ha_ulb/55-1TI.usfm

223 lines
14 KiB
Plaintext

\id 1TI
\ide UTF-8
\h Wasikar Bulus Manzo Ta Fari Zuwa Ga Timoti
\toc1 Wasikar Bulus Manzo Ta Fari Zuwa Ga Timoti
\toc2 Wasikar Bulus Manzo Ta Fari Zuwa Ga Timoti
\toc3 1ti
\mt Wasikar Bulus Manzo Ta Fari Zuwa Ga Timoti
\s5
\c 1
\p
\v 1 Bulus, manzon Almasihu Yesu bisa ga umarnin Allah Mai cetonmu, da Almasihu Yesu begenmu,
\v 2 zuwa ga Timoti, dana na gaske cikin bangaskiya: Alheri, jinkai da salama daga wurin Allah da Almasihu Yesu Ubangijinmu.
\s5
\v 3 Kamar yadda na nanata maka ka yi, da zan tafi Makidoniya cewa, ka dakata a Afisa domin ka umarci wadansu mutane kada su koyar da wata koyarwa dabam.
\v 4 Kada su bata lokacinsu wajen sauraron tatsunniyoyi da kididdiga marar iyaka. Wannan yana haddasa gardandami, maimakon taimakawa shirin Allah, da ke ta wurin bangaskiya.
\s5
\v 5 Manufar shari'a kuwa kauna ce daga tsabtacciyar zuciya, da tsatstsakan lamiri, da kuma sahihiyar bangaskiya.
\v 6 Wadansu sun kauce daga tafarkin sun juya zuwa ga maganganun banza.
\v 7 Suna so su zama malaman sha'ria, amma basu fahimci abin da suke fada ba ko abin da suka tsaya akai.
\v 8 Amma mun sani shari'a tana da kyau idan an yi amfani da ita bisa ga ka'ida.
\s5
\v 9 Gama mun san wannan, shari'a ba domin mai adalci take ba, amma domin marasa bin doka, mutane masu tawaye, da marasa bin Allah, da masu zunubi, da marasa Allah, da masu sabo. An bada shari'a domin masu kisan iyaye maza da iyaye mata, da masu kisan kai,
\v 10 Domin fasikai da 'yan ludu, domin masu satar mutane su kai su bauta, domin makaryata, da masu shaidar zur, da kuma dukan abin da ke gaba da amintaccen umarni.
\v 11 Wannan umarni bisa ga daukakkiyar bisharar Allah ne mai albarka, wadda aka bani amana.
\s5
\v 12 Ina gode wa Almasihu Yesu Ubangijimu. wanda ya karfafa ni, gama ya karbe ni amintacce, ya sani cikin hidimarsa.
\v 13 Dama can ni mai sabo ne, mai tsanantawa kuma dan ta'adda. Amma duk da haka aka yi mani jinkai domin na yi su cikin jahilci da rashin bangaskiya.
\v 14 Amma alherin Ubangijinmu ya kwararo mani tare da bangaskiya, da kauna da ke cikin Almasihu Yesu.
\s5
\v 15 Wannan bishara amintacciya ce, ta isa kowa ya karba, cewa Almasihu Yesu ya zo cikin duniya domin ceton masu zunubi, a cikinsu kuwa ni ne mafi lalacewa.
\v 16 Saboda haka ne na sami jinkai, domin ta wurina ni na farko, a nuna hakurin Yesu Almasihu. Ya yi wannan domin in zama misali ga wadanda za su bada gaskiya zuwa rai madawwami.
\v 17 Yanzu, ga Sarkin zamanai, marar mutuwa, boyayye, Allah makadaici girma, da daukaka su tabbata a gare shi har abada abadin. Amin.
\s5
\v 18 Ina danka wannan umarni gareka, dana, Timoti. Ina haka ne bisa ga anabcin da aka yi a baya game da kai, domin ka shiga yaki mai kyau.
\v 19 Ka yi wannan domin ka zama da bangaskiya da kyakkyawan lamiri. Wadansu mutane sun ki sauraron wannan suka yi barin bangaskiyarsu.
\v 20 Kamar su Himinayus da Iskandari, wadanda na bada su ga shaidan domin su horu su koyi kin yi sabo.
\s5
\c 2
\p
\v 1 Don haka da farko dai, Ina roko a yi roke-roke da addu'o'i, da yin roko domin jama, a dukka, da ba da godiya, a yi haka domin dukkan mutane,
\v 2 domin sarakuna da dukkan masu mulki, domin mu yi zaman salama da rayuwa a natse cikin Allahntaka da daraja.
\v 3 Wannan yana da kyau da karbuwa a gaban Allah mai cetonmu.
\v 4 Yana so dukkan mutane su sami ceto, su kai ga sanin gaskiya.
\s5
\v 5 Domin Allah daya ne, Matsakanci kuma daya ne, tsakanin Allah da mutum, wannan mutum Almasihu Yesu ne.
\v 6 Ya bada kansa fansa domin kowa, domin shaida a daidaitaccen lokaci.
\v 7 Sabo da wannan dalilin, aka sa ni kaina, na zama mai shelar bishara da manzo. Gaskiya nake fada. Ba karya nake yi ba. Ni mai koyarwa ne na al'ummai cikin gaskiya da kuma imani.
\s5
\v 8 Saboda haka, ina so maza da ke a kowanne wuri suyi addu'a, kuma suna daga hannuwa masu tsarki a sama ba tare da fushi da gardama ba.
\v 9 Kazalika, ina so mata su sa kayan da ya cancanta, da adon da ya dace da kamun kai. Kada su zama masu kitson gashi da zinariya da azurfa da tufafi masu tsada.
\v 10 Ina so su sa tufafin da ya cancanci matan da ke rayuwar Allahntaka ta wurin kyawawan ayyuka.
\s5
\v 11 Mace ta koya cikin natsuwa da saukin kai a cikin komai.
\v 12 Ban ba da izini mace ta koyar ko ta nuna iko a kan namiji ba, amma ta zauna da natsuwa.
\s5
\v 13 Adamu ne aka fara halitta, kafin Hauwa'u.
\v 14 Ba Adamu ne aka yaudara ba, amma macen ce aka yaudara cikin laifi.
\v 15 Duk da haka, zata sami ceto ta wurin haifuwar 'ya'ya, idan suka ci gaba cikin bangaskiya, da kauna da tsarki da sahihiyar zuciya.
\s5
\c 3
\p
\v 1 Wannan magana tabattaciya ce: Idan wani na da marmari ya zama shugaban Ikilisiya, ya na marmarin aiki mai kyau.
\v 2 Don haka, wajibi ne shugaban Ikilisiya ya zama mara abin zargi. Ya zama mai mace daya. Wajibi ne ya zama mai kamewa, mai hankali, mai natsuwa mai karbar baki. Wajibi ne ya iya koyarwa.
\v 3 Kada ya zama mashayin giya, da mai tankiya. A maimakon haka ya zama da natsuwa, mai salama. Ba mai son kudi ba.
\s5
\v 4 Wajibi ne ya iya lura da gidansa da kyau, 'ya'yansa su zama masu yi masa biyayya da dukkan bangirma.
\v 5 Gama idan mutum bai iya sarrafa gidansa ba, ta yaya zai iya lura da Ikkilisiyar Allah?
\s5
\v 6 Bai kamata ya zama sabon tuba ba, domin kada ya kumbura da girman kai, kada ya fadi cikin irin hukunci da aka yi wa Ibilis.
\v 7 Wajibi ne kuma ya kasance mai kyakyawar shaida a cikin wadanda ba masubi ba, domin kada ya fadi cikin kunya da kuma tarkon Ibilis.
\s5
\v 8 Hakanan kuma Dikinoni su kasance da halin mutunci, ba masu magana biyu ba. Bai kamata su zama mashayan giya ko masu hadama ba.
\v 9 Su zama masu rikon bayyananniyar gaskiyar bangaskiya da lamiri mai tsabta.
\v 10 Daidai ne kuma a fara tabbatar da su, daga nan su fara hidima domin basu da abin zargi.
\s5
\v 11 Hakanan ma mata su zama masu mutunci. Bai kamata su zama magulmanta ba, amma masu kamewa da aminci cikin komai.
\v 12 Tilas Dikinoni su zama masu mata daya daya. Su iya kulawa da 'ya'yansu da gidajensu.
\v 13 Gama wadanda suka yi hidima da kyau sun sami tsayawa mai kyau da gabagadi cikin bangaskiyar da ke cikin Almasihu Yesu.
\s5
\v 14 Ina rubuta maka wadannan abubuwa, da sa zuciya zan zo wurin ka ba da jimawa ba.
\v 15 Amma idan na yi jinkiri, ina rubuta maka ne domin ka san yadda za ka gudanar da al'amuranka a cikin gidan Allah, wato Ikklisiyar Allah rayyayiya, ginshiki da kuma mai tallafar gaskiya.
\s5
\v 16 Babu musu an bayyana cewa ibadarmu ta gaskiya da girma take: "Ya bayyana kansa cikin jiki, Ruhu ya baratar da shi, mala'iku suka gan shi, aka yi shelarsa a cikin al'ummai, aka gaskanta shi a duniya, sa'an nan aka dauke shi sama cikin daukaka.
\s5
\c 4
\p
\v 1 To Ruhu ya fada a fili cewa, a zamanin karshe wadansu mutane za su kauce daga bangaskiya, su mai da hankalin su ga ruhohi masu rudi, da koyarwar aljannu,
\v 2 cikin karya da munafunci. Lamirinsu zai yi kanta.
\s5
\v 3 Za su haramta aure da karbar abincin da Allah ya halitta, domin su raba da godiya a cikin wadanda suka bada gaskiya suka kuma san gaskiyar.
\v 4 Gama duk abin da Allah ya halitta yana da kyau. Domin duk abin da muka karba da godiya, bai kamata mu ki shi ba.
\v 5 Gama an tsarkake shi ta wurin maganar Allah da addu'a.
\s5
\v 6 Idan ka tuna wa 'yan'uwa wadannan abubuwa za ka zama bawan kirki na Almasihu. Domin ana gina ka ne ta wurin maganar bangaskiya da kuma kyakkyawar koyarwa wadda ka bi.
\v 7 Amma ka guji labaran almara wadanda tsofaffin mata ke so. Maimakon haka sai ka hori kanka cikin bin Allah.
\v 8 Domin horon jiki ya na da amfani kadan. Amma horon kai cikin bin Allah yana da amfani ga dukkan abubuwa. Gama a cikinsa akwai alkawari domin wannan rayuwar da kuma rayuwa mai zuwa.
\s5
\v 9 Maganan nan amintacciyace ta isa a karbe ta dungum.
\v 10 Dalilin da ya sa kenan mu ke aiki tukuru. Domin muna sa bege ga Allah mai rai, mai ceton dukkan mutane, musamman masu ba da gaskiya.
\s5
\v 11 Ka yi shela ka kuma koyar da wadannan abubuwa.
\v 12 Kada ka yarda kowa ya rena kuruciyarka. Maimakon haka, ka zama abin koyi ga dukkan masubi: a furci, hali, kauna, aminci da kuma tsarki.
\v 13 Har sai na zo, ka himmatu da yin karatu, da wa'azi, da kuma koyarwa.
\s5
\v 14 Kada ka yi sakaci da baiwar da ka ke da ita wadda aka baka ta wurin anabci sa'ad da dattawa suka dibiya maka hannayensu.
\v 15 Ka kula da wadannan abubuwa. Ka himmatu a cikinsu. Domin ci gabanka ya zama sananne a idanun kowa.
\v 16 Ka kula da kanka da kuma koyawarka. Ci gaba a cikinsu. Domin ta yin haka ne za ka ceci kanka da masu sauraronka.
\s5
\c 5
\p
\v 1 Kada ka tsauta wa dattijo. Sai dai ka gargade shi kamar mahaifi. Ka gargadi samari kamar 'yan'uwa.
\v 2 Gargadi dattawa mata kamar iyaye mata, 'yan mata kamar 'yan'uwa mata cikin dukkan tsarki.
\s5
\v 3 Ka girmama gwamraye, gwamraye na gaske.
\v 4 Amma gwamruwar da take da 'ya'ya ko jikoki, bari su fara nuna bangirma cikin danginsu. Bari su sakawa iya-yensu, domin Allah yana jin dadin haka.
\s5
\v 5 Amma gwamruwa ta gaske da ke ita kadai, ta kafa begenta ga Allah. Kullum tana tsananta yin roke-roke da addu'o'i dare da rana.
\v 6 Amma, mace mai son zaman annashuwa ta riga ta mutu, ko da shike tana raye.
\s5
\v 7 Kuma ka yi wa'azin wadannan al'amura donsu zama marasa abin zargi.
\v 8 Amma idan mutum bai iya biyan bukatun 'yan'uwansa ba, musamman iyalin gidansa, ya musunci bangaskiya, kuma gara marar bi da shi.
\s5
\v 9 Bari a lisafta mace gwamruwa idan ba ta kasa shekara sittin ba, matar miji daya.
\v 10 A san ta da kyawawan ayyuka, ko ta kula da 'ya'yanta, ko tana mai karbar baki, ko mai wanke kafafun masubi, ko mai taimakon wadanda ake tsanantawa, mai naciya ga kowanne kyakkyawan aiki.
\s5
\v 11 Amma game da gwamraye masu kuruciya, kada a sa su cikin lissafi. Domin idan suka fada cikin sha'awoyin jiki da ke gaba da Almasihu, sukan so su yi aure.
\v 12 Ta wannan hanya ce sun tara wa kansu tsarguwa saboda sun tada alkawarinsu na fari.
\v 13 Sun saba da halin ragwanci, suna yawo gida gida. Ba zama raggwaye kawai su ka yi ba. Amma sun zama magulmata, masu shishshigi, masu karambani. Suna fadin abin da bai dace ba.
\s5
\v 14 Saboda haka ina so gwamraye masu kuruciya su yi aure, su haifi 'ya'ya, su kula da gida, domin kada a ba magabci zarafin zargin mu ga aikata mugunta.
\v 15 Domin wadansu sun rigaya sun kauce zuwa ga bin shaidan.
\v 16 Idan wata mace mai bada gaskiya tana da gwamraye, bari ta taimakesu, don kada a nawaita wa Ikilisiya, domin Ikilisiya ta iya taimakon gwamraye na gaske.
\s5
\v 17 Dattawa wadanda suke mulki da kyau sun cancanci girmamawa ninki biyu, musamman wadanda suke aiki da kalma da kuma koyarwa.
\v 18 Gama nassi ya ce, "Kada a sa takunkumi a bakin takarkari lokacin da yake sussukar hatsi," kuma "Ma'aikaci ya cancanci a biya shi hakinsa."
\s5
\v 19 Kada ka karbi zargi game da dattijo sai shaidu sun kai biyu ko uku.
\v 20 Ka tsauta wa masu zunubi gaban kowa domin sauran su ji tsoro.
\s5
\v 21 Na umarce ka a gaban Allah, da Almasihu Yesu, da zababbun mala'iku ka kiyaye ka'idodin nan ban da hassada kuma kada ka yi komai da nuna bambanci.
\v 22 Kada ka yi garajen dibiya wa kowa hannuwa. Kada ka yi tarayya cikin zunuban wani. Ka tsare kanka da tsabta.
\s5
\v 23 Kada ka ci gaba da shan ruwa. Amma, maimakon haka ka sha ruwan inabi kadan saboda cikinka da yawan rashin lafiyarka.
\v 24 Zunuban wadansu mutane a bayyane suke, sun yi gaba da su cikin hukunci. Amma wadansu zunubansu na bin baya.
\v 25 Haka kuma, wadansu kyawawan ayyukansu a bayyane suke, amma wadan sun ma ba su boyuwa.
\s5
\c 6
\p
\v 1 Bari duk wadanda ke bayi a karkashin karkiya su ga iyayengijinsu sun cancanci dukan daraja. Su yi haka domin kada a sabawa sunan Allah da koyarwarsa.
\v 2 Bayin da suke da iyayengiji da ke masu ba da gaskiya kada su rena su saboda su 'yan'uwa ne. A maimakon haka, su yi masu hidima da kwazo. Gama iyayengijin da suke cin ribar aikinsu masu bi ne, kaunattatu kuma. Ka koyar ka kuma bayyana wadannan abubuwa.
\s5
\v 3 Idan ya kasance wani na koyar da wani abu dabam bai kuma yarda da amintaciyar koyarwa ba, wato maganar Ubangijinmu Yesu Almasihu. Alal misali ba su amince da koyarwa da ke kai ga Allahntaka ba.
\v 4 Wannan mutum mai girman kai ne, kuma bai san komai ba. A maimakon haka, yana da matukar jayayya da gardama game da kalmomi. Wadannan kalmomi na kawo kishi, da husuma, da zage-zage, da miyagun zace-zace, da
\v 5 yawan rashin jituwa tsakanin mutane masu rubabbun hankula. Sun bijire wa gaskiya. Suna tunani cewa ibada hanya ce ta yin arziki." Ka zame daga wadannan abubuwa.
\s5
\v 6 Yanzu bin Allah tare da dangana babbar riba ce.
\v 7 Gama ba mu kawo komai a duniya ba, ba zamu iya fita cikinta da komai ba.
\v 8 A maimakon haka, mu dangana da abinci da kuma sutura.
\s5
\v 9 To wadanda ke son zama mawadata su kan fada cikin jaraba, cikin tarko. Suna fadawa cikin abubuwan wauta da sha'awoyi masu illa da kowanne abu da ke sa mutane su dulmaya cikin lallacewa da hallaka.
\v 10 Gama son kudi shine tushen kowacce irin mugunta. Wadansu mutane garin neman kudi sun kauce daga bangaskiya, sun kuma jawowa kansu bakin ciki mai yawa.
\s5
\v 11 Amma kai, mutumin Allah, ka guji wadannan abubuwa, ka bi adalci, ibada, aminci, kauna, jimiri, da tawali'u.
\v 12 Ka yi fama, fama mai kyau na bangaskiya. Ka kama rai madawami da aka kira ka gare shi. A kan wannan ne ka ba da shaida a gaban shaidu masu yawa game da abin da ke da kyau.
\s5
\v 13 Ina ba ka wannan umarni a gaban Allah wanda ke rayar da dukan abubuwa, da gaban Almasihu Yesu, wanda ya fadi abin da ke gaskiya ga Bilatus Babunti.
\v 14 Ka bi doka daidai, babu abin zargi har bayanuwar Ubangijinmu Yesu Almasihu.
\s5
\v 15 Allah zai nuna bayyanuwarsa a daidai lokaci- Allah, mai albarka, Makadaicin iko, Sarkin da ke sarauta, Ubangiji mai mulki.
\v 16 Shine kadai marar mutuwa, mai zama cikin hasken da ba ya kusantuwa. Ba wanda ke ganinsa, ko ya iya hango shi. Girma ya tabbata a gare shi da kuma madawwamin iko. Amin.
\s5
\v 17 Ka gaya wa masu dukiya a cikin wannan duniya kada su daga kai, kada su sa bege ga arziki mara dawwama. Maimamakon haka, su sa begensu ga Allah wanda ke ba mu wadatar gaske domin jin dadin mu.
\v 18 Gaya masu su yi nagarta su arzurta a ayyuka nagari, su zama masu bayarwa hannu sake.
\v 19 Ta haka za su ajiye wa kansu harsashi mai kyau kan abin da ke zuwa domin su amshi rayuwa ta kwarai.
\s5
\v 20 Timoti, ka kare abin da aka ba ka. Ka nisanci maganar wauta da gardamomin da ke sabawa juna wanda ake kira ilimi a karyace.
\v 21 Wadansu mutane suna shelar wadannan abubuwa, don haka sun kauce wa bangaskiyar. Bari alheri ya kasance tare da kai.