ha_ulb/46-ROM.usfm

867 lines
54 KiB
Plaintext

\id ROM
\ide UTF-8
\h Romawa
\toc1 Romawa
\toc2 Romawa
\toc3 rom
\mt Romawa
\s5
\c 1
\p
\v 1 Bulus, bawan Yesu Almasihu, kirayayye ya zama manzo, kuma kebabbe domin bisharar Allah.
\v 2 Wannan itace bisharar da ya alkawarta tuntuni ta wurin annabawansa ta wurin tsarkakakkun littattafan sa.
\v 3 Game da Dansa ne, haifaffe daga zuriyar Dauda ga zancen jiki.
\s5
\v 4 Ta wurin tashinsa daga mattatu aka aiyana shi ya zama Dan Allah ta wurin ikon Ruhu na tsarkakewa. Yesu Almasihu Ubangijimu.
\v 5 Ta wurinsa muka karbi alheri da manzanci sabo da biyayyar imani a cikin dukkan al'ummai, domin darajar sunansa.
\v 6 cikin wadannan al'ummai kwa, ku ma an kiraku ku zama na Yesu Almasihu.
\s5
\v 7 Wannan wasika ga dukkanku ne da kuke cikin Roma, kaunatattu na Allah, kirayayyun mutane tsarkakakku. Bari alheri ya kasance tare daku, da salama daga Allah Ubanmu, da kuma Ubangiji Yesu Almasihu.
\s5
\v 8 Abu na farko dai ina yi wa Allah na godiya ta wurin Yesu Almasihu domin ku duka, domin kuwa ana labarta bangaskiyarku ko ina a cikin dukkan duniya.
\v 9 Domin kuwa Allah shi ne shaida ta, wanda nake bautawa a cikin ruhuna a cikin bisharar Dansa, yadda a koyaushe na ke ambaton ku.
\v 10 A kullum ina roko cikin addu'o'ina domin ta kowanne hali in yi nasarar zuwa gare ku da izinin Allah.
\s5
\v 11 Gama ina marmarin ganin ku, domin in baku wata baiwa ta ruhaniya, domin in karfafa ku.
\v 12 Wato ina dokin in sami cikakkiyar karfafawa a cikin ku, ta wurin bangaskiyar junanmu, wato tawa da taku.
\s5
\v 13 Yanzu fa bana so ku rasa sani, yan'uwa, sau da yawa nake yin niyyar zuwa wurinku, amma har yanzu hakan din bata samu ba. Na so yin hakan din ne don in sami 'ya'ya na ruhu a cikinku kamar dai yadda ya ke a sauran Al'ummai.
\v 14 Ina dauke da nawayar Hellinawa da ta sauran jama'a, masu hikima da marasa hikima.
\v 15 Don a shirye na ke in sanar da bishara a gare ku, ku da kuke cikin Roma.
\s5
\v 16 Don kuwa ni ba na jin kunyar yin bishara, don ita ce ikon Allah don samun ceto ga duk wanda ya gaskata, da farko dai Yahudawa kana kuma Hellinawa,
\v 17 Domin a cikin ta adalcin Allah ya bayyana daga bangaskiy zuwa bangaskiya, kamar yadda yake a rubuce, "Mai adalci zai rayu ne tawurin bangaskiya."
\s5
\v 18 Domin fushin Allah ya bayyana ne daga sama gaba da rashin ibada da rashin adalci na yan'adam, wadanda suke danne gaskiya ta wurin rashin adalcin su.
\v 19 Dalili kuwa abinda yakamata a sani game da Allah a bayyane ya ke a gare su. Domin kuwa Allah ya bayyana masu shi a zahiri.
\s5
\v 20 Domin al'amuransa da ba'a iya gani a bayyane suke tun halittar duniya. A na iya gane su ta wurin halitatattun abubuwa. Wadannan al'amura kuwa sune madawwamin ikonsa da Allahntakarsa. Sakamakon haka, wadannan mutane ba su da hujja.
\v 21 Dalili kuwa, koda suna jin sun san Allah, amma basu darajanta shi a matsayin Allah ba, ko kuma su nuna masa godiya. Maimakon haka, suka zama wawaye a cikin tunaninsu, zukatansu marasa tunani sun duhunta.
\s5
\v 22 Suna daukar kansu akan masu hikima ne su, amma sai ga su sun zama wawaye.
\v 23 Sun musanya daukakar Allah madawwami da ta kamannin abubuwan da basa dawwama, kamar mutum, da tsuntsaye, da dabbobi masu kafafu hurhudu, da masu jan ciki.
\s5
\v 24 Saboda haka Allah ya bashe su ga sha'awoyin kazantar zukatansu, su wulakantar da jukunansu a junansu.
\v 25 Sune suka musanya gaskiyar Allah da karya, Kuma suke sujada da bauta ga halittaccen abu, maimakon Mahaliccin, Wanda yake abin yabo har abada. Amin.
\s5
\v 26 Saboda haka Allah ya bashe su, ga sha'awowin su na lalata da wulakanci, har matansu suka canza ka'idar jima'i da aka saba zuwa madigo mace da mace.
\v 27 Mazajensu ma suka sauya ka'idar jima'i tsakanin mace da miji zuwa namiji da namiji suna yin aikin lalata. Maza su na kwana da maza suna aikata aikin ban kyama, suna kuwa girbe sakamakon aiknsu na ban kyama.
\s5
\v 28 Tunda shike ba su amince da Allah a cikkin al'amuransu ba, Allah ya bashe su ga bataccen hankalinsu, su aikata wadannan munanan abubuwa.
\s5
\v 29 Suna cike da dukkan rashin adalci, mugunta, kyashi, keta, kuma cike da kishi, kisan kai, tarzoma, makirci, da kuma munanan manufafofi.
\v 30 Masu gulma da kage, makiyan Allah. Masu tada zaune tsaye, masu taurin kai, da ruba, masu kaga kowadanne miyagun abubuwa, kuma masu kin yin biyayya ga iyayensu.
\v 31 Masu duhun zuciya; masu cin amana, marasa soyayya, da kuma rashin tausayi.
\s5
\v 32 Suna sane da tsarin Allah cewa masu yin irin wadannan al'amura sun cancanci hukuncin mutuwa. Ba kuwa yin wadannan abubuwan ka dai suke yi ba, harma goyon bayan masu yinsu suke yi.
\s5
\c 2
\p
\v 1 Saboda da haka baka da hujja, kai mutum, kai mai shara'antawa, domin kuwa abinda kake shara'antawa akan wasu kana kada kanka da kanka. Domin kuwa kai mai shar'antaawa kana aikata wadannan abubuwa.
\v 2 Amma mun san cewa shari'ar Allah ta gaskiya ce sa'adda zata fado wa masu aikata wadannan irin abubuwa.
\s5
\v 3 Amma ka lura da wannan, ya kai mutum, mai shara'anta masu aikata wadannan ababuwa. Duk da shike kaima kana aikatawa. Kana jin zaka kubucewa hukuncin Allah?
\v 4 Ko kana raina falalar alheransa da yake yi ta wajen jinkirin hukuncinsa, da hakurinsa? Baka san cewa alheransa musanman domin su kai ka ga tuba bane?
\s5
\v 5 Amma saboda taurin kanka da zuciyarka marar tuba, kana tanadarwa kanka fushi, a ranar fushi, wato ranar bayyanuwar shari'ar adalci ta Allah.
\v 6 Zai baiwa kowanne mutum daidai sakamakon ayyukansa:
\v 7 Ga wadanda kuma suka nace da yin ayyukan alheri ba fasawa, sun samarwa kansu, yabo da daraja, da rai na har'abada.
\s5
\v 8 Amma ga masu son kai, wadanda suka ki yin biyayya ga gaskiya, suka yiwa rashin adalci biyayya, fushi da hasala mai zafi zai afko masu.
\v 9 Allah kuma zai sauko da bala'i da bakin ciki ga dukkan rayukan da suka aikata mugunta, ga Yahudawa da fari, sannan kuma Hellinawa.
\s5
\v 10 Amma yabo daraja da salama zasu kasance ga dukkan wadanda suka aikata ayukan alheri, ga Yahudawa da fari sannan Hellanawa.
\v 11 Domin kuwa Allah ba mai tara bane.
\v 12 Ga wadanda suka yi zunubi batare da shari'aba, zasu hallaka ba tare da shari'a ba, ga wadanda suka yi zunubi cikin shari'a kuma za'a hukunta su bisa ga shari'a.
\s5
\v 13 Domin kuwa ba masu jin shari'ar ne masu adalci agaban Allah ba, amma masu aikatawa ne zasu samu barata.
\v 14 Gama al'umai da basu san shari'a ba, bisa ga dabi'a sun yi abinda ke na shari'a, sun kuma zame wa kansu shari'a, koda shike basu da shari'ar.
\s5
\v 15 Dalilin haka kuwa sun nuna cewa ayukan da shari'a take bukata na nan a rubuce a zuciyarsu. lamirinsu kuma na yi masu shaida, tunanainsu kuma, ko dai yana kashe su, ko kuma yana karesu.
\v 16 hakanan kuma ga Allah. Wannan zai faru ranar da Allah zai shara'anta asiran boye na dukkan mutane, bisa ga bishara ta cikin Yesu Almasihu.
\s5
\v 17 Da shike kana kiran kanka Bayahude, kana zaune akan shari'a, kana alfahari cikin Allah,
\v 18 ka san nufinsa, ka kuma san abubuwan da suka bambanta da hakan, ka kuma sami koyarwa cikin shari'ar.
\v 19 Da shike kana da gabagadi akan cewa kai jagora ne ga makafi, haske ga wadanda suke cikin duhu,
\v 20 mai horo ga marasa hikima, mai koyar da jarirai, kuma a cikin shari'ar kana da abin da ya shafi sani da kuma gaskiya.
\s5
\v 21 ku da kuke koyar da wadansu, ba ku koyar da kanku? ku da kuke wa'azi kada ayi sata, ba ku yin sata?
\v 22 Ku da ke wa'azi kada ayi zina, ba ku yin zina? ku da ke hana bautar gumaka, ba ku yin sata a haikali?
\s5
\v 23 ku masu murna da tinkaho cikin shari'ar, ba kwa wulakanta Allah cikin kurakuranku na rashin bin shari'a?
\v 24 "Domin kuwa an wulakanta sunan Allah cikin Al'umai sabili da ku," kamar yadda aka riga aka rubuta.
\s5
\v 25 Lallai kuwa kaciya tana da riba a gare ku, idan kuka kiyaye doka, amma idan ku marasa bin doka ne kaciyarku ta zama rashin kaciya.
\v 26 domin kuwa idan mutum marar kaciya zai kiyaye dukkan bukatun doka, baza'a iya daukan rashin kaciyarsa a matsayin mai kaciya ba?
\v 27 Sannan idan mutum marar kaciya ta jini zai kiyaye dukkan dokoki, ba zai iya shara'anta ku masu kaciya ta shari'a ba? Haka kuma ya kasance ne domin kuna da shari'a a rubuce da kuma kaciya amma ba kwa bin doka!
\s5
\v 28 Domin shi kuwa ba Bayahude bane a waje; ba kuwa mai kaciyar da aka tsaga fata ba.
\v 29 Amma Bayahude ne ta ciki, sanna kuma mai kaciyar zuciya da kuma ruhu ba wasika ba, irin wanna mutumin yabonsa ba daga wurin mutane yake zuwa ba, amma daga Allah.
\s5
\c 3
\p
\v 1 To ina fifikon da bayahude yake dashi? Kuma ina ribar kaciya?
\v 2 Akwai muhimmancinsu ta kowacce hanya. Tun farko dai, yahudawa ne aka dankawa wahayi daga Allah.
\s5
\v 3 Idan wasu yahudawa basu bada gaskiya ba fa? Rashin bangaskiyarsu zai hana amincin Allah aiki?
\v 4 Bazai taba zama haka ba. Maimakon haka, bari Allah ya zama mai gaskiya, ko da kowanne mutum makaryaci ne. Kamar yadda aka rubuta, "Domin a nuna kai mai adalci cikin maganganunka, kuma kayi nasara a lokacin da aka kawo ka gaban shari'a."
\s5
\v 5 Amma idan rashin adalcinmu ya nuna adalcin Allah, to me zamu ce? Allah ba marar adalci ba ne, wanda ke aiwatar da fushinsa, ko kuwa? Ina magana bisa ga tunanin mutuntaka.
\v 6 Bazai taba zama haka ba. Domin idan haka ne ta yaya Allah zai shar'anta duniya?
\s5
\v 7 Amma idan gaskiyar Allah ta wurin karyata ta habaka yabonsa, To me yasa ake shar'anta ni a matsayin mai zunubi?
\v 8 To me zai hana ace kamar yadda ake fadin zancen karya a kanmu, wasu kuma sun dauka cewa mun fadi hakan, "Bari muyi mugunta, domin nagarta tazo?" Hukuncin su halal ne.
\s5
\v 9 To me kenan? Zamu ba kanmu hujja ne? ko kadan. Domin mun riga munyi zargin yahudawa da hellinawa, da cewar dukkansu, suna karkashin zunubi.
\v 10 Kamar yadda aka rubuta, babu wani mai adalci, babu ko daya.
\s5
\v 11 Babu wani mai fahimta. Babu wani mai neman Allah.
\v 12 Dukansu sun kauce hanya, dukansu gaba daya sun zama marasa amfani. Babu mai aikin nagarta, a'a, babu ko da guda daya.
\s5
\v 13 Makogwaronsu a bude yake kamar kabari. Harsunansu na dauke da cuta. Dafin macizai na karkashin lebunansu.
\v 14 Bakunansu cike suke da la'ana da daci.
\s5
\v 15 Sawayensu na saurin zuwa zubar da jini.
\v 16 Tafarkinsu wahala ce da lalacewa.
\v 17 Wadannan mutane basu san hanyar salama ba.
\v 18 Babu tsoron Allah a idanunsu."
\s5
\v 19 To mun san dai duk abin da shari'a tace, shari'a na magana ne da wadanda ke karkashinta, domin a rufe kowanne baki, domin dukan duniya ta bada amsa a gaban Allah.
\v 20 Domin a gabansa babu wanda zai barata ta wurin ayukan shari'a. Domin ta wurin shari'a ne sanin zunubi yazo.
\s5
\v 21 Amma yanzu ba tare da shari'a ba an bayyana sanin adalcin Allah, wanda shari'a da annabawa suke shaidawa.
\v 22 Wato, adalcin Allah ta wurin bangaskiya cikin Yesu Almasihu ga dukkan wadanda ke bada gaskiya. Domin babu bambanci:
\s5
\v 23 Domin duk sun yi zunubi sun kuma kasa kaiwa ga darajar Allah,
\v 24 Da alherinsa an baratar da mu ta wurin fansar dake cikin Yesu Almasihu.
\s5
\v 25 Amma Allah ya bayar da Yesu Almasihu wanda yake hadayar fansa ta wurin bangaskiya cikin jininsa. Ya mika Almasihu a matsayin tabbacin hukuncinsa, sabo da kuma ketarewar zunubanmu na baya
\v 26 cikin hakurinsa. Duk wannan ya faru ne domin a bayyana adalcinsa cikin wannan zamani, domin ya tabbatar da kansa mai hukunci, kuma ya nuna shine mai baratar da kowa saboda bangaskiya cikin Yesu.
\s5
\v 27 To ina fahariya? An fitar da ita. A kan wane dalilin? Don ayyuka? A'a, amma ta dalilin bangaskiya.
\v 28 Domin wannan muka kammala cewar ana baratar da mutum ta wurin bangaskiya ba tare da ayyukan shari'a ba.
\s5
\v 29 Ko kuwa Allah Allahn yahudawa ne kadai? Shi ba Allahn al'ummai bane? I, na al'ummai ne kuma.
\v 30 Idan dai lallai Allah daya ne, zai baratar da mai kaciya ta wurin bangaskiya, da marar kaciya kuma ta wurin bangaskiya.
\s5
\v 31 Mun kawar da shari'a kenan ta wurin bangaskiya? ba zai taba kasancewa haka ba. Maimako ma, muna inganta shari'a kenan.
\s5
\c 4
\p
\v 1 Me kenan zamu ce game da Ibrahim, kakanmu a jiki, me ya samu?
\v 2 Domin idan Ibrahim ya sami kubutarwa ta wurin ayuka, ai da ya sami dalilin fahariya, amma ba a gaban Allah ba.
\v 3 Kuma fa me nassi ke fadi? "Ibrahim ya bada gaskiya ga Allah, sai aka lisafta ta adalci gare shi."
\s5
\v 4 Yanzu fa shi dake yin ayyuka, ladansa ba a lisafta shi alheri ba ne, amma abun da ke nasa.
\v 5 Amma kuma shi da bai da ayyuka kuma maimakon haka ya gaskanta ga wanda ke kubutar da masu zunubai, bangaskiyarsa an lisafta ta a misalin adalci.
\s5
\v 6 Dauda ya yi furcin albarka bisa mutumin da Allah ya lisafta mai adalci da rashin ayyuka.
\v 7 Sai ya ce, "Masu albarka ne wadanda aka yafe laifofinsu, kuma wadanda zunubansu a rufe suke.
\v 8 Mai albarka ne mutumin da ko kadan Ubangiji ba zaya lisafta zunubin sa ba."
\s5
\v 9 To albarkar da aka fadi ko a bisansu wadanda aka yi wa kaciya ne kadai, ko kuwa a bisan su ma marasa kaciya? Domin mun yi furcin, "Bangaskiyar Ibrahim an lisafta ta adalci ce agare shi."
\v 10 Yaya aka lisafta ta? Bayan Ibrahim ya yi kaciya, ko kuwa a rashin kaciya? Ba a cikin kaciya ba, amma a rashin kaciya.
\s5
\v 11 Ibrahim ya amshi alamar kaciya. Wannan shi ne hatimin adalcin bangaskiyar da ya ke da ita tun cikin rashin kaciyarsa. Albarkacin wannan alama ce, ta sa shi ya zama uban dukkan wadanda suka badagaskiya, ko da shike ba su da kaciya. Wato ma'ana, adalci za a lisafta masu.
\v 12 Wannan kuma yana da ma'anar cewa Ibrahim ya zama uban kaciya ga wadanda suka fito ba domin masu kaciya kadai ba, amma kuma domin wadanda ke biyo matakin ubanmu Ibrahim. Kuma wannan itace bangaskiyar da ya ke da ita a rashin kaciya.
\s5
\v 13 Domin ba ta wurin shari'a aka bada alkawarin nan da aka yi wa Ibrahim da zuriyarsa ba, wannan alkawarin da ya ce zasu gaji duniya. Maimako, a ta wurin adalcin bangaskiya ne.
\v 14 Domin idan su da ke na shari'a magada ne, bangaskiya bata da komai, kuma alkawarin an wofintar da shi kenan.
\v 15 Domin shari'a ta kan jawo fushi, amma ta wurin rashin shari'a, babu karya umarni.
\s5
\v 16 Saboda wannan dalili haka ta faru ta wurin bangaskiya, domin ya zama bisa ga alheri. Kamar haka, alkawarin ya tabbata ga dukkan zuriya. Kuma wannan zuriya ba zata kunshi wadanda suke da sanin shari'a ba kadai, har ma da wadanda ke daga bangaskiyar Ibrahim. Saboda shi ne uban dukkan kowa,
\v 17 kamar yadda aka rubuta, "Na maishe ka uba ga kasashe masu yawa." Ibrahim na gaban aminin sa, wato, Allah, mai bada rai ga mattatu kuma ya kan kira abubuwan da basu da rai su kuma kasance.
\s5
\v 18 Duk da halin da ke a bayyane, Ibrahim ya gaskata ga Allah kai tsaye game da abubuwan da ke nan gaba. Sai ya zama uba ga kasashe masu yawa, kamar yadda aka ambata, "... Haka zuriyarka zata kasance."
\v 19 Ba ya karaya a bangaskiya ba. Ibrahim ya yarda da cewa jikinsa ya rigaya ya tsufa (shekarun sa na misalin dari). Ya kuma yarda da cewa mahaifar Saratu bata iya bada 'ya'ya ba.
\s5
\v 20 Amma domin alkawarin Allah, Ibrahim bai ji nauyin rashin bangaskiya ba. Maimakon haka, ya sami karfafawa a bangaskiyarsa sai ya daukaka Allah.
\v 21 Ya na da cikakkiyar gamsuwa cewa idan Allah ya yi alkawari, shi mai iya kammalawa ne.
\v 22 Haka nan ne kuma aka lisafta masa wannan a matsayin adalci.
\s5
\v 23 To ba'a rubuta kawai damin amfaninsa kadai ba, da aka lisafta dominsa.
\v 24 A rubuce yake domin mu, domin wadanda za'a lisafta su, mu da muka bada gaskiya gare shi wanda ya tada Yesu Ubangijinmu daga matattu.
\v 25 Wannan shi ne wanda aka bashe shi domin zunubanmu kuma an tada shi saboda fasar mu.
\s5
\c 5
\p
\v 1 Tun da shike mun sami barata, sabili da bangaskiya, mun sami salama tare da Allah ta wurin Yesu Almasihu.
\v 2 . Ta wurin sa kuma mun sami iso zuwa ga alheri inda muke tsayawa albarkacin bangaskiyarmu. Muna murna da gabagadin da Allah ya ba mu game da abin da zai faru, gabagadin da zamu dandana nan gaba cikin daukakar Allah.
\s5
\v 3 Ba kuwa haka kadai ba, amma muna murna da shan wahalolinmu. Mun san cewa shan wuya na haifar da
\v 4 Jimiri, Jimiri kuma na kawo amincewa, amincewa na kawo gabagadi game da abin da zai zo nan gaba.
\v 5 Wannan gabagadi wato begen da muke da shi baya kunyatarwa, domin kuwa an kwarara mana kaunar Allah a cikin zuciyarmu ta wurin Ruhu Mai Tsarki, da aka ba mu.
\s5
\v 6 Domin kuwa ko yayin da muke raunana, Almasihu ya mutu a lokacin da ke dai dai domin marasa ibada.
\v 7 To ai kuwa yana da wuya kwarai wani mutum ya yarda ya mutu don mutumin kirki ma. Watakila, wani na iyayin kasada ya yarda ya mutu don nagarin mutum.
\s5
\v 8 Amma Allah ya tabbatar mana da kaunarsa a gare mu, don kuwa tun muna masu zunubi, Almasihu ya mutu domin mu.
\v 9 Balle ma yanzu, da muka barata ta wurin jininsa, za mu sami tsira daga fushin Allah.
\s5
\v 10 Domin kuwa, in tun muna makiya, aka sulhunta mu da Allah ta wurin mutuwar Dansa, balle ma, yanzu da muka sami sulhu, zamu sami tsira ta wurin ransa.
\v 11 Bama haka kadai ba, amma muna murna a cikin Allah ta wurin Ubangijinmu Yesu Almasihu, wanda ta wurinsa ne muka sami wannan sulhu.
\s5
\v 12 Saboda haka, kamar yadda ta wurin mutum daya zunubi ya shigo cikin duniya, ta haka mutuwa ta shigo ta dalilin zunubi.
\v 13 Domin kuwa tun kafin a bada shari'a, zunubi na nan a duniya, amma ba' a lissafin zunubi in da ba shari'a.
\s5
\v 14 Duk da haka, mutuwa ta mallake tun daga Adamu har Musa, har ma wadanda basu yi zunubin keta umarni irin na Adamu ba, wanda yake misalin mai zuwan nan a gaba.
\v 15 Amma kyautar ba kamar keta umarnin take ba. Domin in sabo da laifin mutum dayan nan ne, da yawa suke mutuwa, haka ma alherin sa da baiwarsa ta wurin mutum dayan nan, Yesu Almasihu, sai baiwar ta wadata zuwa ga masu yawa.
\s5
\v 16 Domin kyautar ba kamar sakamakon wannan da yayi zunubin bace. Ta haka din nan ne, hukuncin nan mai tsanani ya zo sabo da zunubin mutum dayan. Har yanzu dai, wannan baiwa ta yanci ta zo ne bayan laifuffuka masu yawa.
\v 17 Domin, idan sabo da laifin mutum dayan nan ne, mutuwa ta mallake, saboda dayan, haka ma wadanda suka karbi alheri mai yawa da kuma baiwar adalci ta wurin ran, Yesu Almasihu.
\s5
\v 18 Don haka, kamar yadda zunubin dayan ya sa hukunci ya zo kan dukka, haka ma aikin adalci na dayan zai kawo barata da rai ga mutane masu yawa.
\v 19 Kuma kamar yadda rashin biyayyar dayan ta sa mutane masu yawan gaske su zama masu zunubi, haka ma ta biyayyar dayan mutane da yawan gaske za su sami adalci.
\s5
\v 20 Amma shari'a ta zo, inda ta sa zunubi ya habaka. Amma inda zunubi ya habaka, alheri ma ya habaka ribin ribi.
\v 21 Wannan ya faru ne, don kamar yadda zunubi yai mallaka zuwa mutuwa, haka kuma alheri ya mallaka zuwa adalci da rai na har abada ta wurin Yesu Almasihu Ubangijin mu.
\s5
\c 6
\p
\v 1 Me kuwa zamu ce yanzu? Sai mu ci gaba da yin zunubi domin Alheri ya yawaita?
\v 2 Ba zai taba faruwa ba. 'Yaya za'ace mu da muka mutu cikin zunubi mu ci gaba da rayuwa cikin sa?
\v 3 Ba ku san cewa duk wadanda aka yi masu baftisma cikin Almasihu Yesu an yi masu baftisma har ya zuwa mutuwarsa ne ba?
\s5
\v 4 An kuwa binne mu tare da shi, ta wurin baftisma cikin mutuwarsa. Haka kuma ya kasance ne domin kamar yadda Almasihu ya tashi daga matattu cikin daukakar Uba. Sakamakon haka muma zamu yi tafiya cikin sabuwar rayuwa.
\v 5 Domin kuwa idan muna tare dashi cikin kamannin mutuwarsa zamu kuwa zauna tare dashi har ga kamannin tashinsa.
\s5
\v 6 Mun kuma san cewa, an giciye wannan tsohon mutunmin nan namu tare dashi, domin a hallaka jikin zunubi. wanna kuwa ya kasance ne domin kada mu ci gaba da bautar zunubi.
\v 7 Duk kuma wanda ya mutu an ambace shi a matayin adali akan zunubi.
\s5
\v 8 Amma idan muka mutu tare da Almasihu, mun bada gaskiya zamu yi rayuwa tare dashi.
\v 9 Muna da sanen cewa an tada Almasihu daga matattu, don haka kuwa ba matacce yake ba. Mutuwa kuma bata da iko a kansa.
\s5
\v 10 Game da mutuwar da yayi ga zunubi yayi sau daya kuma domin dukka. Rayuwar da yake yi kuma yana yi wa Allah ne.
\v 11 Don haka ku ma sai ku dauki kanku a matsayin matattu ga zunubi amma rayayyu ga Allah cikin Almasihu Yesu.
\s5
\v 12 Sabili da haka kada ku bar zunubi yayi mulki a cikin jikinku, har ku yi biyayya ga sha'awarsa.
\v 13 Kada ku mika gabobin jikinku ga zunubi a matsayin kayan aikin rashin adalci. Amma ku mika kanku ga Allah rayayyu daga mutuwa. Ku kuma mika gabobin jikinku ga Allah a matsayin kayan aiki na adalci.
\v 14 kada ku ba zunubi dama yayi mulki a kanku, domin ba karkashin doka kuke ba, amma karkashin alheri kuke.
\s5
\v 15 To sai me? Sai mu yi zunubi wai don ba a karkashin doka muke ba amma alheri. ba zai taba faruwa ba.
\v 16 Ba ku san cewa duk ga wanda kuka mika kanku a matsayin bayi, a gareshi ku bayi ne ba? Wannan fa gaskiya ne, ko dai ku bayi ne ga zunubi wanda kaiwa ga mutuwa ko kuma bayi ga biyayya wanda ke kaiwa ga adalci.
\s5
\v 17 Amma godiya ta tabbata ga Allah! domin da ku bayin zunubi ne, amma kun yi biyayya daga zuciyarku irin salon koyarwar da aka baku.
\v 18 An 'yantar daku daga bautar zunubi, an kuma maishe ku bayin adalci.
\s5
\v 19 Ina magana da ku kamar mutum, domin kasawarku ta nama da jini. Kamar yadda kuka mika gabobin jikinku ga kazamta da miyagun ayyuka, haka ma yanzu ku mika gabobin jikinku a matsayin bayi na adalci.
\v 20 Domin a lokacin da kuke bayin zunubi, ku yantattu ne ga adalci.
\v 21 A wannan lokacin wanne amfani kuka samu na ayyukan da yanzu kuke jin kunyarsu? Domin kuwa sakamakon wadannan ayyuka shine mutuwa.
\s5
\v 22 Amma yanzu da da aka yantar daku daga zunubi aka mai da ku bayin Allah, amfaninsa ku kuwa shine tsarkakewarku. Sakamakon kuwa shine rai na har abada.
\v 23 Don kuwa sakamakon zunubi mutuwa ne. Amma kyautar Allah itace rai madauwami cikin Almasihu Yesu Ubangijinmu.
\s5
\c 7
\p
\v 1 'Yan'uwa, ko baku sani ba (domin ina magana da wadanda suka san shari'a), cewar shari'a na mulkin mutum muddin ransa?
\s5
\v 2 Domin ta wurin shari'a matar aure a daure take muddin mijinta nada rai, amma idan mijinta ya mutu, ta kubuta daga shari'ar aure.
\v 3 To don haka idan, mijinta na da rai, sai ta tafi ta zauna da wani mutumin, za'a kirata mazinaciya. Amma idan mijin ya mutu, "yantarciya ce daga shari'a, domin kada ta kasance mazinaciya idan ta auri wani mutum.
\s5
\v 4 Domin wannan, 'yan'uwana, ku ma an sa kun mutu ga shari'a ta wurin jikin Almasihu, saboda a hada ku aure da wani, wato, ga wanda aka tashe shi daga matattu, domin mu haifawa Allah 'ya'ya.
\v 5 Domin sa'adda muke cikin jiki, ana motsa dabi'armu ta zunubi dake cikin jikunan mu ta wurin shari'a domin mu haifi 'ya'ya zuwa mutuwa.
\s5
\v 6 Amma yanzu an kubutar damu daga shari'a, mun mutu daga abin da ya daure mu, domin mu yi bauta cikin sabuntuwar Ruhu, ba cikin tsohon rubutun shari'a ba.
\s5
\v 7 To me zamu ce kenan? ita shari'ar kanta zunubi ce? ba zai taba faruwa ba. Duk da haka. Idan ba ta wurin shari'a ba, ba zan taba sanin zunubi ba, in ba ta wurin shari'a ba. Ba zan taba kyashin abin wani ba, har sai da shari'a tace, "Kada kayi kyashi."
\v 8 Amma zunubi, sai ya dauki zarafi ta wurin dokar, ya jawo dukkan sha'awa dake cikina. Domin in da babu shari'a, zunubi matacce ne.
\s5
\v 9 Ada na rayu sau daya ba tare da shari'a ba, amma da dokar ta zo, sai zunubi ya farfado, ni kuma na mutu.
\v 10 Dokar wadda ta kamata ta kawo rai, sai na same ta matacciya.
\s5
\v 11 Domin zunubin, ya dauki zarafi ta wurin dokar, ya rude ni, kuma ta wurin dokar ya kashe ni.
\v 12 Domin haka, shari'ar na da tsarki, dokar na da tsarki, adalci da kuma kyau.
\s5
\v 13 To abu mai kyau ya zamar mani mutuwa kenan? ba zai taba zama haka ba. Amma zunubi, domin ya nuna shi zunubi ne ta wurin abin da ke mai kyau, sai ya kawo mutuwa a cikina. Wannan ya kasance haka ne domin ta wurin dokar, zunubi ya zama cikakken zunubi.
\v 14 Domin mun san shari'a mai Ruhaniya ce, amma ni ina cikin jiki. An sai da ni karkashin bautar zunubi.
\s5
\v 15 Domin ni ma ban fahimci abin da nake aikatawa ba. Domin abin da nake so in aikata, ba shi nake aikatawa ba, kuma abin da bana so, shi nake aikatawa.
\v 16 Amma idan na aikata abin da bana so, na amince da shari'a kenan, cewar shari'a nada kyau.
\s5
\v 17 Amma yanzu ba ni ke aikata abin ba, amma zunubi da ke zaune a cikina.
\v 18 Domin na san a cikina, wato cikin jikina, babu wani abu mai kyau. Domin marmarin aikata abu mai kyau na tare da ni, amma ba ni iya aikatawa.
\s5
\v 19 Domin abu mai kyau da na ke so in aikata bana iyawa, amma muguntar da ba na so ita na ke aikatawa.
\v 20 To idan na yi abin da ba ni so in aikata, wato kenan ba ni bane ke aikatawa, amma zunubin da ke zaune a cikina.
\v 21 Don haka, sai na iske, akwai ka'ida a cikina dake son aikata abu mai kyau, amma kuma ainihin mugunta na tare dani.
\s5
\v 22 Domin a cikina ina murna da shari'ar Allah.
\v 23 Amma ina ganin wasu ka'idoji daban a gabobin jikina, su na yaki da wannan sabuwar ka'idar da ke cikin tunanina, suna kuma sanya ni bauta ta wurin ka'idar zunubi wadda ke cikin gabobin jikina.
\s5
\v 24 Ni wahalallen mutum ne! wa zai kubutar dani daga wannan jiki na mutuwa?
\v 25 Amma godiya ga Allah ta wurin Yesu Almasihu Ubangijinmu! Domin haka ni kaina a wannan hannu bisa ga tunani na ina bautawa shari'ar Allah. Duk da haka, ta wani gefen ina bautawa ka'idar zunubi da ke tare da jikina.
\s5
\c 8
\p
\v 1 Saboda haka babu kayarwa yanzu ga wadanda ke cikin Almasihu Yesu.
\v 2 Domin ka'idar ruhun rai a cikin Almasihu Yesu ta maishe mu 'yanttatu daga ka'idar zunubi da mutuwa.
\s5
\v 3 Saboda abin da shari'a bata iya aikatawa ba domin kasawa ta wurin jiki, Allah ya yi. Ya aiko da dansa a kamanin jiki mai zunubi domin ya zama hadaya domin zunubi, sai ya yi Allah wadai da zunubi a cikin jiki.
\v 4 Ya yi haka domin bukatar shari'a ta sami cika a cikinmu, mu da muke tafe ba ta gwargwadon jiki ba, amma ta gwargwadon ruhaniya.
\v 5 Wadanda ke rayuwa gwargwadon jiki sukan lura da al'amuran jiki, amma su da ke rayuwa a gwargwadon Ruhu sukan mai da hankali ga al'amuran Ruhu.
\s5
\v 6 To kwallafa rai ga jiki mutuwa ce, amma kwallafa rai ga Ruhu rai ne da salama.
\v 7 Haka yake domin kwallafa rai ga jiki gaba yake da Allah, gama baya biyyaya ga shari'ar Allah, balle ma ya iya.
\v 8 Wadanda ke a jiki ba su iya faranta wa Allah zuciya.
\s5
\v 9 Duk da haka, ba ku cikin jiki amma a cikin Ruhu, idan gaskiya ne, Ruhun Allah na rayuwa cikinku. Amma idan wani ba shi da Ruhun Almasihu, shi ba na sa bane.
\v 10 In Almasihu na cikinka, jikin ka fa matacce ne ga zunubi, amma ruhu na rayuwa bisa ga adalci.
\s5
\v 11 Idan Ruhun wanda ya tada Yesu daga matattu na raye a cikinku, to shi wanda ya tada Almasihu da ga matattu za ya bada rai ga jikinku masu matuwa ta wurin Ruhunsa, da ke rayuwa a cikin ku.
\s5
\v 12 To, 'yan' uwa, muna da hakki amma ba bisa jiki ba, da za mu yi rayuwa bisa ga dabi'ar jiki.
\v 13 Gama idan kun yi rayuwa gwargwadon jiki, za ku mutu kenan, amma idan ta wurin Ruhu ku ka kashe ayyukan jiki, za ku rayu.
\s5
\v 14 Gama duk wadanda Ruhun Allah ke bishe su, su 'ya 'yan Allah ne.
\v 15 Gama ba ku karbi ruhun bauta da ke sa tsoro ba. Maimakon haka, kun karbi ruhun diyanci, ta wurinsa muke tadda murya muna kira, "Abba, Uba!"
\s5
\v 16 kansa na bada shaida tare da namu ruhun cewa mu 'ya'yan Allah ne.
\v 17 Idan mu 'ya'ya ne, ai mu magada ne kenan, magadan Allah. Kuma mu magada ne tare da Almasihu, hakika idan mun sha wahala tare da shi za a kuma daukaka mu tare da shi.
\s5
\v 18 Gama na yi la'akari cewa wahalonin zamanin nan ba su isa a kwatanta su da daukakar da za'a bayyana mana ba.
\v 19 Saboda yadda halitta ke marmarin bayyanuwar 'ya'yan Allah.
\s5
\v 20 Gama an kaskantar da halitta ga banza, ba da nufin ta ba, amma na shi wanda ya kaskantar da ita. Ta na cikin tabbacin alkawarin.
\v 21 Cewa halitta kanta za ta kubuta daga bautar rubewa, kuma za a kawo ta zuwa ga 'yantarwa na yabon daukakar 'ya'yan Allah.
\v 22 Gama mun sani dukan halitta na nishi da zafin nakuda tare har ya zuwa yanzu.
\s5
\v 23 Ba haka kadai ba, amma ko mu kanmu, da ke nunar farko na Ruhu--mu kanmu muna nishi acikin mu, muna jiran diyancinmu, wato ceton jikinmu kenan.
\v 24 Gama ta wanan hakikancewa aka cece mu. Amma dai abin da muke da tabbacin zai faru ba mu gan shi ba tukuna, domin wanene wa ke begen tabbatacce abin da yake gani?
\v 25 Amma idan muna da tabbacin abin da ba mu gani ba tukuna, to sai mu jjira shi da hakuri.
\s5
\v 26 Hakanan, Ruhu kuma ke taimako a kasawarmu. Gama ba mu da san yadda zamu yi addu'a ba, amma Ruhu kansa na roko a madadinmu da nishe-nishen da ba'a iya ambatawa.
\v 27 Shi da ke bidar zuciya yana sane da tunanin Ruhu, domin yana roko a madadin masu badagaskiya ta wurin nufin Allah.
\s5
\v 28 Mun san cewa ga wadanda ke kaunar Allah, yakan aikata dukan al'amura domin su zuwa ga alheri, ga duk wadanda aka kira bisa ga nufinsa. Dukan abubuwa sukan zama alheri.
\v 29 Saboda wadanda ya sani tuntuni su ne ya kardara su zama da kamanin dansa, domin ya zama dan fari a cikin 'yan'uwa masu yawa.
\v 30 Su da ya kaddara, ya kiraye su. Wadanda ya kira, su ya kubutar. Su da ya kubutar, sune kuma ya daukaka.
\s5
\v 31 Me zamu ce game da wadannan al'amura? Idan Allah na tare da mu, wake gaba da mu?
\v 32 Shi da baya hana dansa ba, amma ya bada shi a madadinmu dukka, me zai hana shi bamu dukkan abubuwa a yalwace tare da shi?
\s5
\v 33 Wa zaya kawo wata tuhuma ga zababbu na Allah? Allah ne ke "yantarwa.
\v 34 Wanene ke hukumtawa? Almasihu ne da ya mutu sabili da mu har ma fiye da haka, shi wanda kuma aka tasar. Yana mulki tare da Allah a wuri mai daukaka, shi ne kuma ya ke roko sabili da mu.
\s5
\v 35 Wa za ya raba mu da kaunar Allah? Kunci, ko bacin rai, ko tsanani, ko yunwa, ko tsiraci, ko hadari, ko takobi?
\v 36 Kamar yadda aka rubuta, "Saboda kai ake kisanmu dukkan yini. An mai da mu kamar tumaki yanka."
\s5
\v 37 A dukan al'amuran nan mun fi karfi a ce da mu masu nasara ta wurin shi da ke kaunar mu.
\v 38 Gama na tabata cewa ko mutuwa, ko rai, ko mala'iku, ko mulkoki, ko al'amuran yanzu, ko al'amura masu zuwa, ko iko,
\v 39 ko tsawo, ko zurfi, kai ko wace irin halitta, ba su isa su raba mu da kaunar Allah, da ke a cikin Almasihu Yesu Ubangijin mu ba.
\s5
\c 9
\p
\v 1 Gaskiya ne nake gaskiya nake fada cikin Almasihu. Ba karya nake yi ba. Lamirina, na shaida a cikin Ruhu Mai Tsarki.
\v 2 cewa ina da matukar bakin-ciki da takaici marar karewa a zuciyata.
\s5
\v 3 Dama ace, a la'anta ni, in rabu da Almasihu saboda 'yan'uwana, wato dangina da suke zuriyata bisa ga jiki.
\v 4 Sune Isra'ilawa, sun sami karbuwa, da daukaka, da baiwar shari'a, da yi wa Allah sujada, da alkawarai.
\v 5 Dukkan ubanni nasu ne daga cikinsu Almasihu ya fito bisa ga jiki- wanda shi ke Allah bisa kowa. Yabo ya tabbata a gare shi har abada. Amin.
\s5
\v 6 Amma ba wai alkawarin Allah ya kasa ba ne, ba dukkan Isra'ilawa ne suke Isra'ilawa na gaskiya ba.
\v 7 Haka nan, ba dukkan zuriyar Ibrahim ne 'ya'yansa ba. Amma "ta wurin Ishiyaku ne za'a kira zuriyarka."
\s5
\v 8 Yana nuna mana cewa ba 'ya'yan jiki su ne 'ya'yan Allah ba. Amma 'ya'yan alkawari ne ake kirga su, kuma aka kebe su.
\v 9 Wanna ce kalmar alkawari, "badi warhaka zan dawo, Saratu kuwa zata sami da."
\s5
\v 10 Amma ba wannan kadai ba, bayan Rifkatu ta dauki ciki daga gun mijinta, ubammu Ishiyaku.
\v 11 Yaran nan kafin ma a haife su, balle ma a ce sun yi wani abu mai kyau ko laifi, saboda zaben da Allah yayi, bai danganta da abin da suka yi ba, ko don aiki ba, amma don shine mai kira--
\v 12 kamar yadda Ya ce, mata, "babban zaya yiwa karamin bauta," haka nassi yace,
\v 13 "Kamar yadda aka rubuta: "Yakubu na ke kauna, amma Isuwa na ki shi."
\s5
\v 14 To me zamu ce kenan? Allah ya yi rashin adalci kenan? Ko kadan.
\v 15 Gama ya ce wa Musa, "Ina nuna jinkai ga wanda zan yi wa jinkai, zan ji tausayi ga wanda zan tausaya masa."
\v 16 Saboda haka, ba don wanda ke da aniya ba ne, ko kuwa wanda yake kokari ba, amma saboda Allah mai nuna jinkai.
\s5
\v 17 Gama nassi ya ce da Fir'auna, "Saboda wannan dalilin ne, na tada kai, don in nuna ikona mai karfi a kanka, don sunana ya yadu ga dukkan duniya."
\v 18 Ta haka Allah ya nuna jinkansa ga wanda ya so, ya taurarar da zuciyar wanda ya ga dama.
\s5
\v 19 Za kuce mani, to don me, "Yake kama mu da llaifi? Wa ya taba yin jayayya da nufinsa?"
\v 20 In ma mun duba, kai mutum wanene kai da zaka ja da Allah? Ko abin da aka gina zai ce wa magininsa, "Don me yasa ka ginani haka?"
\v 21 Ko maginin ba shi da iko akan yimbu daya da zai gina tukunya mai daraja, wata kuma tukunyar don kowanne irin aiki?
\s5
\v 22 In ace Allah, dake niyyar nuna fushinsa da ikonsa, ya sanu, sai ya jure da matukar hakuri mai yawa da tukwanen fushi da ya shirya don hallakarwar fa?
\v 23 To ko ma ya yi haka don ya nuna yalwar daukakarsa da take dauke da alheri, wanda ya shirya don daukakarsa tun farko?
\v 24 Zai yiwu ma ya yi haka ne domin mu, mu da ya kira, ba ma daga cikin Yahudawa kadai ba, amma har ma daga cikin al'ummai?
\s5
\v 25 Kamar yadda ya ce a cikin littafin Yusha'u: "zan kira wadanda ba mutanena ba mutanena, da kuma kaunatattunta wadanda ba kaunatattu ba.
\v 26 Zai zama kuma a inda aka ce da su, "ku ba mutanena bane, za a kisa su 'ya'yan Allah mai rai."'
\s5
\v 27 Ishaya ya yi kira game da Isra'ila, "in a ce yawan 'ya'yan Isra'ila zasu zama kamar yashi a bakin teku, ragowarsu ne kawai za su sami ceto.
\v 28 Ubangiji zai tabbatar da cikar kalmarsa a duniya, ba kuwa da dadewa ba.
\v 29 Yadda Ishaya ya rubuta ada, "In da ba Ubangiji mai runduna bai bar mana zuriya ba, da zamu zama kamar Saduma, da kuma an maida mu kamar Gomarata.
\s5
\v 30 To me za mu ce kenan? Ko al'ummai, da ba sa neman adalci, sun samu adalci ta wurin bangaskiya.
\v 31 Amma Isra'ila, wadanda suka nemi adalcinsu ta wurin shari'a, ba su kai ga gaci ba.
\s5
\v 32 To don me? don ba su neme shi da bangaskiya ba, amma ta ayyuka. Sun yi tuntube a kan dutse da zai sa laifi.
\v 33 Kamar yadda aka rubuta, "Ga, shi na ajiye dutse a kan Sihiyona dutsen tuntube mai sa laifi. Ga wanda ya bada gaskiya gare shi ba zai ji kunya ba."
\s5
\c 10
\p
\v 1 'Yan'uwana, muradin zuciyata da dukkan addu'oi na ga Allah dominsu shine don su sami ceton.
\v 2 Domin na shaida game da su cewa suna da kwazo game da Allah, amma ba a kan sani ba.
\v 3 Don, ba su da sani akan adalcin Allah, suna kokarin tabbatar da adalcin kansu. Ba su bada kan su ga adalcin Allah ba.
\s5
\v 4 Gama Almasihu shi ne cikar doka zuwa ga adalci ga dukkan wadanda suka gaskata.
\v 5 Musa kam ya rubuta game da adalci da zai samu ta shari'a: "mutumin da ya aikata adalcin shari'a, zai rayu ta wurin wannan adalcin."
\s5
\v 6 Amma adalcin da ya zo ta wurin bangaskiya yace, "Kada ku ce a zuciyarku, wa zai hau zuwa sama?"(don ya sauko da Almasihu kasa).
\v 7 Kada ku ce, "Wa zai gangara zuwa kasa?" (Wato wa zai fito da Almasihu daga cikin matattu).
\s5
\v 8 Amma me yake cewa? "kalmar tana kusa da kai a cikin bakinka da kuma cikin zuciyarka." Wato kalmar bangaskiya, wadda muke shaidawa.
\v 9 Don idan da bakinka, ka shaida Yesu Ubangiji ne, kuma ka gaskata a zuciyarka cewa Allah ya tashe shi daga matattu, za ka sami ceto.
\v 10 Don da zuciya ne mutum yake gaskatawa zuwa ga adalci, da kuma baki ne yake shaida zuwa ga ceto.
\s5
\v 11 Don nassi na cewa, "Duk wanda ya gaskata da shi ba zai ji kunya ba,"
\v 12 Gama ba bambanci tsakanin Bayahude da Ba'al'ume. Gama dukkansu Ubangijinsu daya ne, Shi mayalwaci ne ga dukkan wanda ya kira shi.
\v 13 Duk wanda ya kira sunan Ubangiji zai sami ceto.
\s5
\v 14 To ta yaya zasu kira ga wanda basu gaskata ba? Kuma ta yaya zasu gaskata ga wanda ba su taba jin labarinsa ba?
\v 15 Kuma ta yaya zasu ji in ba ayi masu wa'azi ba? Kuma ta yaya zasu yi wa'azin in ba an aike su ba? - Kamar yadda yake a rubuce, "Ina misalin kyau na kafafun wadanda ke shaida labarin farin ciki na abubuwa masu kyau!"
\s5
\v 16 Amma ba dukkansu ne suka ji bishara ba. Gama Ishaya ya ce, "Ubangiji, wa ya gaskata da sakon?
\v 17 Saboda haka bangaskiya na zuwa ta wurin ji, jin kuwa daga maganar Almasihu.
\s5
\v 18 Amma na ce, "ko basu ji ba ne? I, tabbas" muryarsu ta kai dukkan duniya, kuma kalmominsu sun kai har karshen duniya."
\s5
\v 19 yau, na ce, "Ko Isra'ila basu sani ba ne?" Da farko Musa ya ce, "Zan sa kuyi fushi da kishi da abin da ba al'umma ba. Abin da nake nufi nan shine al'ummar da basu da fahinta, zan more su, in tayar maku da hankali."
\s5
\v 20 Amma Ishaya da karfin hali ya ce, "Ga wadanda basu neme ni ba suka same ni. Na bayyana ga wadanda basu nemi ni ba.
\v 21 "Amma ga Isra'ila kam ya ce, "na mika hannu na ga masu rashin biyayya dukkan tsawon rana, domin su mutane ne masu taurin kai."
\s5
\c 11
\p
\v 1 Sai na ce, Allah ya ki mutanensa ne? Ba zai taba yiwuwa ba. Domin ni ma ba-Isra'ile ne, na zuriyar Ibrahim, a kabilar Bilyaminu.
\v 2 Allah bai ki mutanen sa da ya ke da rigyasaninsu ba. Ko kun san abin da nassi ya ce game da Iliya, yadda ya kai karar Isra'ila a gaban Allah?
\v 3 Ya ce, "Ubangiji, sun kashe annabawanka, sun rushe alfarwanka kuma, Ni kadai ne na rage, ga shi suna neman su kashe ni."
\s5
\v 4 Amma wacce amsa ce Allah ya ba shi? Ya ce, "Ina da mutane dubu bakwai da na kebe don kaina, da ba su taba rusuna wa Ba'al ba."
\v 5 Ban da haka ma, ban da haka ma a wannan lokacin akwai sauran zabe na alheri.
\s5
\v 6 Amma tun da ta wurin alheri ne, ba ga ayyuka ba. In ba haka ba, alheri ba zai zama alheri ba kenan.
\v 7 Sai kuma me? Abin da Isra'ila ke nema, ba su samu ba, amma zababbun sun same shi, saura kuma sun taurare.
\v 8 Kamar yadda yake a rubuce, "Allah ya ba su ruhun rashin fahimta, ga idanu amma ba za su gani ba, ga kunnuwa amma ba za su ji ba, har zuwa wannan rana."
\s5
\v 9 Dauda kuma ya ce, "bari teburinsu ya zama taru, da tarko, ya zama dutsen tuntube da abin ramako a gare su.
\v 10 Bari idanunsu ya duhunta domin kada su gani; bayansu kuma a duke kullum."
\s5
\v 11 Na ce, "sun yi tuntube domin su fadi ne?" Kada abu kamar haka ya faru. A maimakon haka, juyawa baya da suka yi ya sa, ceto ya zo ga Al'ummai, domin ya sa su kishi.
\v 12 Idan yanzu juyawa baya da sun yi ya zama arziki ga duniya, rashin su kuma arziki ga Al'ummai, yaya kwatancin girmansa zai kasance in sun zo ga kammala?
\s5
\v 13 Yanzu ina magana da ku ku da ke Al'ummai. Tunda yake ni ne manzo ga Al'ummai, ina kuma fahariya cikin hidimata.
\v 14 Yana yiwuwa in sa "yan'uwa na kishi, domin mu ceci wadansu su.
\s5
\v 15 Idan kinsu ya kawo sulhuntawa ga duniya, Karbarsu kuma zata zama yaya? Zata zama rai ne daga mutuwa.
\v 16 'ya'yan farko sunan haka ma kakkabensu yake, Idan saiwar itace na nan, haka ma rassan za su zama.
\s5
\v 17 Amma idan an karye wasu daga cikin rassan, idan ku rassan zaitun na ainihi ne, da aka samu daga cinkinsu, kuma idan kuna da gado tare da su, acikin saiwar itacen zaitun din.
\v 18 Kada ku yi fahariya a kan rassan. Amma idan kuka yi fahariya to ba ku bane masu karfafa saiwar amma saiwar ce ke karfafa ku.
\s5
\v 19 Kana iya cewa, "An karye rassan domin a same ni a ciki."
\v 20 Wannan gaskiya ne! Saboda rashin bangaskiyarsu ne ya sa aka karye su daga rassan, amma ku tsaya da karfi acikin bangaskiyarku. Kada ku dauki kanku fiye da yadda ya kamata, amma ku ji tsoro.
\v 21 Domin idan Allah bai bar ainihin rassan ba, to ba zai bar ku ba.
\s5
\v 22 Ku duba yadda irin ayyuka masu tsananni na Allah. Ta daya hannun kuma, tsanannin kan zoa kan Yahudawa wadanda suka fadi. Har 'ila yau jinkai Allah ya zo maku, idan kun cigaba cikin alherinsa baza a sare ku ba. Amma in kun ki za a sare ku.
\s5
\v 23 Hakanan, idan ba su ci gaba cikin rashin bangaskiyarsu ba, za a maida su cikin itacen. Domin Allah zai iya sake maida su.
\v 24 Idan an yanke ka daga itacen zaitun da ke na jeji, har ya yiwu an hada ka cikin itacen zaitun na ainihi, yaya kuma wadannan Yahudawa wadanda sune ainihin rassan, da za'a maido cikin zaitun da ke na ainihi?
\s5
\v 25 Yan'uwa, ba na so ku kasance cikin duhu a game da wannan asirin, domin kada ku zama da hikima cikin tunaninku. Wannan asirin shine cewa wannan taurarewa ta faru a Isra'ila, har sai da Al'ummai suka shigo ciki.
\s5
\v 26 Ta haka dukan Isra'ila za su tsira, kamar yadda yake a rubuce: "Daga cikin Sihiyona mai Kubutarwa zai fito; Zai kawar da kazanta daga cikin Yakubu.
\v 27 Wannan zai zama alkawarina da su, sa'adda na kawar da zunubansu."
\s5
\v 28 A wani bangaren kuma game da bishara, su makiya ne amamadinku, ta wani fannin kuma bisa ga zabin Allah su kaunattatu ne saboda ubanni.
\v 29 Domin baye-baye da kiran Allah basa canzawa.
\s5
\v 30 Domin ku ma da ba ku yin biyayya ga Allah, amma yanzu kun sami jinkai saboda rashin biyayyarsu.
\v 31 Ta wannan hanyar dai, wadannan Yahudawan sun zama marasa biyayya. Sakamakon haka shine ta wurin jinkan da aka nuna maku, suma su samu jikai yanzu.
\v 32 Domin Allah ya rufe kowa ga rashin biyayya, domin ya nuna jinkai ga kowa.
\s5
\v 33 Ina misalin zurfin wadata da kuma hikima da sani na Allah! Hukunce-hukuncensa sun fi gaban a bincika, hanyoyinsa kuma sun fi gaban ganewa!
\v 34 Don wanene ya san tunanin Ubangiji? Wanene kuma ya zama mai bashi shawara?
\s5
\v 35 Ko kuma, wanene ya fara ba Allah wani abu, domin a biya shi?"
\v 36 Daga wurinsa ne, ta wurinsa ne kuma, a gare shi ne kuma dukan abu suka fito. A gare shi daukaka ta tabbata har abada. Amin.
\s5
\c 12
\p
\v 1 Ina rokon ku 'yan'uwa, saboda yawan jinkan nan na Allah, da ku mika jikunanku hadaya mai rai, mai tsarki kuma abar karba ga Allah. wannan itace hidimarku ta zahiri.
\v 2 Kada ku kamantu da wannan duniya, amma ku sami canzawa ta wurin sabunta tunaninku, kuyi haka don ku san abin da ke nagari, karbabbe, kuma cikakken nufin Allah.
\s5
\v 3 Don ina cewa, saboda alherin da aka bani, ka da waninku ya daukaka kansa fiye da inda Allah ya ajiye shi; a maimakon haka ku kasance da hikima, gwargwadon yadda Allah yaba kowa bangaskiya.
\s5
\v 4 Domin muna da gababuwa da yawa a jiki daya, amma ba dukansu ne ke yin aiki iri daya ba.
\v 5 haka yake a garemu, kamar yadda muke da yawa haka cikin jikin Almasihu, dukkanmu gabobin juna ne.
\s5
\v 6 Muna da baye-baye dabam-dabam bisa ga alherin da aka bayar a gare mu. Idan baiwar wani anabci ne, yayi shi bisa ga iyakar bangaskiyarsa.
\v 7 In wani yana da baiwar hidima, sai yayi hidimarsa. Idan baiwar wani koyarwa ce, yayi koyarwa.
\v 8 Idan baiwar wani karfafawa ce, yayi ta karfafawa; Idan baiwar wani bayarwa ce, yayi ta da hannu sake; Idan baiwar wani shugabanci ne, yayi shi da kula; Idan baiwar wani nuna jinkai ne, yayi shi da sakakkiyar zuciya.
\s5
\v 9 Ku nuna kauna ba tare da riya ba. Ku Ki duk abin da ke mugu ku aikata abin da ke nagari.
\v 10 Akan kaunar 'yan'uwa kuma, ku kaunaci juna yadda ya kamata; akan ban girma kuma, ku ba juna girma.
\s5
\v 11 Akan himma kuma, kada ku yi sanyi; akan ruhu kuma, ku sa kwazo; Game da Ubangiji kuma, ku yi masa hidima.
\v 12 Akan gabagadi kuma, ku yi shi da farin ciki; akan tashin hankali kuma, ku cika da hakuri; akan adu'a kuma, ku nace.
\v 13 Ku zama masu biyan bukatar tsarkaka, ku zama masu karbar baki a gidajenku.
\s5
\v 14 Ku albarkaci masu tsananta maku, kada ku la'anta kowa.
\v 15 Ku yi farinciki tare da masu farinciki; Ku yi hawaye tare da masu hawaye.
\v 16 Tunanin ku ya zama daya. Kada tunaninku ya zama na fahariya, amma ku yi abokantaka da matalauta. Kada wani a cikin ku ya kasance da tunanin yafi kowa.
\s5
\v 17 Kada ku rama mugunta da mugunta. Ku yi ayukan nagarta a gaban kowa.
\v 18 Ku yi duk abin da za ku iya yi domin ku yi zaman salama tare da kowa.
\s5
\v 19 'Yan'uwa, kada ku yi ramako, ku bar Allah ya rama maku. A rubuce yake, "'Ramako nawa ne; zan saka wa kowa,' in ji Ubangiji."
\v 20 "Amma idan makiyin ka na jin yunwa, ba shi abinci ya ci. Idan yana jin kishin ruwa, ba shi ruwan sha. Idan kun yi haka, garwashin wuta ne za ku saka akan duk makiyi."
\v 21 Kada mugunta ta rinjaye ku, amma ku rinjayi mugunta ta wurin yin aikin nagarta.
\s5
\c 13
\p
\v 1 Bari kowa yayi biyayya da hukuma, saboda babu wata hukuma sai dai in tazo daga Allah; mahukunta da suke nan kuwa daga Allah ne.
\v 2 Saboda da haka duk wanda ya ja hukuma ya ja da dokar Allah; kuma dukan wadanda suka ki hukuma za su sha hukunci.
\s5
\v 3 Don kuwa mahukunta ba abin tsoro ne ga masu nagarta ba, amma ga masu aikata laifi. Kuna so ku zama marasa tsoron hukuma? Kuyi abu nagari, zaku sami yabo daga yin hakan.
\v 4 Saboda shi bawan Allah ne a gare ku don nagarta. Amma in kun yi abu mara kyau, kuyi tsoro, saboda ba ya dauke da takobi ba tare da dalili ba. Don shi bawan Allah ne mai saka wa mugu da fushi.
\v 5 Saboda haka dole kuyi biyayya, ba don fushi ba, amma saboda lamiri.
\s5
\v 6 Saboda wannan ne kuke biyan haraji. Don masu mulki bayin Allah ne, wadanda suke yin haka kullum.
\v 7 Ku bawa kowa hakkinsa; haraji ga mai haraji; kudin fito ga mai fito; tsoro ga wanda ya cancanci tsoro; girma ga wanda cancanci girmamawa.
\s5
\v 8 Kada ku rike bashin kowa, sai dai ku kaunaci juna. Domin duk wanda ya kaunaci dan'uwansa ya cika doka.
\v 9 To, "Kada kuyi zina, kada kuyi kisa, kada kuyi sata, kada kuyi kyashi, idan har akwai wata doka kuma, an takaita ta a wannan jimlar: "Ka kaunaci dan'uwanka kamar kanka."
\v 10 Kauna bata cutar da makwabci. Domin haka, kauna tace cikar shari'a.
\s5
\v 11 Saboda wannan, kun san lokaci yayi, ku farka daga barci. Domin cetonmu yana kusa fiye da yadda muke tsammani.
\v 12 Dare yayi nisa, gari ya kusan wayewa. Don haka, sai mu rabu da ayyukan duhu, mu yafa makaman haske.
\s5
\v 13 Sai muyi tafiya yadda ya kamata, kamar da rana, ba a cikin shashanci ko buguwa ba. Kada kuma muyi tafiya cikin fasikanci da muguwar sha'awa, ba kuma cikin husuma ko kishi ba.
\v 14 Amma ku yafa Ubangiji Yesu Almasihu, kada kuwa ku tanadi halin mutumtaka, don biye wa muguwar sha'awarsa.
\s5
\c 14
\p
\v 1 Ku karbi duk wanda yake da rarraunar bangaskiya, ba tare da sukar ra'ayinsa ba.
\v 2 Wani yana da bangaskiyar yaci komai, wani wanda yake da rauni yakanci ganye ne kawai.
\s5
\v 3 Kada wanda yake cin komai ya raina wanda baya cin kowanne abu. Kada kuma wanda baya cin kowanne abu ya shara'anta sauran da suke cin komai. Saboda Allah ya karbe shi.
\v 4 Kai wanene, kai wanene da kake ganin laifin bawan wani? Tsayawarsa ko faduwarsa ai hakin maigidansa ne, amma Ubangiji yana da ikon tsai da shi.
\s5
\v 5 Wani yakan daukaka wata rana fiye da sauran. Wani kuma yana daukan ranakun daidai. Kowa ya zauna a cikin hakakkewa akan ra'ayinsa.
\v 6 Shi wanda ya kula da wata rana, ya kula da ita don Ubangiji. Kuma wanda yaci, yaci ne domin Ubangiji, domin yana yi wa Allah godiya. Shi wanda bai ci ba, yaki ci ne domin Ubangiji. Shima yana yi wa Allah godiya.
\s5
\v 7 Domin babu wanda yake rayuwa don kansa a cikinmu, kuma babu mai mutuwa don kansa.
\v 8 Domin in muna raye, muna raye don Ubangiji. Kuma in mun mutu, mun mutu ne don Ubangiji. Ashe, ko muna raye, ko a mace mu na Ubangiji ne.
\v 9 Domin wannan dalilin Almasihu ya mutu ya kuma tashi, saboda ya zama Ubangiji ga matattu da rayayyu.
\s5
\v 10 Amma ku don me kuke shara'anta yan'uwanku? kai kuma don me kake raina dan'uwanka? Dukan mu zamu tsaya gaban kursiyin shari'ar Allah.
\v 11 Domin a rubuce yake, "Na rantse, "inji Ubangiji", kowacce gwiwa zata rusuna mani, kowanne harshe kuwa zai yabi Allah."
\s5
\v 12 Domin kowannenmu zai fadi abin da shi yayi da bakinsa a gaban Allah.
\v 13 Saboda da haka kada muyi wa juna shari'a, amma maimakon haka ku dauki wannan kudduri, don kada kowa ya zama sanadin tuntunbe ko faduwa ga dan'uwansa.
\s5
\v 14 Na sani na kuma tabbata tsakani na da Ubangiji Yesu, ba abin da yake mara tsarki ga asalinsa. Sai dai ga wanda ya dauke shi marar tsarki ne yake zama marar tsarki.
\v 15 Idan har abincinka na cutar da dan'uwanka, ba ka tafiya cikin kauna. Kada ka lalata wanda Yesu ya mutu domin sa da abincinka.
\s5
\v 16 Saboda haka, kada abubuwan da aka dauka kyawawa su zama abin zargi ga wadansu.
\v 17 Saboda mulkin Allah ba maganar ci da sha ba ne, amma game da adalci ne, salama, da farin ciki a cikin Ruhu Mai Tsarki.
\s5
\v 18 Domin wanda yake bautar Almasihu a wannan hanya, karbabbe ne ga Allah, kuma jama'a sun yarda da shi.
\v 19 Don haka, mu nemi abubuwa na salama da abubuwan da zasu gina juna.
\s5
\v 20 Kada ku lalata aikin Allah don abinci. Komai yana da tsarki, amma kaiton mutumin da yake cin abin da zai sa shi ya fadi.
\v 21 Bashi da kyau a ci nama ko a sha ruwan inabi, ko duk abin da zai jawo faduwar dan'uwanka.
\s5
\v 22 Wannan bangaskiyar da kuke da ita, ku adana ta tsakaninku da Allah. Mai albarka ne wanda zuciyarsa bata da laifi akan abin da hankalinsa ya ga daidai ne.
\v 23 Duk wanda yayi shakka amma kuma yaci, ya sani yayi laifi kenan, domin ba tare da bangaskiya bane. Duk abin da ba na bangaskya bane zunubi ne.
\s5
\c 15
\p
\v 1 Yanzu mu da muke da karfi ya kamata mu dau nauyi raunana, kuma bai dace mu nuna son kai ba.
\v 2 Bari kowannenmu ya faranta wa makwabcinsa rai, domin wannan yana da kyau, don a gina shi.
\s5
\v 3 Domin Almasihu bai faranta wa kansa rai ba. Kamar yadda aka rubuta, "zagin da wadansu suka yi masa ya sauka a kaina."
\v 4 Don abin da aka rubuta a baya an rubuta ne domin a gargade mu, domin ta hakuri da karfafawar litattafai mu sami karfi.
\s5
\v 5 Yanzu Allah mai hakuri da karfafawa ya baku zuciya daya ta zaman tare da juna bisa ga halin Yesu Almasihu.
\v 6 Domin ya yi haka ne da zuciya daya domin ku yi yabo da bakinku daya.
\v 7 Domin ku karbi juna, kamar yadda Yesu ma ya karbe ku domin a daukaka Allah.
\s5
\v 8 Saboda na ce an mai da Almasihu bawan kaciya a madadin gaskiyar Allah. Ya yi wannan ne don a tabbatar da alkawarai da aka ba kakanin kakaninmu.
\v 9 Domin Al'umai su daukaka Allah saboda jinkansa, kamar yadda ya ke a arubuce, "Domin ta haka zan yabe ka cikin Al'umai in yi wakar yabon sunanka."
\s5
\v 10 Kuma an ce. "Ku yi faranciki, ku Al'ummai tare da mutanensa."
\v 11 Kuma." Ku yabi Ubangiji, ku dukan Al'ummai; bari dukan mutane su yabe shi."
\s5
\v 12 Kuma, Ishaya ya ce "Za a sami tsatson Yessi, wanda zai tashi ya yi mulki a kan Al'umai, Al'umai za su sami karfin hali a cikinsa."
\s5
\v 13 Yanzu Allah mai karfafawa ya cika ku da dukkan farin ciki salama, saboda da bangaskiyarku, domin ku sami cikkakiyar karafafawa, ta wurin ikon Ruhu Mai Tsarki.
\s5
\v 14 Ni kaina na amince da ku, yan'uwa. Kuma na amince cewa ku da kanku kuna cike da alheri, cike da dukkan sani. Na amince cewa za ku sami zarafi ku gargadi juna.
\s5
\v 15 Amma ina rubuta maku da gabagadi kan wadansu abubuwa, domin in tunasheku, saboda baiwar da aka bani daga wurin Allah.
\v 16 Cewa baiwar ta sa na zama bawan Almasihu Yesu da aka aika ga Al'ummai, limami na bisharar Allah. Zan yi wannan saboda baikon Al'ummai ya zama karbabbe, kuma kebbabe ga Allah ta wurin Ruhu Mai Tsarki.
\s5
\v 17 Don haka ina jin dadi cikin Yesu Almasihu da abubuwa na Allah.
\v 18 Domin ba ni da abin da zan ce, sai abin da Yesu ya aikata ta wurina, domin Al'ummai su yi biyayya ta magana da aiki.
\v 19 Ta wurin alamu, da al'jibai, da ikon Ruhu Mai Tsarki. Daga Urushalima, da kewaye har zuwa Ilirikum, an kai bisharar Almasihu ko'ina dukka.
\s5
\v 20 A cikin hanyar nan, burina in sanar da bishara, amma a inda ba a san Yesu ta wurin sunansa ba, don kada in sa gini akan harshashi wani.
\v 21 Kamar yadda yake a rubuce."Wadanda ba a taba fada wa labarinsa ba, su gane. Wadanda ba su taba jin labarinsa ba su fahimta."
\s5
\v 22 Saboda an hana ni zuwa wurin ku a lokatai da dama.
\v 23 Amma yanzu bani da sauran wani wuri a lardin nan, kuma cikin shekaru masu yawa ina da marmarin in zo wurin ku.
\s5
\v 24 Duk lokacin da zan tafi Asbaniya ina begen ganin ku yayin wucewa, don ku raka ni bayan na ji dadin zama da ku na dan lokaci.
\v 25 Amma yanzu ina tafiya Urushalima don in yi wa tsarkaka hidima.
\s5
\v 26 Domin abin farinciki ne ga mutanen Makidoniya da Akaya su yi bayarwa domin gajiyayyu masu bada gaskiya wadanda suke a Urushalima.
\v 27 Suna jin dadi domin hakika kamar bashi ne a kansu. Domin Al'ummai sun yi tarayya da su cikin ayyukan ruhaniya, ya zama hakki a kansu su ma su taimake su da abubuwa.
\s5
\v 28 Domin lokacin da na gama basu kudin, zan zo gareku a hanyata ta zuwa Asbaniya.
\v 29 Na san cewa lokacin da na zo gareku, zan zo da cikakkun albarku na Almasihu.
\s5
\v 30 Yanzu ina rokonku, yan'uwa, ta wurin Ubangiji Yesu Almasihu, da kaunar Ruhu Mai Tsarki, ku yi ta fama tare da ni a cikin yin addu'o, inku ga Allah saboda ni.
\v 31 Kuyi haka saboda in tsira daga wadanda suke masu biyayya ga Yahudiya, domin kuma hidimata saboda Urushalima ta zama karbabbiya.
\v 32 Ku yi addu'a cewa in zo wurinku da farinciki ta wurin nufin Allah, cewa tare da ni da ku, mu sami hutu.
\s5
\v 33 Allah na salama ya kasance tare da ku duka. Amin.
\s5
\c 16
\p
\v 1 Ina gabatar muku da fibi 'yar'uwarmu, wanda take hidima a Ikilisiya dake cikin Kankiriya.
\v 2 Domin ku karbe ta cikin Ubangij. A hanyar da ta dace ga masu bada gaskiya, ku tsaya tare da ita cikin kowacce bukata. Domin ita da kanta ta zama da taimako ga masu yawa, har da ni ma.
\s5
\v 3 Ku gai da Bilkisu da Akila abokan aiki cikin Yesu Almasihu.
\v 4 Wadanda sabo da ni suka sadaukar da ransu. Ina godiya garesu, ba ni kadai ba, amma kuma da dukan Ikilisiyoyin Al 'mmai.
\v 5 Gaida Ikilisiya da ke gidansu. Ku gai da Abainitas kaunataccena. Wanda shi ya fara bada gaskiya ga Almasihu a Asiya.
\s5
\v 6 Ku gai da Maryamu, wadda ta yi maku aiki tukuru.
\v 7 Ku gai da Andaranikas da Yuniyas, yan'uwana da abokan kurkukuna. Su sanannu ne cikin manzani, wadanda suke cikin Almasihu kafin ni.
\v 8 Ku gai da Amfiliyas kaunatace na cikin Ubangiji.
\s5
\v 9 Ku gai da Urbanas abokin aikinmu cikin Almasihu, da Istakis kaunataccena.
\v 10 Ku gai da Abalis amintacce cikin Almasihu. Ku gai da wadanda su ke gidan Aristobulus.
\v 11 Ku gai da Hirudiya, dan'uwa na, da wadanda ke gidan Narkissa, wadanda ke cikin Ubangiji.
\s5
\v 12 Ku gai da Tarafina daTarafusa, masu aikin Ubangiji.
\v 13 Ku gai da Barsisa kaunatacciya, wadda ta yi aikin Ubangiji da yawa. Ku gai da Rufas zababbe cikin Ubangiji da mamarsa da ni.
\v 14 Ku gai da Asinkiritas da Filiguna da Hamis da Baturobas da Hamisu da kuma yan'uwa da ke tare da su.
\s5
\v 15 Ku gai da Filolugus daYuliya da Niriyas da yan'uwansa, da Ulumfas da kuma dukan tsarkaka da ke tare su.
\v 16 Ku gaggai da juna da tsatsarkar sumba. Dukan Ikilisiyoyin Almasihu na gaishe ku.
\s5
\v 17 Yanzu ina rokon ku, yan'wa, ku yi tunani fa game da masu kawo rabuwa da tuntube. Sabanin koyarwar da ku ka koya. Ku yi nesa da su.
\v 18 Domin irin mutanen nan ba sa bauta wa Ubangiji Yesu, sai dai tumbinsu. Ta dadin bakinsu suke rudin zuciyar marasa laifi.
\s5
\v 19 Domin rayuwar biyayyarku takai ga kunnen kowa, na yi farin ciki da ku, amma ina so ku zama da hikima game da abin ya ke mai kyau, ku zama marasa laifi ga abin da ke na mugunta.
\v 20 Allah na salama zai sa ku tattake Shaidan da sauri kalkashin sawayen ku. Alherin Ubangijin mu Yesu Almasihu ya kasance tare da ku.
\s5
\v 21 Timoti abokin aikina, yana gaishe ku, haka Lukiyas da Yason da Susibataras da kuma yan'uwana.
\v 22 Ni Tartiyas wanda ya rubuta wasikan nan, na gaisheku cikin Ubangiji.
\s5
\v 23 Gayus mai masaukina da kuma dukan Ikilisiya, suna gaishe ku. Arastas ma'ajin birni na gaishe ku, da Kwartus dan'uwanmu.
\v 24 Alherin Ubangijinmu Yesu Almasihu ya kasance tare da ku dukka. Amin.
\s5
\v 25 Yanzu ga wanda ke da Ikon karfafa ku bisa ga bisharata da wa'azin Yesu Almasihu, wanda ta gare shi ne aka bayyana asiran nan da suke boye tun da dadewa,
\v 26 amma yanzu sanannu ne ta wurin litattafan Annabawa bisa umarnin Allah madauwami, domin biyayyar bangaskiya cikin Al'ummai dukka.
\s5
\v 27 Ga Allah mai hikima kadai, ta wurin Yesu Almasihu daukaka ta tabbata har abada. Amin.