ha_isa_tn_l3/34/05.txt

14 lines
1.1 KiB
Plaintext

[
{
"title": "Sa'ad da takobina ya sha ya ƙoshi a sama",
"body": "Yahweh ya bayyana kansa a matsayin jarumi mai ɗaukar takobi. Kalmar \"sha ta cika\" tana\nmagana ne game da takobin Yahweh kamar dai mutum ne wanda ya ci ya ƙoshi. Yahweh yayi\namfani da wannan hoton don ya nanata cewa za a yi halaka mai yawa a sama kuma a faɗi\nyadda aka gama. AT: \"idan na gama lalata abubuwa a sama\" (Duba: figs_metaphor da figs_personification)"
},
{
"title": "yanzu zai gangara a kan Idom, akan mutanen da na keɓe domin hallakarwa",
"body": "Kalmar \"shi\" tana nufin takobin Yahweh. Wannan yana ci gaba da kwatanci game da Yahweh\nyana lalata abubuwa da takobi. AT: \"Zan zo in hukunta mutanen Idom, mutanen\nda na keɓe domin in hallaka\" (Duba: figs_metaphor)"
},
{
"title": "Gama Yahweh yana da hadaya a Bozra da kuma babban yanka a ƙasar Idom",
"body": "Za a iya bayyana kalmomin \"sadaukarwa\" da \"yanka\" a nan kamar kalmomin aiki. AT: \"Gama Yahweh zai sadaukar da mutane da yawa a Bozra kuma ya kashe mutane da\nyawa a ƙasar Edom\" (Duba: figs_abstractnouns)"
}
]