ha_ulb/56-2TI.usfm

159 lines
10 KiB
Plaintext

\id 2TI
\ide UTF-8
\h Wasikar Bulus Manzo Ta Biyu Zuwa Ga Timoti
\toc1 Wasikar Bulus Manzo Ta Biyu Zuwa Ga Timoti
\toc2 Wasikar Bulus Manzo Ta Biyu Zuwa Ga Timoti
\toc3 2ti
\mt Wasikar Bulus Manzo Ta Biyu Zuwa Ga Timoti
\s5
\c 1
\p
\v 1 Bulus, manzon Almasihu Yesu ta wurin nufin Allah, bisa ga alkawarin rai da ke cikin Almasihu Yesu,
\v 2 zuwa ga Timoti, kaunataccen da: Alheri, jinkai, da salama daga Allah Uba da Almasihu Yesu Ubangijinmu.
\s5
\v 3 Na gode wa Allah, wanda na ke bautawa tun daga kakannina, da lamiri mai tsabta, sa'adda na ke tuna wa da kai cikin addu'o'ina koyaushe (dare da rana).
\v 4 Sa'adda na tuna da hawayenka, na yi marmarin ganinka, saboda in cika da farin ciki.
\v 5 An tunashshe ni game da sahihiyar bangaskiyarka, wadda ta samo asali daga kakarka Loyis da mahaifiyarka Afiniki. Na kuma tabbata ta na zaune a cikinka.
\s5
\v 6 Wannan shine dalilin da ni ke tunashshe ka cewa ka sake rura baiwar Allah da ke cikinka wadda ka samu sa'adda na dibiya maka hannuwana.
\v 7 Domin Allah bai ba mu ruhun tsoro ba, amma na iko da kauna da kamun kai.
\s5
\v 8 Saboda haka kada ka ji kunyar shaida ga me da Ubangijinmu, ko ni, Bulus, daurarrensa. Maimakon haka, ka zama a shirye ka sha wahala domin bishara bisa ga ikon Allah.
\v 9 Allah ne ya cecemu kuma ya kira mu da kira mai tsarki. Ya yi wannan, ba ta wurin ayyukanmu ba, amma ta wurin shirinsa da alherinsa. Ya ba mu wadannan abubuwan a cikin Almasihu Yesu kafin farkon zamanai.
\v 10 Amma yanzu an bayyana ceton Allah ta wurin bayyanuwar mai cetonmu Almasihu Yesu. Almasihu ne ya kawo karshen mutuwa ya kuma kawo rai marar karshe da ya bayyana ta wurin bishara.
\v 11 Domin wannan, an zabe ni mai wa'azi, manzo da mallami zuwa ga al'ummai.
\s5
\v 12 Domin wannan dalili na ke shan wahalar wadannan abubuwa. Amma ban ji kunya ba, domin na san shi, wanda na gaskanta. Na sakankance zai iya adana abinda na mika masa har zuwa ranan nan.
\v 13 Ka adana misalin amintattun sakwanni da ka ji daga gare ni, ta wurin bangaskiya da kauna da ke cikin Almasihu Yesu.
\v 14 Abu mai kyau da Allah ya danka maka, ka tsare shi ta wurin Ruhu Mai Tsarki, da ke zaune a cikinmu.
\s5
\v 15 Ka dai sani, dukkan wadanda su ke zama a Asiya sun juya mani baya. A cikin kungiyar akwai Fijalas da Harmajanas.
\v 16 Bari Ubangiji ya yi wa iyalin Onisifaras jinkai, domin ya na yawan yi mani hidima, kuma ba ya jin kunyar sarkata.
\v 17 Maimakon haka, sa'adda ya ke a Roma, ya neme ni da kokarin gaske, ya kuma same ni.
\v 18 Bari Ubangiji ya sa, ya sami jinkai daga gare shi a wannan rana. Dukkan hanyoyin da ya taimake ni a kasar Afisa, kun sani sarai.
\s5
\c 2
\p
\v 1 Domin wannan kai, dana, ka karfafa cikin alherin da ke cikin Almasihu Yesu.
\v 2 Abubuwan da ka ji daga gare ni a bainar jama'a masu yawa, ka danka su ga mutane masu aminci da za su iya koya wa wadansu kuma.
\s5
\v 3 Ka daure shan tsanani tare da ni, kamar amintaccen sojan Almasihu Yesu.
\v 4 Ba bu sojan da zai yi bauta yayin da ya nannade kansa da al'amuran wannan rayuwar, domin ya gamshi shugabansa.
\v 5 Hakanan, idan wani yana gasa a matsayin dan wasa, ba zai sami rawani ba tukuna har sai in ya karasa tseren bisa ga ka'idodin gasar.
\s5
\v 6 Wajibi ne manomi mai kwazon aiki ya fara karbar amfanin gonarsa.
\v 7 Ka yi tunani game da abin da na ke gaya maka, gama Ubangiji zai ba ka ganewa a cikin komai.
\s5
\v 8 Ka tuna da Yesu Almasihu, daga zuriyar Dauda, wanda a ka tayar daga matattu. Bisa ga wa'azin bisharata,
\v 9 wanda na ke shan wahala har ya kai ga dauri kamar mai laifi. Amma maganar Allah ba a daure ta ba.
\v 10 Saboda haka na jure wa dukkan abubuwa domin wadanda aka zaba, saboda su ma su sami ceton da ke cikin Almasihu Yesu, da daukaka madawwamiya.
\s5
\v 11 Wannan magana tabbatacciya ce: "Idan mun mutu tare da shi, za mu kuma rayu tare da shi.
\v 12 Idan mun jure, zamu kuma yi mulki tare da shi. Idan mun yi musun sa, shi ma zai yi musun mu.
\v 13 Idan mun zama marasa aminci, shi mai aminci ne koyaushe, domin shi ba zai yiwu ya musunta kansa ba."
\s5
\v 14 Ka yi ta tuna masu da wadannan abubuwan. Ka yi masu kashedi a gaban Allah kada su yi ta dauki ba dadi game da kalmomi. Saboda wannan bai da wani amfani. Domin wannan zai halakar da ma su sauraro.
\v 15 Ka yi iyakacin kokarika domin ka mika kanka ma'aikacin Allah wanda aka tabbatar, wanda babu dalilin kunya a gareshi. Wanda ya ke koyar da kalmar gaskiya daidai.
\s5
\v 16 Ka guje wa masu maganar sabo, wanda ya kan kara kaiwa ga rashin bin Allah.
\v 17 Maganarsu za ta yadu kamar ciwon daji. Daga cikinsu akwai Himinayus da Filitus.
\v 18 Wadannan mutanen sun kauce wa gaskiya. Sun fadi cewa an rigaya an yi tashin matattu. Suka birkitar da bangaskiyar wadansu.
\s5
\v 19 Duk da haka, ginshikin Allah ya tabbata. Ya na da wannan hatimi: "Ubangiji ya san wadanda ke nasa," Kuma "Duk mai kira bisa ga sunan Ubangiji dole ya rabu da rashin adalci."
\v 20 A gida mai wadata, ba kayayyaki na zinariya da azurfa ba ne kawai. Haka kuma akwai kayayyaki na itace da yunbu. Wadansu domin aikin mai daraja, wadansu kuma ga aiki mara daraja.
\v 21 Idan wani ya tsarkake kansa daga rashin daraja, shi kayan aiki ne mai daraja. An kebe shi, abin aiki domin mai gidan, kuma a shirye domin kowanne aiki mai kyau.
\s5
\v 22 Ka guje wa sha'awoyi na kuruciya, ka nemi adalci, bangaskiya, kauna da salama da wadanda suke kira ga sunan Ubangiji daga zuciya mai tsabta.
\v 23 Amma ka ki tambayoyi na wauta da jahilci. Ka sani sukan haifar da gardandami.
\s5
\v 24 Tilas bawan Ubangiji ya guje wa jayayya. A maimakon haka dole ya zama mai tawali'u ga kowa, mai iya koyarwa, kuma mai hakuri.
\v 25 Dole ne ya koyarwa mutane da su ke jayayya da shi a cikin tawali'u. Watakila Allah ya ba su ikon tuba domin sanin gaskiyar.
\v 26 Suna iya sake dawowa cikin hankalinsu kuma su bar tarkon Ibilis, bayan da ya cafke su domin nufinsa.
\s5
\c 3
\p
\v 1 Amma ka san da wannan: a cikin kwanakin karshe za a yi lokuta masu matsananciyar wahala.
\v 2 Gama mutane za su zama masu son kansu, masu son kudi, masu Kumburi, da girman kai, masu sabo, marasa biyayya ga iyaye, marasa godiya, da kuma marasa tsarki.
\v 3 Za su kasance marasa dabi'a, wadanda basu son jituwa da kowa, masu tsegumi, marasa kamun kai, 'yan tawaye, marasa kaunar nagarta.
\v 4 Za su zama masu zagon kasa, taurin kai, masu takama, da masu kaunar anishuwa fiye da kaunar Allah.
\s5
\v 5 Za su kasance da siffar ibada amma za su musunci ikonta. Ka juya daga wadannan mutanen.
\v 6 A cikinsu akwai wadanda suke shiga gidaje suna yaudarar mataye marasa hikima. Wadannan ne mataye wadanda suke cike da zunubi, kuma sun kauce hanya sabili da sha'awoyi dabam daban.
\v 7 Wadannan matayen suna ta koyo, amma ba za su taba kai wa ga sanin gaskiya ba.
\s5
\v 8 Kamar yadda Yannisu da Yambrisu suka yi jayayya da Musa. Haka nan wadannan malaman karya kuma suke yin tsayayya da gaskiya. Mutane ne lalatattu a zuciya, marasa sahihiyar bangaskiya.
\v 9 Amma ba za su yi nisa ba. Domin wautarsu za ta bayyana a fili ga kowa, kamar wadannan mutane.
\s5
\v 10 Amma kai, ka bi koyarwata, da dabi'ata, nufe nufena, da bangaskiyata, da jimriyata, da kaunata, da hakurina,
\v 11 da yawan kuncina, da wahalolina, da duk abubuwan da suka faru da ni a Antakiya, da Ikoniya da kuma Listra. Na jure a cikin kuncina. Amma a cikinsu dukka, Ubangiji ya cece ni.
\v 12 Duk wadanda su ke so su yi rayuwa ta ibada a cikin Almasihu Yesu za su sha tsanani.
\v 13 Miyagun mutane da masu hila za su yi ta kara lalacewa. Za su badda wasu. Su da kansu ma sun bijire.
\s5
\v 14 Amma kai, ka ci gaba da abubuwan da ka koya kuma ka gaskata da zuciya daya. Ka san daga wurin wanda ka koya.
\v 15 Ka san da cewa, tun kana dan karamin yaro ka san wadannan littattafai masu tsarki. Wadannan suna iya mai da kai mai hikima domin ceto ta wurin bangaskiya a cikin Almasihu Yesu.
\s5
\v 16 Dukkan Nassi hurarre ne daga Allah. Yana da amfani domin koyarwa, domin tsautawa, domin gyara, kuma domin horarwa cikin adalci.
\v 17 Wannan domin mutumin Allah ya zama cikakke ne, shiryayye domin dukkan ayyukan nagarta.
\s5
\c 4
\p
\v 1 Ina bada wannan umarni a gaban Allah da Yesu Almasihu, wanda zai yi wa rayayyu da matattu shari'a, kuma saboda bayyanuwarsa da mulkinsa:
\v 2 Ka yi wa'azin Kalma. Ka himmantu a kai ko da zarafi ko ba zarafi. Ka tsautar, ka kwabar, ka gargadar, da dukan hakuri da koyarwa.
\s5
\v 3 Gama lokaci na zuwa wanda mutane ba za su jure wa koyarwar kirki ba. Maimakon haka, zasu tattara wa kansu malamai bisa ga sha'awowin zuciyarsu. Za su rika fada masu abin da kunnuwansu ke so.
\v 4 Za su juya kunnuwansu daga koyarwar gaskiya, za su koma wa tatsunniyoyi na banza.
\v 5 Amma kai, sai ka natsu a cikin dukan abubuwa. Ka jure wa wahala; ka yi aikin mai bishara, ka cika hidimarka.
\s5
\v 6 Gama ana-tsiyaye ni. Lokacin yin kaurata yayi.
\v 7 Na yi tsere na gaskiya; na kuma kammala tseren; na rike bangaskiya.
\v 8 An adana mani rawani na adalci, wanda Ubangiji, alkali mai adalci, zai ba ni a ranan nan. Ba ni kadai ba, amma kuma ga dukkan wadanda suke kaunar zuwansa.
\s5
\v 9 Ka yi iyakacin kokarinka ka zo wurina da sauri.
\v 10 Domin Dimas ya yashe ni. Ya kaunaci wannan duniyar, ya tafi Tassalonika, Kariskis ya tafi Galatiya, Titus kuma ya tafi Dalmatiya.
\s5
\v 11 Luka ne kadai yake tare da ni. Ka nemo Markus ka zo tare da shi domin yana da amfani a gareni a cikin aikin.
\v 12 Na aiki Tikikus zuwa Afisus.
\v 13 Ka kawo mani mayafin da na bari a Taruwasa wurin Karbus, idan za ka zo ka taho da shi, duk da littatafan nan, musanman takardun nan.
\s5
\v 14 Iskandari makerin dalma ya kulla mani makirci ba kadan ba. Ubangiji zai biya shi gwargwadon ayyukansa.
\v 15 Kai ma ka yi hankali da shi, domin yana tsayyaya da maganganunmu sosai.
\v 16 Da farkon kariyar kaina, babu wanda ya goyi bayana. Maimakon haka kowa ya guje ni. Bana so dai a lissafta wannan a kansu.
\s5
\v 17 Amma Ubangiji ya kasance tare da ni, ya kuma karfafa ni, yadda ta wurina, shelar ta sami cika da kyau, domin dukan al'ummai su ji. An kwato ni daga bakin zaki.
\v 18 Allah zai kubutar ni daga dukan ayyukan mugunta, ya kuma cece ni domin mulkinsa na sama. Daukaka ta tabatta a gareshi har abada abadin. Amin.
\s5
\v 19 Ka gayar da Briskilla, da Akila, da gidan Onisifurus.
\v 20 Arastus ya nan zaune a Korinti, amma na bar Turufimus ya na zazzabi a Militus.
\v 21 Ka yi iyakar kokarinka, ka zo kamin hunturu. Yubulus yana gayar da kai, haka ma Budis da Linus da Kalafidiya da dukan 'yan'uwa.
\v 22 Bari Ubangiji ya kasance tare da ruhunka. Bari Alheri ya kasance da kai.