ha_jer_tn_l3/18/15.txt

14 lines
1.1 KiB
Plaintext

[
{
"title": "sasu tuntuɓe a cikin tafarkunsu",
"body": "Yahweh yana maganar salon rayuwar mutum kamar wata hanya ce da yake tafiya, da kuma\nrayuwa rashin aminci a gare shi kamar dai mutumin ya yi tuntuɓe ne a kan hanyar. Ana iya\nbayyana wannan ta hanyar aiki. AT: \"wannan ya sa suka yi tuntuɓe a hanyoyinsu\"\nko \"yana kama da sun yi tuntuɓe yayin tafiya a kan hanya\" (Duba: figs_activepassive)"
},
{
"title": "Zan warwatsa su gaban maƙiyansu kamar iskar gabas",
"body": "Yahweh yayi magana akan sa mutane su gudu a gaban abokan gabansu kamar dai shi ne iskar\ngabas mai watsa ƙura da tarkace. AT: \"Zan kasance kamar iskar gabas in\nwarwatsa su a gaban abokan gabansu\" ko \"Zan watsa su a gaban abokan gabansu kamar\nyadda iskar gabas take watsa ƙura da tarkace\" (Duba: figs_simile)"
},
{
"title": "Zan nuna masu bayana, amma ba fuskata ba, a ranar masifarsu",
"body": "\"Zan juya wa su baya, ba fuskata ba.\" Juya baya ga wani aiki ne na alama wanda ke wakiltar\nƙin yarda da juya fuska ga wani aiki ne na alama wanda ke wakiltar ni'ima. AT:\n\"Zan ƙi su kuma ba zan yi musu alheri ba\" (Duba: translate_symaction)"
}
]