ha_ulb/52-COL.usfm

181 lines
11 KiB
Plaintext

\id COL
\ide UTF-8
\h Kolosiyawa
\toc1 Kolosiyawa
\toc2 Kolosiyawa
\toc3 col
\mt Kolosiyawa
\s5
\c 1
\p
\v 1 Bulus manzon Almasihu Yesu ta wurin nufin Allah da Timoti dan'uwanmu,
\v 2 zuwa ga masu bada gaskiya da amintattun 'yan'uwa cikin Almasihu da suke a Kolosi. Bari alheri da salama su kasance tare da ku daga wurin Allah Ubanmu.
\v 3 Muna godiya ga Uban Ubangijinmu Yesu Kristi, kuma kullum muna addu'a dominku.
\s5
\v 4 Mun ji bangaskiyar ku cikin Almasihu Yesu da kaunar da kuke da ita wa dukan kebabbu ga Allah.
\v 5 Kuna da kaunar nan domin bege na hakika ga abin da aka tanadar maku a sama. Kun riga kun ji game da begen nan na hakika maganar gaskiya da bishara,
\v 6 wanda ta zo maku. Wannan bishara tana ba da yaya tana kuma hayayyafa da kuma girma a cikin dukan duniya. Tana yin haka a cikinku kuma tun ranar da kuka ji ta kun kuma yi koyi game da alherin Allah cikin gaskiya.
\s5
\v 7 Wannan itace bishara kamar yadda kuka koye ta a wurin Abafaras, kaunataccen abokin bautar mu, wanda ke amintacce mai hidimar Almasihu a madadin mu.
\v 8 Abafaras ya bayyana mana kaunarku a Ruhu.
\s5
\v 9 Saboda da wannan kauna, tun daga ranar da muka ji haka, ba mu fasa yi maku addu'a ba. Muna ta roko domin ku cika da sanin nufinsa cikin dukan hikima da fahimta ta ruhaniya.
\v 10 Muna ta addu'a domin ku yi tafiya da ta cancanci Ubangiji a kowace hanya da za ta faranta masa rai. Muna ta addu'a cewa za ku ba da 'ya'ya cikin kowanne aikin nagari kuma za ku yi girma cikin sanin Allah.
\s5
\v 11 Muna addu'a ku karfafa a cikin kowanne iyawa bisa ga ikon daukakarsa zuwa ga matukar jimrewa da hakuri.
\v 12 Muna addu'a za ku yi godiyar farinciki ga Uban, wanda ya sa kuka samu rabo cikin gado na masu bangaskiya cikin haske.
\s5
\v 13 Ya kwato mu daga mulkin duhu ya kuma maishe mu ga mulkin kaunataccen Dansa.
\v 14 Ta wurin Dan ne muka sami fansa, gafarar zunubai.
\s5
\v 15 Dan shine surar Allah mara ganuwa. Shine farkon dukan hallitta.
\v 16 Domin ta wurinsa ne aka halicci dukan abubuwa, wadanda ke sama da wadanda ke duniya, masu ganuwa da marasa ganuwa. Ko kursiyai ko mulkoki ko sarautai ko ikoki, dukan abubuwa shi ya hallice su kuma dominsa.
\v 17 Ya kasance kafin dukan abubuwa, a cikinsa ne kuma komai yake hade.
\s5
\v 18 Kuma shine kan jikin, ikilisiya. Shine farko da kuma dan fari daga cikin matattu, don haka yana da wuri na fari a cikin dukan abubuwa.
\v 19 Domin Allah ya yi farinciki cewa dukan cikarsa ta kasance a cikinsa,
\v 20 kuma ya sulhunta kowanne abu zuwa gare shi ta wurin Dan. Allah ya kawo salama ta wurin jinin giciyensa. Allah ya sulhunta duka zuwa gare shi, ko abubuwan da ke duniya ko abubuwan da ke sama.
\s5
\v 21 Domin a da ku baki ne ga Allah, kuma makiyansa ne cikin zuciya da cikin mugun ayyuka.
\v 22 Amma yanzu, ya sulhunta ku ta wurin mutuwarsa ta jiki. Ya yi haka domin ya mika ku tsarkakaku, marasa aibu da marasa abin zargi a gabansa,
\v 23 idan kuka ci gaba cikin bangaskiya, kafaffu da tsayayyu, marasa kaucewa daga begen ku na hakika na bishara da kuka ji. Wannan itace bishara da aka yi wa kowanne halitaccen taliki a karkashin sama. Wannan itace bishara wadda ni, Bulus, na zama bawa.
\s5
\v 24 Yanzu ina murna da wahala ta domin ku. A jikina cika abin da ya rage cikin wahalar Almasihu domin jikinsa wadda itace ikilisiya.
\v 25 Saboda wannan ikilisiya na zama bawa, bisa ga haki da Allah ya ba ni domin ku, domin cika sakon Allah.
\v 26 Wannan shine asirin gaskiya da yake a boye shekara da shekaru da zamanai. Amma a yanzu an bayyana shi ga wadanda suka gaskanta da shi.
\v 27 A gare su ne Allah ya so ya bayyana yalwar daukakar asirin gaskiyarsa a tsakanin al'ummai. Ya nuna Almasihu ne ke cikin ku, tabbacin daukaka mai zuwa.
\s5
\v 28 Wannan shine wanda muke shella. Muna gargadar da kowanne mutum, muna kuma koyar da kowanne mutum tare da dukan hikima, don mu mika kowanne mutum cikakke cikin Almasihu.
\v 29 Domin wannan nake aiki da himma bisa ga karfinsa da yake aiki a cikina da iko.
\s5
\c 2
\p
\v 1 Ina so ku san yadda na sha faman gaske dominku, domin wadanda ke a Lawudikiya, da kuma wadansu da yawa da a jiki basu taba ganin fuska ta ba.
\v 2 Na yi aiki saboda zuciyar su ta sami karfafawa ta wurin hada su cikin kauna zuwa dukan arziki na tabbaci da fahimtar asirin gaskiya na Allah, wato Almasihu.
\v 3 A cikinsa dukan taskar hikima da sani ke boye.
\s5
\v 4 Na fadi haka domin kada wani ya yaudare ku da jawabi mai jan hankali.
\v 5 Ko da yake ba na tare da ku a jiki, duk da haka ina tare da ku a cikin Ruhu. Ina murnar ganin ku a yanayi mai kyau da kuma karfin bangaskiyar ku cikin Almasihu.
\s5
\v 6 Kamar yadda kuka karbi Almasihu Ubangiji, ku yi tafiya cikinsa.
\v 7 Ku kafu da karfi a cikinsa, ku ginu a kansa, ku kafu cikin bangaskiya kamar yadda aka koya maku, ku yawaita cikin yin godiya.
\s5
\v 8 Ku lura kada wani ya rinjaye ku ta hanyar ilimi da yaudarar wofi bisa ga al'adun mutane, bisa ga bin abubuwan duniya, ba na Almasihu ba.
\v 9 A cikinsa ne dukan Allahntaka ta bayyana ta jiki.
\s5
\v 10 Ku kuwa kun cika a cikinsa. Shine gaban kowanne iko da sarauta.
\v 11 A cikinsa ne aka yi maku kaciya, ba kaciya irin da yan adam suke yi ba, ta cire fatar jiki, amma ta kaciyar Almasihu.
\v 12 An binne ku tare da shi ta wurin baftisma. Kuma a cikinsa ne aka ta da ku ta bangaskiya a cikin ikon Allah, wanda ya tashe shi daga mutattu.
\s5
\v 13 A lokacin da kuke matattu cikin laifofinku, a cikin rashin kaciyar ku ta jiki, ya rayar da ku tare da shi kuma ya yafe maku dukan laifofinku.
\v 14 Ya share rubutattun basussukanku da ka'idodin da suke gaba da mu. Ya cire su duka ya kafa su a kan giciye.
\v 15 Ya cire ikoki da sarautu. A fili ya falasa su ya shugabance su zuwa ga bukin nasara ta wurin giciyensa.
\s5
\v 16 Saboda haka, kada kowa ya shari'anta ku ta wurin ci ko sha, ko kuma sabon wata, ko game da ranakun Assabaci.
\v 17 Wadannan sune inuwar abubuwan da ke zuwa nan gaba, amma ainihin shi ne Almasihu.
\s5
\v 18 Kada kowa wanda ke son kaskanci da sujadar mala'iku ya sharantaku ku rasa sakamakonku. Irin wannan mutum yana shiga cikin abubuwan da ya gani ya zama mai girman kai a tunaninsa na jiki.
\v 19 Ba ya hade da kai. Daga kan ne dukan jiki da gabobi da jijiyoyi ke amfani suna kuma hade tare; yana girma da girman da Allah yake bayarwa.
\s5
\v 20 In kun mutu tare da Almasihu ga ala'muran duniya, don me kuke rayuwa kamar kuna karkashin duniya:
\v 21 "Kada ku rike, ko ku dandana ko ku taba?"
\v 22 Dukan wadannan abubuwa karshen su lalacewa ne in ana amfani da su, bisa ga kaidodi da koyarwar mutane.
\v 23 Wadannan dokoki suna da hikima ta jiki irin ta addini da aka kago na kaskanci da kuma wahalar da jiki. Amma ba su da amfanin komai a kan abin da jiki ke so.
\s5
\c 3
\p
\v 1 Idan dai Allah ya tashe ku tare da Almasihu, ku nemi abubuwan da ke sama, inda Almasihu ke zaune a hannun dama na Allah.
\v 2 Yi tunanin a kan abubuwan da ke sama, ba a kan abubuwan da ke kasa ba.
\v 3 Gama ku kun mutu, ranku kuma yana boye tare da Almasihu cikin Allah.
\v 4 Sa'anda Almasihu ya bayyana, wanda shine ranku, sa'anan ku kuma zaku bayyana tare da shi cikin daukakarsa.
\s5
\v 5 Ku kashe sha'awacce-sha'awaccen da suke a duniya - zina da fasikanci, rashin tsarki, muguwar sha'awa, mummunar buri, da kuma kwadayi, wadda shine bautar gumaka.
\v 6 Saboda wandannan abubuwa ne fushin Allah ke zuwa a kan marasa biyayya.
\v 7 A cikin wadannan abubuwa ne kuka yi rayuwa a da da kuke zauna a cikinsu.
\v 8 Amma yanzu dole ku kawar da wadannan - zafin rai, fushi, mugayen manufofi, zage-zage, da kazamar magana daga bakinku.
\s5
\v 9 Kada ku yi wa juna karya, domin kun tube tsohon mutumin da ayyukansa,
\v 10 kun kuma yafa sabon mutum, wanda ake sabontawa cikin sani bisa ga surar wannan da ya hallice shi.
\v 11 A nan ne inda babu Baheline da Bayahude, mai kaciya da marar kaciya, bare, baubawa, ko Basikitiye, bawa ko yantacce, amma Almasihu shine duka, yana kuma cikin duka.
\s5
\v 12 A matsayin ku na zababbun Allah, masu tsarki da kaunatattu sai ku yafa jinkai, ayyukan kirki, saukin kai, kamewa da hakuri.
\v 13 Yi hakuri da juna. Ku yi wa juna alheri. Idan wani na da damuwa da wani, ku gafarta kamar yadda Ubangiji ya gafarta maku.
\v 14 Fiye da wadanan abubuwa duka, ku kasance da kauna, wanda itace cikakkiyar kammalla.
\s5
\v 15 Bari salamar Almasihu ta mallaki zukatanku. Sabili da wannan salama ce aka kiraye ku cikin jiki daya. Ku yi godiya.
\v 16 Ku bar maganar Almasihu ta zauna a cikinku a yalwace. Da dukan hikima, ku koyar, ku kuma gargadi juna da zabura, wakoki, da wakokin yabo na ruhaniya. Kuna rairawa tare da godiya cikin zukatanku ga Allah.
\v 17 Kuma duk abin da zaku yi cikin magana ko aiki ku yi duka cikin sunan Ubangiji Yesu. Kuna yin godiya ga Allah Uba ta wurinsa.
\s5
\v 18 Mata, ku yi biyayya ga mazajenku, yadda yakamata a cikin Ubangiji.
\v 19 Mazaje, ku kaunaci matayenku, kada ku muzguna masu.
\v 20 Yaya, ku yi wa iyayen ku biyayya cikin dukan komai, domin wannan yana faranta wa Ubangiji rai.
\v 21 Ku Ubanni, kada ku cakuni 'ya'yanku domin kada su karaya.
\s5
\v 22 Bayi, ku yi wa iyayengijinku na jiki biyayya cikin kowane abu, ba tare da bautan ganin ido ba don faranta wa mutane rai, amma da sahihiyar zuciya. Ji tsoron Ubangiji.
\v 23 Duk abin da kuke yi, ku yi aiki daga zuci domin Ubangiji ba domin mutane ba.
\v 24 Kun san cewa, zaku karbi sakamako na gado daga wurin Ubangiji. Domin Ubangiji Almasihu kuke bauta wa.
\v 25 Domin kowa ya yi rashin adalci zai karbi sakamakon rashin adalcin da ya yi, kuma babu son kai.
\s5
\c 4
\p
\v 1 Ku iyayengiji, ku ba bayinku abin ke daidai ya kuma dace garesu. Kun sani cewa ku ma, kuna da Ubangiji a sama.
\s5
\v 2 Ku cigaba da himmantuwa ga yin addu'a. Ku zauna a fadake cikin addu'a da godiya.
\v 3 Ku yi addu'a tare domin mu kuma, domin Allah ya bude kofa domin kalmar, a fadi asirin gaskiyar Almasihu. Don wannan ne nake cikin sarka.
\v 4 Ku yi addu'a domin in iya fadinsa daidai, yadda yakamata in fada.
\s5
\v 5 Ku yi tafiya da hikima game da wadanda suke a waje, ku yi amfani da lokaci.
\v 6 Bari maganarku ko yaushe ta zama ta alheri. Bari ta zama da dadin ji domin ku san yadda za ku amsa wa kowanne mutum.
\s5
\v 7 Game da abubuwan da nake ciki, Tikikus zai sanar maku da su. Shi kaunataccen dan'uwa, amintaccen bawa, shi abokin barantaka na ne a cikin Ubangiji.
\v 8 Na aike shi wurinku don wannan, domin ku iya sanin halin da muke ciki, don kuma ya karfafa zukatanku.
\v 9 Na aike shi tare da Onisimus, amintacce da kuma kaunataccen dan'uwa, wanda daya ne daga cikin ku. Za su gaya maku duk abin da ya faru anan.
\s5
\v 10 Aristarkus, abokin sarka na, yana gaishe ku da Markus, dan'uwan Barnaba (wanda a kansa ne kuka sami umarni; in yazo, ku karbe shi),
\v 11 da kuma Yesu wanda ake kira Yustus. Wadannan ne kadai daga cikin masu kaciya abokan aiki na domin mulkin Allah. Sun zama ta'aziya a gare ni.
\s5
\v 12 Abafaras na gaishe ku. Shi daya daga cikinku ne kuma bawan Almasihu Yesu ne. Kullum yana maku addu'a da himma, don ku tsaya cikakku da hakikancewa a cikin nufin Allah.
\v 13 Gama ina shaidarsa a kan ya yi aiki da himma domin ku, domin wadanda ke Lawudikiya, da na Hirafolis.
\v 14 Luka kaunataccen likita da Dimas suna gaishe ku.
\s5
\v 15 Ku gai da 'yan'uwa dake a Lawudikiya, da Nimfa da ikilisiyar da ke cikin gidanta.
\v 16 Lokacin da aka karanta wannan wasika a tsakanin ku, sai a karanta ta kuma a cikin ikilisiyar Lawudikiya, ku kuma tabbata kun karanta wasika daga Lawudikiya.
\v 17 Ku gaya wa Arkibas, "Mai da hankali ga hidimar da ka karba cikin Ubangiji, don ka cika shi."
\s5
\v 18 Wannan gaisuwa da hannu na ne - Bulus. Ku tuna da sarka na. Alheri ya tabbata a gare ku.