ha_ulb/38-ZEC.usfm

449 lines
33 KiB
Plaintext
Raw Permalink Blame History

This file contains invisible Unicode characters

This file contains invisible Unicode characters that are indistinguishable to humans but may be processed differently by a computer. If you think that this is intentional, you can safely ignore this warning. Use the Escape button to reveal them.

\id ZEC
\ide UTF-8
\h Littafin Zakariya
\toc1 Littafin Zakariya
\toc2 Littafin Zakariya
\toc3 zec
\mt Littafin Zakariya
\s5
\c 1
\cl Sura 1
\p
\v 1 A cikin wata na takwas na shekara ta biyu na mulkin Dariyos maganar Yahweh ta zo ga Zakariya ɗan Berekaya ɗan Iddo, annabi, yana cewa,
\v 2 "Yahweh ya ji haushin ubanninku ƙwarai!
\v 3 Ka faɗi masu, 'Yahweh mai runduna ya faɗi haka: ku juyo gare ni! - wannan furcin Yahweh mai runduna ne - ni ma zan dawo gare ku, Yahweh mai runduna ya faɗa.
\s5
\v 4 Kada ku zama kamar ubanninku waɗanda Annabawa suka yi wa shela a lokatan baya, suna cewa, "Yahweh mai runduna ya faɗi haka: Ku juyo daga miyagun hanyoyinku da ayyukanku na mugunta!" Amma basu ji ba ko kuma su saurare ni - wannan ne furcin Yahweh.'
\v 5 Ubanninku, ina suke? Ina Annabawan, suna nan ne har abada?
\v 6 Amma maganganuna da dokokina da na umarci bayina Annabawa, ba sun zarce ubanninku ba? Sai suka tuba suka ce, 'Kamar yadda Yahweh mai runduna ya shirya ya yi mana abin da ya yi wa hanyoyinmu da ayyukanmu dai-dai, hakanan ya yi da mu.'"
\s5
\v 7 A cikin rana ta ashirin da huɗu na watan sha ɗaya, wanda shi ne watan Shibat, cikin shekara ta biyu na mulkin Dariyos, maganar Yahweh tazo wurin Annabi Zakariya ɗan Berekaya ɗan Iddo, cewa,
\v 8 "Da dare na gani, na duba kuma! ga mutum na sukuwa bisa jan doki, yana tsakiyar itatuwan cizaƙi dake cikin kwari; bayan shi kuma akwai dawakai da ja da jaja-jaja-ruwan ƙasa-ƙasa da kuma farare."
\v 9 Na ce, "Ubangiji mene ne waɗannan?" Sai mala'ikan da ke magana da ni yace mani, "zan nuna maka ko mene ne waɗannan."
\s5
\v 10 Sai mutumin dake tsaye tsakiyar itatuwan cizaƙi ya amsa yace, "Waɗannan su ne Yahweh ya aika su yi yawo cikin duniya duka."
\v 11 Suna ba da amsa ga mala'ikan Yahweh wanda ke tsaye a tsakiyar itatuwan cizaƙi; suna ce masa, "Muna ta yawatawa cikin duniya dukka; duba, dukkan duniya na zaune tsit kuma cikin hutawa."
\s5
\v 12 Sai mala'ikan Yahweh ya amsa yace, "Yahweh mai runduna, har yaushe ne ba za ka nuna tausayi ga Yerusalem ba da kuma biranen Yahuda da suka sha wahalar zafin fushi shekarun nan saba'in?"
\v 13 Yahweh ya amsa wa mala'ikan da ya yi magana da shi, da kalmomi masu daɗi, kalmomin ta'aziya.
\s5
\v 14 Sai mala'ikan dake magana da ni yace mani, "Ka yi kira ka ce, 'Yahweh mai runduna ya faɗi haka: Ina kishi game da Yerusalem da Sihiyona da babban kishi!
\v 15 Ina jin haushi ƙwarai game da al'umman dake zaune cikin hutu. Yayin da haushina kaɗan ne game da su, sai suka maida bala'in ya zama da tsanani.
\s5
\v 16 Saboda haka Yahweh mai runduna ya faɗi wannan: Na komo ga Yerusalem tare da jinkai. Za a sake gina gidana cikinta - wannan furcin Yahweh mai runduna ne - kuma za a ja layin gwaji bisa Yerusalem!'
\v 17 Ka sake kira, kuma, ka ce, 'Yahweh mai runduna ya faɗi haka: Biranena zasu sake malala da nagarta, Yahweh kuma zai sake yi wa Sihiyona ta'aziya, zai kuma sake zaɓen Yerusalem.'"
\s5
\v 18 Sai na ɗaga idanuna na ga ƙahonni huɗu!
\v 19 Sai na yi magana da mala'ikan dake magana da ni, "Mene ne waɗannan?" Ya amsa mani, "Waɗannan ne ƙahonnin da suka warwatsa Yahuda, da Isra'ila, da Yerusalem."
\s5
\v 20 Sai Yahweh ya nuna mani masassaƙa huɗu.
\v 21 Na ce, "Me waɗannan mutanen suka zo yi?" Ya amsa, yace, "Waɗannan ne ƙahonnin da suka warwatsa Yahuda har ba mai iya ɗaga kansa. Amma waɗannan mutane sun zo ne su kore su, su kakkarya ƙahonnin al'ummai waɗanda suka ɗaga ƙahon tsayayya da ƙasar Yahuda domin watsar da ita."
\s5
\c 2
\cl Sura 2
\p
\v 1 Daga nan na ɗaga idanuna sai na ga mutum da ma'auni a hannunsa.
\v 2 Na ce, "Ina zaka?" Sai ya ce mani, "Domin in auna Yerusalem, a tantance faɗinta da tsawonta."
\s5
\v 3 Sai mala'ikan da yake magana da ni ya yi tafiyar sa sai wa ni mala'ika kuma ya tafi domin ya same shi.
\v 4 Mala'ikan na biyu yace masa, "Yi gudu ka yi magana da saurayin can; ka ce, 'Yerusalem zata zauna a buɗaɗɗiyar ƙasa saboda yawan mutane da dabbobi dake cikinta.
\v 5 Gama ni - wannan furcin Yahweh ne - zan zama katangar wuta kewaye da ita, kuma zan zama ɗaukakar dake cikinta.
\s5
\v 6 Tashi! Tashi! Ku gudu daga ƙasar arewa - wannan furcin Yahweh ne - gama na warwatsa ku kamar kusurwoyin iska huɗu a sasarin sama! - wannan furcin Yahweh ne.
\v 7 Tashi! Ku tsere zuwa Sihiyona, ku da kuke zaune tare da ɗiyar Babila!'"
\s5
\v 8 Gama bayan da Yahweh mai runduna ya darajantani ya kuma aike ni ga al'umman nan da suka washe ku - gama duk wanda ya taɓa ku, ya taɓa ƙwayar idon Allah! - bayan da Yahweh ya yi wannan, sai ya ce,
\v 9 "Ni da kaina zan girgiza hannuna a bisansu, kuma za a washe su domin bayinsu. "Daga nan zaku sani Yahweh mai runduna ne ya aiko ni.
\s5
\v 10 "Ki raira waƙa domin farinciki, ke ɗiyar Sihiyona, gama ni da kaina ina gaf da zuwa in kafa sansani a cikinki! - wannan ne furcin Yahweh."
\v 11 Daga nan manyan al'ummai zasu haɗu da juna zuwa ga Yahweh a wannan rana. Ya faɗi, "Daga nan zaku zama mutanena; kuma zan kafa sansani a cikinku," daga nan kuma zaku sani Yahweh mai runduna ya aiko ni zuwa gare ku.
\s5
\v 12 Gama Yahweh zai gãji Yahuda a matsayin mai 'yancin gãdonta cikin ƙasa mai tsarki kuma zaya sake zaɓen Yerusalem domin kansa.
\v 13 Ku yi tsit, dukkanku masu rai, a gaban Yahweh, domin an zugo shi daga wurinsa mai tsarki!
\s5
\c 3
\cl Sura 3
\p
\v 1 Sai Yahweh ya nuna mani Yoshuwa babban firist a tsaye a gaban mala'ikan Yahweh ga kuma Shaiɗan a tsaye a hannun damansa domin ya zarge shi da zunubi.
\v 2 Mala'ikan Yahweh yace da Shaiɗan, "Bari Yahweh ya tsauta ma, Shaiɗan; bari Yahweh, wanda ya zaɓi Yerusalem, ya tsauta maka! Wannan ba reshe ba ne da aka ciro daga wuta?"
\v 3 Yoshuwa dai na sanye da ƙazantattun tufafi yayin da yake tsaye a gaban mala'ikan.
\s5
\v 4 Sai mala'ikan ya yi magana yace da waɗanda ke tsaye a gabansa, "Ku tuɓe ƙazantattun tufafin daga jikinsa." Sai yace da Yoshuwa, "Duba! na sa laifuffukanka su kawu daga gare ka kuma zan sanya maka kaya masu tsafta."
\v 5 Sai yace, "Bari a sa rawani mai tsafta a bisa kansa!" Sai suka sa rawani mai tsafta a bisa kan Yoshuwa kuma suka sanya masa tufafi masu tsafta yayin da mala'ikan Yahweh ke tsaye tare dasu.
\s5
\v 6 Daga nan sai mala'ikan Yahweh ya yi umarni mai juyayi ga Yoshuwa yace,
\v 7 "Yahweh mai runduna ya faɗi wannan: Idan za ka yi tafiya cikin hanyoyina, ka kuma kiyaye dokokina, to za ka yi mulkin gidana kuma ka yi tsaron harabaina, domin zan ba ka dama ka shiga ka fita a tsakiyar waɗannan dake tsayawa a gabana.
\s5
\v 8 Ka saurara, Yoshuwa babban firist, kai da masu tarayya da kai dake zaune tare da kai! Domin waɗannan mutane alama ne, gama ni da kaina zan taso da bawana Reshen.
\v 9 Yanzu ka duba dutsen da na sa a gaban Yoshuwa. Akwai idanu bakwai a kan wannan dutse ɗaya, kuma zan sassaƙa hatimi -wannan ne furcin Yahweh mai runduna - kuma zan cire zunubin daga wannan ƙasa a rana ɗaya.
\s5
\v 10 A wannan rana - wannan furcin Yahweh mai runduna ne - kowanne mutum zai gayyaci maƙwabcinsa ya zauna a gindin inabinsa da gindin itacen ɓaurensa."
\s5
\c 4
\cl Sura 4
\p
\v 1 Sai mala'ikan dake magana da ni ya juya ya farko da ni kamar mutumin dake farkarwa daga barci.
\v 2 Ya ce da ni, "Me ka gani?" na ce, "Na ga mazaunin fitila da aka yi da zinariya baki ɗaya, da kwano a bisansa. Yana da fitilu bakwai a bisansa da kuma lagwanin fitilu bakwai a kan kowacce fitila.
\v 3 Akwai itatuwan zaitun biyu a kowanne gefensa, ɗaya na gefen dama da kwanon ɗaya kuma na gefen hagu."
\s5
\v 4 Sai na ƙara magana da mala'ikan dake magana da ni. Na ce, "Mene ne ma'anar waɗannan abubuwa ya shugabana?"
\v 5 Mala'ikan dake magana da ni ya amsa yace da ni, "Baka san ma'anar waɗannan abubuwa ba?" Na ce, "A'a, ya shugabana."
\s5
\v 6 Sai ya ce ma ni, "Wannan ce maganar Yahweh ga Zerubabel: Ba ta ƙarfi ba, ba ta iko ba amma ta Ruhuna, Yahweh mai runduna ya faɗa.
\v 7 Kai wane ne, babban dutse? A gaban Zerubabel za ka zama sarari, zai kuma kawo dutsen dake sama tare da sowace - sowacen 'Alheri! Alheri a gare shi!'"
\s5
\v 8 Maganar Yahweh tazo gare ni, cewa,
\v 9 "Hannun Zerubabel ya ɗora harsashen ginin wannan gida hannunsa kuma zai kammala shi. Daga nan zaku sani Yahweh mai runduna ya aiko ni gare ku.
\v 10 Wane ne ya rena ranar ƙananan abubuwa? Waɗannan mutane zasu yi farinciki kuma zasu ga dunƙulen dutsen a hannun Zerubabel. (Waɗannan fitilu bakwai idanun Yahweh ne dake dubawa ko ina cikin duniya)."
\v 11 Daga nan na tambayi mala'ikan, "Mene ne waɗannan itatuwan zaitun biyu dake hagu da dama na mazaunin fitilar?"
\s5
\v 12 Na sake tambayar shi kuma, "Mene ne waɗannan rassan zaitun biyu dake gefen bututun zinari biyu dake ɓulɓulo da mạn zinariya daga cikinsu?"
\v 13 Sai ya ce ma ni, "Baka san ko mene ne waɗannan ba?" Na ce, "A'a, ya shugabana."
\s5
\v 14 Sai ya ce, "Waɗannan 'ya'ya maza ne na sabon man zaitun dake tsaye a gaban Ubangijin dukkan duniya."
\s5
\c 5
\cl Sura 5
\p
\v 1 Daga nan na juya na ɗaga idanuna, sai na gani, duba, ga littafi naɗaɗɗe na shawagi a sama!
\v 2 Sai mala'ikan yace mani, "Me ka gani?" Na amsa, "Na ga littafi naɗaɗɗe na shawagi a sama, tsawonshi kamu ashirin fadinshi kamu goma."
\s5
\v 3 Sai ya ce da ni, "Wannan ce la'anar dake yawo a fuskar dukkan ƙasar, za a datse kowanne ɓarawo bisa ga yadda ya faɗa a gefe ɗaya, dukkan wanda kuma ya yi rantsuwa da alƙawarin ƙarya za a datse shi bisa ga yadda ya faɗa a gefe ɗayan, bisa ga maganganunsu.
\v 4 "Zan aika da ita - wannan shi ne furcin Yahweh mai runduna - saboda haka zata shiga gidan ɓarawo da gidan wanda ya yi rantsuwar ƙarya da sunana. Zata zauna a gidanshi ta cinye katakan da duwatsun."
\s5
\v 5 Daga nan sai mala'ikan dake magana da ni ya fita ya ce mani, "Ɗaga idanunka ka ga abin dake tahowa!"
\v 6 Sai na ce, "Mene ne?" Ya ce, "Wannan kwando ne dake ɗauke da garuwa dake zuwa. Wannan laifuffukansu ne cikin dukkan ƙasar."
\v 7 Sai aka ɗauke murfin ƙarfen dake rufe da kwandon sai ga wata mace a cikinsa zaune!
\s5
\v 8 Mala'ikan yace, "Wannan mugunta ce!" Sai ya sake jefa ta cikin kwandon, kuma ya sake rufe shi da murfin ƙarfen.
\v 9 Na ɗaga idanuna sai na ga mata biyu na zuwa wurina, kuma iska na cikin fukafukansu - gama suna da fukafukai kamar fukafukan shamuwa. Suka ɗaga kwandon nan tsakanin duniya da sama.
\s5
\v 10 Sai na ce da mala'ikan nan dake magana da ni, "Ina zasu kai kwandon?"
\v 11 Ya ce da ni, "Zasu gina mashi haikali a ƙasar Shina, domin idan suka gama ginin haikalin, sai su ɗora kwandon a dai-dai wurinda suka shirya dominshi."
\s5
\c 6
\cl Sura 6
\p
\v 1 Sai na juya na hango karusai huɗu suna zuwa sun fito daga tsakanin duwatsu biyu; duwatsun nan biyu kuwa an yi su daga tagulla ne.
\v 2 Karusa na farko dawakansa jajaye ne, karusa na biyu dawakansa baƙaƙe ne,
\v 3 karusa na uku dawakansa farare ne, karusa na huɗu dawakansa dabbare - dabbaren ruwan toka ne.
\v 4 Sai na amsa na ce da mala'ikan dake magana da ni, "Mene ne waɗannan, ya shugabana?"
\s5
\v 5 Sai mala'ikan ya amsa yace ma ni, "Waɗannan su ne iskoki huɗu na sararin samaniya waɗanda ke fitowa daga wurin da suke tsayawa a gaban Ubangijin dukkan duniya.
\v 6 Mai baƙaƙen dawakai na tafiya zuwa ƙasar arewa; fararen dawakan na tafiya zuwa ƙasar yamma; dawakai masu dabbare-dabbaren ruwan toka na tafiya zuwa ƙasar kudu."
\s5
\v 7 Waɗannan dawakai masu ƙarfi suka tafi suka nemi su kewaye dukkan duniya, sai mala'ikan yace, "Ku tafi ku kewaye bisa duniya!" Sai suka tafi domin dukkan duniya.
\v 8 Sai ya kira ni ya yi magana da ni ya ce, "Dubi waɗanda ke tafiya zuwa ƙasar arewa; zasu tausar da ruhuna game da ƙasar arewa."
\s5
\v 9 Sai maganar Yahweh ta zo gare ni, cewa,
\v 10 "Ka karɓi baiko daga 'yan gudun hijirar - daga Heldai, da Tobiya, da Yedaya - sai ka tafi dai-dai cikin wannan ranar ka kai cikin gidan Yosaya ɗan Zafaniya, wanda ya zo daga Babila.
\v 11 Sai ka ɗauki azurfar da zinarin, sai ka yi rawani dasu ka ɗora bisa kan Yoshuwa ɗan Yehozadak, babban firist.
\s5
\v 12 Ka yi magana da shi ka ce, 'Yahweh mai runduna ya faɗi wannan: Wannan mutum, sunansa Reshe! Zai yi girma inda ya ke sa'an nan kuma ya gina haikalin Yahweh!
\v 13 Shi ne wanda zai gina haikalin Yahweh sa'an nan ya ɗaga darajarsa; daga nan zai zauna ya yi mulki akan kursiyinsa. Zai zama firist a bisa kursiyinsa kuma fahimtar salama za ta kasance tsakanin su biyun.
\s5
\v 14 Za a bayar da rawani ga Heldai, da Tobiya da Yedaya da Hen ɗan Zakariya a matsayin abin tunawa a cikin haikalin Yahweh.
\v 15 Daga nan waɗanda ke daga nesa zasu zo su gina haikalin Yahweh, domin ku sani Yahweh mai runduna ne ya aiko ni zuwa gare ku; wannan zai faru idan da gaske kun saurari muryar Yahweh Allahnku!'"
\s5
\c 7
\cl Sura 7
\p
\v 1 Da sarki Dariyos ya yi mulki shekaru huɗu, a ranar huɗu ga watan Kisleb (wanda shi ne watan tara), maganar Yahweh ta zo ga Zakariya.
\v 2 Mutanen Betel suka aika da Shareza da Regem Melek da kuma mazajensu domin su yi roƙo gaban fuskar Yahweh.
\v 3 Suka yi magana da firistocin dake gidan Yahweh mai runduna da kuma annabawan; suka ce, "Ko zan yi makoki cikin watan biyar ta wurin yin azumi, kamar yadda na yi cikin shekarun nan masu yawa?"
\s5
\v 4 Sai maganar Yahweh mai runduna ta zo gare ni, cewa,
\v 5 "Yi magana da dukkan mutanen ƙasar da firistocin ka ce, 'Da kuka yi azumi da makoki watan biyar da watan bakwai cikin shekarun nan saba'in, da gaske ni kuka yi wa azumi?
\v 6 Da kuka ci ku ka sha, ba don kanku ku ka ci kuka sha ba?
\v 7 Waɗannan ba sune maganganun da Yahweh ya yi shela ba ta bakin annabawan dã, sa'ad da kuke zaune a Yerusalem da biranen kewaye cikin wadata kuma kuka yi zamanku a Negeb, da gefen tsaunukan yamma?'"
\s5
\v 8 Maganar Yahweh ta zo wurin Zakariya, cewa,
\v 9 "Yahweh mai runduna ya faɗi haka, 'Ku zartar da hukunci mai gaskiya, da amintaccen alƙawari, da kuma jinƙai. Bari kowanne mutum ya yi wa ɗan'uwansa haka.
\v 10 Game da gwauruwa da maraya, da kuma baƙo, da matalauci-- kada ku ƙuntata masu, kada kuma wani ya shirya wani mugun abu game da ɗan'uwansa a cikin zuciyarsa.'
\s5
\v 11 Amma suka ƙi maida hankali kuma suka ɗaga kafaɗunsu cikin taurinkai. Suka toshe kunnuwansu domin kada su ji.
\v 12 Suka maida zukatansu taurara kamar dutse domin ka da su ji shari'a ko maganganun Yahweh mai runduna. Ya aika da saƙonnin nan ga mutanen ta wurin Ruhunsa a lokatan farko, ta bakin annabawa. Amma mutanen suka ƙi saurare, domin wannan Yahweh mai runduna ya ji haushin su ƙwarai.
\s5
\v 13 Sai ya kasance da ya yi kira, basu saurara ba. Ta haka kuma," Yahweh mai runduna yace, "Zasu yi kira zuwa gare ni, amma ba zan saurare su ba.
\v 14 Gama zan warwatsasu da guguwa cikin dukkan al'umman da basu taɓa gani ba, ƙasar za ta zama kufai bayansu. Gama ba wanda zai iya ratsawa ta cikin ƙasar ko ya dawo gareta tun da mutanen sun maida ƙasarsu ta farinciki zuwa watsartsiyar ƙasa."
\s5
\c 8
\cl Sura 8
\p
\v 1 Maganar Yahweh mai runduna ta zo gare ni cewa,
\v 2 "Yahweh mai runduna ya faɗi wannan: Ina kishi domin Sihiyona da kuma babban kishi da hasala mai zafi ƙwarai!
\v 3 Yahweh mai runduna ya faɗi wannan: Zan komo wurin Sihiyona in kuma zauna a tsakiyar Yerusalem, gama za a kira Yerusalem Birnin Gaskiya kuma dutsen Yahweh mai runduna za a ce da shi Dutse Mai Tsarki!
\s5
\v 4 Yahweh mai runduna ya faɗi haka: Tsofaffi maza da mata zasu ƙara kasancewa a titunan Yerusalem, kowannensu za shi buƙaci sanda a hannunsa domin yạ tsufa.
\v 5 Titunan birnin zasu cika da matasa maza da mata, masu wasanni a cikinsu.
\s5
\v 6 Yahweh mai runduna ya faɗi haka: Idan wani al'amari ya zama mai wuya a ganin mutanen nan da suka rage, a wannan kwanaki, shi ma za shi zama abu mai wuya a idanuna? -- wannan furcin Yahweh ne.
\v 7 Yahweh mai runduna ya faɗi wannan; Duba, Ina gaf da kuɓutar da mutanena daga ƙasashe na fitowar rana da na faɗuwar rana!
\v 8 Gama zan dawo dasu, kuma zasu zauna a tsakiyar Yerusalem, haka zasu zama mutanena kuma, ni kuma zan zama Allahnsu cikin gaskiya da adalci!
\s5
\v 9 Yahweh mai runduna ya faɗi haka: Ku da kuka ci gaba da sauraron maganganuna daga bakin annabawa tun farkon kafa harsashen ginin wannan haikali, - wannan gida nawa, Yahweh mai runduna: Ku ƙarfafa hannayenku domin a gina haikalin.
\v 10 Domin kamin wannan lokaci babu hatsin da aka tara daga wurin wani, babu wata riba domin mutum ko dabba, kuma ba a sami salama ba daga magabci ko ga mai shiga ko mai fita. Na maishe da kowanne mutum magabci ga makwabcinsa.
\s5
\v 11 Amma yanzu baza shi kasance kamar kwanakin baya ba, zan zauna tare da mutanena waɗanda suka rage - wannan ne furcin Yahweh mai runduna.
\v 12 Gama za a shuka irin salama; kuringa mai haurawa sama zata ba da 'ya'ya, duniya kuwa zata ba da amfanin ƙasa; sammai zasu ba da raɓarsu, gama zan sa sauran jama'ar da suka rage su gãji dukkan waɗannan abubuwa.
\s5
\v 13 Kun zama misali na la'ana ga al'ummai, gidan Yahuda da na Isra'ila. Yanzu fa zan kuɓutar da ku da haka kuma zaku zama albarka. Kada ku ji tsoro; amma bari hannuwanku su ƙarfafa!
\v 14 Gama Yahweh mai runduna ya faɗi wannan: kamar yadda na shirya yi maku lahani a lokacin da kakanninku suka cakuneni - Yahweh mai runduna ya fadi wannan - kuma bai fasa ba,
\v 15 haka kuma zan yi shiri mai kyau a wannan kwanaki zuwa ga Yerusalem da kuma gidan Yahuda! Kada ku ji tsoro!
\s5
\v 16 Ga abubuwan da dole ku aikata: ku faɗi gaskiya, kowanne mutum ga makwabcinsa. Ku yi shari'a da gaskiya, da adalci, da kuma salama a ƙofofinku.
\v 17 Kada ku yi shirin aikata mugunta a cikin zuciyarku ga junanku, kuma kada ku ƙaunaci alƙawaran ƙarya -- gama waɗannan sune abubuwan da na ƙi! - wannan furcin Yahweh ne."
\s5
\v 18 Sa'an nan maganar Yahweh mai runduna ta zo gareni, cewa,
\v 19 "Yahweh mai runduna ya faɗi haka: Azumi na watan huɗu, da na watan biyar, da na watan bakwai, da na watan goma, duk zasu zama lokatan farinciki, da jin daɗi, da bukukuwan murna na gidan Yahuda! Saboda haka ku ƙaunaci gaskiya da salama!
\s5
\v 20 Yahweh mai runduna ya faɗi haka: Mutane zasu sake zuwa, harma da waɗanda suke zama a birane daban - daban.
\v 21 Mazaunan birni ɗaya zasu je wani birnin su ce, "Mu yi sauri mu je mu yi roƙo a gaban fuskar Yahweh mu kuma nemi Yahweh mai runduna! Mu ma zamu tafi da kanmu.
\v 22 Mutane dayawa da manyan al'umma zasu zo Yerusalem su nemi Yahweh mai runduna kuma su roƙi tagomashin Yahweh!
\s5
\v 23 Yahweh mai runduna ya faɗi haka: A wannan kwanakin, maza goma daga kowanne harshe da kuma al'umma zasu kama haɓar rigarku su ce, "Bari mu tafi tare da ku, gama mun ji cewa Allah na tare da ku!"'
\s5
\c 9
\cl Sura 9
\p
\v 1 Wannan furcin maganar Yahweh ne game da ƙasar Hadrak da Damaskus. Gama idanun Yahweh na bisan dukkan 'yan'adam, da kuma bisa dukkan kabilun Isra'ila.
\v 2 Furcin nan kuma ya shafi Hamat wadda take maƙwabciya da Damaskus, ta kuma shafi Taya da Sidon, ko da shi ke suna da hikima ƙwarai.
\s5
\v 3 Taya ta gina wa kanta mafaka mai karfi ta kuma lafta azurfa kamar ƙura da kuma tatacciyar zinariya kamar laƙa a bisa titunanta.
\v 4 Duba! Ubangiji za ya kawar da ita ya kuma lallata karfinta na teku, da haka zata hallaka da wuta.
\s5
\v 5 Ashkelon zata gani ta kuma ji tsoro! Gaza kuma zatayi rawar jiki ƙwarai! Ekron, begenta ba zai tabbata ba! Sarkin zaya hallaka daga Gaza, ba kuma za a sake zama cikin Ashkelon ba!
\v 6 Baƙi zasu gina gidaje a Ashdod, zan kuma datse girman kan Filistiyawa.
\v 7 Gama zan fitar da jininsu daga bakinsu, abubuwan banƙyamarsu kuma daga tsakiyar haƙoransu. Da haka zasu zama ragowa ga Allahnmu kamar zuriya a Yahuda, Ekron kuma zata zama kamar Yebusawa.
\s5
\v 8 Zan kafa sansani kewaye da ƙasata gãba da sojojin maƙiya domin kada wani ya ratsa ta cikinta ko ya je ko ya dawo, domin ba bu mai tsanantawar da zai ƙara shigowa ta cikin ƙasata. Yanzu dai zan kula da ƙasata da idanuna!
\s5
\v 9 Yi sowa da farinciki mai girma, ɗiyar Sihiyona! Yi sowa da murna, ɗiyar Yerusalem! Duba! Sarkinki na zuwa gare ki da adalci yana kuma kuɓutar dake. Mai tawali'u ne yana bisa kan jaki, a bisa kan ɗan jaki.
\v 10 Daga nan zan datse karusa daga Ifraimu doki kuma daga Yerusalem, Za a kuma datse baka daga yaƙi; gama za ya yi maganar salama ga al'ummai, mulkinsa kuma za ya zama daga teku zuwa teku, kuma daga Ƙogi har zuwa ƙarshen duniya!
\s5
\v 11 Amma ke, saboda jinin alƙawarina dake, zan fitar da 'yan sarƙarki daga ramin da babu ruwa.
\v 12 Ku dawo cikin mafaka mai ƙarfi dukkan ku 'yan kurkukun bege! Ko yau ina shaida maku zan maido maku ruɓi biyu,
\v 13 gama na lanƙwasa Yahuda kamar baka na. Na cika ƙwarina da Ifraimu. Na motso da 'ya'ya mazanki, Sihiyona, gãba da 'ya'ya mazanki, Giris, kuma na yi ki, Sihiyona, kamar takobin mayaƙi!
\s5
\v 14 Yahweh za ya bayyana gare su, kuma kibiyoyinsa zasu harba kamar walƙiya! Gama Ubangijina Yahweh za ya busa ƙahon kuma za ya cigaba cikin hadari daga Teman.
\v 15 Yahweh mai runduna zai kare su, zasu kuma haɗiyesu, su kuma ci nasara da duwatsun majaujawa. Sa'an nan zasu sha suna sowa kamar mutanen da suka bugu da ruwan inabi, zasu kuma cika da ruwan inabi kamar dãro, kamar kusurwoyin bagadi.
\s5
\v 16 Yahweh Allahnsu zai cece su a wannan rana; zasu zama kamar garke mai ɗauke da mutanensa, gama zasu zama duwatsun kambi, wanda aka ɗaukaka bisa ƙasarsa.
\v 17 Duba yadda zasu zama da kyau da kuma ban sha'awa! Samarin zasu yalwata kan hatsi, budurwan kuma bisa inabi mai zaƙi!
\s5
\c 10
\cl Sura 10
\p
\v 1 Ku roƙi Yahweh ruwan sama a lokacin bazara -Yahweh shi ne mai yin hadarun-aradu -- kuma yana ba da ruwan sama ga kowa da kuma dukkan tsire tsiren gona.
\v 2 Gama ƙarya kawai gumakan gãdo ke faɗi; masu sihiri kuma suna ƙirƙiro ƙarya; suna faɗin mafarkai na ruɗani su kuma yi ta'aziyar wofi, da haka suke yawo kamar tumaki suna shan azaba domin babu makiyayi.
\s5
\v 3 Fushina na ƙuna akan makiyayan; sune bunsuran -- shugabannin -- waɗanda zan hora. Yahweh mai runduna za ya kuma lura da garkensa, gidan Yahuda, za ya mai dasu kamar dokin yaƙinsa a yaƙi!
\s5
\v 4 Daga gare su dutsen kusurwar gini zaya fito; daga gare su turken rumfar za ya fito; bakan yaƙi za shi fito daga nan; daga can dukkan shugabanni zasu fito tare.
\v 5 Zasu zama kamar jarumawa masu tattaka maƙiyansu a cikin laka a bisa titunansu a yaƙi; zasu ja dagar yaƙi, gama Yahweh na tare da su, zasu kuma kunyatar da mahayan dawakan yaƙi.
\s5
\v 6 Zan ƙarfafa gidan Yahuda in kuma ceci gidan Yosef; gama zan maido dasu in kuma nuna masu jinƙai. Ba za su yi kamar na yashe su ba, gama ni ne Yahweh Allahnsu, kuma zan amsa masu.
\v 7 Daga nan Ifraim zaya zama kama da mayaƙi, zuciyarsu kuma zata yi farinciki kamar da inabi; 'Ya'yansu zasu gani su yi farinciki. Zuciyarsu zata yi farinciki a ciki na!
\s5
\v 8 Zan yi masu busa in kuma tara su, gama zan kuɓutar dasu, kuma zasu zama da girma kamar yadda suke a dã!
\v 9 Na shuka su cikin al'ummai amma zasu tuna da ni a ƙasashe masu ni sa, su da 'ya'yansu zasu rayu su kuma dawo gida.
\v 10 Gama daga Asiriya zan tattara su in kuma maido dasu daga Masar. Zan dawo dasu ƙasar Giliyad da Lebanon har sai ba sauran wuri dominsu.
\s5
\v 11 Zan bi ta cikin tekun azabarsu; Zan tsautawa igiyoyin tekun nan in kuma busar da dukkan zurfafun Nilu. Za a saukar da ƙasaitar Asiriya, sandar mulkin Masar kuma zata tafi daga Masarawa.
\v 12 Zan ƙarfafa su a cikina, za su yi tafiya kuma cikin sunana - wannan furcin Yahweh ne.
\s5
\c 11
\cl Sura 11
\p
\v 1 Ki buɗe ƙofofinki, Lebanon, don wuta ta cinye itatuwanki na sida!
\v 2 Yi makoki, itatuwan siferes, gama itatuwan sida sun faɗi! Abin da yake ƙasaitacce ya lalace sarai! Yi makoki, ku rimaye na Bashan, gama babban kurmi dukka ya faɗi.
\v 3 Makiyaya suna ta kururuwa, gama an lalatar da ɗaukakarsu! Muryar 'ya'yan zakuna na ruri, gama an lallatar da fahariyar Kogin Yodan!
\s5
\v 4 Wannan ne abin da Yahweh Allahna ya faɗi: "Kamar makiyayi, mai kiwon garken da aka ƙaddara domin yanka!
\v 5 (Su waɗanda suka sayesu suka yankasu kuma ba a yi masu horo ba, kuma waɗanda suka sayar da su sukace; "Mai albarka ne Yahweh! Na zama mai arziƙi! gama makiyayan dake yi wa masu garken aiki basu jin tausayinsu).
\v 6 Gama ba zan ƙara jin tausayin mazaunan ƙasar ba! --- wannan furcin Yahweh ne. Duba! Ni da kaina ina gaf da bayar da kowanne mutum cikin hannun makwabcinsa da kuma cikin hannun sarkinsa, zasu kuma lallatar da ƙasar ba bu wanda zan kuɓutar daga hannunsu."
\s5
\v 7 Don haka na zama makiyayin garken da aka ƙaddara domin yanka, ga masu cinikin tumaki. Na ɗauko sanduna biyu; ɗaya na kira ta "tagomashi" ɗayar kuma na kira ta "haɗin kai." da haka na yi kiwon garken.
\v 8 A cikin wata ɗaya na hallaka makiyayan uku, gama hakurina ya gaza a kansu, haka su ma suka ƙi ni.
\v 9 Sai na cewa masu garken, "Ba zan sake yi maku aikin makiyayi ba. Tumakin da ke mutuwa-- bari su mutu; tumakin da ke hallaka --- bari su hallaka. Bari tumakin dasu ka rage kowanne ya ci naman maƙwabcinsa."
\s5
\v 10 Sai na ɗauki sandata "tagomashi" sai na karyata domin in karya alƙawarina da nayi da dukkan kabiluna.
\v 11 A wannan ranar aka karya alƙawarin, masu cinikin tumaki da waɗanda ke kallona suka sani cewa Yahweh ya yi magana.
\v 12 Na ce masu, "Idan kun ga ya dace ku biya ni ladata. Amma idan ba haka ba, kada kuyi." Sai suka auna mani ladata --- sulallan azurfa talatin.
\s5
\v 13 Sai Yahweh yace dani, "Zuba azurfar cikin ma'aji, darajar farashin da aka kimantaka!" Sai na ɗauki sulallan azurfar talatin na zuba su cikin ma'aji a gidan Yahweh.
\v 14 Sa'an nan na karya sandata ta biyu "Haɗin kai," domin a karya 'yan'uwantakar dake tsakanin Yahuda da Isra'ila.
\s5
\v 15 Yahweh yace da ni, "Ka sake, ɗaukarwa kanka kayan aiki irin na wawan makiyayi,
\v 16 gama duba, ina gaf da naɗa makiyayi a ƙasar. Ba za ya kula da tumakin dake hallaka ba. Ba za ya tafi neman ɓatattun tumaki ba, ko ya warkar da tumakin da suka gurgunce ba. Ba zaya ciyar da lafiyayyun tumakin ba, amma za ya cinye naman tumaki masu ƙiba, ya kuma saɓe ƙofatunsu.
\s5
\v 17 Kaiton makiyayi mara amfani da ya yi watsi da garken! Bari takobi ta yi tsayayya da hannusa da kuma idonsa na dama! Bari hannunsa ya shanye idonsa na dama ya makance!"
\s5
\c 12
\cl Sura 12
\p
\v 1 Wannan furcin maganar Yahweh game da Isra'ila - furcin Yahweh, shi wanda ya shimfiɗa sararin sammai ya kuma kafa harsashen duniya, wanda ya sa ruhun ɗan adam cikin mutum,
\v 2 "Duba, ina gaf da sa Yerusalem ta zama kofi mai sa maƙwabtanta tangaɗi. Haka kuma za shi zama ga Yahuda a lokacin da aka yiwa Yerusalem sansani.
\v 3 A wannan rana, Zan maida Yerusalem dutse mai nauyi domin dukkan mutane. Duk wanda ya yi ƙoƙarin ɗaga wannan dutse za ya ji wa kansa rauni mai tsanani, dukkan al'umman duniya kuma zasu tattaru yin gãba da wannan birni.
\s5
\v 4 A ranan nan --- wannan ne furcin Yahweh --- zan bugi kowanne doki da firgita da kuma kowane mahayi da hauka. Zan dubi gidan Yahuda da tagomashi in kuma bugi kowanne dokin sojojin da makanta.
\v 5 Daga nan shugabannin Yahuda zasu ce cikin zuciyarsu, 'Mazaunan Yerusalem sune ƙarfinmu saboda Yahweh mai runduna, Allahnsu.'
\s5
\v 6 A wannan rana zan mai da shugabannin Yahuda kamar tukunyar wuta a tsakiyar itatuwa da kuma fitila mai ci balbal a cikin hatsin dake tsaye, gama zasu hallaka dukkan mazauna kewaye dasu dama da hagu. Yerusalem zata sãke zaunawa a wurinta."
\s5
\v 7 Yahweh zai ceci rumfunan Yahuda da farko, don kada darajar gidan Dauda da kuma na mazaunan Yerusalem su fi na sauran mazaunan Yahuda.
\v 8 A wannan ranar Yahweh zaya zama kariyar mazaunan Yerusalem, kuma a wannan ranar, waɗanda basu da ƙarfi cikinsu zasu zama kamar Dauda, yayin da gidan Dauda zaya zama kamar Allah, kamar mala'ikan Yahweh a gabansu.
\v 9 "A ranan nan da zan fara hallaka dukkan al'umman dasu ka yi tsayayya da Yerusalem.
\s5
\v 10 Amma zan zubo da ruhun tausayi da na roƙo a bisa gidan Dauda da mazaunan Yerusalem, domin su dube ni, wanda suka soke. Zasu yi makoki domina, kamar wanda ke makoki domin tilon ɗansa; za su yi matuƙar makoki dominsa kamar waɗanda su ke makokin mutuwar ɗan fari.
\v 11 A wannan ranar makokin cikin Yerusalem za shi zama kamar makokin da aka yi cikin Hadad Rimon cikin kwarin Megido.
\s5
\v 12 Ƙasar zata yi makoki, kowacce zuriya daban da wasu zuriyoyin. Zuriyar gidan Dauda zata zama a ware matayensu kuma zasu zama a ware daga mazajen. Zuriya daga gidan Natan zasu zama a ware matayensu kuma zasu zama a ware da mazajen.
\v 13 Zuriyar gidan Lebi zasu zama a ware, matayensu kuma a ware da mazajen. Zuriyar Shimeyawa zasu zama a ware matayensu kuma a ware daga mazajen.
\v 14 Kowacce zuriya ta sauran zuriyar da suka ragu - kowacce zuriya zata zama a ware matayensu kuma zasu zama a ware daga mazajen."
\s5
\c 13
\cl Sura 13
\p
\v 1 "A wannan rana za a buɗe wa gidan Dauda magudanar ruwa da kuma mazaunan Yerusalem, saboda zunubansu da rashin tsarkinsu.
\v 2 A wannan ranar -- wannan furcin Yahweh mai runduna ne - cewa zan datse sunayen gumaka daga ƙasar don kada a ƙara tunawa dasu. Zan kuma sa dukkan annabawan ƙarya da ƙazamin ruhunsu su fita daga ƙasar.
\s5
\v 3 Idan wani mutum ya ci gaba da yin annabci, mahaifinsa da mahaifiyarsa waɗanda suka haifeshi zasu ce masa, 'Ba za ka rayu ba, don kana ƙarya da sunan Yahweh! Sa'an nan mahaifinsa da mahaifiyarsa waɗanda suka haife shi zasu soke shi yayin da yake anabce-anabce.
\s5
\v 4 A wannan ranar kowanne annabi zayaji kunyar wahayinsa yayinda yake gaf da yin annabci. Waɗannan annabawan ba zasu ƙara sanya rigar gashi ba don su ruɗi jama'a.
\v 5 Gama kowanne zai ce, 'Ni ba annabi ba ne! Ni manomi ne, na fara aikin gona tun ina yaro!'
\v 6 Amma wani zai ce masa, 'ina ka samo waɗannan raunukan a hannuwanka? shi kuwa za ya amsa, 'An yi mani rauni tare da waɗanda ke gidan abokaina."'
\s5
\v 7 "Takobi! Motsa kanki gãba da makiyayina, mutumin da ya tsaya kusa da ni -- wannan furcin Yahweh ne - mai runduna. Bugi makiyayin, tumakin kuma zasu warwatse! Gama zan juya hannuna gãba da ƙasƙantattun.
\s5
\v 8 Daga nan zaya kasance game da wannan a cikin dukkan ƙasar --- wannan furcin Yahweh ne --- kashi biyu cikin uku za a datse! Waɗannan mutane zasu hallaka; kashi ɗaya cikin uku kawai zaya rage a wurin.
\v 9 Kashi ɗayan da ya rage zan bi dasu ta cikin wuta in tãcesu kamar yadda ake tãce azurfa; zan gwada su kamar yadda ake gwada zinariya. Zasu kira bisa sunana, ni kuwa zan amsa masu in ce, 'Waɗannan mutanena ne!' su kuma zasu ce, 'Yahweh ne Allahna!"'
\s5
\c 14
\cl Sura 14
\p
\v 1 Duba! Ranar Yahweh na zuwa da za a raba ganimarku a tsakiyarku.
\v 2 Gama zan tattara dukkan al'umma tsayayya da Yerusalem domin yaƙi kuma za a ci birnin. Za a warwashe gidajensu kuma za a yiwa matayensu fyaɗe. Rabin birnin za ya tafi zuwa bautar talala, amma ragowar mutanen ba za a datse su ba daga birnin.
\s5
\v 3 Amma Yahweh zaya fita ya kuma jãdagar yaƙi da waɗannan al'ummai kamar yadda ya jãgadar yaƙi a ranar yaƙi.
\v 4 A wannan rana tafin sawayensa zasu tsaya bisa Dutsen Zaitun, wanda yake gefen Yerusalem maso gabas. Za a raba Dutsen Zaitu kashi biyu tsakanin gabas da yamma ta kwari mai girma kuma sashe ɗaya na dutsen za shi janye zuwa arewa ɗaya sashen kuma za shi janye zuwa kudu.
\s5
\v 5 Sa'an nan zaku tsere zuwa cikin kwarin tsakanin duwatsun Yahweh, domin kwarin dake tsakanin duwatsun za ya kai har Azel. Zaku yi ta gudu kamar yadda kuka guje wa girgizar ƙasa a kwanakin Uzaya, sarkin Yahuda. Sa'an nan Yahweh Allahna za ya zo kuma dukkan tsarkaka zasu kasance tare dashi.
\s5
\v 6 A wannan ranar da ba za a sami haske ba, babu sanyi ko ƙanƙara.
\v 7 A wannan ranar, Yahweh kaɗai ya san ta, ba za a sake yin rana ko dare ba, gama maraice za ya zama lokacin haske.
\v 8 A wannan rana ruwayen rai za su ɓulɓulo daga Yerusalem. Rabin ruwan za shi yi gudu zuwa tekun gabas rabin kuwa zuwa tekun yamma, damina da lokacin sanyi.
\s5
\v 9 Yahweh zai zama sarki a bisa dukkan duniya. A wannan rana Yahweh kaɗai zai zama, Allah ɗaya, babu wani suna sai na sa.
\v 10 Dukkan ƙasa za ta zama kamar Arabah, daga Geba har zuwa Rimon kudu da Yerusalem. Yerusalem zata ci gaba da haurawa bisa a mazamninta, daga Ƙofar Benyamin zuwa inda kofar ta ke a dã, zuwa Ƙofar Kusurwa, kuma zuwa Hasumiyar Hananel zuwa wurin matsewar ruwan inabin sarki.
\v 11 Mutane zasu zauna cikin Yerusalem kuma babu sauran hallaka da zata zo gare su daga wurin Allah. Yerusalem zata zauna cikin kariya.
\s5
\v 12 Wannan ita ce annobar da Yahweh zai hari dukkan al'umman da suka tayarwa Yerusalem da yaƙi: Naman jikinsu zai ruɓe lokacin da suke a tsaye bisa sawayensu. Idanunsu zasu ruɓe cikin kwarminsu kuma harsunansu zasu ruɓe daga cikin bakunansu.
\v 13 A wannan rana babban tsoro daga Yahweh za shi abko masu. Kowannensu zai kama hannun wani, kuma hannun wani zai ɗaga hannunsa domin tsayayya da hannun wani.
\s5
\v 14 Yahuda kuma zai yi yaƙi da Yerusalem. Zasu tara dukiya daga al'umman dake zagaye dasu - zinariya, da azurfa da kuma kyawawan riguna tuli.
\v 15 Annoba zata faɗo wa dawakai da alfadarai, raƙuma da jakai, da dukkan dabbobin da suke a sansaninsu zasu wahala da wannan annobar.
\s5
\v 16 Za shi zama kuma dukkan waɗanda suka rage cikin ƙasashen da suka zo yaƙi da Yerusalem a maimako zasu zo kowacce shekara domin su yi wa sarki sujada, Yahweh mai runduna, sụ kuma kiyaye Idin Bukkoki.
\v 17 Za shi zama kuma idan wani daga cikin al'umman duniya ya kasa zuwa Yerusalem don ya yi sujada ga sarki, Yahweh mai runduna, daga nan Yahweh kuma ba zai aiko masu da ruwan sama ba.
\v 18 Idan al'ummar Masar basu je ba, to ba zasu sami ruwan sama ba. Annoba daga Yahweh zata abko wa duk mutanen dasu ka ƙi zuwa domin su yi Bikin Idin Bukkoki.
\s5
\v 19 Wannan zai zama horon da za a yi wa Masar da kuma horo ga kowacce al'ummar da ba ta zo Yerusalem ta halarci Bikin Idin Bukkoki ba.
\s5
\v 20 Amma a wannan ranar, ƙararrawar dawakai zasu ce, "ku keɓe ga Yahweh," kuma darurrukan da suke gidan Yahweh zasu zama kamar darurruka a gaban bagadi.
\v 21 Gama kowacce tukunya a Yerusalem da Yahuda za a ƙeɓeta ga Yahweh mai runduna kuma duk wanda zai kawo hadaya zai ci daga cikinsu ya kuma tafasa a cikinsu. A wannan rana 'yan kasuwa ba zasu ƙara kasancewa a cikin gidan Yahweh mai runduna ba.