ha_ulb/47-1CO.usfm

833 lines
53 KiB
Plaintext

\id 1CO
\ide UTF-8
\h 1 Korintiyawa
\toc1 1 Korintiyawa
\toc2 1 Korintiyawa
\toc3 1co
\mt 1 Korintiyawa
\s5
\c 1
\p
\v 1 Bulus, kirayayye daga Almsihu Yesu don zama manzo ta wurin nufin Allah, da dan'uwanmu Sastanisu,
\v 2 zuwa ga Ikilisiyar Allah da ke korinti, zuwa ga wadanda aka kebe su cikin Almasihu Yesu, wadanda aka kira domin su zama al'umma maitsarki. Muna kuma rubuta wa dukan masu kira bisa sunan Ubangijinmu Yesu Almasihu a ko'ina, wato Ubangijinsu da Ubangijinmu kuma.
\v 3 Bari alheri da salama su zo gare ku daga Allah Ubanmu da Ubangiji Yesu Almasihu.
\s5
\v 4 Kodayaushe ina gode wa Allahna domin ku, saboda alherin Allah da Almasihu Yesu ya yi maku.
\v 5 Ya ba ku arziki ta kowace hanya, cikin dukkan magana da dukkan ilimi.
\v 6 Kamar yadda shaida game da Almasihu ta tabbata gaskiya a tsakaninku.
\s5
\v 7 Saboda haka baku rasa wata baiwa ta ruhaniya ba yayinda kuke marmarin jiran bayyanuwar Ubangijinmu Yesu Almasihu.
\v 8 Zai kuma karfafa ku zuwa karshe, saboda ku zama marasa aibi a ranar Ubangijinmu Yesu Almasihu.
\v 9 Allah mai aminci ne shi wanda ya kira ku zuwa zumunta ta Dansa, Yesu Almasihu Ubangijimu.
\s5
\v 10 Ina rokon ku, yan'uwa, cikin sunan Ubangijinmu Yesu Almasihu, ku yarda da juna, kada tsattsaguwa ta kasance tsakanin ku. Ina rokon ku ku zama da zuciya daya da kuma nufi daya.
\v 11 Gama mutanen gidan Kulowi sun kawo kara cewa akwai tsattsaguwa a cikin ku.
\s5
\v 12 Ina nufin: kowannen ku na cewa, "Ina bayan Bulus," ko " Ina bayan Afollos," ko "Ina bayan Kefas," ko "Ina bayan Almasihu."
\v 13 Almasihu a rarrabe yake? An gicciye Bulus domin ku? Ko an yi maku baftisma a cikin sunan Bulus?
\s5
\v 14 Na godewa Allah domin ban yi wa wanin ku baftisma ba, sai dai Kirisfus da Gayus.
\v 15 Na yi wannan saboda kada wani ya ce an yi maku baftisma a cikin sunana.
\v 16 (Na kuma yi wa iyalin gidan Sitifanas baftisma. Banda haka, ban sani ko na yi wa wani baftisma ba.)
\s5
\v 17 Gama Almasihu bai aiko ni domin yin baftisma ba, amma domin yin wa'azin bishara. Bai aiko ni domin in yi wa'azi da kalmomin hikimar mutum ba, saboda kada giciyen Almasihu ya rasa ikonsa.
\s5
\v 18 Gama wa'azin gicciye wauta ne ga wadanda su ke mutuwa. Amma cikin wadanda Allah ke ceto, ikon Allah ne.
\v 19 Gama a rubuce yake, "Zan watsar da hikimar masu hikima. Zan dode fahimtar masu basira."
\s5
\v 20 Ina mai hikima? Ina masani? Ina mai muhawara na duniyan nan? Allah bai juya hikimar duniya zuwa wauta ba?
\v 21 Tunda duniya cikin hikimarta bata san Allah ba, ya gamshi Allah ta wurin wautar wa'azi ya ceci masu bada gaskiya.
\s5
\v 22 Gama Yahudawa suna bidar al'ajibai, Helinawa kuma suna neman hikima.
\v 23 Amma muna wa'azin Almasihu gicciyayye, dutsen tuntube ga yahudawa da kuma wauta ga Helinawa.
\s5
\v 24 Amma ga wadanda Allah ya kira, Yahudawa da Helinawa, muna wa'azin Almasihu a matsayin iko da kuma hikimar Allah.
\v 25 Gama wautar Allah tafi mutane hikima, kuma rashin karfin Allah yafi mutane karfi.
\s5
\v 26 Dubi kiranku, yan'uwa. Ba dukkan ku ke da hikima a ma'aunin mutane ba. Ba dukkan ku ke da iko ba. Ba dukkan ku ke da haifuwa ta sarauta ba.
\v 27 Amma Allah ya zabi abubuwan da suke wofi na duniya domin ya kunyatar da masu hikima. Allah ya zabi abin da ke marar karfi a duniya domin ya kunyatar da abinda ke mai karfi.
\s5
\v 28 Allah ya zabi abinda ke marar daraja da kuma renanne a duniya. Ya ma zabi abubuwan da ake dauka ba komai ba, domin ya wofinta abubuwan da ake dauka masu daraja.
\v 29 Ya yi wannan ne domin kada wani ya sami dalilin fahariya a gabansa.
\s5
\v 30 Domin abinda Allah ya yi, yanzu kuna cikin Almasihu Yesu, wanda ya zamar mana hikima daga Allah. Ya zama adalcinmu, da tsarkinmu da fansarmu.
\v 31 A sakamakon haka, kamar yadda nassi ya ce, "Bari mai yin fahariya, ya yi fahariya cikin Ubangiji."
\s5
\c 2
\p
\v 1 Lokacin da na zo wurin ku, yan'uwa, ban zo da gwanintar magana ko hikima ba yayinda na yi shelar boyayyun bayanai game da Allah. \f + \ft Wasu 'yan mahimman da tsoffin kwafin Girkanci suna karantawa, \fqa a yayinda na bada shaida game da Allah \fqa* . \f*
\v 2 Domin na kudura a zuciyata kada in san komai lokacin da nake tare da ku, sai dai Yesu Almasihu, gicciyayye.
\s5
\v 3 Ina tare da ku cikin kasawa, da tsoro, da fargaba mai yawa.
\v 4 Kuma sakona da shelata basu tare da kalmomin hikima masu daukar hankali. Maimakon haka, sun zo da bayyanuwar Ruhu da iko,
\v 5 saboda kada bangaskiyarku ta zama cikin hikimar mutane, amma cikin ikon Allah.
\s5
\v 6 Yanzu muna maganar hikima ga wadanda suka ginu, amma ba hikima ta duniyan nan ba, ko ta masu mulkin wannan zamani, wadanda suke shudewa.
\v 7 Maimakon haka, muna maganar hikimar Allah ta boyayyar gaskiya, boyayyar hikima da Allah ya kaddara kafin zamanin daukakarmu.
\s5
\v 8 Babu wani mai mulki na zamanin nan da ya san wannan hikimar, domin inda sun gane ta a wancan lokacin, da basu gicciye Ubangijin daukaka ba.
\v 9 Amma kamar yadda yake a rubuce, "Abubuwan da babu idon da ya gani, babu kunnen da ya ji, babu zuciyar da ta yi tsammanin sa, abubuwan da Allah ya shirya wa wadanda suke kaunarsa.
\s5
\v 10 Wadannan ne abubuwan da Allah ya bayyana mana ta wurin Ruhu. Gama Ruhu yana bincika komai, har ma abubuwa masu zurfi na Allah.
\v 11 Gama wanene ya san tunanin mutum, sai dai ko ruhun mutumin da ke cikinsa? Haka ma, babu wanda ya san abubuwa masu zurfi na Allah sai dai Ruhun Allah.
\s5
\v 12 Ba mu karbi ruhu na duniya ba, amma Ruhun da ya zo daga wurin Allah, domin mu san abubuwan da aka bamu a sake daga wurin Allah.
\v 13 Muna maganar wadannan abubuwa da kalmomin da hikimar da mutum baza ta iya koyarwa ba, amma wadanda Ruhu ke koyar da mu. Ruhu yana fassara kalmomi na ruhaniya da hikima ta ruhaniya.
\s5
\v 14 Mutum marar ruhaniya ba ya karbar abubuwan da suke daga Ruhun Allah, gama wauta suke a gareshi. Ba zai iya sanin su ba domin Ruhu ne yake bayyana su.
\v 15 Shi wanda yake mai ruhaniya yana shari'anta dukan abubuwa, amma shi baya karkashin shari'ar sauran mutane.
\v 16 "Wa zai iya sanin zuciyar Ubangiji, da zai iya ba shi umarni?" Amma mu muna da lamiri irin na Almasihu.
\s5
\c 3
\p
\v 1 Amma ni, yan'uwa, ba zan iya magana da ku kamar mutane masu ruhaniya ba, amma kamar mutane masu jiki, kamar jarirai cikin Almasihu.
\v 2 Na shayar da ku da Madara ba da nama ba, don baku isa cin nama ba, kuma ko yanzu ma baku isa ba.
\s5
\v 3 Gama har yanzu ku masu jiki ne. Muddin akwai kishi da jayayya a tsakaninku, ashe, ku ba masu jiki ba ne, kuma kuna tafiya bisa magwajin mutane?
\v 4 Domin in wani ya ce, "Ina bayan Bulus," wani kuma ya ce, "Ina bayan Afollos," ashe, ba zaman mutuntaka kuke yi ba?
\v 5 To wanene Afollos? Wanene kuma Bulus? Bayi ne wadanda kuka bada gaskiya ta wurin su, kowannen su kuwa Allah ya bashi ayyuka.
\s5
\v 6 Ni nayi shuka, Afolos yayi banruwa, amma Allah ne ya sa girma.
\v 7 Don haka, da mai shukar da mai banruwan, ba komi bane. Amma Allah ne mai sa girman.
\s5
\v 8 Da mai shukar, da mai banruwan, duk daya suke, kuma kowannen su zai sami nasa lada, gwargwadon aikinsa.
\v 9 Gama mu abokan aiki ne na Allah. Ku gonar Allah ne, ginin Allah kuma.
\s5
\v 10 Bisa ga alherin Allah da aka bani a matsayin gwanin magini, na kafa harsashi, wani kuma yana dora gini a kai. Sai dai kowane mutum, ya lura da yadda yake dora ginin.
\v 11 Gama ba wanda ke iya kafa wani harsashin daban da wanda aka rigaya aka kafa, wato, Yesu Almasihu.
\s5
\v 12 Yanzu fa in wani ya dora gini a kan harashin da zinariya, ko azurfa, ko duwatsu masu daraja, ko itace, ko ciyawa, ko tattaka,
\v 13 aikinsa zai bayyanu, domin ranar nan zata tona shi. Gama za a bayyana shi cikin wuta. Wutar kuwa zata gwada ingancin aikin da kowa ya yi.
\s5
\v 14 Duk wanda aikinsa ya tsaya, zai karbi lada;
\v 15 amma duk wanda aikinsa ya kone, zai sha Asara, amma shi kansa zai tsira, sai dai kamar ta tsakiyar wuta.
\s5
\v 16 Ashe, baku san ku haikalin Allah ne ba, Ruhun Allah kuma yana zaune a cikin ku?
\v 17 Idan wani ya lalata haikalin Allah, Allah zai lalata shi. Gama haikalin Allah mai tsarki ne, kuma haka ku ke.
\s5
\v 18 Kada kowa ya rudi kansa. Idan wani a cikin ku na ganin shi mai hikima ne a wannan zamani, bari ya zama" wawa" domin ya zama mai hikima.
\v 19 Gama hikimar duniyar nan wauta ce a gun Allah. Gama a rubuce yake, "Yakan kama masu hikima a cin makircin su."
\v 20 Har wa yau, "Ubangiji ya san tunanin masu hikima banza ne."
\s5
\v 21 haka ba sauran fariya akan mutane! Domin kuwa kome naku ne,
\v 22 Ko Bulus, ko Afollos, ko kefas, ko duniya, ko rai, ko mutuwa, ko abubuwa na yanzu, ko abubuwa masu zuwa. Duka naku ne,
\v 23 Ku kuwa na Almasihu ne, Almasihu kuma na Allah ne.
\s5
\c 4
\p
\v 1 Ga yadda za ku dauke mu, kamar bayin Almasihu da kuma masu rikon asiran Allah.
\v 2 Hade da wannan, ana bukatar wakilai su zama amintattu.
\s5
\v 3 Amma a gare ni, karamin abu ne ku yi mani shari'a, ko a wata kotu irin ta mutane. Gama bani yi wa kaina shari'a.
\v 4 Ban sani ko akwai wani zargi a kaina ba, amma wannan bai nuna cewa bani da laifi ba. Ubangiji ne mai yi mani shari'a.
\s5
\v 5 Sabili da haka, kada ku yanke shari'a kafin lokaci, kafin Ubangiji ya dawo. Zai bayyana dukkan boyayyun ayyuka na duhu, ya kuma tona nufe-nufen zuciya. San nan kowa zai samu yabonsa daga wurin Allah.
\s5
\v 6 Yan'uwa, ina dora wadannan ka'idoji a kaina da Afollos domin ku, yadda ta wurin mu za ku koyi ma'anar maganar nan cewa, "kada ku zarce abin da aka rubuta." Ya zama haka domin kada waninku ya kumbura yana nuna fifiko ga wani akan wani.
\v 7 Gama wa yaga bambanci tsakanin ku da wasu? Me kuke da shi da ba kyauta kuka karba ba? Idan kyauta kuka karba, don me kuke fahariya kamar ba haka ba ne?
\s5
\v 8 Kun rigaya kun sami dukkan abubuwan da kuke bukata! Kun rigaya kun zama mawadata! Kun rigaya kun fara mulki- kuma ba tare da mu ba! Hakika, marmarina shine ku yi mulki, domin mu yi mulki tare da ku.
\v 9 A tunanina, mu manzanni, Allah ya sa mu a jerin karshe kamar mutanen da aka zartar wa hukuncin mutuwa. Mun zama abin kallo ga duniya, ga mala'iku, ga mutane kuma.
\s5
\v 10 Mun zama marasa wayo sabili da Almasihu, amma ku masu hikima ne a cikin Almasihu. Mu raunana ne, amma ku masu karfi ne. Ana ganin mu marasa daraja, ku kuwa masu daraja.
\v 11 Har zuwa wannan sa'a, muna masu yunwa da kishi, marasa tufafi masu kyau, mun sha kazamin duka, kuma mun zama marasa gidaje.
\s5
\v 12 Mun yi fama sosai, muna aiki da hanuwanmu. Sa'adda an aibata mu, muna sa albarka. Sa'adda an tsananta mana, muna jurewa.
\v 13 Sa'adda an zage mu, muna magana da nasiha. Mun zama, kuma har yanzu an dauke mu a matsayin kayan shara na duniya da abubuwa mafi kazamta duka.
\s5
\v 14 Ban rubuta wadannan abubuwa domin in kunyata ku ba, amma domin in yi maku gyara kamar kaunatattun yayana.
\v 15 Ko da kuna da masu riko dubu goma a cikin Almasihu, ba ku da ubanni da yawa. Gama ni na zama ubanku cikin Almasihu Yesu ta wurin bishara.
\v 16 Don haka, ina kira gare ku da ku zama masu koyi da ni.
\s5
\v 17 Shiyasa na aiko Timoti wurin ku, kaunatacce da amintaccen dana cikin Ubangiji. Zai tunashe ku hanyoyina cikin Almasihu, kamar yadda nake koyar da su ko'ina da kowace Ikilisiya.
\v 18 Amma yanzu, wadansun ku sun zama masu fahariya, suna yin kamar ba zan zo wurinku ba.
\s5
\v 19 Amma zan zo gare ku ba da dadewa ba, idan Ubangiji ya nufa. Sannan zan san fiye da maganar masu fahariya, amma kuma zan ga ikonsu.
\v 20 Gama Mulkin Allah ba magana kadai ya kunsa ba, amma ya kunshi iko.
\v 21 Me kuke so? In zo wurin ku da sanda ne ko kuwa da kauna da ruhun nasiha?
\s5
\c 5
\p
\v 1 Mun ji cewa akwai lalata mai kazanta a cikin ku, irin lalatar ba ba a yarda da ita ba ko a cikin al'ummai. Labarin da na samu shine, wani daga cikin ku yana kwana da matar mahaifinsa.
\v 2 Kuma kuna fahariya sosai! Ba bakinciki ya kamata ku yi ba? Shi wanda ya yi haka, dole a fitar da shi daga cikin ku.
\s5
\v 3 Gama Kodashike ba ni tare da ku cikin jiki, amma ina tare daku a ruhu, na rigaya na hukunta wanda yayi wannan, tamkar ina wurin.
\v 4 Lokacin da ku ka taru a cikin sunan Ubangijinmu Yesu, ruhuna yana nan tare da ku cikin ikon Ubangiji Yesu, na rigaya na hukunta wannan mutum.
\v 5 Na yi haka ne domin in mika wannan mutum ga Shaidan domin a hallaka jikin, don ruhunsa ya tsira a ranar Ubangiji.
\s5
\v 6 Fahariyarku bata yi kyau ba. Ko baku sani ba yisti dan kadan ya kan bata dukan dunkule?
\v 7 Ku tsarkake kan ku daga tsohon yisti domin ku zama sabon dunkule, wato gurasar da ba ta da yisti. Gama an yi hadayar Almsihu, dan ragonmu na idi.
\v 8 Don haka, bari mu yi idinmu ba da tsohon yisti ba, wato yisti irin na rashin tabi'a da mugunta. Maimakon haka, bari muyi bukin idi da gurasa marar yisti ta aminci da gaskiya.
\s5
\v 9 Na rubuta maku a cikin wasikata cewa kada ku yi hudda da fasikan mutane.
\v 10 Ba ina nufin fasikan mutane na wannan duniya ba, ko masu zari, ko 'yan'damfara, ko masu bautar gumaka, tunda kafin ku rabu da su sai kun bar wannan duniya.
\s5
\v 11 Amma yanzu ina rubuta maku cewa kada ku yi hudda da duk wanda ake kira dan'uwa amma yana zama cikin fasikanci, ko zari, ko bautar gumaka, ko in shi mai ashar ne, ko mashayi, ko dan'damfara. Kada ko abinci ku ci da irin wannan mutum.
\v 12 Domin ta yaya zan iya shar'anta wadanda ba 'yan Ikklisiya ba? Maimakon haka, ba ku ne zaku shar'anta wadanda ke cikin ikilisiya ba?
\v 13 Amma Allah ke shar'anta wadanda ke waje. "Ku fitar da mugun mutumin daga cikin ku."
\s5
\c 6
\p
\v 1 Idan wani a cikin ku yana jayayya da wani, to sai ya tafi kotu gaban alkali marar bada gaskiya, a maimakon gaban masu bi?
\v 2 Ko ba ku sani ba, masubi ne za su yiwa duniya shari'a? Kuma idan ku za ku yi wa duniya shari'a, sai ku kasa sasanta al'amura marasa mahimmanci?
\v 3 Baku sani ba mu za mu yiwa mala'iku shari'a? Balle shari'ar al'amuran wannan rai?
\s5
\v 4 Idan kuna shar'anta al'amuran yau da kullum, don me ku ke kai irin wadannan matsaloli gaban wadanda ba 'yan ikilisiya ba?
\v 5 Na fadi wannan domin ku kunyata. Babu wani mai hikima a cikin ku ko daya da zai iya sasanta gardama a tsakanin 'yan'uwa?
\v 6 Amma kamar yadda yake, mai bi ya na kai karar mai bi a kotu, kuma a gaban mai shari'a wanda ba mai bi ba!
\s5
\v 7 Kasancewar rashin jituwa a tsakanin Kirista na nuna cewa kun rigaya kun gaza. Don me ba za ka shanye laifi ba? Don me ba za ka yarda a kware ka ba?
\v 8 Amma kun yi wa wadansu laifi kun kuma cutar su, su kuwa 'yan'uwanku ne!
\s5
\v 9 Ba ku sani ba marasa adalci ba za su gaji Mulkin Allah ba? Kada ku gaskata karya. Da fasikai, da masu bautar gumaka, da mazinata, da karuwai maza, da masu ludu,
\v 10 da barayi, da masu zari, da mashaya, da masu zage-zage, da 'yan damfara - ba waninsu da zai gaji Mulkin Allah.
\v 11 Kuma da haka wadansu a cikinku suke, amma an tsarkake ku, an mika ku ga Allah, an maida tsayuwar ku dai-dai a gaban Allah a cikin sunan Ubangji Yesu Almasihu, kuma ta wurin Ruhun Allahnmu.
\s5
\v 12 Dukkan abu halal ne a gare ni", amma ba kowanne abu ne mai amfani ba. "Dukan abu halal ne a gare ni," amma ba zan yarda wani abu ya mallake ni ba.
\v 13 "Abinci don ciki ne, kuma ciki don abinci ne", amma Allah za ya kawar da su duka. Ba a yi jiki saboda fasikanci ba. Maimakon haka, jiki don Ubangiji ne, kuma Ubangiji zai yi wa jiki tanaji.
\s5
\v 14 Allah ya tada Ubangiji, kuma za ya tashe mu ta wurin ikonsa.
\v 15 Ba ku sani ba jikunanku gabobi ne na Almasihu? Na dauki gabobin Almasihu in hada su da karuwa? Allah ya sawwake!
\s5
\v 16 Ko baku sani ba dukan wanda yake hade da karuwa, ya zama jiki daya da ita kenan?
\v 17 Kamar yadda Littafi ya fadi, "Su biyun za su zama nama daya." Amma wanda yake hade da Ubangiji ya zama ruhu daya da shi kenan.
\s5
\v 18 Ku gujewa fasikanci! Kowane zunubi mutum yake aikatawa a waje da jikinsa yake, amma mutum mai fasikanci yana zunubi gaba da jikinsa.
\s5
\v 19 Ba ku sani ba jikinku haikali ne na Ruhu Mai-tsarki, wanda yake zaune a cikinku, wanda ku ka samu daga wurin Allah? Ba ku sani ba cewa ku ba na kanku ba ne?
\v 20 An saye ku da tsada. Don haka, ku daukaka Allah da jikin ku.
\s5
\c 7
\p
\v 1 Game da abubuwan da kuka rubuto: "Yayi kyau ga mutum kada ya taba mace."
\v 2 Amma Saboda jarabobi na ayyukan fasikanci masu yawa, ya kamata kowane mutum ya kasance da matarsa, kowace mace kuma ta kasance da mijinta.
\s5
\v 3 Kowanne maigidanci ya ba matarsa hakin ta, kuma kowace mace ta ba maigidan ta hakinsa na saduwa da juna.
\v 4 Matan ba ta da iko akan jikin ta amma maigidan ne. Haka ma, maigidan bashi da iko akan jikinsa amma matar ce.
\s5
\v 5 Kada ku hana wa junanku saduwa, sai dai da yardar junanku domin wani dan lokaci. Kuyi haka domin ku bada kanku ga addu'a. Daganan sai ku sake saduwa, domin kada Shaidan ya jarabce ku saboda rashin kamun kanku.
\v 6 Amma ina fada maku wadannan abubuwa ne a matsayin nuni, ba a matsayin umurni ba.
\v 7 Na so da kowa da kowa kamar ni yake. Amma kowa na da baiwarsa daga wurin Allah. Wani na da irin wannan baiwar, wani kuma waccan.
\s5
\v 8 Ga marasa aure da gwamraye, Ina cewa, yana da kyau a garesu su zauna ba aure, kamar yadda nike.
\v 9 Amma idan baza su iya kame kansu ba, ya kamata su yi aure. Gama yafi masu kyau su yi aure da su kuna da sha'awa.
\s5
\v 10 Ga masu aure kwa, ina bada wannan umarni- ba ni ba, amma Ubangiji: "Kada mace ta rabu da mijinta."
\v 11 Amma idan har ta rabu da mijinta, sai ta zauna ba aure ko kuma ta shirya da shi. Haka kuma " Kada miji ya saki matarsa."
\s5
\v 12 Amma ga sauran ina cewa-Ni, ba Ubangiji ba-idan wani dan'uwa yana da mata wadda ba mai bi ba, kuma idan ta yarda ta zauna da shi, to kada ya sake ta.
\v 13 Idan kuwa mace tana da miji marar bi, idan ya yarda ya zauna tare da ita, to kada ta kashe aure da shi.
\v 14 Gama miji marar bada gaskiya ya zama kebabbe saboda matarsa, sannan mata marar bada gaskiya ta zama kebbiya saboda mijinta mai bi. In ba haka ba 'ya'yanku za su zama marasa tsarki, amma a zahiri su kebabbu ne.
\s5
\v 15 Amma idan abokin aure marar bi ya fita, a bar shi ya tafi. A irin wannan hali, dan'uwa ko 'yar'uwa ba a daure suke ga alkawarinsu ba. Allah ya kira mu da mu zauna cikin salama.
\v 16 Yaya kika sani, ke mace, ko za ki ceci mijinki? ko yaya ka sani, kai miji, ko za ka ceci matarka?
\s5
\v 17 Bari dai kowa ya yi rayuwar da Ubangiji ya aiyana masa, kamar yadda Allah ya kirawo shi. Wannan ce ka'idata a dukkan ikilisiyu.
\v 18 Mutum na da kaciya sa'adda aka kira shi ga bada gaskiya? Kada yayi kokarin bayyana kamar marar kaciya. Mutum ba shi da kaciya sa'adda aka kira ga bangaskiya? To kada ya bidi kaciya.
\v 19 Gama kaciya ko rashin kaciya ba shine mahimmin abu ba. Mahimmin abu shine biyayya da dokokin Allah.
\s5
\v 20 Kowa ya tsaya cikin kiran da yake lokacin da Allah ya kira shi ga bada gaskiya.
\v 21 Kai bawa ne lokacin da Allah ya kirawo ka? Kada ka damu da haka. Amma idan kana da zarafin samun 'yanci, ka yi haka.
\v 22 Domin wanda Ubangiji ya kira shi lokacin da yake bawa, shi 'yantacce ne na Ubangiji. Hakanan kuma, wanda shike 'yantacce lokacin da aka kira shi ga bada gaskiya, Bawan Almasihu ne.
\v 23 An saye ku da tsada, donhaka kada ku zama bayin mutane.
\v 24 Yan'uwa, a kowace irin rayuwa kowannenmu ke ciki lokacin da aka kira mu ga bada gaskiya, bari mu tsaya a haka.
\s5
\v 25 Game da wadanda basu taba aure ba, ba ni da wani umarni daga wurin Ubangiji. Amma ina bada ra'ayina kamar mutum wanda, ta wurin jinkan Allah, yake yardajje.
\v 26 Don haka, Ina ganin saboda yamutsin dake tafe ba da jimawa ba, ya yi kyau mutum ya zauna yadda yake.
\s5
\v 27 Kana daure da mace? Kada ka nemi 'yanci daga gare ta. Baka daure da mace? Kada ka nemi auren mace.
\v 28 Amma idan ka yi aure, ba ka yi zunubi ba. Kuma idan mace marar aure ta yi aure, bata yi zunubi ba. Saidai su wadanda suka yi aure za sha wahalhalu iri-iri a yayinda suke raye, kuma ina so in raba ku da su.
\s5
\v 29 Amma wannan nike fadi ya'nuwa: lokaci ya kure. Daga yanzu, bari wadanda suke da mata suyi rayuwa kamar basu da su.
\v 30 Masu kuka su zama kamar marasa kuka, masu farinciki kamar marasa farinciki, masu sayen abubuwa kamar marasa komai.
\v 31 Wadanda suke harka da duniya kamar ba su harka da ita, domin ka'idar duniyan nan tana kawowa ga karshe.
\s5
\v 32 Ina so ku kubuta daga damuwa mai yawa. Mutum marar aure yana tunani akan al'amuran Ubangiji, yadda zai gamshe shi.
\v 33 Amma mai aure yana tunani akan al'amuran duniya, yadda za ya gamshi matarsa,
\v 34 hankalinsa ya rabu. Mace marar aure ko budurwa tana tunanin al'amuran Ubangiji, yadda za ta kebe kanta a jiki da ruhu. Amma mace mai aure tana tunanin al'amuran duniya, yadda za ta gamshi mijinta.
\s5
\v 35 Ina fadar wannan domin amfaninku ne, ba domin in takura ku ba. Na fadi wannan domin abinda ke daidai, yadda zaku bi Ubangiji ba tare da hankalinku ya rabu ba.
\s5
\v 36 Amma idan wani yana tunani da cewa baya yin abinda ya dace ga budurwarsa- idan ta wuce shekarun aure, kuma hakan ya zama dole- sai yayi abinda yake so. Ba zunubi yake yi ba. Sai suyi aure.
\v 37 Amma idan ya tsaya da karfi a zuciyarsa, idan baya shan wani matsi kuma yana iya kame kansa, har ya kudurta a zuciyarsa yayi haka, wato ya kiyaye budurwarsa da yake tashi, to hakan ya yi daidai.
\v 38 Don haka, shi wanda ya auri budurwarsa yayi daidai, sannan shi wanda ya zabi yaki yin aure yafi yin daidai.
\s5
\v 39 Mace tana a daure ga mijinta a duk tsawon rayuwarsa. Amma idan mijin ya mutu, tana da 'yanci ta auri duk wanda take so ta aura, amma a cikin Ubangiji.
\v 40 Amma a ganina, za ta fi farinciki idan za ta zauna yadda take. Kuma ina tunanin ni ma ina da Ruhun Allah.
\s5
\c 8
\p
\v 1 Game da abinci da ake yiwa gumakai hadaya: Mun sani cewa, "Dukanmu muna da ilimi." Ilimi ya kan kawo takama, amma kauna tana ginawa.
\v 2 Idan wani yana tunanin ya san wani abu, wannan mutumin bai rigaya ya san abinda ya kamata ya sani ba.
\v 3 Amma idan wani yana kaunar Allah, to ya san da wannan mutum.
\s5
\v 4 Game da abincin da aka yiwa gumakai hadaya: Mun san cewa, "Gunki a duniyan nan ba wani abu bane," kuma cewa" Babu wani Allah sai guda daya."
\v 5 To wata kila ma a ce wadanda ake kira alloli sun kasance, ko a cikin sama ko duniya, kamar yadda akwai wadanda ake ce dasu "alloli dabam dabam a duniya ko a sama," kamar yadda akwai "alloli da iyayengiji" da yawa.
\v 6 "Amma a wurin mu, Allah daya ne, Uban dukan duniya, daga wurinsa aka halita dukan abu, domin sa muke rayuwa, Ubangiji Yesu Almasihu daya, wanda ta wurin sa kome ya kasance, mu kuma daga wurinsa muke."
\s5
\v 7 Amma ba kowa ke da wannan ilimi ba. Shi ya sa tun da, wadan su na bauta wa gunki, kuma suna cin wannan abincin kamar abin da aka mika wa gunki. Lamirin su ya kazantu sabo da yana da rauni.
\s5
\v 8 Amma ba abinci ke bamu tagomashi a wurin Allah ba. Ko mun ci, bamu kara karbuwan mu ba, ko ba mu ci ba, ba mu rage karbuwan mu ba.
\v 9 Amma, ka yi hatara kada 'yancin ka ya zama sanadiyar tuntuben wani mai rarraunar bangaskiya.
\v 10 Anar misali, idan wani mai rarraunar lamiri ya hango ka mai ilimi, kana cin abincin da aka mika wa gunki, ai ba ka bashi kwarin gwiwa kenan yaci abincin da aka mika wa gunki ba?
\s5
\v 11 Sabili da ganewar ka akan yanayin gumaka, dan'uwa rarrauna wanda Yesu ya mutu domin sa ya hallaka.
\v 12 Saboda haka, idan ka saba wa 'yan'uwa masu raunin a lamiri, ka yi zunubi a gaban Almasihu.
\v 13 Idan abinci zai sa dan'uwa na yayi tuntube, zan huta cin nama, domin kada in jawo wa 'yan'uwana faduwa.
\s5
\c 9
\p
\v 1 Ni ba yantacce bane? Ni ba Manzo ba ne? Ban ga Ubangijinmu Yesu ba? ba ku ne aikin hannuna cikin Ubangiji ba?
\v 2 Idan ni ba Manzo ba ne ga wadansu, hakika ni Manzo ne a gare ku. Ai kune shedar manzanci na cikin Ubangiji.
\s5
\v 3 Ga kariya ta zuwa masu zargi na,
\v 4 Ba mu da 'yanci mu ci mu sha?
\v 5 Ba mu da 'yanci mu dauki mace mai bada gaskiya kamar sauran manzanni da Kefas da 'yan'uwan Ubangiji?
\v 6 ko ni da Barnabas ne kawai muka cancanci aiki?
\s5
\v 7 Wake aikin soja daga aljihunsa? Wake shuka gonar inabi baya ci daga 'ya'yan ta ba? Ko kuwa wake kiwon tumaki ba ya shan madarasu?
\v 8 Ina wannan zance da ikon mutum ne? Doka bata fadi haka ba?
\s5
\v 9 Gama a rubuce yake a attaura ta Musa cewa, Takarkari mai tattake hatsi kada a sa masa takunkumi. Amma shanu ne Ubangiji ke zance a kai?
\v 10 Ba don mu yake magana ba? An rubuta domin mu ne. Domin wanda yake noma, yayi cikin bege. mai tattake hatsi kuma yayi da begen samu.
\v 11 Idan mun yi shuka ta ruhaniya a rayuwarku, mai wuya ne mu girbi kayan ku na jiki?
\s5
\v 12 Idan wadansu sun mori wannan 'yanci a gurin ku, ba mu fi su cancanta ba? duk da haka bamu yi amfani da wannan 'yancin ba, maimakon haka, mun yi jimriya da duk abin da zaya hana bisharar Yesu Almasihu.
\v 13 Baku sani ba masu bauta a haikali suna samun abincinsu ne daga haikalin? Baku sani ba masu bauta a bagadi, suna da rabo daga abin da ake kawowa kan bagadin?
\v 14 Haka kuma Ubangiji ya umarta masu aikin bishara zasu ci abincinsu ta hanyar bishara.
\s5
\v 15 Amma ban yi amfani da wannan 'yanci ba, ba kuma ina rubuta maku domin ayi mani wani abu bane, na gwanmace in mutu maimakon wani ya hana ni wannan fahariya.
\v 16 Ko nayi shelar bishara, ba ni da dalilin fahariya domin ya zama dole in yi. Kaito na idan ban yi shelar bishara ba
\s5
\v 17 Idan na yi hidimar nan da yardar zuciyata, ina da sakamako, idan kuma ba da yaddar zuciyata ba, harwa yau akwai nauwaya akai na.
\v 18 To menene sakamako na? shi ne in yi shelar bishara kyauta, da haka ba zan yi amfani the 'yanci na cikin bishara ba
\s5
\v 19 Ko da shike ni 'yantacce ne ga duka, amma na mai da kaina bawan kowa domin in ribato masu yawa,
\v 20 Ga yahudawa, na zama bayahude, domin in ribato yahudawa, ga wadanda ke karkashin shari'a, na maishe kaina kamarsu, domin in ribato wadanda ke karkashinta. Na aikata wannan ko da shike bana karkashin shari'a
\s5
\v 21 Ga wadanda basu karkashin shari'a, na maishe kaina kamar su. Ko da shike ban rabu da shari'ar Allah ba. Amma ina karkashin dokar Almasihu. Na yi haka ne domin in ribato wadanda ba sa karkashin shari'a.
\v 22 Ga marasa karfi, na maishe kaina kamar marar karfi, domin in ribato raunana. Na mai da kaina dukan abu ga dukan mutane domin in sami zarafin da zan ribato wadansu zuwa ceto.
\v 23 Ina dukan abu sabili da bishara, domin kuma in sami albarkar da ke cikinta
\s5
\v 24 Baku sani ba mutane da dama suna shiga tsere amma daya neke karbar sakamakon, saboda haka ku yi tsere domin ku karbi sakamako.
\v 25 Dan wasa yana motsa jiki da kame kansa. Yana yi saboda ya karbi wannan sakamako mai lalacewa, amma muna tsere domin mu karbi sakamako marar lalacewa.
\v 26 Saboda haka ba na tsere ko fada haka nan kamar mai bugun iska.
\v 27 Amma ina matse jiki na in maishe shi bawa, kada bayan na yi wa wadansu wa'azi ni kuma a karshe a fitar da ni.
\s5
\c 10
\p
\v 1 Ina son ku sani, 'yan'uwa, cewa ubaninmu duka suna karkashin gajimarai kuma sun bi ta cikin teku.
\v 2 Dukansu an yi masu baftisma cikin gajimarai da kuma teku,
\v 3 kuma dukansu sun ci abincin ruhaniya iri daya.
\v 4 Dukansu sun sha abin sha na ruhaniya iri daya. Gama sun sha daga wani dutsen ruhaniya da ya bisu, kuma wannan dutsen Almasihu ne.
\s5
\v 5 Amma Ubangiji bai ji dadin yawancinsu ba, saboda haka gawawakin su suka bazu a jeji.
\v 6 Wadan nan al'amura, an rubuta mana su domin muyi koyi da su, kada mu yi sha'awar miyagun ayyuka kamar yadda suka yi.
\s5
\v 7 Kada ku zama masu bautar gumaka kamar yadda wadansun su suka yi. Wannan kamar yadda aka rubuta ne, "Mutanen sukan zauna su ci su sha kuma su tashi suyi wasa."
\v 8 Kada mu shiga zina da faskanci kamar yadda yawancin su suka yi, a rana guda mutane dubu ashirin da uku suka mutu.
\s5
\v 9 Kada mu gwada Almasihu kamar yadda yawancinsu suka yi, macizai suka yi ta kashe su.
\v 10 kada kuma ku zama masu gunaguni kamar yadda suka yi, suka yi ta mutuwa a hannun malaikan mutuwa.
\s5
\v 11 Wadannan abubuwa sun faru dasu ne a matsayin misalai a garemu. An rubuta su domin gargadinmu - mu wadanda karshen zamanai yazo kanmu.
\v 12 Saboda haka, bari duk wanda yake tunanin shi tsayyaye ne, to yayi hattara kada ya fadi.
\v 13 Babu gwajin da ya same ku wanda ba a saba da shi ba cikin dukan mutane. A maimako, Allah mai aminci ne. Da ba zaya bari ku jarabtu ba fiye da iyawarku. Tare da gwajin zai tanadar da hanyar fita, domin ku iya jurewa.
\s5
\v 14 Saboda haka ya kaunatattu na, ku guji bautar gumaka.
\v 15 Ina magana da ku kamar masu zurfin tunani, domin ku auna abin da ni ke fadi.
\v 16 Kokon albarka da muke sa wa albarka, ba tarayya bane cikin jinin Almasihu? Gurasa da muke karyawa ba tarayya bane cikin jikin Almasihu?
\v 17 Domin akwai gurasa guda, mu da muke dayawa jiki daya ne. Dukanmu munci daga gurasa daya ne.
\s5
\v 18 Dubi mutanen Isra'ila: ba wadanda ke cin hadayu ke da rabo a bagadi ba?
\v 19 Me nake cewa? gunki wani abu ne? Ko kuma abincin da aka mika wa gunki hadaya wani abu ne?
\s5
\v 20 Amma ina magana game da abubuwan da al'ummai suke hadaya, suna wa aljannu ne hadaya ba Allah ba. Ba na son kuyi tarayya da al'janu!
\v 21 Ba zaku sha daga kokon Ubangiji ku kuma sha na Al'janu ba, ba za kuyi zumunta a teburin Ubangiji ku yi a na Al'janu ba.
\v 22 Ko muna so mu sa Ubangiji kishi ne? Mun fi shi karfi ne?
\s5
\v 23 "Komai dai dai ne," amma ba komai ke da amfani ba, "Komai dai dai ne," amma ba komai ke gina mutane ba.
\v 24 Kada wani ya nemi abinda zaya amfane shi. A maimako, kowa ya nemi abinda zaya amfani makwabcinsa.
\s5
\v 25 Kana iya cin duk abin da ake sayarwa a kasuwa, ba tare da tamboyoyin lamiri ba.
\v 26 Gama "duniya da duk abin da ke cikin ta na Ubangiji ne."
\v 27 Idan marar bangaskiya ya gayyace ka cin abinci, kana kuma da niyyar zuwa, ka je ka ci duk abinda aka kawo maka, ba tare da tamboyoyin lamiri ba.
\s5
\v 28 Amma idan wani ya ce maka, "Wannan abinci an yi wa gumaka hadaya da shi ne" To kada ka ci. Wannan za ka yi ne saboda wanda ya shaida maka, da kuma lamiri (gama duniya da dukan abinda ke cikin ta na Ubangiji ne).
\v 29 Ba ina nufin lamirin ka ba, amma lamirin wanda ya fada maka. Don me za a hukunta 'yanci na domin lamirin wani?
\v 30 Idan na ci abincin tare da bada godiya, don mi za a zage ni don abin da na bada godiya a kansa?
\s5
\v 31 Saboda haka, ko kana ci ko kana shi, ka yi komai domin daukakar Allah.
\v 32 Kada ka zama sanadiyyar tuntube, ga Yahudawa, ko Helenawa, ko ikilisiyar Allah.
\v 33 Na yi kokari in farantawa dukan mutane rai cikin dukan abubuwa. Ba riba nake nema wa kaina ba, amma domin kowa. Na yi wannan ne domin su sami ceto.
\s5
\c 11
\p
\v 1 Ku yi koyi da ni, kamar yadda nake koyi da Almasihu.
\v 2 Yanzu ina yaba maku ne, don kuna tunawa da ni cikin abu duka. Ina kuma yaba maku wajen bin al'adun da na ba ku daidai yadda na ba ku.
\v 3 Amma fa ina son ku fahimta da cewa, shugaban kowane mutum Almasihu ne, shugaban kowace mace mutumin ne, shugaban Almasihu Allah ne.
\v 4 Kuma duk mutumin da ya yi addu'a ko annabci kansa a rufe, ya wulakanta shugabansa.
\s5
\v 5 Amma duk macen da ta yi addu'a ko annabci kanta a bude, ta wulakanta shugabanta. Gama yayi dai dai da idan tayi aski.
\v 6 Gama idan mace ba zata rufe kanta ba, to ta yanke gashinta ya zama gajere. Idan abin kunya ne mace ta yanke gashinta ko ta aske kanta, bari ta rufe kanta.
\s5
\v 7 Bai kamata na miji ya rufe kansa ba, tun da yake shi siffa ne da daukakar Allah. Amma mace daukakar namiji ce.
\v 8 Don kuwa namiji ba daga jikin mace yake ba. A maimako, matar daga jikin namiji take.
\s5
\v 9 Ba a kuma halicci namiji don mace ba. A maimako, an halicci mace don namiji.
\v 10 Shi ya sa mace za ta kasance da alamar iko a kanta, saboda mala'iku.
\s5
\v 11 Duk da haka, a cikin Ubangiji, mace ba a rabe take da namiji ba, haka kuma namiji ba a rabe yake da mace ba.
\v 12 Kamar yadda mace take daga namiji, haka ma namiji kuma haihuwar mace ne. Amma dukkan abubuwa daga Allah suke.
\s5
\v 13 Ku hukunta da kanku: Daidai ne mace ta yi addu'a ga Allah kanta a bude?
\v 14 Ashe, ko dabi'a bata nuna maku cewa abin kunya ne namiji, ya kasance da dogon gashi ba?
\v 15 Ba dabi'a ta koya maku cewa idan mace tana da dogon gashi, daukakar ta ne ba? Gama domin rufewa aka yi mata baiwar gashin.
\v 16 To idan wani yana da niyyaryin gardama game da wannan, mu dai bamu da wata al'adar, ikilisiyoyin Allah kuma haka.
\s5
\v 17 Amma game da umarnin dake biye, ban yaba maku ba, taruwarku ba ta kirki ba ce, ta rashin gaskiya ce.
\v 18 Farko dai sa'adda kuke, taron ikklisiya, na ji har akwai rarrabuwa tsakaninku, har na fara amincewa da maganar.
\v 19 Dole ne a sami tsattsaguwa a tsakaninku, don a iya gane wadanda suke amintattu a cikinku.
\s5
\v 20 Domin, in kun taru a wuri daya, ba jibin Ubangiji kuke ci ba!
\v 21 Ya yin da kuke ci, kowa na cin abincinsa ne kamin sauran Wani yana jin yunwa, wani kuma ya zarin ci, har ya bugu.
\v 22 Baku da gidajen da zaku ci ku sha, kuna raina ikkilisiyar Allah, kuna kuma wulakanta wa wadanda basu da komai? To, me zan ce maku? Yaba maku zan yi? Ba zan yaba maku ba akan wannan.
\s5
\v 23 Amma abin da na karba a gun Ubangiji shi nake baku cewa Ubangiji Yesu, a daren da aka bashe shi ya dauki gurasa.
\v 24 Bayan ya yi godiya, sai ya kakkarya ya ce, "wanna shi ne jikina wanda yake saboda ku, ku yi domin tunawa da ni."
\s5
\v 25 Ta wannan hanya kuma, sai ya dauki kokon, ya ce, "kokon nan na sabon alkawari ne, da aka tabbatar da shi da cikin jinina. Ku yi haka kuna sha don tunawa da ni."
\v 26 Duk sa'adda kuke cin gurasar nan, kuna kuma sha cikin kokon nan, kuna bayyana mutuwar Ubangiji ke nan, har sai ya dawo.
\s5
\v 27 Saboda haka duk wanda ya ci gurasar nan, ko ya sha a cikin kokon nan, na Ubangiji da rashin cancanta, ya yi laifin wulakanta jikin Ubangiji da jininsa.
\v 28 Sai kowa ya fara auna kansa, kafin ya ci gurasar, ya kuma sha a cikin kokon nan.
\v 29 In kowa ya ci, ya sha ba tare da rarrabewa da jikin Ubangiji ba, lalle ya jawowa kansa hukunci, ta wurin ci da sha da ya yi.
\v 30 Shi ya sa da yawa a cikin ku suke raunana, kuma suna fama da rashin lafiya, har ma wasun ku da dama suka yi barci.
\s5
\v 31 Amma, in mun auna kanmu, ba a za a hukunta mu ba.
\v 32 In kuwa Ubangiji ne ya ke hukunta mu, To, muna horuwa ke nan, don kada a kayar damu tare da duniya.
\s5
\v 33 Saboda haka, ya ku 'yan'uwana, idan kuka tattaru don cin abinci, sai ku jira juna.
\v 34 Idan kuwa wani yana jin yunwa, ya ci a gida, kada ya zama taronku ya jawo maku hukunci. Batun sauran abubuwan da kuka rubuta kuwa, zan ba da umarni a kai sa'ad da na zo.
\s5
\c 12
\p
\v 1 Game da baye bayen Ruhu Mai Tsarki 'yan'uwa, bana so ku zama da jahilci.
\v 2 Kun san cewa lokacin da ku ke al'ummai, an rude ku da alloli marasa magana ta hanyoyi dabam dabam marasa kan gado.
\v 3 Saboda haka ina so ku sani babu wanda ya ke magana da Ruhun Allah da zai ce, "Yesu la'ananne ne." Babu kuma wanda zaya ce, "Yesu Ubangili ne," sai dai ta Ruhu Mai Tsarki.
\s5
\v 4 Akwai bay bye iri iri, amma Ruhu daya ne.
\v 5 Akwai hidimomi iri iri, amma Ubangiji daya ne.
\v 6 Akwai aikace aikace iri iri, amma Allah daya ke bayyanawa kowane mutum yadda zai aiwatar da su.
\s5
\v 7 To ga kowanne an bayar da ikon nuna ayyukan Ruhu a fili domin amfanin kowa.
\v 8 Ga wani ta wurin Ruhu an bayar da baiwar hikima, kuma ga wani kalmar sani ta wurin Ruhu daya.
\s5
\v 9 Ga wani an ba shi baiwar bangaskiya ta wurin Ruhun nan, ga wani kuwa an ba shi baiwar warkarwa ta wurin wannan Ruhun.
\v 10 Ga wani yin ayyukan iko, ga wani kuwa annabci. Ga wani kuwa an ba shi baiwar bambance ruhohi, ga wani harsuna daban daban, kuma ga wani fassarar harsuna.
\v 11 Dukan wadannan Ruhu daya ne ya ke iza su, ya kuma rarraba baye bayen ga kowannen su yadda ya nufa.
\s5
\v 12 Kamar yadda jiki daya ne amma da gabobi da yawa kuma duk gabobin na jiki daya ne, haka nan Almasihu yake.
\v 13 Gama ta Ruhu daya aka yi wa kowa baftisma cikin jiki daya, ko Yahudawa ko al'ummai, ko bayi ko 'ya'ya, dukan mu kuwa an shayar da mu Ruhu daya.
\s5
\v 14 Gama jiki ba daya ba ne sungun, amma gabobi ne da yawa.
\v 15 Idan kafa ta ce, "tun da dai ni ba hannu ba ne to ni ba fannin jikin bane," wannan baya rage masa matsayin sa a jikin ba.
\v 16 Kuma da kunne zaya ce, '"Da yake ni ba ido ba ne, ai, ni ba gabar jiki ba ne," fadar haka ba za ta raba shi da zama gabar jikin ba.
\v 17 Idan dukan jikin ya kasance ido ne da me za a ji? Da dukan jikin kunne ne, da me za a sunsuna?
\s5
\v 18 Amma Allah ya shirya gabobin jiki bisa ga tsarin sa.
\v 19 Amma da duk jiki gaba daya ce, da ina jikin zai kasance?
\v 20 Ga shi akwai gabobi da yawa, kuma jiki daya ne.
\s5
\v 21 Ba da ma ido ya fadawa hannu, "Bana bukatar ka," ko kuma kai ya fadawa kafafu, "Ba na bukatar ku."
\v 22 Amma, sai ma gabobin da ake gani kamar raunannu su ne masu humimmanci, gabobin jiki kuwa da ake gani kamar sun kasa sauran daraja, mu kan fi ba su martaba.
\v 23 Ta haka gabobinmu marasa kyan gani, akan kara kyautata ganinsu. Gabobin mu masu kyan kuma ba sai an yi masu ado ba.
\v 24 Amma Allah ne da kansa ya hada jiki, yana bada mafificiyar martaba ga kaskantacciyar gaba.
\s5
\v 25 Yayi haka ne domin kada a sami tsattsaguwa a cikn jikin, amma domin gabobin su kula da juna da matsananciyar lura.
\v 26 Kuma idan gaba daya na wahala, dukan gabobin suna wahala tare. ko kuma idan an girmama gaba daya, dukan gabobin na farin ciki tare.
\v 27 Yanzu ku jikin Almasihu ne, saboda haka kuma kowannen ku gabarsa ne.
\s5
\v 28 A cikin ikilisiya, Allah ya sa wasu su zama, na farko manzanni, na biyu annabawa, na uku masu koyarwa, sa'an nan sai masu yin ayyukan iko, sai masu aikin warkarwa, da masu bayar da taimako, da masu aikin tafiyar da al'amura, da masu harsuna daban daban.
\v 29 To kowa manzo ne? ko kuwa duka annabawa ne? ko kuma duka masu koyarwa ne? Kowa ne ke yin manyan ayyukan iko?
\s5
\v 30 Ko kuwa dukan su ne suke da baiwar warkarwa? Dukan su ne ke magana da harsuna? ko kuma dukan su ne ke fassara harsuna?
\v 31 Amma bari ku himmantu ga neman baiwa mafi girma. Kuma zan nuna maku wata hanya mafificiya.
\s5
\c 13
\p
\v 1 Koda ya zamanto ina magana da harsunan mutane, har ma da na mala'iku, amma kuma ba ni da kauna, na zama kamar kararrawa mai yawan kara, ko kuge mai amo.
\v 2 Ko da ya zamanto ina da baiwar annabci kuma na fahimci dukkan boyayyar gaskiya, da dukkan ilimi, ko ina da matukar bangaskiya, har ma zan iya kawar da duwatsu. muddin ba ni da kauna, ni ba komai ba ne.
\v 3 Ko da ya zamanto na bayar da dukan mallakata domin a ciyar da matalauta, in kuma mika jikina domin a kona. Amma in ba ni da kauna, ban sami ribar komai ba. (Na bayar da jikina ne domin inyi fahariya).
\s5
\v 4 Kauna na da hakuri da kirki. kauna bata kishi ko fahariya. kauna ba ta girman kai
\v 5 ko fitsara. Bata bautar kanta. Bata saurin fushi, kuma bata ajiyar lissafin laifuffuka.
\v 6 Bata farin ciki da rashin adalci. A maimako, tana farin ciki da gaskiya.
\v 7 Kauna tana jurewa cikin dukan abubuwa, tana gaskata dukan abubuwa, tana da yarda game da dukan abubuwa, tana daurewa dukan abubuwa.
\s5
\v 8 Kauna ba ta karewa. Idan akwai anabce anabce, zasu wuce. Idan akwai harsuna, zasu bace. Idan akwai ilimi, zaya wuce.
\v 9 Domin muna da sani bisa - bisa kuma muna anabci bisa - bisa.
\v 10 Sa'adda cikakke ya zo, sai marar kammalar ya wuce.
\s5
\v 11 Da nake yaro, nakan yi magana irinta kuruciya, nakan yi tunani irin na kuruciya, nakan ba da hujjojina irin na kuruciya. Da na isa mutum na bar halayen kuruciya.
\v 12 Gama yanzu muna gani sama - sama kamar ta madubi, amma a ranar fuska da fuska, yanzu na sani bisa - bisa, amma a lokacin zan sami cikakken sani kamar yadda aka yi mani cikakken sani.
\v 13 To, a yanzu abubuwan nan uku sun tabbata: bangaskiya, da gabagadi mai zuwa, da kuma kauna, amma duk mafi girma a cikinsu ita ce kauna.
\s5
\c 14
\p
\v 1 Ku dafkaci kauna kuma ku himmatu domin baye bayen ruhaniya, musamman domin kuyi anabci.
\v 2 Domin wanda yake magana da harshe bada mutane yake magana ba amma da Allah. domin babu mai fahimtarsa saboda yana zancen boyayyun abubuwa ciki Ruhu.
\v 3 Amma wanda yake anabci da mutane yake magana domin ya gina su, ya karfafa su, kuma ya ta'azantar dasu.
\v 4 Wanda yake magana da wani harshe, kansa yake ginawa, amma mai yin annabci kuwa, ikilisiya yake ginawa.
\s5
\v 5 To, fatana ace dukan ku kuna magana da harsuna. Amma fiye da hakama, fatana ace kuyi anabci. Wanda yake anabci yafi wanda yake magana da harsuna (sai dai idan wani ya fassara domin ikilisiya ta ginu).
\v 6 Amma yanzu, 'yan'uwa, in na zo wurin ku ina magana da harsuna, ta yaya zaku karu dani? ba zaya yiwu ba, sai idan nayi maku magana da wahayi, ko sani, ko anabci, ko koyarwa.
\s5
\v 7 Idan kayan kida marasa rai suna fitar da sauti - kamar su sarewa da algaita - kuma basu fitar da amo daban daban, ta yaya wani zaya san irin amon da sarewar da algaitar suke kadawa?
\v 8 Domin idan aka busa kaho da sauti marar ma'ana, ta yaya wani zaya san lokacin da ya dace ya shirya zuwa yaki?
\v 9 Haka yake game da ku. Idan kuka furta zance marar ma'ana, ta yaya wani zaya fahimci abinda kukace? zaku yita magana, kuma babu wanda zaya fahimce ku.
\s5
\v 10 Babu shakka akwai harsuna daban daban a duniya, kuma babu wanda baya da ma'ana.
\v 11 Amma idan ban san ma'anar wani harshe ba, zan zama bare ga mai maganar, kuma mai maganar zaya zama bare a gareni.
\s5
\v 12 haka yake gare ku. Tun da kuna da dokin bayyanuwar Ruhu, ku himmatu da habaka cikin gina ikilisiya.
\v 13 To wanda yake magana da harshe yayi addu'a domin ya iya fassarawa.
\v 14 Domin idan nayi addu'a da harshe, ruhuna yayi addu'a, amma fahimtata bata karu ba.
\s5
\v 15 To, me zan yi? Zan yi addu'a da ruhuna, in kuma yi addu'a da fahimtata. Zan yi raira waka da ruhuna, kuma in raira waka da fahimtata.
\v 16 In ba haka ba, idan ka yi yabon Allah da ruhu kawai, ta yaya wanda yake waje zai ce, "Amin" a kan godiyar da kake yi in bai san abin da kake fada ba?
\s5
\v 17 Babu shakka kayi godiya sosai, amma wanin baya ginu ba.
\v 18 Nagodewa Allah ina magana da harsuna fiye da ku duka.
\v 19 Duk da haka dai a taron ikilisiya na gwammace in yi magana da kalmomi biyar cikin fahimta saboda inganta wadansu fiye da dubu goma da harshe.
\s5
\v 20 'Yan'uwa, kada ku zama yara cikin tunani, sai dai a wajen aikin mugunta, ku yi halin jarirai, amma a tunaninku ku girma.
\v 21 A rubuce yake a shari'a cewa, "zan yi magana da mutanen nan ta wurin mutane masu bakin harsuna, da kuma lebunan baki. Duk da haka kuwa ba za su saurare ni ba", in ji Ubangiji.
\s5
\v 22 Amma harsuna alamu ne, ba ga masu bada gaskiya ba, sai dai ga marasa ba da gaskiya. Annabci kuwa alama ce ga masu ba da gaskiya, amma ba don marasa bangaskiya ba.
\v 23 Saboda haka, in dukan ikilisiya ta taru, kowa kuwa yana magana da wasu harsuna, wadansu na waje da kuma marasa ba da gaskiya suka shigo, ashe, ba sai su ce kun haukace ba ba?
\s5
\v 24 In kuwa kowa yana yin annabci, wani kuma marar ba da gaskiya ko wani daga waje ya shigo, maganar kuwa zata ratsa shi. Za a ma hukanta shi a kan maganar,
\v 25 asiran zuciyarsa kuma za su tonu. Sakamokon haka, sai ya fadi ya yi wa Allah sujada, zaya furta cewa lallai Allah yana tare da ku.
\s5
\v 26 Sai me kuma 'yan'uwa? idan kuka tattaru, wani yana da zabura, koyarwa, wahayi, harshe, ko fassara. Kuyi komai domin gina ikilisiya.
\v 27 Idan wani yayi magana da harshe, bari a sami mutum biyu ko uku a yawansu, kuma kowa yayi daya bayan daya. Sai wani ya fassara abinda aka fada.
\v 28 Amma idan babu wanda zaya fassara, bari dukansu suyi shiru a ikilisiya. Bari kowa yayi wa kansa maganar a gida shi kadai da kuma Allah.
\s5
\v 29 Bari annabawa biyu ko uku suyi magana, bari sauran su saurara tare da bambance abinda ake fada.
\v 30 Idan kuma anba wani fahimta wanda yana zaune a cikin sujadar, bari wanda yake ta magana kafin yanzu yayi shiru.
\s5
\v 31 Dukanku kuna iya yin annabci daya bayan daya, domin kowannen ku yayi koyi, a kuma samu karfafawa.
\v 32 Gama ruhohin annabawa suna karkashin annabawa,
\v 33 domin Allah ba Allahn rudu ba ne, na salama ne. Haka yake kuwa a duk ikllisiyoyin masu bangaskiya.
\s5
\v 34 Mataye suyi shiru a ikilisiyoyi. Domin ba a basu dama ba suyi magana. A maimako, su zama masu sadaukar da kansu, kamar yadda doka ta ce.
\v 35 Idan akwai abinda suke so su koya, bari su tambayi mazajen su a gida. Domin abin kunya ne mace tayi magana a ikilisiya.
\v 36 Daga wurinku maganar Allah ta zo ne? ko kuwa a gare ku kadai ta iso?
\s5
\v 37 In wani yana zaton shi ma annabi ne, ko kuwa mai ruhaniya, to, sai ya fahimta, abin nan da nake rubuta maku umarni ne daga wurin Ubangiji.
\v 38 In kuwa wani ya ki kula da wannan, shi ma kada a kula da shi.
\s5
\v 39 Saboda haka, 'yan'uwa, ku yi marmarin yin annabci sosai, sa'an nan kada ku hana kow yin magana da harsuna.
\v 40 Sai dai a yi komai ta hanyar da ta dace bisa ga tsari.
\s5
\c 15
\p
\v 1 Yanzu ina tunashshe ku 'yan'uwa, game da bisharar nan da nake shelarwa, wadda kuka karba kuke kuma dogara da ita.
\v 2 Da wannan bishara aka yi maku ceto, idan kuka rike wa'azi da na yi maku da karfi, sai in dama kun gaskanta a banza.
\s5
\v 3 Domin na baku muhimmin sako kamar na farko da na karba: cewa Almasihu ya mutu domin zunubanmu, bisa ga nassosi,
\v 4 cewa kuma an bizne shi, ya kuwa tashi daga matattu a rana ta uku bisa ga nassosi.
\s5
\v 5 Cewa kuma ya bayyana ga Kefas, sa'an nan ga sha biyun.
\v 6 Daga nan ya bayyana ga 'yan'uwa sama da dari biyar a lokaci guda. Wadanda mafi yawan su na da rai har yau, amma wasun su sun yi barci.
\v 7 Daga nan ya bayyana ga Yakubu, da kuma ga manzannin duka.
\s5
\v 8 A karshe, sai ya bayyana a gare ni, kamar dan da aka haifa bakwaini.
\v 9 Gama ni ne mafi kankanta a cikin manzanni. Ban cancanci a kira ni manzo ba, domin na tsanantawa ikklisiyar Allah.
\s5
\v 10 Amma saboda alherin Ubangiji ina matsayin da nake a yau, kuma alherin sa da ke ciki na ba a banza yake ba. A maimako, nayi aiki tukuru fiye da su duka. Amma duk da haka ba ni bane, amma alherin Allah da ke tare da ni.
\v 11 Saboda haka ko nine ko Su, haka mukayi wa'azin, haka kuma kuka gaskata.
\s5
\v 12 To idan anyi shela a matsayin cewa Yesu ya tashi daga matattu, tayaya wadansunku su ke cewa babu tashin matattu?
\v 13 Amma idan babu tashin matattu, Almasihu ma ai ba a tashe shi ba kenan.
\v 14 idan kuwa ba a tashi Almasihu ba, wa'azin mu ya zama banza kenan, haka kuma bangaskiyar ku ta zama banza.
\s5
\v 15 Mun kuma zama shaidun karya game Allah kenan, muna shaida akan Allah cewa ya tashi Almasihu daga matattu alhali ko bai tashe shi ba.
\v 16 Domin idan babu tashin matattu, kai, ko Almasihu ma ba a tashe shi ba kenan.
\v 17 Idan har ba a tashi Almasihu ba, bangaskiyar ku a banza take, har yanzu kuma, kuna cikin zunuban ku.
\s5
\v 18 To wadanda suka mutu cikin Almasihu kuma sun hallaka kenan,
\v 19 idan a wannan rayuwa ce kadai muke da bege cikin Almasihu, to cikin dukkan mutane munfi kowa zama abin tausayi.
\s5
\v 20 Amma yanzu, Almasihu ya tashi daga matattu, wanda ya sa shi ya zama nunar fari cikin tashi daga matattu.
\v 21 Domin yadda mutuwa ta shigo duniya ta hanyar mutum guda, hakkan nan ma tashi daga matattu.
\s5
\v 22 Gama kamar yadda a cikin Adamu duka suka mutu, haka kuma a cikin Almasihu za a rayar da duka.
\v 23 Amma kowanne da tsarinsa: Almasihu, nunan fari, sannan su wadanda ke na Almasihu za a rayar da su lokacin zuwansa.
\s5
\v 24 Sa'an nan karshen zai gabato, lokacin da Almasihu zai mika mulkin ga Allah Uba. sa'an nan ne zaya kawar da dukkan mulki, martaba da iko.
\v 25 Gama mulkinsa zai habaka har sai ya sa dukkan makiyansa a karkashin sawayen sa.
\v 26 Mutuwa kuwa, ita ce makiyi na karshe da za'a hallaka.
\s5
\v 27 Domin " yasa dukkan komai a karkashin ikonsa," Amma da aka ce" yasa dukkan komai a karkashin ikonsa," a sarari yake cewa wannan baya hada da wanda yasa dukan komai a karkashin ikonsa ba.
\v 28 Idan dukan abu na karkashin mulkinsa, to Dan da kansa zaya kasance a karkashin ikon shi wanda yasa komai a karkashin ikonsa. Wannan zaya kasance ne saboda Allah Uba ya zama dukkan komai cikin dukkan komai.
\s5
\v 29 ko kuma me zai faru da wadanda ake yi wa baftisma domin matattu? Idan kuwa babu tashin matattu sam sam, ina amfanin yi masu baftisma domin su?
\v 30 Kuma me yasa muke cikin hadari kowace sa'a?
\s5
\v 31 Ina mutuwa kullum. Wannan nake furtawa ta wurin fahariya, 'yan'uwa, wadda nake da ita cikin Almasihu Yesu Ubangijinmu.
\v 32 Menene ribata, a idanun mutane, idan nayi kokowa da bisashe a Afisa, idan babu tashin matattu? "bari mu ci mu sha, domin gobe zamu mutu."
\s5
\v 33 Kada fa a yaudare ku, domin " tarayya da mugaye takan bata halayen kirki."
\v 34 "Ku natsu! kuyi zaman adalci! kada ku cigaba da zunubi. Domin wasunku basu da sanin Allah. Ina fadar wannan domin in baku kunya.
\s5
\v 35 Amma wani zaya ce, "Yaya za'a yi tashin matattu? Wane irin jiki kuma zasu tashi da shi?
\v 36 Ku jahilai ne sosai! Abinda ka shuka ba zaya fara girma ba sai ya mutu.
\s5
\v 37 Abinda ka shuka ba jikin da zaya kasance bane, amma kwayar irin ne kawai. Wanda zaya zama alkama ko wani abu daban.
\v 38 Amma Allah zaya bashi jiki yadda ya zaba, ga kowane kwayar iri da nashi jikin.
\v 39 Ba duka jiki ne yake iri daya ba. A maimako, akwai jiki irin na mutane, akwai kuma wani irin na dabbobi, kuma wani jikin irin na tsuntsaye, kuma da irin na kifi.
\s5
\v 40 Akwai kuma jikina na samaniya da jikina na duniya. Amma daukakar jikin samaniya wata daban ce kuma daukakar jikin duniya daban ce.
\v 41 Akwai daukaka irin ta rana, da kuma wata daukakar irin ta wata, da kuma wata daukakar irin ta taurari. Domin wani tauraron ya bambanta da wani wajen daukaka.
\s5
\v 42 Haka yake a tashin matattu. Abinda aka shuka mai lalacewa ne, wanda aka tayar marar lalacewa ne.
\v 43 An shuka shi cikin rashin daraja; an tayar da shi cikin daukaka. An shuka shi cikin rauni; an tayar da shi cikin iko.
\v 44 An shuka shi jiki na zahiri; an tayar da shi jiki na ruhaniya. Idan akwai jiki na zahiri, to akwai jiki na ruhaniya.
\s5
\v 45 Haka kuma aka rubuta, "Adamu na farko ya zama rayayyen taliki." Adamu na karshe ya zama Ruhu mai bayar da rai.
\v 46 Amma na ruhaniyar ba shine ya fara zuwa ba amma na zahirin, daga nan na ruhaniyar.
\s5
\v 47 Mutumin farkon ai daga turbaya ya fito, wato na duniya. Amma shi na biyun daga sama yake.
\v 48 kamar yadda mutumin ya fito daga turbaya haka ma wadanda aka halitta da turbaya. kamar yadda mutumin yake daga sama haka ma wadanda ke na sama.
\v 49 Kamar yadda muke dauke da jiki mai kamannin turbaya, haka ma zamu kasance da kamannin mutumin sama.
\s5
\v 50 To wannan na fada, 'yan'uwa, cewa nama da jini ba za su gaji mulkin Allah ba. Haka kuma mai lalacewa ba za ya gaji marar lalacewa ba.
\v 51 Duba! ina gaya maku asirtacciyar gaskiya: Ba dukanmu zamu mutu ba, amma dukanmu za a canza mu.
\s5
\v 52 Za a canza mu nan da nan, cikin keftawar ido, a kaho na karshe. Domin za a busa kaho, kuma za a tada matattu marasa lalacewa, kuma za a canza mu.
\v 53 Domin wannan jiki mai lalacewa dole ya sanya jiki marar lalacewa, kuma wannan jiki mai mutuwa dole ya sanya marar mutuwa.
\s5
\v 54 Amma idan wannan jiki mai lalacewa ya sanya marar lalacewa, kuma wannan jiki mai mutuwa ya sanya marar mutuwa, sai abinda aka rubuta ya cika, "An hadiye mutuwa cikin nasara."
\v 55 "Mutuwa, ina nasararki? Mutuwa, ina dafinki?"
\s5
\v 56 Gama dafin mutuwa zunubi ne, kuma ikon zunubi shari'a ce.
\v 57 Amma godiya ga Allah, wanda ya bamu nasara ta wurin Ubangijinmu Yesu Almasihu!
\s5
\v 58 Saboda haka, ya ku 'yan'uwana kaunatattu, ku dage kuma kada ku jijjigu. Ko yaushe ku habaka da aikin Ubangiji, domin kun san cewa aikinku cikin Ubangiji ba a banza yake ba.
\s5
\c 16
\p
\v 1 Yanzu game da zancen tattara gudunmuwa ga masu bi, kamar yadda na umurci ikilisiyun Galatiya, haka za ku yi.
\v 2 A ranar farko ga mako, kowannen ku ya ajiye wani abu, yana tarawa bisa ga iyawarku. Ku yi haka don in na zo ba sai an tattara ba.
\s5
\v 3 Sa'adda na zo, zan aiki duk wadanda kuka yarda da su da wasiku don su kai sakonku Urushalima.
\v 4 Sannan idan ya dace nima in tafi, sai su tafi tare da ni.
\s5
\v 5 Zan zo wurinku sa'adda na ratsa Makidoniya. Domin zan ratsa ta makidoniya.
\v 6 Meyuwa in jima a wurinku, har ma in yi damuna, domin ku taimaka mani game da tafiyata, duk inda za ni.
\s5
\v 7 Gama ba na so in yi maku gani na gajeren lokaci. Don ina so in dau lokaci tare da ku, idan Ubangiji ya yarda.
\v 8 Amma zan tsaya Afisus har ranar Fentikos.
\v 9 Gama an bude mani kofa mai fadi, kuma akwai magabta da yawa.
\s5
\v 10 Sa'adda Timoti ya zo, ku tabbata ya sami sakewa acikinku, tun da aikin Ubangiji yake yi kamar yadda nake yi.
\v 11 Kada fa kowa ya rena shi. Ku tabbata kun sallame shi lafiya, domin ya komo gare ni, don ina duban hanyarsa tare da yan'uwa.
\v 12 Game da zancen dan'uwanmu Afollos kuwa, na karfafa shi ya ziyarce ku tare da 'yan'uwa. Sai dai baya sha'awar zuwa yanzu. Amma zai zo sa'adda lokaci ya yi.
\s5
\v 13 Ku zauna a fadake, ku tsaya daram cikin bangaskiya, kuna nuna halin maza, ku yi karfin hali.
\v 14 Bari dukan abinda kuke yi ayi shi cikin kauna.
\s5
\v 15 Kun dai sani iyalin gidan Sitefanas su suka fara tuba a Akaya, kuma sun bada kansu ga yi wa masu bi hidima. Yanzu ina rokonku, 'yan'uwa,
\v 16 kuyi biyayya da irin wadannan mutane da duk wanda ke taimakawa a cikin aikin, yana kuma fama tare da mu.
\s5
\v 17 Na yi farinciki da zuwan Sitefanas, da Fartunatas, da Akaikas. Sun debe mini kewarku.
\v 18 Gama sun wartsakar da ruhuna da naku kuma. Don haka, Sai ku kula da irin wadannan mutane.
\s5
\v 19 Ikilisiyoyin kasar Asiya suna gaishe ku. Akila da Bilkisu, tare da ikilisiyar da take taruwa a gidansu, suna gaishe ku cikin Ubangiji.
\v 20 Dukan 'yan'uwa masu bi na gaishe ku. Ku gaida juna da sumba maitsarki.
\s5
\v 21 Ni Bulus, nake rubuta wannnan da hannuna.
\v 22 Duk wanda ba ya kaunar Ubangiji bari ya zama la'ananne. Ubangijinmu, Ka zo!
\v 23 Alherin Ubangiji Yesu ya kasance tare da ku.
\v 24 Bari kaunata ta kasance tare da ku duka a cikin Almasihu Yesu. \f + \ft Copiesan copiesan mahimmanci da tsoffin kwafin Girkanci da wasu tsoffin fassarorin suna da \fqa Amin \fqa* a ƙarshen aya ta 24. Amma da yawa tsoffin kwafin Girkanci, da tsoffin fassarorin da yawa, ba su da \fqa Amin \fqa* a karshen. \f*