ha_2sa_tn_l3/23/03.txt

18 lines
1.1 KiB
Plaintext

[
{
"title": "Muhimmin Bayani:",
"body": "Wannan ya ci gaba da kalmomin Dauda na ƙarshe."
},
{
"title": "Allah na Isra'ila ya faɗi, Dutsen Isra'ila ya ce mani",
"body": "Anan \"Allah na Isra'ila\" dai-dai yake da \"Dutsen Isra'ila.\" Kalmomin guda biyu suna faɗin abu ɗaya. Dauda ya gwada Allah da dutse don ya nanata ikonsa na kāre mutanensa. (Duba: figs_parallelism da figs_metaphor)"
},
{
"title": "Shi wanda ya ke mulkin mutane cikin adalci, mai yin mulki cikin tsoron Allah",
"body": "Waɗannan jimlolin guda biyu duk suna cewa sarki zai girmama Allah kuma ya aikata\nabin da Allah yake so. (Duba: figs_parallelism)"
},
{
"title": "Zai zama kamar hasken safiya ... hasken rana bayan saukowar ruwan sama",
"body": "Anan Allah yana kwatanta sarki da hasken safiya da rana bayan ruwan sama. Duk waɗannan hanyoyi ne na faɗin wannan sarki zai zama abin farin ciki ga Allah da kuma albarka ga mutane. Waɗannan jimlolin guda biyu suna da ma'ana iri ɗaya kuma ana amfani da su don ƙarfafawa. AT: \"Zai kasance mai faranta rai ga duka\" (Duba: figs_simile da figs_parallelism)"
}
]