ha_ulb/36-ZEP.usfm

118 lines
8.3 KiB
Plaintext
Raw Permalink Blame History

This file contains invisible Unicode characters

This file contains invisible Unicode characters that are indistinguishable to humans but may be processed differently by a computer. If you think that this is intentional, you can safely ignore this warning. Use the Escape button to reveal them.

\id ZEP
\ide UTF-8
\h Littafin Zafaniya
\toc1 Littafin Zafaniya
\toc2 Littafin Zafaniya
\toc3 zep
\mt Littafin Zafaniya
\s5
\c 1
\cl Sura 1
\p
\v 1 Wannan maganar Yahweh ce da ta zo ga Zafaniya ɗan Kushi ɗan Gedaliya ɗan Amariya ɗan Hezekiya, a kwanakin Yosiya ɗan Amon, sarkin Yahuda.
\v 2 "Zan hallakar da kome da kome daga doron duniya - wannan furcin Yahweh ne.
\v 3 Zan hallakar da mutum da dabba; Zan hallakar da tsuntsayen sammai da kuma kifayen teku, rusasssun wurare tare da miyagu. Domin zan datse mutum daga sararin duniya - wannan furcin Yahweh ne.
\s5
\v 4 Zan miƙa hannuna kan Yahuda da dukkan mazaunan Yerusalem. Zan datse kowanne ragowar Ba'al daga wannan wurin da kuma sunayen masu bautar gumaka daga cikin firistoci,
\v 5 mutanen da a saman gidaje suke bautawa hallitun sammai, da mutanen da ke sujada da rantsuwa ga Yahweh amma kuma suna rantsuwa ta wurin sarkinsu.
\v 6 Zan kuma datse waɗanda suka juye baya daga bin Yahweh, waɗanda basu neman Yahweh basu kuma neman bishewarsa."
\s5
\v 7 Ku yi shiru a gaban Ubangiji Yahweh! Gama ranar Yahweh ta kusato; Yahweh ya shirya hadaya ya kuma keɓe baƙinsa.
\v 8 "Zai zama kuma a ranar hadayar Yahweh, zan hori hakimai da 'ya'yan sarakuna, da duk wanda ke sanye da baƙin tufafi.
\v 9 A ranan nan zan hukunta masu tsallake dankarin ƙofa, masu cika gidan shugabansu da ta'addanci da yaudara.
\s5
\v 10 Haka zai zama a ranar nan - wannan furcin Yahweh ne - lallai za a ji kukan baƙinciki daga Kofar Kifi, da ƙarar kuka daga Gundumar Biyu, da gagarumar ƙarar farfashewa daga tuddai.
\v 11 Kuyi kuka da ƙarfi, ku mazaunan Gundumar Kasuwa, gama za a rugurguje dukkan fatake; za a datse dukkan masu awon azurfa.
\s5
\v 12 Zai zama a gabatowar lokacin nan ne zan binciki Yerusalem da fitilu in kuma hukunta mutanen da suka kafu a kan ruwan inabinsu suka ce a zuciyarsu, 'Yahweh ba zai yi kome ba, ko nagari ko mugu.'
\v 13 Dukiyarsu zata zama ganima, kuma gidajensu za a maida su kufai da aka yi watsi da shi! Zasu gina gidaje amma baza su zauna a cikinsu ba, zasu dasa gargunan inabi amma baza su sha ruwansu ba.
\s5
\v 14 Babbar ranar Yahweh ta yi kusa, tayi kuma kurkusa da sauri! Ƙarar ranar Yahweh zata zama kukan mayaƙi na ɓacin rai!
\v 15 Ranar nan zata zama ranar tsananin fushi, ranar damuwa da baƙinciki, ranar baƙin hadari da rushewa, ranar duhu da baƙin ƙunci, ranar giza-gizai da baƙin duhu.
\v 16 Zata zama ranar hura kakaoki da ƙararrawa gãba da ƙayatattun birane masu manya manyan wuraren ɓuya da ganuwoyi.
\s5
\v 17 Gama zan kawo ƙunci ga mutane, saboda suyi tafiya kamar makafin mutane tunda sun yiwa Yahweh zunubi. Za a zubar da jininsu kamar ƙura, a kuma cire kayan cikinsu kamar kashin dabba.
\v 18 A ranar hasalar Yahweh zinariyarsu ko azurfarsu ba zasu iya kuɓutar dasu ba. A cikin wutar kishinsa dukkan duniya zata hallaka, gama zai kawo cikakken mummunan ƙarshen dukkan mazaunan duniya."
\s5
\c 2
\cl Sura 2
\p
\v 1 Ku jero kanku tare ku taru, al'umma marar kunya -
\v 2 kafin ranar aiwatar da dokokin kuma waccan ranar ta wuce kamar ƙaiƙayi, kafin zafin fushin hasalar Yahweh ta auko muku, kafin ranar hasalar Yahweh ta zo kanku.
\v 3 Ku nemi Yahweh, ku mutane masu tawali'u da biyayya ga dokokinsa! ku nemi adalci Ku nemi tawali'u, ko wataƙila a yi maku kariya a ranar hasalar Yahweh.
\s5
\v 4 Gama za a yashe da Gaza, kuma Ashkelon zata zama rusasshiya. Zasu kori Ashdod da rana, kuma zasu tunɓuke Ekron!
\v 5 Kaiton mazaunan gaɓar teku, al'ummar Kiritiyawa! Yahweh ya yi magana gãba da ku, Kan'ana, ƙasar Filistiyawa. Zan hallakar dake har sai ba mazaunan da suka ragu.
\s5
\v 6 Yankin gaɓar teku zai zama saurar makiyaya da makwantar dabbobi. Yankin gaɓar zai zama na ragowar mutanen gidan Yahuda, waɗanda zasu yi kiwon garkensu a wurin.
\v 7 Da yamma mutanensu zasu kwanta a gidajen Ashkelon, gama Yahweh Allahnsu zai lura da su ya kuma mayar masu da mallakarsu.
\s5
\v 8 Na ji cakunar Mowab da wulaƙancin mutanen Amon sa'ad da suke cakunar mutanena suna ci masu kan iyaka.
\v 9 Don haka na rantse da kaina - wannan ne furcin Yahweh mai runduna, Allah na Isra'ila, - Mowab zai zama kamar Saduma, mutanen Amon kuma kamar Gomora; wurin ciyayi masu dafi da ramin gishiri da aka yi watsi da shi har abada. Amma ragowar mutanena zasu washe su, ragowar al'ummata kuma zasu mallake su."
\s5
\v 10 Wannan zai faru da Mowab da Amon saboda girman kansu, tunda suka cakuni suka kuma yi ba'a ga mutanen Yahweh mai runduna.
\v 11 Sa'an nan zasu ji tsoron Yahweh, don zai cakuni dukkan allolin duniya. Kowannensu zai yi masa sujada, kowanne daga wurinsa, daga kowacce gaɓar teku.
\s5
\v 12 Ku Kushiyawa kuma za a soke ku da takobina,
\v 13 Hannun Allah kuma zai kawo hari ga arewa ya hallaka Asiriya, don Nineba zata zama rusasshen wurin da aka watsar, busshiya kuma kamar hamada.
\v 14 Sai garkuna su kasance kwance a nan, kowacce dabba ta kowacce al'umma, mujiyar hamada da mujiya mai tsuwwa ma zasu huta a samman ginshiƙanta. Za a yi waƙoƙin kira daga tagogi; Juji zai kasance a bakin ƙofofin; sassaƙaƙƙun ginshiƙanta na sidar za a bayyana su.
\s5
\v 15 Wannan ne maɗaukakin birnin da ya zauna cikin rashin tsoro, da yace a zuciyarsa," Ni ne kuma ba wanda ya kai ni." To Yaya ya zama mafi muni, wurin da dabbobin jeji ke kwance ciki. Duk wanda ya wuce ta wurinsa zai yi tsaki ya kaɗa kai.
\s5
\c 3
\cl Sura 3
\p
\v 1 Kaiton ki birni mai tayarwa! Birni mai ta'addanci ya ƙazantu.
\v 2 Bata saurari muryar Allah ba, ko ta karɓi gyara daga Yahweh. Bata dogara ga Yahweh ba kuma ba zata kusanci Allahnta ba.
\s5
\v 3 Sarakunanta zakuna ne masu ruri a tsakiyarta. Alƙalanta kyarketan yamma ne da basa barin abin yin tuƙa da safe.
\v 4 Annabawanta marasa biyayya ne masu cin amana. Firistocinta sun wulaƙanta abin da ke mai tsarki kuma sun yi ta'addanci ga shari'a.
\s5
\v 5 Yahweh adali ne a cikinta. Ba zai yi kuskure ba. Daga safiya zuwa safiya zai aiwatar da adalci! Ba zai ɓoyu ba cikin haske, duk da haka mutane marasa adalci basu san kunya ba.
\s5
\v 6 Na hallakar da al'ummai; an lalatar da kagarorinsu. Na mai da titunansu kufai, don kar kowa ya bi kan su. An hallakar da biranensu har babu mutumin dake zaune cikinsu.
\v 7 Na ce, 'Hakika zaku ji tsoro na. Ku karɓi gyara don kada a datse ku daga gidajenku ta wurin dukkan abubuwan da na shirya in yi maku.' Amma suna ƙagara su fara kowacce safiya da lalata ayyukansu.
\s5
\v 8 Saboda haka ku jira ni - wannan furcin Yahweh ne. Har sai ranar da zan tashi domin ƙwace wahalallun. Gama ƙudurina shi ne in tara al'ummai, in taro masarautu, in kuma zuba masu fushina-dukkan hasalata mai zafi; domin a cikin wutar kishina za a cinye dukkan duniya.
\s5
\v 9 Amma zan bada leɓuna masu tsarki ga mutanen, a kira dukkan su cikin sunan Yahweh su bauta mani suna tsaye kafaɗa da kafaɗa.
\v 10 Daga ƙetaren kogin Kush masu yi mani sujada - mutanena dake warwatse - zasu kawo baye-bayen dake nawa.
\v 11 A ranan nan baza ku kunyata ba game da dukkan abubuwan da kuka yi mani. Tun da a wannan lokaci zan kawar da waɗanda suka yi bikin girman kanku daga cikinku, saboda kuma baza ku ƙara yin rashin hankali ba a bisa dutsena mai tsarki.
\s5
\v 12 Amma zan bar ku ƙaskantattu matalautan mutane, zaku kuma fake a cikin sunan Yahweh.
\v 13 Ragowar Isra'ila kuma baza su ƙara aikata rashin adalci ba ko su faɗi ƙarairayi ko kuma a sami yaudara a bakin su ba; saboda haka zasu yi kiwo su kwanta, babu kuma wanda zaya tsoratar dasu."
\s5
\v 14 Yi waƙa 'ɗiyar Sihiyona! Yi ihu, Isra'ila. Yi murna da farinciki da dukkan zuciyarki, ɗiyar Yerusalem.
\v 15 Yahweh ya ɗauke hukuncinki; Ya kori maƙiyanki! Yahweh shi ne sarkin Isra'ila a tsakiyarku. Baza ki ƙara jin tsoron mugunta ba!
\v 16 A ranar nan zasu cewa Yerusalem, "Kada ki ji tsoro, Sihiyona. Kada ki bari hannuwanki suyi sanyi.
\s5
\v 17 Yahweh Allahnku yana tsakiyarku, mai ƙarfin nan da zai cece ku. Zai ji daɗin ku da farinciki kuma zai yi shuru a kanku cikin ƙaunarsa. Zai yi murna a kanku kuma zai yi sowa ta farinciki a kanku,
\v 18 Zan tattara waɗanda ke ɓacin, waɗanda baza su iya kasancewa a zaɓaɓɓun bukukuwa ba, domin haka baza ku ƙara jin kunya dominsa ba.
\s5
\v 19 Duba, Ina gab da horon masu tsananta maku. A lokacin nan, zan ƙwato guragu in tattaro waɗanda aka watsar. Zan maishe su kamar yabo, zan musanya kunyarsu zuwa sanannu a dukkan duniya.
\v 20 A lokacin nan zan bi daku; a lokacin nan zan tara ku tare. Zan sa dukkan al'umman duniya su girmama su kuma yabe ku, lokacin kuka gana dawo da ku," inji Yahweh.