ha_isa_tn_l3/19/16.txt

18 lines
1.1 KiB
Plaintext

[
{
"title": "Masarawa za su zama kamar mata",
"body": "Wannan yana nanata cewa mutanen Masar zasu kasance cikin tsoro da rashin taimako idan\nAllah ya hukunta su. (Duba: figs_simile)"
},
{
"title": "saboda ɗagaggen hannun Ubangiji mai runduna a kansu",
"body": "Anan “hannu” yana nufin ikon Allah, kuma ɗaga hannu a kansu yana wakiltar hukunta su.\nAT: \"saboda Yahweh Mai Runduna ya ɗaga ikonsa mai ƙarfi don azabtar da su\"\n(Duba: figs_metonymy da figs_metaphor)"
},
{
"title": "Ƙasar Yahuda za ta zama sanadin tangaɗin Masar",
"body": "“ƙasar Yahuda” da “Masar” suna nuni ga mutanen da ke waɗannan wuraren. Masarawa za su\nyi tuntuɓe domin suna tsoro. AT: \"Mutanen Yahuda za su sa Masarawa su yi\ntuntuɓe\" ko \"Mutanen Yahuda za su sa Masarawa su firgita ƙwarai\" (Duba: figs_metonymy)"
},
{
"title": "Dukkan sa'ad da wani ya tuna masu da ita, za su ji tsoro",
"body": "Anan, \"su\" da \"su\" suna nufin Masarawa kuma \"ita\" tana nufin mutanen Yahuda. AT: \"Duk lokacin da wani ya tunatar da Masarawa game da mutanen Yahuza, Masarawa\nza su ji tsoro\""
}
]