ha_isa_tn_l3/29/03.txt

14 lines
1001 B
Plaintext

[
{
"title": "Zan kafa dãga gãba dake",
"body": "Kalmar \"zan\" tana nufin Yahweh. Wannan yana wakiltar Yahweh ne wanda ya sa sojojin abokan\ngaba suka kewaye Yerusalem. AT: \"Zan umarci sojojin magabtanku su kewaye\nku\" (Duba: figs_metonymy)"
},
{
"title": "Za a jawo ki ƙasa",
"body": "Ana iya bayyana wannan ta hanyar aiki. AT: \"Maƙiyinka zai saukar da kai\" ko\n\"Maƙiyinka zai ƙasƙantar da kai\" (Duba: figs_activepassive)"
},
{
"title": "yi magana daga ƙasa; muryarki zata dushe a cikin ƙura. Muryar ki zata zama kamar ta ruhu dake fitowa daga ƙasa, maganar ki kuma zata zama rarrauna daga cikin ƙura",
"body": "Duk waɗannan maganganun suna nufin abu ɗaya ne. Suna jaddada cewa mutanen da suka\ntaɓa yin magana da kalmomin alfahari za su kasance masu rauni da baƙin ciki bayan abokan\ngaba sun ci su da yaƙi. AT: \"za ku iya magana ne kawai da rada da rauni kamar\nruhun da ke magana daga inda matattu suke zaune\" (Duba: figs_simile da figs_parallelism)"
}
]