ha_gen_tn_l3/01/14.txt

46 lines
2.0 KiB
Plaintext

[
{
"title": "Bari haskoki su kasance a cikin sarari",
"body": "Wannan umurni ne. Ta wurin umurtar haskoki su kasance, Allah kuwa ya sa sun kasance. (Duba: figs_imperative)"
},
{
"title": "haskoki a cikin sarari",
"body": "\"abubuwan da suke haskakawa a cikin sarari\" ko \"abubuwan da suke kawo haske a cikin sarari.\" Wannan na nufin rana, wata, da ta taurari."
},
{
"title": "cikin sarari",
"body": "\"cikin sararin sama\" ko \"a babban sararin sama\""
},
{
"title": "raba tsakanin yini da dare",
"body": "\"su raba yini da dare.\" Wannan na nufin \"su taimake mu bambanta tsakanin yini da dare.\" Rana na nuna yini, wata da taurari kuwa na nuna dare."
},
{
"title": "su zama alamu",
"body": "Wannan umurni ne. Ta wurin umurtar cewa su zama alamu, Allah kuwa ya sa sun zama alamu. AT: \"Bari su kasance alamu\" ko \"su kuma nuna\" (Duba: figs_imperative)"
},
{
"title": "alamu",
"body": "Wannan na nufin wani abu ne da ke bayyanar da wani abu."
},
{
"title": "yanayi na shekara",
"body": "\"yanayin shekara\" na nufin lokaci da aka keɓe domin bukukuwa da wasu abubuwan da mutane ke yi."
},
{
"title": "na yanayin shekara, na kwanaki da shekaru",
"body": "Rana, wata, da taurari na nuna yadda lokaci ke wucewa. Wannan na bamu damar sani aukuwar kowani mako, watani, ko shekara."
},
{
"title": "Bari su kasance haskoki a sarari, su kuma haskaka duniya",
"body": "Wannan umurni ne. Ta wurin umurta cewa su haskaka duniya, Allah kuwa sa sun haskaka duniya. (Duba: figs_imperative)"
},
{
"title": "so haskaka duniya",
"body": "\"su kawo haske a duniya\" ko \"su sa haske a duniya.\" Duniya ba ta hasken kanta amma ana haskakata ne, sai ta kuma maimaita hasken."
},
{
"title": "Haka ya kasance",
"body": "\"Haka ya faru\" ko \"abin da ya faru kenan.\" Abin da Allah ya umurta ya faru kamar yadda ya ce.Wannan maganar ya kasance a wurare dayawa a wannan surar kuma yana da ma'ana ɗaya ne a duk inda ya kasance. Dubi yadda aka juya wannan a Farawa 1:6."
}
]