ha_gen_tn_l3/04/06.txt

26 lines
1.5 KiB
Plaintext

[
{
"title": "Me ya sa ka husata, kuma ya sa har tsikar jikinka ta tashi",
"body": "Allah ya yi amfani da wannan tambayoyi domin ya nuna wa Kayinu cewa ba dai-dai ba ne ya husata ya kuma sa tsikar jikinsa ta tashi. Mai yiwuwa kuma suna ba wa Kayinu zarafi ne ya furta cewa ya yi laifi ne. (Duba: figs_rquestion)"
},
{
"title": "In ka ... da ba za a karɓe ka ba?",
"body": "Allah ya yi amfani da wannan tambaya domin ya tunashe Kayinu game da abin da yakamata a ce ya sani. AT: \"Ka san cewa in da ka aikata abin da ya ke daidai, ai da na karɓe ka\" (Duba: figs_rquestion)"
},
{
"title": "Amma idan ba ka ... tilas ne ka mallake shi",
"body": "Allah na magana game da zunubi kamar wani mutum ne. AT: \"Amma idan ba ka bidar aikata abin da ke dai-dai, to za ka bida ka aikata zunubi, kuma za ka yi abin da ke na zunubi. Tilas ne ka ki yin biyayya da shi\" (Duba: figs_personification)"
},
{
"title": "Zunubi na fako ... ya mallake ka",
"body": "Ana magana game da zunubi anan kamar wani mugun dabba jeji ne da fakon kai hari wa Kayinu. AT: \"Za ka cika da hushi har za ka gagara kin aikata zunubi\" (Duba: figs_metaphor)"
},
{
"title": "zunubi",
"body": "Harsuna da ba su da suna da ke bayana \"zunubi\" na iya juya wannan kamar \"sha'awar aikata zunubi\" ko \"mumunar abubuwan da ka ke so ka yi.\""
},
{
"title": "tilas ne ka mallake shi",
"body": "Yahweh na magana game da sha'awar aikata zunubi da Kayinu ke yi kamar wani mutum ne da Kayinu zai yi mulkin shi. AT: \"dole ka mallake shi domin kar ka yi zunubi\" (Duba: figs_personification)"
}
]