ha_ulb/53-1TH.usfm

171 lines
11 KiB
Plaintext

\id 1TH
\ide UTF-8
\h 1 Tassalunikawa
\toc1 1 Tassalunikawa
\toc2 1 Tassalunikawa
\toc3 1th
\mt 1 Tassalunikawa
\s5
\c 1
\p
\v 1 Bulus, Sila, da Timoti zuwa ga Ikilisiyar Tassalonikawa cikin Allah Uba da Ubangiji Yesu Almasihu. Alheri da Salama su kasance a gare ku.
\s5
\v 2 Kullum muna bada godiya ga Allah domin ku dukka, kamar yadda muke ambaton ku a addu'o'in mu.
\v 3 Muna tunawa da ku ba fasawa a gaban Allahn mu da Ubanmu kuma ayyukanku na bangaskiya, da kauna. Da hakurin bege na abinda ke gaba cikin Ubangijinmu Yesu Almasihu.
\s5
\v 4 'Yan'uwa kaunatattu na Allah, Mun san kiran ku,
\v 5 yadda bishararmu ta zo gare ku ba ta magana kadai ba, amma da iko, ta wurin Ruhu Mai Tsarki, haka kuma tawurin tabbatarwa. Ta haka kuma, kun san irin mutanen da muke acikin ku kuma domin ku.
\s5
\v 6 Kun zama masu koyi da mu da kuma Ubangiji, kamar yadda kuka karbi kalmar cikin tsanani mai yawa da murna tawurin Ruhu Mai Tsaki.
\v 7 Sakamakon haka, kuka zama abin misali ga dukkan wadanda ke Makidoniya da na Akaya wadanda suka bada gaskiya.
\s5
\v 8 Gama daga gare kune maganar Allah ta bazu ko ina, ba kuwa Makidoniya da Akaya kadai ba. A maimako, har ma zuwa ko ina bangaskiyarku cikin Allah ta kai. Don haka, bama bukatar muce maku komai.
\v 9 Domin su da kansu suna bada labarin irin zuwan mu gare ku. Suna fadin yadda kuka juyo ga Allah daga bautar gumaka don ku bautawa Allah mai rai.
\v 10 Suna bayyana cewa kuna jiran bayyanar Dansa daga sama, wanda ya tasar daga matattu. Wannan shine Yesu, wanda ya 'yantad da mu daga fushi mai zuwa.
\s5
\c 2
\p
\v 1 Domin ku da kanku kun sani, 'yan'uwa, cewa zuwan mu gareku, ba a banza yake ba.
\v 2 Kun kuma san yadda aka wulakantar damu, aka kuma kunyatar damu a Filibi, kamar yadda kuka sani. Muna nan kuwa da karfin zuciya cikin Allahnmu domin yi maku bisharar Allah cikin fama da yawa.
\s5
\v 3 Domin kuwa gargadinmu zuwa a gare ku ba gurbatacciya bace, ko cikin rashin tsarki, ba kuma ta yaudara bace.
\v 4 A maimako, kamar yadda Allah ya amince damu, ya kuma damka mana amanar bishararsa, haka kuma muke yin magana. Muna maganar ba domin mu gamshi mutane ba, amma domin mu gamshi Allah. Domin shi ne yake gwada zuciyarmu.
\s5
\v 5 Domin bamu taba yi maku dadin baki ba, ko sau daya, kamar yadda kuka sani, ko kwadayi a asirce, kamar yadda Allah shine shaidar mu.
\v 6 Bamu kuma nemi daukaka daga mutane ko daga gare ku ko kuma wadansu ba. Da mun so da mun mori ikonmu a matsayin manzannin Almasihu.
\s5
\v 7 A maimakon haka, mun kaskantar da kanmu a tsakanin ku kamar yadda uwa take ta'azantar da 'ya'yan ta.
\v 8 Don haka muna da kauna domin ku, ba bisharar Allahnmu kadai muke jin dadin yi maku ba, amma harda bada rayukan mu domin ku. Domin kun zama kaunatattu ne a garemu,
\v 9 Kufa tuna, 'yan'uwa, game da aikinmu da famarmu. Dare da rana muna aiki sosai domin kada mu nawaita wa kowane dayan ku. A lokacin da muke yi maku bisharar Allah.
\s5
\v 10 Ku shaidu ne, haka ma Allah, yadda muka yi rayuwar tsarki da kuma adalci da rashin abin zargi a wajenku wadanda kuka bada gaskiya.
\v 11 Don haka kun kuma sani yadda muka rika yi da kowannenku, kamar uba da 'ya'yansa, yadda muka yi ma ku garadi da kuma karfafa ku, mun kuma shaida.
\v 12 Domin ku yi tafiya a hanyar da ta dace ga Allah, wanda ya kira ku zuwa ga mulkinsa da kuma daukakarsa.
\s5
\v 13 Domin wannan dalili ne yasa muke yi wa Allah godiya a koyaushe. Domin a lokacin da kuka karbi maganar Allah daga wurinmu wadda kuka ji, kun karbeta da gaske ba kamar maganar mutum ba. A maimako, kuka karbeta da gaskiyarta, kamar yadda take, maganar Allah. Wannan kalma kuma ita ce ke aiki a cikin ku wadanda kuka yi bangaskiya.
\s5
\v 14 Domin ku 'yan'uwa, kun zama masu koyi da ikilisiyoyin Allah da ke Yahudiya cikin Almasihu Yesu. Domim kuma kun sha wahala irin tamu daga wurin mutanen kasarku kamar yadda suma suka sha a hannun Yahadawa.
\v 15 Yahudawane suka kashe Ubangiji Yesu da sauran Annabawa, kuma Yahudawane suka koro mu, Basu gamshi Allah ba. A maimako, suna hamayya da dukkan mutane.
\v 16 Sun kuma haramta mana yin magana da Al'ummai domin su sami ceto. Sakamakon haka kuwa kullum suna cika zunubansu. Fushi kuma ya afko kansu daga karshe.
\s5
\v 17 Mu kuma, 'yan'uwa, mun rabu daku na karamin lokaci, a zahiri, ba a zuciya ba, mun kuma yi iyakar kokarinmu da marmarin ganin fuskarku.
\v 18 Domin mun yi maramarin zuwa gareku. Ni, Bulus, ba sau daya ba, amma Shaidan ya hanamu.
\v 19 To menene begenmu a gaba, ko murnarmu ko rawanin alfahari, a gaban Ubangijinmu Yesu a ranar zuwansa? Ko ba ku bane, da kuma sauran jama'a?
\v 20 Don kuwa kune daukakarmu da kuma farin cikinmu.
\s5
\c 3
\p
\v 1 Saboda haka, da bamu iya jimrewa ba, sai mukayi tunanin cewa ya dace mu dakata a Atina tukunna.
\v 2 Sai muka aikaTimoti, dan'uwanmu dakuma bawan Allah a bisharar Almasihu, domin karfafaku ya kuma ta'azantar daku a fannin bangaskiya.
\v 3 Mun yi haka ne saboda kada waninku ya raunana domin wadannan wahaloli. Domin ku da kanku kun sani cewa don haka aka kiraye mu.
\s5
\v 4 Hakika, a lokacin da muke tare daku, mun gaya maku cewa muna daf da shan wahala, haka ya kuma kasance, kamar yadda kuka sani.
\v 5 Domin haka, da ban iya jimrewa ba, sai na aiko domin in san yadda bangaskiyar ku take. Watakila ko magafci a wata hanya ya rinjaye ku, sai ya kasance wahalarmu ta zama a banza.
\s5
\v 6 Amma Timoti da ya dawo daga gareku sai ya kawo mamu labari mai dadi akan bangaskiyarku da kuma kaunarku. Yako gaya mana cewa kuna kyakkyawan tunani a kanmu, kuma kuna marmarin ganinmu yadda muke marmarin ganinku.
\v 7 Sabili da haka, 'yan'uwana, mun sami ta'aziyya tawurinku domin bangaskiyarku, a cikin dukkan bakin cikinmu da shan wuyamu.
\s5
\v 8 Yanzu a raye muke, idan kun tsaya da karfi a cikin Ubangiji.
\v 9 Gama wace irin godiya zamu ba Allah sabili da ku, domin dukan farin cikin da muke dashi a gaban Allah domin ku?
\v 10 Dare da rana muke yi maku addu'a sosai domin muga fuskokinku kuma mu cika abin da kuka rasa cikin bangaskiyarku.
\s5
\v 11 Bari Allah da kuma Ubanmu da kansa, da Ubangijinmu Yesu, ya bida sawayen mu zuwa gareku.
\v 12 Bari Ubangiji yasa ku karu ku kuma ribambamya a kaunar 'yan'uwanku da dukan mutane, kamar yadda muke maku.
\v 13 Bari yayi haka domin ya karfafa zukatanku marassa abin zargi a cikin tsarki a gaban Allah da Ubanmu a lokacin zuwan Ubangijinmu Yesu da dukan tsarkakansa.
\s5
\c 4
\p
\v 1 A karshe, 'yan'uwa, muna karfafa ku kuma muna yi maku gargadi cikin Ubangiji Yesu. Yadda kuka karbi umarni a garemu game da yadda dole za kuyi tafiya kuma ku gamshi Allah, kuma a cikin wannan hanya ku tafi, ku kuma wuce haka.
\v 2 Domin kun san umarnin da muka baku cikin Ubangiji Yesu.
\s5
\v 3 Gama wannan ne nufin Allah: kebewar ku - cewa ku kauce wa zina da fasikanci,
\v 4 Cewa kowannenku ya san yadda zai rike mata tasa cikin tsarki da girmamawa.
\v 5 Kada kayi mata cikin zautuwar sha'awa (kamar al'ummai wadanda basu san Allah ba).
\v 6 Kada wani ya kuskura yaci amanar dan'uwansa akan wannan al'amari. Gama Ubangiji mai ramuwa ne akan dukkan wadannan al'amura, Kamar yadda a baya muka yi maku kashedi kuma muka shaida.
\s5
\v 7 Gama Allah bai kira mu ga rashin tsarki ba, amma ga rayuwar tsarki.
\v 8 Domin haka, duk wanda yaki wannan ba mutane yaki ba, amma Allah, wanda ya bada Ruhunsa Mai Tsarki a gareku.
\s5
\v 9 Game da kaunar 'yan'uwa, baku bukatar wani ya sake rubuta maku, gama ku da kanku Allah ya koyar da ku kaunar 'yan'uwa.
\v 10 Ba shakka, kunayin haka ga dukkan 'yan'uwa wadanda ke cikin dukkan Makidoniya. Amma muna gargadin ku 'yan'uwa, kuyi haka bugu da kari.
\v 11 Kuma muna gargadin ku 'yan'uwa kuyi kokari ku zauna a natse, ku kula da al'amuranku, kuyi aiki da hannuwanku, Yadda muka umarceku a baya.
\v 12 Kuyi haka domin tafiyar ku ta zama dai dai a gaban wadanda basu bada gaskiya ba, kuma ya zama baku cikin bukatar komai.
\s5
\v 13 Bamu so ku zama da rashin fahimta ba, 'yan'uwa, game da wadanda sukayi barci, domin kada kuyi bacin rai kamar sauran wadanda basu da tabbacin abinda ke gaba.
\v 14 Domin idan mun bada gaskiya Yesu ya mutu kuma ya tashi, haka kuma tare da Yesu Allah zai maido da duk wadanda suka yi barci a cikinsa.
\v 15 Gama muna fada maku wannan daga maganar Ubangiji, cewa mu da muke a raye, da aka bari har zuwan Ubangiji, babu shakka ba za mu riga wadanda suka yi barci ba.
\s5
\v 16 Gama Ubangiji da kan sa zai sauko daga sama. Zai zo da muryar babban mala'ika, da karar kahon Allah, sai matattu cikin Almasihu su fara tashi.
\v 17 Sai mu da muke a raye, wadanda aka bari, tare dasu za'a fyauce mu zuwa cikin gizagizai, mu hadu da Ubangiji cikin sararin sama. Haka zamu cigaba da kasancewa da Ubangiji.
\v 18 Domin haka ku ta'azantar da juna da wadannan maganganu.
\s5
\c 5
\p
\v 1 Yanzu fa game da zancen lokatai da zamanai 'yan'uwa, ba ku da bukatar a rubuta maku wani abu.
\v 2 Domin ku da kanku kun sani kwarai cewa ranar zuwan Ubangiji kamar barawo take da dare.
\v 3 Da suna zancen "zaman lafiya da kwanciyar rai," sai hallaka ta zo masu ba zato ba tsammani. Zai zama kamar nakudar haihuwa ce da ke kama mace mai ciki. Ba su kwa da wata hanyar kubuta.
\s5
\v 4 Amma ku, 'yan'uwa, ai ba cikin duhu kuke ba har da wannan rana zata mamaye ku kamar barawo.
\v 5 Domin dukkan ku 'ya'yan haske ne 'ya'yan rana kuwa. Mu ba 'ya'yan dare ba ne ko na duhu,
\v 6 Don haka, kada muyi barci kamar yadda sauran ke yi. Maimakon haka, bari mu kasance muna zaman tsaro kuma muna a fadake.
\v 7 Don masu yin barci da dare suke yin barci, haka kuma masu sha su bugu ma da dare suke yi.
\s5
\v 8 Tunda shike mu 'ya'yan rana ne, bari mu zauna a natse. Bari musa sulke na bangaskiya da kauna, mu kuma sa kwalkwali don ceton mu dake gaba.
\v 9 Domin Allah bai kaddara mu ga fushinsa ba, sai dai ga samun ceto ta wurin Ubangijin mu Yesu Almasihu.
\v 10 Shi ne wanda ya mutu domin mu, don ko da muna raye ko muna mace, mu iya rayuwa tare da shi,
\v 11 Domin haka ku ta'azantar da juna ku kuma inganta juna, kamar yadda kuke yi.
\s5
\v 12 Muna rokon ku, 'yan'uwa, ku bada daraja ga wadanda suke aiki a tsakaninku wadanda kuma suke shugabanci a kan ku cikin Ubangiji, wadanda kuma suke horonku.
\v 13 Muna kuma rokon ku, da ku kula dasu ku kuma kaunacesu sabili da irin ayyukansu. Ku kuma yi zaman lafiya da junan ku.
\v 14 Muna yi maku gargadi 'yan'uwa; ku jawa marassa ji kunne, ku karfafa marassa karfin zuciya, ku taimaki gajiyayyu, kuyi zaman hakuri da kowa.
\s5
\v 15 Ku lura kada wani ya rama mugunta da mugunta, Maimakon haka ma, Ku cigaba da abinda ke mai kyau ga juna da kowa duka.
\v 16 Kuyi farin ciki koyaushe.
\v 17 Kuyi addu'a ba fasawa.
\v 18 A cikin kome kuyi godiya. Domin wannan ne nufin Allah a cikin Yesu Almasihu game daku.
\s5
\v 19 Kada ku hana Ruhun Allah aiki a cikin ku.
\v 20 Kada ku raina anabce anabce.
\v 21 Ku gwada komai. Ku rike abinda ke mai kyau.
\v 22 Ku kaucewa duk wani abinda yayi kama da mugunta.
\s5
\v 23 Bari Allah na salama ya mai da ku cikakun tsarkaka. Bari dukkan ruhun ku, da zuciyar ku, da jikin ku su zama adanannu marassa zargi domin zuwan Ubangijin mu Yesu Almasihu.
\v 24 Wanda ya kira ku mai aminci ne, wanda kuma zai aikata.
\s5
\v 25 Yan'uwa, kuyi addu'a domin mu.
\v 26 Ku gaida dukkan yan'uwa da tsattsarkar sumba.
\v 27 Ina rokon ku saboda Ubangiji ku karanta wasikar nan ga dukkan 'yan'uwa.
\v 28 Bari alherin Ubangijin mu Yesu Almasihu shi kasance tareda ku.