ha_ulb/57-TIT.usfm

108 lines
6.3 KiB
Plaintext

\id TIT
\ide UTF-8
\h Titus
\toc1 Titus
\toc2 Titus
\toc3 tit
\mt Titus
\s5
\c 1
\p
\v 1 Bulus, bawan Allah, kuma manzon Yesu Almasihu, ta wurin bangaskiyar zababbun mutanen Allah da sanin gaskiya da ta yadda da allahntaka.
\v 2 Wadannan na cikin begen rai marar matuka wanda Allah, wanda babu karya a cikinsa, ya alkawarta kafin dukkan lokatan zamanai.
\v 3 A daidai lokaci, ya bayyana maganarsa ta wurin sakonsa da ya damka mani in shelar. Zan yi wannan ta wurin umarnin Allah mai ceton mu.
\s5
\v 4 Zuwa ga Titus, da' na gaske a cikin bangaskiyarmu. Alheri, jinkai da salama daga wurin Allah Uba da Almasihu Yesu mai ceton mu.
\v 5 Sabili da wannan ne na bar ka a Karita domin ka daidaita abubuwan da basu cika ba, ka kuma nada dattibai a dukan birane kamar yadda na umarceka.
\s5
\v 6 Dole ne dattijo ya zama marar abin zargi, mijin mace daya, da amintattun 'ya'ya wadanda babu wani zargi na mugunta ko rashin kamun kai a kansu.
\v 7 Wajibi ne shugaban Ikklisiya, a matsayin sa na mai kulla da haikalin Allah, ya zama marar aibi. Kada ya zama mai surutu ko rashin hakuri. Kada ya zama mai saurin fushi, ko mashayi, ko mai hayaniya, ko mai handama.
\s5
\v 8 Maimakon haka, ya zama mai karbar baki, abokin abinda ke mai kyau. Dole ne ya zama mai hankali, adali, cike da allahntaka, da kuma kamun kai.
\v 9 Ya zama mai rike amintaccen sakon da aka koyar da karfi, yadda zai iya karfafa wasu da koyarwa mai kyau ya kuma yi wa wadanda suke hamayya da shi gyara.
\s5
\v 10 Domin akwai kangararrun mutane dayawa, musamman masu kaciya. Maganganunsu na banza ne. Suna yaudara kuma suna badda mutane.
\v 11 Wajibi ne mu hana su. Suna koyar da abinda bai kamata su koyar ba saboda makunyaciyar riba suna kuma rusar da iyalai dungum.
\s5
\v 12 Daya daga cikinsu, kuma mai hikima ne daga cikinsu, yace, "Kirawa manyan makaryata ne, lalatattu kuma miyagun dabbobi, masu kyiuya da zarin cin abinci."
\v 13 Wannan magana gaskiya ne, ka yi masu gyara da tsanani yadda zasu kafu a cikin bangaskiya.
\s5
\v 14 Kada ka mai da hankalin ka ga tatsunniyoyi na Yahudawa ko dokokin mutane wadanda sun sauya gaskiya.
\s5
\v 15 Ga wadanda suke da tsarki, komai mai tsarki ne. Amma wadanda suke marasa tsarki da rashin bangaskiya, komai marar tsarki ne. Domin zuciyarsu da lamirinsu sun gurbata.
\v 16 Suna cewa sun san Allah, amma sun musanta shi ta wurin ayyukansu. Sun zama abin kyama da marasa biyayya. Ba za a iya tabbaatar dasu ba akan wani aiki maikyau.
\s5
\c 2
\p
\v 1 Amma kai, ka fadi abinda yayi daidai da amintaccen umarni.
\v 2 Dole tsofaffin mazaje su zama masu kamun kai, masu daraja kansu, masu-hankali, masu aminci cikin bangaskiya, cikin kauna da jurewa.
\s5
\v 3 Haka ma tsofaffin mataye su kame kansu da girma, ba magulmata ba. Kada su zama bayi wajen yawan shan ruwan inabi. Su koyar da abubuwa masu kyau
\v 4 domin su koyar da kananan mataye da hikima su kaunaci mazajensu da 'ya'yansu.
\v 5 Su horar dasu su zama masu hikima da tsabtar zuci, masu tsaron gidajensu, kuma masu biyayya da mazajensu. Suyi wadannan abubuwa saboda kada maganar Allah ta sami zargi.
\s5
\v 6 Ta haka kuma, ka karfafa samari, su zama masu hankali.
\v 7 A kowanne fanni, ka mayar da kan ka abin koyi a cikin kyawawan ayyuka; idan kayi koyarwa, ka nuna mutunci da martaba.
\v 8 Ka bada sako lafiyayye marar abin zargi, yadda masu hamayya da maganar Allah zasu ji kunya, domin rashin samun mugun abin fadi akan mu.
\s5
\v 9 Bayi suyi biyayya ga iyayengijin su a cikin komai. Su faranta masu rai, ba suyi gardama dasu ba.
\v 10 Kada suyi sata. Maimakon haka, sai su nuna dukan bangaskiya mai kyau, domin suyi wa koyarwarmu game da Allah mai cetonmu kwalliya a cikin dukan komai.
\s5
\v 11 Domin alherin Allah ya bayyana ga dukan mutane.
\v 12 Yana koya mana mu musanci miyagun ayyuka, da sha'awoyin duniya. Yana horar damu muyi zama cikin hankali, da adalci a cikin hanyar allahntaka a wannan zamani
\v 13 yayin da muke cigaba da jiran karba albarkataccen begenmu, wato bayyanuwar daukakar Ubangiji Allah da kuma mai cetonmu Yesu Almasihu.
\s5
\v 14 Yesu ya bada kansa domin mu, domin ya cece mu daga rashin kiyaye doka ya mai damu masu tsarki, domin sa, mutane na musamman wadanda suke da marmarin aikata kyawawan ayyuka.
\s5
\v 15 Ka yi magana da karfi ka karfafawa wadannan abubuwa. Ka yi gyara da dukan iko. Kada ka bar wani ya raina ka.
\s5
\c 3
\p
\v 1 Ka tuna masu su zama masu sadaukar da kai ga masu mulki da masu iko, suyi masu biyayya, su zama a shirye domin kowane kyakkyawan aiki.
\v 2 Ka tuna masu kada su zagi kowa, su gujiwa gardama, su bar mutane su bi hanyarsu, su kuma nuna tawali'u ga dukan mutane.
\s5
\v 3 Domin a da, mu da kan mu marasa tunani ne kuma masu rashin biyayya. Mun kauce hanya muka zama bayi ga sha'awoyin duniya da annashuwa. Mun yi zama a cikin mugunta da kishi. Mu lalatattu ne kuma muna kiyyaya da junanmu.
\s5
\v 4 Amma da jinkan Allah mai ceton mu da kaunarsa ga 'yan Adam ta bayyana,
\v 5 ba saboda wani aikin adalci da muka yi ba, amma sabili da jinkan sa ne ya cece mu. Ya cece mu ta wurin wankewar sabuwar haihuwa da sabuntuwar Ruhu Mai Tsarki.
\s5
\v 6 Allah ya zubo mana Ruhu Mai Tsarki a wadace ta wurin Yesu Almasihu mai cetonmu.
\v 7 Ya yi wannan saboda, bayan mun samu 'yantarwa ta wurin alherinsa, za mu zama magada a cikin begen rai na har abada.
\s5
\v 8 Wannan amintaccen sako ne. Ina son kayi magana gabagadi game da wadannan abubuwa, yadda dukan wadanda suka bada gaskiya ga Allah za suyi kudirin yin kyawawan ayyuka da Allah ya mika masu. Waddannan abubuwa masu kyau ne da kuma riba ga dukan mutane.
\s5
\v 9 Amma ka guji gardandami na wofi, da lissafin asali, da husuma da jayayya game da dokoki. Wadannan abubuwa basu da amfani kuma marasa riba.
\v 10 Ka ki duk wani dake kawo tsattsaguwa a tsakaninku, bayan ka tsauta masa sau daya ko biyu,
\v 11 ka kuma sani cewa wannan mutumin ya kauce daga hanyar gaskiya, yana zunubi kuma ya kayar da kansa.
\s5
\v 12 Sa'adda na aiki Artimas da Tikikus zuwa wurin ka, kayi hanzari ka same ni a Nikobolis, a can na yi shirin kasancewa a lokacin hunturu.
\v 13 Kayi hanzari ka aiko Zinas wanda shi gwani ne a harkar shari'a, da Afolos ta yadda ba zasu rasa komai ba.
\s5
\v 14 Ya kamata Jama'armu su koyi yadda zasu yi ayyuka masu kyau da zasu biya bukatu na gaggawa yadda ba za suyi zaman banza ba.
\s5
\v 15 Dukan wadanda suke tare da ni suna gaishe ka. Ka gai da masu kaunar mu a cikin bangaskiya. Alheri ya kasance tare da dukan ku.