ha_gen_tn_l3/30/01.txt

22 lines
852 B
Plaintext

[
{
"title": "Da Rahila ta ga cewa ba ta haifa wa Yakubu 'ya'ya ba",
"body": "\"Lokacin da Rahila ta fahimci cewa ta kasa daukar ciki\""
},
{
"title": "Ba ni 'ya'ya",
"body": "\"Ka sa ni in yi ciki\""
},
{
"title": "ko in mutu",
"body": "Rahila tana wuce gona da iri don nuna bacin ranta game da rashin yara. AT: \"Zan ji ba ni da daraja kwata-kwata\" (Duba: figs_hyperbole)"
},
{
"title": "Fushin Yakubu ya ji ƙuna gãba da Rahila",
"body": "An yi maganar fushin Yakubu kamar wuta ne. AT: \"Yakubu ya yi fushi da Rahila\" (Duba: figs_metaphor)"
},
{
"title": "Ina a madadin Allah ne, wanda ya hana ki samun 'ya'ya?",
"body": "Yakubu ya yi amfani da wannan tambayar ne ya tsauta wa Rahila. Ana iya fassara shi azaman bayani. AT: \"Ni ba Allah ba ne, Ba ni ba ne na ke hana ki samun 'ya'ya!\" (Duba: figs_rquestion)\n"
}
]