forked from WA-Catalog/ha_ulb
39 lines
3.3 KiB
Plaintext
39 lines
3.3 KiB
Plaintext
\id OBA
|
|
\ide UTF-8
|
|
\h Littafin Obadiya
|
|
\toc1 Littafin Obadiya
|
|
\toc2 Littafin Obadiya
|
|
\toc3 oba
|
|
\mt Littafin Obadiya
|
|
\c 1
|
|
\cl Sura 1
|
|
\p
|
|
\v 1 Wahayin Obadiya. Ubangiji Yahweh ya faɗi haka a kan Idom: Mun ji bayani daga wurin Yahweh cewa an aika da jakada a cikin al'ummai, da cewa, "Tashi tsaye! Bari mu tashi mu kai mata hari!"
|
|
\p
|
|
\v 2 Ga shi zan mayar dake 'yar ƙarama a cikin al'ummai, za a rena ki ƙwarai.
|
|
\v 3 Girman kai na zuciyarki ya ruɗe ki, ke da ki ke zaune a can cikin kogunan dutse, cikin ƙayataccen gidanki; a cikin zuciyarki, kin ce, "Wane ne zai saukar da ni can ƙasa?"
|
|
\v 4 Ko da zaki tashi sama kamar gaggafa, ko da zaki kai sheƙarki cikin taurari, zan sauko dake ƙasa, inji Yahweh.
|
|
\p
|
|
\v 5 Idan ɓarayi suka zo wurinki, idan 'yan fashi suka zo wurinki da daddare - dubi yadda za a maishe ki kufai! - ba za su saci abin da suke buƙata ba ne kawai? Idan masu tattara inabi suka zo, ba zasu rage kala ba?
|
|
\v 6 Yadda aka bincike Isuwa, harma da abin da ya ɓoye dukka an bincike!
|
|
\v 7 Dukkan mazajen da suka ƙulla amana da ke zasu kore ki har kan iyaka, mazajen da suke zaune lafiya da ke sun ruɗe ki, sun ci nasara a kan ki. Waɗanda suka ci abincinki sun ɗana maki tarko. Babu fahimta a cikinsa.
|
|
\p
|
|
\v 8 Yahweh yace a waccan rana, "Ba zan ce a hallaka ma su hikima daga cikin Idom ba, da masu ganewa daga cikin dutsen Isuwa ba?"
|
|
\v 9 Jarumawanki zasu karaya, Teman, domin a datse kowanne mutum daga dutsen Isuwa ta wurin yankawa.
|
|
\p
|
|
\v 10 Saboda ta'addancin da aka yi wa ɗan'uwanki Yakubu, kunya za ta rufe ki, za a datse ki har abada.
|
|
\v 11 A ranar da ki ka tsaya a ware ke kaɗai, a ranar da bãƙi suka kwashe dukiyarsa, bãƙi suka shiga ƙofofinsa, suka jefa ƙuri'a a kan Yerusalem, kema ki na kamar su.
|
|
\v 12 Amma kada ki yi murna a cikin ranar ɗan'uwanki, a ranar da ya yi asara, kuma kada ki yi farinciki a kan mutanen Yahuda a ranar hallakarsu; kada ki yi fahariya a ranar baƙincikinsu.
|
|
\v 13 Kada ki shiga ƙofar mutanena a ranar masifarsu; kada ki yi murna a cikin ƙuncinsu a ranar bala'insu; kada ki washe dukiyarsu a ranar rushewarsu.
|
|
\v 14 Kada ki tsaya a mararrabar hanyoyi, domin ki datse masu neman tsira da miƙa kuɓutattun mutanensa a ranar ƙuncinsu.
|
|
\p
|
|
\v 15 Gama ranar Yahweh ta kusa a kan dukkan al'ummai. Kamar yadda ki ka yi, haka za a yi maki, abin da kika yi zai dawo kanki.
|
|
\v 16 Kamar yadda kika sha a kan dutsena mai tsarki, haka dukkan al'ummai za suyi ta sha. Za su sha su haɗiye su zama kamar basu taɓa kasancewa ba.
|
|
\p
|
|
\v 17 Amma a Dutsen Sihiyona za a sami waɗanda suka tsira, kuma zai zama da tsarki; gidan Yakubu kuma zasu mallaki mallakarsu.
|
|
\v 18 Gidan Yakubu zai zama wuta, gidan Yosef kuma zai zama harshen wuta mai ci, gidan Isuwa kuma zai zama tattaka, za a ƙone su a hallakar da su. Ba wanda zai tsira daga gidan Isuwa, gama Yahweh ya faɗi."
|
|
\p
|
|
\v 19 Waɗanda suke daga Negeb zasu mallaki dutsen Isuwa, na Sefilah kuma za su mallake ƙasar Filistiyawa. Za su mallaki ƙasar Ifraim da ƙasar Samariya; shi kuma Benyamin zai mallaki Giliyad.
|
|
\v 20 Masu zaman bauta na mutanen Isra'ila masu yawa zasu mallaki ƙasar Kan'ana har zuwa Zerefat. Masu zaman bauta na Yerusalem, waɗanda ke Sefarad zasu mallaki biranen Negeb.
|
|
\v 21 Masu kuɓutarwa za su hau zuwa Dutsen Sihiyona za su yi mulki a ƙasar kan tudu ta Isuwa, mulkin kuma zai zama na Yahweh.
|