ha_isa_tn_l3/01/21.txt

18 lines
1.3 KiB
Plaintext

[
{
"title": "Yadda birni mai aminci",
"body": "Wannan motsin rai ya nuna fushin Ishaya da ɓacin ransa game da mutanen Yerusalem.\nAT: \"Duba yadda mutanen Yerusalem, waɗanda suka kasance da aminci ga\nAllah\" (Duba: figs_metonymy)"
},
{
"title": "ya zama karuwa",
"body": "Ishaya ya kwatanta mutanen da matar da ba ta da aminci ga mijinta amma tana kwana da wasu\nmaza don kuɗi. Mutanen ba su da aminci ga Allah amma suna bauta wa allolin ƙarya. AT: \"tana yin kamar karuwa\" (Duba: figs_metaphor)"
},
{
"title": "amma yanzu ta cika da masu kisan kai",
"body": "Kalmar \"ta\" tana nufin Yerusalem da mutanenta. Waɗanda suka rubuta Littafi Mai Tsarki galibi\nsuna kiran biranen mata. AT: \"amma yanzu mutanen Yerusalem masu kisan kai\nne\" (Duba: figs_metaphor)"
},
{
"title": "Zinariyarki ta zama marar tsarki, ruwan inabinki ya gauraye da ruwa",
"body": "Zai yiwu ma'anoni su ne cewa Ishaya ya yi amfani da azurfa da ruwan inabi a matsayin\nkwatanci na 1) mutanen Yerusalem. AT: \"Kuna kamar azurfar da ba ta da tsarki,\nkuma kamar ruwan inabi wanda yake gauraye da ruwa\" ko 2) kyawawan ayyukan da mutane\nsuka yi a dā. AT: \"Kun kasance kuna aikata kyawawan ayyuka, amma yanzu\nayyukanku marasa kyau sun sa kyawawan ayyukanku sun zama marasa amfani\" (Duba: figs_metaphor)"
}
]