ha_ulb/48-2CO.usfm

511 lines
35 KiB
Plaintext

\id 2CO
\ide UTF-8
\h 2 Korantiyawa
\toc1 2 Korantiyawa
\toc2 2 Korantiyawa
\toc3 2co
\mt 2 Korantiyawa
\s5
\c 1
\p
\v 1 Bulus, manzon Almasihu Yesu ta wurin nufin Allah, da kuma Timoti dan'uwan mu, zuwa ga Ikilisiyar Allah da ke a Korantus, da kuma dukan 'yan'uwa da ke yankin kasar Akaya.
\v 2 Bari alheri ya kasance tare da ku da kuma salama ta Allah Ubanmu da kuma Ubangiji Yesu Almasihu.
\s5
\v 3 Bari yabo ya tabbata ga Allah da kuma Uba na Ubangijinmu Yesu Almasihu. Shine Uba na dukan jiyejiyenkai, da kuma Allah na dukan ta'aziya.
\v 4 Allah yana ta'azantar da mu a cikin dukan wahalarmu, domin mu iya ta'azantar da wadanda ke cikin kowace wahala. Muna ta'azantar da wasu da irin ta'aziyar da Allah ke ta'azantar da mu.
\s5
\v 5 Gama kamar yadda wahalhalun Almasihu suka karu domin mu, haka kuma ta'aziyarmu ta yawaita cikin Almasihu.
\v 6 Amma fa idan muna shan wuya, domin ta'aziyarku ne da cetonku. Haka kuma in mun ta'azantu, domin ta'aziyarku ne. Ta'aziyarku tana aiki ne sosai yayinda kuka jure da irin shan wuyar da mu ma muke sha.
\v 7 Kuma gabagadinmu game da ku tabbatacce ne. Mun kuwa sani kamar yadda kuke tarayya cikin shan wahalhalun, haka kuma za ku yi tarayya cikin ta'aziyyar.
\s5
\v 8 Gama ba mu so ku rasa sani, 'yan'uwa, game da tsananin da ya same mu a Asiya. An murkushe mu gaba daya har fiye da karfin mu, har ma mun fidda zuciya za mu rayu.
\v 9 Hakika, mun ji hukuncin mutuwa akan mu. Amma wannan ya faru ne domin kada mu dogara ga kanmu, sai dai ga Allah, wanda ke tada matattu.
\v 10 Ya kubutar da mu daga wannan mummunan hatsari na mutuwa, kuma zai sake kubutar da mu. Mun kafa begenmu gare shi cewa zai sake kubutar da mu.
\s5
\v 11 Zai aikata wannan yayinda kuka taimake mu da addu'ar ku. Sa'an nan da dama za su bada godiya a madadin mu don tagomashin alheri da aka yi mana ta wurin addu'o'in mutane masu yawa.
\s5
\v 12 Muna kuwa alfahari da haka: wato shaidar lamirinmu. Gama da kyakkyawan nufi da aminci da ke zuwa daga Allah muka tafiyar da rayuwarmu a Duniya. Mun yi wannan ne musamman tare da ku-ba kuwa cikin hikimar Duniya ba, amma ta wurin alherin Allah.
\v 13 Bamu rubuta maku abinda ba za ku iya karantawa ko fahimta ba. Ina fata za ku fahimce mu baki daya,
\v 14 kamar yadda kuka fahimce mu kadan yanzu. Daganan a ranar Ubangijinmu Yesu za mu zama dalilinku na alfahari, kamar yadda za ku zama namu.
\s5
\v 15 Saboda gabagadin da nake da shi game da haka, naso in zo gare ku da farko, domin ku amfana da ziyara sau biyu.
\v 16 Ina da shirin ziyaratar ku a kan hanyata ta zuwa Makidoniya. Daga nan kuma ina da yi niyyar in sake ziyartar ku, a tafiya ta daga Makidoniya, domin ku aike ni a hanyata ta zuwa Yahudiya.
\s5
\v 17 Yayinda nake irin wannan tunani, ina shakka ne? Ina shirya abubuwa ne bisa ga magwajin mutum, ta yadda har zan ce "I, i" da "A, a, a, a" a lokaci guda?
\v 18 Amma kamar yadda Allah yake amintacce, ba ma fadin "I" da "A'a" a lokaci guda.
\s5
\v 19 Gama Dan Allah, Yesu Almasihu, wanda Silbanus da Sila, da Ni muka shaida maku, ba "I" da "A, a" ba ne. Maimakon haka, Shi "I" ne a kodayaushe.
\v 20 Gama dukan alkawaran Allah 'I' ne a cikin sa. Haka kuma ta wurin sa muna cewa "Amin" zuwa ga daukakar Allah.
\s5
\v 21 Yanzu dai Allah ne ya tabbatar da mu da ku a cikin Almasihu, ya kuma kebe mu.
\v 22 Ya sa hatiminsa a kan mu ya kuma ba mu Ruhu a zuciyar mu a matsayin tabbacin abinda zai bamu daga baya.
\s5
\v 23 Maimakon haka, na yi kira ga Allah ya zama shaida domina, cewa dalilin dayasa banzo Korintis ba domin in kare ku ne.
\v 24 Ba muna kokarin mu sarrafa yadda bangaskiyar ku za ta zama ba ne. Maimakon haka, muna aiki tare da ku ne domin farincikinku, yayinda kuke tsaye cikin bangaskiyarku.
\s5
\c 2
\p
\v 1 Don haka na yanke shawara daga bangarena, ba zan sake zuwa wurin ku cikin yanayi mai tsanani ba.
\v 2 Idan na bata maku rai, wa zai karfafa ni, in ba shi wanda na bata wa rai ba?
\s5
\v 3 Na rubuto maku kamar yadda na yi domin idan na zo gareku kada in sami bacin rai a wurin wadanda ya kamata su faranta mani rai. Ina da gabagadi game da dukan ku, cewa farincikin da nake da shi, shine kuke da shi duka.
\v 4 Domin kuwa na rubuto maku cikin kunci da bacin rai da kuma hawaye mai yawa. Ba zan so in sake bata maku rai ba. Maimakon haka, na so ku san zurfin kaunar da nake da ita domin ku.
\s5
\v 5 Idan wani ya kawo sanadin bacin rai, ba ni kadai ya kawo wa wannan abin ba, amma ta wani fannin- domin kada a tsananta- har a gare ku duka.
\v 6 Hukuncin nan da galibinku kuka yi wa mutumin nan ya isa.
\v 7 Don haka, yanzu a maimakon hukunci, ku gafarta masa, ku kuma ta'azantar da shi. Ku yi haka domin kada bakinciki mai yawa ya danne shi.
\s5
\v 8 Don haka ina karfafa ku da ku nuna irin kaunar da kuke yi masa a fili.
\v 9 Wannan shine dalilin da ya sa na rubuto maku, domin in gwada ku, ko kuna biyayya cikin komai.
\s5
\v 10 Duk mutumin da kuka gafarta wa, ni ma na gafarta masa. Abin da na gafarta-idan na gafarta wani abu-an gafarta ne domin ku a gaban Almasihu.
\v 11 Wannan ya zama haka ne domin kada shaidan ya yaudare mu. Don ba mu jahilci irin makircinsa ba.
\s5
\v 12 Na samu budaddiyar kofa daga wurin Ubangiji yayin da nazo birnin Tarwasa, in yi wa'azin bisharar Almasihu a can.
\v 13 Duk da haka, raina bai kwanta ba, domin ban ga dan'uwana Titus a can ba. Sai na bar su a can, na dawo Makidoniya.
\s5
\v 14 Amma godiya ta tabbata ga Allah, wanda cikin Almasihu yake kai mu ga nasara a koyaushe. Ta wurin mu ya baza kamshi mai dadi na saninsa ko'ina.
\v 15 Gama mu, kamshi ne mai dadi na Almasihu ga Allah, a tsakanin wadanda ake ceton su, da kuma tsakanin wadanda suke hallaka.
\s5
\v 16 Ga mutanen da suke hallaka, kamshi ne daga mutuwa zuwa mutuwa. Ga wadanda suke samun ceto kuma kamshi ne daga rai zuwa rai. Wanene ya cancanci wadannan abubuwan?
\v 17 Gama mu ba kamar sauran mutane muke ba, masu sayar da maganar Allah domin samun riba. Maimakon haka, da tsarkakkiyar manufa, muke magana cikin Almasihu, kamar yadda Allah ya aiko mu, a gaban Allah.
\s5
\c 3
\p
\v 1 Muna fara sake yabon kanmu ne? Ba mu bukatar wasikun shaida daga gare ku ko zuwa gare ku, kamar wadansu mutane, ko ba haka ba?
\v 2 Ku da kanku kune wasikar shaidarmu, wadda aka rubuta a zukatanmu, wadda Kuma dukan mutane suka sani suke kuma karantawa.
\v 3 Kuma kun nuna ku wasika ne daga Almasihu, wadda muka isar. Ba da tawada aka rubuta ta ba amma da Ruhun Allah mai rai. Ba bisa allunan duwatsu aka rubuta ta ba, amma bisa allunan zukatan mutane.
\s5
\v 4 Gama wannan ne gabagadin da muke da shi cikin Allah ta wurin Almasihu.
\v 5 Ba mu da wata gwanintar kanmu da za mu yi takamar wani abu ya zo daga gare mu. Maimakon haka, gwanintar mu daga Allah take.
\v 6 Allah ne ya maishe mu kwararrun bayi na sabon alkawari. Wannan alkawari ne ba na rubutu ba amma na Ruhu. Gama rubutu kisa yake yi, amma Ruhu rai yake bayarwa.
\s5
\v 7 To hidimar da ta haifar da mutuwa- wadda aka rubuta bisa duwatsu- ta zo cikin irin wannan daukaka da har Israila ba su iya kallon fuskar Musa kai tsaye ba. Wannan kuwa saboda daukakar da ke fuskarsa ne, daukaka mai shudewa.
\v 8 Ina misalin girman daukakar hidimar da Ruhu ke yi?
\s5
\v 9 Gama idan hidimar kayarwa tana da daukaka, ina misalin yalwatar daukaka da hidimar adalchi za ta yi!
\v 10 Babu shakka, abin da aka maishe shi mai daukaka a da, ba ya da sauran daukaka a wannan fanni, saboda irin daukakar da ta zarce shi.
\v 11 To idan har mai shudewar nan ya na da daukaka, ina misalin daukakar da abu na dindindin zai samu!
\s5
\v 12 Dashike muna da wannan tabbaci, muna da gabagadi sosai.
\v 13 Ba kamar Musa muke ba wanda ya sa mayafi ya rufe fuskarsa, ta yadda mutanen Isra'ila basu iya kallon karshen daukaka mai shudewa ba kai tsaye.
\s5
\v 14 Amma tunaninsu ya zama a rufe. Har yau kuwa mayafin na nan sa'adda ake karanta tsohon alkawari. Ba a bude shi ba, saboda a cikin Almasihu ne kadai ake kawar da shi.
\v 15 Amma har yau, duk lokacin da ake karanta littafin Musa, akwai mayafi shimfide a zukatansu.
\v 16 Amma sa'adda mutum ya juyo wurin Ubangiji, an kawar da mayafin.
\s5
\v 17 To Ubangiji shine Ruhun. Inda Ruhun Ubangiji yake, akwai 'yanci.
\v 18 Dukan mu yanzu, da fuskoki marasa mayafi, muna ganin daukakar Ubangiji. Muna samun sakewa zuwa cikin irin wannan daukaka, daga wannan mataki na daukaka zuwa wani matakin, kamar dai daga wurin Ubangiji, wanda shine Ruhun.
\s5
\c 4
\p
\v 1 Don haka, domin muna da wannan hidima, da kuma yadda muka karbi jinkai, ba mu karaya ba.
\v 2 Maimakon haka, sai muka rabu da dukan hanyoyin da ke na kunya, kuma na boye. Ba mu rayuwar makirci, kuma bamu yiwa maganar Allah rikon sakaci. Ta wurin gabatar da gaskiya, muna mika kanmu ga lamirin kowa a gaban Allah.
\s5
\v 3 Amma, idan bishararmu a rufe take, tana rufe ne ga wadanda ke hallaka.
\v 4 A al'amarinsu, allahn wannan duniya ya makantar da zukatansu marasa bada gaskiya. A sakamakon haka, ba su iya ganin hasken bisharar daukakar Almasihu ba, wanda shine surar Allah.
\s5
\v 5 Gama ba mu yin shelar kanmu, amma Almasihu Yesu a matsayin Ubangiji, mu kuma bayinku saboda Yesu.
\v 6 Gama Allah shine wanda ya ce, "Haske zai haskaka daga cikin duhu." Ya haskaka cikin zukatanmu don ya bada hasken sanin daukakar Allah a gaban Yesu Almasihu.
\s5
\v 7 Amma muna da wannan dukiya a randunan yunbu, yadda zai zama a bayyane cewa mafi girman iko na Allah ne ba namu ba.
\v 8 Muna shan tsanani ta kowace hanya, ba a ci mu dungum ba. Mun rikice amma ba mu karaya ba, an tsananta mana amma ba a watsar da mu ba.
\v 9 Ana tsananta mana amma ba a yashe mu ba. Aka doddoke mu amma ba mu lalace ba.
\v 10 Mu dai a kullayaumin muna dauke da mutuwar Yesu a jikkunanmu, saboda a bayyana rayuwar Yesu a jikkunanmu kuma.
\s5
\v 11 Mu da muke a raye kuwa a kulluyaumin ana mika mu ga mutuwa saboda Yesu, domin rayuwar Yesu ta zama a bayyane a jikunanmu na mutuntaka.
\v 12 Saboda haka, mutuwa tana aiki a cikinmu, amma rai na aiki a cikinku.
\s5
\v 13 Amma dai muna da wannan Ruhu na bangaskiya kammar yadda aka rubuta: "Na gaskata, saboda haka na furta." Mu ma mun gaskata, haka kuwa muke fada.
\v 14 Mun sani cewa wanda ya tada Ubangiji Yesu daga matattu za ya sake tada mu tare da Yesu. Mun san cewa zai gabatar da mu tare da ku a gabansa.
\v 15 Dukan abubuwa sabili da ku suke domin, yayin da aka baza alheri ga mutane dayawa, bada godiya ta karu ga daukakar Allah.
\s5
\v 16 Don haka ba mu karaya ba. Kodashike daga waje muna lalacewa, daga ciki ana sabunta mu kulluyaumin.
\v 17 Domin wannan 'yar wahala ta dan lokaci tana shirya mu zuwa ga nauyin madauwamiyar daukaka wadda ta wuce gaban aunawa.
\v 18 Domin ba muna kallon abubuwan da ake gani bane, amma abubuwan da ba a gani. Abubuwan da muke iya gani ba masu dawwama ba ne, amma abubuwan da ba a gani madawwama ne.
\s5
\c 5
\p
\v 1 Mun san cewa idan wannan gidan da muke zaune a ciki ya rushe, muna da wani ginin daga wurin Allah. Gida ne wanda ba hannuwan mutane suka gina ba, amma madawwamin gida ne a cikin sama.
\v 2 Domin a cikin wannan jiki muna gurnani, muna jira a suturta mu da wurin zaman mu na samaniya.
\v 3 Muna jiran wannan ne domin ta wurin suturtar da mu ba za a same mu tsirara ba.
\s5
\v 4 Gama babu shakka yayinda muke cikin wannan alfarwa, muna gurnani, muna nawaita. Ba mu so muyi zaman hutanci. Maimakon haka, muna so a suturtar da mu, domin rai ya hadiye abu mai mutuwa.
\v 5 Wanda kuwa yake shirya mu domin ainihin wannan abu Allah ne, wanda ya ba mu Ruhu a matsayin alkawarin abinda ke zuwa.
\s5
\v 6 Domin wannan mu zama da gabagadi koyaushe. Mu lura da cewa yayinda muka shagala cikin jiki, muna nesa da Ubangiji.
\v 7 Gama bisa ga bangaskiya muke tafiya, ba bisa ga ganin ido ba.
\v 8 Don haka muna da gabagadi. Mun gwammace mu rabu da jiki domin mu zauna tare da Ubangiji.
\s5
\v 9 Sai muka maishe shi burinmu, ko muna cikin jiki ko nesa, mu gamshe shi.
\v 10 Domin tilas dukanmu mu hallara a gaban kursiyin shari'a na Almasihu, saboda kowa ya karbi sakamakon abubuwan da yayi cikin jiki, ko masu kyau ne ko marasa kyau.
\s5
\v 11 Don haka, domin mun san tsoron Ubangiji, muna rinjayar mutane. Allah na ganin yadda muke a fili. Ina fatan hakan a fili take ga lamirinku.
\v 12 Ba muna kokarin mu rinjaye ku domin ku kalle mu a matsayin amintattun mutane ba. Maimakon haka, muna ba ku dalilin yin takama da mu, domin ku sami amsar da za ku bada ga wadanda ke fahariya da kasancewarsu amma ba game da abinda ke zuciya ba.
\s5
\v 13 Gama idan mun fita daga hankulanmu, saboda Allah ne. Kuma idan muna cikin hankalinmu, domin ku ne.
\v 14 Domin kaunar Almasihu ta tilas ta mu, domin mun tabbatar da wannan: cewa mutum daya ya mutu domin kowa, kuma domin wannan duka sun mutu.
\v 15 Kuma Almasihu ya mutu domin kowa, domin wadanda ke raye kada su sake rayuwa domin kansu. A maimakon haka, su yi rayuwa domin shi wanda ya mutu kuma aka tashe shi.
\s5
\v 16 Domin wannan dalili, daga yanzu ba za mu kara shar'anta kowa bisa ga ma'aunin 'yan'adam ba, ko da yake a baya mun taba duban Almasihu a haka. Amma yanzu mun daina shar'anta kowa ta haka.
\v 17 Saboda haka, duk wanda ke cikin Almasihu, sabon halitta ne. Tsofaffin al'amura sun shude. Duba, sun zama sababbi.
\s5
\v 18 Dukan wadannan abubuwa daga Allah ne. Ya sulhunta mu da kansa ta wurin Almasihu, ya kuma ba mu hidimar sulhu.
\v 19 Wato, cikin Almasihu, Allah na sulhunta duniya zuwa gare shi, ba tare da lissafin zunubansu a kansu ba. Yana damka mana sakon sulhu.
\s5
\v 20 Don haka an zabe mu a matsayin wakilan Almasihu, kamar dai Allah na kira ga mutane ta wurin mu. Muna rokon ku, saboda Almasihu: "ku sulhuntu ga Allah!"
\v 21 Shi ya maida Almasihu ya zama hadaya domin zunubinmu. Shine wanda bai taba zunubi ba. Ya yi haka ne don mu zama adalchin Allah a cikin sa.
\s5
\c 6
\p
\v 1 haka, tundashike muna aiki tare, na roke ku kar ku yi watsi da alherin Allah.
\v 2 Domin ya ce, "A lokacin alheri na saurare ku, kuma a ranar ceto na agaje ku." Yanzu ne fa, lokacin alheri. Duba, yanzu ne ranar ceto.
\v 3 Ba mu sa sanadin faduwa a gaban kowannen ku, domin ba mu so hidimarmu ta zama marar amfani.
\s5
\v 4 Maimakon haka, mun tabbatar da kan mu ta wurin dukan ayyukanmu, cewa mu bayin Allah ne. Mu bayinsa ne ta wurin yawan jimiri, azaba, kunci, wahala,
\v 5 duka, kurkuku, tarzoma, cikin aiki tukuru, cikin rashin barci yawancin dare, cikin yunwa,
\v 6 cikin tsarki, ilimi, hakuri, kirki, cikin Ruhu Mai tsarki, da sahihiyar kauna.
\v 7 Mu bayinsa ne cikin kalmar gaskiya, cikin ikon Allah. Muna kuma da makamai na adalci, a hanun dama da hagu.
\s5
\v 8 Muna aiki cikin daraja da rashin daraja, kushe da yabo. Ana zargin mu a kan mu mayaudara ne, duk da haka mu masu gaskiya ne.
\v 9 Muna aiki kamar ba a san mu ba, gashi kuwa mu sanannu ne. Muna aiki kamar masu mutuwa-duba! -har yanzu muna raye. Muna aiki kamar wadanda aka hukunta, amma ba hukuncin kisa ba.
\v 10 Muna aiki kamar muna bakinciki, amma a koyaushe muna farinciki. Muna aiki kamar matalauta, amma muna azurta mutane dayawa. Muna aiki kamar ba mu da komai, amma mun mallaki komai.
\s5
\v 11 Mun fada maku dukan gaskiyar, Korantiyawa, kuma zuciyar mu a bude ta ke.
\v 12 Ba mu kange zukatan ku ba, ku ne kuka kange zukatanku a gare mu.
\v 13 Yanzu a sabanin haka-Ina magana da ku kamar yara-ku bude mana zukatanku.
\s5
\v 14 Kada ku yi cudanya da marasa bangaskiya. Wace tarayya ke tsakanin adalci da take shari'a? Ko kuma wace zumunta ce ke tsakanin haske da duhu?
\v 15 Wace yarjejeniya ke tsakanin Almasihu da Ibilis? ko kuma me ya hada masu bangaskiya da marasa bangaskiya?
\v 16 ko wace yarjejeniya ce a tsakanin haikalin Allah da gumaka? Domin kuwa mu haikali ne na Allah mai rai, kamar yadda Allah ya ce: "Zan zauna a cikin su, in kuma yi tafiya a tsakanin su. Zan zama Allahnsu, su kuma za su zama mutanena."
\s5
\v 17 Sabili da haka, "Ku fito daga cikin su, kuma ku zama kebabbu," in ji Ubangiji. "Kada ku taba kazamin abu, zan kuma karbe ku.
\v 18 Zan zama Uba a gare ku, ku kuma za ku zama 'ya'ya maza da mata a gare ni," in ji Ubangiji Mai iko duka.
\s5
\c 7
\p
\v 1 Kaunatattu, da shike muna da wadannan alkawura, bari mu tsaftace kanmu, daga dukan abubuwan da ke kazantar da jikinmu da ruhunmu. Bari mu bidi tsarki cikin tsoron Allah.
\s5
\v 2 Ku ba mu dama! Bamu bata wa kowa rai ba. Ba mu cutar da kowa ko mu zambaci kowa ba.
\v 3 Ba domin in kayar da ku na fadi haka ba. Domin kuwa na riga na fada muku, cewa kuna zuciyar mu, domin mu mutu tare mu kuma rayu tare.
\v 4 Ina da muhimmin gabagadi a cikin ku, Ina fahariya da ku. Ina cike da ta'aziya. Farincikina ya cika makil duk da wahalhalunmu.
\s5
\v 5 Yayin da muka zo Makidoniya, jikinmu bai samu hutu ba. A maimakon haka, mun shiga matsaloli ta ko wace hanya ta wurin tashin hankali a waje tsoro kuma a ciki.
\v 6 Amma Allah, mai ta'azantar da raunana, ya ta'azantar da mu ta wurin zuwan Titus.
\v 7 Ba ta wurin isowar sa kadai Allah ya yi mana ta'aziyya ba. Amma kuma ta wurin ta'aziyyar da Titus ya samu daga wurin ku. Ya gaya mana irin matsananciyar kaunarku, bakincikinku, da zurfin kulawarku a kaina. Na kuwa yi farinciki sosai.
\s5
\v 8 Kodashike wasikata, ta bata maku rai, ban yi da na sanin haka ba. Amma sa'adda na ga wasika ta ta bata maku rai, na yi da na sani. Sai dai bacin ranku, na dan lokaci ne.
\v 9 Yanzu kuwa, ina farinciki, ba domin bacin ranku ba, amma domin bacin ranku ya kawo ku ga tuba, kun fuskanci bakinciki na ibada, donhaka ba ku yi rashi ba sabili da mu.
\v 10 Domin bakinciki daga Allah ya kan kai ga tuba da ke kammala ceto ba tare da-da na sani ba. Bakinciki na duniya kuwa ya kan kai ga mutuwa.
\s5
\v 11 Ku dubi irin kyakkyawar niyya da bakincikin nan daga Allah ya haifar a cikin ku. Ina misalin girman niyyar nan taku ta nuna cewa baku da laifi. Ina misalin girman fushinku, tsoronku, da sa zuciyarku, himmar ku, da marmarin ku na ganin cewa an yi adalci! A cikin komai, kun nuna kanku marasa laifi a cikin wannan al'amari.
\v 12 Kodayake na rubuto maku, ban rubuto saboda mai laifin ba, ko kuma saboda wanda aka yi wa laifin. Na rubuto ne domin himmarku gare mu ta sanu gare ku a gaban Allah.
\s5
\v 13 Dalilin haka ne muka samu karfafawa. Baya ga ta'aziyyar mu, mun kuma yi murna sosai saboda farin cikin Titus, domin ruhunsa ya wartsake ta wurin ku duka.
\v 14 Domin kuwa idan na yi fahariya da ku a gaban sa, ban ji kunya ba. A sabanin haka, kamar yadda kowane abu da muka fada maku gaskiya ne, fahariyarmu a kan ku ga Titus ta zama gaskiya.
\s5
\v 15 Kaunarsa a gare ku tana da girma, kamar yadda ya rika tunawa da biyayyarku duka, yadda kuka karbe shi da tsoro da rawar jiki.
\v 16 Ina farinciki matuka domin ina da cikakken gabagadi a cikin ku.
\s5
\c 8
\p
\v 1 Muna so ku sani, 'yan'uwa, game da alherin Allah da aka bayar ga Ikkilisiyoyin Makidoniya.
\v 2 A lokacin babban gwajin wahala, yalwar farincikinsu da tsananin talaucinsu ya haifar da yalwar bayarwa hannu sake.
\s5
\v 3 Domin ina shaida, sun yi bayarwa iya kokarinsu, fiye da abinda ma suke iyawa. Cikin yaddar ransu
\v 4 da roko mai yawa suka nace da a ba su zarafi su yi tarayya a wannan hidima ga masu bi.
\v 5 Haka ya auku ba kamar yadda muka yi zato ba. A Maimakon haka, sai da suka fara bada kansu ga Ubangiji. Kuma suka bada kansu gare mu bisa ga nufin Allah.
\s5
\v 6 Sai muka karfafa Titus, wanda ya rigaya ya fara wannan aiki, domin ya kammala wannan aiki na bayarwa ta fannin ku.
\v 7 Amma kun habaka cikin komai-cikin bangaskiya, cikin magana, cikin sani, cikin aiki tukuru, cikin kaunarku dominmu. Don haka, ku tabbata kun habaka a wannan aiki na bayarwa.
\s5
\v 8 Na fadi haka ne ba kamar ina umurtar ku ba. A maimakon haka, na fadi haka ne in gwada sahihancin kaunarku ta wurin kwatanta ta da himmar sauran mutane.
\v 9 Domin kun san alherin Ubangijinmu Yesu Almasihu. Kodashike shi mai arziki ne, amma ya zama matalauci, domin ta wurin talaucinsa ku yi arziki.
\s5
\v 10 A wannan al'amari zan ba ku shawarar da za ta taimake ku. Shekarar da ta wuce, ba fara wani abu kawai kuka yi ba, amma kun yi marmarin ku yi shi.
\v 11 Yanzu ku kammala shi. Kamar yadda kuke da niyya da marmarin yin haka a lokacin, bari ku yi kokari ku kawo shi ga kammalawa iyakar iyawar ku.
\v 12 Idan kuna niyya ku yi wannan aiki, abu mai kyau ne karbabbe kuma. Tabbas ya zama dai-dai da abinda mutum ke da shi, ba abinda ba ya da shi ba.
\s5
\v 13 Domin wannan aiki ba domin a nawaita maku sannan wadansu su samu sauki ba ne. A maimakon haka, ya kamata a sami daidaituwa.
\v 14 Yalwar ku a wannan lokaci za ta zama abin biyan bukatarsu. Haka nan kuma domin yalwar su ta iya biyan bukatarku, domin a sami daidaituwa.
\v 15 Yana nan kamar yadda aka rubuta: "Wanda ke da shi dayawa bai samu raguwar komai ba, kuma wanda yake da kadan bai rasa komai ba."
\s5
\v 16 Amma godiya ga Allah, da yasa a zuciyar Titus marmarin kulawa da ku kamar wadda nake da ita domin ku.
\v 17 Gama ba rokon mu kadai ya karba ba, amma ya yi da gaske akan haka. Ya zo gare ku ne da yardar kan sa.
\s5
\v 18 Mun aiko tare da shi dan'uwa da ake yaba masa a tsakanin dukan Ikkilisiyoyi domin ayyukansa a cikin shelar bishara.
\v 19 Ba domin wannan kadai ba, amma Ikkilisiyoyi ne suka zabe shi ya tafi tare da mu a cikin yin wannan hidima ta alheri. Wannan domin girmama Ubangiji ne kansa da kuma domin aniyarmu ta taimakawa.
\s5
\v 20 Muna gudun kada kowa ya sa mana laifi game da wannan alheri da muke dauke da shi.
\v 21 Niyyar mu ce mu yi kyakkyawan abu, ba a gaban Ubangiji kadai ba, amma a gaban mutane ma.
\s5
\v 22 Mun kuma aiki wani dan'uwan tare da su. Mun sha gwada shi, kuma mun same shi da himma wajen ayyuka da dama. Yanzu kuma ya kara himma, saboda amincewa mai girma da yake da ita gare ku.
\v 23 Game da Titus, shi abokin tafiyata ne, kuma abokin aikina domin ku. Game da yan'uwanmu, an aiko su ne daga Ikkilisiyoyi. Su kuwa daraja ne ga Almasihu.
\v 24 Don haka, ku nuna masu kaunarku, ku kuma nuna wa Ikilisiyoyi dalilin fahariyarmu game da ku.
\s5
\c 9
\p
\v 1 Game da hidima domin tsarkaka, ya dace in rubuta maku.
\v 2 Na san marmarinku, wanda na yi fahariya da shi a gaban mutanen Makidoniya. Na gaya masu Akaya sun riga sun shirya tun bara. Kwazon ku ya sa yawancin su sun shiga aiki.
\s5
\v 3 To na aiko maku da 'yan'uwa saboda kada fahariyarmu akanku ta zama a banza, domin kuma ku zauna a shirye, kamar yadda na ce za ku yi.
\v 4 Idan kuwa ba haka ba, idan wani cikin makidoniyawa ya biyoni kuma ya tarar da baku shirya ba, za mu ji kunya-ba ni cewa komai game da ku-domin ina da gabagadi a kan ku.
\v 5 Sai na ga ya dace in turo 'yan'uwa su zo wurin ku kafin lokaci yayi suyi shirye shirye game da gudummuwar da kuka yi alkawari. Wannan ya zama haka ne domin a shirya shi a matsayin bayarwar albarka, ba wani abin kwace ba.
\s5
\v 6 Batun shine: wanda ya shuka kadan zai girbi kadan, wanda kuma ya shuka da manufar albarka zai girbi albarka
\v 7 Bari kowa ya bayar bisa ga yadda ya yi niyya a zuciyarsa. Kada ya bayar da bacin rai ko kamar dole. Gama Allah yana kaunar mai bayarwa da dadin rai.
\s5
\v 8 Allah na da ikon ya sa kowace albarka ta ribanbanya domin ku, domin, a koyaushe, a cikin dukan abubuwa, ku sami duk abinda kuke bukata. Hakan zai kasance domin ku ribabbanya kowanne kyakkyawan aiki.
\v 9 Kamar yadda aka rubuta, "Ya rarraba arzikinsa, ya bada shi ga matalauta. Adalcinsa ya dawwama har abada."
\s5
\v 10 Shi wanda ke bayar da iri ga mai shuka da gurasa domin abinci, zai bayar ya kuma ribabbanya maku iri domin shuka. Zai sa girbin adalcinku ya karu.
\v 11 Za ku wadata ta kowace hanya domin ku zama masu bayarwa, wannan kuwa zai sa a yi wa Allah godiya ta wurin mu.
\s5
\v 12 Aiwatar da wannan hidima ba biyan bukatun tsarkaka kawai take yi ba. Tana kuma ribanbanya zuwa ayyuka masu yawa na bada godiya ga Allah.
\v 13 Domin an gwada ku an tabbatar da ku akan wannan hidima, za ku kuma daukaka Allah ta wurin biyayyar ku ga shaidar bisharar Almasihu. Za ku kuma daukaka Allah ta wurin yalwar bayarwarku gare su da kowa duka.
\v 14 Suna marmarin ganin ku, suna kuma yi maku addu'a. Suna yin haka saboda alherin Allah mai girma da ke bisan ku.
\v 15 Godiya ga Allah domin kyautarsa wadda ta fi gaban bayyanawa.
\s5
\c 10
\p
\v 1 Ni, Bulus, da kaina nake rokon ku, ta wurin tawali'u da nasihar Almasihu. Ina da saukin kai yayinda nake gaban ku, amma ina da gabagadi a gare ku yayinda ba na tare da ku.
\v 2 Ina rokon ku, yayinda nake gabanku, ba ni so in zama mai tsaurin hali. Amma ina ganin zan bukaci zama mai gabagadi sa'adda nake tsayayya da su wadanda ke zaton muna zama bisa ga jiki.
\s5
\v 3 Kodashike dai muna tafiya bisa jiki, ba ma yin yaki bisa jiki.
\v 4 Domin makaman da muke yaki da su ba na jiki ba ne. Maimakon haka, makamai ne na Allah da ke da ikon rushe ikokin shaidan. Suna kawar da dukan gardandamin da ke kawo kaucewa.
\s5
\v 5 Muna kuma rushe duk wani abinda ke gaba da sanin Allah. Muna kuma kama kowanne tunani zuwa biyayya ga Almasihu.
\v 6 Muna kuma shirye mu hukunta kowanne irin aiki na rashin biyayya, da zarar biyayyarku ta tabbata.
\s5
\v 7 Dubi abin da aka sa a bayyane a gaban ku. In har wani ya tabbata shi na Almasihu ne, bari fa ya tunatar da kansa cewa kamar yadda shi na Almasihu ne, hakanan muma muke.
\v 8 Ko da zan yi fahariya da ikon da muke dashi, wanda Ubangiji ya ba mu domin mu inganta ku, ba domin mu rushe ku ba, ba zan ji kunya ba.
\s5
\v 9 Ba na so ya zama kamar ina firgita ku ne da wasikuna.
\v 10 Domin wadansu mutane na cewa, "Wasikunsa na da iko da firgitarwa, amma in ka gan shi kumama ne. Kalmominsa ba abin saurare ba ne."
\s5
\v 11 Bari wadannan mutane su sani cewa abinda muke fadi a kalmomin wasikunmu lokacin da ba mu nan, haka za mu yi in muna nan.
\v 12 Mu dai ba mu hada kanmu da kowa, ko kuma mu kwatanta kanmu da wadanda ke yabon kansu. Amma yayin da suke gwada kansu da junansu, suke kuma kwatanta kansu da junansu, ba su da ganewa.
\s5
\v 13 Saidai, ba za mu yi fahariya fiye da yadda ya kamata ba. Maimakon haka, za mu yi haka ne gwalgwadon iyakar abinda Allah ya sa muyi, iyakar da takai gareku.
\v 14 Gama bamu yi zarbabi ba sa'adda muka kai gareku. Mune na farko da muka kai gare ku da bisharar Almasihu.
\s5
\v 15 Ba mu yi fahariya fiye da kima game da aikin wasu ba. Maimakon haka, muna fatan bangaskiyar ku ta karu domin bangaren aikin mu ya kara fadada kwarai, kuma a daidai iyakarsa.
\v 16 Muna fatan haka, domin mu kai bishara zuwa yankunan da ke gaba da naku. Ba za mu yi fahariya akan aikin da aka yi a yankin wani ba.
\s5
\v 17 "Amma bari duk wanda zai yi fahariya, ya yi ta cikin Ubangiji."
\v 18 Domin ba wanda ya ke shaidar kansa shine yardajje ba. Maimakon haka, sai dai wanda Ubangiji ke shaidarsa.
\s5
\c 11
\p
\v 1 Ina fatan za ku jure da ni cikin wauta kadan. Ko da yake lallai kuna jurewa da ni!
\v 2 Domin ina kishi sabili da ku. Kishi na kuwa irin na Allah ne domin ku. Tun da na alkawartar da ku a cikin aure ga miji daya. Na kuma yi alkawarin in gabatar da ku kamar budurwa mai tsarki ga Almasihu.
\s5
\v 3 Gama ina fargaba a kan ku, ko watakila, kamar yadda macijin ya yaudari Hauwa'u ta wurin kissarsa, Ya zamana tunaninku ya kauce daga sahihiyar sadaukarwa ga Almasihu.
\v 4 Anar misali idan wani ya zo ya kawo shelar wani Yesu daban da wanda muka yi maku wa'azinsa. Ko kuma kun karbi wani ruhu daban da wanda muka karba. Ko kuma kun karbi wata bishara daban da wadda muka karba. Amincewar da kuka yi wa wadannan abubuwa ta isa!
\s5
\v 5 Don kuwa ina tsammanin ba a baya nake ba ga sauran wadanda ake kira manyan manzanni.
\v 6 To ko ma ba a ilimantar da ni ba akan yin jawabi, ban rasa horarwar ilimi ba. Ta kowace hanya kuma cikin abubuwa duka mun sanar da ku wannan.
\s5
\v 7 Na yi zunubi ne da na kaskantar da kai na domin a daukaka ku? Domin na yi maku wa'azin bisharar Allah kyauta.
\v 8 Na yi wa sauran Ikilisiyoyi kwace ta wurin karbar gudummuwa daga wurin su domin inyi maku hidima.
\v 9 Lokacin da ina tare da ku kuma na sami kai na cikin bukata, ban dora wa kowa nauyi ba. Domin 'yan'uwa da suka zo daga Makidoniya sun biya bukatuna. A cikin komai na kebe kaina daga zama nawaya a gare ku, kuma zan cigaba da yin haka.
\s5
\v 10 Kamar yadda gaskiyar Almasihu ke ciki na, ba zan yi shiru da wannan fahariya tawa ba a cikin dukan kasar Akaya.
\v 11 Don me? Saboda ba na kaunar ku? Allah ya sani.
\s5
\v 12 Amma abinda na ke yi, zan cigaba da yi. Zan yi haka ne domin in yanke zarafin wadanda ke son samun zarafi kamar mu akan abubuwan da suke fahariya da shi.
\v 13 Don irin wadannan mutane manzannin karya ne masu aikin yaudara. Suna badda kama kamar manzannin Almasihu.
\s5
\v 14 Wannan ba abin mamaki ba ne, domin shaidan ma yakan badda kama ya fito kamar mala'ikan haske.
\v 15 Ba wani babban abin mamaki ba ne idan bayin sa sun badda kamanninsu don a dauka bayin adalci ne su. Karshen su zai zama sakamakon abin da suka aikata.
\s5
\v 16 Ina kara fadi: Kada wani ya yi zaton ni wawa ne. Idan kun yi zaton hakan, to ku dauke ni kamar wawan don inyi fahariya kadan.
\v 17 Abinda nake fadi game da wannan gabagadi mai fahariya ba bisa ga amincewar Ubangiji ba ne, amma ina magana a matsayin wawa.
\v 18 Tun da mutane dayawa suna fahariya bisa ga jiki, ni ma zan yi fahariya.
\s5
\v 19 Gama kuna murnar tarayya da wawaye. Ku masu hikima ne!
\v 20 Kuma kuna hakuri da wanda zai bautar da ku, idan ya tauye ku, yana amfani da ku don ribar kansa, idan ya dauki kansa fiye da ku, ko ya mammare ku a fuska.
\v 21 Ina mai cewa mun kunyata da muka rasa gabagadin yi maku haka. Duk da haka idan wani zai yi fahariya-Ina magana kamar wawa-Ni ma zan yi fahariya.
\s5
\v 22 Su yahudawa ne? Ni ma haka. Su Isra'ilawa ne? Nima haka. Su zuriyar Ibrahim ne? Nima haka.
\v 23 Su bayin Almasihu ne? (Ina magana kamar ba ni cikin hankalina) na fi su ma. Na ma yi aiki tukuru fiye da su duka, shiga kurkuku fiye da kowa, a shan duka babu misali, a fuskantar haduran mutuwa da yawa.
\s5
\v 24 Daga hannun yahudawa sau biyar na sha bulala "Arba'in ba daya".
\v 25 Sau uku na sha dibga da sanduna. Sau daya aka jejjefe ni da duwatsu. Sau uku na yi hadari a jirgin ruwa. Na yi tsawon dare da yini guda a tsakiyar teku.
\v 26 Ina shan tafiye tafiye, cikin hadarin koguna, cikin hadarin 'yan fashi, cikin hadari daga mutane na, cikin hadari daga al'ummai, cikin hadarin birni, cikin hadarin jeji, cikin hadarin teku, cikin hadarin 'yan'uwan karya.
\s5
\v 27 Na sami kaina ina aiki tukuru cikin mawuyacin hali, cikin yin dare dayawa ba barci, cikin yunwa da kishin ruwa, cikin yawan azumi, cikin sanyi da tsiraici.
\v 28 Baya ga wadannan duka, akwai nauyi a kaina kullayaumin saboda damuwata akan Ikkilisiyoyi duka.
\v 29 Waye kumama, wanda ban zama kumama akan shi ba? Wanene aka sa yayi tuntube, kuma ban kuna ba?
\s5
\v 30 Idan zan yi fahariya, zan yi fahariya akan abinda ke nuna kasawata.
\v 31 Allah kuma Uba na Ubangijinmu Yesu, wanda ya isa yabo har abada, ya san ba karya nake yi ba!
\s5
\v 32 A Damasku, gwamnan da ke mulki karkashin sarki Aritas yasa aka yi tsaron birnin Damasku domin a kama ni.
\v 33 Amma ta taga cikin kwando aka ziraro ni bayan ganuwar birni, na kuwa kucce daga hannunsa.
\s5
\c 12
\p
\v 1 Dole ne in yi fahariya, ko dashike bata da ribar komai. Amma zan ci gaba da wahayoyi da ruyoyi daga Ubangiji.
\v 2 Na san wani mutum cikin Almasihu, wanda shekaru goma sha hudu da suka wuce-ko a cikin jiki ne ko ba a jiki ba, ban sani ba, Allah ya sani-an dauke shi zuwa sama ta uku.
\s5
\v 3 Kuma na san wannan mutumin-ko cikin jiki ko kuma ba cikin jiki ba, ban sani ba, Allah ya sani-
\v 4 an dauke shi zuwa Firdausi ya kuma ji madaukakan al'amura wadanda ba mai iya fadi.
\v 5 A madadin irin wannan mutumin zan yi fahariya. Amma a madadin kaina ba zan yi fahariya ba, sai dai game da kumamancina.
\s5
\v 6 Idan ina so inyi takama, ba zai zama wauta ba, domin gaskiya zan rika fada. Amma zan guje wa fahariya, domin kada wani ya dauke ni fiye da abinda ya gani ko ya ji daga gare ni.
\v 7 Zan kuma gujewa fahariya saboda irin wadannan gagaruman ruyoyi. Domin kada in cika da girman kai, an ba ni kaya cikin jikina, manzon shaidan ya wahalshe ni, domin kada in yi girman kai dayawa.
\s5
\v 8 Na roki Ubangiji har sau uku domin ya kawar mini da wannan.
\v 9 Amma ya ce mani, "Alherina isasshe yake a gare ka, domin ta wurin kumamanci karfi yake cika." Don haka zan gwammace takama a akan kasawata, domin ikon Almasihu ya zauna a ciki na.
\v 10 Sabili da haka a gamshe nake ta dalilin Almasihu, cikin kumamanci, ko raini, ko matsaloli, ko jarabobi, ko kuma nawaya. Don ko dayaushe na raunana, ina da karfi kuma.
\s5
\v 11 Na zama wawa! Amma ku ne kuka tilasta mani haka, ya kamata ku yabe ni, domin ban kasa ga wadan da ake kira manyan manzanni ba, ko da shike ni ba komai ba ne.
\v 12 Cikakkun alamun mazanni sun faru a tsakanin ku, da cikakken hakuri, alamu da abubuwan ban mamaki da manyan ayyuka.
\v 13 Ta yaya kuka zama da rashin muhimmanci akan sauran Ikkilisiyoyin, sai dai don ban zama matsala a gare ku ba? Ku gafarce ni a kan wannan laifin.
\s5
\v 14 Duba! A shirye nake domin in zo gare ku karo na uku. Ba zan so in zamar maku nawaya ba, domin ba kayanku nake so ba. Amma ku nake so. Domin ba 'ya'ya ne ya kamata su yi wa iyaye tanadi ba. Amma iyaye ne ya kamata su yi wa 'ya'ya tanadi.
\v 15 Zan yi murnar biyan bukatunku, ko ya kai ga in bada rai na. Idan ni na kaunace ku, sosai, sai ni za a kaunata kadan?
\s5
\v 16 Amma kamar yadda yake, ban nawaita maku ba. Amma, da shike ni mai dabara ne, Ni ne na kama ku da yaudara.
\v 17 Ko na cutar da ku ta wurin wadanda na turo maku?
\v 18 Rokar Titus na yi domin ya zo gare ku, sa'an nan na turo shi da wani dan'uwa. Ko da na turo Titus, ya cutar da ku ne, ba cikin hanya daya muka yi tafiya ba? Ba a sawu daya muka yi tafiya ba?
\s5
\v 19 Kuna tsammanin a dukan wannan lokaci muna kare kan mu a gaban ku ne? A gaban Allah, a cikin Almasihu muke fadin komai domin ku sami karfi.
\s5
\v 20 Ina tsoro domin idan na zo ba zan same ku yadda nake zato ba. Ina tsoro kuma ba za ku same ni kamar yadda ku ke zato ba. Ina tsoron cewa za a sami gardandami, kishi, barkewar fushi, buri na son kai, gulma, girman kai da yamutsi.
\v 21 Ina tsoron cewa bayan na dawo, Allahna zai iya kaskantar da ni a gaban ku. Ina tsoron cewa zan yi bakinciki domin mutane dayawa da suka yi zunubi kafin yanzu, wadanda kuma ba su tuba daga rashin tsarki da zina da fasikanci da ayyukan sha'awa da suka aikata ba.
\s5
\c 13
\p
\v 1 Wannan ne karo na uku da nake zuwa gare ku, "Ana tabbatar da kowanne zargi ta bakin shaidu biyu ko uku."
\v 2 Na riga na yi magana a baya da wadanda suka yi zunubi da kuma sauran a lokacin da ina tare da ku karo na biyu, kuma ina sake fadi: Idan na sake zuwa, ba zan raga masu ba.
\s5
\v 3 Ina fadi maku wannan ne domin kuna neman shaida ko Almasihu na magana ta bakina. Shi ba kasashshe bane zuwa gare ku. Maimakon haka, Shi mai iko ne a cikin ku.
\v 4 Domin an gicciye shi cikin kasawa, amma yana da rai ta ikon Allah. Don mu ma kasassu ne a cikin shi, amma za mu rayu tare da shi cikin ikon Allah dake cikinku.
\s5
\v 5 Ku auna kanku ku gani ko kuna cikin bangaskiya. Ku yi wa kanku gwaji. Ba ku lura da cewa Yesu Almasihu yana cikin ku ba? Yana cikin ku, sai dai in ba a amince da ku ba.
\v 6 Gama ina da gabagadin cewa za ku iske an amince da mu.
\s5
\v 7 Ina addu'a ga Allah cewa ba za a same ku da laifi ba. Ba wai ina rokon mu bayyana kamar mun ci gwadawar ba. Maimakon haka, ina addu'a ku yi abinda ke dai dai, ko dayake mun yi kamar mun fadi gwadawar.
\v 8 Domin bamu iya yin wani abu na tsayayya da gaskiya ba, sai dai mu yi domin gaskiya.
\s5
\v 9 Muna farin ciki idan mun kasa ku kuma kun yi karfi. Muna addu'a kuma domin ku kammalu.
\v 10 Na rubuta wadannan abubuwa yayinda ba ni tare da ku, saboda yayin da zan kasance da ku ba zan zamar maku mai fada ba. Ba na so inyi amfani da ikon da Ubangiji ya bani in tsattsaga ku, sai dai in gina ku.
\s5
\v 11 A karshe, 'yan'uwa, ku yi farinciki, ku yi aiki don sabuntuwa, ku karfafa, ku yarda da juna, ku zauna cikin salama. Kuma Allahn kauna da salama zai kasance tare da ku.
\v 12 Ku gai da juna da tsattsarkar sumba.
\s5
\v 13 Masu bi duka suna gaishe ku.
\v 14 Bari alherin Ubangiji Yesu Almasihu, da kaunar Allah, da zumuntar Ruhu Mai Tsarki su kasance tare da ku duka.