ha_isa_tn_l3/10/05.txt

14 lines
1.4 KiB
Plaintext

[
{
"title": "kulkin fushina, sandar hannunka a bin harzuƙata ne",
"body": "Duk waɗannan kalmomin suna nufin abu ɗaya ne. Ubangiji yana kamanta sarkin Asiriya da\nmakamin da mutum yake riƙe a hannunsa kuma ya buga wasu mutane da shi. Ya nanata cewa\nsarkin Asiriya da sojojinsa kayan aiki ne da Yahweh yake amfani da su don hukunta Isra'ila.\nAT: \"wanene zai zama kamar makami a hannuna wanda zan yi amfani da shi don\nnuna fushina\" (Duba: figs_parallelism da figs_metaphor)"
},
{
"title": "Na aike shi gãba da mutane masu ɗauke da ambaliyar fushina",
"body": "Yahweh yayi magana akan fushin sa kamar wanda ya fi ruwa karfi fiye da kwantena; \"mutane\"\nsuna ƙoƙari su ɗauki wannan kwandon, amma yana da nauyi, kuma Yahweh yana ci gaba da\nzuba ruwa koda bayan ya fara malala. AT: \"wanda nake ci gaba da yin fushi koda\nbayan na hukunta su\" (Duba: figs_metaphor)"
},
{
"title": "ya tattake su kamar laka cikin tituna",
"body": "Mai yiwuwa ma'anoni su ne 1) Yahweh ya kwatanta sojojin Asiriya da ke kai wa Isra'ila hari\nda mutanen da ke tattaka cikin laka waɗanda ba su damu da abin da zai faru da lakar ba.\nAT: \"tattake su har sai sun zama kamar laka\" ko 2) mutane suna taka kan wasu\nmutane don haka suna kwance cikin laka kuma ba sa iya tashi. Wannan wani magana ne na fatattakar su gaba daya. AT: \"ka kayar da su gaba daya\" (Duba: figs_simile da figss_metaphor)"
}
]