ha_ulb/32-JON.usfm

112 lines
6.8 KiB
Plaintext

\id JON
\ide UTF-8
\h Littafin Yona
\toc1 Littafin Yona
\toc2 Littafin Yona
\toc3 jon
\mt Littafin Yona
\s5
\c 1
\cl Sura 1
\p
\v 1 Maganar Yahweh ta zo ga Yona ɗan Amittai, cewa,
\v 2 "Ka tashi ka tafi Nineba, babban birnin nan, ka yi magana gãba da shi, saboda muguntarsa ta zo gare ni."
\v 3 Amma Yona ya tashi ya gudu daga gaban Yahweh ya tafi Tarshish. Ya tafi Yofa ya sami jirgin da zai tafi Tarshish. Ya biya kuɗin tafiya Tarshish. Domin ya gudu daga fuskar Yahweh.
\s5
\v 4 Amma sai Yahweh ya aika da babbar iska a kan teku wadda ta zama hadari mai ƙarfi ta sa jirgin ya yi ta kaɗawa kamar zai fashe.
\v 5 Sai masu tuƙin jirgin su ka ji tsoro sosai mutanen suka yi ta addu'a kowanne ga allahnsa. Sai suka zubar da kayan da ke cikin jirgin a cikin teku domin su rage nauyin jirgin. Amma Yona yana can cikin ƙarshen jirgi yana barci mai nauyi.
\s5
\v 6 Sai mai tuƙin jirgin ya zo ya same shi yace da shi, "Barci ka ke yi? Tashi! Ka kira ga allahnka! Ko allahnka zai ji ya cece mu daga hallaka."
\v 7 Sai suka ce da junansu, "Ku zo mu jefa ƙuri'a mu gani ko wane ne ya sa muka shiga wannan masifa." Da suka jefa ƙuri'a sai ta faɗa kan Yona.
\s5
\v 8 Sai suka ce da Yona, "In ka yarda ka gaya mana wane ne ya sa wannan masifa ta same mu. Mene ne aikinka, daga ina ka ke? Daga wacce ƙasa ka ke, kai ɗan wacce kabila ne?"
\v 9 Yona yace da su, "Ni Ba'ibrane ne; kuma ina jin tsoron Yahweh, Allah na sama, wanda ya halitta sama da teku da busasshiyar ƙasa."
\v 10 Sai mutanen suka ƙara jin tsoro suka ce da Yona, "Me ka yi kenan?" Sun sani cewa ya gudu ne daga wurin Yahweh, gama ya faɗa masu.
\s5
\v 11 Sai suka ce da Yona, "Me za mu yi maka domin tekun ya kwanta?" Saboda tekun na ƙara yin hauka.
\v 12 Sai Yona yace masu, "Ku ɗauke ni ku jefa cikin tekun. Tekun kuwa zai yi shiru domin ku, gama na sani saboda ni ne wannan babban hadari ya same ku."
\v 13 Amma duk da haka, mutanen suka yi ta ƙoƙari domin su mallako jirgin ya dawo bakin gãɓa, amma suka kasa saboda tekun yana ta ƙara yi masu hauka.
\s5
\v 14 Sai suka yi kuka ga Yahweh suka ce, "Mun roƙe ka, Yahweh, mun roƙe ka, kada ka bari mu hallaka saboda wannan mutum, ya Yahweh, kada ka ɗora alhakin mutuwarsa a kan mu, saboda kai Yahweh ka yi adalci ka kuma yi kamar yadda ya gamshe ka."
\v 15 Sai suka ɗauki Yona suka jefa shi cikin teku sai tekun ya daina hauka.
\v 16 Sai mutanen suka ji tsoron Yahweh ƙwarai da gaske. Suka miƙa hadayu ga Yahweh suka kuma yi alƙawura.
\s5
\v 17 Yahweh kuwa ya shirya wani babban kifi don ya haɗiye Yona, Yona kuma ya kasance a cikin cikin kifi har yini uku da kwana uku.
\s5
\c 2
\cl Sura 2
\p
\v 1 Daga can cikin kifi sai Yona ya yi addu'a ga Yahweh Allahnsa.
\v 2 Ya ce, "Na yi kira ga Yahweh game da ƙuncina ya kuwa amsa mani; daga can cikin Lahira na yi kuka na neman taimako! Ka ji muryata.
\s5
\v 3 Ka jefa ni can cikin ƙarƙashin ƙasa, cikin zurfin tekuna, rigyawa da ambaliya, raƙuman ruwa sun bi ta kaina.
\v 4 Na ce, 'An kore ni daga fuskarka; amma duk da haka zan sake duban haikalinka mai tsarki.'
\s5
\v 5 Ruwaye sun sha kaina har zuwa wuyana; zurfi ya kewaye ni ta ko'ina, rigyawa ta sha kaina.
\v 6 Na shiga ƙarƙashin duwatsu; duniya da makullanta sun rufe ni har abada. Amma duk da haka ka tsamo raina daga rami, Yahweh, Allahna!
\s5
\v 7 Lokacin da raina ya sume a cikina, sai na tuna da Yahweh a cikin raina; sai addu'ata ta zo gare ka, a haikalinka mai tsarki.
\v 8 Waɗanda suka juya ga alloli marasa amfani sukan ƙi amincinka zuwa gare su.
\s5
\v 9 Amma ni zan miƙa maka hadaya da murya ta godiya, zan cikasa abin da na alƙawarta. Daga wurin Yahweh ceto yake zuwa!"
\v 10 Sai Yahweh ya yi magana da kifin, sai kifin ya amayar da Yona a gãɓar tekun.
\s5
\c 3
\cl Sura 3
\p
\v 1 Maganar Yahweh ta zo wurin Yona karo na biyu, cewa,
\v 2 "Ka tashi, ka tafi Nineba, babban birnin nan, ka yi shelar saƙon da na umarce ka ka bayar."
\v 3 Sai Yona ya tashi, ya tafi Nineba ya yi biyayya da maganar Yahweh. Nineba dai birni ne babba, kuma tafiya ce ta kwana uku.
\s5
\v 4 A yini guda Yona ya fara shiga birnin ya yi kira ya ce, "A cikin kwana arba'in za a rushe Nineba."
\v 5 Mutanen Nineba suka gaskata Allah, suka yi shelar yin azumi. Dukkan su suka sanya tsummokara, daga manyansu har ya zuwa ƙananansu.
\s5
\v 6 Nan da nan labari ya kai ga sarkin Nineba. Shi kuwa ya tashi daga kursiyinsa, ya tuɓe alkyabbarsa, ya rufe kansa da tsummokara, ya zauna cikin toka.
\v 7 Sai ya aika ayi shelar cewa, "A cikin Nineba, bisa ga ikon sarki da majalisarsa, kada wani mutum ko dabba, ko garken shanu da tumaki, ko na awaki ya ɗanɗana wani abu. Kada su ci abinci ko su sha ruwa.
\s5
\v 8 Amma sai mutum da dabba su rufa da tsummokara kuma su yi kuka mai ƙarfi zuwa ga Allah. Sai kowanne mutum ya juya daga hanyarsa ta mugunta da kuma ta'addancin dake cikin hannuwansa.
\v 9 Wa ya sani? Ko Allah zai iya yin jinkiri kuma ya canza ra'ayinsa ya kuma juya daga fushinsa mai zafi domin kada mu hallaka."
\s5
\v 10 Allah ya ga abin da suka yi, yadda suka juya daga hanyoyinsu na mugunta. Sai Allah ya canza ra'ayinsa game da hukuncin da ya ce zai zartar a kansu, bai kuma zartar da shi ba.
\s5
\c 4
\cl Sura 4
\p
\v 1 Amma hakan bai yi wa Yona daɗi ba, sai ya ji haushi ƙwarai.
\v 2 Saboda haka, Yona ya yi addu'a ga Yahweh ya ce, "Yahweh, ashe ba abin da na ce ba kenan tun ban baro ƙasata ba? Shi ya sa tun da farko na yi ƙoƙarin gudu zuwa Tarshish - domin na san kai Allah ne mai alheri, mai tausayi, mai jinkirin fushi, cike da aminci, ka kan kuma fasa aiko da bala'i.
\v 3 Saboda haka yanzu, Yahweh, na roƙe ka, ka ɗauke raina daga gare ni, gama ya fiye mani in mutu, da in rayu."
\s5
\v 4 Yahweh yace, "Ya dace da ka yi fushi haka?"
\v 5 Sai Yona ya fita daga birnin ya zauna daga gabas da birnin. Can ya yi rumfa ya kuma zauna a ƙarƙashinta domin ya ga abin da zai faru da birnin.
\s5
\v 6 Yahweh Allah ya shirya wata 'yar itaciya ya sa ta yi girma ta kere Yona, domin ta zama inuwa a saman kansa ta sauƙaƙa ƙuncinsa. Yona kuwa ya yi murna sosai sabo da wannan 'yar itaciyar.
\v 7 Amma Allah ya shirya tsutsa da gari ya waye rana ta ɗaga. Tsutsar kuwa ta kawo hari ga 'yar itaciyar, ta cinye 'yar itaciyar, 'yar itaciyar kuma ta bushe.
\s5
\v 8 Kashegari sa'ad da rana ta fito, Allah ya shirya wata iska daga gabas mai zafin gaske. Ranar kuwa, ta yi zafi matuƙa bisa Yona har ya some. Sai Yona ya gwammace ya mutu. Ya ce wa kansa, "Gara ma in mutu da in rayu."
\v 9 Sai Allah yace wa Yona, "Ya dace da ka yi fushi game da 'yar'itaciyar? Sai Yona yace, "Ya dace da in yi fushi, har ma ga mutuwa."
\s5
\v 10 Yahweh yace, "Ka ji tausayin 'yar itaciyar, wadda ba ka yi aiki a kai ba, ba ka kuma sa ta yi girma ba. 'Yar Itaciyar ta yi girma cikin dare ɗaya ta kuma mutu cikin dare ɗaya.
\v 11 To ashe, Ni, ba zan tausayawa Nineba, wannan babban birni, wanda akwai fiye da mutane dubu ɗari da ashirin, da ba su san bambanci tsakanin hannunsu na dama da hannunsu na hagu ba, da kuma dabbobi masu yawan gaske?"