ha_ulb/54-2TH.usfm

97 lines
5.9 KiB
Plaintext

\id 2TH
\ide UTF-8
\h 2 Tasalonikawa
\toc1 2 Tasalonikawa
\toc2 2 Tasalonikawa
\toc3 2th
\mt 2 Tasalonikawa
\s5
\c 1
\p
\v 1 Bulus da Silbanus da Timoti, zuwa ga ikilisiyar Tasolonika cikin Allah Ubanmu da Ubangiji Yesu Almasihu.
\v 2 Bari alheri ya kasance tare da ku da salama daga Allah Ubanmu da Ubangijinmu Yesu Almasihu.
\s5
\v 3 Lallai ne mu godewa Allah kulluyaumin domin ku, yan'uwa. Domin hakan dai dai ne, saboda bangaskiyarku ta karu sosai, kuma kaunar junanku tana karuwa.
\v 4 Mu da kanmu muna fahariya da ku a ikilisiyoyin Allah. Muna maganar hakurinku da bangaskiyarku a cikin dukkan tsananin da kuke fuskanta. Muna maganar kuncin da kuke jimrewa.
\v 5 Wannan itace alamar shari'ar Allah ta adalci. Sakamakon haka shine za a dauke ku cancantattu na mulkin Allah wanda kuke wahala dominsa.
\s5
\v 6 Adalci ne ga Allah ya mayar da kunci ga wadanda suke kuntata maku,
\v 7 ya kuma baku hutu ku dake shan wuya tare da mu. Zai yi haka ne a bayyanar Ubangiji Yesu daga sama da Mala'ikun ikonsa.
\v 8 A cikin wuta mai huruwa zai dau fansa bisa wadanda basu san Allah ba da wadanda basu karbi bisharar Ubangijinmu Yesu almasihu ba.
\s5
\v 9 Za su sha azaba ta hallaka har abada daga fuskar Ubangiji da kuma daukakar ikonsa.
\v 10 Zai yi wannan lokacin da yazo a wannan rana don jama'arsa su daukaka shi, kuma ya zama abin mamaki ga dukkan wadanda suka bada gaskiya. Domin kun gaskata shaidarmu a gare ku.
\s5
\v 11 Saboda wannan muke addu'a kullum domin ku. Muna addu'a domin Allahnmu ya sa ku cancanci kiran ku. Muna addu'a ya biya ku muradin ku na yin nagarta da dukkan wani aikin bangaskiya da kuma iko.
\v 12 Muna addu'a haka domin sunan Ubangijinmu Yesu ya sami daukaka daga gare ku. Addu'armu itace ya daukaka ku, saboda alherin Allahnmu da Ubangijinmu Yesu Almasihu.
\s5
\c 2
\p
\v 1 Yanzu game da zuwan Ubangijinmu Yesu Almasihu da taruwarmu domin kasancewa tare da shi; muna rokonku yan'uwa,
\v 2 kada kuyi saurin damuwa ko ku gigice saboda wani ruhu ko kuma sako ko kuma wasika da ta yi kamar daga wurin mu, da ke cewa ranar zuwan Ubangiji ta rigaya ta zo.
\s5
\v 3 Kada wani ya yaudare ku ta kowace hanya. Domin wannan rana baza ta zo ba sai fandarewar nan ta zo kuma an bayyana mutumin tawayen nan wato dan hallaka.
\v 4 Wannan shi ne wanda ya ke gaba, yana kuma daukaka kansa fiye da duk abin da ake kira Allah ko kuma ake bautawa. Sakamakon haka yana zama a kursiyin Allah har ma yana cewa shine Allah.
\s5
\v 5 Baku tuna ba lokacin da nake tare daku na gaya maku wadannan abubuwa?
\v 6 Yanzu kun san abinda ke tsaida shi, domin a bayyana shi a lokacin da ya dace.
\v 7 Ko yanzu asirin take shari'a ya na aiki, sai dai a kwai wanda ke tsaida shi yanzu har sai an dauke shi.
\s5
\v 8 Sa'anan za'a bayyana dan tawayen, wanda Ubangiji Yesu zai hallaka shi da numfashin bakinsa. Ubangiji zai mayar da shi ba kome ba ta wurin bayyanuwar zuwansa.
\v 9 Mai tawayen nan kuwa, zai zo ne bisa ga aikin shaidan da dukan iko, alamu, da al'ajiban karya,
\v 10 da kuma dukan yaudara ta rashin adalci. Wadannan abubuwa za su zama ga wadanda suke hallaka, saboda ba su karbi kaunar gaskiya ba domin su sami ceto.
\s5
\v 11 Saboda wannan dalilin Allah ya aiko masu da sabani, saboda su yarda da karya.
\v 12 Sakamakon shine dukkan su za'a yi masu shari'a, wato wadanda ba su yarda da gaskiya ba suna kuma jin dadin rashin adalci.
\s5
\v 13 Amma muna masu godiya kulluyaumin ga Allah domin ku, yan'uwa wadanda Ubangiji yake kauna. Ubangiji ya zabe ku a matsayin yayan fari don ceto cikin tsarkakewar Ruhu da gaskatawa da gaskiya.
\v 14 Wannan shine abinda ya kira ku gare shi ta wurin bishararmu domin ku sami daukakar Ubangijinmu Yesu Almasihu.
\v 15 Saboda haka yan'uwa, ku tsaya da gaske. Ku rike al'adun da aka koya maku, ko ta kalma ko kuma ta wasikarmu.
\s5
\v 16 Yanzu bari Ubangiji Yesu Almasihu da kansa, da Allah Ubanmu wanda ya kaunace mu ya ba mu madawwamiyar ta'aziya da gabagadi mai kyau domin gaba ta wurin alheri,
\v 17 ya ta'azantar da ku ya kuma gina zuciyarku cikin kowane aiki mai kyau da kalma.
\s5
\c 3
\p
\v 1 Yanzu yan'uwa, ku yi mana addu'a saboda maganar Ubangiji tayi sauri ta sami daukaka, kamar yadda take tare da ku.
\v 2 Ku yi addu'a domin mu kubuta daga mutane masu mugunta da keta, gama ba kowa ke da bangaskiya ba.
\v 3 Amma Ubangiji mai aminci ne, shi wanda zai kafa ku ya tsare ku daga mugun.
\s5
\v 4 Muna da gabagadi cikin Ubangiji a kan ku, cewa kuna yi, kuma za ku ci gaba da yin abubuwan da muka umurta.
\v 5 Ubangiji ya bi da zuciyarku zuwa kaunar Allah da kuma jimrewar almasihu.
\s5
\v 6 Yanzu muna umurtar ku, yan'uwa, a cikin sunan Ubangiji Yesu Almasihu, ku guji duk dan'uwa wanda yake zaman banza ba kuma akan al'adun da kuka karba daga wurin mu ba.
\v 7 Saboda ku da kan ku kun sani yana da kyau kuyi koyi da mu. Ba mu yi zama a cikin ku kamar wadanda ba su da tarbiya ba.
\v 8 Ba mu kuma ci abincin kowa ba tare da mun biya ba. Maimakon haka, mun yi aiki dare da rana cikin wahala da kunci domin kada mu dora wa kowa nauyi.
\v 9 Mun yi haka ba don ba mu da iko ba. Maimakon haka, mun yi wannan ne saboda mu zama abin koyi a wurin ku, domin ku yi koyi da mu.
\s5
\v 10 Lokacin da muke tare da ku, mun umurce ku, "Duk wanda ba ya son yin aiki, kada yaci abinci."
\v 11 Saboda mun ji cewa wasun ku sun ki yin aiki. Ba su aiki sai dai shiga shirgin wasu.
\v 12 Irin wadannan, muke umurta da kuma karfafa wa cikin Ubangiji Yesu Almasihu, da su yi aiki da natsuwa, suna cin abincin kan su.
\s5
\v 13 Amma ku yan'uwa, kada ku rabu da yin abinda ke daidai.
\v 14 In wani yaki biyayya da kalmominmu cikin wannan wasika, ku kula da shi kuma kada kuyi ma'amalar komai dashi, saboda ya ji kunya.
\v 15 Kada ku dauke shi a matsayin makiyi, amma ku gargade shi a matsayin dan'uwa.
\s5
\v 16 Bari Ubangijin salama da kansa ya ba ku salama kulluyaumin ta kowace hanya. Ubangiji ya kasance tare da ku duka.
\v 17 Wannan ita ce gaisuwa ta, ni Bulus, da hannuna, wanda shine alama a kowace wasika ta. Haka nake rubutu.
\v 18 Bari alherin Ubangijinmu Yesu Almasihu ya kasance tare da ku duka.