\v 8 Saboda haka, ko da ya ke ina da gabagadi a cikin Almasihu domin in ba ka umarni ka yi abinda ya kamata ka yi,
\v 9 duk da haka sabo da kauna, na fi so in roke ka- Ni, Bulus, dattijo, a yanzu kuma ga ni dan kurkuku domin Almasihu Yesu.
\v 10 Ina rokon ka saboda da na Onisimus, wanda na zama uba a gare shi sa'adda nake cikin sarkokina.
\v 11 Domin a da kam, ba shi da amfani a wurin ka, amma yanzu yana da amfani a gare ka da kuma a gare ni.
\v 12 Na kuma aike shi wurinka, shi wanda ya ke a cikin zuciyata kwarai.
\v 13 Na so da na rike shi a wuri na, domin ya rika yi mini hidima a madadin ka, a lokacin da ni ke cikin sarkoki saboda bishara.
\v 14 Amma ba na so in yi wani abu ba tare da sanin ka ba. Ba ni so nagarin aikinka ya zama na dole amma daga kyakkyawar nufi.
\v 15 Watakila dalilin da yasa ya rabu da kai na dan lokaci ke nan, domin ka karbe shi kuma har abada.
\v 16 Daga yanzu ba za ya zama bawa ba kuma, amma fiye da bawa, wato kaunataccen dan'uwa. Shi kaunatacce ne musamman a gare ni, har fiye da haka ma a gare ka, a cikin jiki da kuma cikin Ubangiji.
\v 17 Idan ka maishe ni abokin hidima, ka karbe shi kamar yadda za ka karbe ni.
\v 18 Idan kuwa ya yi maka abinda ba daidai ba ko kuwa kana bin sa wani abu, ka dauka yana wurina.
\v 19 Ni, Bulus, na rubuta wannan da hannuna: zan biya ka. Ba kuwa cewa sai na gaya maka cewa ina bin ka bashin kanka ba.
\v 20 I, dan'uwa, ka yi mani alheri cikin Ubangiji; ka ba zuciyata hutu a cikin Almasihu.