ha_ulb/35-HAB.usfm

131 lines
8.0 KiB
Plaintext

\id HAB
\ide UTF-8
\h Littafin Habakuk
\toc1 Littafin Habakuk
\toc2 Littafin Habakuk
\toc3 hab
\mt Littafin Habakuk
\s5
\c 1
\cl Sura 1
\p
\v 1 Saƙon da annabi Habakuk ya karɓa,
\v 2 "Yahweh, har yaushe zan yi kukan neman taimako, ba za ka ji ni ba? Na yi kuka gareka cikin 'husuma'! amma ba za ka cece ni ba.
\s5
\v 3 Donme kake bari na in kalli mugunta, in kuma dubi rashin gaskiya? Hallaka da tashin hankali na gabana; akwai jayayya, kuma gardama ta taso.
\v 4 Saboda haka shari'a ta yi rauni, adalci kuma bai ɗore ba ko da na ɗan lokaci. Domin muguye sun kewaye masu adalci; shi yasa shari'a ta karkace." Yahweh ya amsa wa Habakuk.
\s5
\v 5 Ka dubi al'ummai ka bincike su; ka yi mamaki da al'ajibi! Domin lallai na kusa in yi wani abu a kwanakin ka da ba za ka gaskata ba idan an faɗa maka.
\v 6 Ka duba! Na kusa ta da Kaldiyawa - waɗannan al'ummai - masu zafin rai da kuma garaje - zasu ratsa dukkan faɗin ƙasar, su ƙwace wurare da ba nasu ba.
\v 7 Masu ban razana ne da kuma ban tsoro; hukunci da darajassu daga gare su suke fitowa.
\s5
\v 8 Dawakansu sun fi damisa gudu, sun fi kyarketan maraice sauri. Dawakan su su na tattakawa, mahayansu sun zo daga nesa sosai - Su kan tashi kamar gaggafar da ke niyyar ci.
\v 9 Duk sun zo domin husuma; rundunarsu sukan tafi kamar iskar hamada, sukan tara bayi kamar yashi.
\s5
\v 10 Suna yi wa sarakuna ba'a, masu mulki kuma abin ba'a ne a gare su. Suna ma duk kagara dariya, domin sukan tula ƙasa su hau su washe su.
\v 11 Sa'an nan iska za ta buga mugayen mutane ta wuce da sauri, waɗanda ƙarfinsu allahnsu ne." Habakuk ya sake tambayar Yahweh
\s5
\v 12 "Kai ba tun fil'azal ka ke ba, Yahweh Allahna, Mai Tsarkin nan? Ba za mu mutu ba. Yahweh ya ƙaddara su ga hukunci, kai kuma, Dutse, ka kafa su domin gyara.
\s5
\v 13 Idanuwanka masu tsarki ne ba za su duba mugunta ba, ba za ka kuma dubi mugun aiki da tagomashi ba; to don me kake duban masu cin amana da tagomashi? Don me ka yi shuru sa'ad da mugaye suke haɗiye waɗanda suka fi su adalci?
\v 14 Ka maida mutane kamar kifi a teku, kamar abubuwa masu rarrafe da basu da shugaba.
\s5
\v 15 Ya kan kawo su dukka da ƙugiyar kamun kifi; yakan ja mutane a tarun kifi su tara su a tãrunsu. Wannan ne ya sa suke murna suna sowa mai yawa.
\v 16 Shi ya sa suke miƙa hadayu ga tarun kama kifinsu suna ƙona wa tarunsu turare, domin dabbobi masu ƙiba ne rabonsu, nama mai kitse ne abincinsu.
\v 17 Saboda wannan ne zasu juye tarun kama kifinsu su ci gaba da yanka al'ummai, ba jin tausayi?"
\s5
\c 2
\cl Sura 2
\p
\v 1 Zan tsaya wurin tsarona in kuma tsaya kan hasumiya, in duba da kyau in ji abin da dai zai faɗi mani da yadda zan amsa masa game da ƙarata.
\s5
\v 2 Yahweh ya amsa mani ya ce, "Ka rubuta wannan ruyar, ka rubuta ta da kyau a kan alluna domin duk wanda ke karanta su ya gudu.
\v 3 Domin ruyar lokacinta ya na gaba a ƙarshe lallai za ta cika ba zata fasa ba. Ko da ta yi jinkiri, ku jira. Tabbas zata zo ba za ta yi jinkiri ba.
\s5
\v 4 Duba! Shi wanda sha'awace sha'awacensa ba dai-dai suke a cikinsa ba hurarra ne. Amma adali ta wurin bangaskiyarsa zai rayu.
\v 5 Gama ruwan inabi abin yaudara ne ga mutum mai fahariya domin kada ya kiyaye, amma ya yawaita marmarinsa, kamar kabari, kuma kamar mutuwa, ba ya ƙoshi. Ya kuma tattara wa kansa kowacce ƙasa ya kuma tattaro wa kansa dukkan mutane.
\s5
\v 6 Ashe ko waɗannan ba zasu sa a ƙirƙiro masa maganganun reni da waƙa da zanbo suna cewa, 'Kaiton wanda yake ƙarawa kansa abin da ba nasa ba! Har yaushe zaka yi ta ƙara wa kanka nauyin al'ƙawuran da ka ɗauka?'
\v 7 Masu cizonka ba zasu tashi farad ɗaya ba, su da ke tsoratar da kai sun farka? Za ka zama ganima a gare su.
\v 8 Saboda ka washe mutane da yawa, dukkan sauran al'ummai za su washe ka. Saboda ka zubar da jinin mutane tare da tashin hankali a ƙasa, da birane da duk waɗanda ke zaune a cikinsu.
\s5
\v 9 'Kaitonsa mai cin ƙazamar riba domin gidansa, yakan gina sheƙarsa a sama domin ya tsare kansa daga hanun mugunta.'
\v 10 Ka jawo wa gidanka kunya ta wurin dạtse mutane da yawa, ka kuma yi wa kanka zunubi.
\v 11 Gama daga cikin katanga duwatsu zasu tada murya, katako kuma daga cikin itatuwan jinka zai amsa masu,
\s5
\v 12 'Kaiton wanda ya gina birni da jini, da wanda ya kafa gari da mugunta.'
\v 13 Ashe ba daga Yahweh mai runduna ba ne mutane ke wahala domin su sami wuta, sauran ƙasashe kuma suna gajiyar da kansu domin abin wofi?
\v 14 Har yanzu ƙasar zata cika da sanin darajar ɗaukakar Yahweh, kamar yadda ruwaye ke rufe teku.
\s5
\v 15 'Kaiton wanda ke tilasta maƙwabcinsa ya sha, ka na nuna fushinka, kana kuwa sa su bugu, domin ka dubi tsiraicinsu.'
\v 16 Maimakon ɗaukaka za ka cika da kunya. Yanzu lokacinka ne! Kai ma ka sha zaka kuma bayyana tsiraicinka. Ƙoƙon hannun dama na Yahweh zai juyo gare ka, kunya kuma zata rufe darajarka.
\s5
\v 17 Tashin hankalin da aka yi wa Lebanon zai komo maka, hallakar dabbobi kuma zata tsoratar da kai. Domin ka zubar da jinin mutane, ka aikata tashin hankali gãba da ƙasa, da birane, da waɗanda ke zaune a cikinsu.
\s5
\v 18 Ina amfanin sassaƙaƙƙiyar siffa a gare ka? Ko gare shi wanda ya sassaƙa ta, gunki na zubi, mai koyar da ƙarairayi; gama ya na sa dogararsa ga aikin hannuwansa sa'ad da ya ke yin waɗannan alloli bebaye.
\v 19 'Kaiton wanda ke ce wa itace, 'Ka farka!' Ko ya ce wa beben dutse, 'Ka tashi!' Waɗannan abubuwa suna koyarwa ne? Duba, an dalaye su da zinariya da azurfa amma ba numfashi ko kaɗan a cikinsa.
\v 20 Amma Yahweh yana cikin haikalinsa mai-tsarki! Ku yi shiru dukkan ƙasa a gabansa."
\s5
\c 3
\cl Sura 3
\p
\v 1 Addu'ar annabi Habakuk a waƙance:
\v 2 Yahweh na ji labarinka, kuma na tsorata. Yahweh, ka farfaɗo da aikinka a cikin waɗannan lokatai; a cikin waɗannan lokatai ka bayyana shi; ka tuna da yin tausayi cikin fushinka.
\s5
\v 3 Allah ya zo daga Teman, kuma Mai Tsarki daga Dutsen Faran. Selah. Ɗaukakarsa ta rufe sammai, kuma duniya na cike da yabonsa.
\s5
\v 4 Sheƙi biyu na hannunsa na haskakawa kamar walƙiya, inda ƙarfinsa yake a ɓoye.
\v 5 Cuta mai hallakarwa ta tafi a gabansa, annoba kuma ta biyo sawunsa.
\s5
\v 6 Ya tsaya ya auna duniya; ya duba kuma ya girgiza al'ummai. Harma daɗaɗɗun duwatsu suka rugurguje, madawwaman tsaunuka kuma suka rusuna ƙasa. Tafarkinsa madawwami ne.
\s5
\v 7 Na ga runfunan Kushan cikin ƙunci, kuma bargunan runfunan cikin ƙasar Midiyan suna raurawa.
\v 8 Yahweh ya fusata da kogunan ne? fushinka a kan kogunan ne, ko hasalarka kan teku ne, da ka yi sukuwa bisa dawakanka da karusanka masu nasara?
\s5
\v 9 Kã fito da bãkanka a ɗane; kạ sa kibiyoyinka ga băkanka! Selah. Kạ raba duniya da koguna.
\v 10 Duwatsu sun gan ka sun murɗe cikin zafi. Ambaliyar ruwa ta bi ta kansu; Teku mai zurfi ya yi ruri. Ya yi tsalle da raƙuman ruwansa.
\s5
\v 11 Rana da wata suka tsaya cik can sama wurarensu masu nisa suka gudu daga hasken kibiyoyinka, daga kuma hasken walƙiyar sheƙin mashinka.
\v 12 Ka tattaka duniya da zafin fushi. A cikin fushi ka sussuke al'ummai.
\s5
\v 13 Ka fita domin ceton mutanenka, domin ceton zaɓaɓɓenka. Ka rugurguza kan gidan mai mugunta domin a kware shi daga ƙasa har zuwa wuyansa. Selah.
\s5
\v 14 Da kibiyoyinsa ka soke kan mayaƙansa tun da sun taho kamar hadari domin su watsar da mu, marmarinsu kamar masu lanƙwame matalauta a ɓoyayyen wuri ne.
\v 15 Ka yi tafiya zuwa ƙetaren teku da dawakanka, ka kuma tattara manyan ruwaye.
\s5
\v 16 Na ji, kuma can cikin gaɓoɓina na yi rawar jiki! Da jin ƙarar leɓunana sun girgiza. Ruɓewa ta shigo cikin ƙasusuwana, a cikina ina rawar jiki yayin da nake jira shiru domin ranar ƙunci da zata zo a kan mutanen da suka mamayemu.
\s5
\v 17 Koda itacen ɓaure bai yi toho ba kuma inabi bai ba da 'ya'ya ba; kuma itacen zaitun bai ba da amfani mai kyau ba kuma gonaki basu ba da abinci ba; koda a ce garke ya tsinke babu shanu a maɗauri, ga abin da zan yi.
\s5
\v 18 Duk da haka, zan yi farinciki cikin Yahweh. Zan cika da murna saboda Allahn cetona.
\v 19 Ubangiji Yahweh shi ne ƙarfina ya kuma maida sawayena kamar na barewa. Yana sa in tafi gaba bisa wurarena na ɗaukaka. - Ga shugaban mawaƙa, bisa kayan kaɗe-kaɗena masu tsarkiya.