ha_ulb/45-ACT.usfm

1871 lines
128 KiB
Plaintext

\id ACT
\ide UTF-8
\h Ayyukan Manzanni
\toc1 Ayyukan Manzanni
\toc2 Ayyukan Manzanni
\toc3 act
\mt Ayyukan Manzanni
\s5
\c 1
\p
\v 1 Littafin da na rubuta da farko, Tiyofilos, ya fadi abubuwan da Yesu ya fara yi ya kuma koyar,
\v 2 har zuwa ranar da aka karbe shi zuwa sama. Wannan kuwa bayan da ya ba da umarni ga zababbun manzanninsa ta wurin Ruhu Mai Tsarki.
\v 3 Bayan ya sha wahala, ya bayyana kan sa da rai a garesu, da alamu da dama masu gamsarwa. Kwana arba'in ya baiyana kansa a garesu yana yi masu magana game da mulkin Allah.
\s5
\v 4 Yayin da yana zaune tare da su ya basu umarni cewa kada su bar Urushalima, amma su jira alkawarin Uban, wanda ya ce, "Kun ji daga gare ni,
\v 5 cewa Yahaya babu shakka ya yi baftisma da ruwa, amma ku za a yi maku baftisma da Ruhu Mai Tsarki nan da kwanaki kadan."
\s5
\v 6 Sa'adda suna tare suka tambaye shi, "Ubangiji, a wannan lokaci ne za ka maido da mulki ga Isra'ila?"
\v 7 Ya ce masu, "Ba naku bane ku san lokaci ko sa'a wanda Uba ya shirya ta wurin ikonsa.
\v 8 Amma za ku karbi iko, idan Ruhu Mai Tsarki ya zo bisanku, sa'annan za ku zama shaidu na cikin Urushalima da kuma cikin dukan Yahudiya da Samariya, har ya zuwa karshen duniya."
\s5
\v 9 Lokacin da Ubangiji Yesu ya fadi wadannan abubuwa, yayin da suna kallon sama, sai aka dauke shi zuwa sama, kuma girgije ya boye shi daga idanunsu.
\v 10 Da suka dinga kallon sama yayin da ya tafi, nan da nan, mazaje biyu suka tsaya a gabansu cikin fararen tufafi.
\v 11 Suka ce, "Ku mazajen Galili me yasa ku ke tsaye a nan kuna kallon sama? Wannan Yesu wanda ya hau zuwa sama zai dawo kamar yadda kuka gan shi yana tafiya zuwa sama."
\s5
\v 12 Da suka dawo Urushalima daga dutsen Zaitun, wanda ke kusa da Urushalima, tafiyar Asabaci daya ne.
\v 13 Da suka iso, sai suka haye zuwa cikin bene inda suke da zama. Sune su Bitrus, Yahaya, Yakubu, Andarawus, Filibus, Toma, Bartalamawus, Matiyu, Yakubu dan Alfa, Siman mai tsattsauran ra'ayi, kuma da Yahuza dan Yakubu.
\v 14 Dukansu kuwa suka hada kai gaba daya, yayin da suka ci gaba da naciya cikin addu'a. Tare da su kuma akwai mata, Maryamu mahaifiyar Yesu, da kuma 'yan'uwansa.
\s5
\v 15 A cikin wadannan kwanaki Bitrus ya tashi tsaye a tsakiyar 'yan'uwa, kimanin mutane dari da ashirin, ya ce,
\v 16 " 'Yan'uwa, akwai bukatar Nassi ya cika, wanda Ruhu Mai Tsarki ya fada a baya ta bakin Dauda game da Yahuza, wanda ya jagoranci wadanda suka kama Yesu
\s5
\v 17 Domin yana daya daga cikinmu kuma ya karbi rabonsa na ladan wannan hidima,"
\v 18 (Wannan mutum fa ya sai wa kansa fili da cinikin da ya yi na muguntarsa, kuma a nan ya fado da ka, cikinsa ya fashe, hanjinsa suka zubo waje.
\v 19 Duka mazaunan Urushalima suka ji wannan, saboda haka suka kira wannan fili da harshensu "Akeldama" wato, "Filin Jini.")
\s5
\v 20 "Domin an rubuta a littafin Zabura, 'Bari filinsa ya zama kufai, kada a bar kowa ya zauna wurin,'kuma, 'Bari wani ya dauki matsayinsa na shugabanci.'
\s5
\v 21 Saboda haka ya zama dole, daya daga cikin wadanda suke tare da mu tun lokacin da Ubangiji Yesu yana shiga da fita, a tsakaninmu,
\v 22 farawa daga baftismar yahaya har zuwa ranar da aka dauke shi daga wurinmu zuwa sama, ya zama daya daga cikin mu wurin shaidar tashinsa."
\v 23 Suka gabatar da mutum biyu, Yusufu wanda ake kira Barsabbas, wanda kuma aka yiwa suna Justus, da kuma Matayas.
\s5
\v 24 Su ka yi addu'a suka ce, "Ubangiji, kai ka san zuciyar dukan mutane, ka bayyana mana wanda ka zaba cikin su biyun nan
\v 25 Domin ya dauki gurbin da kuma manzancin daga inda Yahuza ya kauce zuwa nashi waje"
\v 26 suka jefa kuri'a a kansu; zabe ya fada kan Matayas kuma suka lissafta shi tare da manzanni sha dayan.
\s5
\c 2
\p
\v 1 Da ranar Fentikos ta zo, dukansu suna tare wuri daya.
\v 2 Nan da nan sai ga wata kara daga sama kamar ta babbar iska, kuma ta sauko ta cika duka gidan inda suke zaune.
\v 3 Sai ga wasu harsuna kamar na wuta sun bayyana a garesu aka rarraba su, kuma suka zauna bisa kowannensu.
\v 4 Dukansu suka cika da Ruhu Mai Tsarki suka fara magana da wadansu harsuna, yadda Ruhu ya ba su iko su yi magana.
\s5
\v 5 A lokacin akwai Yahudawa dake zaune a Urushalima, mutanen Allah, daga kowace kasa karkashin sama.
\v 6 Da suka ji wannan kara jama'a duk suka taru suka rude saboda kowannensu ya ji suna magana da harshensa.
\v 7 Suka yi mamaki matuka; suka ce, "Lallai, wadannan duka ba Galiliyawa ba ne?
\s5
\v 8 Yaya mu ke jinsu duka, kowannensu na magana a cikin harshen da aka haife mu?
\v 9 Fisiyawa da Mediyawa da Elimawa, da Yahudawa da Kafadokiya, cikin Fontus da Asiya,
\v 10 cikin Firgia da Bamfiliya, cikin Masar da yankunan Libiya ta wajen Sur, da baki daga Roma,
\v 11 Yahudawa da tubabbun cikin Yahudanci, Kiretawa da Larabawa, duk munji su suna fadi a harshenmu game da manyan ayyukan Allah."
\s5
\v 12 Dukansu suka yi mamaki suka rikice; suka ce da junansu, "Menene ma'anar wannan?"
\v 13 Amma wasu suka yi ba'a suka ce, "Sun bugu ne da sabon ruwan inabi."
\s5
\v 14 Amma Bitrus ya tashi tare da sha dayan, ya daga murya ya ce da su, "Mutanen Yahuda da dukanku dake zaune a Urushalima, bari ku san wannan; ku saurari maganata.
\v 15 Domin wadannan mutanen ba buguwa suka yi ba yadda kuke zato, domin yanzu karfe tara ne na safe kawai.
\s5
\v 16 Amma wannan shine abinda aka fada ta wurin annabi Yowel.
\v 17 Allah ya ce, 'Haka zai kasance a kwanakin karshe, zan zubo Ruhuna a kan dukan mutane, 'ya'yanku maza da mata za su yi anabci, kuma samarinku za su ga wahayoyi, kuma tsofaffinku za su yi mafarkai.
\s5
\v 18 Haka kuma a bisa bayi na maza da mata, a kwanakin nan zan zubo da Ruhuna, kuma za su yi anabci.
\v 19 Zan nuna al'ajibai a sararin sama da kuma alamu a bisa duniya, jini da wuta, da girgije.
\s5
\v 20 Rana zata juya ta koma duhu kuma wata ya koma jini, kafin Babbar ranan nan ta Ubangiji ta zo.
\v 21 Zai kuma zama dukan wanda ya kira ga sunan Ubangiji zai sami ceto.
\s5
\v 22 Mutanen Isra'ila, ku saurari wadannan magana. Yesu Banazare, mutumin da Allah ya tabbatar da shi gareku ta wurin manyan ayyuka da ban mamaki da alamu da Allah ya yi ta wurinsa a tsakiyarku, kamar yadda ku da kanku kuka sani.
\v 23 Saboda tabbataccen shiri da riga sani na Allah, aka bayar dashi, ku kuma, ta hannun mutane 'yan tawaye, kuka gicciye shi kuma kuka kashe shi.
\v 24 Wanda Allah ya tayar, bayan ya cire zafin mutuwa daga gareshi, saboda ba zai yiwu ba ta rike shi.
\s5
\v 25 Gama, game da shi, 'Ina ganin Ubangiji a gabana ko yaushe, domin yana gefen hannun damana saboda kada in firgita.
\v 26 Saboda haka zuciyata na farin ciki harshena yana yin murna. Kuma, jikina zai zauna gabagadi.
\s5
\v 27 Gama ba za ka watsar da raina a lahira ba, ba kuwa za ka bar Mai Tsarkinka ya ga ruba ba.
\v 28 Ka bayyana mani hanyar rai; da fuskarka zaka cika ni da farin ciki.
\s5
\v 29 'Yan'uwa, zan yi magana da ku gabagadi game da baba Dauda: ya mutu kuma aka bizne shi, kuma kabarinsa na nan tare da mu har yau.
\v 30 Domin haka, don shi annabi ne kuma ya san Allah ya yi masa alkawari da rantsuwa cewa daga cikin zuriyarsa zai sanya wani bisa kursiyinsa.
\v 31 Ya hango wannan al'amari kuma ya yi magana game da tashin Almasihu, 'Ba ayi watsi da shi ba a lahira, kuma jikinsa bai ga rubewa ba.'
\s5
\v 32 Wannan Yesun - Allah ya tashe shi, wanda dukanmu shaidu ne.
\v 33 Saboda haka yadda aka tashe shi zuwa hannun dama na Allah kuma ya karbi alkawarin Ruhu Mai Tsarki daga wurin Uba, shine ya zubo mana wannan da kuke gani kuma kuke ji.
\s5
\v 34 Dauda bai hau zuwa sama ba, amma ya ce, "Ubangiji ya ce wa Ubangijina, "Zauna hannun dama na,
\v 35 har sai na maida makiyanka abin takawar sawunka.'"
\v 36 Saboda haka, bari gidan Isra'ila su sani tabbas wannan Yesun wanda kuka gicciye, Allah ya maishe shi Ubangiji da kuma Almasihu.
\s5
\v 37 Da suka ji haka sai suka soku a zukatansu, suka cewa Bitrus da sauran manzanni, '"Yan'uwa me za mu yi?"
\v 38 Sai Bitrus ya ce masu, "Ku tuba ayi wa kowannenku baftisma, cikin sunan Yesu Almasihu domin gafarar zunubanku, kuma za ku karbi baiwar Ruhu Mai Tsarki.
\v 39 Domin alkawarin a gareku ne da 'ya'yanku da duk wadanda ke nesa, dukan iyakar mutanen da Ubangiji Allahnmu zai kira."
\s5
\v 40 Da maganganu da yawa ya ba da shaida kuma ya karfafa su; ya ce, "Ku ceci kan ku daga wannan muguwar tsara."
\v 41 Sai suka karbi maganar sa kuma aka yi ma su baftisma, a wannan rana kuma aka sami karin rayuka wajen dubu uku.
\v 42 Su ka cigaba cikin koyarwar manzanni da zumunta, cikin kakkaryawar gurasa da kuma cikin addu'o'i.
\s5
\v 43 Tsoro ya sauko bisa kowane rai, kuma aka yi abubuwan ban mamaki da alamu da yawa ta wurin manzannin.
\v 44 Duka wadanda suka ba da gaskiya suna tare kuma komai nasu na kowanensu ne,
\v 45 kuma suka saida kadarorinsu da mallakarsu kuma suka rarrabawa kowa, bisa ga irin bukatar da kowannensu yake da ita.
\s5
\v 46 A kowace rana suka cigaba tare da nufi daya a cikin haikali, suna kakkarya gurasa a gidaje, kuma suna raba abinci tsakaninsu cikin farin ciki da tawali'u a zuciya;
\v 47 Suna yabon Allah kuma suna da tagomashi a gaban dukan mutane. Ubangiji kuma kullum yana kara masu wadanda suke samun ceto.
\s5
\c 3
\p
\v 1 Sa'adda Bitrus da Yahaya suna hanya zuwa haikali a lokacin addu'ar karfe uku.
\v 2 Wani mutum, gurgu ne tun daga haihuwa, ana daukar sa kulluyomi zuwa kofar haikali da ake kira Kyakkyawa, domin bara gun mutanen da ke shiga haikalin.
\v 3 Da ya ga Bitrus da Yahaya suna shiga haikalin, sai ya roke su sadaka.
\s5
\v 4 Bitrus da Yahaya kuwa suka zuba masa ido, Bitrus ya ce, "Ka dube mu."
\v 5 Gurgun nan kuwa ya dube su, yana tsammanin zai sami wani abu a wurin su.
\v 6 Amma Bitrus ya ce, "Azurfa da Zinariya ba ni da su, amma abin da nake da shi, zan baka. A cikin sunan Yesu Almasihu Banazare, Yi tafiya"
\s5
\v 7 Bitrus ya kama hannun damarsa, ya daga shi; nan da nan kafafunsa da kashin idon sawayensa suka samu karfi.
\v 8 Da gurgun ya yunkura, ya mike tsaye sai ya fara takawa; ya shiga haikali tare da Bitrus da Yahaya, yana takawa, yana tsalle, yana kuma girmama Allah.
\s5
\v 9 Dukan mutane suka gan shi yana tafiya yana kuma yabon Allah.
\v 10 Sun lura cewa, shine mutumin da ke zama yana bara a Kyakyawar kofar haikali; sai suka cika da mamaki domin abin da ya faru.
\s5
\v 11 Yayin da yake rike da Bitrus da Yahaya, dukan jama'a suka matso wurinsu, a gefen dakalin Sulaimanu, suna ta mamaki kwarai.
\v 12 Da Bitrus ya ga haka ya amsa wa jama'ar, "Ya ku mutanen Isra'ila, don me ku ke mamaki?" Don me ku ka zura mana ido, kamar mu ne muka sa shi ya yi tafiya da ikon kanmu ko adalcin mu?
\s5
\v 13 Allah na Ibrahim, da Ishaku, da Yakubu, Allah na iyayenmu ya girmama bawansa Yesu. Shi kuka ki kun kuma bashe shi a gaban Bilatus da ya so ya sake shi.
\v 14 Kuka ki Mai Tsarkin nan, Mai Adalcin, maimakon haka kuka ce a sakkar maku mai kisan kai.
\s5
\v 15 Kun kashe mai ba da rai, wanda Allah ya tayar daga matattu, mu kuwa shaidu ne ga wannan al'amari.
\v 16 Yanzu, ta bangaskiya ga sunansa - wannan mutum da kuke gani kuma kun san shi - ta wurin wannan sunan ne ya sami karfi. Bangaskiya cikin Yesu ta ba shi cikakkiyar lafiya, a gabanku duka.
\s5
\v 17 Ya ku 'yan'uwa, na san kun yi haka ne cikin rashin sani, yadda shugabaninku suka yi.
\v 18 Amma duk abubuwan da Allah ya fada ta bakin dukan anabawansa, cewa Almasihunsa zai sha wahala, yanzu ya cika.
\s5
\v 19 Saboda haka, Ku tuba, ku juyo, domin a shafe zunubanku, domin lokacin sabuntuwa daga wurin Ubangiji ya zo;
\v 20 domin a aiko maku da Almasihu wanda aka kaddara wato, Yesu.
\s5
\v 21 Shine wanda dole sama ta karbe shi har zuwa lokacin komo da dukan abubuwa, game da abubuwan da Allah ya fada tun da ta bakin annabawansa tsarkaka.
\v 22 Musa hakika ya ce, 'Ubangiji Allah zai tayar maku da wani annabi kamar ni daga cikin, 'yan'uwanku. Za ku saurari dukan abin da zai fada maku.
\v 23 Zai kasance kowanne mutum da bai saurari annabin nan ba za a kau da shi gabadaya daga cikin mutanensa.'
\s5
\v 24 I, dukan annabawa tun daga Sama'ila da wadanda suka zo bayansa, sun yi magana sun ambaci wadannan kwanaki.
\v 25 Kune 'ya'yan annabawa da na alkawari wanda Allah ya yi da kakanninku, yadda ya ce wa Ibrahim, 'Daga zuriyarka dukan al'uman duniya za su sami albarka.'
\v 26 Bayan da Allah ya ta da bawansa, a gareku ne ya fara aiko shi, domin ya albarkace ku tawurin juyadda kowannenku daga muguntarsa."
\s5
\c 4
\p
\v 1 Yayin da Bitrus da Yahaya suna kan magana da mutanen, sai firistoci da shugaban masu tsaron Haikali da kuma Sadukiyawa suka afko masu.
\v 2 Sun damu sosai domin Bitrus da Yahaya suna koyar da mutane game da Yesu kuma suna shelar tashinsa daga matattu.
\v 3 Suka kama su suka jefa kurkuku sai washegari, domin yamma ta riga ta yi.
\v 4 Amma mutane da yawa da suka ji sakon suka ba da gaskiya; kimanin mazaje dubu biyar ne kuwa suka ba da gaskiya.
\s5
\v 5 Washegari, da shugabaninsu, da dattawansu, da Marubuta suka taru a Urushalima.
\v 6 Anas babban firist, yana nan, da Kayafa, da Yahaya da Iskandari, da dukan dangin babban firist
\v 7 Da suka kawo Bitrus da Yahaya a tsakiyarsu sai suka tambaye su, "Da wanne iko, ko cikin wanne suna k ka yi haka?"
\s5
\v 8 Sai Bitrus, cike da Ruhu Mai Tsarki, ya ce, "Ku shugabanni da dattawan jama'a,
\v 9 idan mu yau ana tuhumarmu saboda aikin kirki da aka yi ga wannan mara lafiya - ta yaya wannan mutum ya sami lafiya?
\v 10 Bari ku da dukan mutanen Isra'ila, ku san wannan, cikin sunan Yesu Almasihu Banazare, wanda kuka giciye, wanda Allah ya tayar daga matattu ta dalilinsa ne wannan mutumin yake tsaye a gaban ku lafiyayye.
\s5
\v 11 Yesu Almasihu ne dutsen da ku magina kuka ki, amma an mai da shi kan gini.
\v 12 Babu ceto daga kowanne mutum, domin babu wani suna da aka bayar karkashin sama, a cikin mutane wanda ta wurinsa za a iya samu ceto."
\s5
\v 13 Sa'adda, suka ga karfin halin Bitrus da Yahaya, suka gane mutane ne talakawa marasa ilimi, sai suka yi mamaki, suka kuma lura suka gane Bitrus da Yahaya sun kasance tare da Yesu.
\v 14 Da yake suna ganin mutumin nan da aka warkar tare da su, sai suka rasa abin yi.
\s5
\v 15 Amma bayan sun fitar da manzannin daga majalisa sai suka tattauna a tsakaninsu.
\v 16 Suka ce, "Yaya za mu yi da wadannan mutane? Babu shakka aikin al'ajibi ya faru ta wurinsu, kuma sananne ne ga dukan mazauna Urushalima, kuma ba mu da iko mu musanci haka.
\v 17 Amma saboda kada ya cigaba da yaduwa cikin mutane, bari mu yi masu kashedi kada su kara magana da kowa cikin wannan suna."
\v 18 Suka kira Bitrus da Yahaya suka dokace su kada su kara magana ko kuma koyarwa ko kadan a cikin sunan Yesu.
\s5
\v 19 Amma Bitrus da Yahaya suka amsa suka ce, "Ko ya yi daidai a gaban Allah mu yi maku biyayya fiye da shi, ku hukunta.
\v 20 Baza mu iya daina magana game da abubuwan da muka ji kuma muka gani ba."
\s5
\v 21 Bayan sun sake yi wa Bitrus da yahaya kashedi, sai suka sake su, su tafi. Domin ba su iya samu wata hujja da za su hore su a kai ba, domin dukan mutane suna yabon Allah saboda abin da ya faru.
\v 22 Mutumin da ya sami wannan al'ajibi na warkarwa yana sama da shekara arba'in.
\s5
\v 23 Bayan an sake su, Bitrus da Yahaya suka zo cikin mutanensu suka ba da rahoton duk abin da manyan firistoci da dattawa suka fada masu.
\v 24 Da suka ji haka, suka daga muryarsu tare ga Allah suka ce, "Ubangiji, kai da ka yi sama da duniya da teku da duk abin da ke cikinsu,
\v 25 kai wanda ta wurin Ruhu Mai Tsarki ta bakin ubanmu Dauda bawanka, ya ce, 'Me ya sa al'ummai suka tunzura, kuma mutane suke tunanin abubuwan banza?
\s5
\v 26 Sarakunan duniya sun hada kansu tare, kuma shugabanninsu sun taru don su yi gaba da Ubangiji, da kuma Almasihunsa.'
\s5
\v 27 Hakika, Hiridus da Buntus Bilatus, tare da al'ummai da mutanen Isra'ila, sun taru a wannan birni domin su yi jayayya da bawanka mai tsarki Yesu, shafaffe.
\v 28 Sun taru domin su aiwatar da dukan abin da hannunka da nufinka ya shirya zai faru.
\s5
\v 29 Yanzu, Ya Ubangiji ka dubi kashedin su, ka ba bayin ka ikon furta maganar ka gabagadi.
\v 30 Sa'adda ka mika hannunka domin warkarwa, alamu da al'ajibai su faru ta wurin sunan bawanka mai tsarki Yesu."
\v 31 Bayan sun gama addu'a, wurin da suka taru ya girgiza, suka cika da Ruhu Mai Tsarki, suka furta maganar Allah gabagadi.
\s5
\v 32 Babban taron da suka ba da gaskiya kansu hade yake; kuma ba wanda ya ce da abinda ya mallaka nasa ne; maimakon haka, komai na su daya ne.
\v 33 Da iko mai karfi manzannin suka yi shelar shaidarsu game da tashin Yesu Ubangiji daga matattu, babban alheri kuma na bisansu.
\s5
\v 34 Babu wani a cikinsu wanda ya rasa komai, domin masu filaye da gidaje suka sayar suka kawo kudin abin da suka sayar
\v 35 sai suka kawo kudin gaban manzanni. Aka rarraba wa kowanne mutum bisa ga bukatarsa.
\s5
\v 36 Yusufu, Balawi, mutumin tsibirin Kubrus, wanda manzannisu ka yi wa lakani da suna Barnaba. (wato, mai karfafa zuciya).
\v 37 Yana da fili sai ya sayar da shi ya kawo kudin gaban manzanni.
\s5
\c 5
\p
\v 1 Sai wani mai suna Hananiya da matarsa Safiratu, suka sayar da filinsu,
\v 2 Hananiya kuwa ya boye wasu daga cikin kudin filin, (kuma da sanin matarsa), sa'annan suka kawo ragowar kudin a gaban manzannin.
\s5
\v 3 Amma Bitrus ya ce, "Hananiya don me shaidan ya cika zuciyarka, har ka yi wa Ruhu Mai Tsarki karya? Har ka boye wasu daga kudin filin?
\v 4 Sa'adda ba ka sayar da filin ba, ba mallakarka bane? Bayan da ka sayar ma, ba naka bane? Don me kayi irin wannan tunanin a zuciyarka? To ba mutane ka yi wa karya ba, Allah ka yi wa."
\v 5 Nan take da jin haka, Hananiya ya fadi ya ja numfashinsa na karshe. Dukan mutanen da suka ji labarin kuwa tsoro mai girma ya afko masu
\v 6 Matasa suka zo suka nannade gawarsa, suka fitar da shi waje suka binne shi.
\s5
\v 7 Bayan wajen sa'a uku, sai matarsa ta iso, ba tare da sanin abin da ya faru ba.
\v 8 Sai Bitrus ya ce mata, "ki gaya mini ko nawa kuka sayar da filin?" Sai ta amsa, "ta ce kaza ne."
\s5
\v 9 Sa'annan Bitrus ya ce mata, "Don me kuka shirya wannan makidar tare da mijinki don ku gwada Ruhun Ubangiji? Kiji tafiyar wadanda suka bizne mijinki a bakin kofa, kuma za su dauke ki yanzu."
\v 10 Nan take sai ta fadi a gabansa, ta ja numfashinta na karshe, matasan kuwa suka zo suka same ta ta mutu; sai suka dauki gawarta suka kai waje suka kuma bizne ta kusa da mijinta.
\v 11 Tsoro mai girma kuwa ya afko wa iklisiyar gaba daya da dakan wadanda suka ji wadan nan al'amura.
\s5
\v 12 Ayyukan alamu da ban mamaki masu yawa kuwa sun faru ga mutane, ta hannun manzannin. Dukansu kuma suna nan tare a dakalin Sulaimanu,
\v 13 Sai dai babu mai karfin halin ya hada kai tare dasu; amma suna da kwarjini sosai a gaban jama'a.
\s5
\v 14 Har wa yau aka rika samun karin masu ba da gaskiya, dinbin jama'a, maza da mata,
\v 15 har sukan dauki marasa lafiya su kai su bakin titi, suna kwantar da su a bisa gadaje da shinfidu, domin idan Bitrus ya zo wucewa ko da inuwarsa ma ta taba wasunsu.
\v 16 Mutane dayawa kuwa sukan zo daga garuruwan da ke kewaye da Urushalima, suna kuma kawo masu rashin lafiya, da wadanda aljannu ke damunsu, aka kuma warkar da su duka.
\s5
\v 17 Amma babban firist ya taso tare da duk wadanda ke tare da shi (wato 'yan darikar Sadukiyawa); suka cika da kishi matuka
\v 18 suka kama manzannin suka kuma jefasu a kurkuku.
\s5
\v 19 A cikin dare sai mala'ikan Ubangiji ya bude kofofin kurkukun ya kuma fito da su waje, ya ce,
\v 20 "Kuje ku tsaya a gaban haikali ku kuma gaya wa mutane maganar wannan rai."
\v 21 Sa'adda suka ji haka, sai suka tafi haikalin da wayewar gari suka yi koyarwa. Amma babban firist da jama'arsa suka zo suka kuma kira taro da kuma dukan yan majalisa, da dattawan jama'ar Isra'ilawa suka fito suka kuma ba da umarni, a fito masu da manzannin.
\s5
\v 22 Amma ma'aikatan da suka je kurkukun basu sami kowa, a kurkukunba, sai suka dawo suka ba da rahoto,
\v 23 Su ka ce kurkukun a rufe gam da masu gadi suna nan a tsaye a bakin kofar amma da muka shiga, bamu sami kowa a ciki ba.
\s5
\v 24 Yanzu sa'adda shugaban haikalin da manyan firistoci suka ji wadannan kalamai, sai suka rikice sosai game da su, suka ce yanzu me wannan zai haifar.
\v 25 Sai wani ya zo ya ce masu, "Wadannan mutanen da kuka jefa a kurkuku suna can a cikin haikali suna koyar da jama'a."
\s5
\v 26 Sai shugaban haikalin ya je da ma'aikatansa suka kawosu, ba tare da tashin hankali ba, domin gudun kada jama'a su jejjefesu.
\v 27 Da suka kawo su, sai suka gabatar da su gaban majalisa, babban firist kuwa ya tuhume su,
\v 28 cewa "Ba mun yi maku kashedi da karfi kada ku yi koyarwa cikin wannan sunan ba? Amma ga shi duk kun cika Urushalima da koyarwarku, kuna kuma neman kusa jinin mutumin nan ya sauko kanmu."
\s5
\v 29 Amma Bitrus da manzannin suka amsa suka ce, "Dole mu yi wa Allah biyayya ba mutane ba.
\v 30 Allah na ubanenmu ya ta da Yesu, wanda kuka kashe, ta wurin rateye shi a bisa itace,
\v 31 Allah kuwa ya daukaka shi a hannun damarsa, domin ya zama sarki da kuma mai ceto, ya ba Isra'ila tuba da gafarar zunubai.
\v 32 Mu kuwa shaidu ne ga wadannan al'amura, haka ma Ruhu Mai Tarki, wanda Allah ya bayar ga dukan wadanda suka yi biyayya a gareshi."
\s5
\v 33 Da yan majalisa suka ji haka sai suka fusata kwarai da gaske, har suka nemi su kashe manzannin.
\v 34 Amma wani Bafarise mai suna Gamaliel, malami ne kuma na attaura wanda dukan jama'a suna martabawa, sai ya mike ya ba da umarni cewa a fid da manzannin waje na dan lokaci.
\s5
\v 35 Sai ya ce masu "Ya ku mutanen Isra'ila, ku lura sosai da a binda kuke niyyar yi wa mutanen nan,
\v 36 A kwanakin baya wani ya zo mai suna Tudas ya dauki kansa wani abu, kimanin mutane dari hudu ne suka bishi, amma da aka kashe shi jama'arsa baki daya sai suka watse, ba wanda ya kara jin labarinsu.
\v 37 Bayansa kuma, aka yi wani mai suna Yahuza na Galili wanda a kwanakin kidaya, ya zo ya rinjayi mutane da yawa, shima ya lalace, duk wadanda suka bi shi kuwa suka watse.
\s5
\v 38 Don haka ina gaya maku ku rabu da mutanen nan, domin idan shirinsu ko kuma ayyukansu na mutane ne za su lalace.
\v 39 Amnma idan abin nan daga Allah yake baza ku iya lalata su ba; kada ya zama kuna gaba da Allah." Sai suka rinjayu.
\s5
\v 40 Da suka kira manzannin ciki suka yi masu duka, sai suka umarce su da cewa kada su sake koyarwa a cikin sunan Yesu, sai suka barsu suka tafi.
\v 41 Suka fita daga cikin majalisar, suna murna domin sun cancanta su sha wulakanci saboda sunan.
\v 42 Bayan haka kullayomin suna zuwa haikali, suna bi gida gida, suna wa'azi, suna kuma koyarwa ba fasawa cewa Yesu shine Almasihu.
\s5
\c 6
\p
\v 1 A wadannan kwanaki, yawan almajiran ya ci gaba da ribanbanya, sai Yahudawan da suke zama a kasar Helanawa suka fara gunaguni game da Yahudawan Isra'ila, domin basu damu da gwamrayensu, wajen raba abinci da ake yi kullum.
\s5
\v 2 Manzannin nan sha biyu suka kira taron almajiran suka ce masu, "Bai kamata mu bar maganar Allah mu shiga hidimar rabon abinci ba.
\v 3 Don haka ku zabi 'yan'uwa maza daga cikinku, mutane bakwai wadanda a ke ganin su da daraja, cike da Ruhu da kuma hikima, wadanda za mu zaba suyi wannan hidima.
\v 4 Mu kuwa mu ci gaba da da addu'a da kuma hidimar kalmar."
\s5
\v 5 Maganar su kuwa ta farantawa dukan jama'a rai sosai. Sai suka zabi Istifanus, shi kuwa mutum ne cike da bangaskiya kuma da Ruhu Mai Tsarki da Filibus, da Birokoros, da Nikanar, da Timan, da Barminas, da kuma Nikolas, mutmin Antakiya wanda ya yi tuban Yahudanci.
\v 6 Masu bin kuwa suka gabatar da wadannan mutanen a gaban manzannin, su kuwa suka yi masu addu'a suka kuma dora hannuwansu a kansu.
\s5
\v 7 Sai maganar Allah ta yawaita; yawan almajiran kuwa ya rubanbanya matuka a Urushalima; firistoci da yawa na Yahudawa suka bada gaskiya.
\s5
\v 8 Sai Istifanus, cike da alheri da iko, ya rika yin ayyukan ban mamaki da alamu a cikin jama'a.
\v 9 Amma sai ga wadansu mutane daga wata majami'a da ake kira majami'ar Yantattu, wato su Kuramiyawa da Iskandariyawa, da kuma wasu daga kasar Kilikiya da Asiya. Wadannan mutanen kuwa suna muhawara da Istifanus.
\s5
\v 10 Amma suka kasa yin tsayayya da Istifanus, saboda irin hikima da Ruhun da Istifanus ya ke magana da shi.
\v 11 Sai a asirce suka zuga wasu mutane su je su ce, "Ai munji Istifanus yana maganganun sabo game da Musa da kuma Allah."
\s5
\v 12 Sai suka zuga mutanen, har da dattawa da marubuta suka tunkari Istifanus, suka kama shi, suka kawo shi gaban majalisa.
\v 13 Suka kawo masu shaidar karya suka ce, "Wannan mutumin har yanzu bai dena maganganun gaba akan wannan wuri mai tsarki da kuma shari'a ba.
\v 14 Domin kuwa mun ji shi, yana cewa wannan Yesu Banazarat zai rushe wannan wuri zai kuma canza al'adun da muka gada daga wurin Musa."
\v 15 Dukan wadanda suke zaune a majalisar suka zuba masa ido, sai suka ga fuskarsa kamar ta mala'ika.
\s5
\c 7
\p
\v 1 Sai babban firist ya ce, "Wadannan al'amura gaskiya ne?"
\v 2 Sai Istifanus ya amsa ya ce, "Ya 'yan'uwa da ubanni, ku saurare ni, Allah Madaukaki ya bayyana ga ubanmu Ibrahim tun yana can kasar Mesofotamiya, kafin ma ya zauna a kasar Haran;
\v 3 ya ce masa, 'Ka bar kasarka da danginka, ka tafi kasar da zan nuna maka.'
\s5
\v 4 Sa'annan ya bar kasar Kaldiyawa ya zo ya zauna a Haran; daga can, bayan rasuwar mahaifinsa, sai Allah ya kira shi zuwa wannan kasa da kuke ciki.
\v 5 Amma Allah bai ba shi kasar gado ba tukuna, ko da misalin tafin sawunsa. Amma ya alkawarta - ko da yake bai riga ya haifi da ba tukuna - wanda zai ba shi kasar gado, shi da zuriyarsa, a bayansa.
\s5
\v 6 Allah ya yi magana da shi kamar haka, cewa zuriyarsa za su yi bakonci a wata kasa wadda ba tasu ba, mutanen wannan kasar kuwa za su gwada masu bakar azaba su kuma bautar da su har shekaru dari hudu.
\v 7 'Kuma zan hukunta wannan al'umma da ta bautar da su,' Allah ya ce, 'Bayan haka za su fito daga wannan kasa su bauta mini a wannan wuri.'
\v 8 Allah ya ba Ibrahim alkawarin kaciya, sai Ibrahim ya haifi Ishaku ya yi masa kaciya a rana ta takwas; Ishaku ya haifi Yakubu, Yakubu kuma ya haifi ubanni Isra'ila su goma sha biyu.
\s5
\v 9 Wadannan 'yan'uwa suka yi kyashin danuwansu Yusifu suka sayar da shi bauta zuwa Masar. Amma Allah na tare da shi.
\v 10 Ya kuwa cece shi daga dukan sharin da yan uwansa suka kulla masa, Allah kuwa ya ba shi tagomashi da hikima a gaban Fir'auna, sarkin Masar. Fir'auna kuwa ya mai da shi mai mulki a dukan kasar Masar da kuma dukan mallakarsa.
\s5
\v 11 Sai aka yi babbar yunwa a dukan kasar Masar da ta Kan'ana, iyayenmu suka sha wuya saboda rashin abinci.
\v 12 Amma lokacin da Yakubu ya ji akwai hatsi a kasar Masar, sai ya aiki ubannimu a karo na farko.
\v 13 Da suka je a karo na biyu, sai Yusifu ya bayyana kansa ga yanuwansa; a wannan lokaci ne Fir'auna ya gane da yanuwan Yusufu.
\s5
\v 14 Yusufu ya aiki yanuwansa su kawo Yakubu ubansu da dukan mallakarsu da iyalansu zuwa Masar, Dukansu mutane saba'in da biyar ne.
\v 15 Yakubu ya tafi ya zauna a Masar; shi da zuriyarsa har mutuwar su.
\v 16 Aka dauke su zuwa Shekem aka binne su a kabarin da Ibrahim ya saya da kudin azurfa daga hannun yayan Hamor a Shekem.
\s5
\v 17 Yayin da alkawarin Allah ya kusato wanda Allah ya fada wa Ibrahim, mutanen suka karu suka hayayyafa kwarai a Masar,
\v 18 Sai a ka yi wani sarki a Masar wanda bai san Yusifu ba,
\v 19 Wannan sarki ya yaudari kakkaninmu ya yi masu mugunta kwarai da gaske, har ma ya kai ga suna barin jariransu cikin hasari don su ceci rayukansu.
\s5
\v 20 A wannan lokaci ne aka haifi Musa, kuma kyakkyawan yaro ne sai aka yi renon sa tsawon wata uku a gidan mahaifinsa a asirce.
\v 21 Yayin da aka jefar da shi, sai diyar Fir'auna ta dauke shi ta rene shi kamar danta.
\s5
\v 22 Aka ilimantar da Musa da dukan ilimi irin na Masar; kuma ya shahara cikin fasahar magana da kuma ayyukansa.
\v 23 Amma lokacin da yakai shekara arba'in, sai ya yi niyyar ya ziyarci 'yan'uwansa, Isra'ilawa.
\v 24 Sai ya ga wani na cin zalin Ba Isra'ile, Musa kuwa ya taimaki wanda ake kwara ta wurin murkushe Bamasaren:
\v 25 zaton Musa 'yan'uwansa za su fahimci taimakon Allah ne ya zo masu amma ina! Basu gane ba.
\s5
\v 26 Washegari ya ga wasu Isra'ilawa na fada da junansu; ya yi kokari ya raba su; sai ya ce masu, 'Malamai, ku 'yan'uwan juna ne; don me kuke fada da junanku?'
\v 27 Amma shi wanda ake kwarar makwabcinsa ya ture Musa a gefe guda, ya ce, 'Wa ya nada ka shugaba ko alkali akanmu?
\v 28 Kana so ka kashe ni ne, kamar yadda ka kashe Bamasaren nan jiya?'
\s5
\v 29 Da jin haka sai Musa ya gudu, zuwa kasar Midinawa, a matsayin dan gudun hijira. Anan ya haifi "ya'ya biyu maza.
\v 30 Bayan da shekaru arba'in suka wuce, sai mala'ika ya bayyana gare shi a jeji, kusa da dutsen Sinai, a cikin harshen wuta a cikin jeji.
\s5
\v 31 Sa'adda Musa ya ga wutar, mamaki ya kama shi; sai ya maso kusa don ya kara dubawa, sai ya ji muryar Ubangiji na cewa,
\v 32 'Nine Allah na ubanninka, Ibrahim, da na Ishaku, da na Yakubu.' Musa ya razana har ma bai sake daga kai ya duba ba.
\s5
\v 33 Ubangiji ya ce masa, 'Tube takalminka, domin in da kake tsaye wuri mai tsarki ne.
\v 34 Ba shakka na ga wahalar da mutane na ke sha a Masar, kuma na ji nishinsu, don haka na zo in cece su, yanzu fa sai ka zo, in aike ka zuwa Masar.'
\s5
\v 35 Wannan fa shine Musan da suka ki, harma da cewa, 'Wanene ya nada ka alkali ko shugaba a kanmu?' Shine kuma wanda Allah ya aiko masu a matsayin shugaba da kuma mai ceto. Allah ya aiko shi ta hannun mala'ikan da ya gani a daji.
\v 36 Bayan alamu da al'ajibai iri-iri a Masar da kuma Baharmaliya, Musa ya fito da su daga Masar da kuma cikin jeji, a lokacin da suka yi tafiya shekara arbain.
\v 37 Wannan shine Musan da ya cewa Isra'ilawa, 'Ubangiji zai tayar maku da wani annabi kamar ni daga cikin Yan'uwan ku.'
\s5
\v 38 Wannan shine mutumin da ke tare da mutane a jeji. Karkashin jagorancin mala'ikan da ya yi magana da shi a dutsen Sinai. Wannan ne mutumin da ke tare da ubannen mu, wannan shi ne mutumin da ya ba mu maganar Allah mai rai.
\v 39 Wannan shine mutumin da ubannenmu suka ki su yi masa biyayya; su ka fitar da shi daga cikinsu, suka kudurta a zuciyarsu za su koma masar.
\v 40 A lokacin ne suka cewa Haruna, 'ya yi masu allolin da za su jagorance su zuwa masar. Domin kuwa ga zancen Musan nan da ya fito da mu daga Masar, ba mu san abin da ya faru da shi ba.'
\s5
\v 41 Sai suka kera dan maraki suka kawo wa gunkin hadaya, suka yi murna da abin da hannayensu suka kera.
\v 42 Allah ya bashe su su bauta wa tauraran sama, kamar yadda yake a rubuce cikin littattafafan annabawa, 'Kun mika mani hadayu na yankakkun dabbobi a jeji ne a shekaru arba'in din nan ya ku Isra'ilawa?'
\s5
\v 43 Kun yarda da haikalin Molek da kuma tauraron allahn nan Rafem, da kuma siffofin nan da kuka kera don ku yi masu sujada; don haka zan kai ku bauta har gaba da Babila.'
\s5
\v 44 Kakkaninmu suna da alfarwa ta sujada domin shaida a cikin jeji, kamar yadda Allah ya umarta yayin da ya yi magana da Musa, cewa ya yi shi bisa ga salon da aka nuna mashi.
\v 45 Wannan shine Alfarwar da kakkaninmu suka zo da shi, a lokacin Joshuwa. Wannan ya faru ne yayin da suka mallaki wannan kasa ta al'ummai da Allah ya kora a gaban kakkaninmu. Haka abin yake har ya zuwa zamanin Dauda,
\v 46 wanda ya sami tagomashi a wurin Allah; don ya gina masujada domin Allah na Yakubu.
\s5
\v 47 Amma Sulaimanu ne ya gina Gidan Allah.
\v 48 Sai dai Madaukaki ba yakan zauna a gidan da hannaye suka gina ba, kamar yadda annabin ya ce,
\v 49 'Sama kursiyina ce, duniya kuwa wurin ajjiye sawayena ne. To wane irin gida za ku gina mani? inji Ubangiji: ko kuwa ina ne wurin da zan huta?
\v 50 Ko ba hannayena ne suka yi dukan wadannan ba?'
\s5
\v 51 Ku mutane masu taurin kai masu zuciya mara kaciya da kunnuwa marasa ji, kullum kuna gaba da Ruhu Mai Tsarki, kuna aikata abin da kakkaninku suka aikata.
\v 52 Wane annabi ne kakkaninku ba su tsanantawa ba? Sun kashe annabawan da suka rigayi zuwan Mai Adalcin nan, kuma kun zama wadanda suka kasance masu bashe shi da masu kashe shi,
\v 53 kune mutanen da kuka karbi shari'a wadda mala'iku suka bayar, amma ba ku kiyaye ta ba".
\s5
\v 54 Yayin da majalisar suka ji wannan, sai ransu ya baci kwarai, har suna cizon hakoransu don gaba da Istifanus.
\v 55 Amma shi, cike da Ruhu Mai Tsarki, sai ya daga idonsa sama, ya ga daukakar Allah; ya kuma hango Yesu na tsaye a hannun daman Allah.
\v 56 Istifanus ya ce, "Duba, ina ganin sama ta bude, ga Dan Mutum na tsaye a hannun dama na Allah."
\s5
\v 57 Amma yan majalisar suka daga murya da karfi, suka yi ihu, suka kuma toshe kunnuwansu, gaba dayansu suka afka masa;
\v 58 suka fitar da shi bayan gari, suka jejjefe shi da duwatsu, don shaida sai suka tube manyan rigunansu suka ajiye a gaban wani matashi da ake ce da shi Shawulu.
\s5
\v 59 Lokacin da suke kan jifan Istifanus, ya dinga kira yana cewa, "Ya Ubangiji Yesu, ka karbi ruhu na."
\v 60 Ya durkusa ya daga murya da karfi, ya ce, "Ya Ubangiji, kada ka rike wannan zunubi a kansu." Yayin da ya fadi wannan, sai ya yi barci.
\s5
\c 8
\p
\v 1 Bulus ya amince da mutuwarsa. A wannan rana tsanani mai zafi ya fara tasowa akan Iklisiya da take a Urushalima, sai masu bangaskiya duka suka bazu ko ina a cikin garuruwan Yahudiya da Samariya, sai manzannin kadai aka bari.
\v 2 Amintattun mutane suka bizne Istifanus suka yi babban makoki game da shi.
\v 3 Amma Shawulu ya yi wa Iklisiya mugunta kwarai, ya dinga shiga gida gida yana jawo mutane maza da mata, kuma yana kulle su cikin kurkuku.
\s5
\v 4 Duk da haka masu bangaskiyar nan da suka warwatsu suka tafi suka dinga yada wa'azin maganar.
\v 5 Filibus ya tafi can Samariya ya yi shelar Almasihu.
\s5
\v 6 Da taron mutane suka ji kuma suka ga alamun da Filibus yake yi, sai suka mai da hankali dukansu domin su ji abinda yake fadi.
\v 7 Domin kazaman ruhohi sun fito daga cikin mutane da yawa da suka saurare shi suna kuka da kururuwa; nakasassun mutane dayawa da guragu suka warke.
\v 8 Kuma aka yi farin ciki mai girma a birnin.
\s5
\v 9 Amma akwai wani mutum a cikin birnin da ake kira Siman, wanda tun farko shi masafi ne da kuma dan dabo, yana yi wa mutanen Samariya abubuwan ban mamaki, yayin da yake kiran kansa wani mai muhimmanci.
\v 10 Dukan Samariyawa, manya da yara, suna sauraronsa, su kan ce, "Wannan mutum shine ikon Allahn nan wanda ake kira mai girma."
\v 11 Suna sauraron sa, domin ya dade yana yi masu abubuwan mamaki da tsafe-tsafensa.
\s5
\v 12 Amma da suka yi bangaskiya da wa'azin bisharar da Filibus yake yi game da mulkin Allah da sunan Yesu Almasihu, sai aka yi masu Baftisma dukansu maza da mata.
\v 13 Har shima Siman da kansa ya ba da gaskiya. Bayan an yi masa Baftisma ya cigaba da bin Filibus, da ya ga ana nuna alamu da manyan ayyuka, sai ya yi mamaki.
\s5
\v 14 Da manzannin da ke Urushalima suka ji labarin Samariya ta karbi maganar Allah, sai suka aika masu Bitrus da Yahaya.
\v 15 Da suka iso, suka yi masu addu'a, domin su karbi Ruhu Mai Tsarki.
\v 16 Domin har wannan lokaci, Ruhu Mai Tsarki bai sauko kan kowannensu ba; an dai yi masu baftisma ne kadai cikin sunan Ubangiji Yesu.
\v 17 Sai Bitrus da Yahaya suka dora masu hannuwansu, sai suka karbi Ruhu Mai Tsarki.
\s5
\v 18 Sa'adda Siman yaga ana bayar da Ruhu Mai Tsarki ta wurin dorawar hannuwan manzanni, ya basu kudi.
\v 19 Ya ce, "Ku bani wannan iko, ni ma, don duk wanda na dora wa hannu ya karbi Ruhu Mai Tsarki."
\s5
\v 20 Amma Bitrus yace masa, "Azurfarka ta lalace tare da kai, saboda kana tunanin za ka malaki baiwar Ubangiji da kudi.
\v 21 Baka da wani rabo a wannan al'amari, domin zuciyarka ba daidai take da Allah ba.
\v 22 Saboda haka ka tuba daga wannan muguntarka, ka kuma yi addu'a ga Ubangiji, domin mai yiwuwa ya gafarta maka game da manufar zuciyarka.
\v 23 Domin na gane kana cikin bacin rai da kuma cikin daurin zunubi."
\s5
\v 24 Siman ya amsa ya ce, "Kayi addu'a ga Ubangiji domina, kada wani daga cikin abubuwan nan da ka fada ya faru da ni."
\s5
\v 25 Sa'anda Bitrus da Yahaya suka bada shaida kuma suka fadi maganar Ubangiji, sun koma Urushalima; akan hanya, suka yi wa'azin bishara a kauyukan samariyawa da yawa.
\s5
\v 26 Yanzu kuwa Mala'ikan Ubangiji ya yi wa Filibus magana cewa, "Tashi ka tafi ta kudu da hanyar da ta yi kasa daga Urushalima zuwa Gaza" (wannan hanyar yana cikin hamada.)
\v 27 Ya kuwa tashi ya tafi. Sai ga wani mutum daga Habasha, baba ne mai babban matsayi a karkashin Kandakatu, sarauniyar Habasha. Shine yake mulkin dukan dukiyarta. Ya zo Urushalima domin ya yi ibada.
\v 28 Yana komawa zaune cikin karussarsa, kuma yana karanta Littafin annabi Ishaya.
\s5
\v 29 Ruhun ya ce wa Filibus, "Ka je kusa da karussar nan."
\v 30 Sai Filibus ya gudu ya same shi, kuma ya ji shi yana karanta littafin annabi Ishaya, sai ya ce, "Ka fahimci abin da kake karantawa?"
\v 31 Bahabashen ya ce. "Yaya zan iya, idan ba wani ya bishe ni ba?" Ya roki Filibus ya shigo cikin karussar ya zauna tare da shi.
\s5
\v 32 Wannan kuwa shine nassin da Bahabashen yake karantawa, "An kai shi kamar tunkiya zuwa mayanka; shiru kuma, kamar dan rago a hannun masu sosayarsa, bai bude baki ba.
\v 33 Cikin kaskancinsa aka yi masa shari'a da rashin adalci: Wa zai bada tarihin tsararsa? Domin an dauke ransa daga duniya."
\s5
\v 34 Sai baban ya tambayi Filibus, ya ce, "Na roke ka, gaya mani, game da wa annabin yake magana? Da kansa, ko kuwa wani mutum dabam?"
\v 35 Filibus ya fara magana; akan littafin Ishaya, ya kuwa yi masa wa'azi akan Yesu.
\s5
\v 36 Yayin da suke tafiya akan hanya, sai suka iso bakin wani kogi; Baban ya ce, "Duba, ga ruwa anan; me zai hana ayi mani baftisma?"
\v 37 Filibus ya ce," Idan ka gaskanta da zuciya daya, ana iya yi maka baftisma." Sai Bahabashen ya ce, "Na gaskata Yesu Almasihu shine Dan Allah."
\v 38 Sai Bahabashen ya umarta a tsai da karussar. Sai suka zo wurin ruwa dukan su biyu, Filibus da baban, Filibus kuwa yayi masa baftisma.
\s5
\v 39 Yayin da suka fito daga cikin ruwan, Ruhun Ubangiji ya dauke Filibus; baban bai sake ganin shi ba, sai ya ci gaba da tafiyar sa yana murna.
\v 40 Amma Filibus ya bayyana a Azotus. Ya ratsa wannan yankin yana wa'azin bishara a dukan garuruwan, har sa'anda ya iso Kaisariya.
\s5
\c 9
\p
\v 1 Amma Shawulu, ya cigaba da maganganun tsoratarwa har ma da na kisa ga almajiran Ubangiji, ya tafi wurin babban firist
\v 2 kuma ya roke shi wasiku zuwaga majami'un da ke Dimashku, domin idan ya sami wani da ke na wannan hanya, maza ko mata, ya kawo su Urushalima a daure.
\s5
\v 3 Yayin da yana tafiya, ya kasance da ya iso kusa da Dimashku, nan da nan sai ga wani haske daga sama ya haskaka kewaye da shi;
\v 4 Sai ya fadi a kasa kuma yaji wata murya na ce da shi, "Shawulu, Shawulu, me yasa kake tsananta mani?"
\s5
\v 5 Shawulu ya amsa, "Wanene kai, Ubangiji?" Ubangiji ya ce, "Nine Yesu wanda kake tsanantawa;
\v 6 amma ka tashi, ka shiga cikin birnin, kuma za a gaya maka abinda lallai ne kayi.
\v 7 Mutanen da ke tafiya tare da Shawulu suka tsaya shiru sun rasa abin fada, suna sauraron muryar, amma ba su ga kowa ba.
\s5
\v 8 Shawulu ya tashi daga kasa, kuma daga ya bude idanunsa, baya ganin komai; sai suka kama hannuwansa suka yi masa jagora suka kawo shi cikin birnin Dimashku.
\v 9 Har kwana uku ba ya kallo, kuma ba ya ci balle sha.
\s5
\v 10 Akwai wani almajiri a Dimashku mai suna Hananiya; sai Ubangiji ya yi magana da shi cikin wahayi, ya ce, "Hananiya." Sai ya ce, "Duba, gani nan Ubangiji."
\v 11 Ubangiji ya ce masa, "Tashi, ka tafi titin da ake kira Mikakke, kuma a gidan wani mai suna Yahuza ka tambaya mutum daga Tarsus mai suna Shawulu; gama yana addu'a;
\v 12 kuma ya gani cikin wahayi mutum mai suna Hananiya na shigowa kuma ya daura masa hannu, domin idanunsa su bude."
\s5
\v 13 Amma Hananiya ya amsa, "Ubangiji, na ji labari daga wurin mutane da yawa game da mutumin nan, da irin muguntar da ya aikata ga tsarkakan mutanenka da ke Urushalima.
\v 14 An bashi izini daga babban firist domin ya kama dukan wanda ke kira bisa sunanka."
\v 15 Amma Ubangiji ya ce masa, "Jeka, gama shi zababben kayan aiki na ne, wanda zai yada sunana ga al'ummai da sarakuna da 'ya'yan Isra'ila;
\v 16 Domin zan nuna masa irin wahalar da zai sha sabo da sunana."
\s5
\v 17 Sai Hananiya ya tafi, ya shiga gidan. Ya dora masa hannu a kai, ya ce, "Dan'uwa Shawulu, Ubangiji Yesu, wanda ya bayyana a gareka a hanya sa'adda kake zuwa, ya aiko ni domin ka sami ganin gari ka kuma cika da Ruhu Mai Tsarki."
\v 18 Nan take wani abu kamar bawo ya fado daga idanun Shawulu, kuma ya sami ganin gari; ya tashi aka yi masa baftisma;
\v 19 kuma ya ci abinci sai aka karfafa shi. Ya zauna tare da almajirai a Dimashku kwanaki da yawa.
\s5
\v 20 Nan take ya fara shellar Yesu cikin haikali, yana cewa shine dan Allah.
\v 21 Dukan wadanda suka saurare shi suka yi mamaki suka ce "Ba wannan mutumin ne yake hallaka mutanen Urushalima da ke kira bisa ga wannan suna ba? Ya kuma zo nan domin ya ba da su a daure ga manyan firistoci."
\v 22 Amma Shawulu kuwa ya sami iko sosai, kuma yana haddasa damuwa tare da rinjaya tsakanin Yahudawan dake zama a Dimashku ta wurin tabbatar da Yesu shine Almasihu.
\s5
\v 23 Bayan kwanaki da yawa, sai Yahudawan suka yi shiri domin su kashe shi.
\v 24 Amma shirin su ya zama sananne ga Shawulu. Suna fakkon sa ta wurin tsaron kofar birnin dare da rana domin su kashe shi.
\v 25 Amma da tsakar dare almajiransa suka daukeshi a kwando, suka zurara shi ta katanga.
\s5
\v 26 Sa'adda ya zo Urushalima, Shawulu ya yi niyyar hada kai da almajirai, amma dukansu suna tsoronsa, domin ba su yarda cewa shima ya zama almajiri ba.
\v 27 Amma Barnaba ya dauke shi ya kawo shi wurin manzannin. Ya kuwa gaya musu yadda Shawulu ya sadu da Ubangiji a hanya, har Ubangiji ya yi magana da shi, kuma yadda Shawulu ya yi wa'azi cikin sunan Yesu gabagadi a Dimashku.
\s5
\v 28 Ya sadu da su lokacin shigar su da fitar su a Urushalima. Ya yi wa'azi gabagadi cikin sunan Ubangiji Yesu
\v 29 kuma yana muhawara da Yahudawan Helenanci; amma sun ci gaba da kokarin kashe shi.
\v 30 Da 'yan'uwa suka gane haka, sai suka kawo shi Kaisariya, suka kuwa tura shi zuwa Tarsus.
\s5
\v 31 Sa'annan iklisiya dake dukan kasar Yahudiya, Galili da kuma Samariya suka sami salama da kuma ginuwa; suka kuwa ci gaba da tafiya cikin tsoron Ubangiji, da kuma ta'aziyar Ruhu Mai Tsarki, iklisiyar kuwa ta karu da yawan mutane.
\v 32 Har ta kai, yayin da Bitrus ya zaga dukan yankin kasar, ya dawo wurin masu bi dake zama a garin Lidda.
\s5
\v 33 A can kuwa ya sami wani mutum mai suna Iniyasu, wanda yake shanyayye ne, yana kwance har tsawon shekara takwas a kan gado.
\v 34 Bitrus ya ce masa, "Iniyasu, Yesu Almasihu ya warkar da kai. Tashi ka nade shimfidarka." Nan take sai ya mike.
\v 35 Sai duk mazauna kasar Lidda da kasar Sarona suka ga mutumin, suka kuma juyo ga Ubangiji.
\s5
\v 36 Yanzu kuwa a Yafa akwai wata almajira, mai suna Tabita, ma'ana "Dokas." Wannan matar kuwa tana chike da ayyukan nagarta da halin tausayi da take yi ga mabukata.
\v 37 Ya kai ga cewa a kwanakin can ta yi rashin lafiya har ta mutu; da suka wanke gawar ta suka kwantar da ita a bene.
\s5
\v 38 Da shike Lidda na kusa da Yafa, almajiran kuma sun ji cewa Bitrus yana can, suka aika mutane biyu wurinsa. Suna rokansa, "Ka zo garemu ba tare da jinkiri ba."
\v 39 Bitrus ya tashi ya tafi da su, da isowar sa, suka kai shi benen. Sai dukan gwamrayen suka tsaya kusa da shi suna kuka, sai suka dauko riguna da sutura da Dokas ta dinka lokacin da take tare da su.
\s5
\v 40 Bitrus ya fitar da su duka daga cikin dakin, ya durkusa, ya yi addu'a; sai, ya juya wurin gawar, ya ce, "Tabita, tashi." Ta bude idanunta, da ta ga Bitrus ta zauna,
\v 41 Bitrus kuwa ya mika hannunsa ya tashe ta; sa'annan ya kira masu bi da gwamrayen, ya mika ta a raye garesu.
\v 42 Wannan al'amari ya zama sananne cikin dukan Yafa, kuma mutane da yawa suka bada gaskiya ga Ubangiji.
\v 43 Ya kasance, cewa, Bitrus ya zauna kwanaki da dama a Yafa tare da wani mutum mai suna Saminu, majemi.
\s5
\c 10
\p
\v 1 An yi wani Mutum a birnin Kaisariya, mai suna Karniliyas, shugaban sojoji ne na kungiyar da ake kira Italiya.
\v 2 Mutum ne mai ibada, wanda ya mika kansa da iyalinsa ga bautar Allah; ya kan bada taimakon kudi mai yawa ga Yahudawa, kuma yana addu'a ko yaushe ga Allah.
\s5
\v 3 Wajen sa'a ta tara ga yini, an bayyana masa cikin wahayi mala'kan Ubangiji na zuwa gare shi sai mala'ikan ya ce masa, "Karniliyas!"
\v 4 Karniliyas ya zuba wa mala'ikan ido a tsorace ya ce "Menene, mai gida?" mala'ikan ya ce masa, "Addu'ar ka da taimakon ka ga talakawa ya kai sama matsayin sadaka abin tunawa a gaban Allah,
\v 5 "Yanzu ka aika mutane zuwa birnin Yafa su kawo mutum mai suna Saminu wanda ake kira Bitrus.
\v 6 Yana zama tare da Saminu majemi, wanda gidansa ke bakin teku.
\s5
\v 7 Da mala'ikan da ya yi magana da shi ya tafi, Karniliyas ya kira biyu daga barorin gidansa, da kuma soja guda mai bautar Allah daga cikin sojojin da suke masa hidima.
\v 8 Karniliyas ya fada masu dukan abin ya faru sai ya aike su Yafa.
\s5
\v 9 Washe gari wajen sa'a ta shida (tsakar rana) suna cikin tafiya da suka yi kusa da birni, Bitrus ya hau kan bene don ya yi addu'a.
\v 10 Sai ya ji yunwa kuma yana bukatar wani abinda da zai ci, amma a yayin da mutanen na dafa abinci, sai ya ga wahayi.
\v 11 Sai ya ga sararin sama ya bude kuma wani tasa na saukowa, wani abu kamar babban mayafi yana saukowa zuwa duniya, ana zuro shi ta kusuryoyinsa hudu.
\v 12 A cikinsu kuwa akwai dukan halitun dabbobi masu kafa hudu da kuma masu rarrafe a duniya da tsunstayen sama.
\s5
\v 13 Sai murya ta yi magana da shi; "Tashi, Bitrus, yanka ka ci "
\v 14 Amma Bitrus ya ce "Ba haka ba, Ubangiji, gama ban taba cin abu mara tsarki ko mai kazanta ba."
\v 15 Amma muryar ta sake zuwa masa karo na biyu kuma; "Abinda Allah ya tsarkake, kada ka kira shi kazantacce."
\v 16 Wannan ya faru sau uku; nan da nan sai aka dauki tasar zuwa sama.
\s5
\v 17 A yayin da Bitrus na cikin rudani game da ma'anar wahayin da ya gani, sai ga mutanen da Karniliyas ya aika suna tsaye a bakin kofar gidan, bayan sun tambayi hanyar zuwa gidan,
\v 18 Kuma suka yi sallama suna tambaya ko Saminu wanda ake kira Bitrus ya sauka a nan.
\s5
\v 19 A yayin da Bitrus yana kan tunani akan wahayin, Ruhu ya ce masa, "Duba, mutane uku na neman ka."
\v 20 Tashi ka sauka ka tafi tare da su. Kada ka yi jinkirin tafiya tare da su, domin Nine na aike su."
\v 21 Bitrus kuwa ya sauko wurin mutanen ya ce, "Ni ne wanda kuke nema. Me ya sa kuka zo?"
\s5
\v 22 Suka ce, "Shugaban soja mai suna Karniliyas, adalin mutum kuma mai bautar Allah, yana da kyakkyawar shaida a dukan al'umman Yahudawa, shi ne wanda mala'ika mai tsarki na Allah ya aika domin ka zo gidansa, ya ji sako daga wurinka."
\v 23 Sai Bitrus ya gayyace su su zo ciki kuma su zauna tare da shi. Washegari sai ya tafi tare da su, kuma wadansu 'yan'uwa daga Yafa suka raka shi.
\s5
\v 24 Kashegari suka shiga Kaisariya, Karniliyas kuwa yana jiran su; har ma ya gayyaci 'yan'uwansa da kuma abokansa na kusa.
\s5
\v 25 Ya kasance sa'adda Bitrus ya shiga, Karniliyas ya sadu da shi kuma ya durkusa ya yi masa sujada.
\v 26 Amma Bitrus ya tashe shi yana cewa, "Tashi tsaye! Ni ma mutum ne."
\s5
\v 27 A lokacin da Bitrus yake magana da shi, ya shiga ciki sai ya tarar da mutane da yawa sun taru a wuri daya.
\v 28 Ya ce masu, "Ku da kanku kun sani bai dace Bayahuden mutum ya yi ma'amulla ko ya ziyarci wani ko wata kabila ba. Amma Allah ya ce da ni kada in ce da kowa mara tsarki ko kazantacce.
\v 29 Wannan shine yasa na zo ba tare da musu ba, a lokacin da kuka kira ni. Don haka na tambaye ku me ya sa kuka aika in zo."
\s5
\v 30 Karniliyas ya ce "Kwanaki hudu da sun wuce a daidai wannan lokaci, ina addu'a da cikin sa'a na tara (karfe uku) a gidana, sai na ga mutum tsaye a gabana da tufafi mai haske.
\v 31 Ya ce, "Karniliyas, Allah ya ji addu'ar ka, kuma taimakon ka ga talakawa ya tuna ma Allah da kai.
\v 32 Saboda haka ka aika da wani Yafa, ya kira maka mutum mai suna Saminu wanda ake kira Bitrus. Yana zama a gidan Saminu majemi, da ke bakin teku. \f + \ft Wasu tsoffin kwafi sun ƙara: \fqa Idan ya zo, zai yi magana da kai \fqa* . \f*
\v 33 Don haka nan da nan na aika a kira ku. Kuna da kirki da kuka zo. Yanzu haka, duk muna nan a gaban Allah, don jin duk abin da Ubangiji ya umarce ku da ku faɗi.” \f + \ft Maimakon \fqa Ubangiji ya umarce ya faɗi, \fqa* wasu tsoffin kwafi sun yi, \fqa Allah ya umarce ya faɗi \fqa* . \f*
\s5
\v 34 Sai Bitrus ya bude bakinsa ya ce, "Gaskiya, na fahimci Allah baya nuna bambanci.
\v 35 Maimakon haka, cikin kowace al'umma duk mai ibada kuma mai aikata adalci karbabbe ne a gare shi.
\s5
\v 36 Ku kun san sakon da ya aika wa mutanen Isra'ila, a lokacin da ya sanar da labarin mai kyau na salama ta wurin Yesu Kristi, wanda shine Ubangiji na duka.
\v 37 Ku da kanku kun san al'amuran da suka kasance, wanda ya faru cikin Yahudiya, farawa daga Galili, bayan sanarwar baftismar da Yahaya ya yi.
\v 38 Al'amura game da Yesu Banazare, yadda Allah ya kebe shi da Ruhu Mai Tsarki da iko kuma. Ya kuma ci gaba da aikin alheri da warkarwa ga dukan wadanda shaidan ya daure, domin Allah yana tare da shi.
\s5
\v 39 Mu shaidu ne ga dukan abubuwan da ya yi a kasar Yahudawa da cikn Urushalima, wannan Yesu wanda suka kashe, ta wurin giciye shi a akan itace.
\v 40 Wannan mutumin, Allah ya ta da shi rana ta uku ya kuma maishe shi sananne,
\v 41 ba ga dukan mutane ba, amma ga shaidun da Allah ya zaba tun da farko - mu kanmu, wadanda muka ci muka sha tare da shi bayan tashin sa daga matattu,
\s5
\v 42 Ya umarce mu mu yi wa mutane wa'azi mu kuma tabbatar cewa shine wanda Allah ya zaba ya yi shariya bisa masu rai da matattu.
\v 43 Gareshi ne dukan annabawa suka yi shaida, domin dukan wanda ya bada gaskiya gareshi ya sami gafarar zunubai ta wurin sunansa.`
\s5
\v 44 Sa'adda Bitrus yana kan magana game da wadannan abubuwa, Ruhu Mai Tsarki ya sauko a kan dukan wadanda suke sauraron wa'azin sa.
\v 45 Mutanen da ke kungiyar masu bi da suka yarda da kaciya, dukan wadanda suka zo tare da Bitrus suka yi mamaki, domin baiwar Ruhu Mai Tsarki ya sauko a kan al'ummai.
\s5
\v 46 Domin sun ji al'umman nan suna magana da wasu harsuna suna yabon Allah. Sai Bitrus ya amsa,
\v 47 "Ko akwai wanda zai hana wa wadannan baftisma ta ruwa, da shike suma sun karbi Ruhu Mai Tsarki kamar mu?"
\v 48 Sai ya ba da umarni a yi masu baftisma cikin sunan Yesu Kristi. Sai suka roke shi ya kasance da su na wasu kwanaki.
\s5
\c 11
\p
\v 1 Yanzu Manzani da 'yan'uwa wadanda suke cikin Yahudiya suka ji cewa al'ummai ma sun karbi maganar Allah
\v 2 Lokacin da Bitrus ya je Urushalima, wadanda suke na kaciya suka zarge shi;
\v 3 suka ce, "Ka hada kai tare da mutane marasa kaciya kana ci tare da su!"
\s5
\v 4 Amma Bitrus ya fara bayyana masu dalla-dalla; ya ce,
\v 5 Ina addu'a a cikin birnin Yafa, sai na ga wahayi game da taska yana saukowa, kamar babban mayafi da aka saukar daga sama ta kusurwan nan hudu. Ya sauko gabana.
\v 6 Na zura masa ido kuma na yi tunani a kansa, na ga dabbobi masu kafa hudu na duniya, miyagun dabbobi, da masu rarrafe, da tsuntsayen sama.
\s5
\v 7 Sai na ji murya tana ce da ni, "Tashi, Bitrus, yanka ka ci."
\v 8 Na ce, "Ba haka ba, Ubangiji: gama babu abu mara tsarki ko mai kazanta da ya taba shiga bakina."
\v 9 Amma murya ta amsa kuma daga sama cewa, "Abin da Allah ya kira mai tsarki, kada ka kira shi mara tsarki."
\v 10 Wannan ya faru sau uku, sai dukan komai ya koma sama.
\s5
\v 11 Nan da nan sai ga mutane uku tsaye a gaban gidan da muke; an aike su daga Kaisariya zuwa gare ni.
\v 12 Ruhun ya umurce ni in tafi tare da su, ba tare da nuna banbanci game da su ba. Yan'uwan nan shida sun tafi tare da ni, sai muka shiga gidan mutumin.
\v 13 Ya fada mana yadda ya ga mala'ika tsaye a cikin gidansa yana cewa "Aiki mutane zuwa Yafa, su kirawo Saminu wanda ake kira Bitrus.
\v 14 Zai gaya maku sakon da za ku sami ceto kai da dukan gidanka."
\s5
\v 15 Da na fara magana da su, Ruhu Mai Tsarki ya sauko akansu kamar yadda ya sauko mana tun da farko.
\v 16 Sai na tuna da maganar Ubangiji, yadda ya ce,"Hakika Yahaya ya yi baptisma da ruwa, amma ku za a yi maku baptisma da Ruhu Mai Tsarki."
\s5
\v 17 To, idan Allah ya yi masu baiwa kamar yadda ya yi mana yayin da muka bada gaskiya ga Ubangiji Yesu Almasihu, wane ni da zan yi jayayya da Allah?
\v 18 Da suka ji wadannan abubuwa, suka rasa ta cewa, amma suka daukaka Allah suka ce "Ga al'ummai ma Allah ya basu tuba zuwa rai."
\s5
\v 19 Sai wadanda suka warwatsu saboda tsananin da ya bi bayan mutuwan Istifanas, suka yadu har zuwa Finikiya, Kuburus da Antakiya, amma suka yi wa'azin Yesu ga Yahudawa kadai.
\v 20 Amma wadan sunsu, mutane daga Kuburus da Kurane, suka zo Antakiya suka yi magana da hellenawa, suna yi masu wa'azin Ubangiji Yesu.
\v 21 Kuma ikon Ubangiji yana tare da su, har mutane da yawa suka gaskata kuma suka juyo wurin Ubangiji.
\s5
\v 22 Labari game da su ya iso kunnen ikilisiya da ke Urushalima: sai suka aika da Barnaba zuwa can Antakiya.
\v 23 Da ya iso kuma ya ga kyautar Allah, sai ya yi farinciki; ya karfafa su dukka su kafu cikin Ubangiji da dukan zuciyar su.
\v 24 Domin shi mutumin kirki ne, cike kuma da Ruhu Mai Tsarki da bangaskiya, sai mutane da yawa suka karu ga Ubangiji.
\s5
\v 25 Sai Barnaba ya tafi Tarsus domin ya nemi Shawulu.
\v 26 Da ya same shi, ya kawo shi Antakiya. Ya kasance, shekara guda suna taruwa tare da ikilisiya suka koyar da mutane da yawa. A Antakiya ne aka fara kiran almajiran Krista.
\s5
\v 27 A cikin kwanakin nan wadansu annabawa daga Urushalima suka zo Antakiya.
\v 28 Daya daga cikinsu, mai suna Agabas ya mike tsaye yayi magana da ikon Ruhu cewa za a yi tsanani fari ko'ina a duniya. Wannan ya faru ne a zamanin Kalaudiya.
\s5
\v 29 Sai, almajiran, suka dau niyya kowa gwargwadon karfinsa, su aika wa 'yan'uwa da ke Yahudiya da taimako.
\v 30 Suka yi haka; sun aika wa dattawa da kudi ta hanun Barnaba da Shawulu.
\s5
\c 12
\p
\v 1 A lokacin nan Sarki Hiridus ya sa wa wasu masu bi hannu domin ya musguna masu.
\v 2 Ya kashe Yakubu dan'uwan Yahaya da takobi.
\s5
\v 3 Bayan da ya ga hakan ya gamshi Yahudawa, sai ya kama Bitrus ma.
\v 4 Bayan ya kama shi, sai ya tsare shi a kurkuku ya kuwa sa sojoji hudu su dinga tsaron sa; yana niyyar kawo shi gaban mutanen a bayan Idin katarewa.
\s5
\v 5 To, Bitrus na tsare a kurkuku, amma 'yan'uwa na iklisiya suna yin addu'a ga Allah sosai domin sa.
\v 6 Ana kamar gobe Hiridus zai fitar da shi, a wannan daren, Bitrus yana barci a tsakanin sojoji biyu, daure da sarkoki biyu; sojoji kuma na gadi a bakin kurkukun.
\s5
\v 7 Ba zato, sai ga mala'ikan Ubangiji ya bayyana a gareshi, haske ya haskaka dakin. Ya taba Bitrus a gefe ya tashe shi kuma ya ce, "Tashi da sauri." Sai ga sarkokin suka zube daga hannunsa.
\v 8 Mala'ikan ya ce masa, "Yi damara ka sa takalmanka." Bitrus kuwa yayi haka. Mala'ikan ce ma sa, "Yafa mayafinka, ka biyo ni."
\s5
\v 9 Bitrus kuwa ya bi mala'ikan suka fita waje. Bai gane abin da mala'ikan ke yi zahiri ne ba. Yana zaton ko yana ganin wahayi ne.
\v 10 Bayan da suka wuce masu tsaron fari da na biyu, sun kai kofar da aka yi da karfe wadda ta mike zuwa cikin gari; ta bude masu da kanta. Suka fita sun bi titin, kuma nan take kuma sai mala'ikan ya bar shi.
\s5
\v 11 Da Bitrus ya komo hayyacin sa, ya ce, "Hakika yanzu na gane Ubangiji ya aiko da mala'ikansa don ya kubutar da ni daga hannun Hiridus da abin da Yahudawa suke zato."
\v 12 Da ya gane haka, ya zo gidan Maryamu mahaifiyar Yahaya wanda sunan mahaifinsa Markus; masu bi da yawa sun taru a can suna addu'a.
\s5
\v 13 Da ya kwankwasa kofar gidan, sai baiwar gidan mai suna Roda ta zo don ta bude kofar.
\v 14 Da ta gane muryar Bitrus, don farin ciki ta kasa bude kofar; maimakon haka, ta koma daki a guje, don ta basu labari Bitrus na tsaye a bakin kofa.
\v 15 Suka ce mata, "Kin haukace." Amma ta nace da cewa haka ne. Suka ce, "Mala'ikansa ne."
\s5
\v 16 Amma Bitrus ya ci gaba da kwankwasawa, da suka bude kofar, sai suka ga ai shine, suka sha mamaki kwarai.
\v 17 Bitrus kuwa ya yi masu hannu yana, masu alama su yi shuru. Sai ya gaya masu labarin yadda Ubangiji ya kubutar da shi daga kurkukun. Ya ce, "Ku gaya wa Yakubu da dukan 'yan'uwa abin da ya faru." Sai ya bar su, ya tafi wani wuri.
\s5
\v 18 Sa'anda gari ya waye ba karamar hargowa ce ta tashi a cikin sojojin ba, game da abin da ya faru da Bitrus.
\v 19 Bayan da Hiridus ya neme shi kuma bai same shi ba, sai ya tambayi masu tsaron kuma ya bada umarni a kashe su. Sai ya gangara daga Yahudiya zuwa Kaisariya ya yi zamansa a can.
\s5
\v 20 Yanzu kuwa Hiridus ya yi fushi sosai da mutanen Taya da Sidon. Suka tafi wurinsa tare. Suka roki Bilastasa, mataimakin sarkin, ya taimake su. Sai suka nemi sasantawa don suna samun abinci daga kasarsa ne.
\v 21 A ranan da aka kayyade, Hirudus ya sha damara da kayan saurata kuma ya zauna akan kursiyi; ya yi masu jawabi.
\s5
\v 22 Mutanen suka yi ihu, "Wannan muryar allahce, ba ta mutum ba!"
\v 23 Nan take mala'ika Ubangiji ya buge shi don bai ba Allah daukaka ba, nan take tsutsotsi suka cinye shi har ya mutu.
\s5
\v 24 Maganar Allah ta yadu tana ta ribabbanya.
\v 25 Bayan Barnaba da Shawulu sun gama aikin su a Urushalima. Suna dawowa, suka zo tare da Yahaya wanda sunan mahaifinsa Markus ne.
\s5
\c 13
\p
\v 1 A cikin iklisiyar da take Antakiya, akwai annabawa da malamai. Sune su Barnabas, Saminu (wadda ake kira Baki) da Lukiya Bakurame da Manayin (wanda aka yi renon su tare da sarki Hiridus mai mulki) da Shawulu.
\v 2 Sa'adda suke bauta wa Allah tare da azumi, sai Ruhu Mai Tsarki ya ce, "Ku kebe mani Barnaba da Shawulu domin aikin da na kiraye su".
\v 3 Bayan taron sun yi addu'a da azumi, sai suka sa masu hannu, su suka sallame su.
\s5
\v 4 Sai Shawulu da Barnabas suka yi biyayya da Ruhu Mai Tsarki suka tafi Sulukiya; daga nan suka ketare zuwa tsibirin Kuburus.
\v 5 Sa'adda suke garin Salami, suka koyar da maganar Ubangiji a majami'un Yahudawa, suna kuma tare da Yahaya Markus mai taimakonsu.
\s5
\v 6 Bayan sun zaga tsibirin duka har Bafusa, nan suka iske wani Bayahude mai suna Bar-yeshua mai tsafi kuma annabin karya.
\v 7 Wannan mai tsafin wanda ke tare da Makaddas, shi Sarjus Bulus mutum mai basira ne. Wannan kuwa ya kira Shawulu da Barnaba domin yana so ya ji maganar Allah.
\v 8 Amma Elimas "mai tsafi" (fasarar sunansa kenan) ya yi adawa da su; yana so ya baudar da Makaddashin daga bangaskiya.
\s5
\v 9 Amma Shawulu wanda ake ce da shi Bulus yana cike da Ruhu Mai Tsarki ya kafa masa ido.
\v 10 Sai ya ce, "Kai dan iblis, kana cike da kowace irin yaudara da mugunta. Kai abokin gabar kowanne irin adalci ne. Ba za ka daina karkata mikakkakun hanyoyin Ubangiji ba?
\s5
\v 11 Yanzu ga hannun Ubangiji bisa kanka, zaka zama makaho. Ba za ka ga rana ba nan da dan lokaci." Nan take kuwa sai wani hazo da duhu suka rufe shi ya fara yawo yana neman mutane su yi masa jagora.
\v 12 Bayan da Makaddashin ya ga abin da ya faru ya ba da gaskiya saboda ya yi mamakin koyarwa game da Ubangiji.
\s5
\v 13 Bulus da abokansa suka shirya suka ketare a jirgin ruwa daga Bafusa zuwa Firjiya a Bamfiliya. Amma Yahaya ya bar su ya koma Urushalima.
\v 14 Bulus da abokansa suka tafi daga Firjiya zuwa Antakiya na kasar Bisidiya. Nan suka shiga majami'a ran Asabaci suka zauna.
\v 15 Bayan karatun dokoki da annabawa, shugabanin iklisiyar suka tura sako cewa, "'Yan'uwa, idan kuna da wani sakon karfafawa ga jama'a ku fadi."
\s5
\v 16 Bulus kuwa ya tashi ya yi alama da hannunsa ya ce, "Mutanen Isra'ila da ku wadanda kuke girmama Allah, ku ji.
\v 17 Allahn Isar'ila ya zabi kakkaninmu ya kuma ribabbanya su sa'adda suke kasar Masar da kuma madaukakin iko ya fito da su daga cikinta.
\v 18 Ya yi hakuri da su a jeji har na tsawon shekara arba'in.
\s5
\v 19 Bayan ya hallaka kasashe bakwai a kasar Kan'ana, ya ba kakkaninmu kasar nan gado.
\v 20 Duk wadanan abubuwan sun faru shekaru dari hudu da hamsin da suka wuce. Bayan wadannan, Allah ya ba su alkalai har sai da annabi Sama'ila ya zo.
\s5
\v 21 Sai jama'a suka roka a ba su sarki, Allah kuwa ya ba su Saul dan Kish, mutumin kabilar Binyamin ya zama sarki har na tsawon shekara arba'in.
\v 22 Allah kuwa ya cire shi daga kan kujerar sarauta, ya daga Dauda ya zama sarkinsu. A kan Dauda ne Allah ya ce, 'Na sami Dauda dan Yessi, mutumin da zuciyata ke so; zai yi duk abin da nake so'.
\s5
\v 23 Daga zuriyar mutumin nan Allah ya fito da mai ceto, Yesu, kamar yadda aka alkawarta zai yi.
\v 24 Wannan ya faru kafin Yesu ya zo, Yahaya ya yi shelar baftimar tuba ga jamma'ar Isra'ila.
\v 25 Sa'adda Yahaya ya gama aikin sa, sai ya ce, 'Wanene ni a tsamanin ku? Ba nine shi ba. Amma ku saurara, akwai wani mai zuwa bayana wanda maballin takalminsa ban isa in kwance ba.'
\s5
\v 26 Yan'uwa 'ya'ya daga zuriyar Ibrahim, da wadanda ke bautar Allah a cikinku, saboda mune aka turo sakon ceto.
\v 27 Saboda wadanda ke zaune cikin Urushalima, da masu mulkinsu, ba su gane shi ba, kuma sun cika fadin annabawa da a ke karantawa kowace ranar Asabaci ta wurin kashe shi.
\s5
\v 28 Duk da cewa ba su sami dalilin mutuwa a kansa ba, suka roki Bilatus ya kashe shi.
\v 29 Bayan sun gama duk abin da aka rubuta game da shi, sai suka sauke shi daga giciye suka sa shi a cikin kabari.
\s5
\v 30 Amma Allah ya tashe shi daga matattu.
\v 31 Mutanen da suka zo tare da shi daga Galili da Urushalima kuwa suka yi ta ganinsa har kwanaki da yawa. Wadanan mutane kuma sune shaidunsa ga jama'a a yanzu.
\s5
\v 32 Mun kawo maku labari mai dadi game da alkawaran da aka yi wa kakkaninmu.
\v 33 Ubangiji ya bar mana alkawaran. Don haka ya ta da Yesu daga matattu. Kamar yadda ya ke a littafin zabura ta biyu: "Kai da na ne yau na zama mahaifinka."
\v 34 Kuma dalilin tayar da shi daga matattu shine saboda kada jikinsa ya rube, ya yi magana kamar haka: "Zan baku albarkun Dauda masu tsarki tabatattu."
\s5
\v 35 Wannan shine dalilin da ya yi magana kuma a wata Zabura, 'Ba za ka bar Mai Tsarkinka ya rube ba.'
\v 36 Bayan Dawuda ya yi wa Allah bauta a cikin zuciyarsa da kuma abin da Allah yake so, ya mutu, aka binne shi tare da kakkaninsa, ya kuma ruba,
\v 37 amma wanda Allah ya tayar bai ga ruba ba.
\s5
\v 38 'Yan'uwa, ku sani cewa ta wurin mutumin nan aka yi maku wa'azin gafarar zunubai.
\v 39 Ta wurinsa ne duk wanda ya ba da gaskiya zai kubuta daga dukan abin da dokar Musa bata 'yantar da ku a kai ba.
\s5
\v 40 Saboda haka ku yi hankali da abubuwan da annabawa suka fada kada su faru a kanku:
\v 41 'Ku masu reni, za ku rude don mamaki, ku kuma shude; saboda ina aiki a cikin kwananakinku, aikin da ba za ku yarda ba ko da wani ya gaya maku."
\s5
\v 42 Da Bulus da Barnaba suna fita kenan, sai jama'a suka rokesu, su sake yin irin wannan magana ranar Assabaci mai zuwa.
\v 43 Bayan da sujadar ta kare, Yahudawa da yawa da kuma wadanda suka shiga addinin Yahudanci suka bi Bulus da Barnaba, sai suka gargade su da su cigaba da aikin alherin Allah.
\s5
\v 44 Da Asabaci ta kewayo, kusan dukan garin suka taru domin su ji maganar Ubangiji.
\v 45 Sa'adda Yahudawa suka ga taron jama'a, sai suka cika da kishi suna karyata abubuwan da Bulus ya fada suka kuma aibata shi.
\s5
\v 46 Amma Bulus da Barnaba sun yi magana gabagadi suka ce, "Dole ne a fara fada maku maganar Allah. Amma da yake kun ture ta, kun nuna baku cancanci rai madawwami ba soboda haka zamu juya ga al'ummai.
\v 47 Don haka Ubangiji ya umarce mu, cewa, 'Na sa ku haske ga al'ummai, saboda ku kawo ceto ga iyakar duniya.'"
\s5
\v 48 Da al'ummai suka ji haka, sai suka yi murna suka kuma yabi kalmar Ubangiji. Dukan wadanda aka kaddarawa samin rai madawwami suka tuba.
\v 49 Kalmar Ubangiji kuwa ta bazu a kowanne bangaren yankin.
\s5
\v 50 Amma Yahudawan suka zuga wadansu mata masu sujada, masu daraja da kuma shugabannin mazan garin. Wannan ya tayar da tsanani ga Bulus da Barnaba har suka fitar da su daga iyakar garinsu.
\v 51 Amma Bulus da Barnaba suka kade masu kurar kafarsu. Suka tafi garin Ikoniya.
\v 52 Amma almajiran suka cika da farin ciki da kuma Ruhu Mai Tsarki.
\s5
\c 14
\p
\v 1 A lokacin da Bulus da Barnaba sun shiga garin Ikoniya suka shiga majami'an Yahudawa suka yi wa'azi yadda har mutane da yawa daga cikin Yahudawa da Hellinawa suka ba da gaskiya.
\v 2 Amma Yahudawa da basu yi biyayya ba, suka zuga al'umman har suka yi fushi da 'yan'uwan.
\s5
\v 3 Suka zauna a wurin na tsawon lokaci, suna yni maganarsu gabagadi da ikon Ubangiji, yana kuma shaidar sakon alherinsa. Ya yi wannan ta wurin alamu da al'ajibai ta hannun Bulus da Barnaba.
\v 4 Saboda haka mutanen garin sun rabu: wadansun su suka bi ra'ayin Yahudawa, wasu kuwa sun bi manzannin.
\s5
\v 5 Al'umman garin da Yahudawa sun nemi jan hankali shugabanninsu, don su wulakanta Bulus da Barnaba, su jajjefe su,
\v 6 da suka gane haka suka gudu zuwa biranen Likoniya, Listira da Darbe, da garuruwa wadanda ke kewaye da su,
\v 7 a can suka yi wa'azin bishara.
\s5
\v 8 A Listira akwai wani wanda ke zaune bai taba tashi da kafafunsa ba, don shi gurgu ne tun daga haihuwa.
\v 9 Wannan mutumin ya ji Bulus yana magana. Bulus ya kafa masa ido, ya gane mutumin na da bangaskiya da za a warkar da shi. Sai ya ce masa da murya mai karfi, "Tashi ka tsaya akan kafafunka"
\v 10 Sai mutumin ya yi tsalle ya fara tafiya da kafafunsa, yana yawo.
\s5
\v 11 Da jama'an garin sun ga abin da Bulus ya yi, suka tada muryarsu suna cewa da Likoniyanci, "Ai alloli sun ziyarce mu daga sama, da kamanin mutane."
\v 12 Suna kiran Barnaba da sunan "Zafsa," Bulus kuwa suka kira shi da sunan "Hamisa" domin shine yafi yin magana.
\v 13 Sai firist din zafsa wanda dakin yin masa sujada na kofar birni; ya kawo bijimai biyu da furannin da aka saka su kamar gammo; shi da jama'arsa suna so su yi masa hadaya.
\s5
\v 14 Amma da manzannin, wato Barnaba da Bulus, su ka ji labarin, suka yage rigunansu, suka hanzarta zuwa gun taron mutanen.
\v 15 Suna ta cewa, "Kuji! Ku mutane don me kuke wannan abin? Mu fa mutane ne kamarku. Mun kawo maku labari mai dadi ne, da cewa, ku rabu da abubuwa marar amfani, ku koma ga Allah mai rai, wanda ya hallici sama da kasa da teku da dukan abubuwa da ke cikinsu.
\v 16 A da dai ya bar mutane su yi abinda suka ga dama.
\s5
\v 17 Duk da haka, bai bar kansa ba tare da shaida ba, don yana bada abubuwa masu kyau, yana ba ku ruwan sama, lokatai masu albarka, ya cika ranku da abinci da farin ciki."
\v 18 Duk da wadannan kalmomin da kyar, Bulus da Barnaba suka iya tsayar da su daga yi masu hadaya.
\s5
\v 19 Amma wasu Yahudawa daga Antakiya da wasunsu daga Ikoniya suka rinjayi tarun jama'ar. Suka jajjefi Bulus suka ja shi zuwa wajen garin, suna ganin kamar ya mutu.
\v 20 Duk da haka da almajirai suka kewaye shi a tsaitsaye, sai ya tashi ya koma cikin garin. Washegari, ya tafi Darba tare Barnaba.
\s5
\v 21 Bayan sun yi wa'azin bishara a wannan birnin suka kuma sami almajirai da yawa, suka dawo Listira, da Ikoniya da Antikiya.
\v 22 Suna karfafa zuciyar almajiran su rike bangaskiyarsu, su ci gaba da ita, suna ce masu, "Ta wurin jimrewa mai yawa zamu shiga mulkin Allah, don haka dole ne mu sha wahala."
\s5
\v 23 Da suka zabar masu dattawa a kowace iklisiya, sai suka yi addu'oi da azumi, suka mika su ga Ubangiji, ga wanda suka gaskanta a gareshi.
\v 24 Sa'annan sun bi ta Bisidiya suka kai Bamfiliya.
\v 25 Da suka yi maganarsu a Biriya, sun wuce zuwa har Italiya.
\v 26 Ta jirgin ruwa zuwa Antakiya, a nan ne aka mika su ga alherin Allah don aikin da suka gama a yanzu.
\s5
\v 27 Da isowarsu Antakiya sun tara 'yan iklisiya a wuri daya, sun ba da labarin dukan abin da Allah ya yi ta wurinsu. Da yadda Ya bude kofa a wurin al'ummai ta bangaskiya.
\v 28 Sun zauna tare da almajiran na tsawon lokaci.
\s5
\c 15
\p
\v 1 Wadansu mutane suka zo daga Yahudiya suka koyar da 'yan'uwa, cewa, "Idan ba yi maku kaciya bisa ga al'addar Musa ba, ba za ku sami ceto ba."
\v 2 Da Bulus da Barnaba suka tunkare su da mahawara, sai 'yan'uwa suka yanke shawara Bulus da Barnaba da wasu su je Urushalima wurin manzanni da dattawa a kan wannan magana.
\s5
\v 3 Da shike iklisiya ce ta aike su, sai suka bi ta Finikiya da ta Samariya suka sanar da tuban al'ummai. Ya kawo murna mai yawa a wurin 'yan'uwa.
\v 4 Bayan sun zo Urushalima, sai iklisiya da manzanni da dattawa, suka marabce su, sai suka fada masu abin da Allah ya yi ta wurinsu.
\s5
\v 5 Amma wadansu mutane wadanda suka ba da gaskiya daga cikin Farisawa, suka tashi suka ce, "Dole ne a yi masu kaciya a kuma umarce su su kiyaye dokar Musa."
\v 6 Sai manzanin da dattawan suka taru don su duba wannan lamari.
\s5
\v 7 Bayan mahawara mai tsanani, sai Bitrus ya tashi ya ce masu, "'Yan'uwa, kun san lokacin baya da ya wuce, Allah ya yi zabi a cikinku, cewa ta bakina ne al'ummai za su ji bishara, su kuma ba da gaskiya.
\v 8 Allah, wanda ya san zuciya, ya yi masu shaida, ya kuma basu Ruhu Mai Tsarki kamar yadda ya yi mana;
\v 9 kuma bai bambanta mu da su ba, ya tsabtace zuciyarsu ta wurin bangaskiya.
\s5
\v 10 To, saboda haka don me kuke gwada Allah, kuna sa wa almajirai nauyi a wuya wanda ubanninmu duk da mu ba mu iya dauka ba?
\v 11 Amma mun gaskanta za mu samu ceto ta wurin alherin Ubangiji Yesu, kamar yadda suke."
\s5
\v 12 Dukan taron jama'ar suka yi shiru sa'adda suke sauraron sakon shaidar da mamakin abin da Allah ya yi ta wurin Bulus da Barnaba a cikin al'ummai.
\s5
\v 13 Bayan sun gama magana, Yakubu ya amsa, ya ce, "'Yan'uwa, ku ji ni.
\v 14 Saminu ya fada yadda Allah ya fara nuna jinkai ga al'ummai domin ya dauke jama'a daga cikinsu domin sunansa.
\s5
\v 15 Maganar annabawa ta yarda da wannan, kamar yadda yake a rubuce,
\v 16 'Bayan wadannan abubuwa zan dawo, zan gina gidan Dauda wanda ya fadi kasa; in sake gina bangonsa, in tsayar da shi,
\v 17 saboda sauran jama'a su nemi fuskar Ubangiji, har da al'ummai da ake kira da sunana.
\v 18 Wannan shine abin da Ubangiji ya fadi, shi wanda ya yi wadannan abubuwa da aka sani tun zamanin da.
\s5
\v 19 Saboda haka, a gani na kada mu matsa wa al'umman da suka juyo gun Allah;
\v 20 amma zamu rubuta masu da cewa, su guje wa gumaka da zina da faskanci da maye da cin mushe.
\v 21 Tun zamanin da akwai mutane a kowanne birni wadanda suke wa'azi da karatun Musa a majami'u kowanne Asabaci."
\s5
\v 22 Sai ya yi wa manzanin kyau su da dattawa da dukan iklisiyar su zabi Yahuza da Barnaba da Sila da dattawan iklisiya a tura su Antakiya tare da Bulus da Barnaba.
\v 23 Sai suka rubuta wasika, "Manzani da dattawa da 'yan'uwa zuwa ga al'ummai 'yan'uwa a Antakiya da Suriya da Kilikiya, gaisuwa mai yawa.
\s5
\v 24 Mun ji cewa wasu mutane daga cikinmu wadanda ba mu umarce su ba, sun fita daga cikinmu sun yi maku koyarwar da ta daga maku hankali.
\v 25 Ya yi kyau da dukanmu, muka amince mu zabi wadansu mutane mu tura su wurinku tare da Bulus da Barnaba,
\v 26 mutane wadanda suka sadaukar da ransu domin sunan Ubangiji Yesu Almasihu.
\s5
\v 27 Mun aika Yahuza da Sila su gaya maku wadannan abubuwa.
\v 28 Saboda haka ya yi kyau Ruhu Mai Tsarki da mu, kada mu sa maku nauyi fiye da wadannan abubuwan:
\v 29 ku bar yi wa gumaka hadaya, ku bar cin mushe da shan kayan maye da zina da faskanci, in kun kiyaye wadannan abubuwa za ku zauna lafiya. Ku huta lafiya."
\s5
\v 30 Da aka sallame su, sai suka je Antakiya. Bayan sun tara jama'a sai suka ba su wasikar.
\v 31 Bayan da suka karanta ta, sai suka yi murna sosai saboda karfafawa.
\v 32 Yahuza da Sila, da shike su annabawa ne, suka karfafa 'yan'uwa da kalmomi masu yawa.
\s5
\v 33 Bayan sun yi kwananki a wurin, sai aka sallame su zuwa wurin 'yan'uwa wadanda suka aiko su.
\v 34 Amma ya gamshe Sila ya zauna a wurin.
\v 35 Amma Bulus da Barnaba suka tsaya a Antakiya da sauran 'yan'uwa, suna koyar da maganar Ubangiji.
\s5
\v 36 Bayan kwanaki kadan Bulus ya ce ma Barnaba, "Mu koma yanzu mu ziyarci dukan 'yan'uwa da muka yi masu bisharar Ubangiji, mu ga yadda suke.
\v 37 Barnaba yana so su dauki Yahaya wanda kuma ake kira Markus.
\v 38 Amma Bulus ya yi tunanin bai kamata a tafi da Markus ba, tun da ya bar su a Bamfiliya bai ci gaba da su ba.
\s5
\v 39 Nan jayayya ta tashi tsakaninsu, har suka rabu da juna sai Barnaba ya tafi tare da Markus suka ketare zuwa Kuburus.
\v 40 Amma Bulus ya zabi Sila suka tafi, bayan 'yan'uwa sun yi masu addu'ar alherin Allah ya kiyaye su.
\v 41 Bulus ya tafi ya zazzaga Suriya da Kilikiya yana ta karfafa iklisiyoyin.
\s5
\c 16
\p
\v 1 Bulus ya kuma isa Darbe da Listira, in da akwai wani almajiri mai suna Timoti a wurin, dan wata Bayahudiya wadda ta ba da gaskiya; ubansa kuwa Baheline ne.
\v 2 Ana maganar kirki a kansa ta bakin 'yan'uwa da ke Listira da Ikoniyan.
\v 3 Bulus ya yi wa Timoti kaciya, domin yana so su yi tafiya tare, domin kuma saboda Yahudawan da ke wurin, sun san cewa ubansa Baheline ne.
\s5
\v 4 Suna shiga cikin biranen, suna yi wa iklisiyoyi gargadi da su yi biyayya da umurnan da Manzanni da dattawa suka rubuta a Urushalima.
\v 5 Bangaskiyar iklisiyoyi kuwa ta karu, ana kuma samun karuwa na wadanda suke ba da gaskiya kowace rana.
\s5
\v 6 Bulus da abokan aikin sa sun shiga cikin lardin Firigiya da Galatiya, tun da Ruhu Mai Tsarki ya hana su wa'azin kalmar a cikin yankin Asiya.
\v 7 Sun zo kusa da Misiya, da nufin shiga cikin Bitiniya, Ruhun Yesu ya hana su.
\v 8 Da suka ratse ta cikin Misiya, sai suka shiga birnin Taruwasa.
\s5
\v 9 Bulus ya ga wahayi cikin dare, wani mutumin Makidoniya na kiransa, yana cewa. "Ka zo Makidoniya ka taimake mu".
\v 10 Bulus, da ganin haka, ya kama hanya zuwa Makidoniya, da tunanin Allah ne ya ke so su kai wa mutanen Makidoniya bishara.
\s5
\v 11 Da barin Taruwasa, Bulus da kungiyarsa sun shiga jirgin ruwa zuwa Samutaraki, da gari ya waye kuma sun tafi Niyafolis;
\v 12 Daga nan kuma suka tafi Filibi, birni na Makidoniya, mai muhimmanci ne a yankin Roma, in da mun yi zango kwanaki da dama.
\v 13 Ranar Asabaci mun je kofar gari, gefen rafi, da tunanin samun wurin addu'a. Mun zauna mun kuma yi magana da matan da sun taru a wurin.
\s5
\v 14 Wata mace mai suna Lidiya, 'yar kasuwa ce a birnin Tiyatira, mai bautar Allah ce, ta saurare mu. Ubangiji ya bude zuciyarta, ta mai da hankali ga maganar da Bulus ke fadi.
\v 15 Sa'anda da aka yi mata Baftisma tare da mutanen gidanta, ta ce da mu, "Idan kun dauke ni mai bautar Allah, ku zo gidana ku zauna." Sai ta rinjaye mu.
\s5
\v 16 A daidai wannan lokaci, muna tafiya wurin addu'a, wata yarinya mai ruhun duba ta hadu da mu. Iyayen gijinta na arziki da ita sosai.
\v 17 Tana bin Bulus, tare da mu, tana fadi da murya mai karfi cewa, "Wadannan mutanen, bayin Allah mafi daukaka ne, suna sanar maku hanyar ceto ne".
\v 18 Ta dauki kwanaki tana haka. Amma Bulus ya yi fushi da ita ainun, ya juya ya umarci ruhun, ya ce, "Na umarce ka, ka rabu da ita a cikin sunan Yesu Almasihu". Ruhun ya yi biyayya ya rabu da ita nan take.
\s5
\v 19 Da iyayengijinta suka ga cewa hanyar shigar kudinsu ta toshe, sai suka kama Bulus da Sila, suka ja su cikin kasuwa suka kai su gaban mahunkunta.
\v 20 Da suka kai su Kotu, suka ce, "Wadannan mutane Yahudawa ne, suna kawo tashin hankali a birninmu.
\v 21 Suna koyar da abubuwa da ba su karbuwa a gare mu, balle mu aikata, a matsayinmu na Romawa."
\s5
\v 22 Sai jama'a gaba daya sun tayar wa Bulus da Sila; alkalan kuma sun yage rigunansu, sun ba da umarni a duki Bulus da Sila da bulala.
\v 23 Bayan dukan, an jefa su Bulus a kurkuku, an ba mai tsaron kurkukun umurni ya kulle su da kyau, kada su gudu.
\v 24 Shi kuma ya yi hakanan, ya sa masu sarkoki a kafafun su, kamar yadda aka umurce shi.
\s5
\v 25 Da tsakar dare, Bulus da Sila suna yin adu'a, su na raira wakoki ga Allah, sauran 'yan sarkar su na jin su.
\v 26 Nan da nan sai ga wata girgizar kasa, wadda ta sa ginshikan kurkukun sun kadu, nan da nan kofofin kurkukun sun bude, 'yan sarka kuma, sarkokin su sun karkatse.
\s5
\v 27 Mai tsaron kurkukun ya tashi daga barci ya ga kofofin kurkukun a bude, ya zaro takobi, zai kashe kan sa, a tunanin sa, 'yan sarkar sun gudu.
\v 28 Amma Bulus ya ta da murya da karfi, ya ce, "kada kayi wa kanka barna, domin dukan mu muna nan".
\s5
\v 29 Mai tsaron kurkukun ya aika a kawo fitila, ya shiga ciki a gurguje da rawan jiki, ya fadi a gaban Bulus da Sila,
\v 30 ya fitar da su waje ya ce, "Shugabanni, me ya kamata in yi domin in tsira?"
\v 31 Sun ce masa, "ka ba da gaskiya ga Yesu Ubangiji, da kai da gidan ka, za ku sami tsira".
\s5
\v 32 Bulus da Sila suka fada masa maganar Ubangiji, tare da iyalinsa.
\v 33 Shi mai tsaron kurkukun ya dauke su cikin daren, ya wanke raunukansu, an kuma yi masa Baftisma nan da nan tare da iyalinsa.
\v 34 Ya kai Bulus da Sila gidansa, ya ba su abinci. Murna ta cika gidan mai tsaron kurkukun, domin iyalin sa duka sun ba da gaskiya ga Allah.
\s5
\v 35 Da gari ya waye, alkalai sun ba da sako a saki Bulus da Sila.
\v 36 Mai tsaron kurkukun kuwa ya sanar wa Bulus wannan magana ta alkalan, saboda haka ya ce wa Bulus, "Ku tafi cikin salama".
\s5
\v 37 Amma Bulus ya ce masu, "Sun yi mana duka a fili a gaban mutane mu da muke Romawa, ba a kashe mu ba, sun kuma sa mu a kurkuku; suna koran mu a asirce? Su zo da kansu su fitar da mu.
\v 38 Masu tsaron kurkuku sun mayar da maganar Bulus ga alkalan, wanda ya sa sun firgita, da jin cewa Bulus da Sila Romawa ne.
\v 39 Alkalai da kansu sun zo sun roki Bulus da Sila; da suka fitar da su daga kurkukun, sun ce wa Bulus da Sila su bar birnin.
\s5
\v 40 Da hakanan ne Bulus da Sila suka fita daga kurkuku, sun je gidan Lidiya. Da Bulus da Sila sun ga 'yan'uwa, sun karfafa su, sa'annan suka bar birnin.
\s5
\c 17
\p
\v 1 Bayan sun wuce biranen Amfibolis da Aboloniya, sun iso birnin Tasalunika, in da akwai wata majami'ar Yahudawa a wurin.
\v 2 Bulus, kamar yadda ya saba, ya nufi wurinsu, yana tattaunawa da su har Asabaci uku, daga cikin littattafai.
\s5
\v 3 Bulus ya bude littattafai yana bayyana masu cewa, dole ne Almasihu ya sha wahala, ya kuma tashi daga matattu. Ya ce, "Wannan Yesu kuwa da nake sanar maku, shine Almasihu".
\v 4 Wasu Yahudawa sun yarda, sun bi Bulus da Sila, da wadansu Helenawa, da Shugabannin Mata da jama'a da yawa.
\s5
\v 5 Yahudawan da basu ba da gaskiya ba suka cika da kishi, suka dauki wadansu 'yan ta'adda daga cikin kasuwa, suka tada tarzoma cikin birnin, mutane da yawa na bin su. Sun kai hari a gidan Yason, da niyyar fitar da Bulus da Sila a gaban jama'a.
\v 6 Amma da ba su ga Bulus da Sila ba, suka ja Yason da wasu 'yan'uwa masu bi zuwa gaban mahukuntar birnin, suna cewa, "Wadannan ne fa masu ta da zaune tsaye, gashi sun zo mana.
\v 7 Wadannan mutane da Yason ya marabta, sun saba wa dokokin Kaisar; Suna cewa akwai wani sarki mai suna - Yesu."
\s5
\v 8 Da taron jama'a, da mahukuntan birnin suka ji haka, sun damu.
\v 9 Bayan da sun amshi kudi daga wurin Yason da sauran 'yan'uwan, sai suka sake su.
\s5
\v 10 A wannan daren, 'yan'uwa masu bi suka fitar da Bulus da Sila, suka aike su garin Biriya. Da isar su can, su ka nufa majami'ar Yahudawa.
\v 11 Mutanen Biriya daban suke da na Tasalunika, sun yarda da sakon Bulus da zuciya daya, suna kuma binciken littattafai kowace rana domin su tabbatar da sakon Bulus, ko gaskiya ne.
\v 12 Saboda haka mutane da yawa cikin su sun ba da gaskiya, tare da wadansu sannanun mata Helenawa da maza da yawa.
\s5
\v 13 Amma da Yahudawan Tasalunika suka ji cewa Bulus yana wa'azin kalmar Allah a Biriya, sun haura can, sun tada hankulan jama'a.
\v 14 Nan da nan, masu bi na Biriya sun dauki Bulus sun aika shi zuwa teku, an bar Sila da Timoti a Biriya tukuna.
\v 15 Wadanda sun fitar da Bulus, sun kai shi har zuwa birnin Atina. Bulus ya ba su sako, su fada wa Sila da Timoti suyi hanzari su same shi.
\s5
\v 16 Sa'anda Bulus yana jiran zuwan Sila da Timoti a Atina, ya yi fushi a ransa, da ya ga birnin cike da gumakai.
\v 17 Ya tattauna da Yahudawa a cikin majami'a tare da masu yin sujada ga Allah, da kuma wadanda yake samu a kowace rana, a kasuwa.
\s5
\v 18 Amma wadan su Abikuriyawa da masana sun yi karo da shi. Wadansun su na cewa, "Menene wannan sakaren ke cewa?" Wadansu kuma sun ce, "Da alama mai wa'azi ne na wasu alloli dabam," domin yana wa'azin Yesu da tashin sa daga matattu.
\s5
\v 19 Suka dauki Bulus zuwa Tudun Arasa, suna cewa, "Ko za ka sanar mana da wannan sabuwar koyaswar taka?
\v 20 Abubbuwan da kake fadi, baki ne a gare mu. Muna so mu san ma'anar su."
\v 21 (Atiniyawa da bakin da ke cikinsu, suna ba da lokacin su ga fadin sabobbin abubuwa da sauraron su).
\s5
\v 22 Bulus ya tsaya a tsakiyar Tudun Arasa ya ce, "Ku mutanen Atiniya na lura masu kwazon addini ne ku.
\v 23 Na lura da abubuwan sujadar ku yayin da nake zagawa, amma na ga wani bagadi da rubutu a kansa mai cewa, "Ga Allah wanda ba a sani ba." Abin da kuke bauta wa cikin rashin sani, shi nake sanar maku.
\s5
\v 24 Allahn da ya yi duniya da kome da ke cikinta, tun da ya ke shine Ubangijin sama da kasa, ba ya zama a haikalin da mutane suka gina da hannu.
\v 25 Ba ya neman taimakon kowa, babu kuma wanda ya isa ya ba shi. Shine ke ba da rai, da numfashi da kowanne abu.
\s5
\v 26 Daga mutum daya ya hallici dukan al'umman duniya, ya rarraba, ya kuma sanya kowa a inda ya shirya masa.
\v 27 Domin su nemi Allah ko za su iya kaiwa zuwa gareshi su same shi, ga shi kuwa ba ya nesa da kowannenmu.
\s5
\v 28 A cikinsa muke rayuwa, muna walwala, kamar yadda wani daga cikin masananku yace, 'Mu 'ya'yansa ne'.
\v 29 Idan mu 'ya'yan Allah ne, bai kamata mu danganta Allah da zinariya ko azurfa, ko kuma duwatsu da itatuwa da an sassaka ba.
\s5
\v 30 Saboda haka ne, Allah ya kawar da kwanakin jahilci, amma ya ba da umarni kowa a ko'ina ya tuba.
\v 31 Akwai ranar da ya shirya zai yi wa duniya shari'a cikin adalci, ta wurin mutumin da ya zaba. Allah ya nuna wannan mutumin, ta wurin ta da shi daga matattu".
\s5
\v 32 Da mutanen Atina sun ji batun tashi daga matattu, wadansu suka yi wa Bulus ba'a; amma wadansu kuma sun ce, "Za mu saurare ka kuma, a kan wannan maganar."
\v 33 Bayan haka, Bulus ya bar su.
\v 34 Amma wasu maza a cikinsu sun yarda da bisharar, sun ba da gaskiya, hade da Diyonisiyus dan Majalisar Tudun Arasa da wata mace mai suna Damaris, da wadansu tare da su.
\s5
\c 18
\p
\v 1 Bayan haka sai Bulus ya tafi Antakiya daga nan, ya wuce Korinti.
\v 2 A can ya sadu da wani Bayahude mai sunan Akila, dan kasar Buntus ne; bai dade da zuwa garin ba, daga Italiya ya zo da matarsa mai suna Balkisu, saboda Kalaudiyas ya ba da umarni dukan Yahudawa su bar Roma; sai Bulus ya je wurinsu.
\v 3 Bulus ya zauna a gidansu don sana'arsu daya ce, wato, masu aikin Tanti ne.
\s5
\v 4 Saboda haka Bulus na zuwa majami'a, yana yin nazari tare da su a kowace Asabaci. Yana kokari ya rinjayi Yahudawa da Helinawa.
\v 5 Amma a lokacin da Sila da Timoti suka iso Makidoniya, Ruhu ya matsa Bulus ya shaida wa Yahudawa cewa Yesu Almasihu ne.
\v 6 Lokacin da Yahudawa suka tayar masa suna zarginsa. Bulus ya kakkabe rigansa a gabansu yana cewa, "Alhakin jininku yana kanku; daga yanzu zan koma wurin al'ummai."
\s5
\v 7 Da ya bar wurinsu, ya tafi gidan Taitus Yustus mai wa Allah sujada. Gidansa na kusa da majami'a.
\v 8 Kiristus shine shugaban majami'a, sai shi da dukan iyalin gidansa sun ba da gaskiya ga Ubangiji. Korantiyawa da yawa suka ji jawabin Bulus suka ba da gaskiya, aka yi masu Baftisma.
\s5
\v 9 Da dare Ubangiji ya ce wa Bulus a cikin wahayi, "Kada ka ji tsoro, amma ka yi magana kada kuma ka yi shuru.
\v 10 Gama ina tare da kai, ba wanda zai cutar da kai, gama ina da mutane anan garin."
\v 11 Bulus ya zauna a nan tsawon shekara daya da wata shida, yana koyar masu da maganar Allah.
\s5
\v 12 Amma da Galiyo ya samu zaman gwamnan Akaya, sai Yahudawa suka tayar wa Bulus har suka kai shi gaban dakalin shari'a.
\v 13 Suna cewa, "Wannan mutumin yana kokarin rinjayar mutane su yi sujadar da ta saba wa dokarmu."
\s5
\v 14 Duk da haka kafin Bulus ya yi magana, Galiyo ya ce wa Yahudawa, "Ku Yahudawa in da karar ku ta wani babban laifi ce wanda ya aikata, da sai in hukunta.
\v 15 Amma tun da ya ke akan al'amurar, kalmomi ne, da ta sunaye da dokokin ku, ku je ku sasanta al'amuran ku."
\s5
\v 16 Galiyo ya kore su daga dakalin shari'a.
\v 17 Saboda haka sai suka kama Sastanisu, suka yi masa duka sosai a gaban dakalin shari'a. Amma Galiyo bai damu da yadda suka karasa ba.
\s5
\v 18 Bulus kuwa, bayan ya zauna tare da su na wasu kwanaki masu yawa, ya bar 'yan'uwan zuwa Suriya ta jirgin ruwa, tare da Balkisu da Akila. Kafin ya bar tashar jiragen ruwa da ke a Sankuriya, ya tafi saboda ya aske kansa, domin ya dauki alkawarin Banazare.
\v 19 Da suka iso Afisa, Bulus ya bar Balkisu da Akila anan. Shi kuwa ya shiga majami'ar Yahudawa yana nazari tare da su.
\s5
\v 20 Da suka roki Bulus ya zauna da su na tsawon lokaci, bai yarda ba.
\v 21 Ya kama hanyarsa ya bar su ya ce, "In Allah ya yardar mani zan dawo wurinku wata rana." Sai ya shiga jirgin ruwa daga Afisa.
\s5
\v 22 Daga saukar su a Kaisariya, sai ya haura zuwa Urushalima ya gai da iklisiya daga nan ya tafi Antakiya.
\v 23 Bayan ya zauna na dan lokaci a wurin, Bulus ya kama hanyarsa zuwa yakin Galatiya da Firjiya anan ya karfafa almajirai.
\s5
\v 24 A nan dai akwai wani Bayahude mai suna Afolos, dan asalin Iskandariya ne da haihuwa, ya zo Afisa. Shi masani ne a maganar Allah.
\v 25 Afolos dai ya sami horo daga maganar Ubangiji. Shi mai kokari ne a ruhu, yana wa'azi da koyarwa daidai game da Yesu. Amma ya san da Baftismar Yahaya ne kadai.
\v 26 Afolos ya fara wa'azinsa da gabagadi a cikin majami'a. Da Balkisu da Akila suka ji shi sai suka yi abokantaka da shi, suka kara bayyana masa game da labarin hanyar Allah mafi daidai.
\s5
\v 27 Da ya so ya wuce zuwa cikin Akaya 'yan'uwa suka karfafa shi, sun rubuta wa almajiran da ke a Akaya, don su karbe shi da hannu biyu. Da ya iso wurinsu, ya kuwa karfafa 'yan'uwa da sun ba da gaskiya ta wurin alheri.
\v 28 Afolos ya ba Yahudawa mamaki da irin ikon da yake da shi da gwanintarsa, yadda yake nunawa daga nassoshi cewa Yesu shine Almasihu.
\s5
\c 19
\p
\v 1 Sa'adda Afolos yake a Koranti, Bulus ya zagaya kasar tudu ya zo birnin Afisa, a nan kuma ya sami wadansu almajirai.
\v 2 Bulus ya ce masu, "Ko kun karbi Ruhu Mai Tsarki sa'anda kuka ba da gaskiya?" Suka amsa, "A'a bamu taba jin labarin Ruhu Mai Tsarki ba.
\s5
\v 3 Bulus ya ce, "Wacce irin baftisma aka yi maku?" Suka ce, "Baftismar Yahaya"
\v 4 Bulus ya amsa ya ce, "Yahaya ya yi wa mutane baftismar tuba, ya ce su ba da gaskiya wanda zai zo bayansa, wato, Yesu kenan."
\s5
\v 5 Da mutanen suka ji haka, sai aka yi masu baftisma cikin sunan Ubangiji Yesu.
\v 6 Sa'adda Bulus ya dibiya hannu a kansu, Ruhu Mai Tsarki kuma ya sauka a kansu suka yi magana da harsuna da kuma annabci.
\v 7 Su wajen mutum goma sha biyu ne.
\s5
\v 8 Bulus ya shiga majami'a ya yi ta koyarwa gabagadi misalin tsawon wata uku. Yana bi da su cikin nazarin maganar yana fahimtar da mutane su gaskanta game da abubuwa da suka shafi mulkin Allah.
\v 9 Amma sa'adda wadansu Yahudawa suka taurare, suka ki yin biyayya, sai suka fara bata hanyar Almasihu a gaban taron. Saboda haka sai Bulus ya janye daga wurinsu tare da wadanda suka ba da gaskiya. Ya fara koyarwa a makarantar Tiranus.
\v 10 Haka ya cigaba shekaru biyu har duk mazaunan Asiya suka ji maganar Ubangiji, Yahudawa da Helenawa.
\s5
\v 11 Allah ya yi manyan al'ajibai ta hannun Bulus,
\v 12 har marasa lafiya suka warke, mugayen ruhohi suka fito daga cikin mutane, sa'adda suka karbi kyallaye da mayafai daga jikin Bulus.
\s5
\v 13 Amma akwai Yahudawa masu tsubu da suka biyo ta wajen, suka dauka wa kansu su yi amfani da sunan Yesu. Suka ce, "Mun dokace ku cikin sunan Yesu wanda Bulus yake wa'azinsa, ku fita."
\v 14 Wadanda suka yi wannan su bakwai ne 'ya'yan wani babban firist Bayahude mai suna Siba.
\s5
\v 15 Mugun ruhun ya amsa ya ce, "Na san Yesu, na san Bulus, amma ku, su wanene?"
\v 16 Sai mugun ruhun da ke cikin mutumin ya fada a kan matsubatan ya fi karfinsu ya kuma bubuge su. Suka runtuma da gudu suka fice daga dakin tsirara da raunuka.
\v 17 Wannan ya zama sanannen abu ga dukan mutane, Yahudawa da Helenawa mazaunan Afisa. Suka ji tsoro kwarai, sunan Ubangiji Yesu ya sami daukaka.
\s5
\v 18 Masu bi da yawa kuma, suka zo suka furta mugayen ayyukan da suka aikata.
\v 19 Masu sihiri suka kawo littattafansu suka kona a gaban mutane. Da aka yi jimilar tamaninsu, aka samu sun kai dubu hamsin na azurfa.
\v 20 Sai maganar Ubangiji ta yadu da iko ta hanyoyi da yawa.
\s5
\v 21 Da Bulus ya kammala aikinsa na bishara a Afisa, Ruhu ya bishe shi sai ya bi ta Makidoniya da Akiya a kan hanyarsa zuwa Urushalima. Ya ce, "Bayan na je can, dole in je Roma."
\v 22 Bulus ya aiki almajiransa biyu Timoti da Irastus zuwa Makidoniya, wadanda suka taimake shi. Amma shi da kansa ya jira a Asiya na dan lokaci.
\s5
\v 23 A wannan lokacin sai aka yi babban tashin hankali a Afisa game da wannan Hanyar.
\v 24 Wani Makeri mai suna Damatrayus wanda ke kera sifoffin gunkin azurfa na Dayana, wanda sana'a ce mai kawo wa makera riba sosai.
\v 25 Ya tattara makera ya ce da su, "Kun sa ni da wanan sana'a ne muke samun kudi mai yawa.
\s5
\v 26 Kun gani kun kuma ji cewa, ba a Afisa kadai ba, amma har da fadin kasar Asiya wannan Bulus ya rinjayi mutane da yawa. Yana cewa babu alloli da ake kerawa da hannu.
\v 27 Ba sana'ar mu kadai ke cikin hatsari ba, amma har da haikalin allahnmu Dayana babba zai zama mara amfani. Ta haka za ta rasa girmanta, ita da dukan kasar Asiya da duniya ke wa sujada."
\s5
\v 28 Da suka ji haka sai suka fusata kwarai, suka yi kira mai karfi suna cewa "Mai girma ce Dayana ta Afisa."
\v 29 Gari gaba daya ya rude, jama'a kuma sun hanzarta zuwa wurin taron. Kafin wannan lokaci, sun riga sun kama abokan tafiyar Bulus, wato Gayus da Aristakas wadanda suka zo daga Makidoniya.
\s5
\v 30 Bulus ya yi niyya ya shiga cikin taron jama'ar, amma almajiran suka hana shi.
\v 31 Haka nan ma wadansu abokan Bulus da ke shugabanin yankin al'umma Asiya sun aika masa da roko mai karfi kada ya shiga dandalin.
\v 32 Wadansu mutane na kirarin wani abu, wadansu kuma na kirarin wani abu dabam, domin jama'a sun rude. Da yawa daga cikinsu ma ba su san dalilin taruwarsu ba.
\s5
\v 33 Yahudawa suka kawo Iskandari ya tsaya a gaban taruwan jama'a. Iskandari ya mika hannunsa sama domin ya yi bayani ga jama'a.
\v 34 Amma da suka gane shi Bayahude ne, sai dukansu suka kwala ihu wajen sa'a biyu, "Mai girma ce Dayana ta Afisa."
\s5
\v 35 Da magatakardar garin ya sha kan jama'a, sai ya ce, "Ya ku mutanen Afisa, wanene bai san cewa birnin Afisa cibiya ce na allahn nan Dayana mai girma da na sifar da ta fado daga sama ba?
\v 36 Tun da ba a karyata wadannan abubuwa ba, ya kamata ku yi shuru don kada ku yi wani abu a gaggauce.
\v 37 Gama kun kawo wadannan mutane a wannan dakin sharia ba a kan su mafasa ne na haikali ba ko kuma masu sabo ga allahnmu ba.
\s5
\v 38 Saboda haka idan Damatrayas da makeran da ke tare da su na da wata tuhuma a kan wani, kotuna suna nan a bude masu shari'a kuma suna nan. Ba ri su kai karar junansu.
\v 39 Amma idan akwai maganganu na dubawa, za a daidaita su a taronmu na lokaci lokaci.
\v 40 Domin hakika muna cikin hatsarin zargi game da hargitsin yau. Babu dalilin wanan yamutsi domin ba mu da bayani a kansa."
\v 41 Da ya fadi haka, sai ya sallami taron.
\s5
\c 20
\p
\v 1 Bayan da rikici ya kare, Bulus ya aika a kira al'majiran, ya karfafa su. Sa'annan ya yi bankwana da su, ya tashi zai tafi Makidoniya.
\v 2 Bayan ya ratsa cikin lardunan yana yi wa masu bi gargadi sosai, sai ya zo kasar Helenawa.
\v 3 Sa'adda ya yi wata uku a wurin, Yahudawa suka kulla masa makirci, yayin da yake shirin hawa Jirgi zuwa Suriya, sai ya canza ra'ayi ya koma ta Makidoniya.
\s5
\v 4 Masu yi wa Bulus rakiyar zuwa yankin Asiya sun hada da Sobatarus dan Burus daga Biriya; Gayus mutumin Derbe; Timoti da Aristakus da Sakundus, dukansu masu bi ne daga Tasalonika; da Tikikus da Trofimus daga Asiya.
\v 5 Amma wadansu har suka rigaye mu, suka jira mu a Taruwasa.
\v 6 Da muka shiga Jirgi daga Filibi bayan kwanakin Gurasa mara yisti; bayan kwanaki biyar muka iske su a Taruwasa; kwananmu bakwai a wurin.
\s5
\v 7 A rana ta fari ga mako, da muka taru domin karya gurasa. Bulus ya yi wa masubi jawabi, don ya yi niyyar ya tafi da wayewar gari; jawabinsa ya kai har tsakar dare.
\v 8 A benen da suka taru akwai fitilu da yawa.
\s5
\v 9 Wani matashi mai suna Aftikos yana zaune a kan taga, barci mai nauyi ya dauke shi; da shike Bulus ya tsawaita jawabinsa, saurayin da shike barci mai nauyi ya dauke shi sai ya fado daga kan bene na uku aka dauke shi matacce.
\v 10 Sai Bulus ya sauka ya mike a bisansa ya rungume shi, sa'annan ya ce, "Kada kowa ya damu; domin yana darai bai mutu ba."
\s5
\v 11 Sa'annan ya hawo kan bene domin cin gurasa tare da su, ya yi magana da su har gari ya waye daga nan ya bar su.
\v 12 Suka kawo saurayin da rai, sun sami ta'aziya ba kadan ba.
\s5
\v 13 Amma mu, da muka riga Bulus zuwa gun Jirgin, muka shiga zuwa Asos, mun shirya mu dauki Bulus a jirgi amma shi ya kudurta ya yi tafiya a kasa.
\v 14 Da muka sadu a Asos, mun dauke shi a Jirgin ruwa zuwa Mitilitus.
\s5
\v 15 Bayan tashin mu daga can, washegari muka zo tsibirin Kiyos. Washegari kuma muka zo birnin Militus.
\v 16 Amma Bulus ya kudurta wucewa Afisa a Jirgi, don kada ya bata lokaci a Asiya, don yana sauri in ya yiwu ranar Fentekos ta same shi a Urushalima.
\s5
\v 17 Daga Militus ya aika a kira masa dattawan iklisiyar Afisa.
\v 18 Da suka zo wurinsa sai ya ce masu, "Ku da kanku kun san tun daga ranar da na sa kafata a Asiya, irin zaman da muka yi da kasancewar mu tare.
\v 19 Na bauta wa Ubangiji da tawaliu har da hawaye, da wahalun da na sha saboda makircin Yahudawa.
\v 20 Kun sani ban ji nauyin sanar da ku kowanne abu mai amfani ba, na bi ku gida gida ina koyar da ku abubuwa a sarari.
\v 21 Kunsan yadda na gargadi Yahudawa da Hellenawa game da tuba ga Allah da bangaskiya ga Ubangiji Yesu.
\s5
\v 22 Yanzu fa, gashi, zan tafi Urushalima, Ruhu Mai Tsarki ya nuna mani a fili dole in je, ban san abin da zai faru da ni a can ba.
\v 23 Sai dai Ruhu Mai Tsarki ya nuna mani a kowanne gari cewa, sarkoki da wahalu suna jira na.
\v 24 Amma ban dauka cewa raina yana da wani amfani gare ni ba, domin in cika tsere da hidimar da na karba daga wurin Ubangiji Yesu, ta shaidar bisharan alherin Allah.
\s5
\v 25 Yanzu fa, duba, na san dukanku, wadanda na yi wa wa'azin mulkin Allah, ba za ku kara gani na ba.
\v 26 Don haka na shaida maku a wannan rana, ba ni da alhakin jinin kowanne mutum.
\v 27 Don banji nauyin sanar maku da dukan nufin Allah a gare ku ba.
\s5
\v 28 Saboda haka ku kula da kanku, da masubi da Ruhu Mai Tsarki ya sanya ku shugabanni. Ku kula ku yi kiwon iklisiyar Allah, wadda ya saya da jininsa.
\v 29 Na sani cewa bayan tafiyata, kyarketai masu zafi za su shiga tsakaninku, kuma baza su rangwanta wa masubi ba.
\v 30 Na sani har daga cikinku wadansu mazaje za su zo su fadi gurbattatun zantattuka, domin su janye almajirai zuwa gare su.
\s5
\v 31 Saboda haka ku yi lura. Ku tuna da cewa shekara uku ban fasa yi wa kowannenku gargadi da hawaye dare da rana ba.
\v 32 Yanzu ina mika ku ga Allah, da maganar Alherinsa, wadda take da ikon gina ku ta kuma ba ku gado tare da dukan wadanda ke cikin kebabbu na Allah.
\s5
\v 33 Ban yi kyashin azurfa, ko zinariya, ko tufafin wani ba.
\v 34 Ku da kanku kun sani na yi aiki da hannuwana, na biya bukatu na da na wadanda ke tare da ni.
\v 35 Na zama maku abin koyi a kowace hanya game da yadda za ku taimaka wa nakasassu ta wurin aiki, da yadda za ku tuna da maganar Ubangiji Yesu, maganar da shi da kansa ya ce: "Bayarwa tafi karba albarka."
\s5
\v 36 Bayan da ya yi magana haka, ya durkusa ya yi addu'a tare da su duka.
\v 37 Dukansu kuwa suka yi kuka mai tsannani, suka rungume shi kuma suka sunbace shi.
\v 38 Suka yi bakin ciki musamman domin abin da ya ce masu, ba za su kara ganinsa ba. Sai dukansu suka yi masa rakiya zuwa wurin jirgin ruwa.
\s5
\c 21
\p
\v 1 Da muka rabu da su, muka shiga jirgin ruwa muka mike hanya zuwa birnin Kos, washegari sai birnin Rodusa, daga nan sai kuma zuwa birnin Batara.
\v 2 Da muka sami jirgi mai hayewa zuwa Fonisiya sai muka shiga.
\s5
\v 3 Da muka hango tsibirin Kubrus muka bar shi a hagun mu muka nufi Suriya, muka sauka a birnin Taya domin a nan ne jirgin ruwan zai sauke kayansa.
\v 4 Bayan mun sami almajirai sai muka zauna can kwana bakwai. Al'majiran suka ce ma Bulus, ta wurin Ruhu, kada ma ya je Urushalima.
\s5
\v 5 Bayan 'yan kwanaki muka cigaba da tafiyarmu. Dukansu da matansu da 'ya'yansu suka raka mu har bayan birnin. Sa'annan muka durkusa a bakin gacci muka yi addu'a muka yi sallama da juna.
\v 6 Sai muka shiga jirgin ruwa, su kuma suka koma gida.
\s5
\v 7 Da muka gama tafiyarmu a Taya muka iso Talamayas. A nan ne muka gaisa da 'yan'uwa, muka zamna kwana daya da su.
\v 8 Washegari muka tashi muka tafi Kaisariya. Muka shiga gidan Filibus mai shaida bishara, daya daga cikin bakwai din, muka zauna da shi.
\v 9 Wannan mutum yana da 'ya'ya hudu mata, budurwai masu yin annabci.
\s5
\v 10 Sa'anda muka zauna can 'yan kwanaki, wani annabi ya zo daga Yahudiya mai suna Agabus.
\v 11 Ya zo wurinmu ya dauki damarar Bulus ya daure tasa kafar da hannayensa ya ce, "Ruhu Mai Tsarki ya ce, 'Haka Yahudawa za su daure mai wannan damarar, zasu kuma bashe shi ga al'ummai.'"
\s5
\v 12 Da muka ji wannan sakon, sai dukanmu da mazaunan wurin muka roki Bulus kada ya tafi Urushalima.
\v 13 Sai Bulus ya amsa ya ce, "Me kuke yi, kuna kuka kuna karya mani zuciya? Bama a shirye don dauri kadai nake ba har ma da mutuwa a Urushalima, sabili da sunan Ubangiji Yesu."
\v 14 Tun da Bulus bashi da niyyar a rinjaye shi, muka daina kuka muka ce, "Bari nufin Ubangiji ya tabbata."
\s5
\v 15 Bayan wadannan kwanaki, muka dauki jakkunanmu muka haura Urushalima.
\v 16 Wadansu almjirai daga Kaisariya suka bi mu. Sun zo ne tare da wani ana ce da shi Manason, mutumin Kuburus mai bi na farko, wanda za mu zauna da shi.
\s5
\v 17 Da muka isa Urushalima, 'yan'uwa suka marabce mu da farin ciki.
\v 18 Washegari Bulus ya tafi tare da mu zuwa wurin Bitrus, dukan dattawa kuma suna nan.
\v 19 Bayan ya gaishe su, sai ya shaida masu daya bayan daya abubuwan da Allah ya yi cikin al'ummai ta wurin hidimarsa.
\s5
\v 20 Da suka ji haka, suka yabi Ubangiji suka ce masa, "Ka gani, dan'uwa, dubban Yahudawa sun bada gaskiya suna kuma da niyyar kiyaye shari'a.
\v 21 An kuma gaya masu a kanka cewa, kana koya wa Yahudawan da suke zaune cikin al'ummai su yi watsi da Musa. Kana koya masu kada su yi wa 'ya'yansu kaciya, kada kuma su bi tsofaffin al'adu.
\s5
\v 22 Me ya kamata mu yi? Hakika za su ji ka zo.
\v 23 Sabo da haka ka yi abin da muka fada maka yanzu. Muna da maza hudu da suka dauki wa'adi.
\v 24 Tafi da wadannan ka tsarkake kanka tare da su, ka dauki dukan dawainiyar su dana askin kai. Ta haka kowanne mutum zai sani abubuwan da ake fadi a kanka karya ne. Za su sani cewa kai mai kiyaye shari'a ne.
\s5
\v 25 Game da al'umman da suka bada gaskiya mun yi masu wasika, mun bada umarni su kaurace kansu daga sadakokin da aka mika wa gumaku, da jini, da abin da aka makare da kuma fasikanci.
\v 26 Sai Bulus ya dauki mazannan, washegari ya tsarkake kansa tare da su, suka shiga haikali, domin ya sanar da cikar ranakun tsarkakewarsu, wato ranar ba da sadaka domin kowanne dayansu.
\s5
\v 27 Da kwanakin nan bakwai suka yi gab da cika, wadansu Yahudawa daga Asiya suka ga Bulus a haikali, sai suka zuga taro, suka danke shi.
\v 28 Suna ta kururuwa, "Mutanen Isra'ila ku taimaka mana. Wannan shine mutumin da ke koya wa dukan mutane ko'ina abubuwa gaba da mutane, da shari'a da kuma wannan wurin. Banda haka ya kawo Helenawa cikin haikalin nan ya kazantar da wannan wuri tsatsarka."
\v 29 Domin dama sun ga Tarofimas mutumin Afisa tare da Bulus cikin birni, suka yi zaton ya kawo shi cikin haikali.
\s5
\v 30 Sai duk gari ya rude, mutane suka runtuma suka danke Bulus. Suka ja shi waje daga cikin haikalin, nan da nan aka rufe kofofin.
\v 31 Suna kokarin kashe shi kenan, sai labari ya kai wurin hafsan sojoji cewa Urushalima duk ta yamutse da tarzoma.
\s5
\v 32 Nan take ya dauki mayaka da jarumawa, suka sheka da gudu wurin taron. Da mutane suka ga hafsan sojoji da rundunansa sai suka daina dukan Bulus.
\v 33 Sai hafsan ya tafi ya danke Bulus ya sa aka daure shi da sarkoki biyu. Ya tambaya ko shi wanene da kuma laifinsa.
\s5
\v 34 Wadansu cikin taron suna ta kururuwa wadansu su ce wannan, wadansu su ce, wancan. Tunda hafsan bai fahimci abin da suke fadi ba, sabo da ihunsu, ya dokaci a shigar da Bulus farfajiyar sojoji.
\v 35 Da suka kai matakala, sojoji suka dauki Bulus sabo da tsananin husatar taron jama'a.
\v 36 Domin taron suka biyo baya suna ihu suna cewa, "A kashe shi."
\s5
\v 37 An kusa shigar da shi farfajiyan kenan sai Bulus ya ce wa babban hafsan, "Ko ka yarda inyi magana da kai?" Hafsan ya ce, "Ka iya Helenanci?
\v 38 Ashe ba kai ne Bamasaren nan da kwanakin baya ka haddasa tawaye, ka dauki 'yan ta'adda dubu hudu ka kai su jeji ba?"
\s5
\v 39 Bulus ya ce, "Ni Ba'ibrane ne daga birnin Tarsus a Kilikiya. Ni dan kasar babban birni ne. Ka amince mani in yi magana da mutanen."
\v 40 Da hafsan ya bashi izni, Bulus ya mike a kan matakala ya daga hannayensa sama ya yi nuni su yi shuru. Da wuri ya yi tsit, Bulus ya yi masu magana da Ibraniyanci. Ya ce,
\s5
\c 22
\p
\v 1 "Yanuwa da Ubanni, ku saurari kariya ta zuwa gare ku yanzu."
\v 2 Da taron sun ji Bulus na magana a harshen Ibraniyawa sai sun yi tsit. Ya ce,
\s5
\v 3 Ni Bayahude ne daga garin Tarwasa na Kilikiya, amma a karkashin Gamaliyal aka ilimantar da ni. An horar da ni sosai bisa ga bin hanyar dokokin kakkaninmu. Ina da himma ga bin Allah kamar yadda ku ma kuna da ita.
\v 4 Na tsananta wa wannan Hanyan har ga mutuwa; na daure maza da mata sa'annan na jefa su cikin gidan yari.
\v 5 Hakannan ma babban firist da dukan dattawa za su ba da shaida cewa na karbi izini daga wurinsu domin 'yan'uwa da ke a Dimashku, saboda in tafi can. Haki na shine in daure mabiyan Hanyan nan, in kawo su Urushalima domin a hukunta su.
\s5
\v 6 Sa'anda ina cikin tafiya, ina kuma kusa da Dimashku, da tsakar rana sai farat daya ga babban haske daga sama ya haskaka kewaye dani.
\v 7 Na fadi kasa sa'anan na ji murya na ce da ni, 'Shawulu, Shawulu, don me kake tsananta mani?'
\v 8 Na amsa, 'Wanene kai, Ubangiji?' Ya ce mani, 'Nine Yesu Banazarat wanda kake tsananta wa.'
\s5
\v 9 Wadanda ke tare da ni sun ga hasken, amma ba su gane muryar wanda ya yi magana da ni ba.
\v 10 Na ce, 'Me zan yi ya Ubangiji?" Ubangiji ya ce mani, 'Tashi ka tafi cikin Dimashku, a can za a fada maka abinda wajibi ne ka yi.
\v 11 Ban iya ganin wuri ba domin walkiyar hasken, sai na tafi cikin Dimashku ta wurin jagorancin wadanda ke tare da ni.
\s5
\v 12 A can na sami wani mai suna Ananiya, mai tsoron Allah bisa ga sharia, da kyakyawan suna kuma a gaban Yahudawa da ke zama a can.
\v 13 Ya zo gare ni ya ce, 'Dan'uwa Shawulu, karbi ganin gari.' A daidai wannan sa'a na gan shi.
\s5
\v 14 Sa'annan ya ce, 'Allah na kakkaninmu ya zabe ka ka san nufinsa, ka ga Mai Adalcin nan, ka kuma ji muryar da ke fitowa daga bakinsa.
\v 15 Gama za ka zama mashaidinsa ga dukan mutane game da abinda ka gani da wanda ka ji.
\v 16 A yanzu me ka ke jira? 'Tashi a yi maka baftisma a wanke zunubanka, kana kira bisa sunansa.'
\s5
\v 17 Bayan da na dawo Urushalima, sa'anda ina addu'a a cikin haikali, sai na karbi wahayi.
\v 18 Na gan shi ya ce mani, 'Gaggauta ka bar Urushalima yanzu, domin ba za su yarda da shaidarka game da ni ba.'
\s5
\v 19 Na ce, 'Ubangiji, su da kansu sun san yadda na sa su a kurkuku na kuma doddoke wadanda suka gaskanta da kai a kowacce masujada.
\v 20 A sa'anda a ke zubar da jinin mashaidinka Istifanus, ina nan tsaye ina goyon baya, ina kuma lura da rigunan wadanda suka kashe shi.'
\v 21 Amma ya ce mani, 'Tafi, domin zan aike ka can wurin Al'ummai.'
\s5
\v 22 Mutanen sun bar shi yayi magana har zuwa ga wannan lokacin. Amma sai suka ta da murya suna cewa, 'A kawar da wannan dan taliki daga duniya: don bai kamata ya rayu ba.'
\v 23 Sa'anda suke tadda muryarsu, suna jefar da tufafinsu da kuma baza kura a iska,
\v 24 babban hafsan ya umarta a kawo Bulus a farfajiyan. Ya umarta da cewa a bincike shi da bulala, domin ya san dalilin da suka ta da ihu gaba da shi haka.
\s5
\v 25 Bayan da suka daure shi da tsirkiya, Bulus ya ce wa Jarumin da ke kusa da shi, "Ko daidai ne bisa ga doka a yi wa Barome wanda ma sharia ba ta kashe shi ba bulala?"
\v 26 Da Jarumin ya ji haka, ya tafi wurin babban hafsan, yana cewa, "Me kake so ka yi? Gama wanan mutumin dan asalin Roma ne."
\s5
\v 27 Babban hafsa ya zo ya ce masa, "Gaya mani, kai dan asalin Roma ne?" Bulus ya ce, "Haka ne."
\v 28 Babban hafsan ya amsa masa, "Da kudi masu yawa na sayi yancin zama dan kasa." Amma Bulus ya ce, "An haife ni dan kasar Roma.
\v 29 "Sai mutanen da sun zo su tuhume shi sun bar shi nan da nan. Babban hafsa shi ma ya tsorata da ya gane Bulus dan asalin Roma ne, domin ya riga ya daure shi.
\s5
\v 30 Washegari, babban hafsan ya so ya san gaskiyar tuhuma da Yahudawa suke yi a kan Bulus. Sai ya kwance shi daga sarka, ya kuma umarci babban firist da dukan majalisa su sadu. Sai ya kawo Bulus ya sa shi a tsakiyarsu.
\s5
\c 23
\p
\v 1 Bulus ya kura wa yan majalisa ido yace, '"Yan'uwa, na yi rayuwa tare da Allah da lamiri mai kyau har wannan ranan."
\v 2 Babban firist Hannaniya ya ba wandanda suke tsaye tare da shi urmarni su buge bakinsa.
\v 3 Bulus ya ce, "Allah zai buge ka, kai munafiki. Kana zama domin ka shari'anta ni da shari'a, kuma ka umarce a buge ni, gaba da sharia?"
\s5
\v 4 Wanda suka tsaya a gefe suka ce, "Kada ka zage babban firis na Allah." Bulus yace, "Ban sani ba, 'yan'uwa, cewa shi babban firis ne.
\v 5 Domin a rubuce yake, Ba za ku zargi shugaban mutanenku ba."
\s5
\v 6 Da Bulus ya ga cewa, daya bangaren Sadukiyawa ne dayan kuma Farisawa, ya yi magana da karfi a majalisa, '"Yan'uwa, ni Bafarise ne, dan Farisawa. Don tabbacin tashin matattu ne kuna shari'anta ni."
\v 7 Daya fadi haka, mahawara ta fara a tsakanin Farisawa da Sadukiyawa, sai taron ya rabu kashi biyu.
\v 8 Don Sadukiyawa suka ce babu tashin matattu, babu mala'iku, babu kuma ruhohi, amma Farisawa suka ce dukan abubuwan nan sun kasance.
\s5
\v 9 Sai mahawara ta tashi, wadansu marubutan Farisawa suka tashi da mahawara cewa, "Ba mu same mutumin nan da laifi ba sam. Ko mala'iku da ruhohi ne suka yi masa magana?"
\v 10 Da jayayya ta tashi, babban hafsa ya ji tsoro kada su yayaga Bulus, sai ya umarce sojoji suje su kwato shi da karfi daga 'yan majalisa, su tafi da shi farfajiya.
\s5
\v 11 Da dare Ubangiji ya tsaya kusa da shi yace, "Kada ka ji tsoro, kamar yadda ka ba da shaida game da ni a Urushalima, dole zaka sake zama shaida a Roma."
\s5
\v 12 Da gari ya waye, wadansu Yahudawa sun yi yarjejeniya suka dauka wa kansu la'ana: suka ce ba za su ci ba ba za su sha ba sai sun kashe Bulus.
\v 13 Mutane fiye da arba'in suka kulla wannan makirci.
\s5
\v 14 Suka je wurin manyan firistoci da dattawa suka ce, "Mun sa wa kanmu la'ana, ba za mu ci ba, ba za mu sha ba sai mun kashe Bulus.
\v 15 Yanzu, bari majalisa ta ba wa babban hafsa izini a kawo shi a gaba, kamar zai yanke hukunci. Mu kam, a shirye muke mu kashe shi kafin ya iso nan.
\s5
\v 16 Amma dan yar'uwan Bulus ya ji suna labe, sai ya tafi ya shiga farfajiyar ya fada wa Bulus.
\v 17 Bulus ya kira daya daga cikin jarumai yace, "Dauki saurayin nan ka kai shi wurin babban hafsa, don yana da abin da zai fada masa."
\s5
\v 18 Jarumin ya dauke saurayin ya kai shi wurin babban hafsa yace, "Bulus dan sarka ne yace in kawo saurayin nan a gaban ka. Yana da abin da zai fada maka."
\v 19 Babban hafsa ya kai shi wani lungu, sai ya tambaye shi, "Menene kake so ka fada mani?"
\s5
\v 20 Saurayin yace, "Yahudawa sun yarda su roke ka ka kawo Bulus gobe a majalisa, kamar zasu kara bincike a kan al'amarin.
\v 21 Amma kada ka yarda da su, mutane fiye da arba'in suna jiransa. Sun sa wa kansu la'anna, ba za su ci ba ba za su sha ba sai dai sun kashe shi. Yanzu a shirye suke; suna jira ka ba su izini."
\s5
\v 22 Sai babban hafsa yace wa saurayin ya tafi, da ya gama masa magana, "Kar ka fada wa wani al'amuran."
\v 23 Sai ya kira jarumai biyu yace, "Ku shirya sojoji dari biyu, yan dawakai saba'in, masu daukar mashi dari biyu su tafi kaisariya karfe uku na dare."
\v 24 Ya umarta a shirya dabbobin da Bulus zai hawo da zasu kai shi lafiya wurin Filikus gwamna.
\s5
\v 25 Sai ya rubuta wasika a misalin haka:
\v 26 Gaisuwa zuwa Kuludiyas Lisiyas zuwa ga mai martaba gwamna Filikus.
\v 27 Yahudawa sun kama wannan mutumin suna shirin kashe shi, na abko masu da sojoji na kwace shi, bayan da na ji shi Barome ne.
\s5
\v 28 Inna son sani dalilin zarginsa, sai na kai shi majalisa.
\v 29 Na gane cewa ana zarginsa ne a kan tambayoyi game da shari'ansu, amma ba wani zargi da ya cancanci dauri ko mutuwa.
\v 30 Da aka sanar da ni shirin makircin, sai na tura shi wurinka ba da bata lokaci ba, na umarce masu zarginsa su kawo zarginsu wurinka. Huta lafiya."
\s5
\v 31 Sai sojoji suka yi biyayya da umarni da aka basu: suka dauki Bulus suka kawo shi dadare a wurin Antibatris.
\v 32 Da gari ya yawe, yan dawakai suka tafi tare da shi kuma sauran sojoji suka koma farfajiya.
\v 33 Bayan da yandawakan suka isa Kaisiririya sun mika wasika ga gwamna, suka kuma danka Bulus a hanunsa.
\s5
\v 34 Da gwamna ya karanta wasikar, sai ya tambaye su daga wani yanki ne Bulus ya fito; da ya ji daga yankin kilikiya ne,
\v 35 Yace zan saurare ka sosai lokacin da masu zargin ka sun zo. Sai ya umarta a tsare shi a fadar Hiridus.
\s5
\c 24
\p
\v 1 Bayan kwanaki biyar, sai Ananiyas babban firist, Wasu dattawa da wani masanin shari'a mai suna Tartilus, sun tafi can. Suka kai karar Bulus gaban gwamna.
\v 2 Lokacin da Bulus ya tsaya gaban gwamna, Tartilus ya fara zarginsa yace wa gwamnan, "Saboda kai mun sami zaman lafiya; sa'annan hangen gabanka ya kawo gyara a kasarmu;
\v 3 don haka duk abin da ka yi mun karba da godiya, ya mai girma Filikus.
\s5
\v 4 Domin kada in wahalsheka, ina roko a yi mani nasiha don in yi magana kadan.
\v 5 An iske mutumin nan yana barna irir iri, yana kuma zuga jama'ar Yahudawa a dukan duniya su yi tayarwa.
\v 6 Har ma ya yi kokarin kazantar da haikali; saboda haka muka kama shi. \f + \ft Wasu tsoffin kwafi suna ƙarawa, \fqa Mun so mu shari'anta masa bisa ga dokarmu \fqa* . \f*
\s5
\v 7 Amma Lisiyas jami'i ya zo ya kwace shi da karfi daga hannunmu.
\v 8 Idan ka binciki Bulus game da wadannan al'amura, kai ma, zai tabbatar maka abin da muke zarginsa a kai.
\v 9 Dukan Yahudawa suna zargin Bulus cewa wadannan abubuwa gaskiya ne.
\s5
\v 10 lokacin da gwamnan ya alamta wa Bulus ya yi magana sai yace, "Yanzu na fahimci cewar da dadewa kana mulkin kasarnan, don haka da farin ciki zan yi maka bayani.
\v 11 Zaka iya tabbatarwa cewa bai kai kwana sha biyu ba tun da nake zuwa Urushalima don yin sujada.
\v 12 Da suka same ni a haikali, ban yi jayayya ko kawo rudami a tsakanin jama'a ba.
\v 13 Don haka ba su da tabbas akan abinda suke zargina a kansa yau.
\s5
\v 14 Amma na sanar da kai, bisa ga abin da suke kira darika, haka ni ma nake bautawa Allah na kakanninmu. Na yi aminci wajen kiyaye dukan abin da ke a rubuce a Attaurat da litattafan annabawa.
\v 15 Ina sa bege ga Allah, kamar yadda za a yi tashin matattu, masu adalci da miyagu;
\v 16 a kan haka kuma, nake kokarin zama mara abin zargi a gaban Allah da mutane ina yin haka cikin dukan al'amura.
\s5
\v 17 Bayan wadansu shekaru na zo in kawo wasu sadakoki da baikon yardar rai.
\v 18 Cikin kudurin yin haka, sai wasu Yahudawa daga kasar Asiya suka iske ni a cikin ka'idodin tsarkakewa a haikali, ba da taro ko ta da hargitsi ba.
\v 19 Yakamata wadannan mutanen su zo gabarka a yau, har idan suna da wani zargi a kai na.
\s5
\v 20 In kuwa ba haka ba bari mutanennan su fada in sun taba iske ni da wani aibu a duk lokacin da na gurfana a gaban majalisar Yahudawa;
\v 21 sai dai ko a kan abu daya da na fada da babbar murya sa'adda na tsaya a gabansu, 'Wato batun tashin matattu wanda ake tuhumata ake neman yi mani hukunci yau.'"
\s5
\v 22 Filikus yana da cikakken sanin tafarkin Hanyar, shi yasa ya daga shari'ar. Yace da su, "Duk sa'anda Lisiyas mai ba da umarni ya zo daga Urushalima, zan yanke hukunci."
\v 23 Sa'annan ya umarci jarumin ya lura da Bulus, amma ya yi sassauci, kada ya hana abokansa su ziyarce shi ko su taimake shi.
\s5
\v 24 Bayan wadansu kwanaki, Filikus da mai dakinsa Druskila, ita Bayahudiya ce, ya kuma aika a kira Bulus ya saurare shi game da bangaskiya cikin Kristi Yesu.
\v 25 Amma sa'adda Bulus yake bayyana zancen adalci, kamunkai, da hukunci mai zuwa, Filikus ya firgita ya ce, "Yanzu ka tafi. Amma idan na sami zarafi an jima, zan sake neman ka."
\s5
\v 26 A wannan lokacin, yasa zuciya Bulus zai bashi kudi, yayi ta nemansa akai-akai domin yayi magana da shi.
\v 27 Bayan shekaru biyu, Borkiyas Festas ya zama gwamna bayan Filikus, domin neman farin jini a wurin Yahudawa, ya ci gaba da tsaron Bulus a gidan yari.
\s5
\c 25
\p
\v 1 Da Festas ya shiga lardin, kuma bayan kwana uku, ya tashi daga Kaisariya ya tafi Urushalima.
\v 2 Sai babban firist da manyan Yahudawa suka kawo wa Festas sara a kan Bulus.
\v 3 Suka roki tagomashi wurin Festas ya kira Bulus zuwa Urushalima domin su kashe shi a hanya.
\s5
\v 4 Amma Festas ya amsa masu cewa, Bulus dan sarka ne a Kaisariya, kuma ba da dadewa ba shi da kansa zai koma can.
\v 5 "Saboda haka duk wadanda za su iya, su biyo mu. Idan akwai wani laifi game da mutumin, sai ku zarge shi."
\s5
\v 6 Bayan kwana takwas ko goma, sai ya gangara zuwa Kaisariya. Washegari ya zauna bisa kursiyin shari'a ya bada umarni a kawo Bulus a gabansa.
\v 7 Da Bulus ya iso, Yahudawa daga Urushalima suka tsaya kusa, suka yi ta kawo kararraki, amma basu iya tabbatar da su ba.
\v 8 Bulus ya kare kansa ya ce, "Ban yi wa kowa laifi ba, ko Yahudawa, ko haikali, ko kuma Kaisar."
\s5
\v 9 Amma Festas yana neman farin jini wajen Yahudawa, sabo da haka ya tambayi Bulus ya ce, "Kana so ka je Urushalima in shari'anta ka a can game da wadannan abubuwa?"
\v 10 Bulus ya ce, "Ina tsaye a Ddakalin Shari'ar Kaisar inda dole a shari'anta ni. Ban yi wa Yahudawa laifi ba, kamar yadda ka sani sosai.
\s5
\v 11 Idan lallai na yi laifi kuma na yi abin da ya chanchanci mutuwa, ban ki ba in mutu. Amma idan zarginsu karya ne, kada kowa ya bashe ni gare su. Ina daukaka kara zuwa ga Kaisar."
\v 12 Bayan Festas ya tattauna da majalisa ya amsa ya ce, "Kana kira ga Kaisar; za ka tafi wurin Kaisar."
\s5
\v 13 Bayan wadansu kwanaki, sarki Agaribas da Barniki suka iso Kaisariya domin su ziyarci Festas.
\v 14 Da ya kasance kwanaki da yawa, Festas ya fada wa sarki labarin Bulus ya ce, "Akwai wani mutum dan sarka da Filikus ya bari a kurkuku.
\v 15 Sa'anda nake a Urushalima, babban firist da dattawan Yahudawa suka kawo kararsa gare ni, suka roka a kashe shi.
\v 16 Game da wannan na amsa na ce masu, ba al'adar Romawa ba ce a ba da mutum tagomashi; sai wanda ake kararsa an bashi zarafi ya kare kansa a gaban masu kararsa, ya kuma bada hujjojinsa game da kararakin.
\s5
\v 17 Saboda haka, da duk suka taru ban bata lokaci ba, washegari na zauna a kujerar shari'a, na ba da umarni a kawo mutumin.
\v 18 Da masu karar suka fadi kararsu, sai na fahimci karar ba wani muhimmin abu a cikinta.
\v 19 Sai dai na ga cewa jayayya ce tsakanin su ta addini a kan wani Yesu da ya mutu, wanda Bulus ya ce yana da rai.
\v 20 Na rasa yadda zan bincike wannan al'amarin, sai na tambaye shi ko zai je Urushalima a shari'anta shi kan wadannan abubuwa.
\s5
\v 21 Amma da Bulus ya nemi a lura da shi, Kaisar ya shari'anta shi, sai na ba da umarni a ajiye shi har sai na aika shi wurin Kaisar."
\v 22 Agaribas yace wa Festas. "Zan so ni ma in saurari mutumin nan." "Gobe za ka ji shi," in ji Fostus.
\s5
\v 23 Washegari Agaribas da Barniki suka zo tare da kasaitaccen taro suka shiga dakin taro tare da hafsoshi da shugabanin gari. Da Festas ya ba da umarni, aka fito da Bulus wurinsu.
\v 24 Festas ya ce, "Sarki Agaribas da dukanku da kuke tare da mu a nan, kun ga mutumin nan, dukan Yahudawa sun gana da ni a Urushalima da nan kuma. Suna mani ihu cewa, bai chanchanta a bar shi da rai ba.
\s5
\v 25 Na gane bai yi wani abin da ya chanchanci mutuwa ba; amma saboda ya daukaka kara zuwa Kaisar, na yanke shawara in aika shi.
\v 26 Amma ba ni da wani dalili na musamman da zan rubuta wasika ga Kaisar. Saboda wannan dalili na kawo shi gabanku, masamman kai ya sarki Agaribas. Domin in sami karin abin da zan rubuta game da shi.
\v 27 Gama a ganina wauta ce in aika dan sarka ba tare da na rubuta laifi a kansa ba."
\s5
\c 26
\p
\v 1 Sai Agaribas ya ce wa Bulus, "Za ka iya kare kan ka." Sai Bulus ya daga hannunsa ya fara kare kansa.
\v 2 "Ina farinciki, ya sarki Agaribas, game da saran da Yahudawa ke kawowa a kaina yau;
\v 3 musamman ma don kai masani ne game da al'adun Yahudawa da al'amuransu. Don haka, ina rokanka ka yi hakuri ka saurare ni.
\s5
\v 4 Hakika, dukan Yahudawa sun san yadda na yi rayuwa ta daga kurciyata a kasa ta, da kuma Urushalima.
\v 5 Sun san ni tun farko, kuma yakamata su yarda cewa na yi rayuwa kamar Bafarase, darikan nan mai tsatsauran ra'ayi ta addininmu.
\s5
\v 6 Yanzu ina tsaye a nan dominn a shari'anta ni, saboda alkawalin da Allah ya yi wa ubanninmu.
\v 7 Domin wannan shine alkawalin da kabilunmu goma sha biyu suka sa zuciya su karba, yayin da suke yin sujada da himma ga Allah dare da rana. Saboda wanan bege, Sarki Agaribas, Yahudawa ke tuhuma ta.
\v 8 Me ya sa wani zai yi tunani cewa abin mamaki ne Allah ya ta da mattatu?
\s5
\v 9 Da, na yi tunanin yin abubuwa gaba da sunan Yesu Banazarat.
\v 10 Na yi wadanan a Urshalima. Na kulle masu bi da yawa a kurkuku, sanadiyar iko da na samu daga wurin manyan firistoci, kuma da ake kashe su ma, ina ba da goyon baya.
\v 11 Na wahalshe su sau dayawa a cikin dukan majamiu ina kuma yin kokari in tilasta masu su yi sabo. Na yi gaba mai zafi da su kuma na tsananta masu har zuwa birane na wadansu kasashe.
\s5
\v 12 A sa'anda nake yin wannan, na tafi Dimashku da izinin manyan firistoci;
\v 13 a cikin tafiyata kuma, da tsakar rana, ya sarki, na ga haske daga sama da ya fi rana sheki, ya haskaka kewaye da ni da kuma wadanda ke tafiya tare da ni.
\v 14 Da dukanmu muka fadi kasa, na ji wata murya na magana da ni a harshen Ibraniyawa tana cewa, 'Shawulu, Shawulu, don me kake tsananta mani? Yana da wuya ka hauri abin da ke mai tsini.'
\s5
\v 15 Sai na ce, 'Wanene kai ya Ubangiji?' Ubangiji ya amsa, 'Ni ne Yesu wanda kake tsanantawa.
\v 16 Yanzu ka tashi tsaye domin saboda wannan dalili ne na bayyana gare ka in sanya ka, ka zama bawa da mashaidi na game da abubuwan da ka sani a kaina yanzu da wadanda zan bayyana maka daga bisani;
\v 17 Zan kubutar da kai daga wurin mutane da kuma al'ummai da zan aike ka wurinsu,
\v 18 domin ka bude idanunsu ka juyo su daga duhu zuwa haske da daga ikon Shaidan zuwa ga Allah, domin su karbi gafarar zunubai da gado da zan ba wadanda na kebe wa kaina ta wurin bangaskiya gare ni.'
\s5
\v 19 Saboda haka, sarki Agaribas, ban yi rashin biyayya da wahayin da na gani daga sama ba;
\v 20 amma, da farko ga wadanda ke a Dimashku, sa'annan a Urushalima da kasar Yahudiya gaba daya, da dukan Al'ummai, na yi wa'azi domin su tuba su kuma juyo ga Allah, su yi ayyukan da suka chanchanci tuba.
\v 21 Domin wannan dalili ne Yahudawa suka kama ni a cikin haikali kuma suke kokari su kashe ni.
\s5
\v 22 Allah ya taimake ni har wa yau, domin in iya tsayawa gaban mutane kanana da manya, in bada shaida game da iyakar abin da annabawa da Musa suka fada zai faru;
\v 23 wato lallai Almasihu zai sha wahala, ya kuma zama na farko da za'a rayar daga matattu ya kuma yi shelar haske zuwa ga mutanen Yahudawa da Al'ummai."
\s5
\v 24 Da Bulus ya gama kare kansa, Festas ya yi magana da babban murya, "Bulus, kana hauka; yawan iliminka yasa ka hauka."
\v 25 Amma Bulus ya ce, "Ba na hauka, ya mai girma Festas; amma da karfin zuciya nake fadi kalmomin gaskiya da na natsuwa.
\v 26 Saboda sarkin ya san wadannan abubuwa duka; shi ya sa nake magana gabagadi, don na hakikance cewa, ba abin da ke a boye gare shi; gama ba a yi wadannan abubuwa a boye ba.
\s5
\v 27 Ko ka gaskanta da annabawa, Sarki Agaribas? Na sani ka gaskanta."
\v 28 Agaribas ya ce wa Bulus, "A cikin karamin lokaci kana so ka rinjaye ni ka mai da ni Krista?"
\v 29 Bulus ya ce, "Ina roko ga Allah, domin ko a karamin lokaci ko a dogon lokaci, ba kai kadai ba, amma har da wadanda ke sauraro na yau su zama kamar ni, amma ban da wadannan sarkokin."
\s5
\v 30 Sai sarki ya tashi tsaye tare da gwamna da Barniki da dukan wadanda ke zaune tare da su;
\v 31 da suka bar dakin taron, suka ci gaba da magana da juna suna cewa, "Wannan mutum bai yi wani abin da ya chanchanci mutuwa ko kuma dauri ba."
\v 32 Agaribas ya ce wa Fastos, "Da mutumin nan bai daukaka kara zuwa ga Kaisar ba da an sake shi."
\s5
\c 27
\p
\v 1 Bayan da aka amince zamu tafi Italiya, sun mika Bulus tare da wadansu daurarru a hanun wani jarumi mai suna Yuliyas, daga batalian Agustas.
\v 2 Muka shiga Jirgin ruwa daga Adramatiya, wanda ke shirin tashi zuwa kusa da gefen tekun Asiya. Sai muka je teku. Aristakus mutumin Tasalonika a Makidoniya ya tafi tare damu.
\s5
\v 3 Washegari muka sauka birnin Sidon, inda Yuliyas ya nuna wa Bulus karamci ya kuma yarda abokansa su bi shi don ya kula da su.
\v 4 Daga wurin, muka bi teku muka tafi ta Tsibirin Kubrus, domin matsananciyar iska da ke gaba damu.
\v 5 Sa'adda muka ketare ruwa zuwa sassan Kilikiya da Bamfiliya, muka zo Mira ta birnin Lisiya.
\v 6 Anan, jarumin ya sami jirgin ruwa daga Iskandariya wanda za shi Italiya. Ya samu cikinsa.
\s5
\v 7 Kwana da kwanaki muna tafiya a hankali a karshe da kyar muka sauka kusa da Sinidus, iska ta hana mu tafiya, sai muka ratsa ta Karita, kusa da Salmina.
\v 8 Da wahala muka bi ta makurda har muka zo wani wuri da ake kira Mafaka Mai Kyau wanda ke kusa da birnin Lasiya.
\s5
\v 9 Yanzu mun dauki dogon lokaci, gashi lokacin azumin Yahudawa ya wuce, tafiyar kuma ta zama da hatsari. Bulus ya gargade su,
\v 10 ya ce, "Jama'a, na gane tafiyarmu zata zamar mana da barna da asara mai yawa, ba ga kaya da jirgin kadai ba amma har da rayukan mu."
\v 11 Amma jarumin ya fi mai da hankali ga maganar shugabansa da mai jirgin ruwan, fiye da abubuwan da Bulus ya fadi.
\s5
\v 12 Da shike tashar ba za ta yi dadin zama da hunturu ba, mafi yawa sun ba da shawara a bar wurin, in maiyiwuwa ne muga mun kai birnin Finikiya, don mu yi hunturu a can. Finikiya tashar jirgin ruwa ce a Karita, tana fuskantar arewa maso gabas da kudu maso gabas.
\v 13 Sa'adda iska daga kudu ta huro a hankali, sun tsammaci bukatarsu ta biya. Sai suka janye linzamin jirgin ruwan sukabi ta Karita kusa da gaba.
\s5
\v 14 Amma bayan wani dan lokaci sai iska mai karfi da ake kira Yurokilidon, ta fara bugun mu daga tsibirin.
\v 15 Sa'adda Jirgin ruwan ya kasa fuskantar iskar, sai muka bi inda iskar ta nufa.
\v 16 Sai muka bi ta inda muka sami kariya kusa da wani dan tsibiri wanda ake kira Kauda; kuma da wahala muka daure karamin jirgin a jikin babban.
\s5
\v 17 Bayanda suka daga shi, sun yi amfani da igiyoyi don su daure jirgin don gudun fadawa kan yashin Sirtis, suka bar jirgin yana ta korarsu.
\v 18 Mun yi ta fama da hadari ba kadan ba, da gari ya waye ma'aikatan jirgin suka fara zubar da kaya daga jirgin.
\s5
\v 19 A rana ta uku, ma'aikatan jirgi suka jefar da kaya daga cikin jirgin da hannuwansu.
\v 20 Kwanaki dayawa ba mu ga hasken rana da taurari a bisan mu ba. Babban hadari kadai ke dukanmu, duk mun fidda zuciya zamu tsira.
\s5
\v 21 Sa'adda sun dade basu ci abinci ba, sai Bulus ya tashi a gaban ma'aikatan jirgi yace, "Jama'a, da kun saurare ni, da bamu tashi daga Karita ba, balle mu fuskanci wannan barna da asarar.
\v 22 Yanzu fa ina karfafa ku kuyi karfin hali, domin ba wanda zai rasa ransa a cikinku, sai dai jirgin kadai za a rasa.
\s5
\v 23 Domin daren da ya gabata mala'ikan Allah wanda ni nasa ne, wanda kuma nake bautawa -mala'ikansa ya tsaya kusa dani
\v 24 ya ce, "Kada ka ji tsoro, Bulus, dole ka tsaya gaban Kaisar, duba kuma, Allah cikin jinkansa ya baka dukan wadannan da ke tafiya tare da kai.
\v 25 Domin haka, jama'a, kuyi karfin hali, domin na gaskanta da Allah, kamar yadda aka fada mani haka zai faru.
\v 26 Amma lallai dole ne a jefa mu kan wani tsibiri".
\s5
\v 27 Sa'adda dare na goma sha hudu ya yi, ana ta tura mu nan da can a cikin tekun Adriyat, wajen tsakar dare, ma'aikatan jirgin sun tsammaci sun kusanci wata kasa.
\v 28 Da suka gwada sai suka iske kamu ashirin; bayan dan lokaci kadan, sun sake aunawa sai suka iske kamu sha biyar ne.
\v 29 Tsoro ya kama su ko watakila a jefar da mu kan duwatsu, sai suka jefa linzami hudu daga karshen jirgin suka yi addu'a don gari ya waye da sauri.
\s5
\v 30 Ma'aikatan jirgin ruwan suna neman hanyar da za su rabu da jirgin kuma sun jefa karamin jirgin a cikin teku. Suka yi kamar zasu jefa wasu linzamai daga gaban jirgin.
\v 31 Amma Bulus ya ce ma jarumi da sojojin, "Idan mutanen nan ba zasu tsaya cikin jirgin ba, ba zaku tsira ba".
\v 32 Sai sojojin suka yanke igiyoyin jirgin suka kuma barshi ya fadi.
\s5
\v 33 Da gari ya fara wayewa, Bulus ya roke su duka su dan ci abinci, ya ce, "Yau kwana goma sha hudu kenan ba ku ci kome ba.
\v 34 Saboda haka na roke ku ku ci abinci, domin wannan saboda lafiyarku ne; kuma ko gashin kanku daya baza ku rasa ba".
\v 35 Da ya fadi haka sai ya dauki gurasa ya yi godiya ga Allah a idanun kowa. Sai ya gutsutsura gurasa ya fara ci.
\s5
\v 36 Sai dukansu suka karfafu suka kuma ci abinci.
\v 37 Mu mutane 276 (dari biyu da saba'in da shida) ne cikin jirgin.
\v 38 Da suka ci suka koshi, suka zubar da alkamar cikin teku domin su rage nauyin jirgin.
\s5
\v 39 Da gari ya waye, basu fahimci kasar ba, amma suka hangi wani lungu a gacci, sai suka yi shawara tsakaninsu ko su tuka jirgin zuwa cikin lungun.
\v 40 Sai suka yanke linzaman suka bar su cikin tekun. Cikin lokaci guda suka kwance igiyoyin da ke juya jirgin, suka saki filafilan goshin jirgi suka nufi gabar tekun.
\v 41 Da suka iso inda ruwa biyu suka hadu, sai jirgin ya tsaya kasa. Gaban jirgin ya kafe a nan, ba damar matsawa, sai kuma kurar jirgin ta fara kakkaryewa saboda haukan rakuman ruwa.
\s5
\v 42 Shirin sojojin ne su kashe 'yan kurkukun domin kada su yi iyo su tsere.
\v 43 Amma shi hafsan ya so ya ceci Bulus, sai ya tsai da shirin su, ya ba da umarni, duk masu iya iyo su yi tsalle su fada ruwa su kai gacci.
\v 44 Sa'annan sauran mazajen su biyo baya, wadansu a kan karyayyun katakai, wadansu akan abubuwan da ke a jirgin. Ta haka ne dukanmu muka kai gacci lafiya.
\s5
\c 28
\p
\v 1 Sa'adda muka sauka lafiya, sai muka ji cewa sunan tsibirin Malita.
\v 2 Mutanen garin sun nuna mana alheri matuka don sun hura wuta don mu ji dimi, saboda ruwan sama da sanyin da ake yi.
\s5
\v 3 Amma sa'adda Bulus ya tara kiraruwa don hura wuta, sai maciji saboda zafin wuta, ya fito ya nade hannuwansa.
\v 4 Da mazaunan garin suka ga maciji ya nade hannuwansa, sai suka cema junansu, "Ba shakka wannan mutumin mai kisan kai ne, koda shike ya tsira daga Teku, sharia baza ta barshi da rai ba".
\s5
\v 5 Amma ya karkade macijin cikin wuta ba tare da ya cutar da shi ba.
\v 6 Sun saurara su gani ko zai kumbura ko ya fadi matacce. Amma da suka jira dan lokaci basu ga wata matsala ta same shi ba sai suka canza tunaninsu sukace shi wani allah ne.
\s5
\v 7 A kusa da wannan wurin tsibirin akwai wasu gonakin wani babban mutumin tsibirin, mai suna Babiliyas. Ya karbe mu ya biya bukatun mu har kwana uku.
\v 8 Ana nan ashe mahaifin Babiliyas yana fama da zazzabi da atuni. Bulus ya shiga, yayi masa addu'a, ya dibiya masa hannu, ya sami warkarwa.
\v 9 Sa'adda wannan ya faru, sauran marasa lafiya da ke tsibirin sun zo sun sami warkarwa.
\v 10 Mutanen sun mutunta mu kwarai. Yayin da muke shirin tafiya, sun bamu duk abinda muke bukata.
\s5
\v 11 Bayan watanni uku, mun shiga jirgin Iskandariya wanda tun da hunturu yake a tsibirin mai zane kamannin Tagwaye Maza.
\v 12 Bayan saukar mu a birnin Sirakus, mun yi kwana uku a wurin.
\s5
\v 13 Daga nan sai muka tafi, har muka zo birnin Rigiyum. Bayan kwana daya iska mai karfi daga kudu ta taso, a cikin kwana biyu muka iso Butiyoli.
\v 14 A can muka iske wasu 'yan'uwa suka roke mu mu zauna tare da su har kwana bakwai. Ta wannan hanyar ce muka zo Roma.
\v 15 Daga can da 'yan'uwa suka ji labarin mu, suka fito don su tarbe mu tun daga Kasuwar Abiyas da kuma Rumfuna Uku. Da Bulus ya gan su, ya yi wa Allah godiya ya kuma sami karfafawa.
\s5
\v 16 Sa'adda muka shiga Roma, aka yardar wa Bulus ya zauna shi kadai tare da sojan da ke tsaronsa.
\v 17 Ana nan bayan kwana uku, Bulus ya kira shugabannin Yahudawa. Bayan da suka taru, sai ya ce masu, "Yan'uwa, ko da shike ban yi wa kowa laifi ko keta al'adun Ubanninmu ba, duk da haka an bashe ni daurarre tun daga Urushalima zuwa ga hannunwan mutanen Roma.
\v 18 Bayan tuhumata, sun yi kudirin saki na, domin ban yi laifin da ya cancanci mutuwa ba.
\s5
\v 19 Amma da Yahudawa suka tsaya a kan ra'ayin su, ya zama dole in daukaka kara zuwa ga Kaisar, ba domin ina da wani dalilin da zan yi karar al'ummata ba ne.
\v 20 Saboda wannan ne na bukaci ganinku in yi magana da ku. Saboda begen da Isra'ila suke da shi ya sa nake daure da wannan sarkar".
\s5
\v 21 Sai suka ce masa, "Bamu karbi wasiku daga Yahudiya game da kai ba, babu kuma wani daga cikin 'yan'uwa wanda ya kawo mana wani rahoto ko wata magana game da kai.
\v 22 Amma muna so mu ji daga gare ka abin da kayi tunani ka kuma gani game da wannan darikar, gama mun sani ana kushenta a ko'ina."
\s5
\v 23 Sa'adda suka sa masa rana, mutane da dama suka same shi a masaukinsa. Ya gabatarda zantattukan a gare su, yana tabbatar da bayyanuwar mulkin Allah. Har ya nemi ya rinjaye su a kan zancen Yesu, tun daga attaurat ta Musa zuwa litattafan annabawa, ya yi wannan tun daga safiya har yamma.
\v 24 Wasu sun kawar da shakkar abin da aka fada, amma wadansu basu gaskanta ba.
\s5
\v 25 Da shike ba su yarda da junansu ba, sai suka tafi bayan da Bulus ya fadi kalma daya, "Ruhu Mai Tsarki ya yi magana ta bakin annabi Ishaya zuwa ga kakanninku.
\v 26 Ya ce, 'Jeka wurin al'umman nan ka ce, cikin ji zaku ji amma ba zaku fahimta ba; zaku gani amma ba zaku gane ba.
\s5
\v 27 Amma zuciyar mutanen nan ta yi kanta, kunnuwansu sun ji da kyar, sun rufe idanunsu; don kada su gani su gane, su kuma ji da kunuwansu, kuma su fahimta da zuciyarsu, domin su juyo ni kuma in warkar da su."
\s5
\v 28 Saboda haka, sai ku sani cewa wannan ceto na Allah an aikar da shi zuwa ga Al'ummai, za su kuma saurara."
\v 29 \f + \ft Ayyukan Manzanni 28: 29 - Wasu tsoffin kwafi suna da aya ta 29: \fqa Sa'adda ya fadi wannan zantattuka, Yahudawa suka tashi, suna gardama da junansu \fqa* . \f*
\s5
\v 30 Bulus ya zauna shekaru biyu a cikin gidan hayarsa, yana marabtar duk wadanda suka zo wurinsa.
\v 31 Yana wa'azin mulkin Allah, yana koyarwa da al'amuran Ubangiji Yesu Kristi gaba gadi. Ba wanda ya hana shi.