ha_ulb/59-HEB.usfm

581 lines
40 KiB
Plaintext

\id HEB
\ide UTF-8
\h Ibraniyawa
\toc1 Ibraniyawa
\toc2 Ibraniyawa
\toc3 heb
\mt Ibraniyawa
\s5
\c 1
\p
\v 1 A zamanin da, Allah ya yi wa kakanin kakanninmu magana ta hanyoyi ma su yawa iri iri, ta bakin annabawa.
\v 2 Amma a zamanin nan na karshe, ya yi mana magana ta wurin Dansa, wanda ya sa magajin kome, wanda ta wurinsa ya halicci duniya.
\v 3 Shi ne hasken daukakar Allah, ainihin kamanin zatinsa. Ya na rike da dukkan abubuwa ta ikon kalmarsa. Bayan da ya tsarkake zunubanmu, sai ya zauna a hannun dama na madaukaki a can sama.
\s5
\v 4 Ta haka ya ke da fifiko a kan mala'iku, kamar yadda sunansa da ya gada yake da fifiko nesa a kan nasu.
\v 5 Domin kuwa wanene a cikin mala'iku Allah ya taba cewa, "Kai Da na ne, yau na zama Uba a gare ka?" kuma, "Zan kasance Uba a gareshi, shi kuma, zai kasance Da a gare ni?"
\s5
\v 6 Kuma, da Allah ya kawo magaji a duniya, sai ya ce, "Dukan mala'ikun Allah su yi masa sujada."
\v 7 A game da mala'iku kuma sai ya ce, "yakan mai da mala'ikunsa ruhohi, masu hidimarsa kuma harsunan wuta.
\s5
\v 8 A game da Dan, ya ce "kursiyinka, ya Allah, na har abada abadin ne. Sandar sarautarka sanda ce ta tsantsar gaskiya.
\v 9 Ka kaunaci aikin adalci, ka ki aikin sabo. Saboda haka Allah, wato Allahnka, ya shafe ka da man farin ciki fiye da tsararrakinka."
\s5
\v 10 "Tun farko, Ubangiji, kai ne ka hallici duniya. Sammai kuma aikin hannayenka ne.
\v 11 Za su hallaka, amma kai madawwami ne. Duk za su tsufa kamar tufafi.
\v 12 Za ka nade su kamar mayafi, za su kuma sauya, amma kai kana nan ba sakewa, Har abada shekarunka ba za su kare ba."
\s5
\v 13 Amma wanene a cikin mala'ikun Allah ya taba cewa, "Zauna a hannun dama na, sai na sa makiyanka a karkashin kafafunka?"
\v 14 Ashe, ba dukkan mala'iku bane ruhohi, wadanda Allah yakan aika, don su yi wa wadanda za su gaji ceto hidima?
\s5
\c 2
\p
\v 1 Saboda haka, lalle ne mu kara mai da hankali musamman da abubuwan da mu ka ji, don kada mu yi sakaci, su sullube mana.
\s5
\v 2 Idan kuwa maganar nan da aka fada ta bakin mala'iku ta zama tabbatacciya, har kowanne keta umarni da rashin biyayya, suka gamu da sakamakonsu wanda ya kamace su,
\v 3 ta kaka za mu tsira, in mun ki kula da ceto mai girma haka? Domin Ubangiji da kansa, shi ne ya fara sanar da shi, wadanda suka saurare shi kuma suka tabbatar mana da shi.
\v 4 San'nan kuma Allah da kansa ya shaida ta wasu alamu, da abubuwan al'ajabai, da mu'ajizai iri iri, da kuma baiwar Ruhu Mai Tsarki dabam dabam da ya rarraba kamar yadda ya nufa.
\s5
\v 5 Ai ba ga mala'iku ba ne Allah ya sa mulkin duniyar nan da za a yi, wanda muke zance.
\v 6 Amma wani ya shaida a wani wuri cewa, "Mutum ma menene, har da za ka tuna da shi? Ko dan mutum ma, har da za ka kula da shi?
\s5
\v 7 Ka sa mutum ya gaza mala'iku; Ka nada shi da daukaka da girma. Bisa dukkan hallitta.
\v 8 Ka dora shi a kan dukkan halittarka, ka kuma mallakar da kome a karkashin sawayensa. Domin Allah ya mallakar da dukkan abubuwa a karkashinsa. Bai bar kome a kebe ba. Amma kuwa har a yanzu ba mu ga yana sarrafa dukkan abubuwa ba tukuna.
\s5
\v 9 Amma mun ga wani wanda dan lokaci aka sa shi ya gaza mala'iku, shine Yesu, an nada shi da daukaka da girma, saboda shan wuyarsa ta mutuwa, wanan kuwa duk ta wurin alherin Allah ne Yesu ya mutu saboda kowa.
\v 10 Saboda haka, ya dace ga Allah, shi da dukkan abubuwa suka kasance domin sa, ta gare shi, domin ya kawo 'ya'ya masu yawa ga samun daukaka. Domin a kammala cetonsu ta wurin shan wuyarsa.
\s5
\v 11 Domin da shi mai tsarkakewar da kuma wadanda aka tsarkaken, duk tushensu daya ne. Saboda wanan dalili ne shi ya sa ba ya jin kunyar kiran su 'ya'uwansa.
\v 12 Da yace, "zan sanar da sunanka ga ya'uwana, a tsakiyar taronsu zan yabe ka da waka."
\s5
\v 13 Har wa yau, yace, "Zan dogara a gare shi." Da kuma "Ga ni nan, ni da 'ya'yan da Allah ya ba ni."
\v 14 Wato tun da yake 'ya'yan Allah duk suna da nama da jini, Yesu ma ya dauki kamannin haka, ta wurin mutuwa ya hallakar da mai ikon mutuwa, wato Iblis.
\v 15 Ya kuma 'yanta duk wadanda tun haihuwarsu suke zaman bauta sabo da tsoron mutuwa.
\s5
\v 16 Don hakika ba mala'iku yake taimako ba, a'a, zuriyar Ibrahim ne yake taimako.
\v 17 Saboda haka, lalle ne ya zama kamar yan'uwansa ta kowacce hanya, domin ya zama babban Firist, mai jinkai, mai aminci kuma na al'amarin Allah, ya kuma mika hadayar sulhu ta gafarta zunuban jama'a.
\v 18 Tun da yake Yesu ma da kansa ya sha wahala, sa'adda aka gwada shi, don haka, zai taimaki wadanda ake yi wa gwaji.
\s5
\c 3
\p
\v 1 Don haka yanuwana tsarkaka, a bokan kira a samaniya. Yi la'akari da Yesu. wato Manzo da babban firist na shaidar bangaskiyarmu.
\v 2 Shi amintacce ne na Allah, wanda ya bashi hidima, kamar yadda Musa ya kasance amintacce a gidan Allah.
\v 3 Gama Yesu ya cancanci daukaka mafi girma fiye da ta Musa. Domin wanda ya gina gida, ya fi gidan nan daukaka.
\v 4 Gama kowane gida, akwai wanda ya gina shi, amma mai ginin komai shine Allah.
\s5
\v 5 Musa hakika amintaccen bawa ne a gidan Allah, yana ba da shaidar abubuwan da za su faru a nan gaba.
\v 6 Amma Almasihu shi Da ne mai mulki a gidan Allah. Mu ne gidansa idan mun rike begenmu da dukkan zuciyarmu.
\s5
\v 7 Saboda haka, kamar yadda Ruhu Mai Tsarki ya fadi: "Yau, Idan kun ji muryarsa,
\v 8 kada ku taurare zuciyarku kamar yadda 'ya'yan isra'ila suka yi cikin tawaye a lokacin gwaji a jeji.
\s5
\v 9 A lokacin nan ne kakanninku suka yi mani tawaye, ta wurin gwada ni, bayan shekara arba'in suna ganin ayyukana.
\v 10 Saboda haka na yi bakin ciki da wannan tsarar, sai na ce,' Kullum suna yawan bijirewa a zukatansu. Basu san tafarkuna ba.'
\v 11 Don haka na yi rantsuwa a cikin fushina, ba za su shiga cikin hutuna ba."
\s5
\v 12 Ku yi hankali 'yan'uwa kada a tarar da mummunar zuciya marar bangaskiya a tsakaninku, zuciya wadda ke juyawa daga Allah mai rai.
\v 13 Maimakon haka, ku karfafa juna a kowacce rana, muddun muna cikin wannan rana kada wani cikinku ya taurare zuciyarsa saboda yaudarar zunubi.
\s5
\v 14 Gama mun zama abokan aiki da Almasihu, idan mun rike begenmu cikinsa da karfi, daga farko zuwa karshe.
\v 15 Game da wannan, an fadi "Yau idan kun saurari muryarsa, kada ku taurare zuciyarku, kamar a kwanakin tawaye nan."
\s5
\v 16 Su wanene suka ji muryar Allah suka yi tawaye? Ba wadanda Musa ya yi masu jagora daga Masar ba ne?
\v 17 Kuma da su wa Allah ya yi fushi shekara arba'in? Ba da wadanda suka yi zunubi ba ne, wadanda gawawwakinsu suka warwatsu a jeji?
\v 18 Da su wa Allah ya rantse ba za su shiga hutunsa ba? In ba wadanda suka yi masa rashin biyayya ba?
\v 19 Mun kuma gani cewa basu iya shiga hutunsa ba saboda rashin bangaskiyarsu.
\s5
\c 4
\p
\v 1 Saboda haka, sai muyi lura kwarai don kada wani ya kasa kai ga shiga hutun da aka alkawarta maku na Allah.
\v 2 Don mun ji albishir game da hutun Allah kamar yadda aka fada masu. Amma wancan sakon bai anfana ga wadanda suka ji ba tare da sun bada gaskiya ga sakon ba.
\s5
\v 3 Ai mu, wadanda muka gaskata-mune zamu shiga wannan hutun, kamar yadda ya ce, "Yadda na yi rantsuwa cikin fushina, baza su shiga hutu na ba." Ya fadi hakan, ko da yake ya gama aikin hallittarsa tun daga farkon duniya.
\v 4 Domin yayi fadi a wani wuri game da rana ta bakwai, "Allah ya huta a rana ta bakwai daga dukkan ayyukansa."
\v 5 Ya sake cewa, "Baza su taba shiga hutu na ba."
\s5
\v 6 Saboda haka, tun da hutun Allah na kebe domin masu su shiga, kuma tun da Isra'ilawa da yawa wadanda suka ji sakon nan mai kyau game da hutunsa ba su shiga ba saboda rashin biyayya,
\v 7 Allah ya sake shirya wata rana da ake kira, "Yau." Ya sa wannan rana sa'adda yayi magana ta wurin Dauda, wanda ya ce tun da dadewa da aka fara fada, "Yau idan kun ji muryarsa, kada ku taurare zukatanku."
\s5
\v 8 Don idan Joshua ya ba su hutu, da Allah ba zai sake magana a kan wata rana ba.
\v 9 Saboda haka, akwai hutun asabar kebabbe ga mutanen Allah.
\v 10 Don shi wanda ya shiga hutun Allah shi kansa ma ya huta daga ayyukansa, kamar yadda Allah yayi da nasa.
\v 11 Saboda haka muyi marmarin shiga wancan hutun, don kada kowa ya fadi ga irin rashin biyayyar da suka yi.
\s5
\v 12 Maganar Allah kuwa rayayyiyace, kuma mai ci, fiye da takobi mai kaifi-biyu. Takan ratsa har tsakanin rai da ruhu, kuma tana kaiwa bargo. Takan iya bincika tunanin zuciya da manufarta.
\v 13 Babu halittaccen abu da ke boye a idon Allah. Sai dai, kome a sarari yake, kuma a bayyane yake a idonsa wanda lallai ne zamu bada lissafin kanmu a gare shi.
\s5
\v 14 Da yake muna da babban firist wanda ya ratsa sammai, Yesu Dan Allah, sai mu riki bangaskiyarmu da karfi.
\v 15 Domin babban firist namu ba marar tausayi ga kasawarmu bane, amma wanda aka jarraba ne ta ko wanne hali irin yadda aka yi mana, sai dai ba'a same shi da zunubi ba.
\v 16 Sai mu zo wurin kursiyin alheri gabagadi, domin a yi mana jinkai mu kuwa sami alherin da zai taimake mu a lokacin bukata.
\s5
\c 5
\p
\v 1 Kowanne babban firist, da yake an zabe shi ne daga cikin mutane, a kansa shi ya wakilci mutane ga al'amarin Allah, don ya mika sadakoki da kuma hadayu domin kawar da zunubai.
\v 2 Yana kuma iya tafiyar da jahilai da sangartattu a cikin salihanci, tun da shi ke rarrauna ne shi ta ko'ina.
\v 3 Saboda haka, wajibi ne ya mika hadayu, ba saboda kawar da zunuban jama'a kadai ba, har ma da na kansa.
\s5
\v 4 Ba wanda zai kai kansa wannan matsayi mai girma, sai dai Allah ya yi kiransa ga haka, kamar yadda aka kirayi Haruna.
\v 5 Haka kuma, Almasihu, ba shi ya daukaka kansa ya zama Babban firist ba, sai dai wannan ne ya sa shi, wanda ya ce da shi, "Kai Dana ne; Yau na zama Uba a gare ka."
\s5
\v 6 Kamar dai yadda a wani wuri kuma ya ce, "Kai firist ne na har abada, bisa ga kwatancin Malkisadak."
\s5
\v 7 Almasihu, a lokacin zamansa a duniya, ya yi addu'o'i da roke-roke, tare da kuka mai tsanani, har da hawaye, ga wannan da yake da ikon cetonsa daga mutuwa, aka kuwa saurare shi saboda tsannin mika kansa.
\v 8 Ko da yake shi Da ne, ya koyi biyayya ta wurin wuyar da ya sha.
\s5
\v 9 Har ya kai ga kammala, sai ya zama tushe madawwami, ceto ga dukkan wadanda suke masa biyayya.
\v 10 Gama Allah yana kiransa Babban firist, bisa ga kwatancin Malkisadak.
\v 11 Muna da abu da yawa da za mu fada a game da Yesu, amma zai yi wuyar bayani, da yake basirarku ta dushe.
\s5
\v 12 Ko da yake yanzu kam, ya kamata ku zama masu koyarwa, duk da haka, ashe, ba ku wuce wani ya sake koya muku jigajigan farko na Maganar Allah ba? har ya zamana sai an ba ku madara ba abinci mai tauri ba?
\v 13 To, duk wanda yake madara ce abincinsa, bai kware da maganar adalci ba, kamar jariri yake.
\v 14 Amma abinci mai tauri, ai, na manya ne, wato wadanda hankalinsu ya horu yau da kullum, don su rarrabe nagarta da mugunta.
\s5
\c 6
\p
\v 1 Saboda haka, sai mu ci gaba a kan ka'idodin farko na al'amarin Almasihu, har ya zuwa kammala, ba wai mu sake koyar da jigajigan nan na tuba da ibada marar tasiri ba, da na gaskatawa da Allah,
\v 2 da kuma na koyarwa a kan wanke-wanke, da dora hannu, da tashin matattu, da dawwamammen hukuci.
\v 3 Za mu kuwa ci gaba in Allah ya yarda.
\s5
\v 4 Domin wadanda aka haskaka zukatansu sarai, har suka dandana baiwar nan Basamaniya, suka kuma sami rabo na Ruhu Mai Tsarki,
\v 5 har su ka dandana dadin Maganar Allah, da ikon zamani mai zuwa,
\v 6 sa'an nan kuma suka ridda--ba mai yiwuwa ba ne a sake jawo su ga tuba, tun da yake sake gicciye Dan Allah suke yi su da kansu, suka kuma wulakanta shi a sarari.
\s5
\v 7 Kasa ma da take shanye ruwan da ake yi a kai a kai, take kuma fid da tsire-tsire masu amfani ga wadanda ake nomanta dominsu, Allah yakan sa mata albarka.
\v 8 Amma idan tsire-tsirenta kaya ne da kashin yawo, ba ta da amfani ke nan, tana kuma gab da la'antarwa, karshenta dai konewa ne.
\s5
\v 9 Ko da yake mun fadi haka, a game da ku kam, ya kaunatattu mun tabbata kuna abubuwa mafiya kyau na zancen ceto.
\v 10 Gama Allah ba marar adalci ba ne, har da zai ki kula da aikinku, da kuma kaunar sunansa da kuke yi, wajen yi wa tsarkaka hidima, har yanzu ma kuna yi.
\s5
\v 11 Muna dai bukata kwarai kowannanku ya nuna irin wannan himma ga yin cikkaken bege, tabbatacce, har ya zuwa karshe.
\v 12 Don kada ku yi ragwanci, sai dai ku yi koyi da wadanda suka karbi cikar alkawaran nan, ta wurin bangaskiyarsu da hakurinsu.
\s5
\v 13 Sa'adda Allah ya yi wa Ibrahim alkawari, da yake ba wani wanda ya fi shi girma da zai rantse da shi, sai ya rantse da kansa,
\v 14 Ya ce, "Hakika zan yi maka albarka, in kuma ribambamya zuriyarka."
\v 15 Ta haka, Ibrahim bayan da ya jure da hakuri, ya karbi cikar alkawarin.
\s5
\v 16 Hakika mutane sukan rantse da abin da ya fi su. Rantsuwa kuma ita ce abar da take tabbatarwa da kowacce magana.
\v 17 Don haka, sa'adda Allah yake son kara tabbatar wa magadan alkawarin nan dahir, cewa nufinsa ba mai sakewa ba ne sam, sai ya hada da rantsuwa,
\v 18 Domin albarkacin abubuwa guda biyun nan marasa sakewa, masu nuna, cewa ba shi yiwuwa Allah ya yi karya, mu da muka gudu muka sami mafaka, mu karfafa kwarai mu riski abin da muka kafa bege a kai.
\s5
\v 19 Muna da bege, kamar yadda yake ga rai, kafaffe, tabbatacce, shi ne kuma yake shiga har can ciki bayan labulen.
\v 20 Inda saboda mu ne Yasu ya riga mu shiga, da yake ya zama Babban Firist na har abada, kwatancin Malkisadak.
\s5
\c 7
\p
\v 1 Wannan ne Malkisadak, sarkin Salem, firist na Allah Madaukaki, wanda ya gamu da Ibrahim na dawowa daga yaki da wasu sarakuna ya kuma albarkace shi.
\v 2 Ibrahim ya ba shi ushirin dukkan ganimar da ya samu. Sunansa," Malkisadak," ma'anar itace, "Sarkin adalci," haka ma, "sarkin salem," ma'anar iitace," Sarkin salama,"
\v 3 Bashi da uwa bashi da uba, ba shi da lissafin asalin zuriya, ba shi da farkon rayuwa ba shi da karshen rai. Shi firist ne na har abada, kamar Dan Allah.
\s5
\v 4 Yanzu fa dubi irin girman wannan mutum. Kakan kakanninmu Ibrahim ya bada ushira ta abubuwan da ya samo na ganimar yaki gare shi.
\v 5 Kuma hakika, zuriyar Lawi da suka karbi aikin nan na firistanci suna da umarni daga shari'ar Allah cewa su karbi zakka a gun jama'a, wato, daga yan'uwan su Isra'ilawa, koda shike suma zuriyar Ibrahim ne.
\v 6 Amma Malkisadak, shi da ba zuriyar Lawi ba ne, ya karbi zakka daga Ibrahim, ya kuma albarkace shi, shi wanda ya ke da alkawarai.
\s5
\v 7 Ba jayayya, karami shi ke karban albarka daga babba wanda ya girme shi.
\v 8 A wannan tsarin mutanen da ke karban zakka wata rana sai ka ga sun mutu, amma a wani kauli mutumin da ya karbi zakka a wurin Ibrahim, ance, wanzaje ne har yau.
\v 9 Kuma bisa ka'ida Lawi, wanda ke karban zakka, shi ma ya bada zakka ga Ibrahim,
\v 10 Saboda kuwa Lawi na cikin tsatson Ibrahim lokacin da Malkisadak ya gamu da Ibrahim.
\s5
\v 11 Yanzu in da mai yiwuwa ne a sami kammala cikin aikin firistanci na Lawiyawa (domin ta wurin ta ne aka bada shari'a), to ina amfanin wani firist ya zo bisa ga ka'ida irin ta Malkisadak, ba'a kuma ambaci ka'idar Haruna ba?
\v 12 Don kuwa lokacin da aka canza firistanci, shari'a kuma dole ne a sauya ta.
\s5
\v 13 Domin mutumin da aka fadi wadannan abubuwa a kansa na wata kabila ne, wadda ba wani mutumin da ya taba yin aiki a kan bagadi.
\v 14 Wannan a bayyane yake Ubangijinmu ya zo ne daga zuriyar Yahuza, kabilar da Musa bai taba anbatonsu game da zancen firistanci ba.
\s5
\v 15 Abinda muke fadi a bayyane yake cewa, idan wani firist ya taso da kamanin Malkisadak.
\v 16 Wannan sabon firist, ba firist ne da ya taso bisa ga ka'idar zuriya ta yan'adam ba, amma ya zama firist ne ta rayuwa mai iko marar shudewa.
\v 17 Domin a rubuce yake cikin littafi ga me da shi; "Kai firist ne na har'abada bisa ga tsari irin na Malkisadak."
\s5
\v 18 Domin doka ta fari an ajiye ta a gefe guda saboda rarrauna ce kuma marar amfani.
\v 19 Don kuwa shari'a ba ta iya kamalta kome. Amma fa a kwai bege mai kyau a nan gaba wanda ta gare shi ne zamu sami iso a gun Allah.
\s5
\v 20 Kuma wannan kyakkyawan bege baya faruwa ba tare da rantsuwa ba, don kuwa su wadancan firistocin ba su dauki wata rantsuwa ba.
\v 21 Amma Allah yayi rantsuwa game da Yesu cewa, "Ubangiji ya rantse ba kuwa zai fasa tunaninsa ba; 'Kai firist ne har'abada.'"
\s5
\v 22 Ta wurin haka Yesu ya bada tabbatacce da kuma ingataccen alkwari.
\v 23 Hakika, mutuwa ta hana firistoci su yi aiki har'abada. Wannan shi ya sa akwai firistoci da yawa daya bayan daya.
\v 24 Amma da shi ke Yesu na rayuwa ne har'abada, aikinsa na firist ba a musanya shi sam sam.
\s5
\v 25 Domin haka kuma yana da cikakken ikon ceton wadanda ke gusowa ga Allah ta wurinsa, domin kullum a raye ya ke yana kuma roko dominsu
\v 26 . Domin irin wannan babban firist shi ne ya dace da mu. Ba shi da zunubi, marar abin zargi, tsarkakakke, kebabbe daga masu zunubi, ya na sama da sammai dukka.
\s5
\v 27 Ba shi da bukata, kamar manyan firistoci, da ke mika hadayu kullum, da farko don zunubin kansu, sa'annan don zunubin jama'a dukka. Amma Yesu yayi wannan sau daya tak ba kari don kowa da kowa, yayin da ya mika kansa.
\v 28 Domin shari'a na nada mutane da ke da gazawa a matsayin firistoci, amma maganar rantsuwa, wadda ta zo a bayan shari'a, ta nada Dan, wanda ya ke cikakke har'abada.
\s5
\c 8
\p
\v 1 Yanzu abin da muke kokarin cewa shine: Muna da babban firist wanda ke zaune a hannun dama na kursiyi mai martaba dake sammai.
\v 2 Shi kuwa bawa ne a wannan wuri mai tsarki, haikali na gaskiya wanda Allah ya shirya ba wani bil'adama ba.
\s5
\v 3 Kowanne babban firist kuwa yana mika bayebaye da hadayu. Don haka ya kamata a sami abin hadaya.
\v 4 Da a ce Almasihu yana duniya ba zai zama firist ba ko kadan.
\v 5 Domin a kwai masu mika hadaya bisa ga shari'a. Suna hidimar misalin abubuwan da suke inuwar sama. Kamar yadda Allah ya yi wa Musa gargadi yayin da ya ke shirin gina Alfarwa: "Duba" Allah ya ce, "kayi komai bisa ga salon da aka koya maka a bisa dutse."
\s5
\v 6 Amma yanzu hidimar da Almasihu ya karba ta dara tasu dukka, domin kuwa shine matsakancin muhimmin alkawari, wanda aka kammala a kan muhimman alkawura.
\v 7 Domin kuwa idan alkawarin fari ba shi da laifi babu anfanin neman alkawari na biyu.
\s5
\v 8 Da Allah ya sami laifi akan mutane, sai ya ce "Zan sake sabon alkawari da gidan Isra'ila da kuma gidan Yahuza.
\v 9 kuma ba zai zama kamar yadda nayi da kakanninku ba, kamar yadda na rike su a hannu har Na fidda su daga kasar Masar. Basu kuma ci gaba da Alkawarina ba, ni kuwa na yi watsi da su," inji Ubangiji.
\s5
\v 10 Gama wanna shine alkawarin da zan yi da gidan Isra'ila bayan wadannan kwanaki, Inji Ubangiji. Zan sa shari'a ta a bakinsu in kuma rubuta ta a zuciyarsu, Zan kuma zama Allah a garesu, su kuma su zama jama'ata.
\s5
\v 11 Ba za su kuma koyar da makwabta ko yan'uwansu cewa, "ku san Ubangiji" gama dukkanin su za su san ni, daga karami har zuwa babba.
\v 12 Zan kuma nuna tausayi ga ayyukan su na rashin adalci, ba kuma zan kara tunawa da zunubansu ba.
\s5
\v 13 A kan fadin "sabo" ya mayar da alkawarin fari tsoho. Wannan kuma da aka ambata tsoho na shirin bacewa.
\s5
\c 9
\p
\v 1 To ko da alkawarin farko ma ya na da wurin sujada da kuma ka'idojin sujada a nan duniya.
\v 2 Domin a cikin alfarwar akwai daki da aka shirya, daki na waje wanda ake kira wuri mai tsarki. A wannan wuri akwai kebabbun fitilu, akwai teburi da kuma gurasa.
\s5
\v 3 Kuma bayan labule na biyun akwai wani daki, wanda ake kira wuri mafi tsarki.
\v 4 Yana da bagadin zinariya domin turare. Yana kuma da akwatin alkawarin, wanda aka lailaye shi gaba daya da zinariya. A cikinsa a kwai kaskon zinariya dake dauke da manna, da sandar Haruna wadda tayi toho, da kuma allunan duwatsu na alkawarin.
\v 5 A sama da akwatin alkawarin akwai siffofin kerubobi masu daukaka da suke wa marfin jinkai inuwa, wadanda yanzu ba zamu iya yin bayani akansu ba daki daki.
\s5
\v 6 Bayan an shirya wadannan abubuwa, firistocin alfarwar sukan shiga daki na wajen alfarwar akai akai suna aikin hidimominsu.
\v 7 Amma babban firist din ne kadai yake shiga daki na biyun, sau daya tak a shekara, kuma tilas sai tare da jinin hadaya domin kansa, da kuma domin laifuffukan mutane da a kayi ba dagangan ba.
\s5
\v 8 Ruhu Mai Tsarki yana nuna cewar ba'a riga an bayyana hanyar zuwa wuri mafi Tsarki ba muddin alfarwar nan ta farko na a tsaye.
\v 9 Wannan ya zama bayani ne game da lokacin yanzu. Da kyaututtuka da hadayu dukka da ake mikawa basu iya sun kammala lamirin mai yin sujadar ba.
\v 10 Abinci ne da abin sha kawai wadanda aka hada da bukukuwan wanke wanke dabam dabam. Wadannan duka tsare tsare ne da aka shirya a dinga yi a zahiri har sai an shirya sabuwar ka'ida.
\s5
\v 11 Almasihu yazo a matsayin babban firist na abubuwa masu kyau da suka zo, ta wurin alfarwa babba, kammalalla kuma mafi tsarki wadda ba hannuwan mutane suka gina ba, wadda ba ta wannan duniyar aka halicce ta ba. Amma almasihu ya zo a matsayin babban firist na abubuwa masu kyau da ke zuwa.
\v 12 Ba ta jinin awaki da 'yan, maruka bane, amma Almasihu da jininsa ya shiga wuri mafi tsarki sau daya tak domin kowa dukka ya karbo mana fansa ta har abada.
\s5
\v 13 To idan jinin awaki da na bajimai da yayyafa tokar karsana bisa wadanda suka bata tsarkinsu yana tsarkake su ya wanke jikkunansu.
\v 14 To balle kuma jinin Almasihu, wanda ta wurin Ruhu madawwami ya mika kansa hadaya marar aibi ga Allah, wanda yake wanke lamirinmu daga matattun ayyuka domin muyi bautar Allah mai rai?
\v 15 Domin wannan dalili, Almasihu shine magamin sabon alkawari. Wannan kuwa ya kasance ne domin anyi mutuwar da ta 'yantar da wadanda ke karkashin tsohon alkawari daga sakamakon zunubansu, saboda wadanda Allah ya kira su karbi alkawarin gadonsu madawwami.
\s5
\v 16 Gama duk inda wani ya rubuta wasiyya ya bari, dole ne a tabbatar da mutuwar wanda yayi wasiyyar nan.
\v 17 Gama sai inda akayi mutuwa ake amfani da wasiyya, amma ba ta da amfani idan wanda ya rubuta ta yana nan da rai.
\s5
\v 18 Ko alkawari na farko bai tabbata ba sai tare da jini.
\v 19 Gama bayan Musa ya bada dukkan dokoki da ke cikin shari'ar ga dukkan mutanen, sai ya dauki jinin 'yan marukan da awakin, tare da ruwa, da jan yadi, da reshen itacen doddoya mai soso, ya yayyafa bisa mutanen da kuma littafin dokokin.
\v 20 Daga nan yace, "Wannan ne jinin alkawarin da Allah ya bayar da dokoki gareku."
\s5
\v 21 Ta haka kuma, ya yayyafa jinin bisa alfarwar da dukkan kayayyakin da ke cikinta wanda ake hidimar firistanci da su.
\v 22 Kuma bisa ga shari'a, kusan komai da jini ake tsarkake shi. Idan babu zubar da jini to babu gafarar zunubi.
\s5
\v 23 Saboda haka ya zama tilas wadannan kayayyaki na kwaikwayon abubuwan dake cikin sama a tsarkake su da hadayar dabbobi. Duk da haka abubuwa na sama dole a tsarkake su da hadaya mafi kyau.
\v 24 Domin Almasihu bai shiga cikin wuri mafi tsarki da aka yi da hannuwa ba, wanda kwaikwayo ne kawai na abin da ke na gaske. Maimakon hakan, ya shiga cikin samaniya da kanta, sa'an nan yaje gaban Allah domin mu.
\s5
\v 25 Bai je wurin don ya mika kansa sau da yawa, kamar yadda firist din alfarwa yake yi ba, wanda yake shiga wuri mafi tsarki kowacce shekara da jinin wata dabba.
\v 26 Idan haka ne, to dole ke nan ya sha wahala akai akai tun farkon duniya. Amma yanzu sau daya ne tak aka bayyana shi a karshen zamanai domin ya kauda zunubi ta wurin mika hadayar kansa.
\s5
\v 27 Kamar yadda aka kaddara wa kowa ya mutu sau daya tak, kuma bayan haka sai shari'a.
\v 28 Haka kuma Almasihu, wanda aka mika shi sau daya tak domin ya dauke zunuban mutane da yawa, zai kuma bayyana karo na biyu, ba domin yin aikin kawar da zunubi ba, amma domin ceton wadanda suke jiran zuwansa da hakuri.
\s5
\c 10
\p
\v 1 Domin shari'a hoto ce na kyawawan abubuwan da ke zuwa, ba ainihin siffar wadannan abubuwa ba. Wadanda ke gusowa kusa da Allah ba za su taba ingantuwa ta wurin hadayu da firistoci ke mikawa shekara da shekaru ba.
\v 2 In ba haka ba, ba sai a dena mika hadayun ba? Bisa ga wannan al'amari, inda sun tsarkaka sau daya tak da masu sujada ba su san menene zunubi ba.
\v 3 Amma wadannan hadayun sun zama matuni ne na zunubi shekara biye da shekara.
\v 4 Domin ba shi yiwuwa jinin bijimai da awakai su kawar da zunubai.
\s5
\v 5 Yayin da Almasihu ya zo duniya, ya ce, "Ba hadayu da sadakoki kake marmari ba. Maimakon haka, ka shirya mini jiki domin hadaya.
\v 6 Baka murna domin sadakoki da hadayu na konawa domin zunubi.
\v 7 Sai na ce, 'Duba, gani na zo in yi nufinka, kamar yadda aka rubuta akaina.'"
\s5
\v 8 Da fari Yace "ba hadayu, ko sadakoki, ko kuma hadaya ta konawa domin zunubi kake bukata ba. Ba ka kuwa jin dadinsu." Wadannan sune hadayun da ake bayarwa bisa ga shari'a.
\v 9 Sa'annan sai ya ce "gani na zo domin in aikata nufinka." Ya kawar da hidimar farko domin ya kafa hidima ta biyu.
\v 10 A hidima ta biyu, an kebe mu ga Allah ta wurin nufinsa ta wurin hadayar jikin Yesu Almasihu bugu daya ba kari.
\s5
\v 11 Haka, kowanne firist ya ke tsayawa kulliyomi domin ya yi hidima ga Allah. A kullum yana mika hadayu, iri daya, koda shike ba za su taba kawar da zunubai ba.
\v 12 A ta wata hanya kuma, Almasihu ya mika hadaya sau daya tak domin zunubai har abada, ya zauna a hannun dama na Allah.
\v 13 Yana jiran har a maida makiyansa matashin sawayensa.
\v 14 Domin ta wurin hadaya guda dayan nan ya kammala har abada ga wadanda suka sadaukar da kansu ga Allah.
\s5
\v 15 Kuma Ruhu mai Tsarki ya shaida mana. Abu na farko yace,
\v 16 "Wannan shi ne alkawarin da zan yi da su a bayan kwanakin nan,' inji Ubangiji Zan sa dokokina a cikin zukatansu, kuma zan rubuta su a lamirinsu.
\s5
\v 17 Ba zan sake tunawa da zunubansu da kurakuransu ba."
\v 18 Yanzu fa duk in da aka sami gafara domin wadannan abubuwa, babu wata hadaya domin zunubi.
\s5
\v 19 Saboda haka, yan'uwa, ba mu da shakkar shigowa wurin nan mafi tsarki ta wurin jinin Yesu.
\v 20 Wannan ita ce sabuwar rayayyar hanya da ya bude mana ta wurin labulen, wato ta wurin jikinsa.
\v 21 Saboda muna da babban firist a gidan Allah.
\v 22 Bari mu matso kusa da sahihiyar zuciya, da kuma cikakken gabagadi cikin bangaskiya, da zuciyarmu wadda aka tsarkake daga mummunan tunani, da kuma jikunanmu wankakku da ruwa mai tsabta.
\s5
\v 23 Bari mu rike da karfi shaidar bangaskiyar begenmu, ba tare da raurawa ba, domin Allahn, da ya yi alkawari, mai aminci ne.
\v 24 Bari mu kuma yi lura yadda za mu iza juna ga kauna da ayyuka masu dacewa.
\v 25 Kada mu fasa zumunci da juna, kamar yadda wadansu sukan yi. A maimakon haka, bari mu karfafa juna a kulluyomin, kamar yada kuke ganin kusantowar ranan nan.
\s5
\v 26 Saboda idan mun ci gaba da zunubin ganganci bayan mun rigaya mun sami wannan sanin gaskiyar, hadayar irin wannan zunubi bata samuwa.
\v 27 Maimakon haka, sai fargabar babban tsoron hukunci, da kuma wuta mai zafi, da zata cinye makiyan Allah.
\s5
\v 28 Dukkan wanda ya ki bin dokar Musa zai mutu ba tausayi ta wurin shaidu biyu ko uku.
\v 29 Wanne irin hukunci kuke tsammani ya dace ga wadanda suka raina Dan Allah, duk wadanda suka maida jinin alkawarin nan kamar ba tsarkakakke ba, wanda ta wurin jinin nan ne aka kebe shi ga Allah- wadanda suka wulakantar da Ruhun alheri?
\s5
\v 30 Domin mun san wanda yace, "Ramako nawa ne; Zan yi sakayya." Sa'annan kuma, "Ubangiji zai hukumta jama'arsa."
\v 31 Abin tsoro ne a fada cikin hannuwan Allah mai rai!
\s5
\v 32 Amma ku tuna da kwanakin baya, bayan da ku ka sami haske, yadda kuka jure babban fama cikin wahala.
\v 33 Aka kunyatar da ku a gaban jama'a, ta wurin ba'a da cin mutunci, kuna kuma dandana irin azabar da wadansu suka shiga ciki.
\v 34 Domin kuna da tausayi ga wadanda suke kurkuku, da farin ciki, kun amince da kwace na dukiyarku da aka yi, kun mallaki madauwamiyar mallaka mafi kyau. Dominn kun ji tausayina sa'adda na ke a kurkuku.
\s5
\v 35 Don haka kada ku yarda gabagadinku, wanda ke da babban sakamako.
\v 36 Domin kuna bukatar hakuri don ku sami abin da Allah ya alkawarta, bayan kun aikata nufinsa.
\v 37 "Domin a dan karamin lokaci, mai zuwan nan zai zo ba zai yi jinkiri ba.
\s5
\v 38 Adalina kuwa zai rayu ta wurin bangaskiya. In kuwa ya ja da baya, ba zan yi farin ciki dashi ba."
\v 39 Amma mu bama cikin wadanda suka ja da baya zuwa hallaka. Maimakon haka, muna cikin wadanda suke da bangaskiya domin kula da rayukanmu.
\s5
\c 11
\p
\v 1 Bangaskiya ita ce tabbatawar al'muran da muke begensu. Ita ce tabbatawar al'amuran da idanu basu gani.
\v 2 Domin ta wurin ta ne kakanninmu suka sami yardar Allah.
\v 3 Ta wurin ta ne aka hallicci duniya da umarnin Allah, har ma abubuwan da ake gani ba'a yi su daga abubuwan da suka kasance ba.
\s5
\v 4 Ta dalilin bangaskiya ne Habila ya mikawa Allah hadaya da ta fi dacewa fiye da ta Kayinu. Don haka ne kuma aka yaba masa akan cewa shi adali ne. Ya sami yardar Allah sabili da sadakarsa da ya bayar. Don haka kuma, harwayau Habila yana magana, ko da shike ya rigaya ya mutu.
\s5
\v 5 Ta dalilin bangaskiya aka dauki Anuhu zuwa sama domin kar ya ga mutuwa. "Ba a same shi ba kuwa, domin Allah ya dauke shi." Kamin a dauke shi an shaida da cewa ya faranta wa Allah zuciya.
\v 6 Zai yi wuya matuka a faranta wa Allah zuciya in ba tare da bangaskiya ba. Domin ya kamata dukkan wanda zai zo ga Allah, tilas ne ya bada gaskiya da kasancewar sa, kuma shi mai sakamako ne ga dukkan masu nemansa.
\s5
\v 7 Ta dalilin bangaskiya Nuhu, ya karbi sako daga Allah akan al'amuran da ba'a gani ba, ta wurin girmamawa da rawar jiki. ya gina jirgin ruwa domin ya ceci iyalan sa. Dalilin haka kwa, Allah ya hallakar da duniya, Nuhu kwa ya gaji adalci wadda ke bisa ga bangaskiya.
\s5
\v 8 Ta dalilin bangaskiya ne Ibrahim, sa'an da aka kira shi, ya yi biyayya sai ya tafi wurin da zai karba a matsayin gado. Ya kwa fita bai ma san inda za shi ba.
\v 9 Ta dalilin bangaskiya kuma ya zauna bare a kasar alkawari. Ya yi zama cikin Alfarwa tare da Ishaku da Yakubu, magadan alkawari guda tare da shi.
\v 10 Domin yana hangar birnin da ke da tushi, Birnin da mai zaiyanar sa da ginin sa shine Allah.
\s5
\v 11 Ta dalilin bangaskiya, Ibrahim ya sami haihuwa ko da shike shi da matarsa Saratu sun yi nisa a cikin shekaru, kuma Saratu bakarariya ce, ta kuma wuce lokacin haihuwa. Tun da shike sun amince da wanda ya yi musu alkawari mai aminci ne.
\v 12 Sabo da haka, ta wurin mutumin nan daya, wanda ya ke kamar matacce ne, aka haifi zuriya mai dimbin yawa, su ka yawaita kamar taurari a sama kamar yashi a bakin teku, wanda ba shi kidayuwa.
\s5
\v 13 Dukkan su kuwa suka mutu a cikin bangaskiya ba tare da sun karbi alkawarin ba. Maimakon haka, sun hango, kuma sun marabcesu daga nesa, sai suka amince su baki ne kuma matafiya ne a duniya.
\v 14 Gama wadanda suka yi furci haka sun nuna a fili cewa suna bidar kasa ta kansu.
\s5
\v 15 Da kamar suna tunanin kasar da suka fita daga ciki, da sun sa mi damar komawa.
\v 16 Amma kamar yadda yake, sun bukaci kasa mafi dacewa, wato, wadda take a sama. Saboda haka ne Allah bai ji kunyar a kira shi Allahnsu ba, da shike ya shirya birni dominsu.
\s5
\v 17 Ta dalilin bangaskiya ne Ibrahim, sa'adda aka yi masa gwaji, akan ya mika Ishaku dansa hadaya.
\v 18 Shi ne kuwa makadaicin dansa, wanda aka yi alkawari da cewa, "Ta wurinsa ne za a kira zuriyarka."
\v 19 Ibrahim ya yi tunani da cewa Allah na da ikon tada Ishaku ko daga cikin matattu ma, haka kuwa yake a misalce, daga matattun ne ya sake karbarsa.
\s5
\v 20 Ta dalilin bangaskiya ne kuma Ishaku ya albarkaci Yakubu da Isuwa game da abubuwan da ke zuwa a gaba.
\v 21 Dalilin bangaskiya ne Yakubu, sa'adda yake bakin mutuwa, ya albarkaci 'ya'yan Yusufu dukkansu biyu. Yakubu ya yi ibada, yana tokare a kan sandarsa.
\v 22 Ta dalilin bangaskiya Yusufu, sa'adda karshensa ya kusa, ya yi magana game da fitar 'ya'yan Isra'ila daga Masar har ya umarce su game da kasussuwansa.
\s5
\v 23 Ta dalilin bangaskiya Musa, sa'adda aka haife shi, iyayensa suka 'boye shi kimanin watanni uku domin kyakkyawan yaro ne shi, kuma basu ji tsoron dokar sarki ba.
\v 24 Ta dalilin bangaskiya ne kuma Musa, sa'adda ya girma, yaki a kira shi 'dan diyar Fir'auna.
\v 25 A maimakon haka, ya amince ya sha azaba tare da jama'ar Allah, a kan shagali da annashuwar zunubi na karamin lokaci.
\v 26 Ya fahimci cewa wulakanci domin bin Almasihu babbar wadata ce fiye da dukiyar Masar. Gama ya kafa idanunsa a kan sakamakon da ke gaba.
\s5
\v 27 Ta dalilin bangaskiya Musa ya bar Masar. Bai ji tsoron fushin sarki ba, ya jure kamar yana ganin wannan da ba a iya ganinsa
\v 28 Ta dalilin bangaskiya ya yi idin ketarewa da kuma yayyafa jini, domin kada mai hallaka 'ya'yan fari ya taba 'ya'yan fari na Isra'ila.`
\s5
\v 29 Ta dalilin bangaskiya suka haye baharmaliya kamar bushashiyar kasa. Sa'adda Masarawa su ka yi kokarin hayewa, bahar din ta hadiye su.
\v 30 Ta dalilin bangaskiya ganuwar Yeriko ta fadi, bayan sun kewaya ta har kwana bakwai.
\v 31 Ta dalilin bangaskiya Rahab karuwan nan bata hallaka tare da marasa biyayya ba, don ta saukar da masu leken asirin kasa a gidanta, ta kuma sallame su lafiya.
\s5
\v 32 Me kuma za mu ce? Gama lokaci zai kasa mini idan zan yi magana game da Gidiyon, Barak, Samson, Yefta, Dauda, Sama'ila, da annabawa.
\v 33 Ta dalilin bangaskiya suka ci nasara kan kasashe, suka yi aikin adalci, sa'annan suka karbi alkawura. Suka rufe bakin zakuna,
\v 34 suka kashe karfin wuta, suka tsira daga bakin takobi, suka sami warkaswa daga cutattuka, suka zama jarumawan yaki, sa'annan suka ci nasara akan rundunar sojojin al'ummai.
\s5
\v 35 Mata kuwa suka karbi matattunsu da aka tayar daga mutuwa. Aka azabtar da wadansu, ba su nemi yancin kansu ba, domin suna begen tashi daga mattatu.
\v 36 Wadansu kuwa suka sha ba'a da duka da bulala, har ma da sarka da kurkuku.
\v 37 A ka jejjefe su. Aka tsaga su kashi biyu da zarto. A ka karkashe su da takobi. Su na yawo sanye da buzun tumakai da na awaki, suka yi hijira, suka takura, suka wulakantu.
\v 38 Duniya ma ba ta dauke su a matsayin komai ba. Suka yi ta yawo a jazza, da duwatsu, da kogwanni, da kuma ramummuka.
\s5
\v 39 Ko da yake mutanen nan amintattun Allah ne domin bangaskiyarsu, basu karbi cikar alkawarin ba tukunna.
\v 40 Domin Allah ya shirya mana wani abu mafi kyau ba kuwa za su kammala ba sai tare da mu.
\s5
\c 12
\p
\v 1 Da shike muna kewaye da wannan irin kasaitaccen taro na shaidu, sai mu watsar da dukkan abubuwan dake nawaita mana da kuma zunubin da zai saurin makale ma na. Bari a cikin hakuri mu yi tseren da ke gabanmu.
\v 2 Bari mu kafa idonmu ga Yesu, wanda shine mafarin bangaskiyarmu da cikarta. Wanda sabili da murnar da a ka sa a gabansa ya jimre giciye, ya kuma yi watsi da kunyarsa, wanda kuma ya zauna a hannun dama na kursiyin Allah.
\v 3 Ku dube shi wanda ya jimre irin wannan adawa daga masu zunubi, domin kada ku gaji ko ku karai.
\s5
\v 4 Ba ku yi tsayayya ko jayayya da zunubi har ta kai ga zub da jininku ba tukunna. Kun kuma manta da gargadin da a ka yi maku a matsayin 'ya'ya:
\v 5 "Dana, kada ka dauki horon Ubangiji da wasa, kadda kuma ka yi suwu lokacin da ka sami horonsa,"
\v 6 Domin kuwa Ubangiji yana horon dukkan wadanda yake kauna, yana kuma hukunta duk wadanda ya karba.
\s5
\v 7 Ku daure wahala a matsayin horo. Allah yana yi da ku kamar 'ya'yansa, domin kuwa wanne da ne wanda ubansa bazai yi masa horo ba?
\v 8 Amma idan baku da horo kamar yadda sauran mutane ke da shi, kun zama shegu kenan ba 'ya'ya ba.
\s5
\v 9 Hakannan kuma kamar yadda muke da iyaye a duniya wadanda suke yi mana horo, kuma muna basu daraja. To ba sai mu yiwa Ubanmu na Ruhaniya biyayya don mu rayu ba?
\v 10 Ta wani fanni kuwa iyayenmu suna yi mana horo na kwanaki kadan bisa ga yadda suka ga ya dace, Amma Allah kuwa yana yi mana horo domin anfanin kanmu, domin kuma mu sami rabo daga cikin tsarkinsa.
\v 11 Ba horon da ke da dadi a lokacin yinsa, amma sai zafi. Sai dai kuma bayan haka yakan haifar da 'ya'ya na ruhaniya da kuma adalci ga dukkan wadanda aka yi rainonsu a ciki.
\s5
\v 12 Don haka sai ku karfafa hannayenku da ke reto, da kuma guwawunku da ke kaduwa.
\v 13 Ku bi hanyoyi mikakku domin abin da ya gurgunce kada ya karye amma ya warke.
\s5
\v 14 Ku bidi salama da kowa, da kuma rayuwar tsarki wanda in ba tare da shi, babu wanda zai ga Allah.
\v 15 Ku mai da hankali domin kada waninku ya rasa, alherin Allah, kuma kada wani tushe mai daci ya tsiro a cikinku har ya haifar da fitina, domin kada da dama daga cikinku su gurbata ta wurinsa.
\v 16 Ku yi hankali kuma kada a sami mazinanci ko marar ibada a cikinku, kamar Isuwa, wanda sabili da abinci ya sayar da 'yancinsa na dan fari.
\v 17 Kun kuwa san cewa sa'adda ya yi marmarin ya gaji albarka a gaba, an kishi, domin kuwa bai sami damar tuba ba, ko da shike ya nema har da hawaye.
\s5
\v 18 Domin kuwa baku zo ga dusen da ake tabawa da hannu ba, dutse ne mai ci da wuta, da tukuki da bakin hayaki da hadari.
\v 19 Ba Ku zo ga karar kaho mai ban razana da murya mai firgitarwa ba, da masu sauraro suka yi roko kar su sake jinta.
\v 20 Don basu iya jimre abin da aka yi doka a kan saba: "koma dabba ce ta taba dutsen, sai a jejjefe ta."
\v 21 Abin tsoro ne kuwa kwarai, har Musa yace, "A tsoroce nake kwarai har na firgita."
\s5
\v 22 Maimakon haka kun zone ga Dutsen Sihiyona da kuma birni na Allah mai Rai, kuma na Urushalima ta Samniya, da kuma dubun dubban mala'iku cikin murna da farin ciki.
\v 23 Kun zo taro na dukkan 'ya'yan fari, rubuttatu a sama, kuma kun zo ga Allah wanda shine alkalin dukka, hakannan kuma zuwa ga ruhu na adalai wanda a ka rigaya aka tsarkake.
\v 24 Kun zo ga Yesu, wanda shine matsakancin sabon alkawari, kuma ga jinin yayyafawa da ke magana fiye da na jinin Habila.
\s5
\v 25 Ku yi lura kada ku ki wannan da ke yi mu ku magana. Gama in har basu kubuta yayin da su ka yi jayayya da wanda ya yi mu su gargadi a duniya ba, balle ma mu ba za mu kubuta ba in mun ki wanda ke mana gargadi daga sama.
\v 26 A wani karo, muryar sa ta girgiza duniya. Amma yanzu yayi alkawari da cewa, "Har'ila yau ba duniyar kadai zan girgiza ba, amma har da sammai."
\s5
\v 27 Wannan kalma, "Harl'ila yau," ta bayyana cirewar abubuwan nan da za su girgizu, wato abubuwan da a ka halitta, domin abubuwan da ba zasu girgizu ba su kasance.
\v 28 Don haka, samun mulkin da ba za ya girgizu ba, sai mu zama masu godiya, kuma a cikin wannan yanayi mu yi wa Allah sujada cikin daraja da tsaninin gimamawa.
\v 29 Domin kuwa Allahnmu wuta ne mai konewa.
\s5
\c 13
\p
\v 1 Bari kaunar 'yan'uwa ta cigaba.
\v 2 Kada ku manta da karrama baki, domin ta wurin yin haka, wasu suka marabci mala'iku ba tare da saninsu ba.
\s5
\v 3 Ku tuna da wadanda ke cikin kurkuku, kamar dai kuna tare da su cikin wannan hali. Kuma ku tuna da masu shan azaba kamar tare kuke cikin wannan hali
\v 4 Bari kowa ya girmama aure, bari kuma a tsarkake gadon aure, gama Allah zai shar'anta fasikai da mazinata.
\s5
\v 5 Bari halinku ya kubuta daga kaunar kudi. Ku dangana da abubuwan da kuke dasu, domin Allah da kansa yace, "Bazan barku ba, ba kuma zan yashe ku ba."
\v 6 Bari mu zama da dangana domin mu sami gabagadin cewa, "Ubangiji ne mai taimakona, ba zan ji tsoro ba. To me mutum zai iya yi mani?"
\s5
\v 7 Ku fa lura da wadanda ke shugabanninku, wadanda suka horar da ku cikin maganar Allah, kuma ku lura da sakamakon rayuwarsu, ku yi koyi da bangaskiyarsu.
\v 8 Yesu Almasihu daya ne a jiya, da yau, da har abada.
\s5
\v 9 Kada ku kauce zuwa ga bakin koyarwa daban daban, domin yana da kyau zuciya ta ginu ta wurin alheri, amma ba da dokoki game da abinci ba, wadanda basu taimaki wadanda suka kiyayesu ba.
\v 10 Muna da bagadin da wadanda ke hidima a cikin alfarwa basu da ikon su ci daga bisansa.
\v 11 Babban firist na shiga wuri mai tsarki da jinin dabbobin da aka yanka, hadayar zunubai, amma namansu a kan kai bayan sansani a kone shi.
\s5
\v 12 Domin haka Yesu shima ya sha wahala a bayan kofar birnin, domin ya tsarkake mutane ta wurin jininsa.
\v 13 Domin haka bari mu tafi gare shi a bayan sansani dauke da kunyarsa.
\v 14 Domin bamu da wani birni dawwamamme a nan. Maimako haka muna bidar birni dake zuwa.
\s5
\v 15 Ta wurin sa kuma, bari kullum mu mika hadayu na yabo ga Allah, yabon kuwa shine kalmomin bakinmu da ke daukaka sunansa.
\v 16 Kada kuma mu manta da yin nagarta da kuma taimakon juna, domin Allah na farin ciki sosai da irin wadannan hadayun.
\v 17 Ku yi biyayya da sadaukarwa ga shugabanninku, domin suna aikin tsaro a kanku saboda rayukanku, kamar wadanda zasu bada lissafi. Kuyi biyayya gare su saboda su yi aikin lura daku cikin farin ciki, ba da bakin ciki ba, don in su yi da bakin ciki ba zai amfane ku ba.
\s5
\v 18 Kuyi mana addu'a, domin mun tabbata muna da lamiri mai tsabta, kuma muna burin muyi rayuwar dake daidai cikin dukkan al'amura.
\v 19 Kuma ina karfafa ku dukka kuyi haka, domin in sami dawowa gareku da sauri.
\s5
\v 20 To bari Allahn salama, wanda ya tada babban makiyayin tumakin nan daga matattu, Ubangijinmu Yesu, ta wurin jinin madawwamin alkawari,
\v 21 ya kammala ku da dukan abu mai kyau domin ku aikata nufinsa. Bari yayi aiki a cikinmu wanda zai gamshe shi sosai. Ta wurin Yesu Almasihu, bari daukaka ta tabbata gare shi har abada. Amin.
\s5
\v 22 'Yan'uwa, yanzu dai ina karfafa ku, da ku jurewa takaitacciyar maganar karfafawar da na rubuto maku.
\v 23 Ina so ku sani an saki dan'uwan mu Timoti, tare da shi zan zo in gan ku idan ya iso da sauri.
\s5
\v 24 Ku gaida shugabanninku dukka da kuma dukkan masu bada gaskiya. 'Yan'uwa daga can Italiya suna gaishe ku.
\v 25 Bari alheri ya kasance tare daku dukka.