ha_ulb/49-GAL.usfm

289 lines
18 KiB
Plaintext

\id GAL
\ide UTF-8
\h Galatiyawa
\toc1 Galatiyawa
\toc2 Galatiyawa
\toc3 gal
\mt Galatiyawa
\s5
\c 1
\p
\v 1 Wannan Bulus manzo ne. Manzancina kuwa, bai zo daga mutane ba ko mutum, amma ta wurin Yesu Almasihu da Allah Uba wanda da ya tashe shi daga matattu.
\v 2 Ni da dukan 'yan'uwa da nake tare da su a nan, ina rubuto maku ku iklisiyoyi da ke a Galatiya.
\s5
\v 3 Alheri zuwa gare ku da salama daga Allah Ubanmu da kuma Ubangjinmu Yesu Almasihu,
\v 4 wanda ya ba da kansa domin zunubanmu saboda ya kubutar da mu daga wannan mugun zamani, bisa ga nufin Allah da Ubanmu.
\v 5 Daukaka ta tabbata a gare shi har abada abadin.
\s5
\v 6 Na yi mamaki kwarai yadda kuka juya da sauri zuwa wata bishara daban. Na yi mamakin cewa kuna juyawa daga shi wanda ya kira ku ta wurin alherin Almasihu.
\v 7 Ba wata bishara, amma akwai wadansu mutane da suke kawo maku rudani kuma suna so su gurbata bisharar Almasihu.
\s5
\v 8 Amma, ko da mu ne ko mala'ika daga sama ya yi maku shelar wata bishara ta daban da wadda muka yi shelar ta, la'ananne ne.
\v 9 Kamar yadda muka fadi maku a da, yanzu kuma ina sake fada, "Idan wani ya yi maku shelar wata bishara ta daban da wadda kuka karba, la'ananne ne."
\v 10 To yanzu ina neman shaidar mutane ne ko Allah? Ina neman in gamshi mutane ne? Idan har yanzu ina kokarin in gamshi mutane ne, ni ba bawan Almasihu ba ne.
\s5
\v 11 Ina son ku sani fa 'yan'uwa, cewa bisharar da nake shelar ta ba daga mutane take ba.
\v 12 Ban karbe ta daga mutum ba, ba ma wanda ya koyar mani A maimakon haka, ta wurin wahayin Yesu Almasihu ne zuwa gare ni.
\s5
\v 13 Kun riga kun ji game da rayuwa ta a da cikin Yahudanci, yadda da nake da kwazon tsananta wa iklisiyar Allah fiye da misali kuma ina lalatar da ita.
\v 14 Ina gaba-gaba cikin Yahudanci fiye da yawancin tsararrakina. A kwazo kuwa fiye da kima game da al'adun ubannina.
\s5
\v 15 Amma ya gamshi Allah ya zabe ni daga cikin mahaifiyata. Ya kira ni ta wurin alherinsa.
\v 16 Ya bayyana dansa a gareni, saboda in yi shelar sa cikin al'ummai. Nan da nan, ban nemi shawarar nama da jini ba
\v 17 kuma ban tafi Urushalima ba wurin wadanda suka zama manzanni kafin ni. Maimakon haka sai na tafi Arebiya, daga nan sai na dawo Dimashku.
\s5
\v 18 Bayan shekara uku na je Urushalima don in san Kefas, na zauna da shi na kwana goma sha biyar.
\v 19 Amma ban ga ko daya daga cikin manzannin ba sai Yakubu kadai, dan'uwan Ubangiji.
\v 20 Duba, a gaban Allah, ba karya nake yi ba cikin abin da na rubuta maku.
\s5
\v 21 Daga nan sai na je lardin Suriya da Kilikiya.
\v 22 Har a lokacin babu wanda ya san ni a fuska a iklisiyoyin Yahudiya da suke cikin Almasihu,
\v 23 amma sai labari kawai suke ji, "Wanda a da yake tsananta mana yanzu yana shelar bangaskiyar da a da yake rusarwa."
\v 24 Suna ta daukaka Allah saboda ni.
\s5
\c 2
\p
\v 1 Daga nan, bayan shekara goma sha hudu na koma Urushalima tare da Barnaba. Na kuma dauki Titus tare da ni.
\v 2 Na koma ne domin Allah ya nuna mani in koma. Sai na gabatar masu shelar bisharan da nake yi a cikin al'ummai. (Amma a kebe na yi magana da wadanda aka dauka muhimman shugabanni). Na yi haka ne domin in tabbatar da cewa ba gudun banza nake yi ba, ko kuma na yi gudun banza.
\s5
\v 3 Amma ko Titus wanda yake tare da ni, Baheline, ba wanda ya tilasta masa ya yi kaciya.
\v 4 Wannan maganar ta taso ne daga 'yan'uwan karya da suka zo cikinmu a boye su ga 'yancin mu a cikin Yesu Almsihu. Sun yi marmarin su maishe mu bayi ga doka.
\v 5 Ba mu mika kanmu biyayya gare su ba ko da na sa'a daya, domin gaskiyar bishara ta kasance babu canzawa domin ku.
\s5
\v 6 Amma su wadanda a ke ganin su da muhimmanci ba su taimaka mani da komai ba. Ko su wanene su bai dame ni ba. Allah ba ya karbar wanda mutane suka fi so.
\v 7 Maimakon haka, suka ga an danka mani shelar bishara ga wadanda ba su da kaciya. Kamar yadda aka ba Bitrus shelar bishara ga masu kaciya.
\v 8 Gama Allah wanda yake yin aiki a cikin Bitrus domin manzanci zuwa ga masu kaciya, haka kuma yake aiki ciki na zuwa ga al'ummai.
\s5
\v 9 Da Yakubu, Kefas, da Yahaya, wadanda a ke gani masu gina ikilisiya, suka fahimci alherin da aka ba ni, suka bamu hannun dama na zumunci ni da Barnaba, Sun yi haka ne kawai domin mu mu tafi zuwa wurin al'ummai, su kuma su je wurin masu kaciya.
\v 10 Suna kuma so mu tuna da matalauta. Ni ma ina da aniyar yin haka.
\s5
\v 11 Da Kefas ya kai Antakiya, na yi tsayayya da shi a gabansa domin shine ke da kuskure.
\v 12 Da ma Kefas yana cin abinci tare da al'ummai kafin zuwan wasu mutane daga wurin Yakubu. Amma da wadannan mutane suka iso, sai ya dena kuma ya ware kansa daga al'umman. Yana jin tsoron wadannan mutanen da ke bukatar kaciya.
\s5
\v 13 Hakannan ma sauran Yahudawa da suke tare da shi sun bi munafurcin sa. A sakamakon haka Barnaba ma ya bi munafurcin su.
\v 14 Da na ga basu bin gaskiyar da take cikin bisharar, na gaya wa Kefas a gaban su duka, "Idan kai Bayahude ne kana rayuwar ka ta al'ummai a maimakon rayuwar Yahudawa, to ta yaya za ka tilasta wa al'ummai su yi zaman Yahudawa?"
\s5
\v 15 Mu da muke Yahudawa daga haihuwa, ba "Al'ummai masu zunubi ba."
\v 16 Ku sani fa, babu wanda za a baratar ta ayyukan shari'a. A maimakon haka an baratar da su ta wurin bangaskiya cikin Yesu Almasihu. Mun zo ga cikin Almasihu Yesu domin mu samu baratarwa ta bangaskiya cikin Almasihu, kuma ba ta ayyukan shari'a ba. Domin ta ayyukan shari'a babu wanda zai samu baratarwa.
\s5
\v 17 Amma idan mun nemi Allah ya baratar da mu cikin Almasihu, mun samu kanmu masu zunubi kenan, Almasihu ya zama bawan zunubi ne? Ko kadan!
\v 18 Idan na sake gina dogara ta a kan shari'a, dogarar da na juya wa baya, na nuna kai na mai karya shari'a kenan.
\v 19 Ta wurin shari'a na mutu ga shari'a, domin in yi rayuwa irin ta Allah.
\s5
\v 20 An giciye ni tare da Almasihu, ba nine ke rayuwa ba kuma, amma Almasihu ke rayuwa a cikina. Rayuwar da nake yi a yanzu a cikin jiki, ina yin ta ne, ta wurin bangaskiya ga dan Allah, wanda ya kaunace ni ya ba da kansa domina.
\v 21 Ban yi watsi da alherin Allah ba, domin idan adalci ya wanzu ta wurin shari'a, ashe Almasihu ya mutu a banza kenan.
\s5
\c 3
\p
\v 1 Ku Galatiyawa marasa wayo! Wanne mugun ido ya cuce ku? Ashe, ba Yesu Almasihu gicciyayye aka nuna a gaban idon ku ba?
\v 2 Ina so in gane wannan daga wurin ku ne kawai. Kun karbi Ruhun ta wurin ayyukan doka ne ko ta wurin ba da gaskiya ga abin da kuka ji?
\v 3 Rashin wayonku ya yi yawa haka ne? Kun fara da Ruhu, sai kuma yanzu ku karasa a cikin jiki?
\s5
\v 4 Kun fuskanci abubuwa da yawa a banza ne - har idan a banza ne?
\v 5 To, shi wanda ya ba ku Ruhun, da ayyuka masu iko a tsakanin ku, ya yi ne ta wurin ayyukan shari'a ko ta wurin ji tare da bangaskiya?
\s5
\v 6 Ibrahim "ya ba da gaskiya ga Allah, kuma an lisafta mashi wannan a matsayin adalci."
\v 7 Ta wannan hanya ku fahimta su wadanda suka ba da gaskiya, 'ya'yan Ibrahim ne.
\v 8 Nassi ya riga ya hangi gaba cewa, ta wurin bangaskiya Allah zai baratar da Al'ummai. An yi wa Ibrahim shelar bishara tuntuni: "A cikinka ne dukan al'ummai za su yi albarka."
\v 9 Saboda haka, wadanda suka ba da gaskiya, masu albarka ne tare da Ibrahim wanda ke da bangaskiya.
\s5
\v 10 La'ana na kan wadanda sun dangana ga ayyukan shari'a. Gama a rubuce yake, "La'ananne ne kowanne mutum da bai tsaya ga duk abin da ke a rubuce cikin littafin shari'a ba, ya kuma aikata shi duka."'
\v 11 Yanzu a sarari yake, Allah ba ya baratar da kowa ta wurin shari'a, domin "Mai adalci zai rayu ta bangaskiya."
\v 12 Doka ba daga bangaskiya take ba, 'Amma a maimakon haka, "Shi wanda ke yin wadannan abubuwa cikin shari'a, zai yi rayuwa ta wurin shari'a."
\s5
\v 13 Almasihu ya fanshe mu daga la'anar shari'a da ya zama la'ananne saboda mu. Kamar yadda yake a rubuce, "La'ananne ne duk wanda aka sargafe a bisa itace."
\v 14 Dalilin shine, albarkan da ke bisan Ibrahim ta zo ga al'ummai cikin Almasihu Yesu, domin mu samu karban alkawarin Ruhu ta wurin bangaskiya.
\s5
\v 15 'Yan'uwa, ina magana bisa ga ka'idojin mutane. Idan mutane sun yi yarjejeniya, babu mai kawar da shi ko a kara shi.
\v 16 Yanzu fa, an fada alkawaran nan ne ga Ibrahim da zuriyarsa. Bai ce, "ga zuriya ba" da manufar masu yawa; amma a maimakon haka ga daya kadai, "ga zuriyar ka," wanda shine Almasihu.
\s5
\v 17 Yanzu na fadi wannan. Shari'a, wadda ta zo shekaru 430 daga baya, ba ta kawar da alkawarin da Allah ya tabbatar da shi ba tun a baya.
\v 18 Domin idan da gadon ya zo ta dalilin shari'a ne, da ba za ya zo kuma ta dalilin alkawari ba. Amma Allah ya ba da shi ga Ibrahim kyauta ta wurin alkawari.
\s5
\v 19 Me ya sa kenan aka ba da shari'a? An kara ta ne saboda laifuffuka, har sai zuriyar Ibrahim din nan ta zo ga wadanda aka yi masu alkawarinta. An kaddamar da ikon shari'ar ta wurin mala'iku, ta hannun matsakaici.
\v 20 Yanzu dai matsakanci yana nufin mutum fiye da daya, duk da haka Allah daya ne.
\s5
\v 21 Shari'a tana tsayayya da alkawaran Allah kenan? Ko kadan! Domin idan da an ba da shari'a da ke iya bayar da rai, babu shakka da adalci ya zo ta wurin wannan shari'a.
\v 22 A maimakon haka, nassi ya kulle abubuwa duka a karkashin zunubi. Allah ya yi wannan domin alkawarin sa na ceton mu ta wurin bangaskiya cikin Yesu Almasihu ya samu a ba da shi ga wadanda suka gaskanta.
\s5
\v 23 Amma kafin bangaskiya cikin Almasihu ta zo, an kulle mu kuma aka tsare mu da shari'a har zuwa ga wahayin bangaskiya.
\v 24 Daga nan shari'a ta zama mana jagora har sai da Almasihu ya zo, domin mu samu baratarwa ta wurin bangaskiya.
\v 25 Yanzu da bangaskiya ta zo, ba mu kuma a karkashin jagora.
\v 26 Domin dukanku 'ya'yan Allah ne ta wurin bangaskiya cikin Almasihu Yesu.
\s5
\v 27 Dukanku da aka yi wa baftisma cikin Almasihu, kun suturce kanku da Almasihu.
\v 28 Babu Bayahude ko Baheline, bawa ko 'yantacce, babu na miji ko mace, domin dukanku daya ne cikin Almasihu Yesu.
\v 29 Idan ku na Almasihu ne, ku zuriyar Ibrahim ne kenan, magada bisa ga alkawarin.
\s5
\c 4
\p
\v 1 Ina cewa muddin magaji yaro ne, babu bambancin sa da bawa, ko da yake shine mai mallakan dukan kadarorin.
\v 2 A maimakon haka, yana karkashin masu jagora da amintattu har sai lokacin da mahaifinsa ya ajiye.
\s5
\v 3 Hakannan mu ma, lokaci da muke yara, an rike mu cikin kangi na tushin ka'idojin wannan duniya.
\v 4 Amma da lokacin ya yi daidai, Allah ya aiko da dansa, haihuwar mace, haihuwar karkashin shari'a.
\v 5 Ya yi haka ne domin ya fanshi wadanda ke a karkashin shari'a, domin mu karbi diyanci a matsayin 'ya'ya.
\s5
\v 6 Domin ku 'ya'ya ne, Allah ya aiko da Ruhun Dansa cikin zuciyarmu, Ruhun wanda ke kirar, "Abba, Uba."
\v 7 Saboda wannan dalilin kai ba kuma bawa ba ne amma da. Idan kai da ne, hakannan kuma kai ma magaji ne ta wurin Allah.
\s5
\v 8 Duk da haka a da, da ba ku san Allah ba, bayi ne ku ga alloli wadanda ainihi ba alloli ba ne ko kadan.
\v 9 Amma yanzu da kuka san Allah, ko kuma, yanzu da Allah ya san ku, me ya sa kuke sake komawa zuwa ga tushen ka'idodin nan mara karfi da amfani? Kuna so ku sake komawa zaman bayi kuma daga farko?
\s5
\v 10 Kuna kiyaye ranaku na musamman, sabobin watanni, lokatai, da shekaru.
\v 11 Ina ji maku tsoro. Ina tsoro cewa kamar na yi aiki cikinku a wofi.
\s5
\v 12 Ina rokon ku 'yan'uwa, ku zama kamar yadda nake, domin ni ma na zama kamar ku. Ba ku yi mani laifin komai ba.
\v 13 Amma kun sani cewa saboda rashin lafiya ne na yi maku shelar bishara da farko.
\v 14 Ko da yake halin da nake ciki cikin jiki a zahiri ya sa ku cikin gwaji, ba ku raina ni ba ko kuma kuka watsar da ni. A maimakon haka, kun karbe ni kamar mala'ikan Allah, kamar ni Almasihu Yesu ne da kansa.
\s5
\v 15 Saboda haka, yanzu ina murnar taku? Domin ina shaidar ku, idan mai yiwuwa ne, da kun kwakulo idanunku, kun ba ni.
\v 16 To kenan, na zama makiyin ku ne saboda na gaya maku gaskiya?
\s5
\v 17 Suna neman ku da himma ba domin wani alheri ba ne. Suna so su raba ni da ku domin ku bi su.
\v 18 Yana da kyau ko yaushe a yi himma domin dalilai masu kyau, ba kuma kawai sa'adda ina tare da ku ba.
\s5
\v 19 'Ya'yana kanana, sabili da ku ina cikin zafin nakuda kuma sai Almasihu ya samu kafuwa cikinku.
\v 20 Da ma a ce ina tare da ku yanzu in canza muryata, domin ina damuwa a kanku kwarai.
\s5
\v 21 Ku gaya mani, ku da kuke marmarin ku zo karkashin shari'a, ba ku ji abin da shari'ar ta ce ba?
\v 22 A rubuce yake cewa, Ibrahim yana da 'ya'ya maza biyu, daya dan baiwa ne, dayan kuma dan 'yantaciyar mace ne.
\v 23 Abin lura anan, dan baiwar an haife shi ta hanyar mutuntaka ne, amma dan 'yantaciyar macen, an haife shi ta wurin alkawari ne.
\s5
\v 24 Ana iya bayyana abubuwan nan a hanyar kwatanci kamar haka, wadannan mata na kama da alkawarai ne guda biyu. Dayan alkawarin daga dutsen Sinayi ne. Ta haifi 'ya'ya da ke bayi ne su. Ita ce Hajaratu.
\v 25 Yanzu fa, Hajaratu ita ce dutsen Sinayi da ke Arebiya. Misali ce na Urushalima na yanzu, domin tana cikin bauta tare da 'ya'yanta.
\s5
\v 26 Amma Urushalima da ke bisa 'yantacciya ce, ita ce mahaifiyarmu.
\v 27 Kamar yadda yake a rubuce, "Ki yi murna, ke bakarariya, ke da ba ki taba haihuwa ba. Ki yi shewa na farinciki, ke da ba ki dandana haihuwan da ba. Domin 'ya'yan bakarariya da yawa suke, fiye da ta mace mai miji."
\s5
\v 28 Yanzu fa, 'yan'uwa, kamar yadda Ishaku yake, haka muke, wato 'ya'yan alkawari.
\v 29 A lokacin can, shi wanda aka haife shi ta hanyar mutuntaka ya tsananta wa wanda aka haife shi ta hanyar Ruhu. Haka yake har yanzu.
\s5
\v 30 Amma menene nassi ya ce? "Ka kori baiwar nan tare da danta. Domin dan baiwar nan ba za ya ci gado tare da dan macen nan da ke 'yantacciya ba."
\v 31 Saboda haka 'yan'uwa, mu ba 'ya'yan baiwa ba ne, a maimakon haka, mu 'ya'yan macen nan ne da ke 'yantacciya.
\s5
\c 5
\p
\v 1 Saboda 'yanci ne Almasihu ya yantar da mu. Sai ku dage kada ku sake komawa cikin kangin bauta.
\v 2 Duba, ni Bulus, ina gaya maku cewa idan an yi maku kaciya, Almasihu ba zai zama da amfani a gare ku ba a kowace hanya.
\s5
\v 3 Haka kuma, na shaida ga ko wanda mutum wadda aka yi masa kaciya ya zama dole ya yi biyayya da dukan shari'a.
\v 4 Kun rabu da Almasihu, dukanku wadanda aka "baratar" ta wurin shari'a. Kun fadi daga alheri.
\s5
\v 5 Domin ta wurin Ruhu, cikin bangaskiya, muna jira gabagadi na adalci.
\v 6 A cikin Almasihu kaciya ko rashin kaciya ba shi da ma'ana. Bangaskiya kadai mai aiki ta wurin kauna ita ce mafi muhimmanci.
\v 7 Da kuna tsere da kyau, wanene ya tsayar da ku daga yin biyayya da gaskiya?
\v 8 Rinjayarwa da ke sa yin wannan, ba daga wanda ya kira ku ba ne
\s5
\v 9 Ai karamin yisti shi yake sa dukan kulli ya kumbura.
\v 10 Ina da wannan gabagadin game da ku cikin Ubangiji cewa ba za ku yi tunani a wata hanya daban ba. Shi wanda ya rikita ku zai sha hukunci ko wanene shi.
\s5
\v 11 'Yan'uwa, idan har yanzu wa'azin kaciya nake yi, don me har yanzu ake tsananta mani? Inda haka ne dutsen sanadin tuntube game da gicciye da ya ragargaje.
\v 12 Ina fata wadanda suke badda ku su maida kansu babani.
\s5
\v 13 'Yan'uwa, domin Allah ya kira ku zuwa ga yanci, kada dai ku mori yancin nan ya zama zarafi domin jiki. A maimakon haka ta wurin kauna ku yi wa juna hidima.
\v 14 Saboda dukan shari'a ta cika ne a cikin doka guda daya; "Ka kaunaci makwabcinka kamar kanka."
\v 15 Amma idan kuna cizo da hadiye juna, ku lura kada ku hallakar da junanku.
\s5
\v 16 Na ce, ku yi tafiya cikin Ruhu, ba za ku cika sha'awoyin jiki ba.
\v 17 Domin jiki yana gaba mai karfi da Ruhu, Ruhu kuma yana gaba da jiki. Domin wadannan akasin juna suke. Sakamakon shine ba za ku iya yin abin da kuke so ba.
\v 18 Amma idan Ruhu ne ke bishe ku, ba ku karkashin shari'a.
\s5
\v 19 Yanzu ayyukan jiki a bayyane suke. Sune al'amuran lalata, rashin tsarki, sha'awoyi,
\v 20 bautar gumaka, sihiri, yawan fada, jayayya, kishi, zafin fushi, gasa, tsattsaguwa, hamayya,
\v 21 hassada, buguwa, buguwa da tarzoma, da dai sauran irin wadannan abubuwa. Na gargade ku, kamar yadda a da na gargade ku, cewa wadanda suke aikata wadannan abubuwa ba za su gaji mulkin Allah ba.
\s5
\v 22 Amma 'ya'yan Ruhu kauna ne, farinciki, salama, hakuri, kirki, nagarta, bangaskiya,
\v 23 tawali'u, da kamun kai. Babu wata shari'a da ke gaba da wadannan abubuwa.
\v 24 Wadanda suke na Almasihu Yesu sun giciye halin jiki tare da marmarin sa da miyagun sha'awoyi.
\s5
\v 25 Idan muna zaune cikin Ruhu, mu yi tafiya da Ruhu.
\v 26 Kada mu zama masu girman kai, ko muna cakunar juna, ko muna kishin juna.
\s5
\c 6
\p
\v 1 'Yan'uwa, idan an kama mutum yana yin wani laifi, ku da kuke da ruhaniya sai ku dawo da mutumin a hanya cikin ruhun tawali'u, ka lura da kanka don kada kai ma ka fada a cikin gwaji.
\v 2 Ku dauki damuwar juna, ta yin haka za ku cika shari'ar Almasihu.
\s5
\v 3 Domin idan kowa ya zacci shi wani abu ne alhali shi ba komai ba ne rudin kansa yake yi.
\v 4 Sai kowa ya auna aikin sa. Sa'annan zai sami abin da zai yi takama, ba sai ya kwatanta kansa da wani ba.
\v 5 Domin kowa zai dauki nauyin kayansa.
\s5
\v 6 Wanda aka koya masa maganar, wajibi ne ya ci amfanin abubuwansa masu kyau duka tare da malaminsa.
\v 7 Kada fa a yaudare ku ba a yi wa Allah ba'a. Dukan abin da mutum ya dasa, shine abin da zai girba.
\v 8 Domin shi wanda ya shuka wa kansa dabi'ar zunubi zai girbi hallaka, amma shi wanda ya shuka cikin Ruhu, zai girbi rai madawwami daga Ruhu.
\s5
\v 9 Kada mu gaji da aikata nagarta, domin a lokacin da ya dace za mu yi girbi idan ba mu gaji ba.
\v 10 Saboda haka, lokacin da muke da zarafi, sai mu yi nagarta ga kowa. Mu yi nagarta mussamman ga wadanda suke na iyalin bangaskiya.
\s5
\v 11 Dubi yawan wasikun da na rubuta maku da hannuna.
\v 12 Wadanda suke so su nuna hali mai kyau cikin jiki suke tilasta ku yin kaciya. Suna yin haka ne kadai saboda kada a tsananta masu saboda gicciyen Almasihu.
\v 13 Domin ko su wadanda suke masu kaciya ba su kiyaye shari'a. Maimakon haka suna so ne a yi maku kaciya don su yi fahariya game jikinku.
\s5
\v 14 Bari kada ya zama ina fahariya sai dai ta gicciyen Ubangijinmu Yesu Almasihu. Ta wurinsa ne aka gicciye duniya a gare ni, ni kuma ga duniya.
\v 15 Domin kaciya ko rashin kaciya ba komai ba ne. Maimakon haka, sabon halita ne ke da muhimmanci.
\v 16 Ga dukan wadanda za su zauna cikin wannan ka'ida, bari salama da jinkai su kasance tare da su da kuma bisa Isra'ila na Allah.
\s5
\v 17 Daga yanzu zuwa nan gaba kada wani ya dame ni, domin ina dauke da tabbai na Yesu a jikina.
\v 18 Alherin Ubangijinmu Yesu Almasihu ya kasance da ruhun ku, 'yan'uwa. Amin.