ha_ulb/39-MAL.usfm

123 lines
9.2 KiB
Plaintext

\id MAL
\ide UTF-8
\h Littafin Malakai
\toc1 Littafin Malakai
\toc2 Littafin Malakai
\toc3 mal
\mt Littafin Malakai
\s5
\c 1
\cl Sura 1
\p
\v 1 Furcin maganar Yahweh ga Isra'ila ta hannun Malakai.
\v 2 "Na ƙaunace ku," inji Yahweh. Amma ku kun ce, "Ta yaya ka ƙaunace mu?"
\v 3 "Ashe Isuwa ba ɗan'uwan Yakubu ba ne?" Yahweh ya furta. "Amma na ƙaunaci Yakubu, na ƙi Isuwa. Na maida tuddansa banza abin ƙi, kuma na maida gãdonsa muhallin diloli na daji."
\s5
\v 4 Idan Idomawa suka ce, "An buge mu har ƙasa, amma za mu sake tashi," Yahweh mai runduna zai ce, "Zasu sake tashi kuma su gina, zan kuma sake rushewa. Wasu zasu kirasu, 'Ƙasar masu mugunta' kuma 'Mutanen da Yahweh ya la'anta har abada.'
\v 5 Idanuwanku zasu ga wannan, kuma zaku ce, Yahweh mai girma ne har ma a gaban iyakokin Isra'ila.'"
\s5
\v 6 Ɗa yana girmama ubansa, kuma bawa yana girmama ubangijinsa. Idan ni uba ne, ina ku ka girmama ni? Idan ni ubangijinku ne, me yasa ba ku ba ni daraja, inji Yahweh mai runduna ga ku firistoci, da ku ka rena sunana. "Amma kun ce ta yaya mu ka rena sunanka?'
\v 7 Ta wurin miƙa ƙazantacciyar gurasa da kuke kawo wa bagadina. Amma kun ce, "Ta yaya mu ka ƙazantad da kai?"' Ta cewa teburin Yahweh marar daraja ne.
\s5
\v 8 A lokacin da kuka miƙa hadayun makafin dabbobi ashe wannan ba mugunta ba ce? Duk lokacin da ku ka miƙa hadayun guragun dabbobi da marasa lafiya, wannan ba mugun abu ba ne? Kwa ba da wannan ga gwamnanku! Zai karɓa ko zaku sami tagomashi a wurinsa?" inji Yahweh mai runduna.
\v 9 Yanzu kuna ta neman fuskar Allah, domin ya yi mana alheri. Amma Yahweh mai runduna yace da irin wannan baikon a hannunku, zaku sami tagomashinsa?
\s5
\v 10 "Kash, ina ma da akwai wani daga cikinku wanda zai rufe ƙofofin haikali, don kada ku kunna wuta akan bagadina a banza! Domin ba na jin daɗinku," inji Yahweh mai runduna, "kuma ba zan karɓi kowanne baiko daga hannunku ba.
\v 11 Daga fitowar rana har zuwa faɗuwarta sunana zai zama da girma a cikin al'ummai a dukkan wuraren da ake ƙona turare da kuma baye-baye masu tsabta da za a miƙa da sunana. Domin sunana zai zama da girma a cikin al'ummai," inji Yahweh mai runduna.
\v 12 Amma kuna ɓata shi sa'ad da kuka ce teburi na Ubangiji ya ƙazance, kuma 'ya'yan itacensa da abincinsa abin reni ne.
\s5
\v 13 Kun kuma ce, 'kai wannan abin gajiyarwa ne,' kuma kun wulaƙanta shi," inji Yahweh mai runduna. "kun kawo dabbar da naman daji ya kama ko gurguwa ko marar lafiya; kuma wannan ku ka kawo a matsayin hadayarku. Ko zan karɓi wannan daga hannunku? inji Yahweh.
\v 14 "Bari mayaudari ya zama la'ananne wanda ke da dabba namiji a garkensa kuma ya yi wa'adi zai bayar da ita gare ni, amma duk da haka, Ni da na ke Ubangiji, ya kawo mani hadayar nakasashiya! Gama ni babban sarki ne," inji Yahweh mai runduna, "kuma za a girmama sunana a cikin al'ummai."
\s5
\c 2
\cl Sura 2
\p
\v 1 Yanzu ku firistoci, wannan umurni domin ku ne.
\v 2 "Idan ba zaku saurara ba, kuma in ba zaku yi niyya a zuciyarku ku bani girma ba," inji Yahweh mai runduna, "lallai zan aiko da la'ana zuwa gare ku, kuma zan la'anta albarkunku. Hakika, na la'antar da su, domin ba ku sa dokokina a zuciyarku ba.
\s5
\v 3 Duba, ina shirin tsauta wa zuriyarku, kuma zan watsa kashin dabbobi a fuskokinku, wato kashin dabbobin bukukuwanku, kuma zan kore ku daga gare ni.
\v 4 Za ku sani cewa ni na aiko da wannan umarni gare ku, kuma alƙawarina zai ci gaba da kasancewa tare da Lebi," inji Yahweh mai runduna.
\s5
\v 5 Alƙawarina da shi na rai da salama ne, kuma ni na ba dasu gare shi; Na sa ya girmama ni, kuma ya ji tsoro na, kuma ya darajanta sunana.
\v 6 Umurnin gaskiya ya kasance a bakinsa, kuma ba a sami ƙarya a leɓunansa ba. Ya yi tafiya da ni a cikin salama da daidaituwa kuma ya juyo da yawa ga tuba daga zunubi.
\v 7 Domin ya kamata leɓunan firist su kasance da sani kuma mutane su nemi koyarwa daga bakinsa, domin shi ɗan saƙon Yahweh mai runduna ne.
\s5
\v 8 Amma kun kauce daga hanyar gaskiya. Kun sa da yawa sun yi tuntuɓe game da koyarwar shari'a. Kun karya alƙawarin Lebiyawa," inji Yahweh mai runduna.
\v 9 Haka ni ma na maishe ku marasa daraja kuma abin reni ga dukkan mutane, domin baku bi hanyoyina ba, maimakon haka kuka nuna son kai game da abin da aka umurta."
\s5
\v 10 Ashe dukkanmu ba uba ɗaya muke ba? Ba Allah ɗaya ne ya hallicce mu ba? Me ya sa muka zama marasa aminci kowanne ga ɗan'uwansa, mu na ƙazantar da alƙawarin iyayenmu?
\v 11 Yahuda ya kasance marar aminci. An aikata mummunan abu cikin Isra'ila da Yerusalem. Gama Yahuda ya ƙazantar da wuri mai tsarki na Yahweh da yake ƙauna, kuma ya aure 'yar baƙon allah.
\v 12 Bari Yahweh ya datse irin wannan mutum daga alfarwar Yakubu, ko wane ne shi, ko da ma mai kawo hadaya ga Yahweh mai runduna ne.
\s5
\v 13 Kuna kuma yin wannan: wato kuna rufe bagadin Yahweh da hawaye da kuka da ajiyar zuciya, domin ba ya kula da hadayunku ko karɓar su daga hannunku da tagomashi.
\s5
\v 14 Amma ku ka ce "Don me ya ƙi?" Domin Yahweh shaida ne tsakaninka da matarka ta ƙuruciya, wadda ka yi mata rashin aminci, ko da yake abokiyar tarayyarka ce da matarka ta alƙawari.
\v 15 Ba shi ne ya yi su ɗaya daga ruhunsa ba? To me yasa ya maishe ku ɗaya? Saboda ya na neman 'ya'ya daga Allah. Don haka ku lura da kanku a cikin ruhunku, kada ka zama marar aminci ga matarka ta ƙuruciya.
\v 16 "Gama na ƙi kisan aure," inji Yahweh, Allah na Isra'ila, "da kuma wanda ya rufe tufafinsa da husuma," inji Yahweh mai runduna. "To sai ku yi lura da kanku cikin ruhu don kada ku zama marasa aminci."
\s5
\v 17 Kun gajiyar da Yahweh da maganganunku. Amma kun ce "Ta yaya muka gajiyar da shi?" Ta cewa "Duk wanda ya yi mugunta managarci ne a idanun Yahweh, kuma yana jin daɗin su, ko "Ina Allah na adalci?"
\s5
\c 3
\cl Sura 3
\p
\v 1 "Duba, na kusa aiko da manzona, kuma zai shirya mani hanya a gabana. Sa'an nan Ubangiji da kuke nema, zai zo haikalinsa ba zato. Manzon da aka alƙawarta, da kuke farinciki da shi, duba, zai zo," inji Yahweh mai runduna.
\v 2 Amma wa zai jure ranar zuwansa? Wa zai iya tsayawa sa'ad da ya bayyana? Domin zai zama kamar wutar maƙera, kamar sabulun wanki.
\v 3 Zai zama kamar mataci mai tace azurfa, zai tsarkake 'ya'yan Lebiyawa. Zai tace su kamar zinariya da azurfa, sa'an nan ne zasu kawo baikon adalci ga Yahweh.
\s5
\v 4 Sa'an nan ne baikon Yahuda da na Yerusalem zai gamshi Yahweh, kamar a kwanakin dă, a shekarun baya.
\v 5 "Sa'an nan zan zo gare ku domin hukunci. Nan da nan zan zama shaida gãba da masu sihiri, da mazinata, da masu shaidar zur, da masu zaluntar ma'aikata wajen albashinsu, da masu cutar gwauraye, da marayu, da masu korar baƙi, da marasa girmama ni," inji Yahweh mai runduna.
\s5
\v 6 Domin ni Yahweh ban canza ba; saboda haka ne ku 'zuriyar Yakubu ba ku ƙare ba.
\v 7 Tun daga zamanin ubanninku kun kauce daga bin farillaina ba ku kuma kiyaye su ba. Ku dawo gare ni, ni ma zan dawo gare ku," inji Yahweh mai runduna, "Amma kun ce, 'Ƙaƙa zamu dawo?'
\s5
\v 8 Mutum zai iya yi wa Allah fashi? Duk da haka kuna yi mani fashi. Amma kun ce, 'Ta yaya muka yi maka fashi?' A zakkoki da baye-baye.
\v 9 La'anannu ne ku da la'ana, domin kuna yi mani fashi, dukkan al'umma.
\s5
\v 10 Ku kawo dukkan zakka a cikin ma'aji, domin a sami abinci a cikin gidana, ku gwada ni a wannan," inji Yahweh mai runduna, "idan ba zan buɗe maku tagogin sama, in zubo da albarku a kan ku, har ba wurin tara su.
\v 11 Zan kwaɓi masu ɓarnata maku amfani domin su dena lalatar maku da amfanin ƙasarku. Gonakin inabinku ba zasu kakkaɓe 'ya'yansu ba, inji Yahweh mai runduna.
\v 12 "Dukkan al'ummai zasu ce da ku masu albarka. Zaku zama ƙasa mai ban sha'awa," inji Yahweh mai runduna.
\s5
\v 13 "Maganganunku a kaina suna da ƙarfi," inji Yahweh. "Amma kuka ce, 'Me muka ce a tsakaninmu gãba da kai?'
\v 14 Kun ce, "Ba amfani a bauta wa Allah. Wacce riba ce muka samu da yin biyayya da dokokinsa ko kuma da tafiya rai ɓace a gaban Yahweh mai runduna?
\v 15 Yanzu muna kiran masu girman kai masu albarka. Masu aikata mugunta bama azurta kaɗai suke ba, amma har ma suna gwada Allah su kuɓuta."'
\s5
\v 16 Sai waɗanda ke jin tsoron Yahweh suka yi magana da junansu. Yahweh kuma ya ji su ya saurare su, sai aka rubuta littafin tunawa a gabansa game da waɗanda ke jin tsoron Yahweh masu girmama sunansa.
\s5
\v 17 "Zasu zama nawa," inji Yahweh mai runduna, dukiyata mai tamani, a ranar da zan yi wannan. Zan yi masu jinƙai, kamar yadda uba ya kan yi wa ɗansa jinƙai wanda yake bauta masa.
\v 18 Sa'an nan ne kuma zaku bambance tsakanin adalai da miyagu da tsakanin masu bauta wa Allah da marasa bauta masa.
\s5
\c 4
\cl Sura 4
\p
\v 1 Duba rana na zuwa, mai ƙuna kamar tanderu, inda dukkan masu girman kai da masu aikata mugunta zasu zama tattaka. Ranar dake zuwa zata ƙone su, "inji Yahweh mai runduna, "Baza ta bar masu tushe ko reshe ba"
\v 2 Amma a gare ku ku dake tsoron sunana, ranar adalci zata fito da warkarwa a fukafukanta. Zaku fita, ku yi ta tsalle kamar 'yan maruka a dangwali.
\v 3 A wannan rana zaku tattake mugaye, zasu zama tattaka a ƙarƙashin sawayenku a ranar da zan aikata wannan", inji Yahweh mai runduna.
\s5
\v 4 "Ku tuna da koyarwar bawana Musa wadda na ba shi a Horeb domin dukkan Isra'ila, farillai ne da dokoki.
\v 5 Duba, zan aiko ma ku da annabi Iliya kafin babbar ranar nan mai tsoratar wa ta Yahweh.
\v 6 Zai juyar da zuciyar ubanni zuwa wajen 'ya'ya, da zuciyar 'ya'ya zuwa ga ubanninsu, domin kada in kawo hari in hallakar da ƙasar ɗungum."