ha_ulb/33-MIC.usfm

236 lines
16 KiB
Plaintext

\id MIC
\ide UTF-8
\h Littafin Mika
\toc1 Littafin Mika
\toc2 Littafin Mika
\toc3 mic
\mt Littafin Mika
\s5
\c 1
\cl Sura 1
\p
\v 1 Wannan ita ce maganar Yahweh wadda ta zo wurin Mika, Bamorashtite a cikin kwanakin Yotam, da Ahaz, da Hezekiya, sarakunan Yahuda, abin da ya gani game da Samariya da Yerusalem.
\s5
\v 2 Dukkan jama'a ku saurara, ke duniya ki saurara da dukan abin dake cikinki. Bari Ubangiji Yahweh ya zama shaida a kan ki daga haikalinsa mai tsarki.
\v 3 Duba, Yahweh ya sauko daga kursiyinsa, zai bi ta wurare masu tudu a bisa ƙasa.
\v 4 Duwatsu zasu narke a ƙarƙashinsa, kwarurruka kuma zasu farfashe kamar saƙar zuma a gaban wuta, kamar an zubar da ruwa a kan wuri mai tsauri.
\s5
\v 5 Dukkan wannan saboda tawayen Yakubu ne, kuma saboda zunubin gidan Isra'ila ne. Mene ne dalilin tawayen Yakubu? Ba Samariya ba ce? Mene ne dalilin wurare masu tsawo na Yahuda? Ba Yerusalem ba ce?
\s5
\v 6 "Zan maida Yahuda ta zama kamar kufai kawai kamar wurin dasa itatuwan inabi. Zan tura gininta na duwatsu cikin rami, zan kware harsasanta.
\v 7 Za a farfasa sifofinta, dukkan kyaututtukanta za a ƙone su. Dukkan gumakanta zan rushe su. Gama daga wurin karuwancinta ta tattara su, zasu zama kamar abin da aka biya ta saboda karuwanci."
\s5
\v 8 Domin wannan zan yi makoki in yi kuka, zan fita tsirara ba takalma; zan yi kuka kamar dila, zan yi makoki kamar mujiya.
\v 9 Domin rauninta marar warkewa, domin ta zo Yahuda. Ta kawo ƙofar mutanena, wato Yerusalem.
\v 10 Kada a yi maganar ta a Gat; kada a yi mata kuka. A Bet Lefra na yi birgima a ƙura.
\s5
\v 11 Ki wuce ta mazaunan Shafir, a tsiraice cikin kunya. Mazauna Za'ana basu fito waje ba. Bet Ezel tana makoki saboda an ɗauke kariyarta.
\v 12 Mutanen Marot suna da marmarin jin labari mai daɗi, saboda masifa daga Yahweh ta zo har ƙofofin Yerusalem.
\s5
\v 13 Ku mutanen Lakish ku haɗa karusai na dawaki. Ke, Lakish, ke ce kika zama sanadin zunubin ɗiyar Sihiyona, saboda an sami kurakuran Isra'ila a cikinki.
\v 14 To za ki bada kyauta ta ban kwana ga Morashet Gat; garin Akzib zai ba sarakunan Isra'ila kunya.
\s5
\v 15 Zan sake kawo wanda zai mamaye ku, ku mazaunan Maresha, martabar Isra'ila zata dawo Adullam.
\v 16 Ki aske kanki ki share gashinki saboda 'ya'yan da ki ke jin daɗin su. Ki sa kanki ya yi saiƙo kamar na gaggafa, domin 'ya'yanki za su tafi bauta daga wurinki.
\s5
\c 2
\cl Sura 2
\p
\v 1 Kaiton masu shirya mugunta, ga waɗanda ke shirya mugunta a kan gadajensu. Idan gari ya waye sukan aikata ta domin suna da iko.
\v 2 Sukan yi sha'awar gonaki su kuma ƙwace su; sukan yi sha'awar gidaje su kuma ƙwace su. Suna tsanantawa mutum da gidansa, da kuma abin gãdonsa.
\s5
\v 3 Saboda haka Yahweh yace, "Duba, na kusa kawo bala'i ga wannan kabila, wadda ba zaku cire kanku daga ciki ba. Ba zaku yi tafiya da taƙama ba, gama zaya zama mugun lokaci.
\v 4 A wannan rana abokan gãbarku zasu rera waƙa game da ku, zasu yi makoki da makoki mai zafi. Zasu yi waƙa, 'Mu Isra'ilawa mun hallaka sarai, Yahweh ya canza gundumar mutanena.' Ya ya zaya ɗauke shi daga wurina? Ya bayar da filayanmu ga maciya amana!"'
\v 5 Saboda haka, ku masu arziki baza ku sami zuriyar da za a raba gundumominku a cikin taruwar mutanen Yahweh ba.
\s5
\v 6 "Sun ce, "kada ka yi anabci." "Ba zasu yi anabcin waɗannan abubuwa ba; reni ba zaya zo ba."
\v 7 Ko lallai za a iya faɗin gidan Yakubu, "Ko Ruhun Yahweh ya ji haushi ne?" Ko waɗannan su ne ainihin ayyukansa?" Ko kalmomina ba su yi wani aikin kirki ga kowa ba ne?
\v 8 A makare mutanena suka tashi kamar abokan gãba. Kun tuɓe sutura, da riga, daga masu wucewa ba tare da tsarguwa ba, kamar sojoji suna dawowa daga yaƙi zuwa wurin da suke tsammani lafiyayye ne.
\s5
\v 9 Kun kori matan mutanena daga gidajen da suke jin daɗi, kun ɗauke albarkuna daga wurin 'ya'yansu har abada.
\v 10 Tashi ka tafi, nan ba wurin da za ka iya zama ba ne, saboda rashin tsafta; hallakakke ne sarai.
\v 11 Idan wani ya zo da ruhun ƙarya ya yi ƙarya ya ce, "Zan yi maka anabci a kan ruwan inabi da abin sa maye," zasu ɗauke shi annabi domin wannan jama'a.
\s5
\v 12 Tabbas, zan tattara dukkan ku, Yakubu. Tabbas zan tattara sauran mutanen Isra'ila. Zan kawo su kamar garken tumaki a cikin tsakiyar wurin kiwonsu. Saboda yawan mutanen za a ji ƙara mai ƙarfi.
\v 13 Wanda ya fara ɓalle ƙofa shi ne zai yi masu jagora. Sun ɓalle ƙofa sun fita; sarkinsu zai wuce gabansu. Yahweh zai kasance a gabansu.
\s5
\c 3
\cl Sura 3
\p
\v 1 Na ce, "Yanzu ku saurara, ku shugabannin Yakubu da masu mulki na gidan Isra'ila: Ashe ba dai-dai ba ne a gare ku ku fahimci adalci?
\v 2 Ku da ke ƙin nagarta kuke kuma ƙaunar mugunta? Ku da ke yayyage fatarsu, da namansu daga ƙasusuwansu --
\v 3 ku da ke cin naman mutanena, kun yage fatarsu, kun kakkarya ƙashinsu, kun daddatsa su gunduwa-gunduwa kamar naman da za a sa a tukunya, kamar nama domin dafawa.
\s5
\v 4 Sa'an nan ku shugabanni zaku yi kuka ga Yahweh, shi kuwa ba zai amsa maku ba. Zai ɓoye fuskarsa daga gare ku, da yake kun yi aikin mugunta.
\s5
\v 5 Yahweh ya faɗi haka, "Game da annanbawan da suke ɓatar da mutanena, idan wani ya basu wani abu su ci, sukan yi shelar 'Salama'. Amma ga waɗanda ba su sa komi a bakinsu ba, sai su fara yaƙi da su.
\v 6 Saboda haka zai zama duhu a gare ku, babu ruya domin ku, zai zama duhu sosai har da ba zaku yi duba ba. Rana za ta faɗi a kan annabawa, yini zai yi masu duhu.
\v 7 Masu duba zasu ji kunya, masu sihiri zasu rikice. Dukansu zasu rufe leɓunansu, domin babu amsa daga gare ni."
\s5
\v 8 Amma ni ina cike da iko ta wurin Ruhun Yahweh, kuma ina cike da adalci da ƙarfi, don in furtawa Yakubu kuskurensa, Isra'ila kuma zunubinsa.
\s5
\v 9 Yanzu ku ji wannan, ku shugabanni na gidan Yakubu, da masu mulki na gidan Isra'ila, ku da ke ƙyamar adalci, kuna wulaƙanta kowanne abu mai kyau.
\v 10 Kun gina Sihiyona da jini, Yerusalem kuma da mugunta.
\v 11 Shugabanninku suna hukunci da cin hanci, firistocinku suna koyarwa don a biya su, kuma annabawanku suna dubã saboda kuɗi. Duk da haka kun dogara ga Yahweh kun ce, "Ba Yahweh yana tare da mu ba? Ba masifa da za ta same mu."
\s5
\v 12 Domin haka, saboda ku za a huɗe Sihiyona kamar gona, Yerusalem za ta zama juji, tudun haikali zai zama tsaunin daji.
\s5
\c 4
\cl Sura 4
\p
\v 1 Amma zaya zama a rana ta ƙarshe dutsen gidan Yahweh zaya kafu a bisa sauran duwatsu. Zai ɗaukaka bisa sauran tuddai mutane kuma za su yi tururuwa wurinsa.
\s5
\v 2 Al'ummai da yawa zasu ce, "Ku zo, mu je bisa dutsen Yahweh, zuwa gidan Allah na Yakubu. Zaya koya mana hanyoyinsa, kuma zamu yi tafiya cikin tafarkunsa." Gama daga Sihiyona shari'a zata fito, maganar Yahweh kuma daga Yerusalem.
\v 3 Shi zaya hukunta tsakanin mutane da yawa, ya kuma yanke hukunci a kan mulkoki masu yawan gaske masu nisa kuma. Zasu maida takubbansu su zama garmuna mãsun su kuma su zama lauzuna. Wata al'umma baza ta ɗaga takobi gãba da wata al'umma ba, baza su ƙara koyar da yaƙi ba.
\s5
\v 4 Maimakon haka kowanne mutum zai zauna ƙarƙashin kuringar inabinsa ko ƙarƙashin itacen ɓauransa. Ba wanda zai ƙara basu tsoro, gama bakin Yahweh mai runduna ne ya faɗi.
\v 5 Gama dukkan mutane suna tafiya, kowanne ɗaya cikin sunan allahnsu. Amma mu zamu yi tafiya cikin sunan Yahweh Allahnmu har abada abadin
\s5
\v 6 "A waccan ranar" - wannan furcin Yahweh ne - "Zan tattaro guragu da korarru, da waɗanda na tsanantawa.
\v 7 Zan sa guragun su zama su ne saura, waɗanda a ka kora su zama al'umma mai ƙarfi, ni kuma Yahweh zan yi mulki a bisansu, a kan Dutsen Sihiyona daga yanzu da har abada.
\v 8 Ke fa, hasumiya ta tsaron garke, tsaunin ɗiyar Sihiyona, mallakarki ta dã za ta dawo gare ki, da mulki na ɗiyar Yerusalem.
\s5
\v 9 Yanzu, me yasa kuke ihu da ƙarfi haka? Babu sarki a cikinku ne? Mai shawararku ya mutu ne? Wannan shi ne yasa ciwo ya kama ku kamar mace mai naƙuda?
\v 10 Ki zama da ciwo da naƙuda ta haifuwa, ke ɗiyar Sihiyona, kamar mace mai naƙuda. Gama yanzu ke zaki fita waje daga birnin, ki zauna a waje, kuma ki tafi Babila. A can za a kuɓutar da ke. A can Yahweh zaya kuɓutar da ke daga hannun abokan gãbarki.
\s5
\v 11 Yanzu al'ummai da yawa sun taru gãba da ke; sun ce, 'Bari ta ƙazance; bari idanunmu su yi murna a kan Sihiyona'
\v 12 Basu san tunanin Yahweh ba, basu gane shirye-shiryansa ba, gama ya tara su kamar dammai a masussuka.
\s5
\v 13 Tashi ki yi shiƙa ɗiyar Sihiyona, gama zan maida ƙahonki ya zama ƙarfe, kofatanki kuma su zama jan ƙarfe. Zaku hallaka mutane da yawa kuma zaku miƙa dukiyarsu ta zilama ta zama ta Yahweh, mallakarsu kuma ga Ubangijin dukan duniya."
\s5
\c 5
\cl Sura 5
\p
\v 1 Yanzu ku taru da shirin yaƙi, ɗiyan sojoji; sojoji sun yi sansani sun kewaye birni, zasu bugi alƙalin Isra'ila da sanda a kunci.
\s5
\v 2 Amma ke Betlehem Ba'ifrata, ko da yake ke ƙanƙanuwa ce a cikin dangi Yahuda, wani daga cikinki zaya zo gare ni ya yi mulkin Isra'ila, wanda farkonsa tun daga lokacin dã ne, tun daga can farko.
\v 3 Saboda haka zaya bashe su, har sai wadda ta ke naƙuda ta haifi ɗa, kuma sauran 'yan'uwansa su dawo wurin mutanen Isra'ila.
\s5
\v 4 Zaya tashi ya yi kiwon mutanensa cikin ƙarfin Yahweh, a cikin darajar sunan Yahweh Allahnsa. Zasu kasance, sa'annan shi zaya zama babba har iyakar duniya.
\v 5 Zaya zama salamarmu. Sa'ad da Asiriyawa suka shigo cikin ƙasarmu, sa'ad da suka yi gangami gãba da kagarunmu, sa'an nan zamu tashi gãba da su, makiyaya bakwai da shugabanni takwas a kan mutane.
\s5
\v 6 Zasu kiwaci ƙasar Asiriya da takobi, ƙasar Nimrod kuma a cikin ƙofofinta. Zaya kuɓutar da mu daga Asiriyawa, sa'ad da suka shiga cikin ƙasarmu, sa'ad da suka yi gangami cikin iyakokinmu.
\v 7 Waɗanda suka rage na wajen Yakubu zasu zama cikin tsakiyar mutane da yawa, kamar raɓa daga wurin Yahweh, kamar ruwa a kan ciyawa, wadda ba mutum take jira ba, ba kuma 'ya'yan mutane take jira ba.
\s5
\v 8 Waɗanda suka rage na wajen Yakubu zasu zama a cikin al'ummai, cikin mutane da yawa, kamar zãki a cikin namomin jeji masu yawa, kamar ɗan zaki a cikin garken tumaki. Sa'ad da ya shiga cikinsu zai tattaka su, ya daddatsa su, ba wanda zaya cece su.
\v 9 Za a ɗaga hannunka gãba da abokan gãbarka, zaya kuma hallaka su.
\s5
\v 10 "Haka zaya kasance a wannan rana" - wannan furcin Yahweh ne -- "zan hallakar da dawakanka a gabanka in narkar da karusanka.
\v 11 Zan hallakar da biranen ƙasarka in lalatar da wuraren ɓoyewarka dukka.
\s5
\v 12 Zan hallakar da maita da ke wurinka, baza ka ƙara samun masu duba ba.
\v 13 Zan hallakar da sassaƙaƙƙun sifofinka da ginshiƙai na duwatsu daga wurinka. Baza ka ƙara bautawa aikin hannuwanka ba.
\v 14 Zan tumɓuke ginshiƙan Asherarka daga wurinka, kuma in hallakar da biranenka.
\v 15 Zan ɗauki fansa cikin fushi da hasala a kan al'umman da basu saurara ba."
\s5
\c 6
\cl Sura 6
\p
\v 1 Yanzu ji abin da Yahweh ya faɗi, "Ka tashi ka kai ƙararka ga duwatsu; bari tsaunuka su ji muryarka.
\v 2 Ku ji ƙarar Yahweh, ku duwatsu, da ku ginshiƙan duniya masu juriya. Gama Yahweh yana da shari'a da mutanensa, zai yi faɗa da Isra'ila a kotu."
\s5
\v 3 Mutanena, me na yi ma ku? Ta yaya na gajiyar da ku? Ku faɗi laifin da na yi!
\v 4 Gama na fito da ku daga ƙasar Masar na kuɓutar da ku daga gidan bauta. Na aiki Musa da Haruna da Miriyam zuwa wurinku.
\v 5 Mutanena, ku tuna abin da Balak sarkin Mowab ya ƙulla, da yadda Bala'am ɗan Biyo ya amsa masa sa'ad da kuke tafiya daga Shittim zuwa Gilgal, ta haka za ku san aikin adalci na Yahweh."
\s5
\v 6 Me zan kawo gaban Yahweh, sa'ad da na durƙusa gaban Allah mai girma? Na zo da hadayu na ƙonawa, da ɗan maraƙi bana ɗaya?
\v 7 Yahweh zai yi murna da dubban raguna, ko da dubban rafukan mai? Zan ba da ɗan farina saboda laifina, ɗiyan jikina domin zunubina?
\v 8 Ya dai gaya maka, mutum, abin da ke mai kyau, abin da Yahweh ke nema daga wurinka: Aikin adalci, jinƙai da tafiya cikin tawali'u tare da Allahnka.
\s5
\v 9 Yahweh, yana yin furci da muryarsa zuwa ga birnin - ko yanzu hikima ta san sunanka: "Ku saurari sandar, da wanda ya ajiye ta a wurin.
\v 10 Akwai dukiya a gidajen masu mugunta wannan rashin aminci ne, mudun ƙarya abin ƙyama.
\s5
\v 11 Ko zan lura da mutumin daya yi amfani da ma'auni mara kyau, da bahu wanda nauyinsa na cuta ne?
\v 12 Masu arziki sun zama cike da ta'addanci, mazaunan sun faɗi ƙarairayi, kuma harshensu da bakinsu na cike da ruɗi.
\s5
\v 13 Saboda haka na buge ku da ciwo mai zafi, na mai da ku kango saboda zunubanku.
\v 14 Za ku ci ba za ku ƙoshi ba, yunwarku za ta zauna a cikinku, za ku ajiye kayayyaki amma ba za ku adana su ba, abin da kuka adana zan bayar ga takobi.
\v 15 Za ku yi shuka amma ba za ku yi girbi ba; za ku sawo zaitun amma ba za ku shafe kanku da mai ba; za ku matse kuringar inabi amma ba za ku sha ruwan ba.
\s5
\v 16 Farillan da Omri ya bayar an kiyaye su, haka kuma dukkan abin da gidan Ahab suka yi. Kun yi tafiya bisa ga shawararsu. To haka zan mai da birnin kango, mazauna ciki kuma abin ƙi, ku mazaunan za ku yi ta fama da ba'a a matsayinku na mutanena."
\s5
\c 7
\cl Sura 7
\p
\v 1 Kaito na! Gama a gare ni ya zama kamar an riga an gama girbi na kaka, har ma da kalar abin da ya rage na kuringar inabi a gonaki: Ba sauran 'ya'yan itatuwan da za a samu, babu nunar fari na 'ya'yan ɓaure waɗanda rai na ke so.
\v 2 Babu sauran amintattun mutane a ƙasar, babu sauran na kirki a cikin dukkan 'yan adam. Dukkan su sun yi kwanto domin su zãbar da jini, kowanne ɗayansu yana farautar ɗan'uwansa da tãru.
\s5
\v 3 Hannayensu sun iya yin ɓarna sosai: sarki yana nema a ba shi kuɗi, alƙali yana shirye ya karɓi cin hanci, ƙaƙƙarfan mutum yana gaya wa waɗansu abin da yake so ya samu. Haka suke rigima tare.
\v 4 Mafi kyau a cikinsu kamar laka yake, mafi aminci a cikinsu yana kamar shingen ƙaya. Dãma masu tsaronmu sun yi magana a kan wannan rana, ranar da za a hore ku. Ranar ruɗewarsu ta zo.
\s5
\v 5 Kada ka amince da kowanne maƙwabci, kada ka dogara ga kowanne aboki. Ka yi hankali da abin da za ka faɗi ko ma ga matar da ke kwance a kafaɗunka.
\v 6 Gama ɗa yana rena ubansa, ɗiya kuma tana tayarwa uwatta, suruka tana tayarwa uwar mijinta. Abokan gabar mutum, mutanen gidansa ne.
\s5
\v 7 Amma ni zan duba wajen Yahweh, zan jira ga Allah na cetona, Allahna zai ji ni.
\v 8 Kada ka yi murna a kaina kai maƙiyina, ko na faɗi zan tashi. Sa'ad da na zauna cikin duhu, Yahweh zai zama haske a gare ni.
\s5
\v 9 Saboda na yi wa Yahweh zunubi, zan jure da fushinsa har yayi mani shari'a, yayi mani hukunci. Zai kawo ni cikin haske, zan gan shi yana kuɓutar da ni cikin adalcinsa.
\s5
\v 10 Sa'an nan maƙiyina zai gani, kunya za ta rufe wanda yake ce da ni, "Ina Yahweh Allahnka?" Idanuna zasu gan ta, za a tattake ta kamar taɓo a kan hanyoyi.
\s5
\v 11 Ranar da za ka gina ganuwarka tana zuwa; a ranar nan za a faɗaɗa iyakokinka da nisa ƙwarai.
\v 12 A ranar nan mutanenka zasu zo wurinka daga Asiriya da biranen Masar, daga Masar har zuwa babban Kogi, daga teku zuwa teku, daga dutse zuwa dutse.
\v 13 Waɗancan ƙasashen za a watsar da su saboda mutanen da ke zaune, a wurin yanzu, saboda sakamakon ayyukansu.
\s5
\v 14 Ka yi kiwon mutanenka da sandarka, garke abin gãdonka. Suna zaune su kaɗai a jeji, a tsakiyar fadama. Bari su yi kiwo a Bashan da Giliyad kamar kwanakin dã.
\v 15 Kamar rana da ka fito daga kasar Masar, zan basu mamaki.
\s5
\v 16 Al'ummai zasu gani su ji kunya a kan dukkan ikonsu. Zasu sa hannuwansu a bakinsu, kunnuwansu zasu toshe.
\v 17 Zasu lashi ƙasa kamar macizai, kamar hallittun dake rarrafe a ƙasa. Zasu fito daga cikin kogunansu da tsoro, zasu zo wurinka da tsoro, Yahweh Allahnmu, kuma za su ji tsoro saboda kai.
\s5
\v 18 Wane ne Allah kamar ka, kai da kake ɗauke zunubi, wanda yake ƙetare kurakuran mutanensa da suka rage, abin gãdonsa? Ba ka riƙe fushinka har abada, saboda kana ƙaunar ka nuna mana amincin alƙawarinka.
\s5
\v 19 Za ka sake jin tausayinmu, kuma; za ka take muguntarmu a ƙarƙashin sawayenka. Za ka jefa dukkan zunubanmu cikin zurfin teku.
\v 20 Za ka bada gaskiya ga Yakubu alƙawari da aminci kuma ga Ibrahim, kamar yadda ka rantsewa kakanninmu tun kwanakin dã.