ha_ulb/37-HAG.usfm

84 lines
5.8 KiB
Plaintext

\id HAG
\ide UTF-8
\h Littafin Haggai
\toc1 Littafin Haggai
\toc2 Littafin Haggai
\toc3 hag
\mt Littafin Haggai
\s5
\c 1
\cl Sura 1
\p
\v 1 A shekara ta biyu ta mulkin Sarki Dariyos, a wata na shida, a rana ta fari ga watan, maganar Yahweh ta zo ta hannun annabi Haggai ga gwamnan Yahuda, wato Zerubabel ɗan Shiltiyel, da kuma babban firist Yoshuwa ɗan Yehozadak cewa
\v 2 "Yahweh mai runduna ya faɗi haka: Waɗannan mutanen na cewa, 'lokaci bai yi ba da za mu zo ko mu gina wa Yahweh gida.'"
\s5
\v 3 Sai maganar Yahweh ta zo ta hannun annabi Haggai, cewa,
\v 4 "Lokaci ya yi da za ku zauna a shiryayyun gidajenku, amma kuma wannan gidan na kwance a lalace?
\v 5 To Yahweh mai runduna ya faɗi haka: Ku lura da hanyoyinku!
\v 6 Kun shuka iri da yawa amma kun girbi kaɗan, kun ci amma bai ishe ku ba, kun sha amma ba ku ƙoshi ba. Ku na sa tufafi amma ba ku ji ɗumi ba, kuma mai ƙarbar albashi yana ƙarba kawai ya sa shi cikin jakka mai hudoji!
\s5
\v 7 Yahweh mai runduna ya faɗi haka: "Ku lura da hanyoyinku!
\v 8 Ku hau bisa tudu, ku kawo katako ku gina mani gida, ta haka zan ji daɗi, kuma za a ɗaukaka ni!- in ji Yahweh."
\v 9 "Kun nema da yawa amma duba kun kawo gida kaɗan, don na hure shi! Don me?" Yahweh mai runduna ya furta. "Saboda gidana na kwance a lalace, alhali kowanne ɗayan ku na aiki a nasa gidan.
\s5
\v 10 Saboda haka sammai sun riƙe raɓa, ƙasa kuma ta riƙe amfaninta,
\v 11 Ni na kawo ƒãri ga ƙasar kuma ga tuddai, ga ƙwayar hatsi, kuma ga sabon ruwan inabi, ga mai kuma ga girbin ƙasa, ga mutane da kuma ga dabbobi, kuma ga dukkan ayyukan hannuwanku!"
\s5
\v 12 Sai Zarubabel ɗan Shaltiyel da babban firist Yoshuwa ɗan Yehozadak, tare da dukkan sauran mutanen, suka yi biyayya da muryar Yahweh Allahnsu da kuma kalmomin annabi Haggai, saboda Yahweh Allahnsu ya aiko shi kuma mutanen sun ji tsoron fuskar Yahweh.
\v 13 Sai Haggai, mai kawo saƙon Yahweh, ya faɗi saƙon Yahweh zuwa ga mutanen ya ce, "Ina tare da ku! - wannan furcin Yahweh ne!"
\s5
\v 14 Yahweh ya zuga ruhun gwamnan Yahuda, wato Zerubabel ɗan Shiltiyel, da kuma ruhun babban firist Yoshuwa ɗan Yehozadak, da kuma ruhun dukkan sauran mutanen, domin haka suka je su ka yi aiki a gidan Yahweh mai runduna, Allahnsu
\v 15 a rana ta ashirin da hudu ta watan shida, a shekara ta biyu ta mulkin sarki Dariyos.
\s5
\c 2
\cl Sura 2
\p
\v 1 A wata na bakwai ranar ashirin da ɗaya a watan, maganar Yahweh ta zo ta hannun annabi Haggai, cewa,
\v 2 "Yi magana da gwamnan Yahuda, Zerubabel ɗan Shiltiyel, da babban firist Yoshuwa ɗan Yehozadak, da dukkan mutane da aka rage. Ka ce,
\s5
\v 3 "Wa ya rage a cikinku wanda ya ga wannan gida da darajarsa ta dã? Ya ya ku ka ganshi a yanzu? Shin kamar ba kome ya ke a idanunku ba?
\v 4 Yanzu, sai ka yi ƙarfin hali, Zerubabel! - wannan furcin Yahweh ne, kai ma Yoshuwa ɗan Yehozadak babban firist sai ku yi ƙarfin hali, dukkan mutanen cikin ƙasar! - wannan furcin Yahweh ne, kuma ku yi aiki, domin ina tare da ku! - wannan furcin Yahweh mai runduna ne.
\v 5 Wannan shi ne alƙawarin da na yi da ku sa'ad da kuka fito daga ƙasar Masar, kuma Ruhuna na tare da ku. Kada ku ji tsoro!
\s5
\v 6 Domin Yahweh mai runduna ya faɗi wannan: Ba da jimawa ba zan girgiza sammai da ƙasa, da teku da duk abin da ke a busarshiyar ƙasa!
\v 7 Zan kuma girgiza kowacce al'umma, kuma kowacce al'umma za ta kawo abubuwa ma su daraja a gare ni, kuma zan cika wannan gidan da ɗaukaka, in ji Yahweh mai runduna.
\s5
\v 8 Azurfa da zinariya nawa ne! - wannan furcin Yahweh mai runduna ne.
\v 9 Ɗaukakar wannan gidan ta zama da girma a nan gaba fiye da farkonsa, inji Yahweh mai runduna, zan ba da salama ga wannan wuri! - wannan furcin Yahweh mai runduna ne."
\s5
\v 10 A rana ta ashirin da hudu ga watan tara a shekara ta biyu ta Dariyos, maganar Yahweh ta zo ga annabi Haggai cewa,
\v 11 "Yahweh mai runduna ya faɗi wannan: A tambayi firistoci a kan shari'a, a ce,
\v 12 "Idan mutum ya ɗauki nama da aka keɓe don Yahweh a rigarsa, sa'an nan ta taɓa gurasa, ko miya, ko ruwan inabi ko mai, ko kowanne irin abinci, ko wannan zai sa abin ya tsarkaka?" Firistoci suka amsa suka ce, "A'a."
\s5
\v 13 Sai Haggai yace, "Idan wani wanda ya ƙazantu ta wurin taɓa gawa, daga cikin waɗannan, sun zama ƙazantattu? Sai firistoci suka amsa suka ce, "I sun ƙazantu.
\v 14 Sai Haggai ya amsa yace, "Haka ya ke da mutane da al'umma da ke gabana! - wannan furcin Yahweh ne - haka ya ke game da dukkan abin da suke yi da hannuwansu. Da kuma abin da suke miƙawa a gare ni marar tsarki ne!
\s5
\v 15 To yanzu, sai ku yi tunani a cikin lamirinku a kan abin da ya wuce har zuwa wannan rana. Kafin a ɗora dutse a kan dutse na haikalin Yahweh,
\v 16 yaya ya ke? Lokacin da ku ka zo tarin da aka auna maku mudu ashirin na hatsi, sai aka iske mudu goma kaɗai; idan kuma kun zo wurin matsar ruwan inabi don a ɗebo mudu hamsin, sai aka tarar da mudu ashirin kawai.
\v 17 Na aika maku da bala'i a aikin hannuwanku ta wurin darɓa da raɓa amma duk da haka ba ku komo wurina ba - wannan furcin Yahweh ne.
\s5
\v 18 Lura tun daga wannan rana zuwa gaba, daga rana ta ashirin da huɗu ga watan tara, tun daga ranar da aka aza harsashin ginin haikalin Yahweh. Ku lura da shi!
\v 19 Akwai sauran iri a rumbun? Inabin da itacen ɓauren, da ruman, da itacen zaitun ba su bada amfani ba! Amma daga wannan rana zan albarkace ku!"
\s5
\v 20 Sai maganar Yahweh ta zo a karo na biyu ga Haggai a rana ta ashirin da huɗu ga watan ya ce,
\v 21 "Yi magana da gwamnan Yahuda, Zerubabel, ka ce, 'Zan girgiza sammai da ƙasa.
\v 22 Zan kuma hamɓare kursiyin mulkoki in kuma lalata ƙarfin mulkokin al'ummai! Zan kuma hamɓare karusai da mahayansu; dawakai da mahayansu zasu faɗi ƙasa, kowanne saboda takobin ɗan'uwansa.
\s5
\v 23 A wannan rana - wannan furcin Yahweh mai runduna ne - Zan ɗauke ka, Zerubabel ɗan Shiltiyel, bawana - wannan furcin Yahweh ne. Zan mai da kai kamar zoben hatimi, gama na zaɓe ka!' - wannan furcin Yahweh mai runduna ne!"