ha_ulb/60-JAS.usfm

210 lines
14 KiB
Plaintext

\id JAS
\ide UTF-8
\h Yakubu
\toc1 Yakubu
\toc2 Yakubu
\toc3 jas
\mt Yakubu
\s5
\c 1
\p
\v 1 Yakubu, bawan Allah, da kuma Ubangiji Yesu Almasihu, zuwa ga kabilun nan goma sha biyu da suke warwatse: ina gaishe ku.
\v 2 Ku dauke su duka da farin ciki, 'yan'uwana, duk sa'adda kuke fuskantar jarabobi.
\v 3 Ku sani cewa gwajin banskiyar ku ta kan haifi jimiri.
\s5
\v 4 Bari jimiri ya cika aikin sa, domin ku kai ga cikakken girma kuma ku kammalu, domin kada ku rasa komai.
\v 5 Amma idan waninku yana bukatar hikima, sai ya roki Allah, wanda yake bayarwa a yalwace, ba tare da gori ba ga duk wanda ya roke shi, zai kuwa ba shi.
\s5
\v 6 Amma fa sai ya roka da banskiya ba tare da shakka ba, don mai shakka kamar rakumin ruwan teku yake, wanda iska take korarwa tana tunkudawa.
\v 7 Tilas ne wannan mutum kada ya yi tunanin zai karbi wani abu a wurin Ubangiji.
\v 8 Irin wannan mutumin mai zuciya biyu ne, mara tsai da hankali a dukan hanyoyin sa.
\s5
\v 9 Bari dan'uwa matalauci ya yi takama da matsayin sa babba,
\v 10 amma mutum mai arziki kuma a kaskantaccen matsayin sa, gama zai shude kamar furen ciyawa na jeji.
\v 11 Domin rana na bullowa da zafi mai konarwa kuma ya busar da ciyawa. Furen ya fadi, kuma kyaun sa ya lalace. Haka ma, mai arziki zai bushe yana cikin tsakiyar tafiyarsa.
\s5
\v 12 Albarka ta tabbata ga mutum mai jurewa da gwaji. Domin in ya jure gwajin, zai sami rawanin rai, wanda aka yi alkawarin sa ga wadanda ke kaunar Allah.
\v 13 Kada wani ya ce idan aka gwada shi, "Wannan gwaji daga wurin Allah ne," domin ba a gwada Allah da mugunta, shi kan sa kuwa ba ya gwada kowa.
\s5
\v 14 Amma kowanne mutum yakan sami gwaji daga muguwar sha'awar sa, wadda take janye shi kuma ta rinjaye shi.
\v 15 Bayan da muguwar sha'awar ta dauki ciki, sai ta haifi zunubi. Kuma bayan da zunubi ya yi girma, yakan haifi mutuwa.
\v 16 Kada fa ku yaudaru, 'yan'uwana kaunatattu.
\s5
\v 17 Kowace kyakkyawar baiwa, da kowace cikakkiyar baiwa daga sama take. Ta sauko ne daga wurin Uban haskoki. Wanda babu sauyawa ko wata alamar sakewa kamar yadda inuwa ke yi.
\v 18 Allah ya zabi ya haife mu ta wurin maganar gaskiya, domin mu zama kamar nunar fari na dukan halittar sa.
\s5
\v 19 Kun san wannan, 'yan'uwana kaunatattu: bari kowanne mutum ya yi hanzarin kasa kunne, da jinkirin yin magana, da kuma jinkirin yin fushi.
\v 20 Domin fushin mutum ba ya aikata adalcin Allah.
\v 21 Saboda haka, sai ku yar da kowanne irin aikin kazanta da yalwar mugunta. A cikin tawali'u ku karbi dassashiyar maganar, wadda ke iya ceton rayukan ku.
\s5
\v 22 Ku zama masu aikata maganar, kada ku zama masu jin ta kawai, kuna yaudarar kanku.
\v 23 Domin duk wanda ya ke mai jin maganar ne kawai, ba mai aikatawa ba, kamar mutum yake mai duba fuskarsa a madubi.
\v 24 Yakan dubi kansa sai ya tafi, nan da nan kuwa sai ya manta da kamannin sa.
\v 25 Amma duk mai duba shari'ar da bin ka'idar nan ta 'yanci, ya kuma nace biyayya da ita, ba zai zama kamar wanda zai ji ya manta ba, wannan mutum zai zama da albarka a cikin abin da yake yi.
\s5
\v 26 Idan wani yana zaton shi mai addini ne, amma bai kame bakinsa ba, yana yaudarar zuciyarsa ne, addinin mutumin nan na banza ne.
\v 27 Addini sahihi kuma marar aibi a gaban Allahnmu da Ubanmu, shine a kula da gwauraye da marayu a cikin kuntatar su, kuma mutum ya kebe kansa ya zama marar aibi daga duniya.
\s5
\c 2
\p
\v 1 Ya ku 'yan'uwana, muddin kuna rike da bangaskiyar ku ga Ubangijinmu Yesu Almasihu, Ubangijin daukaka, kada ku nuna bambanci ga wadansu mutane.
\v 2 Idan wani mutum ya halarci taron ku da zobban zinariya da tufafi masu kyau, wani matalauci kuma ya shigo da tufafi marasa tsabta.
\v 3 Sa'adda kuka kula da mai tufafi masu kyau nan, har kuka ce masa, "Idan ka yarda ka zauna a nan wuri mai kyau," mataulacin nan kuwa kuka ce masa, "Kai ka tsaya daga can," ko kuwa, "Zauna a nan kasa a gaba na,"
\v 4 Ashe ba kuna zartar da hukunci a tsakanin ku ba ke nan? Ba kun zama alkalai na mungayen tunani kenan ba?
\s5
\v 5 Ku saurara, ya 'yan'uwana kaunatattu, ashe, Allah bai zabi matalautan duniyar nan su zama mawadata cikin bangaskiya ba, su kuma zama magada a cikin mulkin nan da ya yi wa masu kaunar sa alkawari ba?
\v 6 Amma, kun wulakanta matalauta! Ashe, ba masu arzikin ne suke matsa maku ba? Ba su ne kuwa suke jan ku zuwa gaban shari'a ba?
\v 7 Ba kuma sune ke sabon sunan nan mai girma da ake kiran ku da shi ba?
\s5
\v 8 Duk da haka, idan kuka cika muhimmiyar shari'ar da nassi ya ce, "Ka kaunaci makwabcin ka kamar kanka," to, madalla.
\v 9 Amma in kun nuna bambanci, kun yi zunubi kenan, shari'a ta same ku da laifin keta umarni.
\s5
\v 10 Duk wanda yake kiyaye dukan shari'a, amma ya yi tuntube a hanya daya kadai, ya sabi shari'a gaba daya ke nan.
\v 11 Domin wanda ya ce, "Kada ka yi zina," shi ne kuma ya ce, "Kada ka yi kisan kai." Idan ba ka yi zina ba amma ka yi kisan kai, ai, ka zama mai taka shari'a kenan.
\s5
\v 12 Saboda haka, ku yi magana ku kuma yi aiki kamar wadanda za a hukunta ta wurin 'yantacciyar shari'a.
\v 13 Gama hukunci yana zuwa ba tare da jinkai ba ga wadanda ba su nuna jinkai. Jinkai ya yi nasara a kan hukunci.
\s5
\v 14 Ina amfanin haka, 'yan'uwana, idan wani ya ce yana da bangaskiya, kuma ba shi da ayyuka? Wannan bangaskiyar ba za ta cece shi ba, ko za ta iya?
\v 15 Misali, idan wani dan'uwa ko 'yar'uwa ba su da tufa mai kyau ko suna rashin abincin yini.
\v 16 Misali, idan waninku kuma ya ce masu, "Ku tafi cikin salama, ku kasance da dumi ku koshi." Idan baku ba su abubuwan da jiki ke bukata ba, ina amfanin wannnan?
\v 17 Haka ma, bangaskiya ita kadai, ba tare da aikin da ya nuna ta ba, matacciya ce.
\s5
\v 18 To, wani zai ce, "Ai, kai kana da bangaskiya, ni kuwa ina da ayyuka." Nuna mani bangaskiyar ka ba tare da ayyuka ba, ni kuma in nuna maka bangaskiya ta ta wurin ayyuka na.
\v 19 Ka gaskanta cewa Allah daya ne; ka yi daidai. Amma ko aljannu ma sun gaskata, kuma suna rawar jiki.
\v 20 Kana so ka sani, kai marar azanci, cewa bangaskiya ba tare da ayyuka ba banza ce?
\s5
\v 21 Ba an baratar da Ibrahim mahaifinmu ta wurin ayyuka ba, sa'adda ya mika Ishaku dansa a bisa bagadi?
\v 22 Ka gani, ashe, bangaskiyar sa ta yi aiki da ayyukan sa, kuma da cewa ta wurin ayyuka bangaskiyar sa ta ginu sosai.
\v 23 Nassi kuma ya cika da ya ce, "Ibrahim ya gaskata Allah, aka kuma lisafta masa ita a matsayin adalci." Aka kuma kira shi abokin Allah.
\v 24 Kun ga, ta wurin ayyuka ne mutum yake samu baratarwa ba ta wurin bangaskiya kadai ba.
\s5
\v 25 Ta wannan hanyar kuma, ba Rahab karuwar nan ta samu baratarwa ta wurin ayyuka, da ta marabci masu leken asirin nan ta fitar da su ta wata hanya dabam ba?
\v 26 Kamar yadda jiki idan ba tare da ruhu ba matacce ne, haka kuma, bangaskiya ba tare da ayyuka ba matacciya ce.
\s5
\c 3
\p
\v 1 Ba mutane dayawa za su zama masu koyarwa ba, 'yan'uwana. Mun san cewa za mu karbi hukunci mafi tsanani.
\v 2 Domin mukan yi tuntube ta hanyoyi dayawa. Duk wanda bai yi tuntube ta hanyar kalmomi ba, shi mutum ne ginanne sosai, wanda ke iya kame dukan jikinsa.
\s5
\v 3 Idan muka sa linzami a bakunan dawakai, domin su yi mana biyayya, za mu iya sarrafa jikunan su gaba daya.
\v 4 Ku lura kuma da jiragen ruwa, ko da yake suna da girma sosai kuma iska mai karfi tana kora su, da karamin karfe ne matukin yake juya su inda ya so.
\s5
\v 5 Haka kuma harshe dan karamin gaba ne a jiki, sai fahariyan manyan abubuwa. Ku lura yadda dan karamin wuta yake cinna wa babban jeji wuta.
\v 6 Harshe ma wuta ne, a cikin dukan gabobin mu, duniyar zunubai da aka sa cikin fannonin jikunan mu. Yana gurbata dukan jiki, ya kuma sa al'amurar rayuwa su kama da wuta. Shi kuwa gidan wuta ne yake zuga shi.
\s5
\v 7 Domin kowace irin dabbar jeji, tsunsu, da masu jan ciki, da hallittar teku, ana sarrafa su kuma dan Adam har ya sarrafa su ma.
\v 8 Amma game da harshe, babu wani a cikin 'yan Adam da ya iya sarrafa shi. Mugunta ne mara hanuwa, cike da dafi mai kisa.
\s5
\v 9 Da wannan harshe muke yabon Ubangiji da kuma Uba, da shi kuma muke la'antar mutane wandanda aka hallitta cikin kamanin Allah.
\v 10 Bakin da ake sa albarka, da shi kuma ake la'antarwa. 'Yan'uwana, ai, wannan bai kamata ba.
\s5
\v 11 Mabulbulan ruwa ba zai iya bubbugowa da ruwan dadi da na zartsi tare ba, ko zai iya?
\v 12 "Yan'uwana, itacen baure ba zai iya yin zaitun ba, zai iya? Ko kuwa gonar inabi ya yi baure? Haka kuma, ruwan zartsi ba zai iya bayar da ruwan dadi ba.
\s5
\v 13 Ina mai hikima da fahimta a cikin ku? Bari wannan mutumin, ta kyakkyawan zaman sa ya nuna aikin da halin tawali'u da hikima ke sawa.
\v 14 Amma in kuna da matsanancin kishi da kazamin buri a cikin zuciyar ku, kada ku yi fahariya da karya game da gaskiya.
\s5
\v 15 Wannan hikima ba irin wadda take saukowa daga sama ba ce, a maimakon haka, ta duniya ce, mara ruhaniya, ta aljanu.
\v 16 Domin duk inda kishi da kazamin buri suke, a nan ake samun hargitsi da kowanne irin aikin mugunta.
\v 17 Amma hikiman nan ta sama, da farko dai tsattsarka ce, mai lumana ce, kamila ce, mai saukin kai, mai tsananin jinkai, mai yawan alheri, mara gajiya, sahihiya kuma.
\v 18 Kuma 'ya'yan adalci wanda ake shukawa a cikin salama a tsakanin wadanda ke kulla zumunci.
\s5
\c 4
\p
\v 1 Me ke kawo gaba da rashin jituwa a tsakanin ku? Ba yana tasowa ne daga muguwar sha'awa da ke yaki a cikin ku ba?
\v 2 Kuna sha'awa, kuma ba ku da shi. Kuna kisa da kyashi, kuma ba za ku iya samu ba. Kuna danbe da fada. Har wa yau baku samu ba domin baku tambaya ba.
\v 3 Kun roka kuma ba a baku ba saboda kuna roko ta hanya mara kyau, kuna so ku yi amfani da shi domin miyagun sha'awoyin ku.
\s5
\v 4 Ku mazinata! Baku sani ba, abokantaka da duniya, tawaye ne ga Allah? Don haka duk wanda ya shiga abokantaka da duniya ya zama magabcin Allah.
\v 5 Ko kuna zaton nassi ya fadi haka a banza ne, "Ruhun nan da ke a cikinmu yana da kishi matuka?"
\s5
\v 6 Amma Allah ya bayar da karin alheri, shi ya sa nassi ya ce, "Allah yana gaba da mai girman kai, Amma yana ba da alheri ga mai tawaliu."
\v 7 Saboda haka ku mika kan ku ga Allah. Ku yi tsayayya da shaidan, zai kuma guje maku.
\s5
\v 8 Ku matso kusa da Allah, shi kuma za ya matsa kusa da ku. Wanke hannayen ku, ku masu zunubi, ku tsabtace zukatan ku, ku masu zuciya biyu.
\v 9 Ku yi bakin ciki, makoki, da kuka! Ku mayar da dariyar ku ta koma bakin ciki, farin cikinku kuma zuwa ga bakin ciki.
\v 10 Ku kaskantar da kanku a gaban Ubangiji, shi kuma za ya daukaka ku.
\s5
\v 11 Kada ku rika zargin juna, 'yan'uwa. Wanda ya ke zargin dan'uwa ko shari'anta dan'uwansa, yana zargin shari'a kuma yana hukunta shari'a. Idan ka hukunta shari'a, ya nuna ba ka biyayya da shari'ar, amma mai hukunci.
\v 12 Mai ba da shari'a da yin hukunci daya ne. Shine mai iya ceto kuma ya hallakar. Kai wanene, da ke hukunta makwafcin ka?
\s5
\v 13 Saurara, ku da kuke cewa, "Yau ko gobe za mu tafi wancan birnin mu yi shekara guda a wurin, muna kasuwanci, mu kuma yi riba."
\v 14 Wa ya san abin da zai faru gobe, kuma yaya rayuwan ka zai kasance? Kai kamar hazo ne mai bayyana bayan dan lokaci kadan ya bace.
\s5
\v 15 Maimakon haka, sai ka ce, "Idan Ubangiji ya nufa, za mu rayu kuma mu yi wannan ko wancan."
\v 16 Amma yanzu kana fahariya da shirye shiryen ka na takama. Irin wannan fahariya, mugunta ce.
\v 17 Saboda haka ga wanda ya san abin da ya kamata ya aikata amma bai yi ba, ya zama zunubi a gare shi.
\s5
\c 5
\p
\v 1 Ku zo yanzu, ku da kuke masu arziki, ku yi ta kuka da kururuwa domin bakin ciki iri-iri da ke zuwa gare ku.
\v 2 Arzikin ku ya rube, tufafinku kuma duk cin asu ne.
\v 3 Zinariya da azurfarku sun yi tsatsa. Tsatsar su kuwa zai zama shaida a kanku. Zai cinye naman ku kamar wuta. Kun yi ajiyar dukiyarku domin ranakun karshe.
\s5
\v 4 Duba, hakin ma'aikata yana kuka - hakin da kuka hana wa wadanda suka girbe maku gonaki. Kuma kukan masu girbin ya tafi ya kai ga kunnuwan Ubangiji mai Runduna.
\v 5 Kun yi zama cikin annashuwa a duniya kuma kun tsunduma kanku. Kun sa zukatan ku sun yi kiba domin ranar yanka.
\v 6 Kun hukunta kuma kun kashe adalin mutum. Bai kuwa yi tsayayya da ku ba.
\s5
\v 7 Saboda haka ku yi hakuri, 'yan'uwa, har sai zuwan Ubangiji. Duba, yadda manomi ya kan jira kaka mai amfani daga gona. Da hakuri yake jiran ta har sai ta karbi ruwa na fari da na karshe.
\v 8 Ku, ma, ku yi hakuri. Ku karfafa zukatan ku, domin zuwan Ubangiji ya yi kusa.
\s5
\v 9 Kada ku yi gunaguni, 'Yan'uwana, game da juna, don kada a hukunta ku. Duba, mai shari'a na tsaye a bakin kofa.
\v 10 Dauki misali, 'yan'uwa, daga shan wuya da hakurin annabawa, wadanda suka yi magana a cikin sunan Ubangiji.
\v 11 Duba, mukan kira wadanda suka jimre masu albarka. Kun dai ji irin jimiri da Ayuba ya yi, kun kuma san nufin Ubangiji, yadda yake mai yawan tausayi da jinkai.
\s5
\v 12 Fiye da komai duka, 'yan'uwana, kada ku yi rantsuwa, ko da sama, ko da kasa, ko da kowace irin rantsuwa ma. A maimakon haka bari "I" ya zama "I", in kuwa kun ce "A'a", ya zama "A'a", don kada ku fada a cikin hukunci.
\s5
\v 13 Akwai wanda ke fama a tsakanin ku? Sai ya yi addu'a, akwai wanda yake murna? Sai ya raira wakar yabo.
\v 14 Akwai mara lafiya a tsakanin ku? Sai ya kira dattawan ikilisiya, sai su yi masa addu'a. Suna shafa masa mai a cikin sunan Ubangiji.
\v 15 Addu'ar bangaskiya zai warkar da mara lafiyan, Ubangiji zai tashe shi. Idan ma ya yi zunubi, Allah zai gafarta masa.
\s5
\v 16 Soboda haka, ku furta zunuban ku ga juna, kuna yi wa juna addu'a, don a warkar da ku. Addu'ar mai adalci tana da karfin aiki kwarai da gaske.
\v 17 Iliya dan Adam ne kamar mu. Amma da ya nace da addu'a kada a yi ruwa, ba kuma yi ruwa a kasar ba har shekara uku da wata shida.
\v 18 Sai Iliya ya sake yin addu'a. Sammai suka ba da ruwa, kasa kuma ta ba da amfanin ta.
\s5
\v 19 Ya ku 'yan'uwana, idan wanin ku ya baude wa gaskiya, wani kuma ya dawo da shi,
\v 20 wannan mutum ya sani cewa, duk wanda ya dawo da mai zunubi a hanya daga baudewar sa, zai cece shi daga mutuwa, kuma zai rufe dunbin zunubai.