ha_ulb/63-1JN.usfm

205 lines
13 KiB
Plaintext

\id 1JN
\ide UTF-8
\h Wasikar Yahaya Ta Fari
\toc1 Wasikar Yahaya Ta Fari
\toc2 Wasikar Yahaya Ta Fari
\toc3 1jn
\mt Wasikar Yahaya Ta Fari
\s5
\c 1
\p
\v 1 Abin nan da yake tun daga farko, wanda muka ji, wanda muka gani da idanunmu, wanda muka gani hannuwanmu suka kama, a wajen maganar rai.
\v 2 Ran kuwa aka baiyyana shi, muka gani, muka bada shaida, muka gaya maku labarin rai na har abada, wanda da yake a wurin Uba, aka kuma sanar da mu.
\s5
\v 3 Wannan da muka gani muka ji muka baku labari, domin kuyi zumunci da mu, zumuncinmu kuwa tare da Uba yake da Dansa Yesu Almasihu.
\v 4 Haka nan, muna rubuta maku wadannan abubuwa domin farin cikinmu ya cika.
\s5
\v 5 Wannan shi ne sakon da muka ji daga wurinsa mu kuwa muka sanar da ku: Allah haske ne a wurinsa kuwa babu duhu ko kadan.
\v 6 Idan mun ce muna zumunci da shi kuma muna tafiya cikin duhu, muna yin karya kuma bama aikata gaskiya.
\v 7 Amma idan muna tafiya cikin haske kamar yadda yake cikin haske, muna zumunci da juna, jinin Yesu Dansa ya wankemu daga dukka zunubi.
\s5
\v 8 Idan mun ce bamu da zunubi, muna rudin kanmu kenan, ba kuma gaskiya a cikinmu.
\v 9 Amma idan mun fadi zunubanmu, shi mai aminci ne, mai adalci da zai gafarta mana zunubanmu, ya kuma wankemu daga dukkan rashin adalci.
\v 10 Idan mun ce bamu yi zunubi ba, mun mai da shi makaryaci kenan, maganarsa kuma bata cikinmu.
\s5
\c 2
\p
\v 1 'Ya'yana, na rubuta ma ku wadannan abubuwa domin kada kuyi zunubi. Amma idan wani yayi zunubi muna da matsakanci a wurin Uba, Yesu Almasihu, mai adalci.
\v 2 Shine fansar zunubanmu, ba ma namu kadai ba amma na duniya dukka.
\v 3 Ta haka muka san cewa mun san shi, idan mun kiyaye dokokinsa.
\s5
\v 4 Duk wanda yace, "Na san Allah" amma bai kiyaye dokokinsa ba, makaryaci ne gaskiya kuwa ba ta cikinsa.
\v 5 Amma duk wanda ya kiyaye maganarsa, hakika kaunar Allah ta kammala a cikin wannan mutum. Ta wurin haka muka sani muna cikinsa.
\v 6 Duk wanda yace yana cikin Allah dole ne shi da kansa yayi tafiya kamar yadda Yesu Almasihu yayi.
\s5
\v 7 Kaunatattu, ba sabuwar doka nike rubuta maku ba, amma tsohuwar doka ce wadda kuka ji tun farko. Tsohuwar dokar kuwa itace maganar da kuka ji tun farko.
\v 8 Amma yanzu ina rubuta maku sabuwar doka wadda gaskiya ce a cikin Almasihu da cikinku, saboda duhu yana wucewa, haske na gaskiya yana haskakawa.
\s5
\v 9 Duk wanda yace yana cikin haske amma yana kin dan'uwansa, yana cikin duhu har yanzu.
\v 10 kuma wanda yake kaunar dan'uwansa yana cikin haske babu dalilin tuntube a wurinsa.
\v 11 Amma duk wanda yake kin dan'uwansa yana cikin duhu, yana kuma tafiya cikin duhu, bai san ma inda ya nufa ba, domin duhu ya makantar da shi.
\s5
\v 12 Na rubuta maku, ya ku kaunatun 'ya'yana, saboda an gafarta zunubanku domin sunansa.
\v 13 Na rubuta maku, ubanni, saboda kun san shi wanda yake tun daga farko. Na rubuta maku matasa saboda kun yi nasara da mugun. Na rubuta maku, yara kanana, saboda kun san Uban.
\v 14 Na rubuta maku, Ubanni, saboda kun san shi wanda yake tun daga farko. Na rubuta maku, matasa, saboda kuna da karfi, kuma maganar Allah tana zaune cikinku. Kuma kun yi nasara da mugun.
\s5
\v 15 Kada kuyi kaunar duniya ko abubuwan da suke cikin duniya. Idan wani yayi kaunar duniya, kaunar Uban bata cikinsa.
\v 16 Domin dukkan abubuwan da suke a cikin duniya, kwadayi na jiki, abin da idanu suke sha'wa, da rayuwar girman kai ta wofi, ba na Uban bane amma na duniya ne.
\v 17 Duniya tana wucewa tare da sha'awarta. Amma dukkan wanda ya aikata nufin Allah zaya kasance har abada.
\s5
\v 18 Yara kanana, sa'a ta karshe ce. Kamar dai yadda kuka ji magafcin Almasihu yana zuwa, ko yanzu ma magaftan Almasihu da yawa sun rigaya sun zo, ta haka muka san sa'a ta karshe ce.
\v 19 Sun fita daga cikinmu, dama su bana cikinmu bane. Gama idan da su namu ne da sun ci gaba tare damu. Amma da yake sun fita, ya nuna su ba na cikinmu bane.
\s5
\v 20 Amma ku kun karbi shafewa daga wurin Mai Tsarki, kuma dukkanku kun san gaskiya.
\v 21 Bana rubuta maku bane domin baku san gaskiya ba, amma saboda kun santa, kuma ba wata karya da ta fito daga gaskiya.
\s5
\v 22 Wanene makaryaci shine wanda yayi musu cewa Yesu ba Almasihu bane? Wannan mutumin shi ne magafcin Almasihu, tun da yayi musun Uba yayi musun Dan.
\v 23 Ba wanda yayi musun Dan kuma yake da Uban. Dukkan wanda ya amince da Dan yana da Uban ma.
\s5
\v 24 A game daku kuma, sai ku bari abinda kuka ji daga farko ya zauna a cikinku. Idan abin da kuka ji daga farko ya zauna a cikinku, kuma zaku kasance a cikin Dan da kuma Uban.
\v 25 Alkawarin da ya bamu kenan, rai na har abada.
\v 26 Na rubuta maku wadannan abubuwa ne game da wadanda zasu baudar daku.
\s5
\v 27 Game daku, shafewar daku ka samu daga wurinsa tana nan a cikinku, baku bukatar wani ya koyar daku. Amma kamar yadda shafewar da kuka karba a wurinsa ta koya maku dukkan abu, kuma gaskiya ne ba karya bane, tana nan a cikinku kamar yadda a ka koya maku, ku kasance a cikinsa.
\v 28 Yanzu fa, 'ya'ya na kaunatattu, ku kasance a cikinsa domin sa'adda zai baiyyana mu zama da gabagadi ba tare da kunya ba a gabansa sa'adda zai zo.
\v 29 Idan kun sani shi mai adalci ne, kun sani dukkan wanda ke aikata adalci haifaffe ne daga wurinsa.
\s5
\c 3
\p
\v 1 Dubi irin kaunar da Allah ya bamu, har da za a kira mu 'ya'yan Allah, haka muke kuwa. Saboda wannan dalili ne duniya bata san muba, saboda bata san shi ba.
\v 2 Kaunatattu, yanzu mu 'ya'yan Allahne, kuma ba a bayyana mana yadda zamu zama ba tukuna, mun sani sa'adda Almasihu zai bayyana, zamu zama kamarsa, domin zamu ganshi kamar yadda yake.
\v 3 Dukkan wanda yake da wannan bege game da gidan gobe ya kan tsarkake kansa, kamar yadda shima yake da tsarki.
\s5
\v 4 Dukkan wanda yaci gaba da yin zunubi yana ketare shari'a kenan. Gama zunubi ketare shari'a ne.
\v 5 Kun sani Almasihu ya bayyana domin ya dauke zunubai ne. Kuma a cikinsa babu zunubi.
\v 6 Ba wanda zai kasance a cikinsa da zai cigaba da yin zunubi. Ba wanda zai ci gaba da aikata zunubi da zai ce ya sanshi, ko kuma ya ganshi.
\s5
\v 7 'Ya'yana kaunatattu, kada ku bari kowa ya baudar da ku, wanda yake aikata adalci shi adali ne, kamar yadda Almasihu yake adali.
\v 8 Wanda yake aikata zunubi na ibilis ne, gama ibilis yayi zunubi tun daga farko. Dalilin haka ne Dan Allah ya bayyana, domin ya rushe ayyukan ibilis.
\s5
\v 9 Duk wanda aka haife shi daga Allah ba ya yin zunubi, saboda irin Allah na cikinsa. Ba zaya iya ci gaba da yin zunubi ba domin an haife shi daga wurin Allah.
\v 10 Ta haka ne ake bambanta 'ya'yan Allah da 'ya'yan ibilis. Dukkan wanda baya aikata adalci ba na Allah bane; haka kuma wanda ba ya kaunar dan'uwansa.
\s5
\v 11 Domin wannan shine sakon da kuka ji tun daga farko: cewa mu kaunaci junanmu,
\v 12 ba kamar Kayinu ba wanda yake na shaidan kuma ya kashe dan'uwansa. Me yasa ya kashe shi? Saboda ayyukansa miyagu ne, na dan'uwansa kuma masu adalci ne.
\s5
\v 13 Kada kuyi mamaki 'yan'uwana, idan duniya ta ki ku.
\v 14 Mun sani mun ratsa mutuwa zuwa cikin rai, saboda muna kaunar 'yan'uwa. Dukkan wanda ba ya yin kauna, shi matacce ne.
\v 15 Dukkan wanda yake kin dan'uwansa, mai kisan kai ne. Kun kuma sani babu rai na har abada a cikin mai kisankai.
\s5
\v 16 Ta wurin haka muka san kauna, da ya ke Almasihu ya bayar da ransa saboda mu. Mu ma ya kamata mu bada ranmu saboda 'yan'uwamu.
\v 17 Amma duk wanda yake da kayan duniya, ya ga dan'uwansa cikin bukata, kuma bai ji tausayinsa ba, ta yaya kaunar Allah ke cikinsa?
\v 18 'Ya'yana kaunatattu, kada muyi kauna ta fatar baki kawai, amma muyi aikin kauna da gaskiya.
\s5
\v 19 Ta wurin haka mun sani mu masu gaskiya ne kuma mun tabbatar da zuciyarmu a gabansa.
\v 20 Gama idan zuciyarmu bata kayar damu ba, Allah ya fi zuciyarmu girma, kuma yana sane da kome.
\v 21 Kaunatattu, idan zuciyarmu bata kashe mu ba, muna da gabagadi a gaban Allah.
\v 22 Kuma duk abin da muka nema zamu samu a wurinsa, saboda muna kiyaye dokokinsa, muna yin abubuwan da suka gamshe shi.
\s5
\v 23 Kuma ummurninsa kenan: mu bada gaskiya ga sunan Dansa Yesu Almasihu, mu yi kaunar juna kuma kamar yanda ya bamu wannan doka.
\v 24 Duk wanda yake kiyaye umarnin Allah, yana cikinsa, Allah kuma yana cikin mutumin. Ta haka muka gane cewa yana cikinmu, Ta wurin Ruhu, wanda ya bamu.
\s5
\c 4
\p
\v 1 Kaunatattu, kada ku amince da kowanne ruhu. Amma ku gwada ruhohi ku gani ko na Allah ne, gama annabawan karya masu yawa sun fito zuwa cikin duniya.
\v 2 Ta haka zaku gane Ruhun Allah, dukkan ruhun da ya amince Yesu Almasihu ya zo cikin jiki na Allah ne,
\v 3 kuma dukkan ruhun da bai amince da Yesu ba, ba na Allah bane. Wannan ruhun magafcin Almasihu ne, wanda kuka ji cewa yana zuwa, ya kuwa rigaya yazo cikin duniya.
\s5
\v 4 'Ya'yana kaunatattu, daga Allah ke, kuma kun rigaya kun yi nasara da su da yake wanda ke cikinku ya fi wanda ke cikin duniya girma.
\v 5 Su na duniya ne, saboda haka abin da suke fadi na duniya ne, duniya kuma tana sauraronsu.
\v 6 Mu na Allah ne, duk wanda ya san Allah yana saurarenmu. Wanda ba na Allah bane, ba ya sauraronmu. Ta haka muka gane ruhun gaskiya da ruhun karya.
\s5
\v 7 Kaunatattu, mu yi kaunar juna, gama kauna ta Allah ce, wanda yake kauna an haife shi daga wurin Allah, kuma ya san Allah.
\v 8 Mutumin da baya kauna ba na Allah ba ne, kuma bai san Allah ba, gama Allah kauna ne.
\s5
\v 9 A cikn haka aka bayyana kaunar Allah a garemu, Allah ya aiko tilon Dansa cikin duniya domin mu rayu ta wurinsa.
\v 10 A cikin wannan akwai kauna, ba mune muka kaunaci Allah ba, amma shi ya kaunace mu ya aiko da Dansa ya zama mai gafarta zunubanmu.
\s5
\v 11 Kaunatattu, da yake Allah ya kaunace mu haka, ya kamata mu kaunaci junanmu.
\v 12 Ba wanda ya taba ganin Allah. Idan muna kaunar juna, Allah yana zaune cikinmu, kuma kaunarsa tana zaune a cikinmu.
\v 13 Ta haka mun sani muna zaune a cikinsa shi kuma a cikinmu, saboda ya bamu Ruhunsa.
\v 14 Mun gani mun shaida, cewa Allah ya aiko Dan, domin ya zama mai ceton duniya.
\s5
\v 15 Duk wanda ya amince Yesu Dan Allah ne, Allah na zaune cikinsa, shi kuma a cikin Allah.
\v 16 Mun sani kuma mun gaskata da kaunar da Allah yake da ita dominmu, Allah kauna ne wanda yake zama cikin kauna yana zaune cikin Allah, Allah kuma a cikinsa.
\s5
\v 17 Dalilin wannan kauna ta kammala a cikinmu, domin mu kasance da gabagadi a ranar shari'a, domin kamar yanda ya ke haka muma muke a cikin duniyan nan.
\v 18 Babu tsoro a cikin kauna. Amma cikkakiyar kauna takan kawar da tsoro, domin kuwa tsoro na tafi tare da hukunci. Amma wanda yake da tsoro ba shi da cikkakiyar kauna.
\s5
\v 19 Muna kauna domin Allah ne ya fara kaunarmu.
\v 20 Idan wani ya ce,"Ina kaunar Allah", amma yana kin dan'uwansa, makaryaci ne. Domin wanda baya kaunar dan'uwansa da yake gani, ba zai iya kaunar Allah da bai taba gani ba.
\v 21 Wannan ne umarnin da muke da shi daga wurinsa: Duk wanda yake kaunar Allah dole ne ya kaunaci dan'uwansa.
\s5
\c 5
\p
\v 1 Duk Wanda ya gaskata Yesu shine Almasihu haifaffe na Allah ne. Kuma duk wanda ya kaunaci uba ya kaunaci dan da uban ya haifa.
\v 2 Haka muka sani muna kaunar 'ya'yan Allah: yayin da muka kaunaci Allah, kuma muka aikata umarninsa.
\v 3 Wannan itace kaunar Allah, cewa mu kiyaye umarninsa. Domin umarninsa ba masu nawaitawa bane.
\s5
\v 4 Duk wanda yake haifaffe na Allah yakan yi nasara da duniya. Wannan itace nasarar da ta rinjayi duniya, wato bangaskiyarmu.
\v 5 Wanene wannan mai nasara da duniya? Sai dai wanda ya gaskata Yesu Dan Allah ne.
\s5
\v 6 Wannan shine wanda yazo ta wurin ruwa da jini: Yesu Almasihu. Ya zo ba ta wurin ruwa kadai ba, amma ta wurin ruwa da jini.
\v 7 Domin akwai uku wadanda suke bada shaida:
\v 8 Ruhu, da ruwa, da kuma jini. Wadannan ukun kuwa manufarsu daya ce.
\s5
\v 9 Idan mun karbi shaidar mutane, shaidar Allah ta fi girma. Wannan ita ce shaidar Allah, wato ya bada shaida akan Dansa.
\v 10 Wanda ya gaskata da Dan Allah shaidar tana nan tare da shi. Duk wanda bai bada gaskiya ga Allah ba, ya mai da shi makaryaci kenan, domin bai gaskata da shaidar da Allah ya bayar game da Dansa ba.
\s5
\v 11 Wannan ita ce shaida: Allah ya bamu rai madawwami, wannan rai kuwa yana cikin Dansa.
\v 12 Duk wanda yake da Dan, yana da rai. Duk wanda ba shida Dan Allah kuwa bashi da rai.
\s5
\v 13 Na rubuto maku wannan ne don ku tabbata kuna da rai madawwami--a gare ku wadanda suka gaskata da sunan Dan Allah.
\v 14 Wannan shine gabagadin da muke da shi a gabansa, wato, in mun roki kome bisa ga nufinsa, zai ji mu.
\v 15 Haka kuma, in mun san yana jinmu--Duk abin da mu ka rokeshi--mun sani muna da duk abin da muka roka daga gare shi.
\s5
\v 16 Idan wani ya ga dan'uwansa ya yi zunubin da bai kai ga mutuwa ba, sai yayi masa addu'a, Allah kuwa zai ba shi rai. Ina nufin wadanda suka yi zunubin da bai kai ga mutuwa ba. Akwai zunubin da yake kai wa ga mutuwa: Ban ce a yi addu'a domin wannan ba.
\v 17 Dukkan rashin adalci, zunubi ne, amma akwai zunubin da bai kai ga mutuwa ba.
\s5
\v 18 Mun sani kowanne haiffafe daga wurin Allah ba ya yin zunubi. Amma wanda ke haifaffe daga wurin Allah, ya kan kare shi, mugun nan kuwa ba zai iya yi masa illa ba.
\v 19 Mun sani mu na Allah ne, mun kuma sani dukkan duniya tana hannun mugun nan.
\s5
\v 20 Amma mun sani Dan Allah yazo, kuma ya bamu fahimta, domin mu san wanda yake shi ne mai gaskiya. Haka kuma muna cikin wannan wanda shine gaiskiya, kuma cikin Dansa Yesu Almasihu. Shine Allah na gaskiya, da kuma rai na har abada.
\v 21 'Ya'ya, ku tsare kanku daga bautar gumaka.