ha_gen_tn_l3/08/20.txt

34 lines
1.2 KiB
Plaintext

[
{
"title": "gina bagadi ga Yahweh",
"body": "\"gina bagadi, ya keɓe wa Yahweh\" ko \"gina bagadin sujada ga Yahweh.\" Mai yiwuwa ya gina shi da duwatsu ne."
},
{
"title": "dabbobi ma su tsarki ... tsuntsaye ma su tsarki",
"body": "\"tsarki\" a nan na nufin cewa Allah ya yarda a yi amfani da waɗannan dabbobin domin hadaya. Ba a amfani da wasu dabbbobi wajen miƙa hadaya, ana kiran su \"mara tsarki.\""
},
{
"title": "miƙa hadaya ta ƙonawa",
"body": "Nuhu ya kashe dabbobin, sai ya ƙona su kurmus a matsayin baiko ga Allah. AT: \"ƙona dabbobin a matsayin baiko ga Yahweh\""
},
{
"title": "ƙanshi mai gamsuwa",
"body": "Wannan na nufin ƙanshi mai kyau daga gasashen nama. "
},
{
"title": "nufe nufen mutum a zukatansu mugunta ne tun daga yarintakarsu",
"body": "\"tun daga farkon shekarunsu, sun kasnace da nufin aikata mugunta\" ko \"tun suna ƙuruciya, suna son aikata mugayen abubuwa\""
},
{
"title": "Muddin duniya tana nan ",
"body": "\"muddin jurewa duniya\" ko \"muddin kasancewa duniya\""
},
{
"title": "lokacin shuka",
"body": "\"lokacin da ake yin shuki\""
},
{
"title": "sanyi da zafi, damina da rani",
"body": "Wannan maganar na nufin yanayi lokaci biyu da suke a shekara. (Duba: figs_merism)"
}
]