ha_ulb/51-PHP.usfm

194 lines
13 KiB
Plaintext

\id PHP
\ide UTF-8
\h Filibiyawa
\toc1 Filibiyawa
\toc2 Filibiyawa
\toc3 php
\mt Filibiyawa
\s5
\c 1
\p
\v 1 Bulus da Timoti bayin Almasihu Yesu, zuwa ga dukan wadan da aka kebe cikin Almasihu Yesu da ke a Filibi, tare da masu kula da ikilisiya da dikinoni.
\v 2 Bari alheri ya kasance tare da ku da salama daga Allah Ubanmu da Ubagijinmu Yesu Almasihu.
\s5
\v 3 Ina godiya ga Allahna duk lokacin da na tuna da ku.
\v 4 Ko yaushe cikin addu'a ta dominku duka, da farin ciki na ke addu'a.
\v 5 Ina godiya domin tarayyar ku a cikin bishara tun daga rana ta fari har ya zuwa yanzu.
\v 6 Na tabbata game da wannan abu, shi wanda ya fara aiki mai kyau a cikinku zai ci gaba da shi har ya kai ga kammala zuwa ranar Yesu Almasihu.
\s5
\v 7 Daidai ne in ji haka game da dukanku domin kuna zuciya ta. Dukanku abokan tarayya ta ne cikin alherin Allah wajen dauri na da kuma kariyar bishara, da tabbatar da bishara.
\v 8 Domin Allah mashaidi na ne, a kan yadda ina da marmarin ku duka cikin zurfin kaunar Almasihu Yesu.
\s5
\v 9 Ina yin wannan addu'a: kaunar ku ta habaka gaba gaba a cikin sani da dukan fahimta.
\v 10 Ina addu'a a kan haka domin ku gwada ku zabi mafifitan abubuwa. Ina addu'a domin ku zama sahihai marasa abin zargi a ranar Almasihu.
\v 11 Wannan kuma domin a cika ku da 'ya'yan adalci da ake samu ta wurin Yesu Almasihu, zuwa ga daukaka da yabon Allah.
\s5
\v 12 Yanzu ina so ku sani, 'yan'uwa, cewa al'amuran da suka faru da ni sun zama dalilan cin gaban bishara kwarai da gaske.
\v 13 Sakamakon haka, sarkokina cikin Almasihu sun zama sanannu ga dukan sojojin fada da kuma sauran jama'a,
\v 14 har galibin 'yan'uwa cikin Ubangiji suka karfafa kwarai sabili da sarkokina, suka fito a fili suka yi shelar maganar Allah gabagadi.
\s5
\v 15 Lalle wadansu suna shelar Almasihu cikin kishi da husuma, wadansu kuwa domin kyakyawar manufa.
\v 16 Masu shelar Almasihu domin kauna sun sani cewa an ajiye ni nan domin in kare bishara.
\v 17 Amma wadansu kuwa suna shelar Almasihu saboda sonkai da rashin gaskiya. A zaton su suna wahalar da ni cikin sarkokina.
\s5
\v 18 Sai kuma me? Ta kowace hanya, ko da gangan ko da gaske, shelar Almasihu ake yi, ina kuma murna da wannan! I, zan yi murna.
\v 19 Domin na sani wannan zai kai ga sanadiyar kubuta ta. Wannan zai faru sabili da addu'ar ku, da kuma taimakon Ruhun Yesu Almasihu.
\s5
\v 20 Bisa ga abin da hakikance nake tsammani da tabbaci cewa ba zan kunyata ba. Maimakon haka, da dukan karfin hali kamar kullum, da yanzu kuma, ina da burin kawo daukaka ga Almasihu a cikin jikina. Ina da begen Almasihu ya sami daukaka a cikin jikina ko cikin rayuwa ko cikin mutuwa.
\v 21 Domin ni a gare ni rai Almasihu ne, mutuwa kuwa riba ce.
\s5
\v 22 Amma idan ya zamanto rayuwata cikin jiki za ta kawo amfanin hidima to, ban san wanda zan zaba ba.
\v 23 Amma dukansu biyu suna jan hankali na. Ina da burin in bar nan in kasance tare da Almasihu, wannan ya fiye mani kwarai!
\v 24 Duk da haka rayuwata cikin jiki wajibi ne sabili da ku.
\s5
\v 25 Tunda shike ina da tabbas a kan wannan, na kuma sani zan rayu, in cigaba da kasancewa da ku duka domin cigaban ku, da farincikin ku, cikin bangaskiya.
\v 26 Sakamakon haka, takamar ku cikin Almasihu Yesu za ta bunkasa sabili da dawowa ta a gare ku.
\v 27 Ku tafiyar da al'amuran ku kamar yadda ya cancanci bisharar Almasihu, ku yi haka domin ko na zo in duba ku, ko bana nan inji yadda kuke tsaye daram cikin ruhu guda. Ina fatan in ji cewa da nufi daya kuke fama tare saboda bangaskiyar nan ta bishara.
\s5
\v 28 Kada ku tsorata da kome da magabtanku za su yi. Alama ce a gare su ta hallakar su. Amma ku kuwa alama ce ta ceton ku, wannan kuwa daga Allah ne.
\v 29 Gama an yi maku alheri, sabo da Almasihu, ba gaskantawa da Almasihu kawai ba, amma har ma shan wuya dominsa.
\v 30 Kuna da shan wuya irin tawa wanda kuka gani, wanda kun ji nake sha har yanzu.
\s5
\c 2
\p
\v 1 Idan akwai wani abin karfafawa cikin Almasihu. Idan da wata ta'aziyya daga kaunarsa. Idan akwai zumunta a Ruhu. Idan da tatausan jinkai da tausayi.
\v 2 Ku cika farin cikina don ku zama da tunani irin haka, kuna da kauna daya, kuna tarayya cikin Ruhu daya, ku kasance da manufa iri daya.
\s5
\v 3 Kada ku yi komai cikin sonkai ko girman kai. A maimakon haka cikin zuciya mai tawali'u kowa na duban wadansu fiye da kansa.
\v 4 Kada kowa ya dubi bukatun sa, amma yana lura da bukatun wadansu.
\s5
\v 5 Ku yi tunani cikin hanya wadda ke cikin Almasihu Yesu.
\v 6 Wanda ya yi zama cikin siffar Allah, bai mai da daidaitarsa da Allah wani abin da zai rike ba.
\v 7 Maimakon haka, ya wofintar da kansa. Ya dauki siffar bawa. Ya bayyana cikin kamannin mutane. An same shi a bayyane kamar mutum.
\v 8 Ya kaskantar da kansa, ya yi biyayya har ga mutuwa, mutuwa ta gicciye.
\s5
\v 9 Saboda haka Allah ya ba shi mafificiyar daukaka. Ya ba shi suna wanda yafi kowanne suna.
\v 10 Domin a cikin sunan Yesu kowace gwiwa za ta durkusa, gwiwoyin wadanda ke cikin sama da kuma duniya da kuma karkashin duniya.
\v 11 Kuma kowanne harshe zai furta cewa Yesu Almasihu Ubangiji ne, zuwa daukakar Allah Uba.
\s5
\v 12 Domin wannan kaunatattuna, kamar yadda kullum kuke biyayya ba sai ina nan kadai ba. Balle yanzu da bananan, ku yi aikin cetonku da tsoro da far gaba.
\v 13 Gama Allah ne yake aiki a cikinku ku yi nufi duka da aikata abin da zai gamshe shi.
\s5
\v 14 Ku yi kowanne abu ba tare da gunaguni da gardama ba.
\v 15 Domin ku zama marasa abin zargi kuma masu gaskiya, 'ya'yan Allah marasa aibi. Ku yi haka domin ku haskaka kamar haske a cikin wannan duniya, a tsakiyar karkatacciyar da gurbatacciyar tsara.
\v 16 Ku rike kalmar rai da karfi domin in sami dalilin daukaka Almasihu a ranarsa. Sa'annan zan san cewa ban yi tseren banza ba, ban kuma yi wahalar banza ba.
\s5
\v 17 Ko da ana tsiyaye ni kamar sadaka a kan hadaya da kuma hidimar bangaskiyarku, na yi farin ciki, kuma na yi farin ciki tare da ku duka.
\v 18 Kamar haka kuma sai ku yi farin ciki, ku yi farin ciki tare da ni.
\s5
\v 19 Amma na yi niyya in aiko da Timoti wurin ku ba da dadewa ba, domin ni ma in sami karfafuwa idan na san al'amuran ku.
\v 20 Gama bani da wani wanda halinmu yayi daidai da nasa, wanda yake juyayin ku da gaskiya.
\v 21 Domin duka ribar kansu suke nema bata Yesu Almasihu ba.
\s5
\v 22 Amma kun san darajar sa, kamar yadda da ke hidimar mahaifisa, haka ya bauta mani cikin bishara.
\v 23 Shi nake sa zuciyar in aiko maku ba da dadewa ba idan naga yadda al'amura nake gudana.
\v 24 Amma ina da gabagadi cikin Ubangiji cewa ni da kaina zan zo ba da dadewa ba.
\s5
\v 25 Amma ina tunanin yakamata in sake aiko maku da Abafaroditus, shi dan'uwana ne, abokin aiki, da abokin yaki, manzon ku da kuma bawa domin bukatu na.
\v 26 Da shike yana marmarin ku duka, ya damu kwarai da shike kun ji yayi rashin lafiya.
\v 27 Da gaske yayi rashin lafiya har ya kusan mutuwa. Amma Allah ya ji tausayin sa, ba shi kadai ba, amma har da ni, domin kada in yi bakin ciki kan bakin ciki.
\s5
\v 28 Domin haka na yi niyyar aiko shi, saboda idan kun sake ganinsa za ku yi farin ciki ni kuma in kubuta daga juyayi.
\v 29 Ku karbi Abafaroditus da dukan murna cikin Ubangiji. Ku ga darajar mutane irin sa.
\v 30 Domin saboda aikin Almasihu ne ya kusan mutuwa. Ya sadakar da ransa domin ya bauta mani domin ya cika hidimar da ya kamata ku yi mani.
\s5
\c 3
\p
\v 1 A karshe, 'yan'uwana, ku yi farin ciki cikin Ubangiji. In sake rubuta maku wadannan abubuwa ba wani abu mai nauyi ba ne a gare ni. Wadannan abubuwa zasu tsare ku.
\v 2 Ku yi hankali da karnuka. Ku yi hankali da miyagun ma'aikata. Ku yi hankali da masu yanke-yanke.
\v 3 Gama mune kaciyar. Don mune muke sujada ta wurin Ruhun Allah. Mune masu fahariya chikin Almasihu Yesu, kuma ba mu da gabagadi cikin jiki.
\s5
\v 4 Ko da shike, ni kaina ina gabagadi ga jiki. Idan wani zai iya tunanin gabagadi ga jiki, ni na fi shi.
\v 5 An yi mani kaciya a rana ta takwas, daga mutanen Israila, na kabilar Biliyaminu, Bayahuden Yahudawa; ga zancen shari'a Bafarisiye nake.
\s5
\v 6 Wajen himma na tsanantawa ikilisiya. Ga zancen adalci cikin sharia, na zama mara abin zargi.
\v 7 Amma duk wadannan abubuwan da suka zama riba a gare ni, na dauke su asara ne saboda Almasihu.
\s5
\v 8 I, lallai ina lisafta dukan wadannan abubuwa asara saboda mafificin sanin Almasihu Yesu Ubangijina. Saboda shine na yi asarar dukan abubuwa. Na maishe su marasa amfani domin in ribato Almasihu,
\v 9 a iske ni cikinsa. Ba ni da wani adalcin kaina ta wurin shari'a. Maimakon haka, ina da adalci ta wurin bangaskiya cikin Almasihu, adalcin dake daga wurin Allah ta wurin Bangaskiya.
\v 10 Yanzu ina so in san shi da ikon tashinsa, da tarayya cikin shan wuyarsa. In kuma zama kamarsa wajen mutuwarsa,
\v 11 domin ta ko kaka in kai ga tashi daga cikin matattu.
\s5
\v 12 Ba wai na rigaya na sami wadannan abubuwa bane, ko kuma na riga na zama cikakke. Amma ina nace bi domin in cafki wannan da Almasihu Yesu ya cafko ni dominsa.
\v 13 'Yan'uwa, ban dauka cewa na riga na cafka ba tukuna. Amma akwai abu daya da nake yi: ina mantawa da abin da ke baya, ina kutsawa zuwa ga abin da ke gaba.
\v 14 Ina nacewa zuwa ga manufar nan in kai ga samun ladar nasara na madaukakin kiran Allah cikin Almasihu Yesu.
\s5
\v 15 Dukan mu wadanda muke kammalallu, sai mu yi tunani ta wannan hanyar, idan kuwa kun yi tunanin wani abu daban, to Allah zai bayyana maku wannan kuma.
\v 16 Sai dai, in da muka rigaya muka kai, bari mu rike shi haka.
\s5
\v 17 Ku zama masu koyi da ni, 'yan'uwa. Ku duba da kyau wadannan da suke tafiya yadda muka zama abin koyi a gare ku.
\v 18 Mutane da dama suna tafiya -sune wadanda na ba ku labarin su, yanzu kuma ina fada maku har da hawaye - kamar makiyan gicciyen Almasihu ne.
\v 19 Karshen su hallaka ne. Domin allahn su ciki ne, fahariyar su kuma tana cikin kunyar su. Tunanin su na kan al'amuran duniya.
\s5
\v 20 Amma mu 'yangarincin mu a sama yake, daga inda muke sauraron mai ceto, Ubangiji Yesu Almasihu.
\v 21 Za ya sake jikinmu na kaskanci ya siffanta shi kamar jikin darajarsa, siffantacce ta karfin ikonsa inda ya sarayar da dukan abubuwa a gare shi.
\s5
\c 4
\p
\v 1 Saboda haka, kaunatattu 'yan'uwana da nake marmari, farin ciki na da rawani na, a wannan hanya ku tsaya daram cikin Ubangiji, kaunatattun abokai.
\v 2 Ina rokon Afodiya, ina rokon Sintiki, ku zama da ra'ayi daya cikin Ubangiji.
\v 3 Babu shakka, ina sake rokon ku, abokan tarayyar takunkumina na gaske: ku taimaka wa matayen nan. Domin mun yi wahala tare a cikin yada bishara tare da Kilimas da sauran abokan aiki na, wanda sunayensu na rubuce cikin littafin rai.
\s5
\v 4 Yi farin ciki cikin Ubangiji kullayomi. Ina sake cewa, yi farin ciki.
\v 5 Bari dukan mutane su ga jimirin ku. Ubangiji ya yi kusa.
\v 6 Kada ku damu da kowanne abu, maimakon haka, cikin komai tare da addu'a, da rokeroke, da godiya, bari rokeroken ku su sanu ga Allah.
\v 7 Salamar Allah, da ta zarce dukan ganewa za ta tsare zuciyarku da tunaninku cikin Almasihu Yesu.
\s5
\v 8 A karshe, 'yan'uwa, duk abin da ke mai gaskiya, duk abin da ya isa ban girma, duk abin da ke mai adalci, duk abin da ke mai tsabta, duk abin da ke karbabbe, duk abin da ke kawo kauna, duk abin da ke da kyakkyawan ambato, idan akwai yabo, yi tunani a kan wadannan abubuwan.
\v 9 Wadannan abubuwan da kuka koya kuka karba kuka ji kuka gani a rayuwa ta, ku aikata wadannan abubuwan. Allah mai salama zai kasance tare da ku.
\s5
\v 10 Na yi farin ciki sosai cikin Ubangiji domin yanzu a karshe kun sabunta kulawar ku game da ni. Kun kula da ni da gaske kwanakin baya, amma ba ku samu zarafin taimako ba.
\v 11 Ba don bukata ta bane nake fada wannan. Domin na koyi dangana a kowanne irin yanayi.
\v 12 Na san yadda zan zauna cikin bukata, na kuma san yadda zan samu a yalwace. A kowace hanya cikin kowanne abu na koyi asirin yadda zan ci da yawa da yadda zan zauna da yunwa, yadda zan zama a yalwace kuma in zama cikin bukata.
\v 13 Zan iya yin komai ta wurinsa shi da yake karfafa ni.
\s5
\v 14 Duk da haka, kun yi zumunta da ni cikin kunci na.
\v 15 Kun kuma sani, ku Filibiyawa, cewa da farkon bishara, lokacin da na bar Makidoniya, babu ikilisiya da ta tallafe ni cikin batun bayarwa da karba sai ku kadai.
\v 16 Ko lokacin da nake Tassalonika, kun aika da gudumawar biyan bukatu na fiye da sau daya.
\v 17 Ba domin ina neman kyauta ba ne. A maimakon haka, ina neman amfani da zai kawo karuwa cikin ajiyar ku.
\s5
\v 18 Na karbi dukan abubuwan, ina da shi a yalwace. An kosar da ni. Na karba ta hanun Abafroditus abubuwa daga wurinku. Shesheki na dadin kamshi mai dandanno, karbabbiyar hadaya mai gamsarwa ga Allah.
\v 19 Allah na zai cika dukan bukatunku bisa ga yalwarsa da ke cikin daukaka cikin Almasihu Yesu.
\v 20 Yanzu bari daukaka ta tabbata ga Allah da Ubanmu har abada abadin. Amin.
\s5
\v 21 Gai da kowanne mai bi cikin Almasihu Yesu. Dukan 'yan'uwa da ke tare da ni suna gaisuwa.
\v 22 Dukan masu bi a nan suna gaisuwa, musamman wadanda suke gidan Kaisar.
\v 23 Bari alherin Ubangijin Yesu Almasihu ya zauna tare da ruhunku. Amin