilawa suka tafi ta cikin teku bisa busasshiyar ƙasa. Ruwayen suka yi katanga domin su a hannun dama da hannun hagu.
|
|||
|
|
|||
|
\s5
|
|||
|
\v 23 / Masarawa suka runtume su. Suka tafi bayansu cikin tsakiyar teku - dukkan dawakan Fir'auna, da karusai, da mahaya dawakai.
|
|||
|
\v 24 Amma a sa'o'in farkon safiya, Yahweh ya duba ƙasa bisa mayaƙan Masarawa ta wurin umudin wuta da girgije. Ya sanya firgita tsakanin Masarawa.
|
|||
|
\v 25 Keken karusansu suka cije, mahayan dawakan suka yi tuƙi da wahala. Sai masarawa suka ce, "Bari mu tsere daga Isra'ila, gama Yahweh yana yaƙi domin su gãba da mu."
|
|||
|
|
|||
|
\s5
|
|||
|
\v 26 Yahweh ya cewa Musa, "Ka miƙar da hannunka bisa tekun domin ruwayen su dawo bisa Masarawa, karusansu, da mahaya dawakansu."
|
|||
|
\v 27 Sai Musa ya miƙar da hannunsa bisa tekun, kuma ya koma yadda ya ke da safiya ta bayyana. Masarawa suka tsere cikin teku, Yahweh kuma ya kora Masarawa zuwa cikin tsakiyarsa.
|
|||
|
\v 28 Ruwayen suka dawo suka rufe karusan Fir'auna, mahayan dawakai, da dukkan mayaƙansa dasu ka bi karusan zuwa cikin teku. Babu wanda ya tsira.
|
|||
|
|
|||
|
\s5
|
|||
|
\v 29 Duk da haka, Isra'ilawa suka yi tafiya bisa busasshiyar ƙasa cikin tsakiyar teku. Ruwayen suka zama katanga domin su a hannun damansu da hagunsu.
|
|||
|
\v 30 Sai Yahweh ya ceto Isra'ila a wannan rana daga hannun Masarawa, Isra'ila kuma suka ga matattun Masarawa bisa gaɓar teku.
|
|||
|
\v 31 Sa'ad da Isra'ila suka ga babban iko da Yahweh ya yi amfani da shi gãba da Masarawa, mutanen suka girmama Yahweh, suka kuma amince da Yahweh da kuma bawansa Musa.
|
|||
|
|
|||
|
\s5
|
|||
|
\c 15
|
|||
|
\cl Sura 15
|
|||
|
\p
|
|||
|
\v 1 Daga nan Musa da mutanen Isra'ila suka raira wannan waƙa ga Yahweh. Suka raira, "Zan raira ga Yahweh, gama ya yi ɗaukakakkiyar nasara; doki da mahayinsa ya watsar cikin teku.
|
|||
|
|
|||
|
\s5
|
|||
|
\v 2 Yahweh ne ƙarfina da waƙata, ya kuma zama mai cetona. Wannan ne Allahna, kuma zan yabe shi, Allah na mahaifina, zan kuma ɗaukaka shi.
|
|||
|
\v 3 Yahweh mayaƙi ne; Yahweh ne sunansa.
|
|||
|
|
|||
|
\s5
|
|||
|
\v 4 Ya watsar da karusan Fir'auna da mayaƙansa cikin teku. Zaɓaɓɓun hafsoshin Fir'auna sun nutse cikin Tekun Iwa.
|
|||
|
\v 5 Zurfafa sun rufe su; sun tafi ƙasa cikin zurfafa kamar dutse.
|
|||
|
|
|||
|
\s5
|
|||
|
\v 6 Hannunka na dama, Yahweh, ɗaukakakke ne cikin iko; hannunka na dama, Yahweh, ya rugurguza maƙiyi.
|
|||
|
\v 7 Cikin babban girma ka kayar da waɗanda suka taso gãba da kai. Ka aika da hasalarka; ta cinye su kamar haki.
|
|||
|
\v 8 Da hucin kafofin hancinka ruwaye suka jera; ruwayen dake malala suka tsaya tsaye suka yi tsibi; ruwa mai zurfi ya daskare a cikin zuciyar teku.
|
|||
|
|
|||
|
\s5
|
|||
|
\v 9 Maƙiyi yace, 'Zan runtuma, zan sha kai, zan rarraba ganima; marmarina zai ƙoshi a kansu; zan zaro takobina; hannuna zai hallakar dasu.'
|
|||
|
\v 10 Amma ka busa da iskarka, teku kuma ya rufe su; suka nutse kamar baƙin ƙarfe cikin manyan ruwaye.
|
|||
|
\v 11 Wane ne kamar ka, Yahweh, a tsakanin alloli? Wane ne kamar ka, girma cikin tsarki, daraja cikin yabo, mai aikata al'ajibai?
|
|||
|
|
|||
|
\s5
|
|||
|
\v 12 Ka miƙa hannun damanka, ƙasa kuma ta haɗiye su.
|
|||
|
\v 13 A cikin alƙawarin amincinka ka bida mutanen ka ceto su. A cikin ƙarfinka ka bida su zuwa wuri mai tsarki inda kake zaune.
|
|||
|
|
|||
|
\s5
|
|||
|
\v 14 Mutane zasu ji, zasu kuma yi rawar jiki; fargaba zai afko wa mazaunan Filistiya.
|
|||
|
\v 15 Daga nan shugabannin Idom zasu ji tsoro; sojojin Mowab zasu girgiza; dukkan mazaunan Kan'ana zasu narke.
|
|||
|
|
|||
|
\s5
|
|||
|
\v 16 Tsoro da fargaba zai fãɗo masu. Saboda ikon damtsenka, zasu tsaya cik kamar dutse har sai mutanenka sun wuce, Yahweh - har sai mutanen da ka ceto sun wuce.
|
|||
|
|
|||
|
\s5
|
|||
|
\v 17 Za ka kawo su ka dasa su bisa tsaunin gãdonka, wurin da, Yahweh, ka yi domin ka zauna a ciki, wuri mai tsarki, Ubangijinmu, wanda hannuwanka suka gina.
|
|||
|
\v 18 Yahwah zai yi mulki har abada abadin."
|
|||
|
|
|||
|
\s5
|
|||
|
\v 19 Gama dawakan Fir'auna suka tafi tare da karusansa da mahaya dawakansa cikin teku. Yahweh ya maido da ruwayen teku bisansu. Amma Isra'ilawa suka yi tafiya bisa busasshiyar ƙasa a tsakiyar teku.
|
|||
|
\v 20 Miriyam annabiya, 'yar'uwar Haruna, ta ɗauki kacau-kacau, dukkan mataye kuma suka fita da kacau-kacau, suna rawa tare da ita.
|
|||
|
\v 21 Miriyam ta raira masu waƙa: "Ku raira ga Yahweh, domin ya yi ɗaukakakkiyar nasara. Doki da mahayinsa ya jefar cikin teku."
|
|||
|
|
|||
|
\s5
|
|||
|
\v 22 Daga nan Musa ya bida Isra'ila gaba daga Tekun Iwa. Suka tafi zuwa cikin jejin Shur. Suka yi tafiya kwana uku cikin jeji basu kuma sami ruwa ba.
|
|||
|
\v 23 Daga nan suka iso Mara, amma basu iya shan ruwan wurin nan ba saboda yana da ɗaci. Sai suka kira sunan wannan wuri Mara.
|
|||
|
|
|||
|
\s5
|
|||
|
\v 24 Sai mutanen suka yi gunaguni ga Musa suka kuma ce, "Me zamu sha?"
|
|||
|
\v 25 Musa ya yi kuka ga Yahweh, sai Yahweh ya nuna masa wani itace. Musa ya jefa shi cikin ruwan, ruwan kuma ya zama da daɗin sha. A wannan wurin ne Yahweh ya basu shari'a mai tsauri, a wannan wurin ne kuma ya gwada su.
|
|||
|
\v 26 Ya ce, "Idan a hankali kuka saurari muryar Yahweh Allahnku, kuka kuma yi abin dake dai-dai a idanunsa, idan kuma kuka kasa kunne ga umarninsa kuka kuma yi biyayya da dukkan shari'unsa - ba zan sanya maku ko ɗaya daga cikin cututtukan dana sanya wa Masarawa ba, gama Ni ne Yahweh dake warkar da ku."
|
|||
|
|
|||
|
\s5
|
|||
|
\v 27 Daga nan mutanen suka iso Elim, inda akwai maɓuɓɓugan ruwa sha biyu da itatuwan dabino saba'in. Suka yi sansani a nan bakin ruwa.
|
|||
|
|
|||
|
\s5
|
|||
|
\c 16
|
|||
|
\cl Sura 16
|
|||
|
\p
|
|||
|
\v 1 Mutanen suka kama hanya daga Elim, kuma dukkan taron jama'ar Isra'ila suka iso jejin Sin, wanda ke tsakanin Elim da Sinai, a ranar sha biyar ga watan biyu bayan barowarsu daga ƙasar Masar.
|
|||
|
\v 2 Dukkan taron jama'ar Isra'ila suka yi gunaguni gãba da Musa da Haruna a cikin jejin.
|
|||
|
\v 3 Isra'ilawa suka ce masu, "Da ma kawai mun mutu ta hannun Yahweh a ƙasar Masar sa'ad da muke zama gefen tukwanen nama muke kuma cin gurasa mu ƙoshi. Domin ka fito da mu cikin wannan jeji ka kashe dukkan taron jama"armu da yunwa."
|
|||
|
|
|||
|
\s5
|
|||
|
\v 4 Daga nan Yahweh ya cewa Musa, "Zan yi ruwan gurasa daga sama domin ku. Mutanen zasu fita su tattaro ta yini ɗaya kowacce rana saboda in gwada su in gani ko zasu yi ko kuwa ba zasu yi tafiya cikin shari'a ta ba.
|
|||
|
\v 5 Za ya kasance a rana ta shida, zasu tattaro riɓi biyu na yawan yadda suke tattarawa kowacce rana a baya, sai kuma su dafa abin da suka ɗebo."
|
|||
|
|
|||
|
\s5
|
|||
|
\v 6 Daga nan Musa da Haruna suka cewa dukkan mutanen Isra'ila, "Da maraice zaku sani cewa Yahweh ne ya fito da ku daga ƙasar Masar.
|
|||
|
\v 7 Da safe zaku ga ɗaukakar Yahweh, domin ya ji gunaguninku gãba da shi. Mu su wane ne da zaku yi gunaguni gãba da mu?"
|
|||
|
\v 8 Musa ya sake cewa, "Zaku san wannan sa'ad da Yahweh ya baku nama da maraice da gurasa da safe ku ƙoshi - domin ya ji gunagunan da kuka furta gãba da shi. Su wane ne Haruna da ni? Gunagunanku ba gãba damu ba ne; gãba da Yahweh ne."
|
|||
|
|
|||
|
\s5
|
|||
|
\v 9 Musa ya cewa Haruna, "Ka cewa dukkan taron jama'ar mutanen Isra'ila, 'Ku zo kusa a gaban Yahweh, domin ya ji gunagunanku."'
|
|||
|
\v 10 Sai ya kasance, yayin da Haruna yake magana da dukkan taron jama'ar mutanen Isra'ila, sai suka kalli zuwa jeji, kuma, duba, ɗaukakar Yahweh ta bayyana a girgije.
|
|||
|
\v 11 Daga nan Yahweh ya yi magana da Musa, cewa,
|
|||
|
\v 12 "Na ji gunagunan mutanen Isra'ila. Ka yi magana dasu ka ce, 'Da maraice zaku ci nama, da safe kuma zaku cika da gurasa. Daga nan zaku sani cewa Ni ne Yahweh Allahnku."'
|
|||
|
|
|||
|
\s5
|
|||
|
\v 13 Sai ya kasance da maraice makwarwai suka taso suka rufe sansanin. Da safe raɓa ta kwanta kewaye da sansanin.
|
|||
|
\v 14 Da raɓar ta tafi, a nan birbishin jejin sai ga wasu falle-falle kamar dusar ƙanƙara a ƙasa.
|
|||
|
\v 15 Sa'ad da mutanen Isra'ila suka gan ta, suka ce da juna, "Mene ne wannan?" Ba su san ko mene ne ba. Musa yace masu, "Gurasar da Yahweh ya baku ce ku ci.
|
|||
|
|
|||
|
\s5
|
|||
|
\v 16 Wannan ne umarnin da Yahweh ya bayar: 'Tilas ku tattaro, kowannen ku, adadin da kuke buƙata ku ci, awon kowanne taliki bisa ga lissafin mutanenku. Ga yadda zaku tattara ta: Ku tattara isasshe domin ci ga kowanne taliki dake zaune a rumfarku."'
|
|||
|
\v 17 Mutanen Isra'ila suka yi haka. Wasu suka tãra da yawa, wasu suka tãra kaɗan.
|
|||
|
\v 18 Sa'ad da suka auna da awon gwangwani, waɗanda suka tãra da yawa basu rage komai ba, waɗanda kuma suka tãra kaɗan basu rasa komai ba. Kowanne taliki ya tãra dai-dai da biyan buƙatarsu.
|
|||
|
|
|||
|
\s5
|
|||
|
\v 19 Daga nan Musa yace masu, "Dole ba wanda zai bar komai daga cikin ta har safiya."
|
|||
|
\v 20 Duk da haka, basu saurari Musa ba. Waɗansu suka rage daga cikin ta har safiya, sai ta haifar da tsutsotsi ta kuma yi wãri. Daga nan Musa ya fusata da su.
|
|||
|
\v 21 Suka tattara ta safiya bayan safiya. Kowanne taliki ya tãra isassar wanda zai ci domin wannan ranar. Sa'ad da rana ta yi zafi, ta narke.
|
|||
|
|
|||
|
\s5
|
|||
|
\v 22 Sai ya kasance a rana ta shida kowannensu ya tãra riɓi biyu na gurasar, gwangwani biyu domin kowanne taliki. Dukkan shugabannin jama'ar suka zo suka faɗi wa Musa.
|
|||
|
\v 23 Ya ce masu, "Wannan ne abin da Yahweh yace: 'Gobe hutun nadama ne, Asabar mai tsarki cikin girmama Yahweh. Ku gasa abin da kuke so ku gasa, ku kuma dafa abin da kuke so ku dafa. Duk abin da ya rage, sai ku ajiye shi gefe domin kanku har sai da safe."'
|
|||
|
|
|||
|
\s5
|
|||
|
\v 24 Sai suka ajiye ta gefe har sai da safe, kamar yadda Musa ya bada umarni. Ba ta zama da wãri ba, ko kuma a sami wata tsutsa a cikinta.
|
|||
|
\v 25 Musa yace, "Ku ci wannan abin cin yau, domin yau rana ce wadda aka keɓe a matsayin Asabaci na girmama Yahweh. Yau ba zaku same ta ba a gonaki.
|
|||
|
|
|||
|
\s5
|
|||
|
\v 26 Zaku tattara ta cikin kwanaki shida, amma rana ta bakwai Asabaci ce. A ranar Asabar babu manna."
|
|||
|
\v 27 Sai ya kasance a rana ta bakwai waɗansu mutane suka fita su tattaro manna, amma ba su sami komai ba.
|
|||
|
|
|||
|
\s5
|
|||
|
\v 28 Daga nan Yahweh ya cewa Musa, "Har yaushe zaku ƙi kiyaye umarnai na da shari'u na?
|
|||
|
\v 29 Duba, Yahweh ya baku Asabaci. Don haka a rana ta shida yana baku gurasa domin kwanaki biyu. Kowannen ku tilas ya tsaya a wurinsa; tilas babu wanda zai fita daga wurin shi a rana ta bakwai."
|
|||
|
\v 30 Sai mutanen suka huta a rana ta bakwai.
|
|||
|
|
|||
|
\s5
|
|||
|
\v 31 Mutanen Isra'ila suka kira wannan abinci "Manna." Ita fara ce kamar tsabar riɗi, ɗanɗanon ta kuma kamar wainar da aka yi da zuma.
|
|||
|
\v 32 Musa yace, "Wannan ne Yahweh ya umarta: 'A ajiye gwangwanin manna cikin dukkan tsararrakin mutanenku saboda zuriyarku su ga gurasar dana ciyar da ku a jeji, bayan da na fito daku daga ƙasar Masar."'
|
|||
|
|
|||
|
\s5
|
|||
|
\v 33 Musa ya cewa Haruna, "Ka ɗauki tukunya ka sa gwangwani ɗaya na manna a cikin ta. Ka adana ta gaban Yahweh domin a ajiye ta cikin dukkan tsararrakin mutanen."
|
|||
|
\v 34 Kamar yadda Yahweh ya umarci Musa, Haruna ya ɓoye ta bayan alƙawarin dokoki a cikin akwatin alƙawari.
|
|||
|
\v 35 Mutanen Isra'ila suka ci manna shekaru arba'in har sai da suka zo ƙasar dake da mazauna. Ita suka ci har sai da suka zo kan iyakokin ƙasar Kan'ana.
|
|||
|
\v 36 Yanzu dai gwangwanin kashi ɗaya ne cikin goma na mudu.
|
|||
|
|
|||
|
\s5
|
|||
|
\c 17
|
|||
|
\cl Sura 17
|
|||
|
\p
|
|||
|
\v 1 Ɗaukacin taron jama'ar Isra'ilawa suka yi tafiya daga jejin Sin, biye da umarnan Yahweh. Suka yi sansani a Refidim, amma babu ruwa domin mutane su sha.
|
|||
|
\v 2 Sai mutanen suka ba Musa laifi saboda halin da suke ciki suka kuma ce, "Ka ba mu ruwa mu sha." Musa yace, "Meyasa kuke faɗa da ni? Meyasa kuke gwada Yahweh?"
|
|||
|
\v 3 Mutanen suna jin ƙishi sosai, suka kuma yi gunaguni gãba da Musa. Suka ce, "Meyasa ka fito da mu daga Masar? Don ka kashe mu da 'ya'yanmu da kuma dabbobinmu da ƙishi?"
|
|||
|
|
|||
|
\s5
|
|||
|
\v 4 Daga nan Musa ya yi kuka ga Yahweh, "Me zanyi da waɗannan mutanen? Sun kusa shirya jifa na."
|
|||
|
\v 5 Yahweh ya cewa Musa, "Ka tafi gaba da mutanen, ka tafi kuma tare da wasu dattawan Isra'ila. Ka ɗauki tare da kai sandar daka buga kogi, ka kuma tafi.
|
|||
|
\v 6 Zan tsaya a gabanka can a dutsen Horeb, zaka kuma bugi n. Ruwa zai fito daga cikin sa domin mutanen su sha." Daga nan Musa ya yi haka a gaban dattawan Isra'ila.
|
|||
|
\v 7 Ya kira wannan wuri Massa da Meriba saboda gunagunin Isra'ilawa, saboda kuma sun gwada Ubangiji ta wurin cewa, "Yahweh yana cikinmu ko a'a?"
|
|||
|
|
|||
|
\s5
|
|||
|
\v 8 Daga nan mayaƙan mutanen Amalekawa suka fita suka kuma kai hari ga Isra'ila a Refidim.
|
|||
|
\v 9 Sai Musa ya cewa Yoshuwa, "Ka zaɓi wasu mutane ka fita. Ka yi faɗa da Amalekawa. Gobe zan tsaya bisa tudu tare da sandar Allah a hannuna."
|
|||
|
\v 10 Sai Yoshuwa ya yi faɗa da Amalekawa kamar yadda Musa ya umarta, yayin da Musa, Haruna, da Hor suka hau saman tudu.
|
|||
|
|
|||
|
\s5
|
|||
|
\v 11 Yayin da Musa ke riƙe da hannayensa sama, Isra'ila suna nasara; idan ya sauke hannayensa su huta, sai Amalekawa su fãra yin nasara.
|
|||
|
\v 12 Sa'ad da hannayen Musa suka zama da nauyi, Haruna da Hor suka ɗauki dutse suka sanya ƙasansa domin ya zauna a kai. A dai-dai wannan lokaci, Haruna da Hor suka riƙe hannayensa sama, mutum ɗaya a gefensa ɗaya, mutum ɗaya kuma a ɗayan gefensa. Haka aka riƙe hannayen Musa a tallafe har faɗuwar rana.
|
|||
|
\v 13 Haka Yoshuwa ya kayar da mutanen Amalekawa da takobi.
|
|||
|
|
|||
|
\s5
|
|||
|
\v 14 Yahweh ya cewa Musa, "Ka rubuta wannan cikin littafi ka kuma karanta shi cikin kunnuwan Yoshuwa, saboda da zan share tunawa da Amalekawa kakaf daga ƙarƙashin sammai."
|
|||
|
\v 15 Daga nan Musa ya gina bagadi ya kira shi "Yahweh ne tuta ta."
|
|||
|
\v 16 Ya ce, "Gama an ɗaga hannu sama zu wa kursiyin Yahweh - cewa Yahweh zai ja dagar yaƙi da Amalekawa daga tsara zuwa tsara."
|
|||
|
|
|||
|
\s5
|
|||
|
\c 18
|
|||
|
\cl Sura 18
|
|||
|
\p
|
|||
|
\v 1 Yetro, firist na Midiyan, surukin Musa, ya ji dukkan abin da Allah ya yi domin Musa domin kuma Isra'ila mutanensa. Ya ji cewa Yahweh ya fito da Isra'ila daga Masar.
|
|||
|
\v 2 Yetro, surukin Musa, ya ɗauki Ziffora, matar Musa, bayan da ya tura ta gida,
|
|||
|
\v 3 da 'ya'yanta maza biyu; sunan ɗan ɗaya Gashom, domin Musa yace, "Na zama baƙo a baƙuwar ƙasa."
|
|||
|
\v 4 Sunan ɗayan Eliyeza, domin Musa yace, "Allah na kakannina ne taimako na. Ya cece ni daga takobin Fir'auna."
|
|||
|
|
|||
|
\s5
|
|||
|
\v 5 Yetro, surukin Musa, ya zo tare da 'ya'yan Musa da matarsa a wurin Musa a cikin jeji inda ya yi sansani a tsaunin Allah.
|
|||
|
\v 6 Ya cewa Musa, "Ni, surukinka Yetro, ina zuwa tare da matarka da 'ya'yanta maza biyu."
|
|||
|
|
|||
|
\s5
|
|||
|
\v 7 Musa ya tafi domin ya tarbi surukinsa, ya rusuna ƙasa, ya kuma sumbace shi. Suka tambayi lafiyar juna daganan kuma suka tafi cikin rumfa.
|
|||
|
\v 8 Musa ya gaya wa surukinsa dukkan abin da Yahweh ya yi wa Fir'auna da Masarawa saboda Isra'ila, game da dukkan wahalhalun da suka afko masu a kan hanya, da yadda Yahweh ya cece su.
|
|||
|
|
|||
|
\s5
|
|||
|
\v 9 Yetro ya yi farinciki game da dukkan nagartar da Yahweh ya yi wa Isra'ila, yadda ya cece su daga hannun Masarawa.
|
|||
|
\v 10 Yetro yace, "Bari a yabi Yahweh, domin ya cece ka daga hannun Masarawa daga kuma hannun Fir'auna, ya kuma kuɓutar da mutanen daga hannun Masarawa.
|
|||
|
\v 11 Yanzu na sani cewa Yahweh babba ne fiye da dukkan alloli, saboda sa'ad da Masarawa suka wulaƙanta Isra'ilawa da gadara, Allah ya ceci mutanensa."
|
|||
|
|
|||
|
\s5
|
|||
|
\v 12 Yetro, surukin Musa, ya kawo baikon ƙonawa da hadayu ga Allah. Haruna da dukkan dattawan Isra'ila suka zo su ci abinci a gaban Allah tare da surukin Musa.
|
|||
|
|
|||
|
\s5
|
|||
|
\v 13 Washegari Musa ya zauna domin yi wa mutane hukunci. Mutane suka tsaitsaya kewaye da shi daga safe har yamma.
|
|||
|
\v 14 Sa'ad da surukin Musa yaga dukkan abin da ya yi domin mutanen, ya ce, "Mene ne haka kake yi tare da mutanen?" Meyasa kake zaunawa kai kaɗai kuma dukkan mutanen ke tsayawa kewaye da kai daga safe har yamma?"
|
|||
|
|
|||
|
\s5
|
|||
|
\v 15 Musa ya cewa surukinsa, "Mutanen suna zuwa wurina ne su tambayi bishewar Allah.
|
|||
|
\v 16 Sa'ad da suka sami saɓani, suna zuwa wurina. Ina ɗaukar matsayi tsakanin taliki ɗaya da wani, kuma ina koyar da su farillan Allah da shari'unsa."
|
|||
|
|
|||
|
\s5
|
|||
|
\v 17 Surukin Musa yace masa, "Abin da kake yi bai da kyau sosai.
|
|||
|
\v 18 Tabbas zaka gajiyar da kanka, kai da mutanen dake tare da kai. Wannan ƙangi ya yi maka nauyi sosai. Ba zaka iya yin shi ba kai kaɗai.
|
|||
|
\v 19 Ka saurare ni. Zan baka shawara, kuma Allah zai kasance tare da kai, saboda kai ne a madadin mutane ga Allah, kuma kai ke kawo rikice-rikicensu gare shi.
|
|||
|
\v 20 Dole ka koya masu farillansa da shari'unsa. Dole ka nuna masu hanyar da zasu yi tafiya da kuma aikin da zasu yi.
|
|||
|
|
|||
|
\s5
|
|||
|
\v 21 Gaba da haka, dole ka zaɓi mutane tsayayyu daga cikin mutanen, mutane masu girmama Allah, mutane masu gaskiya masu ƙin ƙazamar riba. Dole ka sanya su bisa mutane su zama shugabannin dubbai, da ɗarurruka, da hamsin-hamsin, da goma-goma.
|
|||
|
\v 22 Za su yi hukunci tsakanin mutane a dukkan al'amuran yau da kullum, amma al'amura masu wuya sai su kawo maka. Game da dukkan ƙananan al'amura kuwa, zasu hukunta waɗannan da kansu. ta wannan hanyar zai yi maka sauƙi, za su kuma ɗauki nauyin tare da kai.
|
|||
|
\v 23 Idan ka yi wannan, idan kuma Allah ya umarce ka kayi haka, daganan zaka iya jurewa, kuma dukkan mutanen zasu iya tafiya gida a barace."
|
|||
|
|
|||
|
\s5
|
|||
|
\v 24 Sai Musa ya saurari maganganun surukinsa ya kuma yi dukkan abin da ya ce.
|
|||
|
\v 25 Musa ya zaɓi tsayayyun mutane daga dukkan Isra'ila ya kuma maida su shugabannin mutanen, shugabanni masu lura da dubbai, da ɗarurruka, da hamsin-hamsin, da goma-goma.
|
|||
|
\v 26 Suka hukunta mutane a al'amura masu sauƙi, al'amura masu wuya kuma suka kawo wa Musa, amma su da kansu suka hukunta dukkan ƙananan al'amura.
|
|||
|
\v 27 Daga nan Musa ya bar surukinsa ya tafi, Yetro kuma ya koma cikin ƙasarsa.
|
|||
|
|
|||
|
\s5
|
|||
|
\c 19
|
|||
|
\cl Sura 19
|
|||
|
\p
|
|||
|
\v 1 A cikin wata na uku bayan da mutanen Isra'ila suka fito daga ƙasar Masar, a wannan ranar, suka zo jejin Sinai.
|
|||
|
\v 2 Bayan da suka bar Refidim suka kuma zo jejin Sinai, suka yi sansani a jejin a gaban tsaunin.
|
|||
|
|
|||
|
\s5
|
|||
|
\v 3 Musa ya hau zuwa wurin Allah. Yahweh ya kira shi daga tsaunin ya kuma ce, "Tilas ka gaya wa gidan Yakubu, mutanen Israi'la;
|
|||
|
\v 4 Kunga yadda na yiwa Masarawa, yadda na ɗauko ku bisa fikafikan gaggafa na kuma kawo ku a gare ni.
|
|||
|
\v 5 To yanzu, idan da biyayya kuka saurari muryata kuka kuma kiyaye alƙawarina, daganan zaku zama mallakata ta musamman daga cikin dukkan mutane, domin dukkan duniya tawa ce.
|
|||
|
\v 6 Zaku zama masarautar firistoci da al'umma mai tsarki domina. Waɗannan maganganun ne tilas ka faɗe su ga mutanen Isra'ila."
|
|||
|
|
|||
|
\s5
|
|||
|
\v 7 Daga nan Musa ya zo ya sammaci shugabannin mutanen. Ya faɗi a gabansu dukkan waɗannan maganganun da Yahweh ya umarce shi.
|
|||
|
\v 8 Dukkan mutanen suka amsa tare suka ce, "Za muyi dukkan abin da Yahweh yace." Daga nan Musa ya zo ya kawo rahoton maganganun mutanen ga Yahweh.
|
|||
|
\v 9 Yahweh ya cewa Musa, "Zan zo gare ka cikin girgije mai kauri saboda mutanen su iya ji sa'ad da zan yi magana tare da kai, su kuma gaskata da kai har abada." Daga nan Musa ya faɗi maganganun mutanen ga Yahweh.
|
|||
|
|
|||
|
\s5
|
|||
|
\v 10 Yahweh ya cewa Musa, "Ka tafi wurin mutanen. Yau da gobe Tilas ka keɓe su a gare ni. ka kuma sanya su su wanke tufafinsu.
|
|||
|
\v 11 Ku shirya domin rana ta uku, gama a rana ta uku Yahweh zai sauko bisa Tsaunin Sinai.
|
|||
|
|
|||
|
\s5
|
|||
|
\v 12 Tilas ka sanya kan iyakoki domin mutanen a dukkan kewayen tsaunin. Ka ce masu, 'Ku kula da cewa baku hau zuwa tsaunin ba koku taɓa kan iyakarsa. Duk wanda ya taɓa tsaunin tabbas za a kashe shi.'
|
|||
|
\v 13 Kada hannun wani ya taɓa irin wannan taliki. A maimako, babu shakka tilas za a jefe shi ko a harbe shi. Ko mutum ne ko dabba tilas a kashe shi. Sa'ad da aka busa ƙaho mai dogon amo, suna iya zuwa gindin tsaunin."
|
|||
|
|
|||
|
\s5
|
|||
|
\v 14 Daga nan Musa ya tafi ya gangara daga tsaunin zuwa ga mutanen. Ya keɓe mutanen ga Yahweh suka kuma wanke tufafinsu.
|
|||
|
\v 15 Ya cewa mutanen, "Ku shirya a rana ta uku; kada ku kusanci matayenku."
|
|||
|
|
|||
|
\s5
|
|||
|
\v 16 A rana ta uku, sa'ad da safiya ta yi, aka yi cida da wurge-wurgen walƙiya da girgije mai kauri a bisa tsaunin, da ƙarar kaho mai ƙarfi sosai. Dukkan mutanen dake cikin sansanin suka yi rawar jiki.
|
|||
|
\v 17 Musa ya fito da mutanen daga cikin sansanin su gamu da Allah, suka kuma tsaya a gindin tsaunin.
|
|||
|
\v 18 Tsaunin Sinai kuwa an lulluɓe shi ɗungum da hayaƙi saboda Yahweh ya sauko bisa kansa cikin wuta da hayaƙi. Hayaƙin kuwa ya yi sama kamar hayaƙin tanderu, tsaunin kuma gabaɗaya ya yi mummunar girgiza.
|
|||
|
|
|||
|
\s5
|
|||
|
\v 19 Da ƙarar ƙahon ta ci gaba da ƙaruwa bisa ƙaruwa, Musa ya yi magana, Allah kuma ya amsa masa da murya.
|
|||
|
\v 20 Yahweh ya sauko bisa Tsaunin Sinai, bisa ƙololuwar tsaunin, ya kuma sammaci Musa zuwa sama. Sai Musa ya haye sama.
|
|||
|
\v 21 Yahweh ya cewa Musa, "Ka gangara ka dokaci mutanen da kada su faso gareni su kalla, ko dayawa daga cikin su su hallaka.
|
|||
|
\v 22 Bari firistocin suma dake kusantata su keɓe kansu - su shirya kansu domin zuwa na - saboda kada in kai masu hari."
|
|||
|
|
|||
|
\s5
|
|||
|
\v 23 Musa ya cewa Yahweh, "Mutanen ba zasu iya zuwa har Tsaunin Sinai ba, domin ka dokace mu: 'Ku sanya kan iyakoki kewaye da tsaunin ku kuma keɓe shi ga Yahweh."'
|
|||
|
\v 24 Yahweh yace masa, "Tafi, ka gangara daga tsaunin, ka kuma kawo Haruna tare da kai, amma kada ka bar firistocin da mutanen su faso shingen su hawo zuwa gare ni, ko in kai masu hari."
|
|||
|
\v 25 Sai Musa ya gangara zuwa ga mutanen ya yi magana da su.
|
|||
|
|
|||
|
\s5
|
|||
|
\c 20
|
|||
|
\cl Sura 20
|
|||
|
\p
|
|||
|
\v 1 Allah ya furta dukkan waɗannan maganganu,
|
|||
|
\v 2 "Ni ne Yahweh Allahnku, wanda ya fito daku daga ƙasar Masar, daga gidan bauta.
|
|||
|
\v 3 Tilas ne ba zaku yi wasu alloli ba baya ga ni.
|
|||
|
|
|||
|
\s5
|
|||
|
\v 4 Ba zaku yi wa kanku sassaƙaƙƙen siffa ba ko kamannin wani abu dake can cikin sama, ko a ƙarƙashin ƙasa, ko a cikin ruwaye.
|
|||
|
\v 5 Dole ne ba zaku rusuna masu ba koku yi masu sujada, gama Ni, Yahweh Allahnku, Allah ne mai kishi. Ina horon muguntar kakanni ta wurin sauko da horo bisa zuriyarsu, har zuwa tsararraki na uku da na huɗu na waɗanda ke ƙi na.
|
|||
|
\v 6 Amma ina nu na alƙawarin aminci ga dubban waɗanda ke ƙaunata suke kuma kiyaye dokokina.
|
|||
|
|
|||
|
\s5
|
|||
|
\v 7 Dole ne ba zaku ɗauki sunan Yahweh Allahnku ba, a wofi, domin ba zan riƙe shi marar laifi ba duk wanda ya ɗauki sunana a wofi.
|
|||
|
|
|||
|
\s5
|
|||
|
\v 8 Ku tuna da ranar Asabaci, ku keɓe ta domina.
|
|||
|
\v 9 Dole kuyi aiki tuƙuru ku kuma yi dukkan aikinku a ranaku shida.
|
|||
|
\v 10 Amma rana ta bakwai Asabaci ce ga Yahweh Allahnku. A wannan rana baza kuyi wani aiki ba, koku, ko 'ya'yanku maza, ko 'ya'yanku mata, ko bayinku maza, ko bayinku mata, ko garken shanunku, ko baƙon da yake cikin ƙofofinku.
|
|||
|
\v 11 Domin a cikin ranaku shida Yahweh ya yi sammai da duniya, da teku, da dukkan abin dake cikin su, sai kuma ya huta a rana ta bakwai. Saboda haka Yahweh ya albarkaci ranar Asabaci ya kuma keɓe ta.
|
|||
|
|
|||
|
\s5
|
|||
|
\v 12 Ka girmama mahaifinka da mahaifiyarka, saboda ka rayu na dogon lokaci a cikin ƙasar da Yahweh Allahnka yake baka.
|
|||
|
\v 13 Tilas ba zaka kashe kowa ba.
|
|||
|
\v 14 Tilas ba zaka yi zina ba.
|
|||
|
|
|||
|
\s5
|
|||
|
\v 15 Tilas ne ba zaka yi sata ba daga wani.
|
|||
|
\v 16 Tilas ne ba zaka bada shaidar ƙarya ba gãba da maƙwabcinka.
|
|||
|
\v 17 Tilas ne ba zaka yi ƙyashin gidan maƙwabcinka ba; tilas ne ba zaka yi ƙyashin matar maƙwabcinka ba, bawansa namiji, baiwarsa mace, sansa, jakinsa, ko dukkan wani abu dake na maƙwabcinka."
|
|||
|
|
|||
|
\s5
|
|||
|
\v 18 Dukkan mutanen suka ga cidar da walƙiyar, suka kuma ji muryar ƙahon, suka kuma ga tsaunin na hayaƙi. Sa'ad da mutanen suka ga haka, suka firgice suka kuma tsaya daga nesa.
|
|||
|
\v 19 Suka cewa Musa, "Ka yi magana da mu, zamu kuma saurara; amma kada ka bari Allah ya yi magana da mu, ko kuwa za mu mutu."
|
|||
|
\v 20 Musa ya cewa Mutanen, "Kada kuji tsoro, domin Allah ya zo ya gwada ku saboda girmamawarsa ya kasance cikin ku, saboda kuma kada kuyi zunubi."
|
|||
|
\v 21 Sai mutanen suka tsaya nesa, Musa kuma ya kusanci duhun mai kauri inda Allah ya ke.
|
|||
|
|
|||
|
\s5
|
|||
|
\v 22 Yahweh ya cewa Musa, "Wannan ne tilas ka gayawa Isra'ilawa: 'Ku da kanku kunga cewa nayi magana da ku daga sama.
|
|||
|
\v 23 Kada ku yiwa kanku wasu alloli tare da ni, allolin azurfa ko allolin zinariya.
|
|||
|
|
|||
|
\s5
|
|||
|
\v 24 Tilas ku gina mani bagadin ƙasa, dole kuma ku yi hadayar baye-baye na ƙonawa a kansa, baye-baye na zumunta, tumaki, da shanu. A cikin dukkan inda nasa a girmama sunana, zan zo gare ku in albarkace ku.
|
|||
|
\v 25 Idan kuka yi mani bagadin dutse, ba zaku gina shi ba da dutsen da aka yanko, domin idan kuka yi amfani da kayan aikinku a kansa, kun riga kun gurɓata shi.
|
|||
|
\v 26 Tilas ne ba za ku hau bisa bagadina ta matakala ba, saboda kada tsirancinku ya bayyana."'
|
|||
|
|
|||
|
\s5
|
|||
|
\c 21
|
|||
|
\cl Sura 21
|
|||
|
\p
|
|||
|
\v 1 To waɗannan su ne sharuɗan da zaka sa a gabansu:
|
|||
|
|
|||
|
\s5
|
|||
|
\v 2 Idan ka sayi bawa Ba'ibrane, zai yi bauta shekara shida, a ta bakwai zai tafi 'yantacce ba tare da ya biya kome ba.
|
|||
|
\v 3 Idan shi kaɗai ya zo, sai ya tafi shi kaɗai, idan kuma ya zo da mata, zata zama 'yantarta ta tafi tare da shi.
|
|||
|
\v 4 Idan ubangijinsa ne ya yi masa aure, da matar da 'ya'yanta zasu zama na ubangijinsa, shi kuwa zai zama 'yantacce ya tafi shi kaɗai.
|
|||
|
|
|||
|
\s5
|
|||
|
\v 5 Amma idan bawan da kansa ya ce, "Ina ƙaunar ubangijina da matata da 'ya'yana; ba zan zama 'yantacce in tafi ba,"
|
|||
|
\v 6 Dole ubangijinsa ya kawo shi wurin Yahweh, dole ubangijinsa zai kawo shi ƙofa ko bakin ƙofa, kuma dole ubangijinsa zai huda kunnensa da allura. Daga nan zai zama bawa har iyakar rayuwarsa.
|
|||
|
|
|||
|
\s5
|
|||
|
\v 7 Idan mutum ya sayar da ɗiyarsa mace ta zama baiwa, ba zata tafi haka nan kamar yadda bayi maza suke yi ba.
|
|||
|
\v 8 Idan ba ta gamshi ubangijinta wanda ya ajiye ta domin kansa ba, to dole ne a fanshe ta. Ba zai sayar da ita ga waɗan su baƙin mutane ba. Ba shi da wannan damar saboda ya yaudare ta.
|
|||
|
|
|||
|
\s5
|
|||
|
\v 9 Idan ubangijinta ya bada ita ga ɗansa ta zama matarsa, sai ya ɗauke ta kamar ɗiyarsa.
|
|||
|
\v 10 Idan ya ɗauko wata matar, kada ya hana ta abinci ko tufafi ko kuwa 'yancinta na aure.
|
|||
|
\v 11 Amma idan bai ba ta waɗannan abubuwa uku ba, to sai ta tafi a matsayin 'yantarta, ba tare da ta biya wasu kuɗi ba.
|
|||
|
|
|||
|
\s5
|
|||
|
\v 12 Ko wane ne ya doki wani mutum har ya mutu, shima sai a kashe shi.
|
|||
|
\v 13 Idan mutumin bada manufa ya yi ba, amma ya yi da kuskure ne, zan tanada wurin da zai gudu.
|
|||
|
\v 14 Idan wani mutum ya kaiwa maƙwabcinsa hari, ya yaudare shi har ya kashe shi, zaka ɗauke shi, koda yana kan bagadin Yahweh, domin a kashe shi.
|
|||
|
|
|||
|
\s5
|
|||
|
\v 15 Dukkan wanda ya doki mahaifinsa ko mahaifiyarsa, dole za a kashe shi.
|
|||
|
\v 16 Dukkan wanda ya yi garkuwa da mutum - ko wanda ya yi garkuwa da mutumin ya sayar da shi, ko kuwa an same shi a hannun mai garkuwar - dole ne a kashe mai yin garkuwar.
|
|||
|
\v 17 Dukkan wanda ya zagi mahaifinsa ko mahaifiyarsa dole za a kashe shi.
|
|||
|
|
|||
|
\s5
|
|||
|
\v 18 Idan mutane suka yi faɗa, ɗaya ya bugi ɗayan da dutse ko ya naushe shi, kuma mutumin bai mutu ba, amma ya kwanta saboda dukan da ya yi masa;
|
|||
|
\v 19 idan mutumin ya samu ya tashi, har yana tafiya yana dogara sanda, shi wanda ya doke shi zai biya shi diyyar lokacin da ya ɓata; dole mutumin ya biya kuɗin jinyar sa har ya warke. Amma mutumin bai tserewa laifin kisan kai ba.
|
|||
|
|
|||
|
\s5
|
|||
|
\v 20 Idan mutum ya doki bawansa ko baiwarsa da sanda, har bawan ya mutu sanadiyar wannan duka, dole ne za a hori mutumin. Duk da haka,
|
|||
|
\v 21 idan bawan ya rayu kwana ɗaya ko biyu, ba za a hori mutumin ba, saboda ya sha wuyar rashin bawansa.
|
|||
|
|
|||
|
\s5
|
|||
|
\v 22 Idan mutane suka yi faɗa suka yi wa mace mai ciki rauni, har ta yi ɓari amma ba wani rauni a jikinta, mai laifin zai biya tara yadda mijinta ya bukata, dole ya biya abin da alƙali ya ce ya biya.
|
|||
|
\v 23 Amma idan akwai rauni mai muni, sai a bada rai maimakon rai,
|
|||
|
\v 24 ido maimakon ido, haƙori maimakon haƙiri, hannu naimakon hannu, ƙafa maimakon ƙafa,
|
|||
|
\v 25 ƙuna maimakon ƙuna, rauni maimakon rauni, ƙujewa maimakon ƙujewa.
|
|||
|
|
|||
|
\s5
|
|||
|
\v 26 Idan mutum ya bugi bawansa ko baiwarsa a ido har idon ya mutu, bawan zai zama 'yantacce ya tafi maimakon idonsa ko idonta.
|
|||
|
\v 27 Idan ya buge wa bawansa ko baiwarsa haƙori har ya cire, bawan ko baiwar zai zama 'yantacce ya tafi maimakon haƙorinsa ko haƙorinta.
|
|||
|
|
|||
|
\s5
|
|||
|
\v 28 Idan să ya soki mutum namiji ko mace har ya mutu, dole za a jejjefe san, kuma ba za a ci namansa ba; amma mai san zai zama baratacce.
|
|||
|
\v 29 Amma idan san ya kan soki mutane dama, kuma an yi wa mai san gargaɗi bai kuwa ɗaure san ba, idan san ya soki wani mutum ko wata mace har ga mutuwa, za a jejjefe san, mai san ɗin shima za a kashe shi.
|
|||
|
\v 30 Idan kuwa an ce a biya diyya domin ransa, to, dukkan abin da aka bukata a biya haka zai biya.
|
|||
|
|
|||
|
\s5
|
|||
|
\v 31 Idan san ya soki ɗan wani ko ɗiyar wani, mai san zai yi kamar yadda wannan ka'ida ta bukaci ya yi.
|
|||
|
\v 32 Idan san ya soki bawan wani mutum na miji ko mace, mai san zai biya azurfa talatin, san kuma za a jejjefe shi.
|
|||
|
|
|||
|
\s5
|
|||
|
\v 33 Idan mutum ya buɗe rami ko ya gina rami bai rufe shi ba, idan să ko jaki ya faɗa cikin sa,
|
|||
|
\v 34 wanda ya yi ramin zai biya diyya. Dole zai biya mai dabbar kuɗi, matacciyar dabbar kuma za ta zama asararsa.
|
|||
|
|
|||
|
\s5
|
|||
|
\v 35 Idan san wani ya yi wa san wani rauni har ya mutu, za a sayar da san mai rai sai su raba kuɗin, su kuma raba san wanda ya mutu.
|
|||
|
\v 36 Amma idan dama san ya saba yin haka, kuma an yiwa mai san gargaɗi amma bai ɗaure sansa ba, zai biya să maimakon să matacciyar dabbar kuma za ta zama ta sa.
|
|||
|
|
|||
|
\s5
|
|||
|
\c 22
|
|||
|
\cl Sura 22
|
|||
|
\p
|
|||
|
\v 1 Idan mutum ya saci bijimi ko tinkiya, ya kashe ko ya sayar, zai biya da bijimai biyar a kan bijimi ɗaya, ko tinkiya huɗu a kan tinkiya ɗaya.
|
|||
|
\v 2 Idan aka kama ɓarawo yana fasa gida, aka buge shi har ya mutu, ba za a kama kowa da laifin kisan kai a kansa ba.
|
|||
|
\v 3 Amma idan rana ta fito kamin ya fasa ya shiga, za a kama wanda ya kashe shi da laifin kisan kai. Dole ɓarawo ya biya diyya. Idan kuwa ba shi da komi, sai a sayar da shi saboda satar sa.
|
|||
|
\v 4 Idan an sami dabbar da ya sata a wurin sa, ko bijimi ne ko jaki ko tinkiya, dole ya biya riɓi biyu na abin da ya sata.
|
|||
|
|
|||
|
\s5
|
|||
|
\v 5 Idan mutum yana kiwo, ya bar dabbarsa ta kwance ta yi kiwo a gonar wani, dole ya biya diyya daga gonarsa mafi kyau ko daga garkarsa mafi kyau.
|
|||
|
|
|||
|
\s5
|
|||
|
\v 6 Idan wuta ta ƙwace ta shiga cikin ƙayoyi har ta tarar da hatsi, ko an girbe ko kuwa yana tsaye har ta cinye gonar, dole wanda ya kunna wutar ya biya diyya.
|
|||
|
|
|||
|
\s5
|
|||
|
\v 7 Idan mutum ya ba maƙwabcinsa ajiyar kuɗi ko kaya, sai aka sace abin a gidansa, idan aka kama ɓarawon dole zai biya diyyar abin da ya sata riɓi biyu.
|
|||
|
\v 8 Amma idan ba a kama ɓarawon ba, sai mai gidan ya zo wurin alƙali a gani ko ya ɗauki wani abu cikin kayan maƙwabcinsa.
|
|||
|
\v 9 Gama kowacce jayayya game da wani abu, ko bijimi ko jaki ko tinkiya ko kayan sawa, ko kowanne abin da ya ɓace wani ya ce, "Wannan nawa ne," dole a zo wurin alƙali da masu jayayyar. Wanda a ka samu da laifi zai biya maƙwabcinsa diyya riɓi biyu.
|
|||
|
|
|||
|
\s5
|
|||
|
\v 10 Idan mutum ya ba maƙwabcinsa ajiyar jaki ko bijimi ko tinkiya ko kowacce irin dabba, sai ta mutu ko aka ji mata rauni ko aka ɗauke ta ba wanda ya gan ta,
|
|||
|
\v 11 dole su biyun suyi rantsuwa domin a gane wani bai ɗauki kayan maƙwabcinsa ba. Sai mai abin ya yarda da haka kuma ɗayan ba zai biya diyya ba.
|
|||
|
\v 12 Amma idan sacewa aka yi, sai mutumin ya biya diyya ga mai shi.
|
|||
|
\v 13 Idan kuma an yayyaga dabbar ne, sai mutumin ya kawo dabbar shaida. Ba zai biya dabbar da aka yayyaga ba.
|
|||
|
|
|||
|
\s5
|
|||
|
\v 14 Idan mutum ya yi aron dabba a wurin maƙwabcinsa, sai aka yi wa dabbar rauni ko ta mutu ba a wurin mai ita ba, dole ɗaya mutumin ya biya diyya.
|
|||
|
\v 15 Amma idan dabbar tana wurin mai ita, ɗaya mutumin ba zai biya ba; idan hayar dabbar aka yi sai a biya kuɗin hayar.
|
|||
|
|
|||
|
\s5
|
|||
|
\v 16 Idan mutum ya ruɗi budurwa wadda ba a yi riƙon ta ba, har ya kwana da ita, dole yasa ta zama matarsa ta wurin biyan dukiya yadda aka bukaci ya biya.
|
|||
|
\v 17 Idan mahaifinta ya ƙi ba shi ita, to dole ya biya dukiya dai-dai da ta budurwa.
|
|||
|
|
|||
|
\s5
|
|||
|
\v 18 Dole ne ba zaka bar mayya ta rayu ba.
|
|||
|
\v 19 Dukkan wanda ya kwana da dabba dole za a kashe shi.
|
|||
|
|
|||
|
\s5
|
|||
|
\v 20 Dukkan wanda ya yi hadaya ga wani allah in ba Yahweh ba dole za a hallaka shi.
|
|||
|
\v 21 Dole ne ba zaku yi wa baƙo laifi ba ko kuwa ku ƙware shi, domin dă ku baƙi ne a Masar.
|
|||
|
|
|||
|
\s5
|
|||
|
\v 22 Kada ka wulaƙanta gwauruwa ko maraya.
|
|||
|
\v 23 Idan ka ƙware su, suka yi kira gare ni, babu shakka zan ji kiran su.
|
|||
|
\v 24 Fushina zai yi, ƙuna kuma zan kashe ka da kaifin takobi; matanka zasu zama gwauraye, 'ya'yanka kuma su zama marayu.
|
|||
|
|
|||
|
\s5
|
|||
|
\v 25 Idan ka bada rancen kuɗi cikin mutanena matalauta, kada ka zama kamar mai bada kuɗi da ruwa, ba zaka sa riba ba.
|
|||
|
\v 26 Idan ka karɓi rigar maƙwabcinka da alƙawari, dole ka dawo masa da ita kafin rana ta faɗi,
|
|||
|
\v 27 gama ita kaɗai ce abin rufarsa; ita ce rigar da zai sa jikinsa. Da me zai rufa? Sa'ad da ya kira gare ni, zan ji kiransa gama ni mai tausayi ne.
|
|||
|
|
|||
|
\s5
|
|||
|
\v 28 Kada ka yi mani saɓo, Allah, ko ka zagi mai mulkin mutanenka.
|
|||
|
|
|||
|
\s5
|
|||
|
\v 29 Kada ku hana baye-baye daga amfanin gonarku ko ruwan inabinku. Dole ku bani nunar fari ta 'ya'yanku.
|
|||
|
\v 30 Dole kuma ku yi haka da bijimanku da tumakinku. Gama kwana bakwai za su yi da iyayensu, a rana ta takwas za ku bada su gare ni.
|
|||
|
\v 31 Za ku zama mutane keɓaɓɓu gare ni. Kada ku ci kowanne abin da naman daji ya kashe a gona. Sai dai, ku jefa wa karnuka shi.
|
|||
|
|
|||
|
\s5
|
|||
|
\c 23
|
|||
|
\cl Sura 23
|
|||
|
\p
|
|||
|
\v 1 Kada ku ba da shaidar ƙarya game da wani. Kada ku haɗa kai da mai mugunta ku zama maƙaryatan shaidu.
|
|||
|
\v 2 Kada ku bi rububi domin ku yi mugunta, ko ku goyi bayan rububi ku yi shaida domin ku ɓata adalci.
|
|||
|
\v 3 Kada ku nuna wa matalauci fifiko idan a na yi ma sa shari'a ko kaɗan.
|
|||
|
|
|||
|
\s5
|
|||
|
\v 4 Idan ka gamu da bijimin maƙiyinka ko jakinsa ya ɓace, dole ka dawo masa da shi.
|
|||
|
\v 5 Idan ka ga jakin wanda yake ƙin ka ya faɗi, kaya ya danne shi, kada ka bar shi shi kaɗai. Dole ka taimake shi ka tada jakinsa.
|
|||
|
|
|||
|
\s5
|
|||
|
\v 6 Kada ka yar da adalci gefe sa'ad da ake yi wa matalaucinka shari'a.
|
|||
|
\v 7 Kada ka haɗa kai da waɗan su ku yi zargi a kan ƙarya, kada ku kashe marar laifi ko mai adalci, gama ba zan 'yantar da mai mugunta ba.
|
|||
|
\v 8 Kada ku karɓi toshi ko kaɗan, gama toshi ya kan sa masu gani su makance, ya hana maganar masu aminci aiki.
|
|||
|
\v 9 Kada ku cuci baƙo, da yake ka san rayuwar baƙo, gama da kuma baƙi ne a Masar.
|
|||
|
|
|||
|
\s5
|
|||
|
\v 10 Shekaru shida za ka shuka iri a gonakinka ka sami amfaninsa.
|
|||
|
\v 11 Amma a shekara ta bakwai za ka bar ta ba za ka noma ba, domin matalauta na cikin ku su ci abinci. Abin da suka rage namun daji za su ci. Haka kuma za ku yi da gonakinku da garkunan inabinku.
|
|||
|
|
|||
|
\s5
|
|||
|
\v 12 Cikin kwanaki shida za ku yi aiki, amma a rana ta bakwai dole za ku huta. Ku yi haka domin bijimanku da jakinku su huta, domin 'ya'yan bayinka da kowanne baƙo ya huta ya wartsake.
|
|||
|
\v 13 Ku yi lura da dukkan abin da na gaya maka. Kada ku ambaci sunayen waɗansu alloli, ko ku bari a ji sunayensu daga bakinku.
|
|||
|
|
|||
|
\s5
|
|||
|
\v 14 Dole ku je ku yi mani biki sau uku a kowacce shekara.
|
|||
|
\v 15 Za ku yi bikin gurasa marar gami. Kamar yadda na umurce ku, za ku ci gurasa marar gami kwana bakwai. A wannan lokaci, za ku zo gabana a watan Abib, wanda aka tsaida domin yin haka. A cikin wannan wata ne kuka fito daga Masar. Amma kada ku zo gabana hannu wofi.
|
|||
|
|
|||
|
\s5
|
|||
|
\v 16 Dole za ku yi Bikin Kaka, na nunar fari na irin da kuka shuka a gonakinku. Kuma dole ku yi Bikin Tattarawa a ƙarshen shekara, sa'ad da kuka tattara amfanin gonakinku gida.
|
|||
|
\v 17 Dole mazajenku dukka su zo gaban Ubangiji Yahweh sau uku a shekara
|
|||
|
|
|||
|
\s5
|
|||
|
\v 18 Dole ba za ku miƙa mani jinin hadayunku da gurasa wadda take da gami ba. Kitsen hadayun idodina ba zai wuce dukkan dare ya kai safiya ba.
|
|||
|
\v 19 Dole ku kawo zaɓaɓɓar nunar fari na gonakinku gidana, gidan Yahweh Allahnka. Ba za ka dafa 'yar burguma mai shan nonon uwarta ba.
|
|||
|
|
|||
|
\s5
|
|||
|
\v 20 Zan aiko da mala'ika ya yi maku jagora a kan hanya, ya kawo ku wurin da na shirya.
|
|||
|
\v 21 Ku saurare shi ku yi masa biyayya. Kada ku cakune shi domin ba zai gafarta laifofinku ba. Sunana yana kansa.
|
|||
|
\v 22 Idan kuka yi biyayya da muryarsa kuka yi dukkan abin da na faɗa maku, zan zama maƙiyi ga maƙiyanku in tayar wa masu tayar maku.
|
|||
|
|
|||
|
\s5
|
|||
|
\v 23 Mala'ikana zai shiga gabanku ya kawo ku wurin Amoriyawa da Hittiyawa da Firizziyawa da Kan'aniyawa da Hibiyawa da Yebusiyawa. Zan hallaka su.
|
|||
|
\v 24 Kada ku rusuna wa allolinsu, ku yi masu sujada, ko ku yi kamar yadda suke yi. Maimakon haka, dole ku kaɓantar da su dukka, ku ragargaza ginshiƙan duwatsunsu rugu--rugu.
|
|||
|
\v 25 Dole Yahweh Allahnku za ku yiwa sujada, kuma zai albarkaci gurasarku da ruwanku. Zan kawar da ciwo daga cikin ku.
|
|||
|
|
|||
|
\s5
|
|||
|
\v 26 Ba matar da za ta zama bakarariya ko ta yi ɓarin jariri a ƙasarku. Zan baku tsawancin kwana.
|
|||
|
\v 27 Zan sa tsoro a cikin waɗanda kuke shiga ƙasarsu. Zan kashe dukkan mutanen da kuka gamu da su. Zan sa dukkan maƙiyanku su juya maku baya a wurin yaƙi.
|
|||
|
\v 28 Zan aiko da zirnaƙo ya kori Hibiyawa da Kan'aniyawa da Hittiyawa daga gabanku.
|
|||
|
\v 29 Ba zan kore su a cikin shekara ɗaya ba domin kada ƙasar ta zama ba kowa, kada namun daji su yi maku yawa ƙwarai.
|
|||
|
|
|||
|
\s5
|
|||
|
\v 30 Maimakon haka zan kore su da kaɗan-kaɗan har ku yi yawa ku gaji ƙasar.
|
|||
|
\v 31 Zan sa iyakokinku daga Tekun Iwa zuwa Tekun Filistiyawa, kuma daga jejin Kogin Yuferatis. Zan baku nasara a kan dukkan mazunan ƙasar. Za ku kore su daga gabanku.
|
|||
|
\v 32 Kada ku yi amana da su koda allolinsu.
|
|||
|
\v 33 Kada su zauna a ƙasarku, domin kada su sa ku yi zunubi a gare ni. Idan kuka yi sujada ga allolinsu, babu shakka zai zama tarko a gare ku."'
|
|||
|
|
|||
|
\s5
|
|||
|
\c 24
|
|||
|
\cl Sura 24
|
|||
|
\p
|
|||
|
\v 1 Sa'an nan Yahweh yace da Musa, "Ku hawo wuri na-kai, da Haruna, da Nadab, da Abihu, da dattawa saba'in na Isra'ila, ku yi mani sujada daga nesa.
|
|||
|
\v 2 Musa kaɗai ne zai zo kusa da ni. Sauran ba zasu zo kusa ba, mutanen ba zasu hawo tare da shi ba."
|
|||
|
|
|||
|
\s5
|
|||
|
\v 3 Musa ya je ya faɗa wa mutanen Isra'ila dukkan maganganun Yahweh da farillai. Dukkan mutanen suka amsa da murya ɗaya suka ce, "Za mu yi dukkan abin da Yahweh yace,"
|
|||
|
\v 4 Sa'an nan Musa ya rubuta dukkan maganganun Yahweh. Tun da sassafe, Musa ya gina bagadi a kusa da tsaunin ya shirya duwatsu goma sha biyu, domin duwatsun goma sha biyu su zama a madadin kabilu goma sha biyu na Isra'ila.
|
|||
|
|
|||
|
\s5
|
|||
|
\v 5 Ya aiki waɗansu samarin Isra'ila su miƙa baye-baye na ƙonawa da hadaya ta baye-bayen zumunta na bijimai ga Yahweh.
|
|||
|
\v 6 Musa ya ɗauki rabin jinin ya sa cikin darurruka; ya yayyafa sauran rabin a bisa bagadin.
|
|||
|
|
|||
|
\s5
|
|||
|
\v 7 Ya ɗauki littafin Alƙawarin ya karanta shi da murya ga mutanen. Suka ce, "Za mu yi dukkan abin da Yahweh ya faɗi. Za mu zama masu biyayya."
|
|||
|
\v 8 Sa'an nan Musa ya ɗauki jinin ya yayyafa shi a kan mutanen. Ya ce, "Wannan shi ne jinin alƙawarin da Yahweh ya yi daku sa'ad da ya baku alƙawari da dukkan waɗannan maganganun."
|
|||
|
|
|||
|
\s5
|
|||
|
\v 9 Sa'an nan Musa da Haruna da Nadab da Abihu, da dattawa saba'in na Isra'ila suka hau bisa tsaunin.
|
|||
|
\v 10 Suka ga Yahweh na Isra'ila. A ƙarƙashin ƙafafunsa a kwai wani dakali wanda aka yi kamar da n safire, yana sheƙi kamar sararin sama.
|
|||
|
\v 11 Yahweh bai ɗora hannu don fushi a kan dattawan Isra'ila ba. Suka ga Yahweh, suka ci suka sha.
|
|||
|
|
|||
|
\s5
|
|||
|
\v 12 Yahweh yace da Musa, "Ka hawo wurina a kan tsaunin ka tsaya a can. Zan baka alluna na dutse da doka da dokokin da na rubuta, domin ka koya masu."
|
|||
|
\v 13 Sai Musa ya shirya, shi da mataimakinsa Yoshuwa suka hau tsaunin Yahweh.
|
|||
|
|
|||
|
\s5
|
|||
|
\v 14 Musa yace da dattawan, "Ku tsaya nan ku jira har sai mun dawo wurin ku. Haruna da Hor suna tare da ku. Idan wani yana da damuwa, ya je wurin su."
|
|||
|
\v 15 To sai Musa ya hau tsaunin, girgije ya rufe tsaunin.
|
|||
|
|
|||
|
\s5
|
|||
|
\v 16 Darajar Yahweh ta sauko a kan Tsaunin Sinai, girgije ya rufe shi har kwana shida. A rana ta bakwai ya kira Musa daga cikin girgijen.
|
|||
|
\v 17 Baiyanuwar darajar Yahweh ta yi kama da wuta mai ci a idanun Isra'ilawa a kan tsaunin.
|
|||
|
\v 18 Musa ya shiga cikin girgijen ya hau kan tsaunin. Yana can kan tsaunin har kwana arba'in da yini arba'in.
|
|||
|
|
|||
|
\s5
|
|||
|
\c 25
|
|||
|
\cl Sura 25
|
|||
|
\p
|
|||
|
\v 1 Yahweh yace da Musa,
|
|||
|
\v 2 "Ka ce da Isra'ilawa, duk mutumin da ya ji yana da niyya a zuciyarsa ya kawo mani baiko. Sai ka karɓi waɗannan baye-baye domi na.
|
|||
|
|
|||
|
\s5
|
|||
|
\v 3 Ga baye-bayen da za ka karɓa daga wurin su: zinariya, da azurfa, da tagulla;
|
|||
|
\v 4 da shuɗi, da shunayya, da jăn kaya; da leshe mai kyau; da gashin awaki;
|
|||
|
\v 5 da fatar rago da aka yiwa jan rini da fatar ragon ruwa; da itacen ƙirya;
|
|||
|
\v 6 da mai domin fitilu na haikali; da kayan yaji saboda mai na shafewa da turare mai ƙanshi da duwatsun
|
|||
|
\v 7 oniks da sauran duwatsu masu daraja da za a manna a alkyabba da ɗamara ta ƙirji.
|
|||
|
|
|||
|
\s5
|
|||
|
\v 8 Sai su yi mani haikali domin in zauna a cikin su.
|
|||
|
\v 9 Sai ka yi dai-dai yadda zan nuna maka tsarinsa da dukkan kayayyakinsa.
|
|||
|
|
|||
|
\s5
|
|||
|
\v 10 Za su yi akwati na itacen ƙirya. Ratarsa za ta zama kamu biyu da rabi; faɗinsa zai zama kamu ɗaya da rabi; tsayinsa zai zama kamu ɗaya da rabi.
|
|||
|
\v 11 Sai ka shafe shi da zinariya tsantsa ciki da waje, dole ka kewaye shi da rawanin zinariya a bisansa.
|
|||
|
|
|||
|
\s5
|
|||
|
\v 12 Sai ka yi ƙawanyu huɗu na zubi da zinariya domin sa, kasa su a ƙafafu huɗu na akwatin, da ƙawanyoyi biyu a ɗaya gefen.
|
|||
|
\v 13 Sai ka yi sanduna na itacen ƙirya ka shafe su da zinariya.
|
|||
|
\v 14 Sai kasa sandunan a cikin ƙawanyoyi na gefen akwatin alƙawarin, yadda za a iya ɗaukar sa.
|
|||
|
|
|||
|
\s5
|
|||
|
\v 15 Za a bar sandunan jikin akwatin; kada a cire su.
|
|||
|
\v 16 Sai ka sa ka'idodi na alƙawarin da zan baka a cikin akwatin.
|
|||
|
\v 17 Sai ka yi marfi na zinariya tsantsa. Ratarsa za ta zama kamu biyu da rabi, faɗinsa kuma kamu ɗaya da rabi.
|
|||
|
\v 18 Sai ka yi sifofi biyu na kerubim da gogaggiyar zinariya saboda gefe biyu na marfin kafara.
|
|||
|
|
|||
|
\s5
|
|||
|
\v 19 Ka yi kerub ɗaya saboda gefe ɗaya na marfin kafara, ɗaya kerub ɗin kuma saboda ɗaya gefen. Za ka yi su dai-dai kamar abu ɗaya da marfin kafara.
|
|||
|
\v 20 Fukafukan kerubobin su miƙe tsaye su yi sama su yiwa marfin kafara inuwa. Kerubobin su dubi juna su kalli tsakiyar marfin kafara.
|
|||
|
\v 21 Sai ka sa marfin kafara a kan akwatin, kuma kasa ka'idodi na alƙawari da zan ba ka a ciki.
|
|||
|
|
|||
|
\s5
|
|||
|
\v 22 A wurin akwatin ne zan sadu da kai. Zan yi magana da kai a inda nake a bisa marfin kafara. Zai zama daga tsakanin kerubobin biyu a bisa akwatin na shaida zan yi magana da kai game da dukkan ka'idodi da zan baka domin Isra'lawa.
|
|||
|
|
|||
|
\s5
|
|||
|
\v 23 Sai ka yi teburi na itacen ƙirya. Ratarsa za ta zama kamu biyu; faɗinsa kamu ɗaya, tsayinsa zai zama kamu ɗaya da rabi.
|
|||
|
\v 24 Sai ka shafe shi da zinariya tsantsa ka yi masa ado da dajiya ta zinariya a sama kewaye da shi.
|
|||
|
|
|||
|
\s5
|
|||
|
\v 25 Sai kayi dajiya ta kewaye shi mai faɗin tafin hannu ɗaya, ka kuma yiwa bakinsa ado da bugaggen zinariya.
|
|||
|
\v 26 Sai ka yi masa ƙawanyoyi na zinariya guda huɗu ka liƙa ƙawanyoyin a kusurwoyinsa huɗu, inda ƙafafun nan huɗu suke.
|
|||
|
\v 27 Sai ka liƙa ƙawanyoyin a wuri domin sandunan, yadda za a iya ɗaukar teburin.
|
|||
|
|
|||
|
\s5
|
|||
|
\v 28 Sai ka yi sandunan da itacen ƙirya ka shafe su da zinariya domin a iya ɗaukar teburin tare da su.
|
|||
|
\v 29 Sai ka yi tasoshinsa da cokulansa da butocinsa da akusoshinsa domin zuba baye-baye na sha. Sai ka yi su da zinariya zalla.
|
|||
|
\v 30 Za ka riƙa ɗora gurasa ta kasancewa a bisa teburin a gabana.
|
|||
|
|
|||
|
\s5
|
|||
|
\v 31 Sai ka yi wurin ɗora fitila da gogaggiyar zinariya. Wurin ɗora fitilar za kayi da wurin zamansa. Kofinansa da leɓunansa da furanninsa za kayi su tare kamar abu ɗaya.
|
|||
|
\v 32 Rassa shida za su fito daga gefunansa-rassa uku daga gefe ɗaya, rassa uku kuma na wurin ɗora fitilar su zarce a ɗaya gefen.
|
|||
|
|
|||
|
\s5
|
|||
|
\v 33 Reshe na farko zai zama da kofuna uku kamar an yi su da lingaɓin itacen almond, da baki mai kamar ganye da fure, kofuna uku kuma an yi su kamar lingaɓin itacen almond a ɗaya reshen, da baki kamar ganye da fure. Dukkan su shida za su zama dai-dai da juna, su zarce daga abin ɗora fitilar.
|
|||
|
\v 34 A kan abin ɗora fitilar kansa, a tsakiyarsa, zai kasance da kofuna huɗu masu kama da lingaɓin itacen almond, da kamannin ganye da furanni.
|
|||
|
|
|||
|
\s5
|
|||
|
\v 35 Tagwayen rassa biyu na farko za su zama da baki kamar ganye-an yi su tare kamar abu ɗaya, tagwayen rassa na biyu kuma an yi su da kamar ganye abu ɗaya tare. Haka kuma tagwayen rassa na uku za a yi su da kamannin ganye sai ka ce abu ɗaya. Haka dukkan rassan shida za su zama su zarce wurin ɗora fitilar.
|
|||
|
\v 36 Bakunansu masu kama da ganye za su zama abu ɗaya, an yi shi da bugaggiyen aikin curin zinariya tsantsa.
|
|||
|
|
|||
|
\s5
|
|||
|
\v 37 Za ka yi abin ɗora fitilar da fitulunsa guda bakwai, kasa fitilun a bisansa domin su bada haske daga wurinsa.
|
|||
|
\v 38 Hantsukan da tasoshin a yi su da zinariya tsantsa.
|
|||
|
\v 39 A yi amfani da awo ɗaya na zinariya a yi wurin ɗora fitilar da kayayyakinsa.
|
|||
|
\v 40 Ka tabbata ka yi su kamar yadda aka nuna maka a kan tsaunin.
|
|||
|
|
|||
|
\s5
|
|||
|
\c 26
|
|||
|
\cl Sura 26
|
|||
|
\p
|
|||
|
\v 1 Rumfar taruwa kuma za ka yi ta da labule goma da aka yi su da lilin mai kyau da shuɗi da shunayya da jan ulu mai zanen cerubim. Wanda gwanin mai aikin hannu ya yi.
|
|||
|
\v 2 Tsawon kowanne labule zai zama kamu ashirin da takwas, faɗi kuma kamu huɗu. Labulen dukkan su su kasance girmansu ɗaya.
|
|||
|
\v 3 Labule biyar su zama haɗe da juna, sauran biyar kuma su zama haɗe da juna.
|
|||
|
|
|||
|
\s5
|
|||
|
\v 4 Kashi ɗaya na labulen za ka yi masa abin ratayewa na shuɗi daga ƙarshensa. Kashi na biyu ma haka za ka yi masu daga ƙarshe.
|
|||
|
\v 5 Kashi na farko za ka yi masu wurin ratayewa hamsin, kashi na biyu ma za ka yi masu wurin ratayewa hamsin. Ka yi haka domin wurin ratayewar labulen su dubi junansu.
|
|||
|
\v 6 Sai ka yi kayan adon labule na zinariya guda hamsin ka haɗa labulen tare da juna domin rumfar sujadar ta zama a haɗe.
|
|||
|
|
|||
|
\s5
|
|||
|
\v 7 Za ka yi labule na gashin awaki domin rumfa ta bisan rumfar sujada. Za ka yi labule guda goma sha ɗaya.
|
|||
|
\v 8 Tsawon kowanne labule zai zama kamu talatin, faɗin kowanne labule kuma kamu huɗu. Labulen nan goma sha ɗaya girmansu ya zama ɗaya.
|
|||
|
\v 9 Labule biyar sai ka haɗa su da juna sauran shida kuma ka haɗa su da juna. Sai ka gwama labule na shida wanda yake a gaban rumfar.
|
|||
|
|
|||
|
\s5
|
|||
|
\v 10 Sai ka yi maratayi hamsin a gefen labule jeri na farko, maratayi hamsin kuma a gefen labulen da ya haɗa jeri na biyu.
|
|||
|
\v 11 Sai ka yi abin maƙalawa hamsin na tagulla ka sa su a maratayin. Sa'an nan ka haɗa rumfar tare ta zama abu ɗaya.
|
|||
|
|
|||
|
\s5
|
|||
|
\v 12 Rabin labulen da ya rage, wato wanda ya zarce ya ragu daga labulen rumfar, sai ka bar shi yana lilo a bayan rumfar sujada.
|
|||
|
\v 13 Zai zama kamu ɗaya na labulen a gefe ɗaya, kamu ɗaya kuma na labulen a ɗaya gafen-wato abin da ya ragu na labulen rumfar a bar shi ya na lilo a gefen rumfar sujada a sashi ɗaya domin ya rufe ta.
|
|||
|
\v 14 Sai ka yi wa rumfar sujadar abin rufewa da fatun rago waɗanda a ka jeme mai rinin jă, wani marfin kuma na fata mai kyau ka sa ya rufe wannan.
|
|||
|
|
|||
|
\s5
|
|||
|
\v 15 Sai ka yi wa rumfar sujadar diraku na itacen ƙirya a kafa su a tsaye.
|
|||
|
\v 16 Ratar kowacce dirka zai zama kamu goma, faɗin ta kuma kamu ɗaya da rabi.
|
|||
|
\v 17 Sai a yi wa dirakun turaka biyu na katako domin su haɗa su da juna. Haka za ka yi dukkan dirakun rumfar sujada.
|
|||
|
\v 18 Sa'ad da ka yi dirakun rumfar sujadar, sai ka yi guda ashirin saboda sashi na kudu.
|
|||
|
|
|||
|
\s5
|
|||
|
\v 19 Sai ka yi darurruka arba'in na azurfa a ƙarƙashin dirakun nan ashirin. Darurruka biyu za su zama matashin dirka ta farko, darurruka biyu kuma za su zama matashin dirakun guda biyu.
|
|||
|
\v 20 Sashi na biyu na rumfar sujada, wato daga arewa, za ka yi masa diraku ashirin
|
|||
|
\v 21 da darurrukansu guda arba'in na azurfa. Dirka ta farko za ta kasance da darurruka biyu, biyu kuma a ta gaba, har a gama su dukka.
|
|||
|
|
|||
|
\s5
|
|||
|
\v 22 Bayan rumfar sujada kuma daga sashin yamma, sai ka yi ma sa diraku shida.
|
|||
|
\v 23 Sai ka yi diraku biyu saboda kusurwar rumfar sujada ta baya.
|
|||
|
\v 24 Waɗannan dirakun ba za a haɗa su daga ƙasa ba, amma daga sama za a haɗa su da ƙawanya ɗaya. Haka kusurwoyi biyu na baya za su zama.
|
|||
|
\v 25 Za su zama diraku takwas, tare da darurrukansu na azurfa. Za a sami darurruka goma sha shida, darurruka biyu a ƙarƙashin dirka ta farko, darurruka biyu kuma a ta gaba, har a gama.
|
|||
|
|
|||
|
\s5
|
|||
|
\v 26 Dole ka shirya katakai da zasu gitta da itacen ƙirya-biyar saboda sashi ɗaya na dirakun rumfar sujada,
|
|||
|
\v 27 katakai biyar na gittawa kuma saboda ɗaya sashin na dirakun rumfar sujada, katakai biyar na gittawa kuma saboda dirakun sashin rumfar sujada na baya wajan yamma.
|
|||
|
\v 28 Katakon da yake tsakiyar dirakun, zai kai daga wannan ƙarshe zuwa wancan ƙarshen.
|
|||
|
|
|||
|
\s5
|
|||
|
\v 29 Sai ka shafe dirakun da zinariya. Za kuma ka yi zobbansu da zinariya, domin su riƙe katakan da aka gitta, na gittawar ma za ka shafe su da zinariya.
|
|||
|
\v 30 Dole ka tsara rumfar sujada ta wurin bin yadda aka nuna maka a kan tsaunin.
|
|||
|
|
|||
|
\s5
|
|||
|
\v 31 Sai ka kayi labule na shuɗi, da shunayya, da jan ulu, da leshe mai kyau da zanen kerubim, wanda ƙwararren mai aikin hannu zai yi.
|
|||
|
\v 32 Sai dole ka rataye shi a kan ginshiƙai na itacen ƙirya shafaffu da zinariya. Waɗannan ginshiƙai za a yi ma su ƙugiyoyi na zinariya a kan darurruka huɗu na azurfa.
|
|||
|
\v 33 Sai kuma dole ka sa labulen a wurin ratayewarsa, sai kuma ka kawo akwatin a ciki. Labulen zai raba tsakanin wuri mai tsarki da wuri mafi tsarki.
|
|||
|
|
|||
|
\s5
|
|||
|
\v 34 Sai kasa marfi na kafara a bisa akwatin shaida, wanda yake a cikin wuri mafi tsarki. Sai kasa teburin a waje daga labulen.
|
|||
|
\v 35 Sai kasa wurin ɗora fitilar ya dubi teburin daga sashin kudu na rumfar sujada. Teburin ya kasance daga sashin arewa.
|
|||
|
|
|||
|
\s5
|
|||
|
\v 36 Sai kuma dole ka yi maratayi a ƙofar shiga rumfar. Sai kuma dole ka yi shi da shuɗi, da shunayya, da jan ƙyalle, da leshe mai kyau, murɗaɗɗe wanda mai iya zane a kan tufa ya yi.
|
|||
|
\v 37 Wurin ratayewar za ka yi masa ginshiƙai biyar na ƙirya shafaffu da zinariya. Ƙugiyoyinsu su zama na zinariya, ka yi darurruka biyar na zubi da tagulla.
|
|||
|
|
|||
|
\s5
|
|||
|
\c 27
|
|||
|
\cl Sura 27
|
|||
|
\p
|
|||
|
\v 1 Sai ka yi bagadi na itacen ƙirya, ratarsa kamu biyar faɗinsa ma kamu biyar. Bagadin zai kasance kamu dai-dai kowanne gefe da tsawonsa kamu uku.
|
|||
|
\v 2 Za ka sa kusurwoyinsa su zarce da kamannin ƙahonin bijimi. Bagadin da ƙahonin za su zama tare kamar abu ɗaya, zaka shafe su da tagulla.
|
|||
|
|
|||
|
\s5
|
|||
|
\v 3 Za ka yi kayan aiki domin bagadin: wato tukunya saboda zuba toka da kuma cebur da darori da cokulan tsamo nama da kasake na tuya. Dukkan waɗannan kayan aikin za kayi su da tagulla.
|
|||
|
\v 4 Za ka yiwa bagadin makari na tagulla da răgă. Za ka yi zobba na tagulla guda huɗu domin kowacce kusurwa.
|
|||
|
|
|||
|
\s5
|
|||
|
\v 5 Za ka sa makarin ƙasa da bagadin, ya kai rabin sa daga ƙasa.
|
|||
|
\v 6 Za ka yiwa bagadin sanduna na itacen ƙirya, ka shafe su da tagulla.
|
|||
|
|
|||
|
\s5
|
|||
|
\v 7 Sandunan za ka sa su shiga cikin zobban, a sassa biyu na bagadin, domin a iya ɗaukar sa.
|
|||
|
\v 8 Za kayi bagadin ba kome a cikinsa, da katakai. Za kayi shi kamar yadda a ka nuna maka a kan tsaunin.
|
|||
|
|
|||
|
\s5
|
|||
|
\v 9 Za ka yi wa rumfar sujada haraba. Za a yi wuraren rataye-rataye a harabar a sashin kudu, ragayu na leshe mai kyau saƙaƙƙe mai ratar kamu ɗari.
|
|||
|
\v 10 Za ka yi diraku ashirin domin ragayun, da darori ashirin na tagulla. Za a yi ƙugiyoyi liƙe da dirakun da sanduna na azurfa.
|
|||
|
|
|||
|
\s5
|
|||
|
\v 11 Haka kuma a sashin arewa, za ka yi ragayu guda ɗari tare da diraku ashirin da darori ashirin na tagulla da ƙugiyoyi liƙe da dirakun da sandunan azurfa.
|
|||
|
\v 12 A sashin yamma na harabar za ka yi labule kamu hamsin. Za ka yi diraku goma da darori goma.
|
|||
|
\v 13 Haraba za ta zama kamu hamsin daga sashin gabas.
|
|||
|
|
|||
|
\s5
|
|||
|
\v 14 Ragayoyi na wurin shiga ratarsa za su zama kamu hamsin. Za su zama da diraku uku da darori uku.
|
|||
|
\v 15 Ɗaya sashin ma zai zama da ragayu kamu goma sha biyar. Da dirakunsu uku da darorinsu uku.
|
|||
|
\v 16 Ƙofar shigowa harabar za ta zama da labule mai ratar kamu ashirin. Za a yi labulen da shuɗi da shunaiya da jăn ƙyalle da saƙaƙƙen leshe mai kyau, wanda ƙwararren mai aikin hannu ya yi. Zai zama da diraku huɗu da darori huɗu.
|
|||
|
|
|||
|
\s5
|
|||
|
\v 17 Dukkan dirakun harabar za su zama da sandunan azurfa da ƙugiyoyin azurfa da darorin tagulla.
|
|||
|
\v 18 Ratar harabar za ta zama kamu ɗari, da faɗin kamu hamsin da tsawon kamu biyar da ragaya ta saƙaƙƙen leshe mai kyau da darori na tagulla.
|
|||
|
\v 19 Dukkan kayan aikin rumfar sujada, da abubuwan kamawar na harabar za a yi su da tagulla.
|
|||
|
|
|||
|
\s5
|
|||
|
\v 20 Za ka umurci mutanen Isra'ila su kawo man zaitun, mai tsabta, domin fitilun su yi ta ci ba fasawa.
|
|||
|
\v 21 A rumfa ta taruwa, bayan labulen rumfar sujada inda akwatin shaida ya ke, Haruna da 'ya'yansa za su sa fitilun suyi ta ci tun daga yamma har zuwa safiya a gaban Yahweh. Mutanen Isra'ila za su lura da wannan ka'idar a dukkan zamanu.
|
|||
|
|
|||
|
\s5
|
|||
|
\c 28
|
|||
|
\cl Sura 28
|
|||
|
\p
|
|||
|
\v 1 Ka kira Haruna ɗan'uwanka da 'ya'yansa maza- wato, Nadab, da Abihu, da Eliyeza, da Itama - daga cikin Isra'ilawa domin su yi mani hidima a matsayin firistoci.
|
|||
|
\v 2 Ka yi wa Haruna, ɗan'uwanka rigunan keɓaɓɓu gare ni. Waɗannan riguna za su zama domin ya fita da kyau da kwarjini.
|
|||
|
\v 3 Ka yi magana da mutane masu hikima a zuciya, waɗanda na cika su da ruhun hikima, domin su yi wa Haruna riguna a keɓe shi domin ya yi mani hidima a matsayin firist.
|
|||
|
|
|||
|
\s5
|
|||
|
\v 4 Rigunan da za suyi su ne, ɗamara ta sawa a ƙirji da alkyabba, da taguwa, da riga mai aiki, da rawani, da ɗamara. Za su yi waɗannan tufafi keɓaɓɓu gare ni. Za su zama saboda Haruna ɗan'uwanka da 'ya'yansa domin su yi mani hidima a matsayin firistoci.
|
|||
|
\v 5 Ma su aikin hannu za su yi amfani da leshe mai kyau mai launin zinariya, da shuɗi, da shunayya, da jã.
|
|||
|
|
|||
|
\s5
|
|||
|
\v 6 Sai su yi alkyabba da launin zinari, da shuɗi, da shunayya, da jan ulu, da leshe mai kyau mai aiki. gwani ne zai yi aikin.
|
|||
|
\v 7 A kusurwoyi biyu za ta kasance da ƙyallayen da za'a sa a kafaɗa.
|
|||
|
\v 8 A yi mata saƙa mai kyau ɗamarar ta zama kamar alkyabbar; kuma a yi su tare da falmarar, ayi su da leshe mai kyau mai aiki da launin zinari da shuɗi da shunaiya da ja.
|
|||
|
\v 9 Ka ɗauki duwatsu biyu na oniks ka rubuta sunayen 'ya'yan Isra'ila goma sha biyu.
|
|||
|
|
|||
|
\s5
|
|||
|
\v 10 Sunaye shida a kan dutsen ɗaya, sauran shidan kuma a kan ɗaya dutsen, bisa ga yadda aka haife su.
|
|||
|
\v 11 Mai iya rubutu a kan dutse ne zai yi rubutun kamar yadda ake rubuta hatimi, ka rubuta sunayen 'ya'yan Isra'ila goma sha biyu a kan duwatsun guda biyu. Ka ɗora duwatsun a kan kasko na zinariya.
|
|||
|
\v 12 Za ka ɗora duwatsun biyu a ƙyallen kafaɗa na falmara, su zama duwatsun tuna wa Yahweh da 'ya'yan Isra'ila. Haruna zai ɗauki sunayensu a gaban Yahweh bisa kafaɗunsa biyu su zama abin tunawa a gare shi.
|
|||
|
|
|||
|
\s5
|
|||
|
\v 13 Sai kayi kasake na zinariya
|
|||
|
\v 14 za kayi sarƙoƙi biyu na zinariya kamar tsarkiyoyi, ka liƙa sarƙoƙin a jikin kasaken.
|
|||
|
|
|||
|
\s5
|
|||
|
\v 15 Za ka yi ƙyalle na ƙirji domin yin shawara, ka sami gwani ya tsara shi kamar alkyabba. A yi shi na zinariya, da shuɗi, da shunayya, da jan ulu, da linin mai kyau.
|
|||
|
\v 16 Ya zama murabi'i. Ƙyallen na ƙirji za ka sa shi riɓi biyu. Ratarsa za ta zama taki ɗaya faɗinsa ma taki ɗaya.
|
|||
|
|
|||
|
\s5
|
|||
|
\v 17 Ka yi jere huɗu na duwatsu masu daraja a jikinsa. Dole jeri na farko a sa rubi, da tofez, da kuma ganet..
|
|||
|
\v 18 A jeri na biyu kuma dole a sa emerald, da saffiya, da lu'u-lu'u.
|
|||
|
\v 19 Jeri na uku kuma dole kasa yasint, da agat, da kuma ametis.
|
|||
|
\v 20 Jeri na huɗu za ka sa beril da oniks, da yasfa. A sa su a kan kasaken zinariya.
|
|||
|
|
|||
|
\s5
|
|||
|
\v 21 Za a jera duwatsun bisa ga sunayen 'ya'yan Isra'ila goma sha biyu, bi da bi a jere. A zana su kamar yadda a ke yin hatimi da zobe, kowanne suna ya zama a madadin kabilu goma sha biyu.
|
|||
|
\v 22 Ƙyalle na ƙirjin ya zama sarƙa kamar tsarkiya, saƙaƙƙe na zinariya tsantsa.
|
|||
|
\v 23 Za ka yi wa ƙyallen zobba biyu liƙe da juna a kusurwoyinsa biyu.
|
|||
|
\v 24 Ka liƙa sarƙoƙin nan biyu a jikin ƙyalle na ƙirji.
|
|||
|
|
|||
|
\s5
|
|||
|
\v 25 Za ka liƙa ƙarshen sarƙoƙin nan biyu a jikin kasaken. Sa'an nan ka liƙa su a jikin ƙyallen kafaɗa na falmara a gaba.
|
|||
|
\v 26 Za ka yi zobba na zinariya guda biyu, ka sa su a ɗaya gefe na ƙyallen na ƙirjin, a ƙarshen kalmasa ta ciki kusa da haɓar.
|
|||
|
|
|||
|
\s5
|
|||
|
\v 27 Dole zaka yi waɗansu zobba na zinariya guda biyu, ka liƙa su jikin ƙyalle na kafaɗar falmara daga ƙasa, a bisa ɗamarar nan ta kyakkawan leshe na falmarar.
|
|||
|
\v 28 Su haɗa ƙyallen nan na ƙirji da zobban falmarar nan masu launin shuɗi, domin su haɗu saƙaƙƙiyar ɗamarar nan ta falmarar. Domin kada ƙyallen na ƙirji ya zama a ware da falmarar.
|
|||
|
|
|||
|
\s5
|
|||
|
\v 29 Sa'ad da Haruna yake shiga cikin wuri mai tsarki, zai ɗauki sunayen mutanen Isra'ila a bisa zuciyarsa cikin ƙyallen nan na ƙirji domin ɗaukar shawara, za ayi ta yin haka domin ya zama abin tunawa a gaban Yahweh.
|
|||
|
\v 30 Zaka sa Urim da Tummim a cikin ƙyalle na ƙirjin domin ɗaukar shawara, domin su zama a bisa zuciyar Haruna sa'ad da yake shiga gaban Yahweh. Ta haka Haruna zai riƙa ɗaukar abin ɗaukar shawara domin mutanen Isra'ila bisa zuciyaarsa a gaban Yahweh.
|
|||
|
|
|||
|
\s5
|
|||
|
\v 31 Rigar wato falmara zaka yi ta duka da shuɗi.
|
|||
|
\v 32 Za a yi mata wurin sa kai a tsakiya. Dole ayi wa wurin sa kai ɗin saƙa domin kada ya yage. Dole a sami mai saƙa ya yi aikin.
|
|||
|
|
|||
|
\s5
|
|||
|
\v 33 Za ka yi wa haɓar rigar, ado na 'yan tutoci da shuɗi, da shunayya, da jan ulu ya kewaye dukka.
|
|||
|
\v 34 Ka yi ƙararrawa ta zinariya ta zagaya dukka a tsakanin tutocin. A sa ƙararrawa ta zinariya da tuta, sai kuma ƙararrawa ta zinariya sai kuma tuta - da sauransu - kewaye tufar dukkan ta.
|
|||
|
\v 35 Haruna zai sa wannan tufar sa'ad da zai yi hidima, domin a iya jin ƙararta sa'ad da yake shiga wuri mai tsarki gaban Yahweh da sa'ad da yake fita. Wannan domin kada ya mutu ne.
|
|||
|
|
|||
|
\s5
|
|||
|
\v 36 Dole ka yi faranti na zinariya ka yi zane a kan sa, kamar zanen hatimi, "Tsarki ga Yahweh."
|
|||
|
\v 37 Za ka liƙa wannan farantin da shuɗiyar iggiya a jikin rawanin.
|
|||
|
\v 38 Haruna zai sa shi a kansa; zai ɗauki laifi da ake yi game da baye-baye masu tsarki na Isra'ilawa waɗanda aka keɓe domin Yahweh. Dole rawanin ya kasance a kansa domin Yahweh ya karɓi baye- bayensu.
|
|||
|
|
|||
|
\s5
|
|||
|
\v 39 Dole ka yi alkyabba da linin mai kyau, da rawani na linin mai kyau. Kuma zaka sa mai zane ya yi masa ado.
|
|||
|
|
|||
|
\s5
|
|||
|
\v 40 Zaka yi riguna saboda 'ya'yan Haruna, da ɗammaru, da abin ɗaurawa a kansu saboda daraja da kwarjini.
|
|||
|
\v 41 Dole ka suturta Haruna ɗan'uwanka, da 'ya'yansa. Dole ka shafe su, ka naɗa su, ka keɓe su domi na, domin su yi mani hidima a matsayin firistoci.
|
|||
|
|
|||
|
\s5
|
|||
|
\v 42 Dole ka yi masu wuyan wanduna na sawa a ciki domin su rufe tsiraicin jikinsu, ya rufe su daga kwankwaso zuwa cinya.
|
|||
|
\v 43 Haruna da 'ya'yansa za su riƙa sa waɗannan tufafi sa'ad da suke shiga wurin taruwa da sa'ad da suke fuskantar bagadi su yi hidima a wuri mai tsarki. Dole su yi haka domin kada su zama da kuskure in ba haka ba za su mutu. Wannan zaunanniyar doka ce domin Haruna da zuriyarsa a bayansa.
|
|||
|
|
|||
|
\s5
|
|||
|
\c 29
|
|||
|
\cl Sura 29
|
|||
|
\p
|
|||
|
\v 1 Ga abin da za ka yi domin ka keɓe su yadda za su iya yi mani hidima a matsayin firistoci. Ka ɗauki ɗan bijimi da raguna biyu marasa cikas da,
|
|||
|
\v 2 gurasa marar gami, da waina marar gami gauraye da mai. Ka kuma ɗauki wainar alkama marar gami ka shafe da mai. wadda aka yi da kyakkyawar alkama. Wadda ake ci da zuma.
|
|||
|
|
|||
|
\s5
|
|||
|
\v 3 Dole ka sa su a cikin kwando ɗaya, ka kawo su a cikin kwandon, ka miƙa su tare da bijimin da ragunan nan biyu.
|
|||
|
\v 4 Dole ne ka miƙa Haruna da 'ya'yansa a ƙofar shiga rumfar ta taruwa. Za ka yi wa Haruna da 'ya'yansa wanka da ruwa.
|
|||
|
|
|||
|
\s5
|
|||
|
\v 5 Dole ka ɗauki rigunan da alkyabba ka sa wa Haruna da maratayin falmara da falmara da ƙyalle na ƙirjin da ɗamara ta leshe mai kyau tare da falmara ka yafa masa.
|
|||
|
\v 6 Ka naɗa rawanin a kansa da kambi na tsarki a bisa rawanin.
|
|||
|
\v 7 Sa'an nan ka ɗauki mai na shafewa ka zuba a kansa, da haka za ka shafe shi.
|
|||
|
|
|||
|
\s5
|
|||
|
\v 8 Dole ka kawo 'ya'yansa su ma ka sa masu alkyabbobi.
|
|||
|
\v 9 Za ka sa wa Haruna da 'ya'yansa ɗammaru da ƙyalle na ado a kansu. Aikin firist zai zama nasu kullum bisa ga doka. Ta haka za ka tsarkake Haruna da 'ya'yansa domin su yi mani hidima.
|
|||
|
|
|||
|
\s5
|
|||
|
\v 10 Dole dukkan ku za ku kawo bijimin a wurin rumfa ta taruwa, Haruna da 'ya'yansa za su sa hannayensu a kan bijimin.
|
|||
|
\v 11 Zaka yanka bijimin a ƙofar rumfar ta taruwa a gaban Yahweh.
|
|||
|
|
|||
|
\s5
|
|||
|
\v 12 Dole ka ɗauki jinin bijimin da yatsarka ka sa a kan ƙahon bagadin, sai ka ɗauki sauran jinin ka zubar da shi a dakalin bagadin.
|
|||
|
\v 13 Dole ka ɗauki kitse na marfin ciki da wanda ya lulluɓe hantar da ƙodojin biyu da kitsen da yake kansu; ka ƙona a kan bagadin.
|
|||
|
\v 14 Amma naman bijimin da fatarsa da sauran abin da ya rage jikinsa, dole ka ƙone su a waje. Za ya zama baiko na zunubi.
|
|||
|
|
|||
|
\s5
|
|||
|
\v 15 Dole ka kuma ɗauki rago ɗaya, Haruna da 'ya'yansa su ɗora hannuwansu a kansa.
|
|||
|
\v 16 Dole ka yanka ragon, ka yayyafa jininsa a kowanne sashi na bagadin.
|
|||
|
\v 17 Dole ka yanka ragon gunduwa--gunduwa da ƙafafunsa, ka sa 'yancikinsa tare da gunduwoyin tare da kansa,
|
|||
|
\v 18 a bisa bagadin. Sa'an nan ka ƙone ragon dukkan sa. Zai zama baiko na ƙonawa ga Yahweh, baiko mai daɗin ƙanshi wanda aka yi domin Yahweh.
|
|||
|
|
|||
|
\s5
|
|||
|
\v 19 Sa'an nan dole ka ɗauki ɗaya ragon, Haruna da 'ya'yansa su ɗora hannuwansu a kansa.
|
|||
|
\v 20 Sa'an nan dole ka yanka ragon ka ɗauki jininsa. Ka sa shi a bisa kunnen Haruna na dama, da bisa kan kunnuwan 'ya'yansa na dama, da kan babban yatsansu na dama, da babban yatsan kowannen su na dama na ƙafa. Sa'an nan ka yayyafa jinin a jikin bagadin a kowanne sashe.
|
|||
|
|
|||
|
\s5
|
|||
|
\v 21 Dole ka ɗauka daga jinin da yake kan bagadi da mai na shafewa, ka yayyafa a kan Haruna da tufafinsa, da kuma kan 'ya'yansa da tufafinsu. Sa'an nan Haruna zai zama keɓaɓɓe domi na, da kuma tufafinsa da 'ya'yansa da tufafinsu tare da shi.
|
|||
|
|
|||
|
\s5
|
|||
|
\v 22 Dole ka ɗauki kitsen ragon da kitsen bindin da kitsen da ya rufe kayan cikin da wanda ya lulluɓe hantar, da ƙodojin biyu da kitsen dake kansu, da cinyar dama-wannan ragon na keɓewar firistoci ne a gare ni.
|
|||
|
\v 23 Ka ɗauki dunƙule ɗaya na gurasa da wainar da aka yi da mai, guda ɗaya da wainar alkama ɗaya daga cikin kwandon wadda bata da gami wadda ke gaban Yahweh.
|
|||
|
|
|||
|
\s5
|
|||
|
\v 24 Dole ka sa waɗannan a cikin hannuwan Haruna da hannuwan 'ya'yansa ka ɗaga su a gabana domin baiko na ɗagawa a gaban Yahweh.
|
|||
|
\v 25 Sa'an nan dole ka ɗauke abincin daga hannuwansu ka ƙone shi a kan bagadin tare da baiko na ƙonawa. Zai kawo ƙanshi mai daɗi a gare ni; zai zama baikon da aka yi mani da wuta.
|
|||
|
|
|||
|
\s5
|
|||
|
\v 26 Dole ka ɗauki haƙarƙarin ragon da aka yanka saboda keɓe Haruna ka ɗaga shi ka karkaɗa shi sama domin ya zama baiko na ɗagawa ga Yahweh, shi ne kuma zai zama rabonka.
|
|||
|
\v 27 Dole ka keɓe ƙirjin da aka karkaɗa a sama domi na, cinyar da firistoci suka kawo gudummuwa-ƙrjin da aka karkaɗa da cinyar da aka kawo gudummuwa saboda Haruna da 'ya'yansa.
|
|||
|
\v 28 Wannan zai zama zaunanniyar ka'ida saboda Haruna da 'ya'yansa. Zai zama gudummuwar da mutanen Isra'ila suka ba Yahweh baye-baye na salama.
|
|||
|
|
|||
|
\s5
|
|||
|
\v 29 Za a ajiye tufafin Haruna masu tsarki saboda 'ya'yansa a bayansa. Za a shafe su a cikin waɗannan tufafi a keɓe su gare ni a cikin su.
|
|||
|
\v 30 Firist ɗin da ya gaje shi daga cikin 'ya'yansa, wanda ya zo rumfa ta taruwa domin ya yi mani hidima a wuri mai tsarki, zai sa waɗannan tufafi har kwanaki bakwai.
|
|||
|
|
|||
|
\s5
|
|||
|
\v 31 Dole ka ɗauki ragon na rantsar da firistoci ka dafa namansa a cikin wuri mai tsarki.
|
|||
|
\v 32 Haruna da 'ya'yansa ne za su ci naman ragon da gurasar dake cikin kwando a ƙofar shiga rumfa ta taruwa.
|
|||
|
\v 33 Dole su ci naman da gurasar da aka bayar domin a yi masu kafara a kuma naɗa su, domin a keɓe su domina. Ba wanda zai ci wannan abincin, saboda zai zama abin da aka tsarkake saboda ni.
|
|||
|
\v 34 Idan naman keɓewar da aka bayar ko gurasar sun rage har sun kai safiya, za ka ƙone shi. Ba za a ci shi ba saboda an riga an keɓe shi saboda ni.
|
|||
|
|
|||
|
\s5
|
|||
|
\v 35 Haka za ka yi, ka bi umarnin dana baka, ka yi wa "ya'yan Haruna haka. Ka shirya su har kwana bakwai.
|
|||
|
\v 36 Kowacce rana zaka miƙa bijimi domin baiko na zunubi damin kafara. Dole ka tsarkake bagadin ta wurin yin kafara domin sa, zaka shafe shi domin ya zama a keɓe domi na.
|
|||
|
\v 37 Dole ka yi kwana bakwai kana yin hadaya saboda bagadin kana keɓe shi saboda Yahweh. Sa'an nan bagadin zai zama keɓaɓɓe saboda ni. Dukkan abin da ya taɓa bagadin zai zama keɓaɓɓe na Yahweh.
|
|||
|
|
|||
|
\s5
|
|||
|
\v 38 Dole ka riƙa miƙa ɗan rago bana ɗaya kowacce rana.
|
|||
|
\v 39 Dole ka miƙa ɗan rago ɗaya da safe, ɗaya ɗan ragon kuma ka miƙa shi da yamma.
|
|||
|
|
|||
|
\s5
|
|||
|
\v 40 Tare da ɗan rago na fari, za a miƙa mudu biyu na garin alkama mai laushi wanda aka kwaɓa da man zaitun kwalba biyu, da ruwan inabi shi ma kwalba biyu baiko na sha.
|
|||
|
|
|||
|
\s5
|
|||
|
\v 41 Rago na biyu tilas ka miƙa shi da faɗuwar rana. Dole ka sa gari kamar yadda ka sa da safe, haka kuma baiko na sha. Waɗannan za su zama da ƙamshi mai daɗi a gare ni; za su zama baiko da aka yi mani da wuta.
|
|||
|
\v 42 Waɗannan za su zama baiko na ƙonawa a cikin dukkan tsararrakinku, a ƙofar shiga rumfa ta taruwa a gaban Yahweh, inda zan sadu da kai in yi magana da kai a can.
|
|||
|
|
|||
|
\s5
|
|||
|
\v 43 A nan ne zan sadu da Isra'ilawa; darajata za ta keɓe rumfar. Zan keɓe rumfar ta taruwa da bagadin domin su nawa ne ni kaɗai.
|
|||
|
\v 44 Zan kuma keɓe Haruna da 'ya'yansa domin su yi mani hidima a matsayin firistoci.
|
|||
|
|
|||
|
\s5
|
|||
|
\v 45 Zan zauna a cikin Isra'ilawa zan zama Allahnsu.
|
|||
|
\v 46 Za su sani Ni ne Yahweh, Allahnsu wanda ya fito da su daga Masar domin in zauna a cikin su. Ni ne Yahweh Allahnsu.
|
|||
|
|
|||
|
\s5
|
|||
|
\c 30
|
|||
|
\cl Sura 30
|
|||
|
\p
|
|||
|
\v 1 Tilas ka yi bagadi na ƙona turare. Tilas ka yi shi da itacen ƙirya.
|
|||
|
\v 2 Ratarsa za ta zama kamu ɗaya, faɗinsa kamu ɗaya. Tilas ka yi shi murabbi'i, tsawonsa kamu biyu. Tilas ka yi shi tare da ƙahonninsa.
|
|||
|
|
|||
|
\s5
|
|||
|
\v 3 Tilas ka shafe bagadin da zinariya tsantsa-bisansa, da sassansa, da ƙahoninsa. Tilas ka kewaye gefensa da zinariya.
|
|||
|
\v 4 Tilas ka yi zobba biyu na zinariya liƙe da shi a kusa da shi daga ƙasa suna duban sa a sassa biyu. Zobban za su zama wurin zura sandunan riƙewa da za a iya ɗaukar bagadin.
|
|||
|
|
|||
|
\s5
|
|||
|
\v 5 Tilas ka yi sandunan da itacen ƙirya, ka shafe su da zinariya.
|
|||
|
\v 6 Tilas ka sa bagadin turaren a gaban labulen dake kusa da akwatin shaida. Zai zauna a gaban marfin kafara na zunubi a bisa akwatin shaida, inda zan sadu da kai.
|
|||
|
|
|||
|
\s5
|
|||
|
\v 7 Tilas Haruna ya ƙona turare mai ƙamshi kowacce safiya. Zai ƙona shi sa'ad da yake gyara fitilun,
|
|||
|
\v 8 da yamma kuma Haruna zai kunna fitilun domin turaren ya riƙa ƙonewa koyaushe a gaban Yahweh, a dukkan tsararraki.
|
|||
|
\v 9 Amma kada ka miƙa wani turaren a kan bagadin turaren, ko wani baiko na ƙonawa ko baiko na hatsi. Kada ka zuba wani baiko na sha a kansa.
|
|||
|
|
|||
|
\s5
|
|||
|
\v 10 Tilas Haruna ya yi hadaya ta zunubi a kan ƙahonninsa sau ɗaya a shekara. Da jinin baikon na zunubi zai yi hadaya ta zunubi sau ɗaya a shekara a dukkan tsararrakinku. Keɓaɓɓe ne sarai saboda Yahweh."
|
|||
|
|
|||
|
\s5
|
|||
|
\v 11 Sa'an nan Yahweh ya yi magana da Musa, cewa,
|
|||
|
\v 12 "Sa'ad da ka ƙidaya Isra'ilawa, kowanne mutum zai kawo abin fansa domin ransa ga Yahweh. Sa'ad da ka ƙidaya su dole ne ka yi haka. Domin kada annoba ta auko a cikin su sa'ad da kake ƙidaya su.
|
|||
|
\v 13 Dukkan wanda aka ƙidaya cikin yin ƙidayar zai biya rabin awo na azurfa, bisa ga kuɗin da ake amfani da su a wuri mai tsarki (awon dai-dai yake da abin da ake auna nauyin ƙaramin abu). Wannan rabin awo baiko ne domin Yahweh.
|
|||
|
\v 14 Dukkan wanda aka ƙidaya, daga shekara ashirin zuwa gaba, dole ya bada wannan baikon gare ni.
|
|||
|
|
|||
|
\s5
|
|||
|
\v 15 Lokacin da mutane suke bada wannan baiko domin fansar rayukansu, masu arziki ma ba zasu bada fiye da rabin awon nan ba, matalauta kuma ba zasu bada abin da bai kai rabin awon nan ba.
|
|||
|
\v 16 Dole ka karɓi wannan kuɗin fansa daga Isra'ilawa ka sa su cikin aikin rumfa ta taruwa. Dole ya zama abin tunawa ga Isra'ilawa a gare ni, su miƙa abin kafara domin rayukansu.
|
|||
|
|
|||
|
\s5
|
|||
|
\v 17 Sa'an nan Yahweh ya yi magana da Musa, cewa,
|
|||
|
\v 18 "Zaka yi babban bangaji na tagulla da wurin zamansa na tagulla, bangajin wanke-wanke. Tilas ka sa shi tsakanin rumfa ta taruwa da bagadi, ka zuba ruwa a cikin sa.
|
|||
|
|
|||
|
\s5
|
|||
|
\v 19 Haruna da 'ya'ansa za su wanke hannuwansa da ƙafafunsu da ruwan dake cikin sa.
|
|||
|
\v 20 Sa'ad da suke shiga rumfa ta taruwa da sa'ad da suke zuwa kusa da bagadi su yi mani hidima ta ƙona baiko, dole su wanke da ruwa domin kada su mutu.
|
|||
|
\v 21 Dole su wanke hannuwansu da ƙafafunsu domin kada su mutu. Dole wannan ta zama dawwamammar doka ga Haruna da zuriyarsa a dukkan tsararrakin mutanensa.
|
|||
|
|
|||
|
\s5
|
|||
|
\v 22 Sa'an nan Yahweh ya yi magana da Musa, cewa,
|
|||
|
\v 23 "Ka ɗauki waɗannan kayan yaji masu kyau: da murr mai zubowa na awo ɗari biyar, da sinamon mai ƙanshi mai daɗi na awo 250, da kayan yaji mai ƙanshi na awo 250,
|
|||
|
\v 24 da kayan yaji mai ƙanshi na kasiya na awo ɗari biyar, wanda aka auna bisa ga ma'aunin wuri mai tsarki, da kwalba ɗaya ta man zaitun.
|
|||
|
\v 25 Dole da waɗannan kayan haɗi za ka sa maiyin turare ya yi mai na shafewa mai tsarki. Zai zama man tsarki na shafewa, ajjiyayye saboda ni.
|
|||
|
|
|||
|
\s5
|
|||
|
\v 26 Dole da wannan mai na shafewa za ka shafe rumfa ta taruwa da akwati na shaida,
|
|||
|
\v 27 sai kuma teburin da kayan aikinsa da abin ɗora fitilar da kayanta da sanduƙin turare,
|
|||
|
\v 28 sai kuma bagadin ƙona baye--baye da dukkan kayansa da bangajin da wurin ɗora shi.
|
|||
|
|
|||
|
\s5
|
|||
|
\v 29 Tilas ka keɓe su saboda ni su zama masu tsarki domi na. Dukkan abin da ya taɓa su zai zama mai tsarki.
|
|||
|
\v 30 Tilas ka keɓe Haruna da 'ya'yansa domin su yi mani hidima a matsayin firistoci.
|
|||
|
\v 31 Dole kace da Isra'ilawa, 'Wannan mai na shafewa ne da aka keɓe domin Yahweh a dukkan tsararrakin mutanenku.
|
|||
|
|
|||
|
\s5
|
|||
|
\v 32 Dole mutane ba za su shafa shi a jikinsu ba, kuma ba za ka yi wani mai da kamar yadda ka yi shi ba, saboda keɓaɓɓe ne saboda Yahweh. Dole ka lura da shi ta wannan hanya.
|
|||
|
\v 33 Dukkan wanda ya yi turare irin sa, ko ya shafa wa wani shi, za a datse shi daga cikin mutanensa."'
|
|||
|
|
|||
|
\s5
|
|||
|
\v 34 Yahweh yace da Musa, "Ka ɗauki kayan yaji - wato su-stakte da onika da galbanum-kayan yaji masu ƙanshi tare da lubban tsantsa, ka auna su dai-dai wa daida.
|
|||
|
\v 35 Ka yi su kamar turaren yadda maiyin turare ya haɗa, gyararre da gishiri, mai tsafta keɓaɓɓe.
|
|||
|
\v 36 Ka yi masa haɗi mai kyau ka niƙa. Ka ɗiba cikinsa ka sa a shaida, wanda yake a cikin rumfa ta taruwa, inda zan sadu da kai. Ka ɗauke shi da tsarki sosai a gare ni.
|
|||
|
|
|||
|
\s5
|
|||
|
\v 37 Wannan turaren da zaka yi, ba zaka yi wani irin sa domin kanka ba. Zai zama mai tsarki sosai a gare ka.
|
|||
|
\v 38 Dukkan wanda ya yi turare irin sa ya yi anfani da shi za a datse shi daga cikin mutanensa."
|
|||
|
|
|||
|
\s5
|
|||
|
\c 31
|
|||
|
\cl Sura 31
|
|||
|
\p
|
|||
|
\v 1 Sai Yahweh ya yi magana da Musa ya ce,
|
|||
|
\v 2 "Duba, na kira sunan Bezalel ɗan Uri ɗan Hour, daga kabilar Yahuda.
|
|||
|
|
|||
|
\s5
|
|||
|
\v 3 Na kuma cika Bezalel da Ruhuna, ya ba shi hikima, basira da ilimi, da dukkan kayayyakin ayyukan hannuwa,
|
|||
|
\v 4 don ya yi fasalin abubuwa da aikin zinariya da azurfa da tagulla;
|
|||
|
\v 5 ya kuma yanka da jera duwatsu da sassaƙa itace -- ya yi kowanne irin aikin fasahar hannu.
|
|||
|
|
|||
|
\s5
|
|||
|
\v 6 Tare da shi, na zaɓi Oholiyab ɗan Ahisamak, daga kabilar Dan. Na sa fasaha a zukatan dukkan masu hikima don su yi dukkan abin dana umarce ka. Wannan ya haɗa da
|
|||
|
\v 7 rumfar taruwa, da akwatin shaida, da abin tuba da yake kan akwatin, da dukkan kayayyakin dake cikin rumfar-
|
|||
|
\v 8 teburi da kayayyakinsa da tsantsa alkuki tare da dukkan kayayyakinsa, da turaren bagadi da
|
|||
|
\v 9 bagadin hadayar konawa da dukkan kayayyakinsa da babbar kwatarniya tare da mazaunin ta.
|
|||
|
|
|||
|
\s5
|
|||
|
\v 10 Wannan ya haɗa da ƙyakkyawan - sakakkun riguna - tsarkakkun tufafin domin Haruna firist da 'ya'yansa maza, na ajiye su domin na, saboda su yi aikin firistoci.
|
|||
|
\v 11 Wannan ya haɗa da man shafewa da turare domin wuri mai tsarki. Waɗannan masu sana'ar hannu dole ne su yi dukkan waɗannan abubuwa kamar yadda na umarce ku."
|
|||
|
|
|||
|
\s5
|
|||
|
\v 12 Sai Yahweh ya yi magana da Musa ya ce,
|
|||
|
\v 13 "Faɗa wa Isra'ilawa: 'Dole ku kiyaye ranakun Asabar na Yahweh, domin dukkan waɗannan za su zama alama tsakanin shi da ku acikin dukkan zuriyar mutanenku har abada don ku sani shi ne Yahweh, wanda ya keɓe ku domin kansa.
|
|||
|
\v 14 Saboda haka dole ku kiyaye Asabar, don ku lura da ita da tsarki, ya keɓe ta dominsa. Duk wanda ya tozarta ta babu shakka kashe shi za a yi. Duk wanda ya yi aiki ranar Asabar, wannan mutum babu shakka za a yanke shi daga mutanensa.
|
|||
|
\v 15 Ku yi aiki a kwana shida kaɗai, amma a rana ta bakwai ranar Asabar ce ku huta, tsattsarka ga Yahweh. Duk wanda ya yi aiki a ranar Asabar babu shakka za a kashe shi.
|
|||
|
|
|||
|
\s5
|
|||
|
\v 16 Saboda haka Isra'ilawa dole su kiyaye Asabar. Dole su kiyaye ta a dukkan tsararrakin mutanensu za ta zama dawwamammar doka.
|
|||
|
\v 17 Asabar za ta zama a kullum alama tsakanin Yahweh da Isra'ilawa, gama a cikin kwana shida Yahweh ya yi sama da ƙasa, a rana ta bakwai kuma ya huta da yin komai.'"
|
|||
|
|
|||
|
\s5
|
|||
|
\v 18 Sa'ad da Allah ya gama magana da Musa a kan Tsaunin Sinai, ya ba shi alluna biyu na alƙawarin ka'idodi, da aka yi da dutse, rubutattu da hannunsa.
|
|||
|
|
|||
|
\s5
|
|||
|
\c 32
|
|||
|
\cl Sura 32
|
|||
|
\p
|
|||
|
\v 1 Da mutanen suka ga Musa ya yi jinkirin dawowa daga tsaunin, sai suka taru kewaye da Haruna, suka ce masa, "Zo, ka yi mana gunki da zai wuce gaban mu. Domin wannan Musa, mutum wanda ya fito damu daga ƙasar Masar, bamu san abin da ya faru da shi ba."
|
|||
|
\v 2 Sai Haruna yace masu, "Ku tuttuɓe zobbanku na zinariya waɗanda suke a kunnuwan matayenku da kunnuwan 'ya'yanku maza da mata ku kawo su gare ni."
|
|||
|
|
|||
|
\s5
|
|||
|
\v 3 Dukkan jama'a suka tuttuɓe zobban da suke a kunnuwansu, suka kawo su wurin Haruna.
|
|||
|
\v 4 Ya karɓi zinariyar daga wurinsu, ya narkar da su, ya mai da shi siffa ta ɗan maraki. Sai mutanen suka ce, "Isra'ila, wannan shi ne allahnku wanda ya fito da ku daga ƙasar Masar."
|
|||
|
|
|||
|
\s5
|
|||
|
\v 5 Sa'ad da Haruna ya ga wannan, ya gina bagadi a gaban siffar marakin ya yi shela; ya ce, "Gobe akwai bikin girmama Yahweh."
|
|||
|
\v 6 Mutane suka tashi da asussuba kashegari suka miƙa hadayu na konawa da bayarwar zumunta. Sai suka zauna suka ci suka sha, sa'an nan suka tashi suna shagalin shashanci.
|
|||
|
|
|||
|
\s5
|
|||
|
\v 7 Sai Yahweh ya yi magana da Musa, "Tafi da sauri, gama mutanenka, waɗanda ka fito da su daga ƙasar Masar, sun ƙazantar da kansu.
|
|||
|
\v 8 Sun yi saurin ƙyale hanyar dana umarce su. Sun yi wa kansu ɗan maraki suna yi masa sujada, suna miƙa masa hadaya. Sun kuma ce, Isra'ila, wannan shi ne allahnka wanda ya fito daku daga ƙasar Masar.'"
|
|||
|
|
|||
|
\s5
|
|||
|
\v 9 Sai Yahweh ya faɗa wa Musa, "Na ga wannan jama'ar. Duba, mutanen nan suna da taurinkai.
|
|||
|
\v 10 Yanzu dai, kada ka yi ƙoƙarin hana ni. Fushina ya yi ƙuna a kansu, saboda haka zan hallaka su. Sai in yi wata babbar al'umma daga gare ka."
|
|||
|
\v 11 Amma Musa ya yi ƙoƙarin roƙon Yahweh Allahnsa. Ya ce, "Yahweh, me ya sa ka husata da mutanenka, waɗanda ka fito da su daga ƙasar Masar da ƙarfin iko da babban hannu?
|
|||
|
|
|||
|
\s5
|
|||
|
\v 12 Me ya sa za ka sa Masarawa su ce, 'Ya sa su sun fito da mugun nufi, don ya kashe su cikin duwatsu ya kuma shafe su daga fuskar duniya?' Ka janye daga zafin fushinka, ka ji tausayi daga wannan hukunci a kan mutanenka.
|
|||
|
\v 13 Ka tuna da Ibrahim da Ishaku da Isra'ila, bayinka, waɗanda kai da kanka ka rantse ka ce, 'Zan riɓaɓɓanya zuriyarka kamar taurarin sammai, in kuma ba zuriyarku dukkan wannan ƙasa wanda na yi maganar ta. Za ku gaje ta har abada.'"
|
|||
|
\v 14 Sai Yahweh ya huce ya janye daga hukuncinsa da ya ce zai sa masifa a kan mutanensa.
|
|||
|
|
|||
|
\s5
|
|||
|
\v 15 Musa kuwa ya juyo ya sauko daga kan tsaunin, yana ɗauke da allunan biyu na shaidar ka'idodi a hannunsa. Allunan rubutattu ne ciki da waje, gaba da baya.
|
|||
|
\v 16 Allunan kuma aikin Allah ne, rubutun kuwa na Allah ne, da ya zana a kan allunan.
|
|||
|
|
|||
|
\s5
|
|||
|
\v 17 Sa'ad da Yoshuwa ya ji hayaniyar mutane kamar suna ihu, ya cewa Musa, "Akwai hargowar yaƙi a zangon."
|
|||
|
\v 18 Amma Musa yace, "Ai ba amon nasara ba ce, ba kuma amon mutanen da aka ci nasara a kansu bane, amma hayaniyar waƙa nake ji."
|
|||
|
|
|||
|
\s5
|
|||
|
\v 19 Sa'ad da Musa ya kusato zangon ya ga siffar ɗan maraki mutane kuma na ta rawa. Ya harzuka da haushi. Ya watsar da allunan da suke hannunwansa suka farfashe a gindin tsaunin.
|
|||
|
\v 20 Ya ɗauki siffar ɗan marakin da mutane suka yi, ya kone ta, ya nike ta zama gari, ya barbada a cikin ruwa. Sa'an nan ya sa mutanen Isra'ila su sha ta.
|
|||
|
|
|||
|
\s5
|
|||
|
\v 21 Musa ya cewa Haruna, "Me waɗannan mutane suka yi maka, da ka jawo babban zunubi a kansu?"
|
|||
|
\v 22 Haruna yace, "Kada ka bar fushinka ya yi ƙuna, ya shugabana. Ka san waɗannan mutane, yadda suke a kan yin mugunta.
|
|||
|
\v 23 Sun ce da ni, 'Ka yi mana allah wanda zai wuce gabanmu. Gama Musa, mutumin da ya fito da mu daga ƙasar Masar, ba mu san abin da ya faru da shi ba.'
|
|||
|
\v 24 Ni kuwa nace da su, 'Duk wanda yake da zinariya, bari ya tuɓe ya kawo ta.' Suka ba ni zinariya ni kuwa na zuba su cikin wuta, daganan wannan maraki ya fito."
|
|||
|
|
|||
|
\s5
|
|||
|
\v 25 Musa ya ga mutanen sun gagara (gama Haruna ya barsu sun fi karfin a shawo kansu, suna sa abokan gãbarsu su yi masu ba'a).
|
|||
|
\v 26 Sai Musa ya tsaya a ƙofar zango ya ce, "Duk wanda yake wajen Yahweh, ya zo wurina." Dukkan Lebiyawa suka tattaru a wurinsa.
|
|||
|
\v 27 Ya ce masu, "Yahweh, Allah na Isra'ila, ya faɗi wannan: 'Bari kowanne mutum ya rataya takobinsa a gefensa da bayansa ya tafi ya dawo daga ƙofa zuwa ƙofa cikin zango kowa kuma ya kashe ɗan'uwansa, ya kashe abokinsa da kuma makwabcinsa.'"
|
|||
|
|
|||
|
\s5
|
|||
|
\v 28 Lebiyawa kuwa suka yi yadda Musa ya umarta. A ranan nan mutane dubu uku suka mutu.
|
|||
|
\v 29 Musa ya cewa Lebiyawa, "Ku bada kanku cikin aikin Yahweh yau, gama kowannenku ya yi gãba da ɗansa da ɗan'uwansa, saboda Yahweh ya iya baku albarka yau."
|
|||
|
|
|||
|
\s5
|
|||
|
\v 30 Washegari Musa ya cewa mutanen, "Kun aikata babban zunubi. Yanzu zan tafi wurin Yahweh. Watakila zan iya yin kafara domin zunubanku."
|
|||
|
\v 31 Musa ya koma wurin Yahweh yace, "Aiya, waɗannan mutane sun aikata zunubi mai girma, sun yi wa kansu gunkin zinariya.
|
|||
|
\v 32 Amma yanzu, idan ka yarda ka gafarta zunubansu; amma idan ba za ka yi ba, ka shafe sunana daga cikin litafin daka rubuta."
|
|||
|
|
|||
|
\s5
|
|||
|
\v 33 Yahweh ya cewa Musa, "Duk wanda ya yi mani zunubi, shi ne kuwa zan shafe sunansa daga cikin littafina.
|
|||
|
\v 34 Saboda haka yanzu ka tafi, ka bida mutanen zuwa wurin da zan faɗa maka. Duba, mala'ikana zai wuce gabanka. Amma a ranar da zan hukuntasu, zan hukuntasu saboda zunubinsu."
|
|||
|
\v 35 Yahweh ya aika da annoba ga mutanen domin sun yi ɗan marakin, da Haruna ya yi.
|
|||
|
|
|||
|
\s5
|
|||
|
\c 33
|
|||
|
\cl Sura 33
|
|||
|
\p
|
|||
|
\v 1 Sai Yahweh ya yi magana da Musa. "Tafi, daganan, kai da mutane waɗanda ka fito da su daga ƙasar Masar. Tafi zuwa ƙasar dana rantse wa Ibrahim, da Ishaku, da Yakubu, da na ce, 'Zan bada ita ga zuriyarku.'
|
|||
|
\v 2 Zan kuma aiki mala'ika a gabanka, zan kori Kan'aniyawa, da Amoriyawa, da Hittiyawa, da Ferizziyawa, da Hibiyawa, da Yebusiyawa.
|
|||
|
\v 3 Tafi zuwa ƙasar, wanda ke fitar da madara da zuma, amma ba zan tafi tare da ku ba, gama ku mutane ne masu taurinkai. Don zan iya hallaka ku a hanya."
|
|||
|
|
|||
|
\s5
|
|||
|
\v 4 Sa'ad da mutane suka ji waɗannan maganganu masu tada hankali, suka damu suka yi nadama babu wanda ya sa kayan ado.
|
|||
|
\v 5 Yahweh yace da Musa, "Faɗa wa Isra'ilawa, 'Ku mutane ne masu taurin kai. Idan na tafi tare daku ɗan lokaci kaɗan, zan hallaka ku. Domin haka yanzu, ku tuɓe kayan adonku don zan iya yin abin dana shawarta da ku.'"
|
|||
|
\v 6 Saboda haka Isra'ilawa ba su sa kayan ado daga Tsaunin Horeb ba har zuwa gaba.
|
|||
|
|
|||
|
\s5
|
|||
|
\v 7 Musa ya ɗauki rumfar ya kafa ta a bayan zango. Ya kuma kira ta da suna rumfar taro. Duk wanda yake neman Yahweh da kowanne abu sai ya tafi rumfar taruwa, wajen zangon.
|
|||
|
\v 8 Duk sa'ad da Musa ya fita daga zango, dukkan mutane nan za su tashi tsaye a ƙofar rumfarsu su kalli Musa har sai ya shiga ciki.
|
|||
|
\v 9 Duk sa'ad da Musa ya shiga rumfa, al'amudin girgije yakan sauko ya tsaya bisa ƙofar rumfar, Yahweh kuwa ya yi magana da Musa.
|
|||
|
|
|||
|
\s5
|
|||
|
\v 10 Duk lokacin da dukkan mutane suka ga al'amudin girgijen nan na tsaye a kofar rumfar, sai su tashi su yi sujada, kowanne mutum a ƙofar rumfarsa.
|
|||
|
\v 11 Yahweh kuwa zai yi magana da Musa fuska da fuska, kamar mutum ne ke magana da abokinsa. Musa kuwa zai koma cikin zango, amma baransa Yoshuwa ɗan Num, saurayin mutum, zai tsaya a rumfar.
|
|||
|
|
|||
|
\s5
|
|||
|
\v 12 Musa ya cewa Yahweh, "Duba, ka faɗa mani cewa, 'Ka fita da mutanen nan a tafiyarsu,' amma ba ka bar ni in san wanda za ka aika tare da ni ba. Ka ce, 'Na san ka ta wurin sunanka, ka kuma sami tagomashi a idanuwana.'
|
|||
|
\v 13 Yanzu idan har na sami tagomashi a idanunka, ka nuna mani hanyoyinka domin in san ka in kuma cigaba da samun tagomashi a idanunka. Ka tuna wannan al'umma mutanenka ne."
|
|||
|
|
|||
|
\s5
|
|||
|
\v 14 Yahweh kuwa ya amsa, "Zan tafi tare da kai, zan kuma baka hutawa."
|
|||
|
\v 15 Musa yace da shi, "Idan ba za ka tafi tare da mu ba, kada ma ka ɗaga mu daga nan.
|
|||
|
\v 16 Domin in ba ta haka ba, ƙaƙa za a sani na sami tagomashi a idanunka, ni da mutanenka? Ba sai ka tafi tare da mu ba, domin ni da mutanenka a ga bambanci daga dukkan sauran jama'ar da suke fuskar duniya?"
|
|||
|
|
|||
|
\s5
|
|||
|
\v 17 Yahweh ya cewa Musa, "Zan kuma yi wannan abu yadda ka roƙa, gama ka sami tagomashi a idanuna, na kuma san ka da suna."
|
|||
|
\v 18 Musa kuwa ya ce, "Idan ka yarda ka nuna mani darajarka."
|
|||
|
|
|||
|
\s5
|
|||
|
\v 19 Yahweh yace, "Zan sa dukkan ɗaukakata ta wuce a gabanka, zan kuma yi alheri ga wanda na yi wa alheri, zan kuma nuna jinkai ga wanda na yi wa jinkai.
|
|||
|
\v 20 Amma Yahweh yace, "Ba za ka iya ganin fuskata ba, gama babu wanda zai gan ni ya rayu."
|
|||
|
|
|||
|
\s5
|
|||
|
\v 21 Yahweh yace, "Duba, a nan ga wani wuri kusa da ni; inda za ka tsaya bisa wannan dutsen.
|
|||
|
\v 22 Sa'ad da ɗaukakata take wucewa, zan sa ka a tsaguwar dutsen, in rufe ka da hunnuna har sai na wuce.
|
|||
|
\v 23 Sa'an nan zan ɗauke hannuna, za ka ga bayana, amma ba za ka ga fuskata ba."
|
|||
|
|
|||
|
\s5
|
|||
|
\c 34
|
|||
|
\cl Sura 34
|
|||
|
\p
|
|||
|
\v 1 Yahweh ya cewa Musa, "Ka datse allunan biyu na dutse kamar allunan farkon. Zan rubuta kalmomin a kan waɗannan allunan yadda suke cikin allunan farkon, allunan da ka farfasa.
|
|||
|
\v 2 Ka yi shiri da safe, ka zo kan Tsaunin Sinai, ka gabatar da kanka gare ni a kan saman tsaunin.
|
|||
|
|
|||
|
\s5
|
|||
|
\v 3 Babu wani da zai zo tare da kai. Kada ka bari a ga wani a ko'ina a kan tsaunin. Kada a bar garken tumaki ko awaki, su yi kiwo a gaban tsaunin."
|
|||
|
\v 4 Sai Musa ya sassaƙa alluna biyu na dutse kamar na farko, ya tashi da sassafe, ya hau kan Tsaunin Sinai, kamar yadda Yahweh ya umarce shi. Musa ya rike allunan na dutse a hannunsa.
|
|||
|
|
|||
|
\s5
|
|||
|
\v 5 Yahweh kuwa ya sauko cikin girgije ya tsaya tare da Musa a can, ya yi shelar sunansa "Yahweh." Yahweh ya wuce ta gabansa ya yi shelar Yahweh,
|
|||
|
\v 6 Yahweh, Allah mai jinkai, mai alheri, mai jinkirin fushi, mai yawan kauna, mai gaskiya,
|
|||
|
\v 7 mai kiyaye alƙawarin aminci ga dubban tsarraraki, mai gafarta mugunta da laifuffuka da zunubai. Gama ba zai kuɓutar da mai mugunta ba. Zai hukunta 'ya'ya da jikoki har tsara ta uku da tsara ta hudu saboda zunubin iyaye."
|
|||
|
|
|||
|
\s5
|
|||
|
\v 8 Musa ya hanzarta ya sukunyar da kansa ƙasa ya yi sujada.
|
|||
|
\v 9 Sai ya ce, "Idan na sami tagomashi a idanunka, Ubangijina, ina roƙonka ka tafi tare da mu, gama waɗannan mutanen suna da taurinkai. Gafarta mana laifinmu da zunubinmu, ka ɗauke mu abin gãdonka."
|
|||
|
|
|||
|
\s5
|
|||
|
\v 10 Yahweh yace, "Duba na kusan yin alƙawari. Gaban dukkan mutanenka, zan aikata al'ajabi irin wanda ba a taba yi ba a cikin dukkan duniya ko a cikin wata al'umma. Dukkan mutanen dake cikinku za su ga aikina, gama abin bantsoro nake yi da ku.
|
|||
|
\v 11 Ku kiyaye abin dana umarce ku yau. Na kusa korar maku Amoriyawa da Kan'aniyawa da Hittiyawa da Ferizziyawa da Hibiyawa da Yebusiyawa.
|
|||
|
|
|||
|
\s5
|
|||
|
\v 12 Ku lura da kada ku yi alƙawari tare da mazaunan ƙasar inda za ku tafi, ko su zama tarko a cikinku.
|
|||
|
\v 13 A maimakon haka dole ku rurrushe bagadansu, ku farfashe al'amudansu na dutse, ku sassare gumakansu.
|
|||
|
\v 14 Gama ba za ku yi wa wani allah sujada ba, domin Yahweh, wanda sunansa mai Kishi, Allah mai kishi ne.
|
|||
|
|
|||
|
\s5
|
|||
|
\v 15 Saboda haka kuyi hankali kada ku ƙulla alƙawari tare da mazaunan ƙasar, domin sun karuwantar da kansu ga allolinsu, kuma suka miƙa hadaya ga allolinsu. Sa'an nan wani daga cikinsu zai gayyace ku kuma za ku ci daga cikin hadayarsa,
|
|||
|
\v 16 sa'an nan kuma za ku ɗauka daga cikin 'ya'yansa mata domin "ya'yanku maza, 'ya'yansa mata za su karuwantar da kansu ga allolinsu, za su kuma sanya 'ya'yanku maza su karuwantar da kansu ga allolinsu.
|
|||
|
\v 17 Kada ku yi wa kanku alloli na zuɓi.
|
|||
|
|
|||
|
\s5
|
|||
|
\v 18 Dole ku kiyaye Bukin Abinci Marar Gami. Kamar yadda na umarce ku, ba za ku ci gurasa marar gami ba har kwana bakwai a kan lokacin da aka sa a watan Abib, gama a watan Abib kuka fito daga cikin Masar.
|
|||
|
|
|||
|
\s5
|
|||
|
\v 19 Dukkan ɗan farin nawa ne, koda ɗan farin mutum ne ko na dabba, dukkan 'ya'yan farin dabbobinku, wato na saniya da tunkiya.
|
|||
|
\v 20 Za ku fanshi ɗan farin jaki da ɗan rago, amma idan kuwa ba za ku fanshi ɗan rago ba, sai ku karya wuyansa. Dole za ku fanshi kowanne ɗan fari 'ya'ya mazanku. Kada wani ya zo gabana da hannu wofi.
|
|||
|
|
|||
|
\s5
|
|||
|
\v 21 Za ku iya yin aiki kwana shida, amma a kan rana ta bakwai dole sai ku huta. Koda lokacin noma ne da lokacin girbi dole ku huta.
|
|||
|
\v 22 Dole ku kuma kiyaye Bukin Makwanni tare da amfanin fari na alkama da kuka cire, kuma dole ku kiyaye bukin Tattarawa a karshen shekara.
|
|||
|
|
|||
|
\s5
|
|||
|
\v 23 Sau uku a cikin shekara dukkan mazajenku dole su hallara a gaban Ubangiji Yahweh, Allah na Isra'ila.
|
|||
|
\v 24 Gama zan kori al'ummai daga gabanku, in faɗaɗa kan iyakokinku. Babu wani da zai yi ƙyashin ƙasarku kamar na su a lokatan da kuka tafi ku bayyana a gaban Yahweh Allahnku sau uku a shekara.
|
|||
|
|
|||
|
\s5
|
|||
|
\v 25 Ba za ku miƙa jinin hadayata tare da wani abu mai gami ba, ko wani nama daga hadaya ta Bikin Ƙetarewa wanda za a bari har zuwa safiya.
|
|||
|
\v 26 Dole ku kawo mai kyau ta nunar farin amfanin gonakinku a cikin gidana. Kada ku yarda ku dafa ɗan akuya da yake shan nonon uwarsa."
|
|||
|
|
|||
|
\s5
|
|||
|
\v 27 Yahweh ya cewa Musa, "Rubuta waɗannan maganganu, gama dai-dai suke da maganganu alƙawarin da ni na ɗauka da Isra'ila."
|
|||
|
\v 28 Musa kuwa yana tare da Yahweh yini arba'in da dare arba'in; bai ci kowanne abinci ba ko ya sha ruwa ba. Ya rubuta maganganun alƙawarin a kan allunan, Dokoki Goma.
|
|||
|
|
|||
|
\s5
|
|||
|
\v 29 Lokacin da Musa ya sauko daga Tsaunin Sinai tare da alluna biyu na alƙawarin a hannunsa, bai sani ba, fuskarsa tana annuri lokacin da yake magana tare da Allah.
|
|||
|
\v 30 Sa'ad da Haruna da Isra'ilawa suka ga fatar fuskar Musa tana annuri, sai suka ji tsoro suka ka sa zuwa kusa da shi.
|
|||
|
\v 31 Amma Musa ya yi magana da Haruna da dukkan shugabannin jama'a su zo gare shi. Musa kuwa ya yi magana da su.
|
|||
|
|
|||
|
\s5
|
|||
|
\v 32 Bayan wannan, dukkan mutanen Isra'ila suka zo wurin Musa, ya faɗa masu dukkan umarnin da Yahweh ya ba shi a Tsaunin Sinai.
|
|||
|
\v 33 Sa'ad da Musa ya gama magana tare da su, sai ya sa mayafi ya rufe fuskarsa.
|
|||
|
|
|||
|
\s5
|
|||
|
\v 34 Duk lokacin da Musa ya je gaban Yahweh ya yi magana da shi, sai ya cire lullubin, har sai ya fito. Idan ya fito, zai faɗawa Isra'ilawa abin da aka umarce shi ya faɗa.
|
|||
|
\v 35 Da Isra'ilawa suka ga fuskar Musa tana haske, sai ya lullube fuskarsa kuma har sai ya koma don ya yi magana tare da Yahweh.
|
|||
|
|
|||
|
\s5
|
|||
|
\c 35
|
|||
|
\cl Sura 35
|
|||
|
\p
|
|||
|
\v 1 Musa ya tattara dukkan jama'ar Isra'ilawa ya ce da su, "Waɗannan su ne abubuwan da Yahweh ya umarce ku da yi.
|
|||
|
\v 2 A rana ta shida za ku yi aiki, amma dominku, rana ta bakwai za ku maida ita rana mai tsarki, ranar Asabar ce ku huta sosai, mai tsarki ta Yahweh. Duk wanda ya yi wani aiki a ranar lalai zai mutu.
|
|||
|
\v 3 Ba za a hura wuta a kowanne gida ba a ranar Asabar."
|
|||
|
|
|||
|
\s5
|
|||
|
\v 4 Musa kuwa ya yi magana da dukkan jama'ar Isra'ilawa, cewa, "Wannan shine abin da Yahweh ya umarta.
|
|||
|
\v 5 Ku karɓi baiko domin Yahweh, dukkan ku wanda ya yi niyya a zuciya. Ku kawo baikon ga Yahweh--zinariya da azurfa da tagulla
|
|||
|
\v 6 da zane shudi da shunayya da mulufi da lallausan zaren lilin da gashin awaki da
|
|||
|
\v 7 fatun raguna da aka rina suka zama ja da fatun awaki da itacen kirya
|
|||
|
\v 8 da man fitila da kayan yaji domin man keɓewa da turaren konawa
|
|||
|
\v 9 da duwatsu masu tamani da duwatsun da za a mammanne a alkyabba da kyallen makalawa a kirji."
|
|||
|
|
|||
|
\s5
|
|||
|
\v 10 Kowanne mutum da yake da fasaha a cikinku ya zo ya yi wani abu ga Yahweh ya umarta-
|
|||
|
\v 11 rumfar sujada da rumfarta, da murfinta da maratayai da katakanta da sandunanta da dirkokinta da kwasfanta
|
|||
|
\v 12 da kuma akwati da sandunansa, da marfin kafara, da labule domin rufewa.
|
|||
|
|
|||
|
\s5
|
|||
|
\v 13 Suka kawo tebur da sandunansa da dukkan kayayyakinsa, kuma da gurasa ta kasancewa,
|
|||
|
\v 14 da alkuki don haske, tare da kayayyakinsa da fitilunansa da man fitilu
|
|||
|
\v 15 da bagadin turaren ƙonawa da sandunansa da man keɓewa mai ƙanshi da turaren ƙonawa da labulen ƙofar rumfa ta sujada
|
|||
|
\v 16 bagadin baye-baye na ƙonawa da ragarsa ta tagulla da sandunansa da kuma kayayyakinsa da babban daro da gammonsa.
|
|||
|
|
|||
|
\s5
|
|||
|
\v 17 Suka kawo labulen domin harabar tare da dirkokinsa da kwasfansu da labulen don ƙofar harabar
|
|||
|
\v 18 da kuma turakun maratayin rumfar da turakun farfajiyar tare da igiyoyinsu.
|
|||
|
\v 19 Suka kawo saƙaƙƙun tufafi na yin aiki a wuri mai tsarki da tsarkakkun tufafi domin Haruna firist da tufafin 'ya'yansa maza na aikin firistoci."
|
|||
|
|
|||
|
\s5
|
|||
|
\v 20 Sai dukkan kabilun Isra'ila suka tashi daga gaban Musa.
|
|||
|
\v 21 Kowanne zuciyarsa ta kada shi da wanda ruhunsa ya iza shi ya yi niyya kawo wa Yahweh baiko domin yin rumfa ta sujada, da dai dukkan ayyuka cikinta da kuma tsarkakkun tufafi.
|
|||
|
\v 22 Suka zo, maza da mata, dukkan waɗanda suke da niyya a zuciya. Suka kawo kayayyakin ƙawanya wato su 'yan kunne da ƙawane da mundaye da kayayyakin dukkan zinariya iri iri. Dukkansu suka bada baikon zinariya kamar su baye-bayen kaɗawa ga Yahweh.
|
|||
|
|
|||
|
\s5
|
|||
|
\v 23 Kowanne mutum da yake da shuɗi ko shunayya ko mulufi ko lallausan lilin ko gashin awaki ko fatun raguna da aka rina suka zama ja ko fatun awaki ya kawo su.
|
|||
|
\v 24 Kowanne ne wanda ya iya yin baikon azurfa da tagulla ga Yahweh, da kowanne wanda aka same shi yana da itacen ƙirya wanda zai zama da amfani a cikin aikin ya kawo shi.
|
|||
|
|
|||
|
\s5
|
|||
|
\v 25 Kowace mace mai fasaha da ta kaɗa zare da hannuwanta ta kawo zaren da ta kaɗa na shuɗi da shunayya da mulufi da lallausan lilin.
|
|||
|
\v 26 Dukkan mataye waɗanda zukatansu suka iza su, suka kaɗa zare da gashin awaki.
|
|||
|
|
|||
|
\s5
|
|||
|
\v 27 Shugabanai suka kawo duwatsu masu daraja da za a jera a kan alkyabba da kyallen makalawa a kirji;
|
|||
|
\v 28 suka kuma kawo kayan yaji da mai don fitilu da mai domin keɓewa da turare mai kanshi don ƙonawa.
|
|||
|
\v 29 Sai Isra'ilawa suka kawo bayarwar yardar rai ga Yahweh; kowanne mutum da mace waɗanda zuciyarsu ta iza su da niyya suka kawo kayayyaki domin dukkan aikin da Yahweh ya umarta ta wurin Musa aka yi shi.
|
|||
|
|
|||
|
\s5
|
|||
|
\v 30 Musa ya cewa Isra'ilawa, "Duba Yahweh ya kira Bezalel ɗan Uri ɗan Hur da sunansa, daga kabilar Yahuda.
|
|||
|
\v 31 Ya cika Bezalel da Ruhunsa, domin ya ba shi hikima da basira da sani da ilimi, don ya iya dukkan kowanne irin aiki,
|
|||
|
\v 32 ya ƙirƙiro zane-zane da aikin zinariya da azurfa da tagulla
|
|||
|
\v 33 da kuma wajen sassaƙar duwatsu na jerawa da sassaƙar itace-ya yi dukkan kowanne irin zane-zane na gwaninta.
|
|||
|
|
|||
|
\s5
|
|||
|
\v 34 Ya sa masa a cikin zuciyarsa ya koyar, shi da Oholiyab dan Ahisamak, daga kabilar Dan.
|
|||
|
\v 35 Ya cika su da fasaha ta yin kowanne irin aiki, da aiki kamar na sassaƙa dana zane-zane dana yin ɗinke-ɗinke da shuɗi da shunayya da mulufi da lallausan lilin dana yin saƙa. Sun iya yin kowanne irin aiki da yin zane-zane.
|
|||
|
|
|||
|
\s5
|
|||
|
\c 36
|
|||
|
\cl Sura 36
|
|||
|
\p
|
|||
|
\v 1 Bezalel da Oholiyab da kowanne mutum mai fasaha waɗanda Yahweh ya ba su fasaha da basira na sanin yin kowanne irin aikin wuri mai tsarki bisa ga dukkan yadda Yahweh ya umarta."
|
|||
|
|
|||
|
\s5
|
|||
|
\v 2 Musa ya kirawo Bezalel da Oholiyab da kowanne mutum mai fasaha wanda Yahweh ya ba shi fasaha a zuciya da dai dukkan wanda zuciyarsa ta iza shi ya zo ya yi aikin.
|
|||
|
\v 3 Su kuwa sun karɓa daga wurin Musa dukkan baye-bayen da Isra'ilawa suka kawo domin aikin wuri mai tsarki. Duk da haka mutane suna kawo baye-bayen yardar ransu kowacce safiya ga Musa.
|
|||
|
\v 4 Sai dukkan mutane masu fasaha suke yin aiki a wuri mai tsarki suka zo daga aikin da suke ta yi.
|
|||
|
|
|||
|
\s5
|
|||
|
\v 5 Masu aikin hannu suka faɗa wa Musa, "Mutane suna ta kawo wa fiye da abin da ake buƙata domin aikin da Yahweh ya umarta a yi."
|
|||
|
\v 6 Sai Musa ya umarce su kada wani a cikin zango ya sake kawo baiko don aikin wuri mai tsarki.
|
|||
|
\v 7 Saboda haka mutane suka dena bada waɗannan kyaututtuka. Sun bada fiye da kayayyakin da ake buƙata domin yin dukkan aikin.
|
|||
|
|
|||
|
\s5
|
|||
|
\v 8 Sai dukkan gwanayen mutane a cikin ma'aikatan suka yi rumfa da labule goman da aka yi daga lallausan zanen lilin da shudi da shunayya da mulufi da kuma zanen kerubim. Wannan shine aikin Bezalel, mai babbar fasahar sassaƙa.
|
|||
|
\v 9 Tsawon kowanne labule kamu ashirin da takwas, faɗinsa kuma kamu hudu ne. Dukkan labule girmansu ɗaya ne.
|
|||
|
\v 10 Bezalel ya haɗa labule biyar ga kowanne ɗayan, sa'an nan kuma ɗayan labule biyar ya kuma haɗa kowanne da ɗan'uwansa.
|
|||
|
|
|||
|
\s5
|
|||
|
\v 11 Ya sa maratayai shuɗi a gefen karshen labule na layin, ya sake yin haka har sau biyu.
|
|||
|
\v 12 Ya sake sa hantuna hamsin a karbun labule na fari, haka kuma ya sa na biyun. Saboda haka dukkan maratayan suna daura da juna.
|
|||
|
\v 13 Ya kuma yi maɗauri hamsin na zinariya, ya harhaɗa labulen da juna da maɗauran saboda rumfar sujadar ta zama ɗaya.
|
|||
|
|
|||
|
\s5
|
|||
|
\v 14 Bezalel ya yi labulai da gashin awaki domin a rufe rumfar; ya yi waɗannan labulai goma sha ɗaya.
|
|||
|
\v 15 Tsawon kowanne labule kamu talatin, faɗinsa kuma kamu huɗu ne. Kowanne ɗaya daga cikin labule goma sha ɗayan girmansu ɗaya ne.
|
|||
|
\v 16 Ya harhaɗa labule biyar wuri ɗaya, labule shida kuma ya harhaɗa su wuri ɗaya da juna.
|
|||
|
\v 17 Sai ya yi hantuna hamsin ya sa a gefe na bisa na labule na farin, haka kuma ya sa maratayai hamsin a gefen sama na labule na biyu.
|
|||
|
|
|||
|
\s5
|
|||
|
\v 18 Bezalel ya yi hamsin maɗaurai da tagulla waɗanda zai harhaɗa maratayan da su domin rumfar ta zama ɗaya.
|
|||
|
\v 19 Ya yi wa rumfar marufi da fatun raguna da aka rina ja, ya kuma sake yin wani abin rufewa na fata mai kyau ya hau sama da shi.
|
|||
|
|
|||
|
\s5
|
|||
|
\v 20 Bezalel ya yi katakan rumfar da itacen ƙirya.
|
|||
|
\v 21 Tsawon kowanne katako kamu goma ne, kaurinsa kuwa kamu ɗaya da rabi ne.
|
|||
|
\v 22 Kowanne katako an feƙe bakinsa biyu domin a harhaɗa su tare. Ya yi wannan domin dukkan katakan rumfar.
|
|||
|
\v 23 Ya yi katakan rumfar ne ta wannan hanya: ya kafa katakai ashirin domin gefen kudu.
|
|||
|
|
|||
|
\s5
|
|||
|
\v 24 Bezalel ya yi kwasfa arba'in da azurfa su shiga ƙarƙashin katakai ashirin. Akwai kuma katako da yana da kwasfa biyu don bakinsa biyu da aka feƙe.
|
|||
|
\v 25 Gama na biyun yana wajen arewa da rumfar, ya kafa katakai ashirin,
|
|||
|
\v 26 kwasfa arba'insu na azurfa. Akwai katako da yake da kwasfa biyu a ƙarƙashin katakon gaba.
|
|||
|
|
|||
|
\s5
|
|||
|
\v 27 Domin bayan rumfar a gefen yamma, Bezalel ya yi tsaikoki shida.
|
|||
|
\v 28 Ya yi kuma katakai biyu don kusurwar baya ta rumfar.
|
|||
|
|
|||
|
\s5
|
|||
|
\v 29 Waɗannan katakai an raba su tun daga ƙasa, amma an haɗa su a sama a ƙawanya ta fari. Haka ya yi da su kusurwoyin nan biyu.
|
|||
|
\v 30 Akwai katakai takwas da kwasfansu na azurfa guda goma sha shida dukkansu, kowanne katako yana ƙarƙashin na fari, katakai biyu kuma suna ƙarƙashin kwasfa ta gaba.
|
|||
|
|
|||
|
\s5
|
|||
|
\v 31 Bezalel ya yi sanduna na itacen ƙirya-sanduna biyar domin katakan gefe ɗaya na rumfar,
|
|||
|
\v 32 sanduna biyar kuwa don katakan ɗaya gefen na rumfar, biyar kuma domin katakan da yake bayan rumfar wajen yamma.
|
|||
|
\v 33 Ya sa sandan da yake a tsakiya ya wuce daga ƙarshe zuwa ƙarshe. Ya dalaye katakan da zinariya.
|
|||
|
\v 34 Ya yi masu ƙawanne na zinariya, don su yi aikin riƙe sarƙafa sandunan, ya kuma dalaye sandunan da zinariya.
|
|||
|
|
|||
|
\s5
|
|||
|
\v 35 Bezalel ya yi labule da shuɗi, da shunayya da mulufi da lallausan zaren lilin, ya kuma yi wa labulen zanen kerubim na aikin gwaninta.
|
|||
|
\v 36 Ya yi wa labulen dirkoki huɗu da itacen ƙirya, sai ya dalaye su da zinariya. Ya kuma yi masu maratayai da zinariya don dirkokin kwasfa huɗu da azurfa.
|
|||
|
|
|||
|
\s5
|
|||
|
\v 37 Ya yi wa ƙofar rumfar labule da shuɗi da shunayya da mulufi da lallausan zaren lilin ya yi wa labulen ado sosai.
|
|||
|
\v 38 Ya kuma haɗa labulen da dirkokinsa biyar. Ya dalaye kawunansu da maɗauransu da zinariya. Kwasfansu guda biyar an dalaye su da tagulla.
|
|||
|
|
|||
|
\s5
|
|||
|
\c 37
|
|||
|
\cl Sura 37
|
|||
|
\p
|
|||
|
\v 1 Bezalel ya yi akwati da itacen ƙirya, tsawonsa kamu biyu da rabi, faɗinsa kamu ɗaya da rabi, tsayinsa kamu ɗaya da rabi.
|
|||
|
\v 2 Ya dalaye shi da zinariya tsantsa ciki da waje, ya kuma yi masa dajiya da zinariya kewaye har sama.
|
|||
|
\v 3 Ya sa ƙawanya huɗu ta zinariya domin kafafunsa huɗu, kawanne biyu a gefensa ɗaya, biyu kuma a ɗaya gefen.
|
|||
|
|
|||
|
\s5
|
|||
|
\v 4 Ya yi sandunan da itacen ƙirya ya kuma dalaye su da zinariya.
|
|||
|
\v 5 Ya zura sandunan cikin ƙawayun da suke a gefen akwatin don ɗaukarsa.
|
|||
|
\v 6 Ya yi murfin kafara da zinariya tsantsa. Tsawonsa kamu biyu da rabi faɗinsa kuma kamu ɗaya da rabi.
|
|||
|
|
|||
|
\s5
|
|||
|
\v 7 Bezalel ya ƙera siffofin kerubobin biyu da zinariya domin ƙarshen kafara biyu.
|
|||
|
\v 8 Kerub ɗaya don ƙarshen kafara, ɗaya kerub kuma domin ƙarshen gefen. An yi su kamar guntu ɗaya ne na murfin.
|
|||
|
\v 9 Kerubobin suka buɗe fikafikansu sama, suka inuwanta murfin da fikakansu. Kerubobin suna fuskantar juna, suna kallon tsakiyar murfin kafara.
|
|||
|
|
|||
|
\s5
|
|||
|
\v 10 Bezalel ya yi tebur da itacen ƙirya. Tsawonsa kamu biyu, faɗinsa kamu ɗaya ne, tsayinsa kamu ɗaya da rabi.
|
|||
|
\v 11 Ya dalaye shi da zinariya tsantsa, ya kuma yi masa dajiya da zinariya tsantsa a kewayan samansa.
|
|||
|
\v 12 Ya yi masa dajiya mai faɗin tafin hannu kewaye da shi, ya kuma yi wata dajiya da zinariya a kewaye da ita.
|
|||
|
\v 13 Ya yi ƙawanye huɗu na zinariya, ya kuma manna kowanne a kursuwoyi huɗu na ƙafafunsa.
|
|||
|
|
|||
|
\s5
|
|||
|
\v 14 Kowannensu na kusa da dajiyar inda za a zura sanduna na ɗaukar teburin.
|
|||
|
\v 15 Ya yi sanduna da itacen ƙirya, ya kuma dalaye su da zinariya domin ɗaukar teburin.
|
|||
|
\v 16 Ya yi kayan da za a ɗora a kan teburin-kwanonin da cokula da kwanonin tuya da butoci waɗanda za ayi baye-baye da su. Ya yi su da zinariya tsantsa.
|
|||
|
|
|||
|
\s5
|
|||
|
\v 17 Ya yi alkuki da zinariya tsantsa. Ya yi alkuki a gindinsa da gorar jikinsa, ƙoƙunan da mahaɗansa da furanninsa dukkansu a haɗe aka yi da ita.
|
|||
|
\v 18 Akwai rassa guda shida daga cikin kowanne gefen-rassa uku daga cikin ɗaya gefen, sa'an nan rassa uku na alkukin daga wancan gefen.
|
|||
|
\v 19 Reshe na fari ya yi da ƙoƙuna uku an yi su kamar tohon almond tare da mahaɗai da furanni da kofuna guda uku wanda aka yi kamar almond ya yi fure a kan reshe da mahaɗan furannin. Tana kamar dukkan rassa shidan daga wajen alkuki.
|
|||
|
|
|||
|
\s5
|
|||
|
\v 20 A bisa alkukinsa, a tsakiyar ƙyauran, akwai kofuna guda huɗu da aka yi su kamar tohon almond da mahaɗai da furanni.
|
|||
|
\v 21 Akwai mahaɗi a ƙarƙashin kowanne reshe biyu biyu-an yi su kamar ɗaya da ita, a ƙarƙashin rassa na biyu biyu-haka nan kuma an yi kamar guda ɗaya a haɗe. Ta wannan hanyar akwai mahaɗi a ƙarƙashin rassa na uku, an yi da maɗauri ɗaya. Haka aka yi don dukkan rassa shida daga cikin alkukin.
|
|||
|
\v 22 Ganyensu da rassan an yi dukka a maɗauri ɗaya, da ƙerarriyar zinariya tsantsa aka yi kome.
|
|||
|
|
|||
|
\s5
|
|||
|
\v 23 Bezalel ya yi alkuki da fitilunsa bakwai da hantsuka da farantansa da zinariya tsantsa.
|
|||
|
\v 24 Ya yi alkuki da kayayyakinsa tare da talanti ɗaya da zinariya tsantsa.
|
|||
|
|
|||
|
\s5
|
|||
|
\v 25 Bezalel ya yi bagadin ƙona turare. Ya yi ta da itacen ƙirya. Tsawonsa kamu ɗaya, faɗinsa kamu ɗaya, murabba'i tsayinsa kuma kamu biyu. Ƙahoninsa an yi su kamar ɗaya ne da shi.
|
|||
|
\v 26 Ya dalaye bagadin da zinariya tsantsa-bisansa da gefensa da ƙahoninsa. Ya kuma kewaye shi da dajiya ta zinariya.
|
|||
|
|
|||
|
\s5
|
|||
|
\v 27 Ya yi masa ƙawanne biyu wanda za a haɗa su da ita a ƙarƙashin dajiya daura da juna. Kowannen su yana riƙe da sandunan da za a ɗauki bagadin.
|
|||
|
\v 28 Ya kuma yi sanduna na itacen ƙirya, ya kuma dalayesu da zinariya.
|
|||
|
\v 29 Ya yi tsattsarkan mai na keɓewa da kuma tsantsa turare mai ƙanshi yadda mai yin turare ya kan yi.
|
|||
|
|
|||
|
\s5
|
|||
|
\c 38
|
|||
|
\cl Sura 38
|
|||
|
\p
|
|||
|
\v 1 Bezalel ya yi bagadin ƙona baye-baye da itacen ƙirya. Tsawonsa kamu biyar faɗinsa kamu biyar - murabba'i ne nan - tsayinsa kuwa kamu uku ne.
|
|||
|
\v 2 Ya yi masa zankaye a kusurwoyinsa huɗu siffar kamar ƙahonnin takarkari. An yi ƙahonnin su haɗe tare da bagadin, ya dalaye shi da tagulla.
|
|||
|
\v 3 Ya yi dukkan kayayyakin domin bagadin-tukwane da cokula da daruna da cokula masu yatsotsi da farantan wuta. Ya kuma yi dukkan kayayyakin da tagulla.
|
|||
|
|
|||
|
\s5
|
|||
|
\v 4 Ya yi raga domin bagadin, an yi aikin ne da tagulla aka sa a ƙarƙashin kanta, yasa ta daga ƙasa zuwa sama.
|
|||
|
\v 5 Ya sa ƙawanyoyi huɗu domin kusurwoyi huɗu na ragar tagulla don zura sandunan.
|
|||
|
|
|||
|
\s5
|
|||
|
\v 6 Bezalel ya yi sanduna da itacen kirya ya kuma dalaye su da tagulla.
|
|||
|
\v 7 Sai ya zura sandunan cikin ƙawanne na gefen bagadin, don ɗaukar shi. Ya yi bagadin da itace sa'an nan ya raba cikinsa.
|
|||
|
|
|||
|
\s5
|
|||
|
\v 8 Bezalel ya yi daron wanka da tagulla da gammonsa na tagulla. Ya yi gammuna daga madubai na mata masu yin aiki a ƙofar rumfar taro.
|
|||
|
|
|||
|
\s5
|
|||
|
\v 9 Ya kuma yi haraba. Ya yi labulenta na gefen kudun harabar da lallausan zaren lilin, tsawonsu kamu ɗari ne.
|
|||
|
\v 10 Labulai suna da dirkokinsu ashirin, tare da tagulla a ƙarƙashin kwasfan ashirin. Akwai maratayan dirkoki, da maɗaurai da aka yi da azurfa.
|
|||
|
|
|||
|
\s5
|
|||
|
\v 11 Kamar yadda yake gefen arewa, akwai labule kamu ɗari da sanduna masu kamu ashirin na tagulla, maɗauran sanduna ƙarafuna na azurfa.
|
|||
|
\v 12 Labule na gefen yamma kamu hamsin ne, dirkokinsa kuwa guda goma ne. Maɗaurai da dirkokin ƙarafuna na azurfa ne.
|
|||
|
|
|||
|
\s5
|
|||
|
\v 13 Tsawon harabar kamu hamsin ne wajen gabas.
|
|||
|
\v 14 Labulai na gefe ɗaya na ƙofar kamu goma sha biyar ne. Suna da dirkoki guda uku tare da kwasfan dirkoki uku.
|
|||
|
\v 15 A gefen ƙofar farfajiyar akwai labule masu tsawo kamu goma sha biyar da dirkoki uku da kuma kwasfan uku.
|
|||
|
\v 16 Dukkan labulai da suke kewaye da harabar an yi su da lallausan zaren lilin.
|
|||
|
|
|||
|
\s5
|
|||
|
\v 17 An yi kwasfan dirkoki da tagulla. Maratayan dirkoki da maɗauransu an yi su ne da azufa. Dukkan dirkokin farfajiyoyin an dalaye su da azurfa, kuma marufan dirkokin suma an yi su da azurfa. Dukkan harabar dirkokan an dalaye su da azurfa.
|
|||
|
\v 18 Labulan ƙofar harabar kamu ashirin tsayinsa. Labulen an yi su da shudi da na shunayya da na mulufi da na lallausan zaren lilin.
|
|||
|
\v 19 Tsawonsa kamu ashirin, tsayinsa kamu biyar dai-dai da labulen haraba. An yi dirkokin labulen guda huɗu da kwasfan dirkoki na azurfa. An dalaye kawunansu da maɗauransu da azurfa.
|
|||
|
\v 20 Dukkan turakun rumfa da harabar an yi su da tagulla,
|
|||
|
|
|||
|
\s5
|
|||
|
\v 21 Wannan shi ne lissafin abubuwan da aka yi na rumfa, rumfar alƙawarin ka'idodi, kamar yadda aka yi bisa ga yadda Musa ya yi umarni. Wannan aikin Lebiyawa ne a ƙarƙashin jagorancin Itamar ɗan Haruna firist.
|
|||
|
\v 22 Bezalel ɗan Uri ɗan Hur daga kabilar Yahuda, an yi dukkan abin da Yahweh ya umarci Musa.
|
|||
|
\v 23 Oholiyab ɗan Ahisamak daga kabilar Dan, wanda ya yi aiki tare da Bezalel gwani ne, cikakken ma'aikacin zane-zane da ɗinki na shuɗi, da na shunayya da na mulufi da na lallausan zaren lilin.
|
|||
|
|
|||
|
\s5
|
|||
|
\v 24 Dukkan zinariya da aka yi aikace-aikacen da ita don wannan aiki, a cikin dukka aikin wanda ya haɗa da wuri mai tsarki - zinariya daga baikon bankwana - talanti ashirin da tara ne da awo 730 bisa ga ma'aunin kuɗin da ake aiki da shi.
|
|||
|
\v 25 Azurfar da aka samu ta wurin taron mutane awonsa talanti ɗari ne da awo 1,775, bisa ga ma'aunin kuɗin da ake aiki da shi,
|
|||
|
\v 26 ko kowanne mutum da aka ƙidaya ya bada rabin awo. Wannan adadin abin da aka samu bisa kowanne mutum wanda aka ƙidaya ta ƙasa, waɗanda sun kai 603,550 daga shekara ashirin zuwa gaba manya da tsoffafi na dukkan maza.
|
|||
|
|
|||
|
\s5
|
|||
|
\v 27 An yi amfani da azurfa talanti ɗari domin yin kwasfa don wuri mai tsarki da labule-an yi kwasfa ɗari da talanti ɗaya don kowanne kwasfa.
|
|||
|
\v 28 Sauran 1,775 na awon azurfa, Bezalel yayi maratayan dirkokin, ya dalaye saman maratayan dirkoki ya kuma yi da ƙarafuna dominsu.
|
|||
|
\v 29 Tagulla daga abin da aka bayar kuwa talati saba'in da awo 2,400.
|
|||
|
|
|||
|
\s5
|
|||
|
\v 30 Tare da wannan ya yi kwasfa domin ƙofar rumfar taruwa, da tagullar bagadi, da tagulla aka yi ragarsa, da dukkan kayayyakin bagadin,
|
|||
|
\v 31 Kwasfa domin harabar, da kwasfa don ƙofar harabar, da dukkan turakun don rumfar sujada da na dukkan turakun harabar.
|
|||
|
|
|||
|
\s5
|
|||
|
\c 39
|
|||
|
\cl Sura 39
|
|||
|
\p
|
|||
|
\v 1 Tare da shuɗi da shunayya da mulufi, suka ɗinka tufafi masu kyau domin aiki a wuri mai tsarki. Sun yi wa Haruna tsarkakun tufafi domin wuri mai tsarki, kamar yadda Yahweh ya umarci Musa.
|
|||
|
|
|||
|
\s5
|
|||
|
\v 2 Bezalel ya yi falmarar da zinariya, da shuɗi da shunayya da mulufi da lallausan lilin.
|
|||
|
\v 3 Suka buga zinariya falle-falle, suka yanyanka ta zare-zare don su yi aikin saƙa da ita tare da zane na shuɗi da shunayya da mulufi da kuma na lallausan lilin, aikin gwani mai fasaha ne.
|
|||
|
|
|||
|
\s5
|
|||
|
\v 4 Suka yi aikin kafaɗu domin falmara, sa'an nan suka haɗa su a gefenta biyu na sama.
|
|||
|
\v 5 An yi anfani da ɗamarar falmarar ta saƙa mai kyau; da irin kayan da aka saƙa falmara ne aka saƙa su da zinariya da shuɗi da shunayya da mulufi da zane lallausan lilin, kamar yadda Yahweh ya umarci Musa.
|
|||
|
|
|||
|
\s5
|
|||
|
\v 6 Sun gyaggyarta duwatsu masu daraja aka jera su a tsaiko, aka zana sunayen 'ya'yan Isra'ila goma sha biyu.
|
|||
|
\v 7 Bezalel ya sa a kan kafaɗun falmarar don su zama duwatsun tunawa da Isra'ila, kamar yadda Yahweh ya umarci Musa.
|
|||
|
|
|||
|
\s5
|
|||
|
\v 8 Ya kuma yi ƙyallen maƙalawa a ƙirji, an yi amfani da gwaninta kamar yadda aka yi wa falmarar. Ya yi ta da zinariya da shuɗi da shunayya da mulufi da lallausan lilin.
|
|||
|
\v 9 Tana nan murabba'i. An yi ƙyallen maƙalawa a kirji riɓi biyu. tsawonsa da faɗinsa kamu ɗaya ne.
|
|||
|
|
|||
|
\s5
|
|||
|
\v 10 Suka sa jeri huɗu na duwatsu masu daraja a bisansa. Jeri na fari aka sa yakutu da tofaz da ganat.
|
|||
|
\v 11 A jeri na biyu aka sa emeral da saffir da lu'u-lu'u.
|
|||
|
\v 12 A jeri na uku aka sa yakinta da idon mage da ametis.
|
|||
|
\v 13 A jeri na huɗu aka sa beril da onis da yasfa. Duwatsun an yi masu maɗauki da zinariya.
|
|||
|
|
|||
|
\s5
|
|||
|
\v 14 An jera duwatsun bisa sunayen 'ya'yan Isra'ila goma sha biyu, kowanne bisa ga yadda sunansa yake. Suna kamar yadda a kan yi hatimin zoɓe, kowanne suna ya tsaya domin ɗaya daga cikin kabilu goma sha biyu.
|
|||
|
\v 15 A kan kirjin sai suka yi tukakkun sarƙoƙi kamar igiyoyin amara da aikinsa zinariya tsantsa.
|
|||
|
\v 16 Sai suka yi tsaiko biyu na zinariya da ƙawanyu biyu na zinariya, suka sa ƙawanen nan biyu a gefe biyu na ƙyallen maƙalawa a ƙirji.
|
|||
|
|
|||
|
\s5
|
|||
|
\v 17 Suka kuma zura sarkokin nan biyu na zinariya a kowannen biyu na ƙyallen maƙalawa a ƙirji.
|
|||
|
\v 18 Sai suka maƙala waɗancan a bakin sarƙoƙin biyu. Sa'an nan suka rataya su a kafaɗun falmarar daga gaba.
|
|||
|
|
|||
|
\s5
|
|||
|
\v 19 Suka yi ƙawanne biyu na zinariya, suka sa su a gefe biyu na kyallen maƙalawa a ƙirji daga ciki kusa da falmaran.
|
|||
|
\v 20 Suka yi waɗansu ƙawanne biyu na zinariya, suka maƙala su kusa a gaban kafaɗu biyu na falmarar kusa da mahaɗin a bisa abin damarar falmarar.
|
|||
|
|
|||
|
\s5
|
|||
|
\v 21 Sai suka ɗaure ƙawanyun kyallen maƙalawa a ƙirji a ƙawanyun falmarar da shuɗiyar igiya saboda kyallen maƙalawa a ƙirji ya kwanta lif a bisa kan abin damarar. An yi wannan don kada falmarar ya kwance daga ƙirjin falmarar. Wannan ya faru ne kamar yadda Yahweh ya umarci Musa.
|
|||
|
|
|||
|
\s5
|
|||
|
\v 22 Bezalel ya saka taguwa ta falmaran da shuɗi ga baki ɗaya, aikin masaƙi ne.
|
|||
|
\v 23 An yi wa taguwar wuya wurin sa kai a tsakiya. An yi wa wayan saƙa saboda kada ta yage.
|
|||
|
\v 24 A ƙasan taguwar, sai suka yi fasalin 'ya'yan rumman da shuɗi, shunayya, da mulufi da lallausan lilin.
|
|||
|
|
|||
|
\s5
|
|||
|
\v 25 Suka yi kararrawa da zinariya tsantsa, suka sa su a tsakankanin rumman dukka kewaye a ƙasa da bakin igiyar, tsakanin rumman --
|
|||
|
\v 26 an sa ƙararrawa da rumman, ƙararrawar da rumman -- a bakin igiya domin Haruna ya yi hidima a ciki. Wannan bisa ga yadda Yahweh ya umarci Musa.
|
|||
|
|
|||
|
\s5
|
|||
|
\v 27 Suka saƙa janfofi da lallausan zaren lilin saboda Haruna da 'ya'yansa.
|
|||
|
\v 28 Suka kuma yi rawani da lallausan lilin, da huluna da mukura da lallausan lilin, da mukurai da lallausan lilin.
|
|||
|
\v 29 Sun kuma yi abin damara da lallausan lilin mai launin shuɗi da shunayya da mulufi, an yi mata dinkin ado. Wannan an yi shi kamar yadda Yahweh ya umarci Musa.
|
|||
|
|
|||
|
\s5
|
|||
|
\v 30 Suka yi allo tsattsarka da zinariya tsantsa suka zana rubutu a kan ta, irin na hatimi a kanta, "Mai Tsarki ga Yahweh."
|
|||
|
\v 31 Suka ɗaura shi da shuɗiyar igiya a gaban rawanin. Wannan an yi shi yadda Yahweh ya umarci Musa.
|
|||
|
|
|||
|
\s5
|
|||
|
\v 32 Haka kuma aka yi aikin rumfar sujada, da rumfar taruwa, kuma an gama ta. Mutanen Isra'ila suka yi shi dukka. Suka bi dukkan umarnin da Yahweh ya ba Musa.
|
|||
|
\v 33 Suka kawo wa Musa rumfar sujada - rumfar da dukkan kayayyakinta, maratayanta da katakanta da sandunanta da dirkokinta da kwasfanta
|
|||
|
\v 34 da murfi na jan fatun raguna da na awaki da labulen rufewa
|
|||
|
\v 35 da akwatin alƙawari da sandunansa da murfin kafara.
|
|||
|
|
|||
|
\s5
|
|||
|
\v 36 Suka kawo tebur da dukkan kayayyakinsa da gurasar ajiyewa
|
|||
|
\v 37 da alkuki na zinariya tsantsa da fitilunsa, tare da kayayyakinsa da mai domin fitilu
|
|||
|
\v 38 da bagadin zinariya da mai na keɓewa da turare mai ƙanshi da labulen ƙofar rumfar sujada
|
|||
|
\v 39 da bagadin tagulla da ragarsa ta tagulla da sandunansa da kayayyakinsa da daro da gammonsa.
|
|||
|
|
|||
|
\s5
|
|||
|
\v 40 Suka kawo labulen harabar da dirakunta da kwasfanta da labulen ƙofarta da igiyoyinta da turakunta da dukkan kayayyaki don aiki a rumfar sujada da rumfar taruwa.
|
|||
|
\v 41 Suka kawo tufafin ado na aiki a wuri mai tsarki da tsarkakan tufafin domin Haruna firist da tufafin 'ya'yansa maza, domin su yi aiki a matsayin firistoci.
|
|||
|
|
|||
|
\s5
|
|||
|
\v 42 Mutanen Isra'ila suka yi dukkan wannan aiki yadda Yahweh ya umarci Musa.
|
|||
|
\v 43 Musa ya duba dukkan aikin, duba, sun yi shi dai-dai. Yadda Yahweh ya umarta, ta wannan hanya suka yi shi. Sai Musa ya sa masu albarka.
|
|||
|
|
|||
|
\s5
|
|||
|
\c 40
|
|||
|
\cl Sura 40
|
|||
|
\p
|
|||
|
\v 1 Sai Yahweh ya yi magana da Musa, cewa,
|
|||
|
\v 2 "A kan rana ta fari a wata na fari a sabuwar shekara dole ka kafa rumfar sujada, rumfar taruwa.
|
|||
|
|
|||
|
\s5
|
|||
|
\v 3 Ka sa akwatin alƙawari a cikin ta sa'an nan ka kare akwatin da labule.
|
|||
|
\v 4 Ka shigar da tebur, ka shirya shi yadda ya kamata da kayayyakinsa dai-dai. Ka kuma shigar da alkukin da fitilu a bisansa.
|
|||
|
|
|||
|
\s5
|
|||
|
\v 5 Ka ajiye bagadi na zinariya na ƙona turare a gaban akwatin alƙawari, sa'an nan ka rataya labulen ƙofar rumfar sujada.
|
|||
|
\v 6 Ka ajiye bagadi na yin baikon ƙonawa a gaban ƙofar rumfar taruwa.
|
|||
|
\v 7 Ka kuma ajiye daro tsakanin rumfar taruwa da bagadin sa'an nan ka zuba ruwa a cikin shi.
|
|||
|
|
|||
|
\s5
|
|||
|
\v 8 Ka yi harabar ka kewaye ta, sa'an nan ka rataya labulen ƙofar harabar.
|
|||
|
\v 9 Ka ɗauki man keɓewa, ka shafa wa rumfar sujada da kome dake cikinta. Ka tsarkake ta da dukkan kayayyakinta gare ni, ta kuma zama tsarkakkiya.
|
|||
|
\v 10 Ka shafe bagadin domin ƙona hadaya da dukkan kayayyakinsa. Za ka tsarkake bagadin a gare ni, zai zama mafi tsarki gare ni.
|
|||
|
\v 11 Ka shafa wa daron tagulla da mazauninsa man keɓewa a gare ni.
|
|||
|
|
|||
|
\s5
|
|||
|
\v 12 Ka kawo Haruna da 'ya'yansa maza a ƙofar rumfar taruwa, kuma dole ka yi masu wanka da ruwa.
|
|||
|
\v 13 Sa'an nan ka sa wa Haruna tufafi masu tsarki ka shafa masa man domin ka tsarkake shi ya yi mani aikin firist.
|
|||
|
|
|||
|
\s5
|
|||
|
\v 14 Ka kawo 'ya'yansa maza, ka kuma sa masu taguwoyi.
|
|||
|
\v 15 Sa'an nan ka shafe su da mai kamar yadda ka shafe mahaifinsu saboda su yi mani aiki a matsayin firistoci. Shafe su da man zai sa su zama firistoci din-din din cikin dukkan tsararrakin mutanen su.
|
|||
|
\v 16 Wannan shine abin da Musa ya yi; ya bi dukkan umarnin da Yahweh ya ba shi. Ya yi dukkan waɗannan abubuwa.
|
|||
|
|
|||
|
\s5
|
|||
|
\v 17 Sai aka kafa rumfar sujadar a kan rana ta fari a wata na fari a sheka ta biyu.
|
|||
|
\v 18 Musa ya kafa rumfar sujadar, ya kafa kwasfanta, ya jera katakanta, ya sa mata sandunanta, ya kakkafa dirkokinta.
|
|||
|
\v 19 Sa'an nan ya baza shinfiɗa a bisa rumfar sujadar ya sanya rumfa a bisan ta, kamar yadda Yahweh ya umarce shi.
|
|||
|
\v 20 Sai ya ɗauki dokokin alƙawaran ka'idodi ya sa a cikin akwatin. Ya kuma zura sandunan a ƙawanen akwatin, sa'an nan ya sa murfin kafara a bisansa.
|
|||
|
|
|||
|
\s5
|
|||
|
\v 21 Ya kawo akwatin a cikin rumfar sujada. Sa'an nan ya sa labulen domin kare akwatin alƙawari yadda Yahweh ya umarce shi.
|
|||
|
\v 22 Ya sa teburin cikin rumfar taruwa, a wajen gefen arewa na rumfar sujada, a wajen labulen.
|
|||
|
\v 23 Sai ya jera gurasa a kan teburin a gaban Yahweh, yadda Yahweh ya umarce shi.
|
|||
|
|
|||
|
\s5
|
|||
|
\v 24 Ya kuma sa alkukin a cikin rumfar taruwa, daura da gaban tebur, a wajen kudu na rumfar sujada.
|
|||
|
\v 25 Ya kunna fitilu a gaban Yahweh, yadda Yahweh ya umarce shi.
|
|||
|
|
|||
|
\s5
|
|||
|
\v 26 Sai ya sa zinariyar turaren bagadi a cikin rumfar taruwa a gaban labule.
|
|||
|
\v 27 Ya ƙona turare a kanta, yadda Yahweh ya umarce shi.
|
|||
|
|
|||
|
\s5
|
|||
|
\v 28 Ya sa labule a ƙofar rumfar sujada.
|
|||
|
\v 29 Ya kuwa sa bagadi domin ƙona hadaya a ƙofar rumfar sujada da rumfar taruwa. Ya kuma miƙa hadaya ta ƙonawa da hadayar gari, yadda Yahweh ya umarce shi.
|
|||
|
\v 30 Ya sa daro a tsakanin rumfar taruwa da rumfar sujada, ya kuma sa ruwa a cikinta domin wankewa.
|
|||
|
|
|||
|
\s5
|
|||
|
\v 31 Musa da Haruna da 'ya'yansa maza su kan wanke hannuwansu da ƙafafuwansu daga daron,
|
|||
|
\v 32 sa'ad da suke shiga cikin rumfar taruwa, da sa'ad da su kan tafi bisa bagadi, yadda Yahweh ya umarci Musa.
|
|||
|
\v 33 Musa kuwa ya yi haraba kewaye da rumfar sujada da bagadin. Ya sa labulen ƙofar harabar. Ta wannan hanya, Musa ya gama aikin.
|
|||
|
|
|||
|
\s5
|
|||
|
\v 34 Sa'ad da girgije ya rufe rumfar taruwar, sai ɗaukakar Yahweh ta cika rumfar sujada.
|
|||
|
\v 35 Musa kuwa bai iya shiga rumfar taruwa ba gama girgijen yana zaune a bisanta, kuma saboda ɗaukakar Yahweh ta cika rumfar sujadar.
|
|||
|
|
|||
|
\s5
|
|||
|
\v 36 Duk lokacin da aka ɗauke girgijen daga kan rumfar sujadar, mutanen Isra'ila su kan kama hanya domin tafiya.
|
|||
|
\v 37 Amma idan girgijen bai tashi daga rumfar sujadar ba, mutanen ba za su iya tafiya ba. Za su tsaya har ranar da ya tashi.
|
|||
|
\v 38 Gama girgijen Yahweh yana bisa kan rumfar sujada da rana, haka nan wutarsa ta na bisan shi da dare, wannan ya sa dukkan mutanen Isra'ila suka yi tafiyarsu ko'ina.
|