ha_ulb/29-JOL.usfm

162 lines
10 KiB
Plaintext

\id JOL
\ide UTF-8
\h Littafin Yowel
\toc1 Littafin Yowel
\toc2 Littafin Yowel
\toc3 jol
\mt Littafin Yowel
\s5
\c 1
\cl Sura 1
\p
\v 1 Wannan ita ce maganar Yahweh da ta zo ga Yowel ɗan Fetuwel.
\v 2 Ku ji wannan ku dattawa, ku kuma kasa kunne dukkan ku mazauna ƙasar. Ko wannan ya taɓa faruwa a kwanakinku ko a kwanakin iyayenku?
\v 3 Ku faɗa wa 'ya'yanku labarinsa, 'ya'yanku kuma su fada wa tsara mai zuwa.
\s5
\v 4 Abin da bãbe ya rage fara ta ci; abin da da fara ta bari burdunnuwa ta ci; abin da burdunnuwa ta rage; ganzari ya cinye.
\s5
\v 5 Ku mashaya, ku tashi, ku yi ta kuka! Ku yi ta baƙin ciki, ku dukkan mashayan ruwan inabi, don an datse inabinku mai zaƙi daga gare ku.
\v 6 Don wata al'umma ta zo kan ƙasata, ƙaƙƙarfa mara ƙidayuwa. Haƙoransu haƙoran zãki ne, kuma suna da haƙoran zãkanya.
\v 7 Sun mayar da kuringar inabina abar wofi. Sun yayyage dangar itacen ɓaurena, sun yayyage dangar sun watsar; rassan sun koɗe sun yi fari.
\s5
\v 8 Ku yi makoki kamar amaryar da ke makokin mutuwar angonta.
\v 9 An dena miƙa baikon hatsi da na abin sha daga gidan Yahweh. Firistoci, bayin Yahweh suna makoki.
\v 10 Filaye sun bushe, ƙasa tana makoki saboda an hallakar da hatsi. Sabon ruwan inabi ya ƙare, mai ya kasa.
\s5
\v 11 Ku manoma ku ji kunya, ku yi baƙinciki, hakan nan ku wuraren matse ruwan inabi, saboda alkama da sha'ir. Don abin da aka girbe ya lalace.
\v 12 Inabi sun kaɗe, itatuwan ɓaure kuma sun bushe, itacen ruman, da kuma na dabino, da gawasa duk da sauran itatuwa sun bushe. Don farinciki ya ƙare daga cikin mutane
\s5
\v 13 Ku firistoci ku sa tufafin makoki, ku firistoci ku yi bakin ciki, ku masu hidima a bagadi ku kwanta cikin tufafin makoki har safiya, ku bayin Allahna. Don an hana miƙa baikon hatsi da na abin sha daga gidan Allahnku.
\v 14 Ku yi kira a yi azumi mai tsarki, ku kuma yi kira a yi tattaruwa mai tsarki. Ku tattara dattatawa da dukkan mazaunan ƙasar zuwa gidan Yahweh Allahnku, ku yi kuka ga Yahweh.
\s5
\v 15 Kaito saboda ranar! Gama ranar Yahweh ta ƙarato. Tare da ita akwai hallakarwa daga Mai iko dukka.
\v 16 Ba a ɗauke abinci daga gabanmu ba, an kuma ɗauke farinciki da fara'a daga gidan Allahnmu ba?
\v 17 Iri ya lalace a kofensa, an wulaƙanta hatsi, an banzantar da wuraren ajiya don hatsi ya yanƙwane.
\s5
\v 18 Yaya dabbobi ke nishi! Makiyayan dabbobi kuma ke shan wahala saboda ba wurin kiwo. Hakannan kuma garken tumaki na shan wahala.
\v 19 Yahweh, ina kuka gare ka. Don wuta ta cinye makiyayar dake jeji, harshen wuta kuma ya ƙone bishiyoyin dake cikin filayen.
\v 20 Har da dabbobin jeji suna yi maka kuka, don ƙoramun ruwa sun bushe, wuta kuma ta cinye makiyayar jeji.
\s5
\c 2
\cl Sura 2
\p
\v 1 Ku hura ƙaho a Sihiyona, ku kuma kaɗa kararrawa a kan duwatsuna masu tsarki! Bari dukkan mazaunan ƙasar su gigice don tsoro, Don hakika ranar Yahweh tana tafe, hakika ta kusa.
\v 2 Rana ce ta duhu baƙiƙƙirin, rana ce ta giza-gizai da baƙin duhu. Kamar yadda duhu ke rufe duwatsu, babbar rundunar sojoji tana kusantowa. Ba a taɓa samun soja kamarta ba, ba kuma za a sake samun kamar ta ba, Koma a bayan tsararraki da yawa.
\s5
\v 3 Wuta na cinye duk abin da ke gabanta, bayanta kuma harshen wutar yana ƙuna. ƙasar ta zama kamar gonar Adnin a gabanta, amma a bayanta akwai jejin da ba komai. Ba kuma abin da zai tsira daga gare ta.
\s5
\v 4 Bayyanuwar sojojin kamar ta dawakai ce, kuma su na gudu kamar mahayan dawakai.
\v 5 Suna tsalle da ƙara kamar na masu karusa a kan duwatsu, kamar kuma ƙarar wutar da ke cin tarin yayi, kamar ta Sojoji masu iko dake shirye domin yaƙi.
\s5
\v 6 A gabansu jama'a na cikin ƙunci, dukkan fuskokinsu kuma suka yi suwu.
\v 7 Suna gudu kamar na jarumawa masu iko; suka hau katanga kamar sojoji; suna tafiya a jere kowanne dai-dai a kan sawu, basu kauce matsayinsu ba.
\s5
\v 8 Ba wanda ya tunkuɗe wani a gefe, kowa yana tafiya a gefensa, suka kutsa ta cikin kariyar basu kuma kauce layi ba.
\v 9 Suka ruga kan birnin, suna gudu a kan ganuwa, suka haura cikin gidaje, suka shiga ta tagogi kamar ɓarayi.
\s5
\v 10 Duniya ta girgiza a gabansu, sammai kuma suka firgita, rana da wata sun duhunta, taurari kuma sun dena haskakawa.
\v 11 Sai Yahweh ya tada muryarsa a gaban sojojinsa, don sojojinsa suna da yawa sosai, suna kuma da ƙarfi, waɗanda ke karɓar umarninsa. Don ranar Yahweh tana da girma da kuma ban tsoro sosai. Wa zai iya jure mata?
\s5
\v 12 "Amma ko yanzu ma, "Yahweh yace, "Ku juyo wurina da dukkan zuciyarku. Ku yi azumi da kuka, da makoki."
\v 13 Ku keta zuciyarku ba tufafinku kawai ba, ku komo wurin Yahweh Allahnku. Don shi mai alheri ne da jinƙai, marar saurin fushi kuma ya na cike da alƙawari mai aminci, kuma zai so ya kawar da aiwatar da hukunci.
\s5
\v 14 Wa ya sani? Ko zai juyo ya ji tausayi, ya kuma sa masa albarka, da baiko na hatsi da na abin sha saboda Ubangiji Allahnku?
\s5
\v 15 A hura ƙaho a Sihiyona, a kira ayi azumi mai tsarki, a kuma yi kira ayi tattaruwa mai tsarki.
\v 16 A tattara jama'a don tattaruwa mai tsarki, a tattara dattawa, a tattara 'yan yara da jarirai masu shan nono. Sai anguna su fito daga ɗakunansu, amare kuma daga kagararsu ta amarcinsu.
\s5
\v 17 Sai firistoci bayin Yahweh su yi kuka a tsakanin bagadi da shirayi. Sai su ce, "Ya Yahweh, ka ceci mutanenka, kada kuma ka mai da gãdonka abin ba a, har al'ummai su yi musu ba a. Me ya sa za su faɗa a cikin al'umai cewa, 'Ina Allahnsu?'"
\s5
\v 18 Sai ya yi kishin ƙasarsa, ya kuma ji tausayin mutanensa.
\v 19 Yahweh ya amsa wa mutanensa, "Duba zan aiko maku da hatsi, da sabon ruwan inabi, da mai. Zasu wadace ku, kuma ba zan ƙara mai da ku abin wulaƙanci ba a cikin al'ummai.
\s5
\v 20 Zan kawar da maharan nan na arewa daga gare ku, kuma za ku kore su zuwa yasassun wurare. jagoran sojojinsu zai fuskanci gabashin teku. Bãshinta zai tashi, mumunan warinta kuma zai tashi.' Hakika, ya yi manyan abubuwa.
\s5
\v 21 Ƙasa kada ki tsorata, ki yi murna da farinciki, domin Yahweh zai yi manyan abubuwa.
\v 22 Kada ku ji tsoro, namomin jejin da ke cikin saura, gama tsire-tsiren dake cikin saura zasu tohu, itatuwa zasu bada 'ya'ya, kuma itacen ɓaure da na inabi za su bada "ya'yansu sosai.
\v 23 Mutanen Sihiyona ku yi murna, kuma ku yi farinciki cikin Yahweh Allanhnku. Don zai baku ruwan sama da bazara ya kuma buɗe sakatun sama dominku, ruwan bazara da na koramunku kuma kamar dã.
\s5
\v 24 Masussuka za ta cika da alkama, wurin matsar inabi kuma zai cika da sabon ruwan inabi da mai.
\v 25 "Zan komo maku da shekarun da kuka yi asarar hatsinku wanda fãra ta cinye wato wannan farar mai hallakarwa da na aiko cikinku.
\s5
\v 26 Za ku ci ku ƙoshi sosai, ku yabi sunan Yahweh Allahnku, wanda ya aikata abubuwan al'ajabi a cikinku, kuma ba zan taɓa sake kawo abin kunya akan mutane na ba.
\v 27 Za ku san cewa ina cikin Isra'iila, kuma ni ne Yahweh Allahnku, kuma babu wani sai ni, kuma ba zan ƙara kawo kunya akan mutanena ba.
\s5
\v 28 Bayan wannan kuma zan zubo da Ruhuna ga dukkan mutane, 'ya'yanku maza da mata za su yi anabci. Tsofaffinku zasu yi mafarkai, samarinku kuma zasu ga wahayi.
\v 29 Kuma ga bayi da mata bayi, a waɗancan kwanaki zan zubo musu da Ruhuna.
\s5
\v 30 Zan nuna al'ajabai a sama da kuma a duniya, jini, da wuta, da murtukewar hayaƙi.
\v 31 Rana zata duhunta, wata kuma zai zama jini, kafin babbar ranar nan ta Ubangiji mai ban tsoro ta zo.
\s5
\v 32 Zai zama kuma dukkan wanda ya yi kira ga sunan Yahweh zai tsira. Don a dutsen Sihiyona da kuma a cikin Yerusalem za a sami waɗanda suka tsira, kamar yadda Yahweh ya ce, da kuma cikin waɗanda suka rayu, wato waɗanda Yahweh ya kira.
\s5
\c 3
\cl Sura 3
\p
\v 1 A waɗannan kwanaki da lokatai, sa'ad da na komar da masu zaman talalar Yahuda da Yerusalem,
\v 2 Zan tattara dukkan al'ummai in kuma kawo su kwarin Yehoshafat. A can zan yi masu shari'a, saboda jama'ata da abin gãdona Isra'ila, waɗanda suka warwatsar cikin al'ummai, saboda kuma sun raba ƙasata.
\v 3 Sun kuma jefa ƙuri'a kan mutanena, sun sayar da yaro saboda da karuwa, sun kuma sayar da yarinya saboda ruwan inabi don su sha.
\s5
\v 4 Yanzu don me kuke fushi da ni, ku Taya, da Sidon da dukkan yankin Filistiya? Ko za ku sãka mani? Ko da ma kun sãka mani nan da nan zan komo muku da ramuwarku a kanku.
\v 5 Don kun ɗauke zinariyata da azurfata, kun kuma kawo kayayyakina masu daraja zuwa cikin masujadanku.
\v 6 Kun sayar da mutanen Yahuda da na Yerusalem ga Girkawa, don ku cire su can nesa da ƙasarsu.
\s5
\v 7 Duba, ina gab da in tayar da su, daga inda kuka sayar dasu, ku ne kuma za ku biya kuɗin fansa da kanku.
\v 8 Zan sayar da 'ya'yanku maza da mata ta hannun mutanen Yahuda. Za su sayar da su ga Sabiyawa, ga al'umma mai nisa, Don Yahweh ne ya furta.
\s5
\v 9 Yi wannan shela a cikin al'ummai, 'Ku shirya kanku domin yaƙi, ku horar da manyan mutane, ku bar su su zo kusa, ku bar dukkan jarumawan yaƙi su hauro nan.
\v 10 Ku mayar da dumɓayen garemaninku takkuba, ku kuma mayar da wuƙaƙenku mãsu. Sai raunana su ce "muna da ƙarfi."
\s5
\v 11 Ku yi sauri ku zo ku makusantan ƙasashe, ku tara kanku wuri ɗaya a can. Yahweh ya kawo ƙarshen mayaƙanku masu iko.'
\s5
\v 12 Bari al'ummai su tada kansu tsaye su zo kwarin Yehoshafat. Don a can zan zauna don in yi wa dukkan al'umman da ke kewaye shari'a.
\v 13 Ku ɗauki lauje don girbi ya nũna. Ku zo, ku mãtsi abin sha, don tulunan ruwan inabi sun cika. sun cika suna zuba, saboda muguntarsu tana da yawa sosai."
\s5
\v 14 Akwai hayaniya, a cikin Kwarin Hukunci. Gama ranar Yahweh ta kusa a cikin Kwarin Hukunci.
\v 15 Rana da wata sun zama baƙi, taurari kuma sun dena bada haskensu.
\s5
\v 16 Yahweh zai yi ruri daga Sihiyona, ya kuma tada murya daga Yerusalem. Duniya da sammai za su girgiza, amma Yahweh zai zama mafaka ga mutanensa, da kuma kagara ga mutanen Isra'ila.
\v 17 "Da haka za ku sani cewa ni ne Yahweh Allahnku wanda ke a Sihiyona, dutsena mai tsarki. Daga nan Yerusalem zata tsarkaka, kuma ba wani sojan da zai ƙara ratsa ta.
\s5
\v 18 A wannan rana kuma duwatsu zasu cika da ruwan inabi mai zaƙi, tuddai kuma za su kwararo da madara, dukkan ƙoramun Yahuda za su ɓulɓulo da ruwa, magudanu za su zo daga gidan Yahweh su jiƙe kwarin Shittim.
\v 19 Masar zata zama yasasshiya, Idom kuma ta zama jejin da a ka yi watsi da shi, saboda tayarwar da a ka yi wa mutanen Yahuda, saboda an zubar da jinin marasa laifi a ƙasarsu.
\s5
\v 20 Gama za a zauna a Yahuda har abada, Yerusalem kuma zata zama wurin zama na dukkan zamanai.
\v 21 Zan yi ramuwar da ban yi ba tukuna a kan jininsu," don Yahweh yana zaune a Sihiyona.