ha_ulb/28-HOS.usfm

449 lines
27 KiB
Plaintext
Raw Permalink Blame History

This file contains invisible Unicode characters

This file contains invisible Unicode characters that are indistinguishable to humans but may be processed differently by a computer. If you think that this is intentional, you can safely ignore this warning. Use the Escape button to reveal them.

\id HOS
\ide UTF-8
\h Littafin Hosiya
\toc1 Littafin Hosiya
\toc2 Littafin Hosiya
\toc3 hos
\mt Littafin Hosiya
\s5
\c 1
\cl Sura 1
\p
\v 1 Wannan ita ce maganar Yahweh da ta zo wurin Hosiya ɗan Biri a kwanakin Uziya, Yotam, Ahaz da Hezekiya, sarakunan Yahuda, da kuma kwanakin Yerobowam ɗan Yoash, sarkin Isra'ila.
\v 2 Sa'ad da Yahweh ya yi magana da fari ta wurin Hosiya, ya ce masa, "Jeka ka ɗaukar wa kanka mata wadda karuwa ce. Za ta sami 'ya'ya ta wurin karuwancinta. Domin ƙasar tana aikata matuƙar karuwanci ta wurin yashe da Yahweh."
\s5
\v 3 Sai Hosiya ya tafi ya auro Gomar ɗiyar Diblayim, sai ta yi ciki ta haifa masa ɗa namiji.
\v 4 Yahweh ya cewa Hosiya, "Ka kira sunansa Yeziril, gama a ɗan lokaci kaɗan zan hukunta gidan Yehu saboda ya zubda jini a Yeziril, zan kuma kawo ƙarshen mulkin gidan Isra'ila.
\v 5 Wannan zai faru randa zan karya bakãr Isra'ila a Kwarin Yeziril."
\s5
\v 6 Sai Gomar ta sake yin ciki ta haifi 'ya mace. Sai Yahweh yace wa Hosiya, "Ka raɗa mata suna Lo Ruhama, gama ba zan ƙara yi wa gidan Isra'ila jinƙai ba, har da zan gafarta masu.
\v 7 Duk da haka zan yi wa gidan Yahuda jinƙai, zan cece su ni da kaina, Yahweh Allahnsu. Ba zan cece su da baka, da takobi, da yaƙi, da dawakai da mahayansu ba,"
\s5
\v 8 Bayan da Gomar ta yaye Lo Ruhama, sai ta yi ciki ta haifi ɗa namiji kuma,
\v 9 Sa'an nan Yahweh yace, "Ka raɗa masa suna, Lo Ammi, domin ku ba mutanena ba ne, ni kuma ba Allahnku ba ne.
\s5
\v 10 Duk da haka yawan mutanen Isra'ila za su zama kamar yashi a bakin teku, wanda ba za a iya aunawa ko ƙirgawa ba. Zai zamana inda aka ce masu, 'Ku ba mutanena ba ne, za a ce masu, "Ku mutanen Allah mai rai ne.'
\v 11 Mutanen Yahuda da mutanen Isra'ila za su taru wuri ɗaya. Za su naɗa wa kansu shugaba ɗaya, za su haura su tafi daga ƙasar, gama ranar Yezril zata zama da girma.
\s5
\c 2
\cl Sura 2
\p
\v 1 Ku cewa 'yan'uwanku maza, 'Mutanena!' ga 'yan'uwanku mata, 'An ji tausayin ku.'"
\s5
\v 2 Ku kawo ƙarar mahaifiyarku, ku kawo ƙara, gama ita ba matata ba ce, ni kuma ba mijinta ba ne. Ta kawar da karuwancinta daga gare ta da halinta na zina daga tsakanin nonnanta.
\v 3 Idan ba haka ba, zan maishe ta tsirara in nuna tsiraicinta kamar a ranar da aka haife ta. Zan maishe ta kamar hamada, kamar busasshiyar ƙasa, in sa ta mutu da ƙishiruwa.
\s5
\v 4 Ba zan nuna jinƙai kan 'ya'yanta ba ko kaɗan, gama 'ya'yan fasikanci ne.
\v 5 Domin uwarsu dăma karuwa ce, ita wadda ta ɗauki cikinsu ta yi abin kunya. Ta ce, "Zan bi masoyana, domin suna bani abincina, da ruwa, da ulu, da gyale, da mai da abin sha."
\s5
\v 6 Sabo da haka zan gina shinge in tare hanyarta da ƙayayuwa. Zan gina katanga gãba da ita don kada ta gane hanyarta.
\v 7 Zata bi masoyanta, amma ba za ta cim masu ba. Zata neme su, amma ba za ta same su ba. Sa'annan za ta ce, "Zan koma wurin mijina na farko, gama a dã ya fiye mani da yanzu."
\s5
\v 8 Gama ba ta sani dama ni ne na ba ta hatsi ba, da sabon ruwan inabi da mai, na kuma yawaita ta da azurfa da zinariya, wanda suke amfani da shi ga Ba'al.
\v 9 Saboda haka zan karɓe hatsinta da kaka, da sabon ruwan inabina a lokacin girbi. Zan karɓe uluna da gyaluluwana da aka mora don a rufe tsiraicinta.
\s5
\v 10 Zan buɗe tsiraicinta a idanun masoyanta, ba wanda zai cece ta daga hannuna.
\v 11 Zan sa dukkan shagulgulanta su ƙare - bukukuwanta, shagalin tsayawar sabon wata, Asabatai, da dukkan ayyanannun bukukuwa.
\s5
\v 12 "Zan lalatar da kuringar inabinta da itatuwan ɓaurenta, da ta ce, "Waɗannan su ne ladar da masoyana suka bani.' Zan maishe su jeji, namun jeji kuma za su cinye su.
\v 13 Zan hore ta domin ranakun bukukuwan Ba'aloli, lokacin da ta ƙona masu turare, sa'ad da ta yiwa kanta ado da zobba da duwatsu masu daraja, ta bi masoyanta ta manta da ni -- wannan shi ne furcin Yahweh."
\s5
\v 14 Saboda haka zan lallashe ta in dawo da ita. Zan kai ta cikin jeji in yi mata tattausar magana.
\v 15 Zan mayar mata da gonakin inabinta, Kwarin Akor zai zama kofar bege. Nan za ta amsa mani kamar kwanakin ƙuruciyarta, kamar ranar da ta fito daga ƙasar Masar.
\s5
\v 16 "Zaya zamana a ranan nan - wannan furcin Yahweh ne - za ki kira ni, 'Mijina,' kuma ba za ki ƙara kira na 'Ba'al Nawa' ba.
\v 17 Gama zan fitar da sunayen Ba'aloli daga bakinta, ba za a ƙara tunawa da sunayensu ba."
\s5
\v 18 A ranan nan zan yi alƙawari domin su da namun jeji, da tsuntsayen sama, da masu rarrafe a ƙasa. Zan kori bakã, da takobi, da kuma yaƙi daga ƙasar, in sa ku zauna lafiya.
\s5
\v 19 Zan yi alƙawari in zama mijinki har abada. Zan yi alƙawari in zama mijinki cikin gaskiya, da adalci, da alƙawarin aminci, da jinƙai.
\v 20 Zan ɗaukar wa kaina alƙawarin aminci da ke, za ki kuma san Yahweh.
\s5
\v 21 A ranar nan zan amsa - wannan furcin Yahweh ne - Zan amsa wa sammai, su kuma za su amsa wa ƙasa.
\v 22 Ƙasa kuma za ta amsa wa hatsi, sabon ruwan inabi da kuma mai, za su amsa wa Yeziril.
\s5
\v 23 Zan dasa ta domin kaina a ƙasar, zan nuna jinkai akan Lo Ruhama, Zan cewa Lo Ammi, 'Ke ce Ammi Attah,' sa'annan za su ce mani, 'Kai ne Allahnmu."'
\s5
\c 3
\cl Sura 3
\p
\v 1 Yahweh yace mani, "Jeka har wa yau, ka ƙaunaci wata mata wadda kaunatacciya ce ga mijinta, amma mazinaciya ce. Ka ƙaunaceta kamar yadda Ni, Yahweh, na ke ƙaunar mutanen Isra'ila, ko da yake sukan juya zuwa ga bin waɗansu alloli, suna ƙaunar wainar 'ya'yan itatuwa."
\v 2 Sai na saye ta domin kaina a bakin azurfa sha biyar da hatsi tiya guda da rabin bali.
\v 3 Na ce mata, "Dole ne ki zauna da ni kwanaki da yawa. Ba za ki zama karuwa ba, ko ki zama ta wani mijin ba. Haka nima kuma zan kasance a gare ki."
\s5
\v 4 Gama mutanen Isra'ila za su kasance kwanaki da yawa ba sarki, ba kuma ɗan sarki, ba hadaya, ba bagadin dutse, ba falmara ko gumakan gida.
\v 5 Daga baya mutanen Isra'ila za su juyo su nemi Yahweh Allahnsu da sarkinsu Dauda, kuma a kwanakin ƙarshe, za su zo da rawar jiki gaban Yahweh da alheransa.
\s5
\c 4
\cl Sura 4
\p
\v 1 Ku ji maganar Yahweh, ku mutanen Isra'ila. Yahweh yana da ƙara game da mazaunan ƙasar, domin babu gaskiya ko alƙawarin aminci, babu sanin Allah a ƙasar.
\v 2 Akwai la'antarwa, ƙarya, kisa, sata da zina. Mutanen sun zarce dukkan iyaka, ana zubda jini kan zubda jini.
\s5
\v 3 Saboda haka ne ƙasar take bushewa, dukkan mazaunanta kuma suna yanƙwanewa; dabbobin jeji da tsuntsayen sama, har ma da kifayen dake a teku, ana kawar dasu.
\s5
\v 4 Amma kada ka bari ko guda ɗaya ya kawo ƙara; kada ka bari wani ya zargi wani. Domin ku firistoci kune nake zargi.
\v 5 Ku firistoci za ku yi tuntuɓe da rana, annabawa kuma za su yi tuntuɓe tare da ku da dare, zan kuma hallaka mahaifiyarku.
\s5
\v 6 Ana hallaka mutanena saboda rashin ilimi. Saboda ku firistoci kun ƙi ilimi, nima zan ƙi ku zama firistocina. Domin kun manta da dokokina, ko da yake ni Allahnku ne, nima zan manta da 'ya'yanku.
\v 7 Yadda firistocin suke ƙaruwa, haka ma zunuban da suke yi mani. Sukan misanya ɗaukakarsu da kunya.
\s5
\v 8 Suna ci daga zunuban mutanena; suna da zarin mugunta da yawa.
\v 9 Zai zama ɗaya saboda mutane da kuma firistoci: Zan hukunta su dukka saboda al'amuransu, zan saka masu saboda ayyukansu.
\s5
\v 10 Za su ci amma ba zai ishe su ba; za su yi karuwanci, amma ba za su ƙaru ba, domin sun yi nisa da Yahweh.
\s5
\v 11 Suna ƙaunar fasiƙanci, ruwan inabi, da sabon ruwan inabi, wanda yake ɗauke fahimtarsu.
\v 12 Mutanena suna neman shawara daga gumakun itacensu, sandar tafiyarsu kuma na basu anabce - anabce. Domin tunanin fasiƙanci ya ɓadda su, sun aikata karuwanci maimakon su zama da aminci ga Allahnsu.
\s5
\v 13 Suka miƙa hadayu a ƙwanƙolin duwatsu, suka ƙona turare bisa tuddai, ƙarƙashin rimaye, foflas da tsamiya, domin inuwar tana da daɗi. Sai 'ya'yanki mata suka yi lalata, surukanki mata kuma suka yi zina.
\v 14 Bazan hori 'ya'yanki mata ba sa'ad da suka zaɓi suyi fasiƙanci, ko surukanki mata idan suka yi zina. Domin maza ma suna bada kansu ga karuwai, suna miƙa hadayu domin su yi lalata da keɓaɓɓun karuwai. Waɗannan mutane da basu da ganewa zan fyaɗa su ƙasa.
\s5
\v 15 Koda yake Isra'ila kin yi zina, bari Yahuda ma kada ta yi saɓo. Ku mutane, kada ku tafi Gilgal, kada ku haye zuwa Bet Aben, kada kuma ku rantse kuna cewa, "Yahweh hakika mai rai ne."
\v 16 Gama Isra'ila ta yi taurin kai, kamar karsana mai gardama. Ƙaƙa Yahweh zai kawosu makiyaya kamar 'yan tumaki wurin kiwo?
\s5
\v 17 Ifraim ya haɗa kansa da gumaka; ku ƙyale shi.
\v 18 Harma idan barasarsu ta ƙare, sukan ci gaba da zinarsu, masu mulkinsu suna amincewa da kunyarsu ƙwarai.
\v 19 Iska za ta nannaɗe ta cikin fukafukanta; za su kuma ji kunya saboda hadayunsu.
\s5
\c 5
\cl Sura 5
\p
\v 1 Ku ji wannan ku firistoci! Ku natsu, gidan Isra'ila! Ku kasa kunne, gidan sarki! Domin hukunci na zuwa bisa kanku dukka. Kun zama tarko a Mizfa tarun da aka baza akan Tabor.
\v 2 'Yan tawaye sun dage da hallakarwa, amma zan hukunta dukkansu.
\s5
\v 3 Na san Ifraim, Isra'ila kuma ba a ɓoye take a gare ni ba. Ifraim yanzu kin zama kamar karuwa; Isra'ila ta ƙazantu.
\v 4 Ayyukansu ba za su barsu su juyo ga Allah ba, domin tunanin zina yana cikinsu, ba su kuwa san Yahweh ba.
\s5
\v 5 Girman kan Isra'ila yana shaida a kansu, saboda haka Isra'ila da Ifraim za suyi tuntuɓe cikin laifinsu. Yahuda ma zai yi tuntuɓe tare dasu.
\v 6 Zasu tafi tare da garkunansu na tumaki dana shanu su biɗi Yahweh, amma baza su same shi ba, gama ya rigaya ya janye kansa daga gare su.
\v 7 Sunyi rashin aminci ga Yahweh, domin sun haifi 'ya'yan haram. Yanzu bukukuwan sabon wata zai cinyesu dasu da gonakinsu.
\s5
\v 8 Ku busa ƙaho a Gibiya, da kakaki a Rama. Ku tada kururuwar yaƙi a Bet Aben: 'Za mu bi ki Benyamin!'
\v 9 Ifraim zata zama kango a ranar hukuncinta. Na yi shelar abin da zai faru lallai a cikin ƙabilar Isra'ila.
\s5
\v 10 Shugabannin Yahuda suna kama da masu kawar da dutsen kan iyaka, zan zuba hasalata a kansu kamar ruwa.
\v 11 An murƙushe Ifraim; an danne shi a shari'a domin da yardar rai ya bi gumaka.
\s5
\v 12 Saboda haka zan zama kamar asu ga Ifraim, kuma kamar tsatsa ga gidan Yahuda.
\v 13 Da Ifraim ya ga cutarsa, Yahuda ma ya ga rauninsa, sai Ifraim ya tafi Asiriya, Yahuda kuwa ya aiki jakadu wurin babban sarki. Amma bai iya warkar da mutanen ku ba, bai kuma iya warkar da raunukanku ba.
\s5
\v 14 Saboda haka zan zama kamar zaki ga Ifraim, kuma kamar dan zaki ga gidan Yahuda. Ni, I, Ni' kaina zan kekketasu in yi tafiya ta; zan kwashe su; ba kuma wanda zai cecesu'
\v 15 Zan tafi in koma wurina, har sai sun yarda su karɓi laifinsu su kuma biɗi fuskata, sai kuma sun biɗe ni da aniya cikin ƙuncinsu."
\s5
\c 6
\cl Sura 6
\p
\v 1 "Zo, mu koma gun Yahweh, gama ya yayyaga mu, amma zai warkar da mu; ya ji mana rauni, amma zai ɗaure mana raunukanmu.
\v 2 Bayan kwana biyu, zai farkar da mu; zai tashemu a rana ta uku, zamu rayu kuma a gabansa.
\v 3 Bari mu san Yahweh, bari mu ƙara nacewa mu san Yahweh. Zuwansa tabbataccene kamar wayewar gari. Zai zo wurinmu kamar ruwan sama, kamar ruwan ƙarshe mai jiƙa ƙasa.
\s5
\v 4 Ifraim me zan yi da ke? Yahuda, me zan yi da ke? Amincinki kamar gajimaren safe ne, kamar raɓar da take kaɗewa da wuri.
\v 5 Saboda haka na daddatse su ta wurin annabawansu, na kashesu da maganganun bakina. Umarninka kamar haske ne mai sheƙi.
\s5
\v 6 Gama ina biɗar aminci ne ba hadaya ba, da kuma sanin Allah fiye da hadayun ƙonawa.
\v 7 Kamar Adamu sun karya alƙawari; sun yi mani rashin aminci.
\s5
\v 8 Giliyad birnin mugaye ne mai sawun jini.
\v 9 Kamar yadda taron mafasa suke wa mutum kwanto haka ƙungiyar firistoci suke haɗa kai su yi kisa a hanya zuwa Shekem; sun aikata laifofi masu ban kunya.
\s5
\v 10 A cikin gidan Isra'ila na ga mummunan abu; karuwancin Ifraim na nan, Isra'ila kuma ta ƙazantu.
\v 11 Ke kuma, Yahuda, an ƙaddara miki girbi, sa'ad da zan mayar wa mutanena albarkunsu.
\s5
\c 7
\cl Sura 7
\p
\v 1 Duk lokacin da nake so in warkar da Isra'ila, sai zunuban Ifraim su bayyana, haka kuma mugayen ayyukan Samariya, domin suna shirya yaudara; ɓarawo ya kan shigo, mafasa kuwa su kai hari a titi.
\v 2 Basu sani ba a zukatansu ina sane da dukkan mugayen ayyukansu. Yanzu ayyukansu sun kewayesu; suna nan a fuskata.
\s5
\v 3 Da muguntarsu suke faranta wa sarki rai, hakimai kuma da ƙarairayi.
\v 4 Dukkansu mazinata ne, kamar tanderun wuta da mai tuya ya dena zuga wutar daga lokacin kwaɓa curi zuwa lokacin sa gami.
\v 5 A ranar sarki, hakimai suka sa wa kansu ciwo da ƙunar barasa. Ya miƙa hannunsa ga masu yin ba'a.
\s5
\v 6 Da zuciya kamar tanderu suna ƙirƙiro dabarun ƙarya. Fushinsu; na ƙuna da dare, da safe yakan tashi kamar harshen wuta.
\v 7 Duk suna da zafi kamar tanderu, suna kuma hallakar da masu mulkinsu. Dukkan sarakunansu sun faɗi; ba wanda yake kira na.
\s5
\v 8 Ifraim ya na cuɗanya da al'umma. Ifraim waina ne mai faɗi da ba a juya shi ba.
\v 9 Bãƙi sun cinye ƙarfinsa, amma bai sani ba. An yayyafa furfura a kansa, amma bai sani ba.
\s5
\v 10 Girman kan Isra'ila na shaida gãba akansa a; duk da haka basu dawo ga Yahweh Allahnsu ba, basu kuma neme shi ba duk da waɗannan abubuwa.
\v 11 Ifraim kamar kurciya yake, mara wayo, ba hankali, yana kiran Masar yana firiya zuwa Asiriya.
\s5
\v 12 Sa'ad da suka tafi, zan baza ragata a kansu, zan jawo su ƙasa kamar tsutsayen sama. Zan hukunta su a tarayyarsu.
\v 13 Kaiton su! Domin sun gudu daga gare ni. Hallaka tana zuwa kansu! Sun yi mani tawaye! Dã na cece su, amma sun yi mani ƙarya.
\s5
\v 14 Basu yi mani kuka da dukkan zuciyarsu ba, amma a kan gadajensu suke rusa kuka. Suna taruwa domin hatsi da sabon ruwan inabi, sun juya daga gareni.
\v 15 Ko da yake ni na koyar dasu na kuma ƙarfafa hannuwansu, amma yanzu suna ƙulla mani mugunta.
\s5
\v 16 Sun dawo, amma ba su dawo wurina ba, Mafi Ɗaukaka. Suna kama da bakan da ya saki. Hakimansu za su fãɗi da kaifin takobi, saboda hasalar harshensu. Wannan zai jawo masu ba'a cikin kasar Masar.
\s5
\c 8
\cl Sura 8
\p
\v 1 Ka sa ƙaho a leɓunanka! Gaggafa na zuwa bisa kan gidan Yahweh domin mutane sun karya alƙawarina sun kuma bijirewa dokokina.
\v 2 Sun yi kuka gare ni, 'Ya Allahna, mu a Isra'ila mun san ka.'
\v 3 Amma Isra'ila taƙi abin dake mai kyau, maƙiyi kuma zai tasar masa.
\s5
\v 4 Sun naɗa sarakuna, amma ba dani ba, sun yi hakimai, amma bada sani na ba. Da zinariyar su da azurfa suka yi wa kansu gumakai, amma lallai za a datse su."
\v 5 "An ƙi ɗan maraƙinki ya Samariya. Fushina yana ƙuna akan waɗannan mutane. Har yaushe zasu kasance cikin laifi?
\s5
\v 6 Gama wannan gunki daga wurin Isra'ila ya fito; mutum ne yayi shi; ba Allah ba ne! Za a farfashe ɗanmaraƙin Samariya.
\v 7 Gama mutane sun shuka iska sun girbe guguwa. Hatsin dake tsaye ba shi da tsaba; bai bada gari ba. Ko da ya nuna, bãƙi ne zasu cinye shi.
\s5
\v 8 An haɗiye Isra'ila; yanzu sun kwanta tare da ƙasashe sai kace abin da ba shi da amfani.
\v 9 Gama sun hau zuwa Asiriya kamar jakin jeji shi ka ɗai. Ifraim tayi hayar masoya domin kanta.
\v 10 Ko da zasu yi hayar masoya daga cikin al'ummai, yanzu zan tara su. Zasu fara lalacewa, saboda danniyar sarkin sarakuna.
\s5
\v 11 Saboda Ifraim ya ruɓanya bagadai domin miƙa baye-baye na zunubi, amma a maimakon haka sai suka zama bagadan aikata zunubi.
\v 12 Ko da zan rubuta masu dokata sau dubu goma, zasu dube ta a matsayin baƙon abu a gare su.
\s5
\v 13 Game da maganar hadayun baye-bayena, suna hadaya da nama su kuma ci. Amma ni, Yahweh, ban karɓe su ba. Yanzu zan tuna da muguntarsu in hukunta zunubansu. Za su koma Masar.
\v 14 Isra'ila ya manta da ni, Mahaliccinsa, ya kuma gina masarautai. Yahuda ya gina garu masu yawa, amma zan aikar da wuta bisa biranen su; zai hallakar da kagara.
\s5
\c 9
\cl Sura 9
\p
\v 1 Isra'ila, kada ka yi farinciki, tare da murna kamar sauran mutane. Gama ka yi ta rashin aminci, ka yashe da Allahnka. Kana son biyan haƙƙoƙin karuwa a dukkan masussukai.
\v 2 Amma masussuka da wurin matsewar inabi ba zasu ciyar da su ba; sabon ruwan inabi kuma zai ƙare.
\s5
\v 3 Ba zasu ci gaba da zama a ƙasar Yahweh ba; maimakon haka, Ifraim zai koma Masar, wata rana zasu ci ƙazantaccen abinci a Asiriya.
\v 4 Ba zasu zuba hadayun inabi ga Yahweh ba, ba kuma zasu zama abin karɓa gare shi ba. Hadayunsu zasu zama kamar abincin makoki: duk wanda ya ci shi zai ƙazantu. Domin abincinsu zai zama nasu ne kaɗai; ba zai zo cikin gidan Yahweh ba.
\s5
\v 5 Me za ku yi a ranar da aka keɓe don taruwa, a ranar idi ta Yahweh?
\v 6 Gama, duba, idan sun kubcewa hallaka, Masar zata tara su, Memfis kuma za ta bizne su, kayayyakin daraja na azurfa - abubuwa masu tsini zasu mallake su, ƙayayuwa kuma za su cika rumfunansu.
\s5
\v 7 Kwanakin hukunci suna zuwa; kwanakin sakamako suna zuwa. Bari dukkan Isra'ila su san waɗannan abubuwa. Annabin wawa ne, masanin kuma taɓaɓɓe ne, saboda girman muguntarka da yawan zafin ranka.
\s5
\v 8 Annabi mai tsaro ne domin Allahna akan Ifraim. Amma tarkon tsuntsu yana kan dukkan hanyoyinsa, rashin jituwa kuma na cikin gidan Allahnsa.
\v 9 Sun ƙazantar da kansu ƙwarai kamar a cikin kwanakin Gibiya. Allah zai tuna da muguntarsu, zai kuma hukunta zunubansu.
\s5
\v 10 Yahweh yace, "Lokacin da na samo Isra'ila, kamar samun 'ya'yan inabi ne a cikin jeji. Kamar nunan farin itacen ɓaure a lokacinsa, na samo ubanninku. Amma suka je wurin Ba'al Fiyo, suka kuma miƙa kansu ga wannan gunki abin kunya. Suka zama abin ƙyama kamar gunkin da suke ƙauna.
\s5
\v 11 Amma ga Ifraim darajarsu zata tashi kamar tsuntsu. Ba mai haihuwa, ba mai juna biyu, ko mai daukar ciki.
\v 12 Ko da yake sun goyi 'ya'ya, zan ɗauke su daga gare su ba wanda zai ragu. Kaiton su sa'ad da na juya daga gare su!
\s5
\v 13 Na ga Ifraim, kamar Taya, an dasa ta a wuri mai dausayi, amma Ifraim zai kawo 'ya'yansa wurin wani wanda zai yayyanka su."
\v 14 Ka ba su, Yahweh - me zaka ba su? Ka ba su mahaifa mai yin ɓari, da nonon da baya ba da madara.
\s5
\v 15 "Saboda muguntarsu a Gilgal, a can ne na fara ƙinsu. Saboda mugayen ayyukansu, zan kore su daga cikin gidana. Bazan ƙara ƙaunarsu ba; dukkan shugabanninsu 'yan tawaye ne.
\s5
\v 16 Ifraim na da cuta, sauyarsa kuma ta bushe; basu ba da 'ya'ya. Ko da zasu sami 'ya'ya, zan kashe ƙaunattatun 'ya'yansu."
\v 17 Allahna zai ƙi su saboda ba suyi masa biyayya ba. Zasu zama masu kai wa da komowa cikin al'ummai.
\s5
\c 10
\cl Sura 10
\p
\v 1 Isra'ila kuringa ce mai yabanya dake ba da 'ya'yansa. Gwargwadon yawan 'ya'yansa gwargwadon yawan gina bagadansa. Bisa ga albarkar ƙasarsa, yakan inganta ginshiƙansa.
\v 2 Zuciyarsu da yaudara; yanzu dole su ɗauki laifinsu. Yahweh zai rushe bagadansu; zai lalatar da ginshiƙansu.
\s5
\v 3 Sa'annan zasu ce, "Bamu da sarki, domin ba mu jin tsoron Yahweh, sarki kuma -- me zai yi mana?"
\v 4 Maganganunsu na wofi ne, su kan ɗauki wa'adodi ta wurin rantsewa kan ƙarya. Domin wannan adalci ya tsuro kamar tsire - tsire masu dafi cikin gona.
\s5
\v 5 Mazaunan Samariya zasu tsorata saboda 'yan'maruƙan Bet Aben. Mutanenta zasu yi makoki a kanta, kamar yadda mazinatan firistoci suka yi murna a kansu da darajarsu, amma yanzu ba su nan.
\v 6 Za a kai su Asiriya a matsayin kyauta ga babban sarki. Za a kunyatar da Ifraim, Isra'ila kuma za ta ji kunya saboda gumakanta.
\s5
\v 7 Za'a hallakar da sarkin Samariya, kamar sassaƙen itace a bisa ruwa.
\v 8 Za a hallakar da wurin zaman mugunta. Wannan shi ne zunubin Isra'ila! Ƙayayuwa da sarƙaƙƙiya zasu fito bisa bagadansu. Mutane zasu cewa duwatsu, "Ku rufe mu!" tuddai kuma, "Ku faɗo mana!"
\s5
\v 9 Isra'ila kayi zunubi tun kwanakin Gibiya; a can ka tsaya. Ko yaƙi ba zai iske 'ya'yan kurakurai a Gibiya ba?
\s5
\v 10 A lokacin da na so, zan horar dasu. Al'ummai zasu taru su ɗaure su saboda laifofinsu.
\v 11 Ifraim horarriyar karsana ce dake son sussukar hatsi, zan sa karkiya a bisa kyakkyawan wuyanta. Zan sa karkiya a wuyan Ifraim; Yahuda zai yi huɗa; Yakubu kuma zai ja garma da kansa.
\s5
\v 12 Ku shuka wa kanku adalci, za ku girbi ɗiyan alƙawarin aminci. Kuyi kaftun saurar ƙasarku, gama lokaci ya yi da za a nemi Yahweh, har lokacin da zai zo ya zuba adalci a kanku.
\v 13 Kun shuka mugunta; kun girbe rashin adalci. Kun ci 'ya'yan yaudara saboda kun dogara ga shirye-shiryenku da kuma yawan sojojinku.
\s5
\v 14 Domin wannan hargitsin yaki zai tashi daga cikin mutanenku, za a kuma lalatar da dukkan garuruwanku masu kagara, zai za ma kamar yadda Shalman ya lalatar da Bet Arbel a ranar yaƙi, aka datse uwaye da 'ya'yansu gunduwa-gunduwa.
\v 15 Haka zai faru dake, Betel, saboda muguntar ki mai yawa. Da wayewar gari za a datse sarkin Isra'ila gaba ɗaya."
\s5
\c 11
\cl Sura 11
\p
\v 1 Lokacin da Isra'ila yake yaro na ƙaunace shi, na kuma kira ɗana daga cikin Masar.
\v 2 Yawan kiran su, yawan gujewar su daga gare ni. Sun miƙa hadaya ga Ba'aloli, suka ƙona turare ga gumaka.
\s5
\v 3 Duk da haka ni na koyawa Ifraim tafiya. Ni ne na ɗaga su da hannuwansu, duk da haka basu sani na kula dasu ba.
\v 4 Na bishe su da linzamin mutune, da ragamar ƙauna. Na zama kamar mai kwance masu karkiya a muƙamuƙinsu, na sunkuya masu na ciyar dasu kuma.
\s5
\v 5 Baza su koma ƙasar Masar ba? Ko Asiriya ba za suyi mulkinsu saboda sunƙi juyowa gare ni ba?
\v 6 Takobi zai faɗa wa biranensu ya hallaka ƙarafan ƙofofinsu; zai hallaka su saboda shirye-shiryensu.
\v 7 Mutanena sun ƙudurta juyawa daga gareni. Ko da sun yi kira ga Maɗaukaki, ba wanda zai taimake su.
\s5
\v 8 Ta yaya zan iya rabuwa da kai, ya Ifraimu? Ta yaya zan mika ka, ya Isra'ila? Ƙaƙa zan maishe ka kamar Adma? Yaya zan maishe ka kamar Zeboyim? A gare ni zuciyata ta canza; dukkan jinƙaina ya harzuƙa.
\v 9 Bazan tabbatar da zafin fushina ba; bazan hallakar da Ifraim ba. Gama Ni Allah ne ba mutum ba; Ni ne Mai Tsarki wanda ke tsakiyar ku, ba kuwa zan zo cikin hasala ba.
\s5
\v 10 Zasu bi Yahweh; shi kuma zai yi ruri kamar zaki. Idan yayi ruri, 'ya'yansa za su zo suna rawar jiki daga yamma.
\v 11 Zasu zo da rawar jiki kamar tsuntsu daga Masar, kamar kurciya daga ƙasar Asiriya. Zan maishe su su zauna a gidajensu - wannan furcin Yahweh ne.
\s5
\v 12 Ifraim ya kewaye ni da ƙarairayi, gidan Isra'ila kuma da yaudara. Amma Yahuda har yanzu yana tare da ni, Allah, yana yi mani aminci, Mai Tsarkin nan."
\s5
\c 12
\cl Sura 12
\p
\v 1 Ifraim yana ci daga iska, ya na bin iskar gabas. Kullum yana yawaita ƙarairayi da ta'addanci. Sun yi alƙawari da Asiriya suna ɗaukar man zaitun zuwa Masar.
\v 2 Yahweh kuma yana da ƙara gãba da Yahuda kuma zai hukunta Yakubu saboda abin da ya yi; zai sãka masa gwargwadon ayyukansa.
\s5
\v 3 A cikin ciki Yakubu ya kama duddugen ɗan'uwansa, a cikin balagarsa kuma yayi kokowa da Allah.
\v 4 Yayi kokowa da mala'ika kuma ya yi nasara. Ya yi kuka ya roƙi tagomashinsa. Ya sadu da Allah a Betel; a can Allah yayi magana da shi.
\s5
\v 5 Wannan shi ne Yahweh, Allah Mai runduna; "Yahweh" shi ne sunansa da za a dinga kira
\v 6 Domin wannan ka juyo wurin Allahnka. Ka kiyaye alƙawarin jinƙai da adalci, kana cigaba da sauraron Allahnka.
\s5
\v 7 'Yan kasuwa na riƙe da ma'aunin algus a hannunsu; suna son yin algus.
\v 8 Ifraim yace, "Hakika na zama mai arzaƙi sosai; na samarwa kaina dukiya. A cikin dukkan aikina ba za a sami laifi a ciki na ba, ko duk wani abin da zai zama zunubi."
\s5
\v 9 "Ni ne Yahweh Allahnku tun daga ƙasar Masar. Zan kuma sa ku sake zama cikin rumfuna, kamar cikin kwanakin ayyanannen idi.
\v 10 Na yi magana da annabawa, na kuma basu wahayi da yawa domin ku. Ta hannun annabawa kuma na ba da misalai."
\s5
\v 11 Idan akwai mugunta a Giliyad, hakika mutane sun zama marasa amfani. A Gilgal sun yi hadayar bajimai; bagadansu zasu zama kamar tsibi -tsibin dutse a cikin gonaki.
\v 12 Yakubu ya gudu zuwa ƙasar Aram; Isra'ila ya yi aiki domin ya sami mata; ya yi kiwon garkunan tumaki domin ya sami mata.
\s5
\v 13 Yahweh ya fitar da Isra'ila daga Masar ta wurin annabi, ta hannun annabi kuma ya kula dasu.
\v 14 Ifraim ya baƙanta wa Yahweh rai. Domin wannan Ubangijinsa zai bar jininsa a kansa, zai kuma sãka masa akan duk abin kunyarsa.
\s5
\c 13
\cl Sura 13
\p
\v 1 "Sa'ad da Ifraim ya yi magana, akwai razanarwa. Ya ɗaukaka kansa a Isra'ila, amma ya zama da laifi wajen bautar Ba'al, kuma ya mutu.
\v 2 Yanzu, sai ƙara zunubi suke tayi, suna yiwa kansu sifofi na zubi daga azurfarsu, gumaka ne da masu hikima suka ƙera, dukkan su aikin gwanayen masu sana'a ne. Mutane suka ce masu, 'Waɗannan mutane masu miƙa hadaya sunyiwa 'yanmaruƙa sumba.'
\s5
\v 3 Domin wannan zasu zama kamar gizagizan safe, kamar raɓa mai kaɗewa da sauri, kamar ƙai-ƙayi wanda iska ke hurewa daga masussuka, kamar hayaƙi daga cikin mafitarsa.
\s5
\v 4 Amma ni ne Yahweh Allahnka tun daga ƙasar Masar, dole ka sani cewa ba bu wani Allah sai ni, dole kuma ka amince cewa banda ni babu wa ni mai ceto.
\v 5 Na san ka a cikin jeji, cikin ƙasa mai tsananin fari.
\v 6 Da kuka sami makiyaya, kun zama ƙosassu; amma bayan da kuka ƙoshi, kun ɗaukaka kanku. Saboda wannan dalili kuka manta da ni.
\s5
\v 7 Zan zama kamar zaki a gare su; kamar damisa zan yi fako a kan hanya.
\v 8 Zan faɗa masu kamar damisa da aka ƙwace mata 'ya'yanta, zan tsaga haƙarƙarin ƙirjin su, a can ne zan cinye su kamar zaki, kamar naman jeji zan yayyage su gunduwa-gunduwa.
\s5
\v 9 Zan hallaka ku, ya Isra'ila; wanene zai iya taimakon ku?
\v 10 Yanzu ina sarkinku, da za ya iya ceton ku daga cikin dukkan biranenku? Ina shugabanninku waɗanda kuka ce mani, 'Ka bamu sarki da hakimai'?
\v 11 Na baku sarki cikin fushina, na kuma kawar da shi cikin hasalata.
\s5
\v 12 Laifin Ifraim a ajiye yake; an kuma ajiye kurakuransa,
\v 13 Zafin naƙudar haihuwa za ta afko masa, amma ɗa ne mara hikima, domin idan lokacin haihuwarsa ya yi, ba zai fita daga cikin mahaifa ba.
\s5
\v 14 ̀̀̀̀̀Zan cece su daga hannun Lahira? Zan cece su daga mutuwa? Mutuwa, ina, annobanki? Lahira, ina hallakarwarki? Babu sauran tausayi daga idanuna."
\s5
\v 15 Koda Ifraim ya azurta cikin 'yan'uwansa, iskar gabas za ta zo; guguwar Yahweh za ta buga daga hamada. Maɓulɓular Ifraim za ta bushe, rijiyarsa ba zata ba da ruwa ba. Abokan gãbarsa zasu washe ɗakin ajiyar dukkan kayansa masu daraja.
\s5
\v 16 Samariya za ta ji kunya, domin ta tayarwa Allahnta. Zasu faɗi ta kaifin takobi; ƙananan 'ya'yansu za a yayyankasu, matansu masu ciki za a farke su.
\s5
\c 14
\cl Sura 14
\p
\v 1 Isra'ila, ka juyo wurin Yahweh Allahnka, gama ka faɗi saboda laifinka.
\v 2 Ka ɗauki maganganun tare da kai ka juyo wurin Yahweh. Ka ce masa, "Ka kawar da dukkan laifinmu ka kuma karɓi abin da ke mai kyau, domin mu iya miƙa maka ɗiyan leɓunanmu.
\s5
\v 3 Asiriya ba za su cece mu ba; ba za mu hau dawakai mu yi yaƙi ba. Ba kuwa zamu ƙara ce da aikin hannuwanmu, 'Ku ne allolinmu,' gama a cikinku marayu ke samun jinƙai."
\s5
\v 4 "Zan warkar da bauɗewarsu; zan ƙaunacesu a yalwace, domin na kawar da fushina daga gare shi.
\v 5 Zan zama kamar raɓa ga Isra'ila; zai yi fure kamar auduga, ya kuma kafu kamar itacen sida a Lebanon.
\v 6 Rassansa zasu yaɗu waje; kyaunsa zai zama kamar itatuwan zaitun, ƙanshinsa kuma kamar itatuwan sida a Lebanon.
\s5
\v 7 Mutanen da ke zaune ƙarƙashin inuwarsa zasu dawo; zasu farfaɗo kamar hatsi zasu yi fure kamar kuringar inabi. Shahararsa za ta zama kamar inabin Lebanon.
\v 8 Ifraim, me zan yi kuma da gumaka? Zan amsa masa in lura da shi. Ni kamar itacen bakin rafi ne wanda kullum ganyayensa kore ne; daga wurina kuke samun 'ya'ya."
\s5
\v 9 Wane ne mai hikima da zai fahimci waɗannan abubuwa? Wane ne ya fahimci waɗannan abubuwa domin ya san su? Gama hanyoyin Yahweh dai-dai suke, adali kuwa zaya yi tafiya cikinsu, amma masu tayarwa zasu faɗi a cikinsu.