ha_ulb/27-DAN.usfm

751 lines
61 KiB
Plaintext
Raw Permalink Blame History

This file contains invisible Unicode characters

This file contains invisible Unicode characters that are indistinguishable to humans but may be processed differently by a computer. If you think that this is intentional, you can safely ignore this warning. Use the Escape button to reveal them.

\id DAN
\ide UTF-8
\h Littafin Daniyel
\toc1 Littafin Daniyel
\toc2 Littafin Daniyel
\toc3 dan
\mt Littafin Daniyel
\s5
\c 1
\cl Sura 1
\p
\v 1 A cikin shekara ta uku ta mulkin Yehoyakim sarkin Yahuda, Nebukadnezza sarkin Babila ya zo Yerusalem ya kewaye birnin domin ya yanke dukkan abin da zai shigo cikinsa.
\v 2 Ubangiji ya ba Nebukadnezza nasara akan Yehoyakim sarkin Yahuda, ya ba shi waɗansu keɓaɓun abubuwa daga gidan Allah. Ya kawo su cikin ƙasar Babila, zuwa gidan allahnsa, kuma ya sa keɓaɓun abubuwan a cikin ma'ajin allahnsa.
\s5
\v 3 Sarkin ya yi magana da Ashfenaz, baban jami'insa, ya kawo waɗansu daga cikin mutanen Isra'ila, waɗanda su ke daga iyalin sarauta da kuma manyan mutane -
\v 4 samari waɗanda ba su da cikas, kyawawa, ƙwararru a kowacce hikima, cike da ilimi da ganewa, waɗanda suka cancanci su yi aiki a fãdar sarki. Shi ne zai koya masu adabin mutanen Babila da harshensu.
\v 5 Sarki ya ɗibar masu abinci daga abincinsa da ruwan inabi wanda ya ke sha. Za a horar da waɗannan samari har shekaru uku, bayan haka, za su yi wa sarki hidima.
\s5
\v 6 A cikin su akwai Daniyel da Hananiya da Mishayel da Azariya, daga cikin mutanen Yahuda.
\v 7 Babban jami'in ya ba su sunaye, Daniyel ya kira shi Beltishazza, ya kira Hananiya Shadrak, ya kira Mishayel, Meshak Azariya kuma ya kira shi Abednego.
\s5
\v 8 Amma Daniyel ya yi niyya a ransa, cewa ba zai ɓata kansa da abincin sarki ba ko da ruwan inabin da ya ke sha. Sai ya roƙi alfarma daga wurin babban jami'in saboda ba ya so ya ɓata kansa.
\v 9 Sai Allah ya ba Daniyel tagomashi da tausayi daga babban jami'in ta wurin girmamawar da da ya ke yi masa.
\v 10 Babban jami'in ya ce da Daniyel, "Ina jin tsoro shugabana sarki. Ya bada ummurni akan abincin da za ku ci da abin shan da za ku sha. Me ya sa zai gan ku da rãma da samari abokanku? Sarki zai fille kaina saboda ku."
\s5
\v 11 Sa'annan Daniyel ya yi magana da mai aikin da babban jami'in ya sa ya kula da su Daniyel, Hananiya, Meshayel da Azariya.
\v 12 Ya ce, "Idan ka yarda ka gwada mu bayinka na kwana goma, ka riƙa ba mu kayan lambu mu ci da kuma ruwa mu sha.
\v 13 Sa'annan ka gwada baiyanarmu da baiyanar samarin da ke cin abincin sarki, ka yi mana mu bayinka, bisa ga abin da ka gani."
\s5
\v 14 Sai mai hidimar ya yarda ya yi haka, ya gwada su kwana goma.
\v 15 A ƙarshen kwanaki goman sai baiyanarsu ta fi lafiya, kuma suka fi duk samarin da ke cin abincin sarki annuri.
\v 16 Sai mai hidimar ya ɗauke abincinsu da ruwan inabinsu ya ba su kayan lambu kawai.
\s5
\v 17 Waɗannan samari huɗu, Allah ya ba su ilimi da ganewa da fahimtar dukkan adabi da hikima, Daniyel kuma ya na iya gane kowanne irin wahayi da mafarkai.
\v 18 Da lokacin da sarki ya bayar a kawo su wurinsa ya yi, sai babban mai hidimar ya kawo su ciki gaban Nebukadnezza.
\s5
\v 19 Sarki ya yi magana da su, a cikin dukkan taron babu wanda za a iya kwatanta shi da Daniyel, Hananiya, Meshayel da Azariya. Suka tsaya a gaban sarki, a shirye su yi masa hidima.
\v 20 A cikin kowacce tambaya ta hikima da ganewa da sarki ya tambaye su, ya tarar sun fi dukkan masu dũba da masu magana da kurwa waɗanda ke cikin dukkan mulkinsa har sau goma.
\v 21 Daniyel ya zauna can har shekara ta fari ta Sairus.
\s5
\c 2
\cl Sura 2
\p
\v 1 A cikin shekara ta biyu ta mulkin Nebukadnezza, sai ya yi mafarkai. Hankalinsa ya tashi, bai iya yin barci ba.
\v 2 Sarki ya umarta cewa masu dũba da masu cewa suna magana da kurwa su zo. Haka kuma ya kira masu sihiri da mutane masu hikima. Ya so su ba shi bayanin mafarkansa. Sai suka zo suka tsaya a gaban sarki.
\s5
\v 3 Sarki ya ce da su, "Na yi mafarki, kuma raina ya ƙagara ya san ma'anar mafarkin."
\v 4 Sai mutanen masu hikima suka yi wa sarki magana cikin harshen Aremiyanci, "Ranka ya dade ya sarki! Ka gaya mana mafarkin, bayinka kuwa za su baiyana maka ma'anarsa."
\s5
\v 5 Sai sarki ya amsawa masu hikimar da cewa, "Wanann maganar a yanke take. Idan ba ku baiyana mani mafarkin da fassararsa ba, za a yayyaga jukkunanku a mayar da gidajenku kufai.
\v 6 Amma idan kun baiyana mani mafarkin da ma'anarsa, za ku karɓi kyautai daga gare ni, da lada da ɗaukaka. To sai ku gaya mani mafarkin da ma'anarsa."
\s5
\v 7 Suka sake amsawa suka ce, "Bari sarki ya gaya mana mafarkin, mu bayinsa mu kuwa za mu baiyana maka ma'anarsa."
\v 8 Sai sarki ya amsa, "Tabbas na sani kuna bukatar ƙarin lokaci, saboda kun ga shawarata ta yi tsauri akan wannan abu.
\v 9 Amma idan ba ku faɗa mani mafarkin ba, hukunci ɗaya ne a kanku. Kun shirya ku gaya mani ƙaryar da kuka shirya ku ka yarda a kanta da maganganu na ruɗi, har sai na canza shawarata. To ku gaya mani mafarkin, sa'annan zan sani za ku ba ni bayaninsa."
\s5
\v 10 Masu hikima suka amsa wa sarki, "Ba wani mutum a duniya da zai iya biyan bukatar sarki. Ba wani babban sarki mai iko da ya taɓa bukatar irin wannan abu daga masu dũba, ko daga wani mai magana da kurwa, ko mutum mai hikima.
\v 11 Abin da sarki ya ke bukata yana da wuya, ba wanda zai iya gaya wa sarki shi sai dai alloli, su kuma ba a cikin mutane suke zama ba."
\s5
\v 12 Wannan ya sa sarki ya ji haushi ya hasala ƙwarai, ya bada ummurni a hallaka dukkan masu hikima na Babila.
\v 13 Shela ta fita a kashe dukkan waɗanda aka sani su masu hikima ne. Saboda wannan doka, aka nemo Daniyel da abokansa domin a kashe su.
\s5
\v 14 Sai Daniyel cikin ladabi da hikima ya amsa wa Ariyok shugaban masu tsaron sarki, wanda ya zo ya kashe dukkan waɗanda aka san masu hikima ne a cikin Babila.
\v 15 Daniyel ya tambayi jami'in sarkin, "Me ya sa shelar sarki ta zo da sauri haka?" Ariyok ya gaya wa Daniyel abin da ya faru.
\v 16 Sai Daniyel ya roƙi a ba shi lokaci ya zo wurin sarki domin ya kawo wa sarki fassara.
\s5
\v 17 Sai Daniyel ya koma gida ya gaya wa su Hananiya, Meshayel da Azariya, abin da ya faru.
\v 18 Ya roƙe su su nemi jinƙai daga Allah na sama akan wannan asiri domin kada a kashe su tare da sauran mutanen Babila waɗanda aka sani saboda da hikimarsu.
\s5
\v 19 A wannan daren a ka baiyana wa Daniyel asirin a cikin ruya. Sa'annan Daniyel ya yabi Allah na sama
\v 20 ya ce, "A yabi sunan Allah har abada abadin; gama hikima da iko nasa ne.
\s5
\v 21 Shi ne mai canza lokatai da zamanai; ya kan cire sarakuna ya sa waɗansu sarakunan akan mulkokinsu. Ya kan ba da hikima da ilimi ga masu fahimta.
\v 22 Yakan baiyana ɓoyayyun abubuwa masu zurfi gama shi ya san abin da ke cikin duhu, haske kuwa tare da shi ya ke zama.
\s5
\v 23 Allah na ubannina, na gode maka na yabe ka saboda hikima da iko da ka ba ni. Yanzu ka sanar da ni abin da muka roƙe ka; ka kuma sa mun san abin da ya dami sarki."
\s5
\v 24 Sai Daniyel ya shiga wurin Ariyok (wanda sarki ya sa ya kashe kowanne mai hikima a cikin Babila). Ya je ya ce masa, "Kada ka kashe masu hikima na cikin Babila. Ka kai ni wurin sarki zan nuna masa fassarar mafarkinsa."
\s5
\v 25 Nan da nan kuwa Ariyok ya kawo Daniyel gaban sarki ya ce, "Na samo wani daga cikin 'yan bauta na Yahuda wanda zai baiyana wa sarki ma'anar mafarkinsa."
\v 26 Sarki ya cewa Daniyel (wanda a ke kira Beltishazza), "Ko ka iya gaya mani mafarkin da na gani da ma'narsa?"
\s5
\v 27 Daniyel ya amsa wa sarki ya ce, "Asirin da sarki ya tambaya game da shi masu hikima ba zasu iya baiyana shi ba, ko masu magana da kurwa da masu dũba, ko masana taurari.
\v 28 Duk da haka, akwai Allah wanda ya ke zaune a cikin sammai, wanda ya ke baiyana asirai, kuma ya sanar da kai, ya sarki Nebukadnezza, abin da zai faru a cikin kwanaki masu zuwa. Wannan shi ne mafarkinka da ruyar ranka lokacin da ka ke kwance akan gadonka.
\s5
\v 29 Amma kai, ya sarki, zace-zacenka sa'ada ka ke kan gadonka game da abubuwan da zasu faru nan gaba ne, kuma shi wanda ya ke baiyana asirai ya sanar da kai abin da ya kusa faruwa,
\v 30 A gare ni ba a baiyana mani wannan asiri domin na fi kowanne mutum da ke rayuwa hikima ba. An baiyana mani asirin ne domin, kai, sarki ka gane ma'anar, domin kuma ka gane zurfin tunanin da ke cikin tunane-tunanenka da ke da zurfi a cikinka.
\s5
\v 31 Sarki, ya dubi sama ya ga siffa mai girma. Wannan siffa mai girma da haske, ta tsaya a gabanka. Haskenta yana da ban tsoro.
\v 32 Kan sifar an yi shi da zinariya mai kyau. Ƙirjinta da hannuwanta na azurfa ne. Tsakiyarta da cinyoyinta an yi su da tagulla,
\v 33 ƙafafunta kuma an yi su da ƙarfe. Tafin sawunta kuma an yi su rabi da ƙarfe rabi da yumɓu.
\s5
\v 34 Da ka duba sama, an saro wani dutse, ko da ya ke ba da hannun mutum ba ne, ya kuma bugi siffar ya farfasa ƙafafunta na ƙarfe da na yumɓu.
\v 35 Sa'annan ƙarfen da yumɓun da baƙin ƙarfen da azurfar da zinariyar aka farfasa su gaba ɗaya suka zama kamar ɗan maraƙi a masussuka lokacin kaka. Iska ta kwashe su ba ta rage komai ba. Amma dutsen da ya faɗo ya farfasa siffar ya zama babban dutse ya cika duniya.
\s5
\v 36 Wannan shi ne mafarkinka. Yanzu zamu gaya maka ma'anarsa.
\v 37 Kai, sarki, kai ne sarkin sarakuna waɗanda Allah na sama ya ba su mulki, da iko da ƙarfi da martaba.
\v 38 Ya bayar da wurin da mutane ke zaune a hannunka. Ya kuma bada dabbobi da tsuntsayen sama a cikin hannunka, ya sa ka yi mulki akan su dukka. Kai ne kan zinariya na siffar nan.
\s5
\v 39 Bayanka, wani mulki zai taso wanda bai kai kamar ka ba, daga nan mulki na uku na baƙin ƙarfe zai yi mulkin dukkan duniya.
\s5
\v 40 Mulki na huɗu zai zo, mai ƙarfi kamar ƙarfe, saboda ƙarfe ya farfasa kome ya lalata su. Zai farfasa duk waɗannan abubuwa ya lalata su.
\s5
\v 41 Kamar yadda ka gani an yi tafin ƙafafun rabi da yumɓu rabi da ƙarfe, mulkin zai rabu kenan; wani sashi zai sami ƙarfi kamar ƙarfe, kamar yadda ka ga an gauraya ƙarfe da yumɓu mai taushi.
\v 42 Kamar yadda aka yi yatsun ƙafafun rabi da ƙarfe, rabi da yumɓu, haka mulkin zai zama wani sashi da ƙarfi wani sashi da rauni.
\v 43 Kamar yadda ka ga ƙarfe gauraye da yumɓu mai taushi, haka mutanen za su zama a gauraye; ba za su tsaya tare ba kamar yadda ƙarfe ba zai gaurayu da yumɓu ba.
\s5
\v 44 A cikin kwanakin waɗannan sarakunan, Allah na sama zai tayar da wani mulkin da ba za a iya rushe shi ba, waɗansu mutane ba zasu iya cin nasara akan sa ba. Zai farfasa sauran mulkokin gutsu-gutsu ya kawo ƙarshensu, shi kuwa zai kasance har abada.
\v 45 Kamar yadda ka ga an saro dutse daga babban dutse, amma ba da hannuwan mutum ba. Ya farfasa ƙarfen da baƙin ƙarfe da yumɓu da azurfa da zinariya gutsu-gutsu. Allah Mai Girma ya sanar da kai, ya sarki, abin da zai faru bayan wannan. Mafarkin gaskiya ne, wannan bayanin kuma tabbas ne."
\s5
\v 46 Nebukadnezza sarki ya faɗi da fuskarsa a ƙasa a gaban Daniyel ya girmama shi; ya ba da ummurni a yi bayarwa dominsa a ba shi turare.
\v 47 Sarkin ya cewa Daniyel, "Hakika Allahnka shi ne Allahn alloli, Ubangijin sarakuna, wanda ya ke baiyana asirai, gama ka iya ka baiyana wannan asiri."
\s5
\v 48 Sai sarki ya sa Daniyel ya zama mai martaba sosai, ya ba shi kyautai da yawa na mamaki. Ya mai da shi mai mulki a bisa dukkan gundumar Babila. Daniyel ya zama babban gwamnan masu hikima na Babila.
\v 49 Daniyel ya roƙi sarki, sarkin kuma ya naɗa Shadrak, Meshak da Abednego su zama masu gudanarwa a gundumar Babila. Amma Daniyel ya zauna a fãdar sarki.
\s5
\c 3
\cl Sura 3
\p
\v 1 Nebukadnezza sarki ya yi siffa ta zinariya wadda tsawonta ƙafa tasa'in ne fadinta kuma ƙafa tara, ya ƙafa ta a Filin Dura wanda ke a gundumar Babila.
\v 2 Sai Nebukadnezza ya aika da 'yan kai saƙo, a tattaro shugabanni, masu riƙe da sassa da yankuna da gundumomi da masu ba da shawara da masu ajjiya da masu shari'a da alƙalai da dukkan manyan jami'an gundumomi, su zo wurin ƙaddamar da siffar da ya kafa.
\s5
\v 3 Sai shugabannin sassa da yankuna da gundumomi da masu bada shawara da masu ajjiya da masu shari'a da alƙalai da dukkan manyan jami'an gundumomi, suka tattaru domin ƙaddamar da siffar da Nebukadnezza ya kafa. Suka tsaya a gaban siffar.
\v 4 Sa'annan aka yi shela mai ƙarfi, "An ummurce ku, ku mutane da al'ummai da harsuna,
\v 5 a lokacin da ku ka ji ƙarar kahonni da sarewa da garaya da molo da caki da kuge da algaita da kowanne irin kayan kiɗa, sai ku faɗi warwas a gaban siffar zinariya wadda Nebukadnezza sarki ya kafa.
\s5
\v 6 Duk wanda bai faɗi ya yi sujada ba, a wannan lokacin, za a jefa shi cikin tanderu mai ci da wuta."
\v 7 To lokacin da dukkan mutane suka ji ƙarar ƙahonni da sarewa da garaya da molo da caki da kuge da algaita da kowanne irin kayan kiɗa, dukkan mutane da al'ummai da harsuna suka faɗi warwas a wurin siffar zinariya wadda Nebukadnezza sarki ya kafa.
\s5
\v 8 To sai waɗansu Kaldiyawa suka zo suka kawo sãra akan Yahudawa.
\v 9 Suka ce da Nebukadnezza sarki, "Ranka ya daɗe, ya sarki!
\v 10 Kai sarki, kai ne ka ba da ummurni, dukkan wanda ya ji ƙarar ƙahonni da sarewa da garaya da molo da caki da kuge da algaita da kowanne irin kayan kiɗa, dole ya faɗi warwas a gaban siffar zinariya.
\s5
\v 11 Duk wanda bai faɗi ya yi sujada ba, dole za a jefa shi cikin tanderu mai ci da wuta.
\v 12 To akwai waɗansu Yahudawa da ka naɗa su lura da harkokin gundumar Babila; sunayensu kenan, Shadrak, Meshak da Abednego. Sarki, waɗannan mutane ba su damu da kai ba. Ba za su yi wa allolinka sujada ba, balle su bauta masu, ko kuma su faɗi warwas a gaban siffar zinariya wadda ka kafa."
\s5
\v 13 Sai Nebukadnezza cike da fushi da hasala, ya ummurta a kawo su Shadrak, Meshak da Abednego a wurin sa. Sai aka kawo waɗannan mutane gaban sarki.
\v 14 Nebukadnezza yace da su, "Ko kun yi shawara, ya Shadrak, Meshak da Abednego, ba za ku yi sujada ga allolina ba ko ku faɗi warwas a gaban siffar zinariya wadda na kafa ba?
\s5
\v 15 Yanzu idan kuna shirye -lokacin da ku ka ji ƙarar ƙahonni da sarewa da giraya da caki da kuge da algaita da kowanne irin kayan kiɗa - ku faɗi warwas a gaban siffa wadda na kafa, ba komai. Amma idan ba za ku yi sujada ba, yanzun nan za a jefa ku cikin tanderu mai ci da wuta. Wanne allah ne zai iya kuɓutar da ku daga hannuna?"
\s5
\v 16 Shadrak, Meshak da Abedinego suka amsa wa sarki, "Nebukadnezza, ba mu da bukata mu amsa maka a kan wannan magana.
\v 17 Idan da wata amsa ita ce, Allahn da muke bauta wa zai iya tsare mu lafiya daga cikin tanderu mai ci da wuta, kuma zai kuɓutar da mu daga hannunka, ya sarki.
\v 18 Amma idan ma ba haka ba, bari ka sani ya sarki, ba za mu bauta wa allolinka ba, kuma ba za mu faɗi warwas a gaban siffar zinariya wadda ka kafa ba."
\s5
\v 19 Sai Nebukadnezza ya cika da hasala; yanayin fuskarsa ya canza game da Shadrak, Meshak da Abednego. Ya ba da ummurni a zuga tanderun har sau bakwai fiye da yadda aka saba zugawa.
\v 20 Sa'annan ya ummurci waɗansu ƙarfafa cikin sojojinsa su ɗaure su Shedrak, Meshak da Abedinego, su jefa su cikin tanderun mai ci da wuta.
\s5
\v 21 Aka ɗaure su saye da tufafinsu da alkyabbunsu da rawunansu da sauran kayan jikinsu, aka jefa su cikin tanderun mai ci.
\v 22 Saboda ummurnin sarki ya yi tsauri kuma haka aka yi, tanderun ya yi zafi ƙwarai, harshen wuta ya kashe mutanen da suka ɗauki su Shedrak da Meshak da Abednego.
\v 23 Waɗannan mutane uku, wato, Shedrak, Meshak da Abednego, suka faɗa a cikin tanderun mai ci da wuta a ɗaure.
\s5
\v 24 Sai Nebukadnezza ya cika da mamaki, ya tashi da sauri. Ya tambayi mashawartansa, "Ba mutane uku mu ka jefa a ɗaure cikin wuta ba?" Suka amsa wa sarki suka ce, "Tabbas haka ne, ya sarki."
\v 25 Ya amsa ya ce, "Na ga mutane huɗu ba a ɗaure ba suna yawo a cikin wutar, kuma ba abin da ya same su. Hasken na huɗun kamar na ɗan alloli."
\s5
\v 26 Sai Nebukadnezza ya zo kusa da ƙofar tanderun mai ci da wuta ya yi kira, "Shedrak, Meshak, da Abednego bayin Allah Mafi Ɗaukaka, ku fito! Ku zo nan!" Sai su Shadrak, Meshak da Abednego suka fito daga cikin wutar.
\v 27 Shugabannin sassa da yankuna da gundumomi da suka taru a wurin suka ga waɗannan mutane. Wuta ba ta ƙona jukkunansu ba; gashin kansu bai taɓu ba; kuma ba abin da ya sami tufafinsu; kuma babu ƙaurin wuta a jikinsu.
\s5
\v 28 Nebukadnezza yace, "Bari mu yabi Allah na Shadrak, Meshak da Abednego wanda ya aiko ɗan saƙonsa ya ba bayinsa saƙo. Sun gaskata da shi lokacin da ba su bi dokata ba, sun ba da jikkunansu a maimakon su yi sujada ga wani allah ko su faɗi warwas a gabansa sai dai Allahnsu kaɗai.
\s5
\v 29 Saboda haka na ba da ummurni ko dukkan mutane ko al'umma ko harshen da ya yi magana gãba da Allah na Shadrak, Meshak da Abednego dole za a yayyaga su a mai, da gidajensu juji saboda ba wani allah da zai iya yin ceto kamar wannan."
\v 30 Sa'annan sarki ya ƙara wa su Shadrak, Meshak da Abednego girma a cikin gundumar Babila.
\s5
\c 4
\cl Sura 4
\p
\v 1 Sarki Nebukadnezza ya aika wannan umarni ga dukkan mutane da al'ummai, da harsuna waɗanda ke zaune a duniya: "Bari salamarku ta ƙaru.
\v 2 Na ga ya yi kyau in faɗa maku akan waɗansu abubuwan alamu da al'ajabai da Maɗaukaki ya yi mani.
\v 3 Ya ya girman alamunsa, kuma ya ya girman al'ajabansa! Sarautarsa har abada ce kuma mulkinsa daga zamani zuwa zamani ne."
\s5
\v 4 Ni, Nebukadnezza ina zaune cike da murna a cikin gidana, ina nishaɗi a fãdata.
\v 5 Sai na yi mafarki wanda ya sa na ji tsoro. lokacin da na ke kwance, kamanni da wahayin da na gani ya dami tunanina ƙwarai.
\v 6 Saboda haka sai na ummarta a kirawo mani dukkan masu hikima na Babila don su yi mani fassarar mafarkin.
\s5
\v 7 Sai masu sihiri da waɗanda ke cewa suna magana da matattu da masu hikima da masu duba suka zo. Na faɗa masu mafarkin, amma ba su iya fassara mani ba.
\v 8 Sai daga baya Daniyel ya zo - wanda a kira Beltishazza wato irin sunan allahna, a gare shi kuwa akwai ruhun alloli tsarkaka-- na faɗa masa mafarkin.
\v 9 Beltishazza, shugaban masu sihiri, na sani ruhun alloli tsarkaka yana cikinka kuma ba wani asirin da zai fi ƙarfin ganewarka. Ka faɗa mani mene ne na gani a mafarkina kuma me ya ke nufi.
\s5
\v 10 Waɗannan su ne alamun da na gani a cikin tunanina lokacin da nake kwance akan gadona: Na duba, akwai wani itace a tsakiyar duniya, yana da tsayi ƙwarai da gaske.
\v 11 Itacen ya yi girma ya zama mai ƙarfi. ƙwanƙolinsa ya kai sammai, kuma ana iya ganinsa har duk ƙarshen duniya.
\v 12 Yana da ganyaye masu kyau, 'ya'yansa kuwa suna da yawa, a kansa kuma akwai abinci domin kowa. Namomin jeji suka sami inuwa a ƙarƙashinsa, tsuntsayen sama kuma suka zauna a rassansa. Dukkan masu rai suna ci daga gare shi.
\s5
\v 13 A tunaninna da nake kwance akan gadona na ga wani tsattsarkan mai saƙo ya sauko daga sammai.
\v 14 Sai ya yi magana da ƙarfi, ya ce, 'A sare itacen, a kuma daddatse rassansa, a zage ganyayensa kakaf, a kuma warwatsar da 'ya'yansa. Bari namomin jeji su yi gudu daga ƙarƙashinsa, tsutsaye kuma su tashi daga rassansa.
\s5
\v 15 A bar kututturen da saiwoyinsa a cikin ƙasa, ɗaure da sarƙar baƙin ƙarfe da tagulla, a cikin tsakiyar ɗanyar ciyawar saura. A bar shi ya jiƙe da raɓa daga sammai. A bar shi ya zauna da namomi a cikin tsirai na ƙasa.
\v 16 Bari tunaninsa ya canja daga tunanin mutum, a kuma ba shi tunanin irin na dabba zai zauna a wannan hali har shekaru bakwai.
\s5
\v 17 Wannan ita ce shawara da hukuncin da ɗan saƙon ya faɗa. Shawarar da masu tsarki suka zartar don waɗanda ke da rai su sani Maɗaukaki ne ke sarautar mulkokin 'yan adam, ya kan kuma ba da ita ga wanda ya ga dama a maimakonsu, har ma da mutane masu tawali'u.'
\v 18 Ni, sarki Nebukadnezza, na yi wannan mafarki. Yanzu kai, Beltishazza, ka faɗa mani ma'anarsa, domin dukkan masu hikima na cikin mulkina ba su iya faɗa mani ma'anar ba. Amma kai za ka iya yi, gama ruhun alloli tsakaka yana cikinka."
\s5
\v 19 Sai Daniyel, wanda aka lakaba wa suna Beltishazza, ya tsaya zugum da ɗan daɗewa, tunaninsa ya ba shi tsoro. Sarki yace, "Beltishazza, kada ka bar mafarkin ko ma'anarsa ya ba ka tsoro." Beltishhazza ya amsa, "Ya shugabana, bari mafarkin ya zama domin waɗanda ke gãba da kai ne; bari ma'anarsa kuma ta zama ta masu gãba da kai.
\s5
\v 20 Itacen nan da ka gani - wanda ya yi girma ya kuma yi ƙarfi, wanda ƙwanƙolinsa kuma ya kai sammai, har ma wanda za a iya ganinnsa daga ko'ina a duniya -
\v 21 wanda ke da ganyaye masu kyau, wanda kuma har ya yi 'ya'ya jingim, don a cikinsa akwai abinci domin kowa, har ma namomin jeji sun sami inuwa a ƙarƙashinsa, wanda tsuntsaye sammai kuma suka zauna a kai -
\v 22 wannan itacen kuwa kai ne, ya sarki, kai ne ka yi girma ka ƙasaita. Girmanka kuma ya kai har sammai, mulkinka kuma ya kai har iyakar duniya.
\s5
\v 23 Kai, sarki, ka ga tsattsarkan ɗan saƙo na saukowa daga sama yana cewa, 'A sare itacen nan, a ragargaje shi, amma a bar kututturen da saiwoyinsa cikin ƙasa, a ɗaure da sarƙar ƙarfe da kuma tagulla, a tsakiyar ɗanyar ciyawar saura. A bar shi can ya jiƙe da raɓa daga sammai. Bari ya zauna tare da namomin jeji har shekaru bakwai.'
\s5
\v 24 Wannan ita ce fassarar, sarki. Wannan hukunci ne na Maɗaukaki ya same ka, shugabana sarki.
\v 25 Za a kore ka daga cikin mutane, zaka kuma zauna tare da namomin jeji. Za ka ci ciyawa kamar sa, zaka jiƙe da raɓa daga sammai, har shekaru bakwai sun cika lokacin nan za ka sani Maɗaukaki ne ke sarautar mulkin 'yan adam, kuma ya kan ba da ita ga kowa yadda ya ga dama.
\s5
\v 26 Kamar yadda aka ummarta a bar kututturen itace da saiwoyinsa, a wannan hanyar mulkinka zai dawo gare ka daga lokacin da ka san Mai sama ne ke mulki.
\v 27 Saboda haka, ya sarki, bari shawarata ta sami karɓuwa gare ka. Ka daina zunubi, ka yi abin da ke da kyau. Ka juyo daga muguntarka ta wurin aikata alheri ga waɗanda ake wulaƙantawa, wataƙila za a ƙara maka tsawon kwanakinka da salama."
\s5
\v 28 Dukkan waɗannan abubuwa sun kasance ga sarki Nebukadnezza.
\v 29 Bayan wata goma sha biyu lokacin da ya ke tafiya akan benen fãdar Babila,
\v 30 sai ya ce, "Ashe wannan ba ita ce babbar Babila ba, wadda ni da kaina na gina domin zama fãdar sarauta, don darajar ɗaukakata ba?"
\s5
\v 31 Lokacin da kalmomi ke fita daga leɓunan sarki, sai ga murya daga sama: "Sarki Nebukadnezza, ana sanar da kai an ɗauke wannan mulkin daga gare ka.
\v 32 Za a kuma kore ka daga cikin mutane, gidanka kuwa zai kasance tare da namomin jeji. Za ka ci ciyawa kamar sa. Shekaru bakwai cur zasu wuce sa'an nan za ka gane Maɗaukaki ne ke mulkin mulkokin mutane, yana kuma ba da su ga wanda ya ga dama."
\s5
\v 33 Wannan hukuncin akan Nebukadnezza ya tabbata nan take. An kore shi daga cikin mutane. Ya shiga cin ciyawa kamar sa, jikinsa kuwa ya jiƙe da raɓa daga sammai. Gashinsa kuma ya yi tsawo kamar gashin gaggafa, farotansa kuma suka yi tsawo kamar na shaho.
\s5
\v 34 A ƙarshen kwanakin ni, Nebukadnezza, sai na ɗaga idanuna sama, hankalina ya komo gare ni. "Na ɗaukaka Maɗaukaki, na yi yabo na kuma ɗaukaka shi wanda ke rayayye har abada. Gama mulkinsa madawwamin mulki ne, sarautarsa kuwa daga dukkan zamanai zuwa zamanai ne.
\s5
\v 35 Dukkan mazaunan duniya yana ɗaukan su kamar ba a bakin kome suke a gare shi ba; yakan yi yadda ya nufa a cikin rundunar sama da mazaunan duniya abin da ya yi masa dai-dai. Babu wanda zai iya hana wa ko ya ƙalubalance shi. Ba wanda zai ce da shi, 'Me ya sa ka yi wannan?"
\s5
\v 36 A lokacin nan hankalina ya komo gare ni, an mayar mani da sarautata da darajar mulkina. 'Yan majalisata da fãdawana suka dawo da mutuncina. Aka maido ni kan gadon sarautata, har ma an darajanta ni fiye da dã.
\v 37 Yanzu ni, Nebukadnezza, na ba da yabo da girma da ɗaukaka ga Sarkin samaniya, domin dukkan abubuwan da ya aikata masu kyau ne, al'amuransa kuma gaskiya ne. Ya kan ƙasƙantar da waɗanda ke da girmankai.
\s5
\c 5
\cl Sura 5
\p
\v 1 Sarki Belshazza ya yi babban liyafa domin manyan mutanensa, ya kuwa sha ruwan inabi a gaban dukkan su su dubu.
\v 2 A lokacin da Belshazza ya kurɓi ruwan inabin, sai ya umarta a kawo tasoshi na zinariya da na azurfa waɗanda Nebukadnezza ubansa ya ɗauko daga cikin haikali a Yerusalem, daga waɗanda shi kansa, da manyan mutanensa da matansa da ƙwaraƙwaransa za su sha.
\s5
\v 3 Barorinsa kuwa suka ɗauko waɗannan kayyayaki da aka kwaso su daga cikin haikali, gidan Allah, a Yerusalem. Sarki da manyan mutanensa da matansa da ƙwaraƙwarnsa suka sha a cikin su.
\v 4 Sun sha ruwan inabin sun yabi allolinsu waɗanda aka yi da zinariya da azurfa da tagulla da baƙin ƙarfe da katako da kuma dutse.
\s5
\v 5 A dai- dai wannan lokaci sai ga yatsun hannun mutum suka bayyana a gaban fitila da rubutu a kan shafen bangon fadar sarki. Sarki ya ga rabin hannun na rubutu.
\v 6 Sai fuskar sarki ta turɓune, tunaninsa ya razanar da shi; gaɓoɓinsa kuwa suka saki, gwiwoyinsa suka soma bugun juna.
\s5
\v 7 Sarki ya yi umarni da babbar murya a kawo masu cewa suna iya magana da matattu, da masu dabo da bokaye, da masu duba. Sarki ya ce da waɗannan da aka san su masu hikima ne a Babila, "Wanda duk ya bayyana wannan rubutu ya kuma faɗi ma'anarsa za a sa masa rigar shunayya, a kuma sa masa sarƙar zinariya a wuyansa. Zai zama da iko ya kuma zama na uku a cikin masu mulkin ƙasar."
\s5
\v 8 Sai dukkan waɗanda aka san masu hikima na sarki ne suka shigo, amma babu wanda ya iya karanta rubutun balle ya faɗa wa sarki ma'anarsa.
\v 9 Sarki Belshazza kuwa ya firgita ƙwarai, fuskarsa ta turɓune. Fãdawansa kuma duk suka ruɗe.
\s5
\v 10 Yanzu da sarauniya ta zo wurin babban liyafa domin abin da sarki da manyan fãdawansa suka ce. Sarauniya ta ce "Ran sarki, ya daɗe! Kada ka bar tunaninka ya sami damuwa. Kada kuma ka bar fuskarka ta turɓune.
\s5
\v 11 Ai, akwai wani mutum a cikin mulkinka wanda ke da ruhun alloli tsarkaka. A kwanakin ubanka, an iske haske da fahimi da hikima da ganewa kamar na alloli a cikinsa. Sarki Nebukadnezza, ubanka sarki, ya naɗa shi shugaba na masu sihiri, da kuma shugaban masu magana da matattu, da bokaye da masu dũba.
\v 12 Ya na da ruhu nagari, da ilimi da ganewa da fassarar mafarkai da bayyana ma'anar ka-cici-ka-cici, da warware al'amura masu wuya - waɗannan ƙwarewa aka sami wannan mutum wato Daniyel da su, wanda sarki ya lakaɓa wa suna Beltishazza. Yanzu sai ka kirawo Daniyel, shi kuwa zai faɗa maka ma'anar abin da aka rubuta."
\s5
\v 13 Sai aka kawo Daniyel a gaban sarki. Sarki ya cewa Daniyel, "Kai ne Daniyel ɗin nan, ɗaya daga cikin waɗanda aka ɗauko a Yahuda, wanda ubana sarki ya kawo daga Yahuda.
\v 14 Na ji labarinka, ruhun alloli tsarkaka na cikinka, haske da ganewa da mafificiyar hikima aka samu a cikinka tare.
\s5
\v 15 Yanzun nan mutanen da aka san su da hikima da waɗanda ke magana da matattu an kawo su gabana don su karanta wannan rubutu su kuma yi mani fassara, amma sun kasa faɗar ma'anar rabutun.
\v 16 Amma na ji kai kana iya fassara, ka kuma iya warware al'amura masu wuya. Yanzu idan fa ka iya karanta rubutun nan, har kuma ka iya faɗa mani ma'anarsa, za a sa maka rigar shunayya, a kuma sa maka sarƙar zinariya a wuyanka, za ka zama na uku a cikin masu mulkin ƙasar."
\s5
\v 17 Sai Daniyel ya amsa a gaban sarki, "Bar kyautarka don kanka, ka ba wani ladan. Duk da haka zan karanta rubutun a gare ka, ya sarki, zan kuma faɗa maka ma'anarsa.
\v 18 Ya sarki, Allah Maɗaukaki ya ba Nebukadnezza ubanka sarauta, da girma, da daraja, da martaba.
\v 19 Saboda girman da Allah ya ba shi, dukkan mutane, da al'ummai, da harsuna suka ji tsoronsa suna rawar jiki a gabansa. Ya kashe duk waɗanda ya ke so ya kashe, ya kuma bar waɗanda ya ke so ya bar su su rayu. Haka nan kuma ya kan ɗaukaka waɗanda ya ke so, ya kuma ƙasƙantar da waɗanda ya ga dama.
\s5
\v 20 Amma sa'ad da zuciyarsa ta kumbura, ruhunsa kuma ya taurare don haka sai ya yi girmankai, sai aka kore shi daga gadon sarautarsa, aka raba shi kuma da darajarsa.
\v 21 Aka kore shi daga cikin mutane, aka ba shi hali irin na dabba, ya kuma zauna tare da jakunan jeji. Yana ta cin ciyawa kamar sã. Jikinsa ya jiƙe da raɓa daga sammai har zuwa lokacin da ya gane ashe Allah Maɗaukaki ne ke mulkin 'yan'adam, ya kan kuma ba da shi ga wanda ya ga dama.
\s5
\v 22 Kai kuma ɗansa, Belshazza, ba ka ƙasƙantar da zuciyarka ba, duk da ka san wannan dukka,
\v 23 Sai ka ɗaukaka kanka kana nuna wa Ubangiji na sama girmankai. Tun daga gidansa suka kawo maka waɗannan abubuwa kai da fãdawanka, da matanka da ƙwaraƙwaranka ku ka sha ruwan inabi daga ciki, kuna yabon gumakan da aka yi da zinariya da na azurfa da na tagulla da baƙin ƙarfe da itace da dutse - gumakan da ba sa gani, ba su ji, ko su gane kome. Ba ka girmama Allah wanda ya ke riƙe da numfashinka a hannunsa ba, wanda kuma ya san dukkan hanyoyinka.
\v 24 Saboda haka ne Allah ya aiko da hannun da ya yi wannan rubutun.
\s5
\v 25 Wannan shi ne rubutun da aka yi: 'Mene, Mene, Tekel, da Pharsin.'
\v 26 Wannan ita ce ma'anar: 'Mene,' 'Allah ya sa kwanakin mulkinka sun ƙare.'
\v 27 'Tekel' 'an auna ka a ma'auni, aka tarar ka kasa.'
\v 28 'Peres,' 'an raba mulkinka, an kuma ba Mediyawa da Fashiyawa.'"
\s5
\v 29 Sai Belshazza ya ba da umarni, suka sawa Daniyel rigar shunayya. Aka sa masa sarkar zinariya a wuyansa, sarki kuma ya yi shela a kansa cewa yanzu shi ne mai iko na uku cikin masu mulkin ƙasar.
\v 30 A wannan dare aka kashe Belshazza, sarkin Babila,
\v 31 Dariyos Bamediye ya karɓi mulkin ya na da shekaru sittin da biyu.
\s5
\c 6
\cl Sura 6
\p
\v 1 Ya gamshi Dariyos ya naɗa dagatai 120 a masarautar domin su yi mulkin dukkan masarautar.
\v 2 Sama da su kuma ya naɗa manyan hakimai uku, Daniyel kuma na ɗaya daga cikin su. Waɗannan manyan hakimai an zaɓe su ne domin su riƙa duba ayyukan dagatan, domin kada sarki ya yi asara.
\v 3 Daniyel ya yi fice daga cikin manyan hakiman da kuma dagatan saboda yana da nagartaccen ruhu. Sarki yana shirin ya sanya shi bisa dukkan masarautar.
\s5
\v 4 Sai manyan hakiman da dagatan suka duba domin su sami kuskure a cikin aikin da Daniyel ya ke yiwa masarautar, amma ba su sami wata rashawa ko kasawa ba saboda shi mai aminci ne. Ba a sami wani kuskure ko watsi da aiki a cikinsa ba.
\v 5 Sai waɗannan mutane suka ce, "Bamu sami wani dalilin da zamu yi ƙarar wannan Daniyel ɗin ba sai dai ko mu sami wa ni abin tsayayya da shi game da shari'ar Allahnsa."
\s5
\v 6 Daga nan waɗannan hakimai da Dagatai suka kawo wani shiri a gaban sarki. Suka ce da shi, "Sarki Dariyos, ranka ya daɗe!
\v 7 Dukkan manyan hakiman masarautar, da dagatan gudumomi, da dagatan lardi, da mashawarta, da gwamnoni sun yi shawara a tsakaninsu sun ɗauki mataki cewa kai, sarki, ka fito da doka kuma ka tilastata, yadda duk wanda ya yi wani roƙo ga wa ni allah ko mutum cikin kwana talatin, sai dai gare ka kaɗai, sarki, wannan mutum tilas a jefa shi cikin ramin zakuna.
\s5
\v 8 Yanzu dai, sarki, ka fito da doka ka kuma sanya hannu a takardar yadda ba za a iya canza ta ba, kamar yadda aka umarta bisa ga shari'un Medeyawa da Fashiyawa, domin baza a iya sauya ta ba."
\v 9 Sai sarki Dariyos ya sa hannu a takardar ya maida dokar ta zama shari'a.
\s5
\v 10 Da Daniyel ya fahimci cewa an sanya hannu a takardar ta zama shari'a, sai ya tafi cikin gidansa (tagoginsa dai a buɗe suke a ɗakinsa na saman bene suna fuskantar Yerusalem), sai ya durƙusa bisa gwiwoyinsa, yadda ya saba sau uku a rana, ya yi addu'a ya kuma bada godiya a gaban Allahnsa, yadda ya ke yi a dã.
\v 11 Daga nan waɗannan mutane waɗanda suka shirya makircin tare suka ga Daniyel yana yin roƙe-roƙe da neman taimako wurin Allah.
\s5
\v 12 Sai suka zo wurin sarki suka yi masa magana game da dokarsa: Ashe ba ka kafa doka ba cewa duk wanda ya yi roƙo ga wani allah ko mutum a cikin kwanaki talatin, in ba gare ka kaɗai ba, ya sarki, tilas a jefa shi cikin ramin zakuna?" Sarkin ya amsa, "Al'amarin zaunannne ne, kamar yadda aka umarta bisa ga shari'ar Medeyawa da Fashiyawa; baza a iya sokewa ba."
\s5
\v 13 Sai suka amsa wa sarki, "Wannan Daniyel ɗin, wanda ke ɗaya daga cikin 'yan bauta da daga Yahuda, bai kula da kai ba, sarki, ko dokar da ka sa hannu. Yana addu'a ga Allahnsa sau uku a rana."
\v 14 Da sarkin ya ji haka, sai hankalinsa ya tashi sosai, sai ya ƙudura a ransa ya ceci Daniyel daga wannan hukunci. Ya yi ƙoƙari har zuwa faɗuwar rana ya ga ya ceci Daniyel.
\s5
\v 15 Sai waɗannan mutane waɗanda suka shirya makircin suka tattaru tare da sarki suka ce masa, "Ka sani, sarki, cewa shari'a ce ta Medeyawa da Fashiyawa, cewa babu wata doka ko umarni da sarki ya fito da shi da za a iya canzawa."
\s5
\v 16 Daga nan sarkin ya bada umarni, sai aka kawo Daniyel, aka kuma jefa shi cikin ramin zakunan. Sarkin ya cewa Daniyel, "Bari Allahnka, wanda ka ke bautawa babu fasawa, ya kuɓutar da kai."
\s5
\v 17 Aka kawo dutse aka rufe ramin, sai sarkin ya hatimce shi da zobensa na sanya hannu da kuma zobunan sanya hannun 'yan, majalisarsa yadda babu wani abin da za a canza game da Daniyel.
\v 18 Daga nan sarki ya koma fãdarsa ya yi azumi tsawon dare. Babu wani abin annashuwa da aka kawo a gabansa, barci kuma ya guje daga gare shi.
\s5
\v 19 Da gari ya waye sarkin ya tashi da sauri ya tafi ramin zakunan.
\v 20 Da ya matso kusa da ramin, ya yi kira ga Daniyel da muryar baƙinciki, "Daniyel, bawan Allah mai rai, ko Allahnka, wanda ka ke bautawa babu fasawa, ya iya cetonka daga zakunan?"
\s5
\v 21 Daga nan Daniyel ya ce da sarki, "Ran sarki, ya daɗe!
\v 22 Allahna ya aiko da manzonsa ya rufe bakunan zakunan, ba su kuma cutar da ni ba. Gama an same ni marar laifi a gabansa da kuma gabanka, sarki, ban kuma cutar da kai ba."
\s5
\v 23 Daga nan sarki ya yi murna ƙwarai. Ya bada umarni a fito da Daniyel daga ramin. Sai aka ciro Daniyel daga ramin. Babu wani abin cutarwa da ya same shi, saboda ya dogara ga Allahnsa.
\s5
\v 24 Sarkin ya bada umarni, sai aka kawo mutanen nan da suka zargi Daniyel aka kuma jefa su cikin ramin zakunan - dukka, da 'ya'yansu, da kuma matansu. Kafin su kai ƙasa, zakunan suka sha ƙarfinsu suka kakkarya ƙasusuwansu suka yi ragargaza su.
\v 25 Sai Sarki Dariyos ya rubuta zuwa ga dukkan mutane, da al'ummai da kuma harsuna da ke zaune a cikin dukkan duniya: "Bari salama ta ƙaru gare ku.
\s5
\v 26 Yanzu na kafa doka a dukkan mulkin masarautata mutane su yi rawar jiki su kuma ji tsoro a gaban Allahn Daniyel, gama shi ne Allah mai rai kuma ya dawwama har abada, sarautarsa kuwa ba za a rushe ba; mulkinsa kuwa za ya kasance har ƙarshe.
\v 27 Yana kiyaye mu yana kuɓutar da mu, yana yin alamu da al'ajibai a sama da kuma duniya; Ya kiyaye Daniyel daga ƙarfin zakuna."
\s5
\v 28 Daniyel kuwa ya wadata a zamanin mulkin Dariyos da mulkin Sairus bafashiye.
\s5
\c 7
\cl Sura 7
\p
\v 1 A shekara ta farko ta Belshazza sarkin Babila, Daniyel ya yi mafarki da wahayoyi a ransa da ya ke kwance bisa gadonsa. Sai ya rubuta abin da ya gani a mafarkin. Ya rubuta al'amura mafi muhimmanci:
\v 2 Daniyel ya bayyana cewa, "A cikin wahayina na dare sai na ga iskokin sama huɗu suna motsa babban teku.
\v 3 Manyan dabbobi huɗu, kowanne ya sha daban da ɗayan, suka fito daga cikin tekun.
\s5
\v 4 Ɗayan ya yi kama da zaki amma yana da fukafukai kamar gaggafa. lokacin da nake kallo, sai aka yage fukafukansa aka kuma ɗaga shi sama aka sa ya tsaya bisa ƙafafu biyu, kamar mutum.
\v 5 Daga nan akwai dabba ta biyu, kamar damisa, a sunkuye kuma; tana da haƙarƙari uku a tsakiyar haƙoranta a cikin bakinta. Aka ce mata, 'Tashi ki lanƙwame mutane da yawa.'
\s5
\v 6 Bayan wannan na sake dubawa. Akwai wata dabbar kuma, kamanninta kamar damisa. Bisa bayanta tana da fukafukai huɗu kamar fukafukan tsuntsu, tana kuma da kawuna huɗu. Aka ba ta ikon yin mulki.
\v 7 Bayan wannan kuma na gani a wahayina na dare dabba ta huɗu, mai ban razana, da ban tsoro, kuma mai ƙarfi ƙwarai. Tana da babban haƙorin ƙarfe; tana haɗiyewa, tana karyawa rugu-rugu, tana kuma tattake abin da ya rage da ƙafafunta. Ta bambanta da sauran dabbobin, kuma tana da ƙahonni goma.
\s5
\v 8 Yayin da nake yin la'akari da ƙahonnin, dana duba sai naga wani ƙaho ya fito daga cikinsu, ƙaramin ƙaho. Uku daga cikin ƙahonnin aka daga jijiyoyinsu. A wannan ƙaho na ga idanu kamar idanun mutum da kuma bakin da ke fahariya game da manyan abubuwa.
\s5
\v 9 Da na duba, sai na ga an shirya kursiyoyi a waje ɗaya, sai Mai dogon zamani ya zauna. Suturarsa fari fat kamar ƙanƙara, gashin kansa kuwa kamar farin ulu. Kursiyinsa harsunan wuta ne, gargarensu kuwa suna ci da wuta.
\s5
\v 10 Ƙoramar wuta na fitowa daga gabansa; miliyoyi na bauta masa, miliyan ɗari kuma na tsaye a gabansa. Ana zaman kotu, aka kuma buɗe litattafai.
\s5
\v 11 Na ci gaba da dubawa saboda maganganun fankama da ƙahon ke furtawa. Ina kallo lokacin da aka kashe dabbar, aka lalatar da jikinta, aka kuma miƙa ta domin a ƙone ta.
\v 12 Sauran dabbobin huɗu kuwa, ikonsu na yin mulki aka ɗauke shi, amma aka ƙarawa rayukansu tsawon kwanaki na wani lokaci.
\s5
\v 13 A cikin wahayoyina na daren nan, sai na ga wani na zuwa da gizagizan sama kamar ɗan mutum; ya zo wurin Mai dogon zamani ya gabatar da kansa a gabansa.
\v 14 Ikon yin mulki da ɗaukaka da ikon sarauta aka bayar a gare shi yadda dukkan mutane, da al'ummai, da harsuna zasu bauta masa. Ikonsa na mulki madawwamin iko ne da ba zai shuɗe ba, masarautarsa kuwa ba za a taɓa iya rusawa ba.
\s5
\v 15 Ni kuwa, Daniyel, ruhuna ya damu a cikina, wahayoyin da na gani kuwa a cikin raina suka dame ni.
\v 16 Sai na kusanci ɗaya daga cikin waɗanda ke tsaye a wurin na kuma tambaye shi ya nuna mani ma'anar waɗannan abubuwa.
\s5
\v 17 Waɗannan manyan dabbobin, guda huɗu, sarakuna huɗu ne da zasu taso a duniya.
\v 18 Amma tsarkakan mutanen Mafi Girma zasu karɓi masarautar, zasu kuma mallake ta har abada abadin.'
\s5
\v 19 Sai kuma na so in ƙara sani game da dabbar nan ta huɗu - ta bambanta sosai da sauran kuma tana da ban razana da haƙoranta na ƙarfe da kofatun tagulla; tana cinyewa, tana karyawa rugu-rugu, ta kuma tattake abin da ya rage da ƙafafunta.
\v 20 Na so in sami sani game da ƙahonnin goma da ke a kanta, game kuma da ƙahon ɗaya da ya tsiro, wanda kuma a gabansa ƙahonni uku suka faɗi. Na so in sami sani game da ƙahon da ke da idanu da kuma game da bakin da ke fahariyar manyan abubuwa wanda kuma ya ke ganin kamar ya fi abokan tarayyarsa girma.
\s5
\v 21 Lokacin da nake kallo, sai wannan ƙaho ya yaƙi tsarkakan mutane yana kuma kayar da su
\v 22 har sai da Mai dogon zamani ya zo, an kuma bayar da hukunci ga tsarkakan mutane na Mafi Girma. Daga nan lokaci ya zo inda tsarkakan mutanen suka karɓi sarautar.
\s5
\v 23 Wannan ne abin da mutumin nan ya faɗa, 'Dabbar nan ta huɗu kuwa, zata kasance masarauta ta huɗu a duniya wadda zata sha bamban da dukkan sauran masarautun. Za ta cinye dukkan duniya, ta tattake ta ta kuma karya ta rugu-rugu.
\v 24 Ƙahonnin goma kuwa, daga cikin wannan masarauta sarakuna goma ne za su taso, wani kuma zai taso bayan su. Zai sha bamban da waɗanda suka wuce, zai kuma yi nasara da sarakunan uku.
\s5
\v 25 Zai furta maganganun tsayayya da Mafi Girma zai kuma tsananta wa tsarkaka mutanen Allah Mafi Girma. Zai yi ƙoƙarin canza shagulgula da kuma shari'a. Za a bayar da waɗannan abubuwa cikin hannunsa har shekara ɗaya, shekaru biyu, da kuma rabin shekaru.
\v 26 Amma zaman kotu zai ci gaba, za a kuma ɗauke ikon sarautarsa domin a gama da shi a kuma lalatar da shi a ƙarshe.
\s5
\v 27 Masarautar da mulkin, da kuma girman masarautun da ke ƙarƙashin dukkan sama, za a bayar ga mutane waɗanda ke tsarkakan mutanen Mafi Girma. Masarautarsa madawwamiyar masarauta ce, dukkan sauran masarautu kuma za su bauta masa su kuma yi masa biyayya.'
\v 28 Ga ƙarshen al'amarin. Ni kuwa, Daniyel, tunane-tunanena sun motsa ni sosai fuskata kuwa ta canza kamanni. Amma na ajiye waɗannan abubuwa a gare ni."
\s5
\c 8
\cl Sura 8
\p
\v 1 A cikin shekara ta uku ta mulkin Sarki Belshazza, Ni, Daniyel, wahayi ya bayyana a gare ni (baya ga wanda ya bayyana a gare ni da farko).
\v 2 A cikin wahayin na gani, yayin da nake dubawa, cewa ina cikin fãdar Susa a gundumar Ilam. Na gani a wahayi cewa ina bakin Rafin Ulai Kanal.
\s5
\v 3 Na duba sama sai na ga rago a gabana mai ƙahonni biyu, yana tsaye bakin rafin. Ƙaho ɗaya ya fi ɗaya tsawo, amma wanda ya fi tsawon girmansa a hankali ne fiye da gajeren har ya zo ya zarce shi a tsawo.
\v 4 Sai na ga ragon na bankawa yamma, daga nan arewa, daga nan kuma kudu; babu wata dabbar da ke iya tsayawa a gabansa. Babu waninsu da ke iya kuɓuto da wani daga hannunsa. Yana yin abin da ya ga dama, ya kuma zama babba.
\s5
\v 5 Yayin da nake tunani game da wannan, sai na ga bunsuru ya fito daga yamma, wanda ya tafi cikin sararin dukkan duniya, yana gudu da sauri, ya yi kamar baya taɓa ƙasa. Bunsurun yana da babban ƙaho a tsakanin idanunsa.
\v 6 Ya zo wurin ragon mai ƙahonni biyu - naga ragon yana tsayawa a bakin rafin - bunsurun kuwa ya ruga wurin ragon cikin matsanancin fushi.
\s5
\v 7 Na ga bunsurun ya zo kusa da ragon. Yana cikin fushi sosai da ragon, sai kuma ya tunkuyi ragon ya ɓalle masa ƙahonnin biyu. Ragon kuwa bai da ƙarfin tsayawa a gabansa. Bunsurun ya fyaɗa shi ƙasa ya take shi. Babu wani da ke iya kuɓuto da ragon daga ikonsa.
\v 8 Sai bunsurun ya zama mai girma sosai. Amma da ya zama mai ƙarfi, sai babban ƙahon ya ɓalle, a gurbinsa kuwa ƙahonni manya huɗu suka fito suka fuskanci kusurwoyin iskoki huɗu na sammai.
\s5
\v 9 Daga kan ɗaya daga cikin su wani ƙahon ya tsiro, da farko dai ƙarami ne, amma ya zama babba sosai a kudu, a gabas, a kuma ƙasa mai kyau.
\v 10 Ya yi girma sosai har ya shiga yaƙi da mayaƙan sama. Waɗansu daga cikin mayaƙan da waɗansu daga cikin taurarin aka watso su ƙasa cikin duniya, ya kuma tattake su.
\s5
\v 11 Ya maida kansa ya zama da girma kamar shugaban mayaƙan. Ya ɗauke baiko na ƙonawa da aka saba yi, wurin haikalinsa kuma aka gurɓata shi.
\v 12 Saboda tawaye za a miƙa mayaƙan ga ƙahon bunsurun, kuma za a tsai da baikon ƙonawa. Ƙahon zai watsar da gaskiya ƙasa, zai kuma yi nasara cikin dukkan abin da ya yi.
\s5
\v 13 Sai na ji wani mai tsarki na magana wani kuma mai tsarkin na amsa masa, "Har yaushe waɗannan abubuwa za su kasance, wannan wahayin game da baikon ƙonawa, zunubin da ya kawo rusarwa, miƙawar haikalin, da kuma tattakawar mayaƙan sama?"
\v 14 Ya ce mani, "Za su kasance har yamma-yamma da safiya-safiya 2,300. Bayan wannan za a maido da haikalin dai-dai."
\s5
\v 15 Lokacin da ni, Daniyel, na ga wahayin, na yi ƙoƙari in fahimce shi. Sai ga wani ya tsaya a gabana mai kamannin mutum.
\v 16 Sai na ji muryar mutum na kira daga tsakiyar bakin Rafin Ulai. Ya ce, "Jibra'il, ka taimaki mutumin nan ya fahimci wahayin."
\v 17 Sai ya zo kusa da inda na tsaya. Da ya zo, sai na tsorata na rusuna ƙasa. Ya ce mani, "Ka fahimta, ɗan mutum, wahayin domin lokacin ƙarshe ne."
\s5
\v 18 Da ya yi mani magana, sai na faɗa cikin barci mai nauyi da fuskata a ƙasa. Daga nan ya taɓa ni ya sa na miƙe a tsaye.
\v 19 Ya ce, "Duba, zan nuna maka abin da zai faru daga bisani a lokacin hasala, saboda wahayin ya shafi zaɓaɓɓen lokacin ƙarshe.
\s5
\v 20 Game da ragon da ka gani, wanda ke da ƙahonni biyu - sune sarakunan Mediya da Fashiya.
\v 21 Bunsurun shi ne sarkin Girka. Babban ƙahon tsakanin idanunsa shi ne sarkin farko.
\s5
\v 22 Game da ƙahon da ya ɓalle kuwa, wanda a gurabunsa huɗu kuma suka taso - masarautai huɗu ne za su taso daga al'ummarsa, amma bada babban ikonsa ba.
\v 23 A ƙarshen lokacin waɗannan masarautai, lokacin da masu kurakurai suka ƙure iyakarsu, wani sarki marar sakin fuska, mai basira sosai, zai taso.
\s5
\v 24 Ikonsa zai zama babba - amma ba da ikonsa ba. Zai zama da ban mamaki cikin abin da ya ke rusarwa; zai aikata ya kuma yi nasara. Zai lalatar da manyan mutane, mutane daga cikin tsarkakan.
\v 25 Da dabararsa zai sa yaudara ta yi nasara a hannunsa. Zai zama babba a cikin tunaninsa. Kamar yadda aka zata zai lalatar da mutane da yawa. Zai kuma yi tsayayya da Sarkin sarakuna, za a kuma karya shi, amma ba da hannun mutum ba.
\s5
\v 26 Wahayi game da yammaci da safiya da aka faɗa gaskiya ne. Amma ka rufe wahayin, gama yana magana ne akan kwanaki masu yawa nan gaba."
\s5
\v 27 Daga nan ni, Daniyel, aka sha ƙarfina na kwanta da kasala har kwanaki da yawa. Daga nan na tashi, na kuma ci gaba da hidimomin sarki. Amma na razana game da wahayin, babu kuma wani wanda ya fahimce shi.
\s5
\c 9
\cl Sura 9
\p
\v 1 Dariyos ɗan Ahazurus ne, daga zuriyar Medeyawa. Ahazurus ne aka naɗa sarki a dukkan ƙasar Babiloniyawa.
\v 2 To a shekara ta farko ta mulkin Dariyos ni, Daniyel, ina binciken litattafai da ke ɗauke da maganar Yahweh, maganar da tazo wa Irmiya annabi. Sai na lura za ayi shekaru saba'in har watsarwar Yerusalem ta kai ƙarshe.
\s5
\v 3 Sai na juya fuskata ga Ubangiji Allah, na biɗe shi cikin addu'a da roƙe-roƙe, tare da azumi, ina sanye da tsumma, ina zaune kuma cikin toka.
\v 4 Nayi addu'a ga Yahweh Allahna, na kuma furta zunubanmu. Na ce, "Ina roƙon ka, Ubangiji - kai ne Allah Mai Girma Mai Ban mamaki - kai ne mai riƙe alƙawari kana kuma da aminci da ƙaunar masu ƙaunarka suna kuma kiyaye dokokinka.
\s5
\v 5 Mun yi zunubi kuma mun yi abin da ba dai-dai ba. Mun aikata mugunta kuma mun kangare, mun kauce daga umarnanka da dokokinka.
\v 6 Ba mu saurari bayinka annabawa ba waɗanda suka yi magana cikin sunanka ga sarakunanmu, da shugabanninmu, da ubanninmu, da kuma dukkan mutanen ƙasar.
\s5
\v 7 A gare ka, Ubangiji, adalci ya tabbata. Ko da ya ke, a gare mu yau, kunya ce ta tabbata a fuskokinmu-ga mutanen Yahuda, da mazauna Yerusalem, da kuma dukkan mutanen Isra'ila. Wannan ya haɗa da waɗanda ke kusa da waɗanda ke nesa a cikin dukkan ƙasashen da ka warwatsa su. Wannan ya zama haka saboda babban tawayen da muka yi maka.
\v 8 A gare mu, Yahweh, kunya a fuskokinmu ta tabbata-ga sarakunanmu, ga shugabanninmu, ga kuma ubanninmu - saboda mun yi maka zunubi.
\s5
\v 9 Jinƙai da gafartawa sun tabbata ga Ubangiji Allahnmu, gama mun yi maka tawaye.
\v 10 Ba mu yi biyayya ga muryar Yahweh Allahnmu ba ta wurin tafiya bisa ga shari'unsa waɗanda ya ba mu ta wurin bayinsa annabawa ba.
\v 11 Dukkan Isra'ila sun karya shari'arka su ka juya gefe ɗaya, suka ƙi biyayya da muryarka. La'ana da rantsuwar da aka rubuta cikin shari'ar Musa, bawan Allah, an zubo ta a kanmu, gama mun yi masa zunubi.
\s5
\v 12 Yahweh ya tabbatar da maganganun da ya furta game da mu da kuma masu mulki a kanmu, ta wurin kawo babban bala'i a kanmu. Gama a ƙarƙashin sama dukka babu wani abu da za a iya kwatantawa da abin da a kayi wa Yerusalem.
\v 13 Kamar yadda aka rubuta a shari'ar Musa, duk wannan bala'i ya sauka akan mu duk da haka ba mu roƙi jinƙai ba daga wurin Yahweh Allahnmu ta wurin kaucewa daga laifuffukanmu da mai da hankali ga gaskiyarka.
\v 14 Saboda haka Yahweh ya ajiye bala'i a shirye ya kuma kawo shi a kanmu, gama Yahweh Allahnmu mai adalci ne cikin dukkan abin da ya yi, duk da haka ba mu yi biyayya da muryarsa ba.
\s5
\v 15 Yanzu, Ubangiji Allahnmu, ka fito da mutanenka daga ƙasar Masar da hannu mai iko, ka yi wa kanka sanannen suna, kamar yadda ya ke a yau. Amma duk da haka mun yi zunubi; mun yi abubuwan mugunta.
\v 16 Ubangiji, domin dukkan ayyukanka na adalci, bari fushinka da hasalarka su kawu daga birninka Yerusalem, tsauninka mai tsarki. Saboda zunubanmu, saboda kuma laifuffukan ubanninmu, Yerusalem da mutanenka sun zama abin ba'a ga dukkan waɗanda ke kewaye da mu.
\s5
\v 17 Yanzu, Allahnmu, ka saurari addu'ar bawanka da roƙe-roƙensa domin jinƙai; Ubangiji, ka sa fuskarka ta haskaka akan haikalinka da ya zama kufai.
\v 18 Allahna, ka buɗe kunnuwanka ka saurara; ka buɗe idanunka ka duba. Mun wulaƙantu; kalli birnin da ake kira da sunanka. Ba muna roƙon taimakonka ba ne saboda adalcinmu, amma saboda jinƙanka mai girma.
\v 19 Ubangiji, ka saurara! Ubangiji, ka gafarta! Ubangiji, ka kula ka ɗauki mataki! Saboda kai, kada ka yi jinkiri, Allahna, saboda birninka da kuma mutanenka ana kiran su da sunanka."
\s5
\v 20 Yayin da na ke magana - ina addu'a da furta zunubina da zunubin mutanena Isra'ila, ina kuma gabatar da roƙe-roƙena a gaban Yahweh Allahna a madadin dutsen Allah mai tsarki -
\v 21 yayin da nake addu'a, mutumin nan Jibra'il, wanda na gani a wahayin da farko, ya taso zuwa wurina da gaggawa, a lokacin hadayar maraice.
\s5
\v 22 Ya ba ni fahimi ya kuma ce mani, "Daniyel, yanzu na zo in ba ka masaniya da fahimta.
\v 23 Da ka fara roƙo domin jinƙai, an bayar da umarni na kuma zo in faɗa maka amsar, gama an ƙaunace ka sosai. Domin haka ka yi la'akari da wannan magana ka fahimci wahayin.
\s5
\v 24 Bakwai-bakwai sau saba'in na shekaru aka zartar domin mutanenka da birninka mai tsarki domin a kawo ƙarshen laifofi a kuma kawo ƙarshen zunubi, a yi kaffara domin mugunta, a kuma kawo madawwamin adalci, a kuma aiwatar da wahayin da anabcin, a kuma keɓe wuri mafi tsarki.
\v 25 Ka sani kuma ka fahimci cewa daga zartar da umarnin maidowa da sake ginin Yerusalem har ya zuwan shafaffen nan (wanda za ya zama shugaba), za a sami bakwai-bakwai sau bakwai da kuma bakwai sittin da biyu. Za a sake gina Yerusalem da tituna da ramin ganuwa, duk da cewa lokutan tsanani ne.
\s5
\v 26 Bayan bakwai-bakwai sittin da biyu na shekaru, za a rugurguza shafaffen zai zama kuma zama ba komai. Mayaƙan shugaba mai zuwa za su rugurguza birnin da kuma wuri mai tsarki. Ƙarshen shi zai zo da ambaliya, za a kuma yi yaƙi har zuwa ƙarshe. An zartar da abubuwan ban ƙyama.
\s5
\v 27 Zai tabbatar da alƙawari da mutane da yawa na bakwai ɗaya. A tsakiyar bakwai ɗin zai kawo ƙarshen hadaya da baiko. A tsakiyar haramtattun al'amura wani mai hallakarwa zai zo. Cikakkken ƙarshe da rusarwa aka zartar da za a zubo akan wanda ya kawo hallakarwar."
\s5
\c 10
\cl Sura 10
\p
\v 1 A cikin shekara ta uku ta Sairus sarkin Fasiya, an bayyana wa Daniyel wani saƙo, wanda kuma ake kira Beltishazza. Wannan saƙon gaskiya ne. Game da babban yaƙi ne. Daniyel ya gane saƙon ya kuma sami fahimta daga wahayin
\s5
\v 2 A cikin waɗannan kwanaki ni, Daniyel ina cikin makoki har sati uku.
\v 3 Ban ci abincin da nake marmari ba, ban ci nama ba, ban sha ruwan inabi ba, ban kuma shafe kaina da mai ba har sai da mako uku ɗin suka cika.
\s5
\v 4 A rana ta ashirin da huɗu ga watan fari, lokacin da nake bakin babban kogi (wato Tigris),
\v 5 Sai Na duba sama sai ga mutum saye cikin linin, ƙugunsa na ɗaure da ɗammara na tsattsarkar zinariya daga Ufaz.
\v 6 Jikinsa na kama da tofaz, fuskarsa tana kamar walƙiya. Idanunsa kamar fitilu na wuta, ƙafafunsa da hannuwan sa kamar gogagiyar tagulla. Muryar kalmominsa tana kama da muryar babban taro.
\s5
\v 7 Ni, Daniyel, kaɗai na ga wahayin, gama mutanen da ke tare da ni ba su ga wahayin ba. Duk da haka, babban tsoro ya sauko masu, suka ruga don su ɓoye kansu.
\v 8 Ni kaɗai aka bari sai na ga wannan babban wahayin. Babu sauran ƙarfi da ya rage a cikina; bayyanata mai haske ta juya ta za ma kallon lalatarwa, ba sauran ƙarfi da ya rage a cikina.
\v 9 Daga nan sai na ji kalmominsa - da na ji su, sai na faɗi kan fuskata cikin barci mai nauyi da fuskata a ƙasa.
\s5
\v 10 Sai hannu ya taɓa ni, ya sa jikina ya yi ta rawa a cikin gwiwoyina da dantsen hannuwana.
\v 11 Mala'ika ya ce mani, "Daniyel, ƙaunataccen mutum na ƙwarai, Ka fahimci maganar da nake faɗa maka. Ka tashi tsaye, gama an aiko ni wurin ka." Sa'ad da ya faɗa mani wannan saƙon, na miƙe tsaye, ina rawar jiki.
\s5
\v 12 Daga nan sai ya ce mani, "Kada ka ji tsoro, Daniyel. Tun ran da ka fara ƙwallafa ranka ka fahimta kuma ka ƙasƙantar da kanka gaban Allahnka, an ji maganganunka, nima na zo ne saboda maganganunka.
\v 13 Sarkin mulkin Fasiya ya yi mani tsayayya, an ajiye ni a can tare da sarakunan Fasiya har kwanaki a shirin da ɗaya. Amma Makyal, ɗaya daga cikin manyan sarakuna, ya zo domin ya taimake ni.
\s5
\v 14 Yanzu na zo in taimake ka fahimtar abin da zai faru da mutanenka a kwanakin ƙarshe. Gama wahayin domin kwanakin da ba su zo ba ne tukuna."
\v 15 Lokacin da ya ke magana da ni yana morar waɗannan kalmomin, sai na juya fuskata wajen ƙasa ban iya yin magana ba.
\s5
\v 16 Wani mai kama da 'ya'ya maza na mutum ya taɓa laɓunana; sai na buɗe bakina na yi magana da shi wanda ke tsaye a gabana. "Ya shugabana, I na cikin tsanani saboda wahayin nan; Ba ni da sauran ƙarfi.
\v 17 Ni bawanka ne. Ta ya ya zan yi magana da shugabana? Gama ba ni da ƙarfi, kuma ba sauran numfashin da ya ragu a cikina."
\s5
\v 18 Har yanzu sai shi mai bayyana irin ta mutum ya taɓa ni ya ƙarfafa ni.
\v 19 Ya ce, "Kada ka ji tsoro, ƙaunataccen mutum na ƙwarai, Salama a gareka! Ka yi ƙarfin hali yanzu, ka yi ƙarfin hali!" Lokacin da ya ke magana da ni, Na sami ƙarfi, Na ce, "Bari shugabana ya yi magana, gama ka ƙarfafa ni."
\s5
\v 20 Ya ce, "Ko ka san dalilin da ya sa na zo gare ka? Ba da jimawa zan dawo in yaƙi sarkin Fasiya. Idan na tafi, sarkin Girka zai zo.
\v 21 Amma zan faɗa maka abin da a ka rubuta cikin Littafin Gaskiya. Ba wanda ya nuna kansa cewa yana da ƙarfi tare da ni gãba da su, sai Makyal sarkinku."
\s5
\c 11
\cl Sura 11
\p
\v 1 Cikin shekara ta fari ta Dariyos Bamedeya, ni da kaina na zo domin in goyi baya in kuma kãre Makyal.
\v 2 Yanzu kuma zan bayyana maka gaskiya. Sarakuna uku zasu tashi daga cikin Fasiya na huɗun zai fi sauran wadata nesa. Yayin da ya sami iko ta wurin wadatarsa, zai zuga mutane su tayarwa mulkin Girka.
\s5
\v 3 Sarki mai girma zai tashi wanda zai yi mulkin masarauta mai girma, zai kuma aikata bisa ga yadda ya so.
\v 4 Sa'ad da ya tashi sama, mulkinsa zai karye za a raba su wajen iskoki huɗu na sama, amma ban da zuriyarsa, ba kuma zai zama da iko kamar lokacin da ya ke mulki ba. Gama za a tunɓuke mulkinsa a raba shi ga waɗansu ba ga zuriyarsa ba.
\s5
\v 5 Sarkin kudu zai zama da ƙarfi, amma ɗaya daga cikin jarumawansa zai fi shi ƙarfi zai yi mulkin masarautarsa da babban iko.
\v 6 Bayan 'yan shekaru idan lokaci ya yi, za su yi ƙawance. Ɗiyar sarkin kudu za ta zo wurin sarkin arewa domin tabbatar da yarjejiniyarsu. Amma ba za ta riƙe da ƙarfin hanunta ba shi kuwa ba zai tsaya ba ko 'ya'yansa. Za a yãshe ta - tare da waɗanda suka kawo ta, da mahaifinta, da shi wanda ya goyi bayanta a waɗancan kwanaki.
\s5
\v 7 Amma reshe daga cikin sauyoyinta zai tashi a maimakonta. Zai kai wa rundunar hari ya shiga sansanin sarkin Arewa. Zai yaƙe su, kuma zai yi nasara da su.
\v 8 Za ya ɗauke su ya kai su Masar bauta. allolinsu da siffofinsu na zubi tare da kyawawan kayansu na azurfa da na zinariya. Har waɗansu shekaru zai janye da ga sarkin Arewa.
\v 9 Daga nan sarkin Arewa zai mamaye daular sarkin Kudu, amma zai janye ya koma ƙasarsa.
\s5
\v 10 'Ya'yansa za su yi shiri su kuma tara babbar rundunar yaƙi. Za su ci gaba da zuwa su yi ambaliyar kowanne abu; za su ratsa ta duk hanyar zuwa kagararsa.
\s5
\v 11 Daga nan sarkin Kudu zai ji haushi ƙwarai; zai je ya yi yaƙi da shi, wato sarkin Arewa. Sarkin Arewa zai tara manyan mayaƙa, amma za a bayar da rundunar a cikin hanunsa.
\v 12 Za a kwashe rundunar, zuciyar sarkin kudu kuma za ta ɗaukaka, zai sa dubbun-dubbai su faɗi amma ba zai yi nasara ba.
\s5
\v 13 Daga nan sarkin Arewa zai tãda wata rundunar, da suka fi ta fari girma. Bayan waɗansu shekaru, lallai sarkin Arewa zai zo da babbar runduna waɗanda sun tănaji kayayyaki masu yawa.
\s5
\v 14 Cikin waɗancan lokatai da yawa za su ṭashi gãba da sarkin kudu. 'Yan tada zaune tsaye daga cikin mutanenka za su shirya kansu domin su cika wahayin, amma za su faɗi.
\s5
\v 15 Sarkin Arewa zai zo, zai zuba ƙasa kewaye domin yin matakalu, ya kuma ci birni tare da sansanonin. Ko zaɓaɓɓun sojojinsu. Ba su da sauran karfin tsayawa.
\v 16 Maimakon haka, shi wanda ya zo zai aikata bisa ga manufofinsa gãba da shi; Ba wanda zai tsaya cikin hanyarsa. Zai tsaya cikin ƙasa mai kyau, hallakarwa kuwa zata kasance cikin hanunsa.
\s5
\v 17 Sarkin Arewa zai ƙudurta ya zo da dukkan ƙarfin mulkinsa, tare da shi kuma zai zama akwai yarjejeniya da sarkin Kudu. Zai ba shi 'ya mace ya aura domin ya lalata mulkin Kudu. Amma dabarar ba za ta taimake shi ba ba kuwa zai yi nasara ba.
\v 18 Bayan wannan, sarkin Arewa zai maida hankali ga ƙasashen bakin teku zai kama da yawa daga cikin su. Amma wani Jarumi zai kawo ƙarshen girmankansa zai sa girmankansa ya koma kansa.
\v 19 Sa'annan zai mai da hankalinsa ga sansanoni na ƙasarsa, amma zai yi tuntuɓe ya faɗi; ba za a ƙara ganinsa ba.
\s5
\v 20 Amma wani zai tashi a madadinsa zai sa mai karɓar haraji ya ratsa saboda darajar mulkinsa. Amma cikin kwanaki masu zuwa za a karya shi, ba cikin fushi ko cikin yaƙi ba.
\v 21 A maimakonsa kuma wani zai tashi mutum abin raini wanda mutane ba za su ba shi darajar sarauta ba; zai zo ba tsammani zai karɓi mulki ta wurin yaudara.
\v 22 Za a share rundunar yaƙi kamar ambaliya a gabansa. Dukan su da rundunar yaƙi da shugaban alƙawari za a hallakar da su.
\s5
\v 23 Daga lokacin da a ka yi ƙawance da shi, zai yi aikin yaudara; da kimanin mutane 'yan kaɗan zai yi ƙarfi.
\v 24 Ba tare da gargaɗi ba zai zo cikin waɗansu lardunan da suka fi wadata, zai yi abin da mahaifinsa ko kakansa bai yi ba. Zai baza wa mabiyansa ganima, ganimar yaƙi, da dukiya. Zai shirya juyar da sansanoni, amma na ɗan lokaci ne.
\s5
\v 25 Zai ta da ikonsa da zuciyarsa gãba da sarkin Kudu da babbar rundunar yaƙi. Sarkin Kudu kuma zai ja dagar yaƙi, da babbar rundunar yaƙi, ba zai iya tsayawa ba saboda waɗansu zasu shirya masa makirci.
\v 26 Har su da suke cin abincisa mai kyau za su yi ƙoƙarin hallaka shi. Rundunarsa za'a share su kamar ambaliya, da yawan su zasu faɗi kisassu.
\v 27 Dukansu sarakunan nan, da zukatansu da ke nufin mugunta gãba da juna, za su zauna a teburi ɗaya suna yiwa juna ƙarya, amma ba za ta zama da amfani ba. Gama matuƙa za ta zo a ƙayadadden lokaci.
\s5
\v 28 Sa'an nan sarkin Arewa zai koma ƙasarsa da dukiya mai yawa, ya sa zuciyarsa ta yi gãba da alƙawari mai tsarki. Zai aikata abin da ya so daga nan ya koma ƙasar sa.
\s5
\v 29 A cikin sanyayyen lokaci zai sake dawowa gaba da Kudu. Amma a wannan lokacin ba zai zama kamar na farin ba.
\v 30 Gama jiragen Kittim za su kawo masa hari, zai tsorata kuma ya koma baya. Zai ji haushin alƙawari mai tsarki, zai nuna amincewa ga waɗanda suka watsar da alƙawari mai tsarki.
\s5
\v 31 Dakarunsa zasu tashi su tozartar da kagarun wuri mai tsarki. Zasu kawar da baikon ƙonawa na kullum, za kuma su kafa abin banƙyama da zai sa hallakarwa.
\v 32 Gare su da suke aikata mugunta saɓanin alƙawari, zai yaudare su ya ɓata su. Amma mutanen da suka san Allahnsu zasu yi ƙarfi su kuma ɗauki mataki.
\s5
\v 33 Su da ke da hikima cikin mutane zasu sa da yawa su fahimta. Amma zasu faɗi ta kaifin takobi da harshen wuta; zasu faɗi cikin bauta da yi masu fashi kwanaki da yawa.
\v 34 Cikin faɗuwarsu, za a taimake su da taimako ƙanƙane. Cikin munafunci da yawa za su haɗa kai da su.
\v 35 Daga cikin masu hikima waɗansu zasu faɗi domin a tace su, a wanke su, a tsarkake su, har kwanakin ƙarshe. Amma lokacin da aka ƙayyade bai yi ba tukuna.
\s5
\v 36 Sarki zai aikata bisa ga son ransa. zai ɗaukaka kansa ya maida kansa babba bisan kowanne allah. Zai faɗi abubuwan ban mamaki gãba da Allahn alloli, zai yi nasara har lokacin da fushi ya cika. Gama abin da aka wajabta zai faru.
\v 37 Ba zai kula da allolin kakanninsa ba ko allahn da mata ke marmari. Ba zai kula da kowanne allah ba. Gama zai maida kansa babba a bisa kowannen su.
\s5
\v 38 Maimakon waɗannan, zai girmama allahn ganuwoyi. Shi ne allahn da ubanninsa ba su sani ba zai girmama shi da zinariya da azurfa da duwatsu masu daraja da kyaututtuka masu amfani.
\v 39 Zai kai hari ga ganuwoyi masu ƙarfi ta wurin taimakon baƙon allah. Ga duk wanda ya yarda da shi, zai ƙara mai ɗaukaka. Zai maishe su masu mulkin mutane da yawa. Zai raba masu ƙasa a matsayin lada.
\s5
\v 40 A kwanakin ƙarshe kuma sarkin Kudu zai kai hari. Sarkin Arewa kuma zai tasar masa da karusan yaƙi da mahaya dawakai, da jirage da yawa. Zai shiga cikin ƙasashe, ya kwarara, ya ratsa.
\v 41 Zai shiga cikin ƙasa mai kyau dubbun-dubban Isra'ilawa za su faɗi. Amma waɗannan zasu tsira daga hanunsa: Idom, Mowab da sauran mutanen Amon.
\s5
\v 42 Zai ƙara miƙa hanunsa cikin ƙasashen; ƙasar Masar ba za ta tsira ba,
\v 43 Zai sami iko bisa kan taskar zinariya da azurfa da kan dukkan wadatar Masar; Libiyawa da Kushawa zasu bi tafin sawayensa.
\s5
\v 44 Amma labari daga gabas da arewa zai tsoratar da shi, zai fita da babbar hasala domin ya hallakar gaba ɗaya ya kuma keɓe da yawa domin hallaka.
\v 45 Zai kafa rumfar fãdarsa tsakanin teku da kyakkyawan dutse mai tsarki. Zai kawo ƙarshen sa, ba kuwa mai taimakon sa.
\s5
\c 12
\cl Sura 12
\p
\v 1 "A wannan lokaci Makyal, babban yarima mai kare mutanenka, zai tashi. Za a yi kwanakin wahala irin waɗanda ba a taɓa yi ba tun da aka yi kowacce al'umma har ya zuwa lokacin nan. A lokacin nan za a ceci mutanenka, duk wanda aka iske sunansa a cikin littafi.
\v 2 Da yawa waɗanda suke barci cikin turɓayar ƙasa za su tashi, waɗansu zuwa rai na har abada waɗansu kuma zu wa kunya da ƙasƙanci marar matuƙa.
\s5
\v 3 Waɗanda suke da hikima zasu haskaka kamar walƙiya ta sararin sama, waɗanda suka juya mutane da yawa zuwa ga adalci za su haskaka kamar taurari har abada abadin.
\v 4 Amma kai Daniyel, ka kulle maganganun nan; ka hatimce littafin har sai kwanakin ƙarshe. Da yawa zasu yi ta gudu nan da can, ilimi kuma zai ƙaru".
\s5
\v 5 Sa'an nan, ni, Daniyel, na duba, akwai waɗansu biyu suna tsaye. Ɗaya yana tsaye a bakin kogi ɗaya kuma yana tsaye a bakin ƙetaren wancan kogin.
\v 6 Ɗaya daga cikin su ya ce da mutumin da ke saye da linin, wanda ya ke kan magudanar kogin ya ce, "Har yaushe zai zama ƙarshen waɗannan al'amura na al'ajabi?"
\s5
\v 7 Na ji mutumin da ke sanye da linin, wanda ya ke bisa magudanar kogin - ya ɗaga hanunsa na dama da na hagu sama ya yi rantsuwa ga shi wanda ya ke rayuwa har abada za a yi lokaci da lokatai, da rabin lokaci. Sa'ad da ikon mutane masu tsarki ya karye a ƙarshe, dukkan waɗannan al'amura zasu cika.
\s5
\v 8 Na ji amma ban fahimta ba. Sai na tambaya, "Ya shugabana, ina mafitar waɗannan al'amura?"
\v 9 Ya ce, "Tafi yi tafiyarka, Daniyel, gama an kulle maganganun nan an hatimce su har sai kwanakin ƙarshe.
\s5
\v 10 Waɗansu da yawa zasu tsarkaka, tsabtattu, su zama tatattu, amma miyagu za su aikata mugunta. Babu wani a cikin mugaye da zai fahimta, amma masu hikima zasu fahimta.
\v 11 Daga lokacin da aka kawar da baiko na ƙonawa aka kuma kafa abin ƙyama mai sa hallakarwa, za'a yi kwanaki 1,290.
\s5
\v 12 Mai albarka ne shi wanda ya jira har ƙarshen kwanaki 1,335.
\v 13 Dole ka yi tafiyarka har ƙarshen, kuma za ka huta. Za ka tashi a cikin wurin da aka keɓe maka, a ƙarshen kwanaki."