ha_ulb/34-NAM.usfm

114 lines
7.1 KiB
Plaintext

\id NAM
\ide UTF-8
\h Littafin Nahum
\toc1 Littafin Nahum
\toc2 Littafin Nahum
\toc3 nam
\mt Littafin Nahum
\s5
\c 1
\cl Sura 1
\p
\v 1 Furci game da Nineba. Littafin wahayin Nahum, mutumin Elkosh.
\s5
\v 2 Yahweh Allah Mai kishi ne da sakayya; Yahweh mai sakayya ne da fushi mai zafi; Yahweh na ɗaukar fansa a kan abokan gãbarsa, kuma yana ci gaba da fushinsa a bisa maƙiyansa.
\v 3 Yahweh na da jinkirin fushi da iko mai girma; ba zai ƙyale miyagu ba hukunci ba. Yahweh na shirya hanyarsa a cikin guguwa da hadari, gizagizai kuma ya maishe su ƙurar tafin sawayensa.
\s5
\v 4 Yana tsauta wa teku ya kuma busar da ita; ya busar da dukkan koguna. Bashan ta yi rauni, haka kuma Karmel; furannin Lebanon sun yi yaushi.
\v 5 Duwatsu suna girgiza a gabansa, tuddai kuma suna na narkewa; duniya tana rushewa a gabansa, hakika, dukkan duniya da mazaunanta.
\s5
\v 6 Wane ne zai iya tsayawa a gaban hasalarsa? Wane ne zai iya tsayayya da zafin fushinsa? Hasalarsa na zubowa kamar wuta, kuma yana farfasa duwatsu.
\s5
\v 7 Yahweh nagari ne, mafaka ne mai ƙarfi a ranar masifa; mai aminci ne kuma ga dukkan masu fakewa a cikinsa.
\v 8 Amma zai hallakar da maƙiyansa kakaf da babbar ambaliya; zai kora su can cikin duhu.
\s5
\v 9 Ku mutane mene ne ku ke shiryawa gãba da Yahweh? Zai kawo ƙarshensa dukka; Masifa ba za ta sake tasowa karo na biyu ba.
\v 10 Gama zasu zama a harɗe kamar sarƙaƙiya; abin shansu zai gundure su; wuta zata cinye su sarai kamar busasshiyar ciyawa.
\v 11 Wani ya tashi daga cikin ki, Nineba, wanda ya yi shirin mugunta game da Yahweh, wani wanda ya haɓaka aikin mugunta.
\s5
\v 12 Ga abin da Yahweh ya faɗi, "Ko da suna cike da ƙarfinsu da kuma yawansu, duk da haka za a datse su; jama'arsu za su ƙare sarai. Amma kai, Yahuda; ko da ya ke na wahalshe ka, ba zan ƙara wahalsheka ba.
\v 13 Yanzu zan karya karkiyar mutanen nan daga gare ka; Zan tsinke sarƙoƙinka."
\s5
\v 14 Nineba, Yahweh ya ba da umarni game da ke; "Babu wata sauran zuriyar da za a kira ta da sunanki. Zan datse sassaƙaƙƙun gumaka da kuma gumakan ƙarfe daga gidajen allolinki. Zan haƙa kaburburanki, gama ke abin raini ce."
\s5
\v 15 Duba, a bisa duwatsu, akwai sawayen wani mai kawo labarai masu daɗi, wanda ya ke shelar salama! Yahuda, yi murnar bukukuwanka, ka kuma cika wa'adodinka, gama mugu ba zai ƙara mamaye ka ba, don an datse shi sarai.
\s5
\c 2
\cl Sura 2
\p
\v 1 Shi wanda zai daddatsa ku yana zuwa gãba da ku. Ku tsare ganuwar birnin, ku yi tsaron hanyoyi. Ku ƙarfafa kan ku, ku shirya sojojinku.
\v 2 Don Yahweh zai dawo da darajar Yakubu, kamar darajar Isra'ila, ko da ya ke maharan sun washe su sun kuma ɓaɓɓata rassan kuringar inabinsu.
\s5
\v 3 Garkuwoyin jarumawansa jajaye ne, kuma sojojinsa sun sa jajayen tufafi, ƙarafan karusansu na walƙiya tun ranar da a ka shirya su, kuma suna karkaɗa mãsunsu masu ƙotar katako a iska
\v 4 Karusai na ta yin gudu a tituna suna kai wa suna kawowa a manyan tituna. Suna kama da harsunan wuta, kuma suna gudu kamar walƙiya.
\s5
\v 5 Wanda zai daddatsa ku gutsu-gutsu ya kira jarumawansa, cikin tafiyarsu suna cin karo da juna, su na sauri don su kawo hari a kan ganuwar birnin. An shirya babbar garkuwa don ta kare masu kawo hari.
\s5
\v 6 An buɗe ƙofofin bakin koguna ta ƙarfi da yaji, fadar kuma ta zama kufai.
\v 7 An tuɓe wa Huzzab tufafinta an kuma tafi da ita; bayinta mata suna makoki kamar kurciyoyi, suna bugun ƙirjinsu.
\s5
\v 8 Nineba ta zama kamar tafki mai maguda, tare da mutanenta suna gudu kamar ruwa mai kwarara. Waɗansu na ihu "ku tsaya, ku tsaya", amma ba wanda ya waiga baya.
\v 9 Ku ɗauki ganimar azurfa, ƙu ɗauki ganimar zinariya don bata da iyaka, kan dukkan abubuwa kyawawa masu daraja na Nineba.
\v 10 Nineba ta zama kango da kufai. Zuciyar kowa ta karaya, gwiwoyin kowa na gugar juna, kowa na cikin baƙinciki; fuskokinsu sun yanƙwane.
\s5
\v 11 Yanzu kuma ina kógon zakokin, inda ake ciyar da 'ya'yan zăki, wurin da zãki da zãkanya ke tafiya da 'ya'yansu ba su tsoron komai?
\v 12 Zãki ya yayyaga abin da ya kama don 'ya'yansa, ya murɗe abin da ya kamo wa zãkanyarsa, ya cika kógonsa da waɗanda ya kamo, ya cika raminsa da yagaggen mushen waɗanda ya yayyaga.
\s5
\v 13 "Duba, ina gãba da ku - wannan furcin Yahweh mai runduna ne. Zan ƙone karusanku, a cikin hayaƙi, takobi kuma zai cinye ƙananan zakunanku. Zan datse ganima daga ƙasarku, kuma ba za a ƙara jin muryoyin masu kawo saƙonku ba."
\s5
\c 3
\cl Sura 3
\p
\v 1 Kaiton birni wanda ke cike da jini! Wanda ke cike da ƙarairayi da kayan sata; a kullum waɗanda aka ƙwara suna cikinsa.
\v 2 Ƙarar bulala na cikinsa, da ƙarar karusan yaƙi da haniniyar dawakai da sukuwar karusai.
\s5
\v 3 Akwai mahayan dawakai masu kawo hari, da walƙiyar takubba da ƙyallin mãsu da tarin gawaye da tsibin jukkuna. Gawarwaki ba su da iyaka; maharan sun yi tuntuɓe a kan su.
\v 4 Wannan na faruwa ne saboda mummunar sha'awa ta ayyuka kyakkyawar karuwar, ƙwararriya a maita, mai sayar da al'ummai ta wurin karuwancinta, ta wurin ta kuma mutane na aikata maitanci.
\s5
\v 5 "Duba, ina gãba da ke - wannan furcin Yahweh mai runduna ne - Zan kware zanen ki in sa ki zama tsirara a gaban al'ummai, ki zama abin kunya ga masarautu.
\v 6 Zan kawo ƙazanta a kan ki, in sa ki zama abin reni; zan mayar dake abin kallo.
\v 7 Zai zama dukkan wanda ya dube ki zai koma da baya, ya ce 'Nineba ta rushe; wa zai yi kuka domin ta?' Ina zan sami wanda zai yi maki ta'aziya?"
\s5
\v 8 Nineba, kin fi Tebes ne wadda aka gina ta kusa da Kogin Nilu, wadda ruwaye ke kewaye da ita, wadda kariyarta teku ne, wadda teku ta yi mata dajiya?
\v 9 Kush da Masar ne ƙarfinta, kuma ba shi da iyaka; Fut da Libiya suka yi amana da ita.
\s5
\v 10 Duk da haka an kwashe Tebes, ta tafi bauta; an fyaɗa 'ya'yanta a ƙasa a kan hanyoyi, abokan gabarta sun jefa ƙuru'u a kan manyan mutanenta, kuma an ɗaure ƙarfafan mutanenta da sarƙoƙi.
\v 11 Ke ma za ki bugu, za ki yi ƙoƙarin ɓoyewa ki nemi mafaka daga abokan gãbarki.
\s5
\v 12 Dukkan hasumiyoyinki zasu zama kamar itacen ɓauren da yake da 'ya'yan fari: idan an girjiza su, zasu faɗo a bakin mai cinyewa.
\v 13 Duba, mutanen dake tare dake mata ne; ƙofofinki suna bude ga abokan gãbarki; wuta ta cinye makaranki.
\s5
\v 14 Ki je ki ɗebo ruwa domin za a kewaye ki, ki ƙarawa kagarorinki ƙarfi, ki je wurin magina ki samo yunɓu ki yi tubula.
\v 15 Wuta zata same ki a wurin, takobi zai hallaka ki. Zai cinye ki kamar yadda fãra ta kan cinye komi da komi. Ki maida kanki kamar 'ya'yan fãra, ki yi yawa kamar fãrin da suka yi ƙwari sosai.
\s5
\v 16 Kin riɓanya abokan cinikayyarki da yawa kamar taurarin sammai; amma suna kamar 'ya'yan fãri sukan washe ƙasa su tashi.
\v 17 'Ya'yan sarakunanki suna da yawa kamar fãrin da suka yi girma sosai, jarumawanki kuma na kamar fãrin da suka yi cincirindo a bango lokacin sanyi. Amma idan rana ta yi sai su tashi su tafi wurin da ba'a sani ba.
\s5
\v 18 Sarkin Asiriya, masu tsaronka sun yi barci; masu mulkinka sun kwanta suna hutawa. Mutanenka sun warwatsu a kan duwatsu ba wanda za ya tattarosu.
\v 19 Raunukanka ba zasu warke ba. Raunukanka sun yi zafi sosai. Dukkan wanda ya ji labarinka zai tafa hannu domin murna a kanka. Wane ne ya tserewa muguntarka ta ko yaushe?